Shurin Fatalwa Hausa Novel Part 1
[17/10, 11:55 am] +234 703 811 7298: 🕷️🕷️ *SHURIN FATALWA* 🕷️🕷️
🐲🐲🐲🐲🐲🐲🐲
🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️
*Muntasir Shehu*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*Da saunan Allah mai Rahama mai jin ƙai*
*FAƊAKARWA*
*Wannan labari bai faru a gaske ba, an kirkire shi ne don nishadin masu karatu, don haka duk abin da ya zo daidai da rayuwar wani to arashi ne*
*GARIN BABBAR KUKA*
Ba wani babban gari ba ne, duka faɗinsa ba zai wuje awon murabba’in kilo mita ɗari da wani abu ba.
A can ƙarshen garin akwai wani tsohon shuri wanda ‘yan garin suke cewa ya kai a ƙalla shekaru talatin da biyar zuwa arba’in da ginuwa, sai dai duk tsawon waɗannan shekaru cikin fargabar dosar wannan shuri ake yi, domin kuwa da zarar an ce rana ta doshi yamma tana shirin yada zango to za a fara jiyo muryar mace na fitowa daga cikin shurin tana gunjin kuka, tsawon wannan shekaru abin da ke faruwa kenan.
Dalili kenan da yake sanyawa duk wanda ya taso a garin bayan samuwar shurin ake tsoratar da shi kar ya raɓi wannan shuri domin kuwa a baya an sha kwantata zuwa don a gano ta inda gunjin kukan yake fitowa da kuma wadda take yi, sai dai duk wanda ya yi kuskuren yin hakan to kuwa sai wani abu ya faru da shi, ko dai mutum ya haukace ya dinga zabure-zabure yana tsorata ko kuma ya rasa wani sashe na halittar jikinsa.
Ganin abin ba na wasa ba ne ya sanya Maigari ya bayar da umarni aka samu jibga-jibgan jajayen ƙosassun duwatsun marmara aka girke su a ƙasan shurin aka zagaye shi tare da sanya alamar akwai matsala in aka tunkari wannan shuri da aka sanya wa suna SHURIN FATALWA, tuni mutane sun gama yin amanna cewa asalin gurin tsohon kabari ne shuri ya fito a kai, to wataƙila ko wadda take cikin kabarin ta bar duniya da wani babban buri ne ya sanya take son yin fatalwa ta dawo duniya amma ta kasa samun damar haka!
Alamar da aka sanya a gurin ita ta sanya ko baƙi aka yi ba sa dosar gurin, an sha zuwa daga birni don a rushe shurin Maigari na hanawa, ya ce “Wannan shuri amanar ƙasa ne, don haka ko bayan raina ban amince a rushe shi ba! Babu wani da zai fito daga tsatsona ya gaji kujerata kuma yana gani a rushe wannan shuri… Babu ruwanmu da shi, babu ruwanmu da abin da yake cikinshi, saboda haka kar mu taɓa in muna son mu zauna lafiya!”
Wannan ita ce maganar Maigari.
A cikin wannan garin dai akwai wasu taƙadiran yara waɗanda la-shakka za a iya kiran su da magadan ifiritai ko kuma ƙannen shaiɗan a wajen rashin ji.
Rana ba za ta taɓa fitowa ta faɗi ba tare da sun yi ta’adi a cikin garin nan ba, su ne kame kajin mutane su tafi bayan gari su yanke su gasa su ci su bar ragowar a nan, hakan nan sai shiga gidan mutane kamar abin arziƙi sai korewa mutum garken awakinsa su kaɗa su daji wanda in ba an yi babbar sa’a ba shikenan sun mila.
Manoma ma dai ba su tsira daga sharrin waɗannan taƙadiran yara ba, don kuwa ɓarnar da suke yi a cikin gonakin mutane ta fi wadda shanun makiyaya ke yi.
Maigari ya sha sanyawa a garƙame su a turu, amma sai sun yadda suka yi suka tsere, har cikin gari mai gari ya aika aka zo da ‘yansanda aka tafi da su aka yi musu mugun duka, amma dai yaran nan kamar darasi aka je aka ƙaro musu, dole aka haƙura aka sanya musu idanu.
A cikin wani dare waɗannan matasan yara guda biyu, Kasimu da Habu sun gama tsara yadda za su saci jiki da asubar fari su je su rushe wannan shuri wanda suka daɗe suna kai masa farmaki ba sa samun sa’a sakamakon hana su da ake yi, to a yau dai sun sauya shawara da asubar fari za su tafi su rushe wannan matsiyacin shurin su ga uwar da take ciki da ake ta gindaya musu sharuɗai a kansa, in suka rushe shikenan kowa ma ya huta.
Wannan shi ne tunaninsu.
Kasimu ne ya fara fitowa daga shi sai rigarsa ‘yar shara wadda ta kanannaɗe ta zama kamar ja-ni-talau saboda wahala, wandon jikinsa a da dogo ne, amma yanzu shi ma ya tattare ya dawo iya ƙasan gwiwa kawai.
Wata jibgegiyar diga ce riƙe a hannunsa ɗaya, ɗayan kuma fankaceciyar fartanya sai wata tsohuwa cocila da ya yi mata mariƙa a tsakanin haƙwarensa.
Tafiyar sanɗa yake yi har ya ci nasarar ficewa daga gidansu, yana fita shi ma Habu na fitowa, kusan dai duk samma-tilo da shi da Kasimun.
Babu ɓata lokaci suka rankaya zuwa bayan gari, bisa sa’a ba su ci karo da ko mutum ɗaya ba balle ya zame musu shamakin da zai kawo musu cikas a aikinsu ba har suka isa.
Abin mamaki yau shurin ya yi tsit babu wannan gunjin kuka wanda a ƙa’ida in ya fara tun goshin magariba sai rana ta fito washegari yake dainawa, ko kukan ƙwaro ɗaya babu balle na mutum.
Ba su ɓata lokaci ba don sun gama tsara komai suka fara ture tiƙa-tiƙan marmarorin nan gefe suka samar wa kansu hanya zuwa inda shuri yake.
Bayan sun kunna tocila suka ajiye gefe suka saɓi kayan aiki suka fara jibgar shurin nan ba ji ba gani.
Nan da nan ƙananan ƙwarin dake rayuwa a cikin wannan shuri suka fara gudun ceton rai, masu bakin kuka na ta fitar da amo wanda wataƙila Allah ya isa suke yi wa su Kasimu da a ce bakunansu na fitar da harafi.
Wasu lafta-laftan gafiyoyi suka fara yin fitar burtu ganin dai yaƙin na gaske ne ake yi a muhallinsu, hakan nan duk sauran halittun ƙasan shurin nan dai suka fice suna neman sabon muhalli wanda ba za a zo a tayar musu da hankali ba.
Da suka gama sauke saman shurin sai ga wani wawakeken rami ya bayyana, da saurin Kasimu ya ce wa Habu “Maza miƙo cocila mu haska mu gani.”
Da sauri Habu ya tashi ya ɗauko tocila ya haska cikin ramin, ashe ramin wata narkekiyar kububuwa ce amma an ci sa’a ta fita farautar dare, sai da ga ɗirka-ɗirkan ƙwayayenta da ta ajiye a ciki suna nan sun yi rau-rau da alamun sun kusa fashewa su zo duniya.
Ba tare da tsoro ba yaran nan suka sanya hannu suna zare ƙwayayen suna cilli da su gefe, suka ci gaba da rushe shurin, sai ga wasu irin curi guda na baƙaƙen gizo-gizo da ba su yi kama da ainahin gizo-gizo na cikin gidaje ba su ma suna fitar burtu daga ramukansu suna neman mafaka.
A daidai wannan lokaci Kasimu ya ɗaga digarsa da ƙarfi ya sauke ta tsakiyar shurin, faruwar hakan ke da wuya sai ga jini na biyo gefen digar daga ƙasa yana yin tsartuwa yana ɓata fuskar Ƙasimu.
Karon farko da Kasimu ya ji tsoro ya kama shi yadda har sai da ya zabura ya ja da baya.
Habu ya tambaya. “Mene ne ka gani?”
“Jini!”
“Jini kuma? Mutum ne a ciki?”
Suka kalli juna a tare, Kasimu ya dafe ƙugu. “Ko dai da gaske abin da ake faɗa ne cewa tsohon kabari ne nan? To amma in tsohon kabari ne ya za a yi a ce wanda yake ciki har yanzu da jini a jikinsa?”
Ba tare da shakkar komai ba Habu ya ce. “Mu cigaba da tonawa mu gani.”
Tare suka cigaba da tona gurin har suka yi rami mai zurfi wanda ya wuce iyakar tsinin da digar ta shiga amma ba su ci karo da komai ba face dai wata iska da ta tashi lokaci ɗaya ta kuma ɗauke dif a lokaci ɗaya.
A karon farko shi ma Habu ya zabura a tsorace sakamako jin wani abu ya yi fut ya shige cikin wandonsa, ya yi sauri ya haska sai ya ga ashe gizo-gizon nan ne ƙwaya ɗaya ya yi tsalle ya haye jikinsa, hannu ya sa ya kaɗe gizo-gizon ya faɗi ƙasa.
A daidai wannan lokaci ne kuma mutane suka ƙaraso gurin a kiɗime cikin matuƙar tashin hankali sakamon wannan ta’asar da taƙadiran yaran suke yi, ashe a hanyarsu ta tahowa wani tsoho ya fito zuwa yin Sallah a masallacin ƙofar gidan Maigari ya ga wucewar su, bayan an yi sallah ya faɗa shi ne aka biyo sawun su, sai dai kuma ga shi an yi fargar jaji, aikin gama ya gama!
Daga can nesa mutane suka tsaya cirko-cirko saboda tsoro an rasa wanda zai tunkari gurin, yayin da su ma su Kasimu suke tsaitsaye riƙe da kugu suna kallon mutanen.
Caraf Kasimu ya ji gizo-gizo ya faɗo jikinsa, yana ƙoƙarin kore shi sai ga wani ma ya faɗo, can sai ga wani ma ya faɗo, wani ma ya faɗo, wani ma ya kuma fadowa, ai nan da nan sai ga gizo-gizo sun gama zagaye jikin Kasimu suna cizonsa, ya fara ihun neman ceto, Habu ya matsa kusa da sauri yana ƙoƙarin karkarɗe masa, ai shi ma sai ga wasu curi guda na gizo-gizon sun rikito masa a jiki, babu kuma wanda ya ga daga inda suka fado duk da cewa gari ya fara haske.
Abu dai kamar wasa sai ga su Habu a kwance suna tumamin ihu da neman ceto amma an rasa wanda zai tunkare su, iyayensu kuwa sai ihu suke suna hanƙoron zuwa gurin ana riƙe su.
Abin mamaki cikin ƙasa da mintuna biyar gizo-gizon nan sun gama cinye naman jikinsu Habu tas ba su bar komai ba sai ƙwarangwal ɗin ƙashi fari sol tamkar ɗigon jini bai taɓa ratsa shi ba.
Akwai mutanen da a take suka dinga yanke jiki suna faɗuwa suna suma saboda tsorata da ganin wannan abu, yayin da wasu kuwa takewa suka yi da ƙafafunsu a guje cikin matuƙar kiɗima suna ihun neman agaji.
Wannan kenan!
*BABBAN ASIBITIN BIRNI, ƊAKIN AJIYAR GAWA*
Likita sanye cikin farar riga da ta rufe baƙar T-shirt ɗin jikinsa ya nufo ɗakin ajiyar gawa (matuary) tare da wasu mutane maza biyu mata biyu, matan sai rufsar kukan fita daga hayyaci suke, tuni idanunsu sun gama zama kamar jan gauta, da alamu dai sun jima suna shan kuka.
Suna isa mai gadin wajen ya buɗe musu suka kutsa kai ciki yayin da ƙirazan mutanen ke duka goma-goma, shi kuwa dai likita ko a jikinsa, inda sabo ya saba, hannu ba baƙon taɓa mazaunai ba ne.
Aka dinga buɗe musu akwatinan ajiyar gawa ɗaya bayan ɗaya suna leƙawa suna kawar da kai alamun dai ba ita suke nema ba.
Mazan ne ke iya yin namijin ƙarfi hali su leƙa, amma matan nan kuwa duk yadda suka nuna ƙwarin zuciya a farko cewa za su iya jure ganin komai sai ga shi ɗaya a cikinsu tana shiɗewa ma har tana neman suma saboda tsoro, su kansu mazan in sun leƙa wata gawar sai sun ji tamkar zuciyarsu za ta tsinko.
Ba tare da kowa ya ankare ba wani lafcecen gizo-gizo baƙi ƙirin mai garima na ban-mamaki domin kuwa ya kai girman tafin hannun irin zabga-zabgan samarin nan masu manyan gabobi har yatsun har komai, ya rarrafo da saurin sa ya yi wuf ya faɗa ɗakin, suna ta cigaba da buɗe akwatinan gawa gizo-gizon na biye da su, can sai gizo-gizon ya rarrafa ya haye jikin bango daidai saitin wata akwatin gawar da likitan ya janyo ta a daskare sai fitar da tiririn sanyi take, mutanen nan suka leƙa suka tabbatar ba ita ce gawar da suke nema ba, likitan ya yunƙura ya tura murfin akwatin zai rufe wannan gizo-gizo ya yi wuf ya faɗa ciki ba tare da kowa ya kula ba.
Wannan ita ce akwati ta ƙarshe da aka buɗe don haka likitan ya tabbatar musu to ba wannan asibitin aka kawo gawar da suke nema ba sai dai su nufi sashen.
Suka juya suka fice maigadin gurin ya mayar da ƙofa ya rufe.
Dare ya tsala sosai, wajen ƙarfe biyu da rabi maigadin mutuwaren nan har ya kwanta ya fara bacci sama-sama can sai ya fara jin wata irin iska mai kama da guguwa ta fara tashi tana fitar da sauti shuuuuuu, da sauri ya buɗe idanunsa, can ƙasa-ƙasa kuma sai ya fara jiyo kamar sautin murya na fitowa daga ɗakin ajiyar gawa, ya yi saurin yin tsaiii da ransa ya kasa kunne sosai yana saurare.
Tabbas murya ce ke fitowa daga cikin ɗakin, wata irin murya marar amo marar fasali da daɗin ji.
“Innnaaaaa sooooooo aaaaaa buɗeeeeee niiiiiii!”
“Kaaaaaaa zooooooo kaaaaaaa buɗeeeeee niiiiiii!”
Tabbas idan har ba yaudarar sa kunnuwansa ke yi ba har motsi yake jiyowa sosai a cikin ɗakin.
Wannan baƙon al’amari ne a gare shi, sama da shekaru ashirin yana aikin gadin wannan ɗaki na ajiyar gawa amma bai taɓa riskar faruwar wani abu makamancin wannan ba, in haka ne to me yake shirin faruwa?
Ya tashi da sauri ya ɗauki tocilarsa saboda babu haske a ɓangaren, an yi rashin sa’a wutar gurin ta lalace kuma ba a kammala gyarawa ba.
Ba zai ce ba ya jin tsoro ba, amma tabbas yana so ya ga me yake faruwa a cikin ɗakin don haka ya sanya mabuɗi ya buɗe ƙofar a hankali ya tura yana ɗan haska tocila kaɗan-kaɗan yana kuma yin tafiyar sanɗa har shiga ainahin tsakiyar ɗakin.
Jin ya ci karo da abu a tsaye ƙiƙam ya sanya gabansa faɗuwa da ƙarfi, da yake ba shiri ya daki abin sai da ya yi baya taga-taga zai faɗi, tocilarsa ta zame daga hannunsa ta faɗi.
Nan da nan mutumin nan ya rikice ya tsorata ainun saboda tabbas wannan abu na tsaye da bai san ko mene ne ba shi ne yake yin wata irin magana tamkar sautin daga cikin hanjin ciki yake fitowa ba ga harshe da leɓe ba.
Ya fara laluben tocila a ƙasa, bisa sa’a sai ya ci karo da ita, hannunsa na mugun rawa ya ɗauko ta ya kunna haske ya bayyana sosai.
Waiiiii Allah!!! Gawa ce dai gawar mace ga ta nan tsaye cikin ledar da ake ajiye su sai layi take idanu a rufe gashin kanta ya barbaje yana tashi sama yana yawo tamkar iskar bazara ce ke kaɗa shi, bakinta a rufe yake ruf amma kuma ga shi sautin magana na fita tana gunji tana cewa.
“Inaaaaa sooooooo in fitaaaaaa! Kaaaaaaa buuuuuudeeeeee niiiiiii!”
Da jan ɗuwawu maigadin ya fara ja da baya yana cigaba da haske-haske a ɗakin har ya hasko can ƙarshe ɗakin inda ya ga tamkar an yi faɗan jaruman indiya a gurin, domin an yi raga-raga da akwatinan gurin, wasu gwarwakin duk ga su nan a ƙasa sun faffaɗo a sandare, kenan dai ita wannan gawar dake tsaye ita ta buɗe kanta da ƙarfin tsiya ta ɓaɓɓalla komai ta fito?
Tirƙashi! Me ke faruwa ne?
Maigadi ya fara ihun neman ɗauki yana cigaba da ja da baya, tuni tocila ɗin hannunsa ta ƙara ƙwacewa ta gangara gefe.
Ganin yana ja da baya ne ya sa ita ma gawar ta fara tafiya cikin wani irin taku irin wanda in an sha giya an yi tatul an maku ake yi, ido a rufe yake don haka duk abin da ta ci karo da shi gaba take yi da shi.
Da taimakon Allah mai gadin nan ya samu ya dangana da bakin ƙofar ɗakin, sai dai wani abin tashin hankali garin gaggawar ya kamo mariƙin ƙofar ya buɗe ai sai ji ya yi tamkar an tankwabe hannun nasa an tura ƙofar da ƙarfi an rufe!
Nan take ya fara karanta dukkan addu’ar da ta zo bakinsa idonsa a runtse ganin yadda gawar ta yo kansa gadan-gadan tana shirin yin tafiyar yaji da shi!
Daga haka bai ƙara sanin abin da ya faru ba sai ta shi ya yi ya gan shi a gadon masu jinya, bakinsa kuma ya rufe ruf ya kasa magana, yana tuna abin da ya faru sai ya fara tsandara ihu yana zabura a tsorace.
*I.C.U*
A wani sashe na cikin asibitin ɓangaren bayar da kulawa ta musamman a wani ɗaki a kan gado zagaye da na’urorin tallafawa numfashi da sauran tarkacen nemo lafiya, wata takusasshiyar tsohuwa ce da duka in an cure ta za a iya zuba ta a leda Viva, gaba ɗaya fatar jikinta ta gama yin tamoji ta zagwanye tana reto a jikin kasangalalin ƙasuwasuwan jikinta.
Ko ba a faɗa ba duk wanda ya kalli wannan tsohuwa ya san ba ƙaramar jinya take sha ba, a yanzu haka likitoci ne birjik a kanta ana ta ƙoƙarin nemo nutsuwarta sakamakon ife-ife da ta fara yi tun daren jiya tana kururwar tsorata ta aka yi a daren, ta dinga fizge-fizge tana ƙoƙarin zare duk wata allura da aka liƙa a jikin takusasshiyar jijiyarta.
Faɗi take ita wallahi ba za ta ƙara kwana a ɗakin ba don ita kaɗai ta ga abin da ta gani a daren jiya, iya tsoratarwa an gama tsorata ta.
Babu wanda ya yarda da abin da take faɗa don tunani ake yi zafin ciwo ne kawai, wanda hakan ta sanya tun a daren ake ta ɗirka mata allurar bacci amma ta ƙi kama jikinta.
Alhaji Falalu sai kai wa da komowa yake a ɗimauce ya rasa inda zai sanya ransa, tunani yake yi gwara kawai ya ɗauke gyatumarsa daga wannan asibitin ya fitar da ita waje a cigaba da nema mata lafiya.
Wata juyawa da ya yi ya hango wani lafcecen gizo-gizo wanda bai taɓa ganin gizo-gizo mai girmansa ba ya taho sim-sim-sim da sauri ya doshi ɗakin da mahaifiyar tashi ke kwance.
Bai ga daga inda gizo-gizon ya fito ba kawai bayyanar sa ya gani a bakin ƙofar ɗakin, kafin ya yi wani yunƙuri kuma tuni gizo-gizon ya yi wuf ya faɗa ɗakin.
Nan da nan hankalin Alhaji Falalu ya kai ƙololuwar tashi, take ya tuna abin da tsohuwarsa ke faɗi cewa abin da ya tsorata ta a daren jiya shi ne, jin abu ya fado mata yif a kan ciki, jin abin yana da ɗan nauyi ne ya sanya ta buɗe idanunta, da ta buɗe shi ne ta yi arba da gizo-gizo baƙiƙƙirin kuma ɗirkeke kansa irin na mutane, ɗauke da wata ruɓaɓɓiyar fuska da take ta zubar da jini da tsutsotsi, gashin dake jikin solelen ƙoƙon kansa bai wuce guda biyar ba sai shegen tsayi sun miƙe suna ta reto a sama, fuskar dai fuskar namiji ce irin tsofaffin nan ma.
Nan take hankalin tsohuwa ya tashi ta sanya ƙarar da ta tayar da jikarta Asma’u da ke aikin jinyar ta.
Cikin ihun kuka tsohuwar ta dinga ɓurari. “Ma’u! Ma’u!! Zo ki cire mini, zo ki cire min tau-tau mai kan mutum! Zo ki cire mini ga shi nan zai kashe ni Ma’u! Wayyo na shiga uku na lalace zai cinye ni Ma’u!”
[17/10, 11:55 am] +234 703 811 7298: 🕷️🕷️ *SHURIN FATALWA* 🕷️🕷️
🐲🐲🐲🐲🐲🐲🐲
🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️
*Muntasir Shehu*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*2*
Asma’u ta tashi a gigice ganin yadda tsohuwar ke neman jefar da kanta daga kan gadon.
Da sauri ta isa gare ta ta daddafe ta tana ɓurarin kwaɗa wa likitoci kira.
Da dai ta ga hakan ba shi ne mafita ba ba jiyo ihunta ake ba sai ta saki tsohuwar ta nufi wajen ƙararrawar sanarwa ta dinga dannawa.
Nan da nan sai ga ma’aikatan jinya sun ɗuru a cikin ɗakin, suka taru a kan tsohuwar suka fara banka mata allurar da za ta sandarar da lakar jikinta ko ta daina zabure-zaburen da take yi.
To fa shi ne har zuwa safiya ake ta fama da ita amma allurar ta ƙi ratsa ta.
Yanzu da Alhaji Falalu ya ga wannan shirgegen gizo-gizo ya wuce cikin ɗakin ai sai shi ma ya taka da sauri ya faɗa ɗakin.
Likitocin suka juyo da sauri suka kalle shi.
“Ku yi haƙuri Doctors, gizo-gizon da ya tsorata Hajiya ne na ga ya ƙara shigowa ɗakin nan yanzu, idan ta gan shi za ta ƙara tsorata!”
Wani irin kallo suka yi masa kafin ɗaya daga cikinsu ya ce.
“Ku kwantar da hankalinku Alhaji, mun ci nasara yanzu allurar ta ratsa ta za ta sanya ta bacci yanzu… Batun wani gizo-gizo kuma ku daina, don babu wani gizo-gizo, zafin ciwo ne kawai yake gigita ta…”
“Da idona fa na ga gizo-gizon ya shigo ɗakin nan yanzun nan…”
Sai ya fara dube-dube.
Da ƙyar likitocin suka shawo kansa ya fita daga ɗakin ba don ya gamsu da cewar shi bai ga gizo-gizon da idanunsa ba.
Ita ma Asma’u cewa aka yi ta fita ta ƙyale Hajiyar ita kaɗai tun da an samu bacci ya kwashe ta.
Alhaji da ‘yar tasa Asma’u suna tsaitsaye a ƙofar ɗakin inda ta dube shi ta ce.
“Daddy ka san me?”
Ya girgiza kai. “A’a”
“Wallahi ni ma na ga gizo-gizon nan fa… Tun jiya lokacin da Hajiya ta fara ihun nan da na tashi na kunna gulof na ga wani abu baƙiƙƙirin ɗirkeke ya fita daga gudu ta window, kuma abin tabbas da gizo-gizo yake kama…”
Tuni Alhaji ya zabura. “Kin ji ba! Amma mutanen nan suna neman mayar da mu shashashai, tabbas zan ɗauke Hajiya daga asibitin nan!”
Ya zaro waya ya fara magana, yayin da ita kuma Asma’u ta buɗe ɗakin ta koma ciki, tana shiga ta hango gizo-gizo a daidai saitin fuskar Hajiya yana yi mata yawo ita kuma sai motsi take amma ta kasa komai.
Ganin shigowar ta ya sanya gizo-gizon ya zabura a guje ya bi ta taga ya fice.
Asma’u ta dafe ƙirji cikin jin tsoro, ta yi ta ‘yan maza ta ƙarasa gadon ta leƙa fuskar Hajiyar, me za ta gani?
Tamkar yadda kaji ke caccakar tuwo su yi masa huda-huda haka gizo-gizon nan ya yi wa fuskar Hajiya.
Ta ja da baya a matuƙar gigice ta tsandara ihun da ya sanya Alhaji jefar da wayar hannunsa ya faɗa ɗakin a guje.
Suka kusa gabza karo da Asma’u da ita ma ta doshi hanyar fita a ɗari da tamanin.
“Lafiya? Me ya samu Hajiya?”
“Gizo-gizo ya cinye wa Hajiya fuska Daddy! Mun shiga uku!!”
Tuni ya isa gaban gadon Hajiya, daidai lokacin ita ma ta farka daga baccin allura ta tsandara ihu sakamakon raɗaɗin zafi da ya ratsa ta, ta fara fizge-fizge.
Likitoci suka ƙara dawowa a guje cikin ɗakin, suna shigowa Alhaji ya damƙi wuyan ɗaya daga cikinsu ya hau masifa.
Da ƙyar aka raba su, Alhaji ya ce ɗauke mahaifiyarsa zai yi daga wannan asibitin ya kai ta waje, ya yi waya ma za a fara shirye-shirye.
Daga haka ya hau fincike duk wani abu da aka jona a jikin tsohuwar da take ta tumami saboda raɗaɗin da fuskarta ke yi, idanunta sun daina buɗewa.
Wani abin mamaki kuma duk wannan caccake da gizo-gizo ya yi a fuskar tata babu ko digon jini da ya fita.
Alhaji ya cicciɓe tsohuwarsa ya yi waje da ita, Asma’u ta fara tattara musu kaya.
Yana zuwa bakin mota ya kira wasu matasa suka buɗe masa motar ya sanya ta a ciki, Asma’u na ƙarasowa ta shige, ya tashi motar.
Abin da ba su sani ba kuma, Gizo-gizo dai ya laɓaɓo ya maƙale a ƙasan motar.
Suna zuwa gida aka shimfiɗe tsohuwar a daki, Alhaji ya zaro wayarsa wadda aka biyo shi da ita aka ba shi lokacin da ya tashi motarsa za su taho.
Wani likita ya kira ya zo ya duba fuskar Hajiyar, allura dai shi ma ya yi mata ta bacci, suka samu ta daina ihu.
Alhaji Falalu na zaune jigum ya haɗa hannaye biyu yana tagumi, kwatsam sai ganin gizo-gizo ya yi sim-sim-sim ya wuce a guje zuwa ɗakin da Hajiya ke kwance.
Ya zabura ya miƙe a guje ya nufi ɗakin, ya dinga dube-dube amma bai ga komai ba, ya isa ga tsohuwar tashi ya duba ta ya ga dai bacci take babu wani abu da ya faru.
Kasa fita daga ɗakin ya yi ya samu waje ya zauna ya ƙura mata idanu.
Ji ya yi daga falo Asma’u ta tsandara ihu, a gigice ya miƙe ya leƙa falon, wayam babu kowa, ya fara kiran sunan Asma’u!
Sai dai yana faɗa zai ji wata muryar ta kwaikwaye shi ta faɗi abin da ya ce.
Ya fara zazzare idanu yana so gane me yake faruwa?
Dariya ya ji an kece da ita a cikin ɗakin da Hajiya ke kwance, yana juyawa me zai gani?
Hajiya ce a tsaye a kan duga-duganta an ƙara mata tsawo tun daga sama har ƙasa kanta na taɓa saman rufin ɗakin. hannayent sun zuƙe sun zama ‘yan mitsi-mitsi.
Ita ce ke yin wata busasshiyar dariya haƙoran bakinta sun zama zaƙwa-zaƙwa, harshen bakinta kuwa har sharar ƙasa yake.
Ta ci gaba da ɓaɓɓaka dariya Alhaji na tsaye yana kallon ta tuni ya gama jiƙe wandonsa da fitsarin tsoro.
Ya ma kasa yin ihun neman ceto.
Lokaci ɗaya kuma sai ya ji ta daina yin dariyar ta koma yin wani irin kuka kamar na kamar na kare. A hankali kuma sai wannan tsawo da aka ƙara mata ya fara raguwa, lokaci ɗaya ta fara rikiɗewa zuwa siffar gizo-gizo tana cigaba da kuka.
Alhaji Falalu ya yunƙura da nufin ya fita a guje amma sai ya ji tamkar an riƙe shi ram a inda yake, ko ƙwaƙƙwaran motsi ba zai iya yi ba.
Yana kallo lokacin da tsohuwarsa ta gama komawa siffar gizo-gizo tana kuka, dogayen hannayen gizo-gizon masu ɗauke da yatsu irin na karnuka da farce mai shegen tsini.
Farcen ta dinga sokawa a cikinta tana ihu tana komai.
A duk lokacin da ta soka farcen a cikinta sai wata ƙara ta fita cusss, sai kuma jinjirin gizo-gizo ya faɗo ya zura a guje ya bi ta taga ya bar ɗakin.
Abin ya cigaba da faruwa har zuwa wani lokaci da komai ya tsaya cak kamar ɗaukewar ruwan sama, kafin daga bisani gagarumar guguwa ta tashi a iyaka ɗakin kawai ta fara hargitsa komai na ciki.
Alhaji ya runtse idanunsa yana fatan abin da yake gani Allah ya sa a mafarki ne!
Yana buɗe idanunsa sai ya hango tsohuwarsa kwance magashiyyan a ƙasa tana ta mata-gugu riƙe da ciki.
Da ya yunƙura sai ya ji kamar an kwance shi daga ɗauri, ya isa gare ta da sauri.
Sai dai inaaaa! Ja baya ya yi a matuƙar firgice.
Hajiya ce dai ga ta a kwance tana malelekuwa, ihun da take yi ma ba ya fita, abin da ya tsorata Alhajin kuwa shi ne ganin cikin Hajiyar a fafake, babu komai a ciki, duk wani nau’i na halittar kayan ciki babu an cire shi, jini kuwa sai ambaliya yake yi ta hanci da bakinta.
Kaɗan-kaɗan ya ji muryarta tana cewa. “Falalu! Falalu… Falalu mutuwa zan yi… zan mutu Falalu! Mutuwa!”
Ta yi ɗif, komai na jikinta ya saki!
Alhaji ya tsandara ihu ya zame jiki ya dire a gwiwowinsa.
Caraf idanunsa suka gane masa lokacin da gizo-gizon nan ya fito daga bakin Hajiya ya tafi cikin sauri ya bi ta taga ya fice.
A duk duniyar rayuwar Alhaji Falalu ba shi da wani abu guda ɗaya da yake masifar so da ƙauna sama da wannan tsohuwar mahaifiyar tashi, ga shi ta yi wata irin mutuwa ta tagayyara sanadiyyar gizo-gizo.
Gizo-gizon da tun bayan mutuwar bai ƙara ganin gilmawar makamancinsa ba, dama can gidan nashi ba inda irin waɗannan kwari ke samun wajen zama ba ne saboda ba a wasa wajen gyaran muhallin.
Wannan abin ya tsaya wa Alhaji Falalu a rai matuƙa, ya dinga tunani a kan hanyar da zai bi don ya gane dalilin da ya sa gizo-gizo ya kashe masa uwa bayan an gama tsorata su da wani shu’umanci!
Wannan kenan!
***
Misalin ƙarfe sha biyu da rabi na daren wata ranar Laraba, matashiyar budurwa kyakkyawa mai suna Anisa tana zaune a ɗakin karatu (study room) ta barbaza takardun handout a gaban irin fitilar nan ta karatun dare, ta mayar da hankali sosai gurin yin karatun.
Aka turo ƙofa aka shigo ɗakin, ta ɗaga kai a hankali ta ga wanda ya shigo.
Mahaifinta ne ya shigo fuska cike da murmushi.
“Shalele ba za ki ajiye karatun nan haka ki je ki kwanta ba?”
Ta yi murmushi ita ma.
“Abba exam ɗin gobe mai zafi ce, dole in dage in yi karatu in cika maka burinka.”
Ya yi murmushi ya ji daɗi sosai sannan ya yi mata sallama ya juya ya fita.
Yana barin gurin gizo-gizo na bayyana, ya wuce da sauri zuwa cikin ɗakin.
Anisa ta mayar da kai sosai tana cigaba da yin karatun sai ji ta yi an ja ƙofar ɗakin daga wajen an kulle gammm har sai da ta ɗaga kai ta kalli ƙofar, tunanin cewa mahaifinta ne ya rufe ta ya sanya ta mayar da kai ta cigaba da karatu.
Ɗif! Ta ga fitilar karatun nata ta ɗauke, da sauri ta lalubi makunnar ta kunna, aka ƙara kashewa, ta ƙara kunnawa, aka ƙara kashewa.
Ai sai ta miƙe da sauri ta lalubi wayarta ta kunna fitilar jiki.
Shuuuu ta ji kamar mutum ya wuce ta bayanta, da sauri ta bi gurin ta haska ba ta ga komai ba.
Jikinta ya soma ɓari, nan da nan ta fara haɗa gumi, tana ƙoƙarin yin taku ta isa bakin ƙofa ta ji an taɓa ta baya…
Numfashinta ya nemi ɗaukewa lokacin da ta juya ta yi arba da wani irin mutum mai jar fuska, babu komai a fuskar face ido ƙwaya ɗaya tal a gefe ga ƙwayar idon nan wata ranƙwaleliya kamar ball sai juyawa take, sai kuma wani wawakeken baki irin na ƙwarangwal mai ɗauke da zanƙala-zanƙalan haƙora da zarmaƙeƙen harshe…
Gizo-gizo ne curi guda ke fitowa daga cikin cikin mutumin.
Wani tsalle ya yi a gabanta ya tsorata ta ta hanyar ɗaga hannayenshi biyu masu ɗauke da yatsu biyu cal ya ce mata “Wah!”
Tuni ta shiɗe, wayar dake hannunta ta ƙwace ta faɗi ta tarwatse, nan da nan duhu ya ƙara mamaye ɗakin.
Wannan halittar ta saki wata muguwar ƙara, cikin wata irin murya ta ƙwarangwal ya fara magana.
“Aaaaniiiisaaaaaaaa! Aaaaniiiisaaaaaaaa kawaaaaaata… Tahooo mu yi wasaaaaa!”
“Daddy! Mummy!”
Sunan iyayenta take kira su kawo mata ɗauki, sai dai ina, ita kaɗai take kiɗanta da rawarta.
Tana cigaba da ihun neman taimako tana jan mazaunai zuwa bakin ƙofa.
A haka har ta isa bakin ƙofar, ta ci sa’a hannunta ya kai saitin makunnar fitila, tana kunnawa haske ya gauraye ɗakin, abin mamaki sai ta ga wayam babu komai, tamkar babu wannan halittar da ta gama tsorata ta yanzu.
Kasa tashi ta yi tsaye tana cigaba da mayar da numfashi tamkar wadda ta ci gudun famfalaƙi.
Kalle-kalle take yi tana ganin yadda ɗakin duk ya hargitse sakamakon buge-bugen da ta yi na gudun ceton rai.
Yif! Ta ga lafcecen gizo-gizo ya faɗo a jikinta… A duniya idan akwai abin da ta tsani ko da ganin shi ne to bai wuce gizo-gizo ba, yau ga shi a jikinta, gizo-gizon ma ba irin wanda ta sani ba, wani kala daban tafkeke mai wani irin ƙwalelen kai, da ta ƙura masa idanu sosai ma sai ta gani ashe kan mutum ne a jiki, wata kyakkyawar fuskar budurwa tana yi mata dariya!
Tuni ta ƙwalla gigitacciyar ƙara tana ƙoƙarin karkaɗe gizo-gizon daga jikinta amma sai ƙara maƙalƙale mata yake yi.
Tsalle ya yi ya dira a kan fuskarta, ta sake tsandara ihu tare da zamewa ta faɗi a sume.
Farkawa ta yi ta gan ta kwance a kan cinyar Mummy ɗinta Daddynta na tsaye hankalinsu a tashe.
Tana kawar da kanta caraf idanunta suka yi arba da gizo-gizon nan a can saman kusurwar ɗakin yana saƙa yana.
Ƙara ta ƙwalla tana nuna saitin gizo-gizon.
“Ga shi can gizo-gizo ne! Gizo-gizo! Ku kore shi! Ku kore shi!”
Hankalin iyayen fa ya tashi, don su ba su ga komai ba, suka fara tunanin ko dai gamo ta yi a daren jiya sakamakon tsayawa yin karatu?
“Shiyasa ba na son karatun daren nan naki Anisa, in ba sa’a gamo kika yi a daren!”
Zabura ta yi ta dubi Mummy. “Ƙarfe nawa yanzu?
“Ƙarfe tara ne!”
Ta ƙwace daga rungumewar da uwar tata ta yi mata ta miƙe da sauri.
“Me kuma ya faru?” Daddy ya tambaye ta.
“Exam!”
“A haka za ki school?”
“E Mummy, ba zan bari in rasa wannan damar ba.”
Daga haka ta shirya ta tafi makarantar.
Suna ɗakin jarabawa wajen su ɗari da wani abu, an karkasa su kashi-kashi ana rarraba musu takardu.
Mai raba takardar na zuwa kanta ya ajiye mata nata, ɗaga kan da za ta yi sai ta ga ya wangale mata fuska, fuskarsa wata iri tamkar ta tsohon da ya shekara ɗari biyu a duniya, haƙori daya ne jal a bakinsa kuma babu harshe a ciki.
Ta ji numfashinta kamar zai ɗauke, ta yi saurin kawar da kai.
Abin da ya ƙara tayar mata da hankali shi ne ganin ya zura hannu a aljihu ya zaro wani ƙwandalelen gizo-gizo ya cilla a baki yana taunawa da haƙori ɗaya…
Ai ba ta san lokacin da ta miƙe a guje tana ihu ta nufi hanyar fita ba, tana cin karo da kujera ta faɗi, sai ga tarin gizo-gizo sama da guda dubu suna rarrafowa a guje suna hawa kanta suna saƙa yana, kafin wani lokaci sun saƙa yanar da ta gama lulluɓe ta baki ɗaya…
[17/10, 11:55 am] +234 703 811 7298: 🕷️🕷️ *SHURIN FATALWA* 🕷️🕷️
🐲🐲🐲🐲🐲🐲🐲
🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️
*Muntasir Shehu*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*3*
Ɗakin jarabwar ya hargitse, mutane suka taru a kan Anisa suna mamakin abin da ya sanya ta shiga wannan hali na firgici da tsoro har ta fita harabar ɗakin jarabawar ta kwanta a ƙasa take birgima.
Wasu suka fara tunanin ko dai tana da matsalar shafar aljanu ne?
Wannan ta sa bayan an ɗauke ta an fice da ita zuwa ɗakin kula da marasa lafiya gwanayen karatu da ƙira’a suka hau yi mata karatu har komai ya warware mata ta dawo cikin hayyacinta.
Yanar da take ganin gizo-gizo sun saƙa mata ta yaye gaba ɗaya, su kansu tarin gizo-gizon gani ta yi wata iska mai ƙarfi ta taso daga sama ta zuƙe su ta bi ta rufin ɗakin ta fice da su.
Jarabawar da Anisa ba ta samu damar yi ba kenan aka kwashe ta aka mayar gida.
Nan hankalin iyayenta ya ƙara tashi, ba kamar Daddyn nata wanda ya yi shiruuuu yana wani tunani lokacin da take yi musu bayani game da wannan gizo-gizo.
Wani tunani ne ya faɗo masa a kan mutuwar mahaifiyar abokinsa wato Alhaji Falalu, gizo-gizo ne sanadin mutuwar ta bayan gama tsorata ta da ya yi.
Nan ma kuma ga shi gizo-gizon ya fara tsorata masa yarinya…
Waya ya zaro da sauri a aljihunsa ya fice, yayin da ita kuma mahaifiyar Anisa ta fara ƙoƙarin tofa mata addu’o’i don tana zargin wataƙila aljanu ne ke neman buɗe wa ɗiyar tata idanu sakamakon yawan karatun dare.
**
Mutanen garin Babbar Kuka suka ƙara wayar gari da wani abin sanya firgici.
Wato wata mata wayi gari aka gani kwance samɓal a sandare tamkar gawa a daidai gurin da shurin fatalwa yake, gaba ɗaya jikin matar a ruɓe yake tsutsotsi na faɗowa daga jikinta. Cikinta a fafake ana hango gizo-gizo a ciki suna ta kai wa da komowa.
Duk wanda ya ga matar nan abin da zai yi zato shi ne gawa ce aka tono daga cikin kabari don jikinta duk ya yi alamun yadda ƙasa take ruɓar da duk abin da aka binne a cikinta.
Lafta-lafta gizo-gizon ne suke ta fitowa daga cikin bakin matar wanda yake a hangame ba komai cikinsa sai wani haƙori guda ɗaya cal a gefe, harshen bakinta dogo ne wanda tamkar an sanya wuƙa an raba shi biyu tun daga tushiyarsa har zuwa tsininsa.
Hankalin mutanen garin ya tashi ainun, tsoro ya cika zuciyar kowa, masu runtuma ihu suka fara yi, masu haɗa kaya don yin gudun hijira ma suka fara yi don a cewar su dama tun da taƙadiran yaran nan su Ƙasimu suka yi gangancin fasa shurin nan ai shi kenan su da zaman lafiya, wa yake taɓa fatalwa ya zauna lafiya?
Mai gari ma da kansa ya zo ya ga wannan lamari, inda ya nemi a tattaro malaman garin su zo su yi ta karatu.
Kafin a kai ga yin haka fatalwar nan ta fara ihu da wata irin murya, daga bisani kuma ta fara magana.
“Ba zan bar kowa ba…! Ba zan ƙyale kowa ba…! Aaaaaniiiiisaaaaa ba zan ƙyale ki ba ba zan karaya a kanki baaaaaa!”
Lokaci ɗaya ta fara kumbura tana zama wata ɗirkekiya, kafin wani lokaci ta kusa girman wani saurayin dutsen.
Tush! Ƙarar fashewar ta ta cika dodon kunnen mutane, nan da nan sai ga wasu ɗirka-ɗirkan gizo-gizo suna yin fitar burtu daga cikinta suna yin kan mutane!
Tuni mutane suka ari ƙafafun zomo suka fara gudun ya-da-kanin-wani!
**
Daf da magariba, Hajiya Malika tana kicin tana ta sauri wajen ganin ta kammala yi wa maigidanta girki kasancewar yau zai dawo daga kudu.
Alla-alla take ‘yar aikinta Laila ta kawo mata kayayyakin da ta aike ta siya a kasuwa, yayin da ita ‘yar aikin take can tana ta ƙoƙarin harhaɗo kayan da ake buƙata.
Ba tare ta lura ba wani ɗan mitsitin gizo-gizo da bai fi girman kiyashi ba ya maƙale mata a silifas ɗinta.
Ta kammala siyan kayan miya da sauran duk abin da ake buƙata ta zuba a leda ta hau baburin a-daidaita, tana zama ta ƙara buɗe ledar don ta tabbatar ba ta yi shirme ba, to a daidai lokacin ne wannan mitsitsin gizo-gizon ya taho saɗaf-saɗaf ya shige cikin ledar, Laila ‘yar aiki ta haɗa da shi ta ƙulle.
Tana isa gidan ta wuce kicin kai tsaye inda ta iske Hajiya Malika na ta fama da aiki.
“Yawwa Laila kin dawo?”
“E na dawo Hajiya.”
“Ajiye kayan miyan maza ki shiga ɗaki ki ɗauki min sabon abin markaɗe da muka siyo jiya.”
Laila ta ajiye ta fice zuwa cika umarnin Hajiya.
Ɗauko ledar Hajiya Malika ta yi ta buɗe da niyyar zazzage kayan miya, ai sai ta ga tana zazzago curi-curi na lafta-laftan gizo-gizo masu kai irin na mutane ɗauke da ido ɗaya ƙwal a kusa da kunne irin na jaki.
Tuni Hajiya Malika ta zabura ta ƙwalla ihu ta yi jifa da ledar ta yi hanyar waje da gudu.
Kafin ta ƙarasa ƙofar ta rufe kanta da kanta.
Nan da nan sai ɗaya daga cikin gizo-gizo da ya fi kowanne girma ya fara ɓaɓɓaka dariya, sauran su ma suka kama yi har da tuntsirawa kamar mutane.
Fitsari kawai Hajiya Malika ke yi ba tare da ta sani ba, jikinta kamar zai tsittsinke ya tarwatse saboda rawa.
Dama ita ba gwanar yin addu’a ba yayin da abin tashin hankali ya faru don haka gizo-gizo nan suka dinga ɓaɓɓaka mata dariya kafin lokaci ɗaya kuma suka yi tsit a tare.
Wannan babban ya miƙe tsaye, sai ga ƙafafunsa sun rikiɗe sun koma irin na mutane, ya fara taku ya nufo ta.
Take ta ji numfashinta na neman ɗaukewa, ihu take so ta yi ta nemi ceton Laila amma ta kasa sai ƙara manne bango take yi tamkar zai tsage ta faɗa ciki.
Gizo-gizon nan ya ɗaga hannunsa ya sanya a ido ya zaƙulo wannan ƙwayar idon nashi guda ɗaya ya cillo mata, ƙwayar idon ta sauka a jikinta ta faɗi ƙasa baƙin da yake ciki sai jujjuyawa yake yi a cikin farin.
Hajiya Malika ta silale a ƙasa tana ƙoƙarin ta suma, daidai lokacin kuma ta ga gaba ɗaya gizo-gizon sun tattaru sun haɗe sun zama guda ɗaya jibgege wanda da kaɗan ta fi shi girma, bakinshi ya buɗe ya fara yi mata feshin wani irin ruwa mai yauƙi, ai sai ta ji komai ya ɗauke mata ɗif, tana kallo lokacin da baƙar ledar nan da aka siyo kayan miya a ciki ta taso ta tsaya a cikin iska, gizo-gizon nan ya ƙanƙance ya shige cikinta, daga haka ba ta ƙara sanin abin da ya faru ba sai farkawa ta yi ta gan ta a gadon asibiti.
Tana farkawa kuwa ta zabura za ta arce, maigidanta Alhaji Nura ya yi zumbur ya danne ta, ta fara ihu tana zabure-zabure.
Alhaji Nura ya fara kwaɗa kiran likitoci a zo a duba ta.
Kamar an ce ta kalli gefenta, sai ta hango baƙar leda iska na kaɗa ta, ta hango wani mutum tsoho tukuf a zaune a cikin ledar yana zaro mata harshe, ai sai ta ƙara rikicewa ta dinga nuna ledar tana faɗin.
“Ga shi can a ciki! Shi ne! Gizo-gizo ne! Zai kashe ni!”
Alhaji Nura ya kai dubanshi ga ledar da ta ke nunawa sai ya ga ledar da aka siyo ayaba ce, ya sake ta ya isa ga ledar don ya janye ta, yana ɗagawa sai ga gizo-gizo a ya kwasa da gudu ya yi cikin wani loko a tsakanin gadon marasa lafiya da kuma wajen ajiye magunguna!
Gabansa ya faɗi, don kuwa girma da siffar gizo-gizon nan sun tsorata shi, bai taɓa ganin gizo-gizo mai girmansa ba, kuma sai ya ga kamar kan mutum ne da shi ma.
Likitan da ke duba matarsa ne ya ce masa. “Wato Alhaji alamu sun nuna dole mu tura ku sashen binciken ƙwaƙwalwa don a duba ƙwaƙwalwarta a gano dalilin da yake sanya ta tsorata ɗin. Yanzu na kuma yi mata allurar bacci, saboda haka kafin ta farka za ku tafi da ita zuwa asibitin ƙwaƙwalwa.”
Alhaji Nura a cikin motar marasa lafiya yana zaune yana kallon matarshi dake baccin allura, ya yi shiru yana tunani.
**
Anisa tare da Mummy ɗinta suna zaune a falo, Anisa na riƙe da carbi duk da ba addu’a take yi ba amma Mummynta na ƙoƙarin koya mata addu’o’i da za ta dinga yi don tsari daga mugun gani, sannan kuma ta ɗauki matakin daina barin Anisa ita kaɗai tana zama a ɗaki, sannan ta daina zama a ɗakin da babu haske.
Can Mummy ɗin ta miƙe ta ce tana zuwa ta shiga ɗaki ta bar Anisa ita kaɗai a falo.
Wucewar kamar mintuna biyu sai ga Mummy ta dawo fuska cike da murmushi ta zo ta zauna kusa da Anisa ta janyo ta ta kwantar da ita a jikinta ta soma shafa ta, a hankali ta karɓe carbin dake hannun Anisa ta cillar gefe, faruwar hakan ke da wuya Anisa ta fara jin sauyi daga yanayin hannun dake shafa mata jiki, a hankali ta kai idanunta ga hannun sai ta yi arba da wani siririn abu mai kaushi mai kuma ɗauke da yastu irin na mutane.
Ta zabura da sauri ta tashi daga kwanciyar da ta yi a kan cinyar da take zaton ta Mummy ce, a kan idanunta jikin Mummy ya fara rikiɗewa a guje yana komawa sifaffar gizo-gizo, nan take kuma wata iska mai ƙarfi ta taso ta banko kofar ɗakin, wutar fitila ta ɗauke ɗakin ya yi duhu sai wani haske kaɗan-kaɗan da ba a san ta inda yake fitowa ba, a cikin hasken ne ta hangi yadda fuksar Mummy ɗinta ta rikiɗe ta zama ta fatalwa mai ɗauke da wani rantalelen kai, fuskar fara tas kamar an shafa mata farin fenti, idanun ma fari fat babu baƙar ƙwaya a ciki.
Gizo-gizo ne da yawa suke ta yawo a kanta yayin da ƙafafuwan gizo-gizon suka zama su ne gashin kanta.
Zancen a ce Anisa ta gama tsorata ma ɓata baki ne, fitsari kawai take tana kururuwar ihu amma babu mai jin ta, sai gudun ceton rai take yi a ɗakin amma duk abin da ta ci karo da shi sai ta ga ya rikiɗe ya zama ƙafar gizo-gizo guda ɗaya tana ta lilo.
Fatalwar nan ta dinga sheƙa dariya tana shuna wa Anisa hannayenta na gizo-gizo.
“Aaaaaniiiiisaaaaa! Taaaaahooooo maaaaanaaaa Aaaaaniiiiisaaaaa!”
Anisa ta sulale ta faɗi ƙasa, tana faɗuwa ta ga hannun gizo-gizo ya nannaɗe ta ya yi sama da ita, sai da ya kai ta daidai saitin fuskar fatalwar ya tsaya.
Fatalwar ta buɗe bakinta, wani baƙin mummunan gizo-gizo ya fito ya biyo zanƙalelen harshenta ya haye jikin Anisa ya fara yi mata yawo, Anisa ta ƙara sautin ihunta amma babu mai jin ta.
Fatalwar ta ƙara runtumewa da dariya.
“Babu wanda yake jin kukan ki, uwarki tana can mun saka ta bacci.” Abin da fatalwar nan ta ce kenan!
Aka saki Anisa ta faɗi ƙasa tim, gizo-gizo ya cigaba da bin jikinta tana ihu tana zabure-zabure kafin kuma gizo-gizon ya yi zaraf ya shige cikin bakinta, faruwar hakan ke da wuya komai ya dawo yadda yake, ɗakin ya buɗe haske ya dawo sai ga Anisa kwace a ƙasa ta riƙe cikinta da take jin gizo-gizo na yi mata yawo a ciki yana cinye mata kayan ciki.
Nan da nan jini ya fara fita ta hanci da bakinta da kunnenta.
Daidai lokacin sai ga Daddyn Anisa ya dawo, yana shigowa falon ya iske abin da ke faruwa ya ƙarasa a guje kan Anisa ya janyo ta ya rungume, sai dai ina, Anisa saura kaɗan ranta ya gama fita daga jikinta.
Ya soma ƙwalla wa Mummyn Anisa kira amma shiru, mayar da idon da zai yi kan Anisa sai ya tarar rai ya yi halinsa, yana kallo wani ƙosasshen gizo-gizo ya fito ta cikin kunnenta ya kwasa da sauri ya nufi hanyar fita, tuni ya saki gawar Anisa ya yi kan gizo-gizon da sauri yana kai masa duka amma bai samu nasara ba don tuni ya bi ta window ya fice.
Sai a lokacin Mummy ta farka a gigice daga baccin da ba ta san yaushe ta fara yi ba, tana farkawa ta tuna mafarkin da ta yi yanzu wai ta ga wani ƙaton gizo-gizo ya cinye jikin Anisa ya bar iya kai kaɗai, kuma Anisar sai ihu take yi ba ta mutu ba tana kiran a taimaka mata.
Tana fita ta iske mahaifin Anisan a kan gawarta ya rungume ta yana kuka.
Shi ma dai mahaifin Anisa mai suna Alhaji Badamasi ga shi ya rasa abu ɗaya tilo da ya fi yi wa ƙololuwar so a rayuwarsa.
Yanzu abin da suke zargi a tsakanin sa da abokinsa Alhaji Falalu ya fara tabbata.
Tabbas akwai wani ɓoyayyen dalili a kan wannan masifaffen gizo-gizo.
**
Alhaji Nura ya rasa inda zai sanya ransa da abin da ke faruwa da matarsa, asibiti sun tabbatar da lafiyar ƙwaƙwalwarta ƙalau, amma abin da ke faruwa shi ne yadda baƙar leda ke tsora ta, duk inda ta ga baƙar leda take za ta hau zabura tana faɗin ga gizo-gizo nan zai cinye ta.
Yanzu ma suna zaune a farfajiyar gidansu yana ta ƙoƙarin kwantar mata da hankali amma ta ƙi sauraron sa, ita kawai so take sai sun bar gidan in ba haka ba ba za a daina tsorata da baƙar leda ba.
A daidai lokacin kuma wani yaro a can wata unguwa daban ya gama haɗa jirgin leda irin na wasan yara ya sake shi a sararin samaniya yana ta sakar masa zare, can kuma sai cikin ikon Allah zaren ya tsinke jirgin ledar ya ƙwace ya dinga gudu a cikin iska har ya faɗo unguwar gidan Alhaji Nura ya yi ƙasa-ƙasa saitin saman gidan, daidai lokacin kuma gizo-gizo ya caraf ya faɗa kan jirgin ledan wanda ya sauka yif a daidai gadon bayan Hajiya Malika.
Ai sai ta zunduma ihu bayan ta zabura ta fara ƙoƙarin cire duk abin da ke jikinta, Alhaji Nura ya yi iyaka bakin ƙoƙarinshi ya riƙe ta amma ya kasa.
Abin mamaki tana cikin wannan ƙoƙarin cire kayan sai gizo-gizon nan ya lulluɓe ta da yana gaba ɗayan ta tamkar yadda ake naɗe wanda ya ƙone da bandeji a asibiti.
[17/10, 11:55 am] +234 703 811 7298: 🕷️🕷️ *SHURIN FATALWA* 🕷️🕷️
🐲🐲🐲🐲🐲🐲🐲
🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️🧚🏿♂️
*Muntasir Shehu*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________________*
*4*
Alhaji Nura ya ruɗe ya gigice ya rasa abin da ya kamata ya yi, yana kallo gizo-gizon nan ya gama nannaɗe jikin Hajiya Malika da yana, ta zame ta faɗi ƙasa kamar gawa.
A guje ya fita daga gidan ya doshi gidan wani malamin soro dake ƙasan layin.
Ya ci sa’ar samun Malamin ya roƙe shi suka taho tare.
Sai dai suna zuwa bai ga Hajiya Malika a kwance a inda ya bar ta ba, bai yi ƙasa a gwiwa ba ya ja Malamin suka shiga ciki.
Abin mamaki Hajiya Malika ce zaune a falo tana kallo a TV, turus! Alhaji Nura ya tsaya yana raba kallo tsakanin Hajiya Malika da Malamin.
A ƙarshe Malam ya yi addu’o’i da kuma yin wasu hayaƙai sannan ya tafi.
Har dare babu wani abu da ya ƙara faruwa don haka ya yi mata sallama ya ce zai je ya yi wa abokinsa gaisuwar rasuwar mahaifiyarsa.
Yana zuwa ya iske Alhaji Falalu da Alhaji Badamasi suna tattaunawa a kan yadda gizo-gizo ya zama ajalin mutane majiɓantansu.
Mamaki ya kama Alhaji Badamasi da ya ga Alhaji Nura.
Baki buɗe yake tambayar sa yaushe a gari? In ya tuna rabon da su haɗu sama da shekaru biyar.
A nan suka cigaba da tattaunawa, jin an sako maganar gizo-gizo ya sanya Alhaji Nura ya ji gabansa ya faɗi.
“Kuna nufin ku ce duk gizo-gizo ne ya yi sanadin faruwar wannan lamari? Hakan na nufin yanzu abin ya zo kan matata kenan? Kenan ita ma kashe ta zai yi?”
Kallon sa suke yi cike da mamaki.
“Kana nufin ka ce kai ma abin da ke faruwa da iyalinka kenan?”
Tuni gumi ya gama jiƙe Alhaji Nura ya cire hularsa ya jefar.
“Da idanuna na ga yadda gizo-gizo ya faɗo jikinta ya nannaɗe ta da yana…”
Tuni suka miƙe tsaye baki ɗayan su, “Akwai babbar matsala kenan!”
Suka fara kallon-kallo da ƙoƙarin tuno wani shuɗaɗɗen al’amari da ya faru a wasu shekaru can baya.
Suka fara kai wa da komawa a falon kowa jiƙe sharkaf da gumi.
Alhaji Nura ne ya samu bakin magana cewa.
“TSOHON GIDAN RAWA! Kun tuna tsohon gidan rawa?”
A tare Alhaji Badamasi da Alhaji Falalu suka waro idanu. “Me kake nufi? Me kake so ka ce Nura?”
Ya fara girgiza tare da sanya hannu ya zaro waya.
“Ya zama dole dukkanninmu mu taru mu yi gaggawar ɗaukar mataki kafin gizo-gizon ya gama bi ɗai-ɗai yana kashe mana abubuwan da muka fi so da ƙauna fiye da komai a rayuwa… Alhaji Falalu ba ka yi tunanin cewa an kashe maka mahaifiya ba ne saboda ita ce abin da ka fi so a duniya? Kai fa Badamasi? Kana da abin da ka fi so sama da ‘yarka Anisa? Ga shi ni ma yanzu ana shirin ɗaukar tawa matar da na fi so fiye da komai! Lallai ya zama dole mu dakatar da wannan abin da ke shirin faruwa!”
“Amma kai yanzu Nura ta ina kake ganin za ka tattaro dukkan abokanmu na samartaka? Kafin mu kai ga kammala nemo dukkan su wannan matsiyacin gizo-gizon ya gama bi ɗai-ɗai ya kashe mana abubuwan da muka fi so!”
***
*NIGHT CLUB*
Zunduma-zunduman amsa amo (speakers) ne suke ta fitar da wani irin sauti na waƙoƙin Turawa, irin dai waɗanda aka saba sakawa a gidan rawa.
A cikin wannan dare a daidai lokacin da samari da ‘yan mata ke ta raƙashewa, Hisham ɗan gidan Alhaji Awaisu yana ɗaya daga cikin samarin da suke ta shan shagali a tsakiyar wasu fitsarartun ‘yanmata.
Can ƙasa kuma gizo-gizo ne ke ta zabga gudu ya ratso ta tsakiyar mutune ya yi ciki har zuwa wani guri mai duhu, yana zuwa ya yi girgiza sai ga shi ya koma wata kyakkyawar budurwa tsaleliya cikin shiga ta bayyana surar jiki.
Hannunta ɗauke da kofin giya ta ratsa ta isa inda Hisham yake, tana zuwa ta sanya hannu ta jawo shi ta kai shi kan wata kujera ta zaunar da shi sannan ta miƙa masa kofin giyar.
An ce dama ƙuda wajen kwaɗayi yakan mutu, ba tare da fargabar komai Hisham ya karɓe giyar ya juye a cikin sa, ta saki murmushin mugunta a lokacin da ta fuskanci dafin da ta zuba a ciki ya fara ratsa shi.
Ba tare da ɓata lokaci ba ta sanya zoƙalelen ɗan yatsanta ɗaya ta jawo rigarsa suka nufi wani ɗaki a cikin gidan rawar.
A kan gado ta jefar da shi a lokacin yana shirin ficewa daga hayyacinsa.
Ita ma gadon ta hau ta bi shi ta janyo ƙaton bargo ta lulluɓe su.
Hannu ta sa ta fara shafa jikinsa, abu na farko da ya fara dawo da shi daga duniyar maye shi jin wani irin abu mai kama da lantarki na ratsa shi a duk lokacin da budurwar ta taɓa shi, sannan ya ji hannunta da kaushi bai yi kama da hannun ‘ya mace budurwa mai kyau kamar wannan ba.
Ya ƙura mata idanu, take ya ga kamar fuskar budurwar na canzawa.
“Wace ce ke?”
Ya fara ƙoƙarin tambaya.
Ta sakar masa murmushi. “Saurin me kake? Kai da za mu kwana tare da kai, za ka san ko wace ce ni…”
Take ya ga yatsun hannunta sun fara tsayi farcen jiki ya soma sauyawa zuwa wasu irin zoƙala-zoƙala, ai sai ya ga hannun nata ma ya fara sauyawa yana ruɓewa da kaɗan da kaɗan.
Nan da nan ya zabura da niyyar ya fice daga cikin bargon amma sai ji ya yi tamkar nannaɗe shi aka yi da bargon ba zai iya tashi ba.
Ya fara gumi cikin jin tsoro.
“Wace ce ke? Me kike nema a wajena?”
“Ruuuuhiiiii! Ruuuuuhiiiiinka nake soooooo!”
Nan fa Hisham ya fara fizge-fizge da fincike-fincike yana so ya fice daga cikin bargon a mugun tsorace amma babu dama.
Budurwar ta tuntsire da dariya lokacin da jikinta ya fara ruɓewa gaba ɗaya tana komawa zuwa suffar horuwa.
Wasu munanan baƙaken gizo-gizo suka fara fitowa daga baki da ido da kunnuwanta suka taho da gudu suka haye jikinsa suka fara yi masa yawo, ya dinga ihu da kurkuruwa yana karkaɗe gizo-gizon amma sai ƙara yawa suke, kafin wani lokaci sun gama rufe masa jiki gaba ɗaya suna ta caka masa farata suna zuba masa wani mummunan baƙin ruwa mai shegen doyi da yauƙi.
Horuwar nan dariya kawai take ɓaɓɓakawa, sai ga ta shuuuu ta ratsa bargon ta fice daga ciki ta bar Hisham shi kaɗai yana ta buge-buge da doke-doke yana ihu da kurkuruwa amma ba mai ceto, wani lafcecen gizo-gizo da ya zo ya tsaya a gaban idonshi yana kallo ya zuro dogon harshe yana yi masa gwalo.
Kawai sai ya ji ɗif, komai ya zama duhu a idanunshi.
**
Hajiya Malika na zaune a falo tana jiran dawowar maigidanta, sama-sama bacci ke ɗan fizgar ta tana girgijewa don tana ɗan jin wani tsoro-tsoro kaɗan a ranta, ko yaya ta ji ɗan motsi sai ta zabura ta kai kallo gurin.
Kamar a cikin bacci kamar kuma a farka ta ji wucewar wani abu shuuu kamar iska.
Ta zabura ta buɗe idanunta, da haske sosai a wadace a ɗakin don haka tana iya ganin komai na ciki.
Ƙirjinta na bugawa kaɗan-kaɗan ta cigaba da zazzare idanu.
Ji ta yi fuuuuu an ƙara wucewa ta gefen fuskarta har ana shafar mata jiki.
Ta zabura ta miƙe a gigice zuciyarta na tsalle a tsakanin ƙirjinta tana barazanar yin ƙunar baƙin wake ta fice daga ƙirjin.
Ba ta ga kowa ba amma ta ji wasu irin hannaye masu kaushi sun kama ta sun zaunar da ita a kan kujera, duk yadda ta yi ƙoƙari ta ƙwace ta tashi amma ta gagara.
Can kuma sai ta ji komai ya yi ɗif ya dawo daidai kamar babu abin da ya faru, tana shirin ƙara miƙewa ta ga wani abu salalalala ya biyo ta bayan kujera ya dafo wuyanta zuwa ƙirjinta, idanunta a gwalele ta kalli abin, hannun gizo-gizo ne mai ɗauke da yatsu sama da guda ɗari, hannun shi kaɗai yake reto babu gangar jiki.
Kuka ta kama yi da ihu da komai, amma babu mai jin ta balle ya kawo mata ɗauki.
Duk da cewa ƙofar falon a rufe take amma sai ta ji iska mai ƙarfi ta tashi daga waje ta fincike ƙofar ta buɗe ta da ƙarfin tsiya, wata baƙar leda ce ta biyo iska ta shigo ɗakin shuuuu ta zo ta tsaya a gabanta tana lilo a cikin iskar, nan take wani ƙwalelen ido mai ɗauke ƙwaleliyar baƙar ƙwaya ya bayyana a tsakiyar ledar, idanun ya fara jujjuyawa baƙar ƙwayar ciki tana wulƙitawa, can kuma sai wasu ƙanana-ƙananan idanu suka cigaba da ɓullowa a jikin ledar suna ta jujjuyawa!
Haba! Nan take fitsari ya ƙwace wa Hajiya Malika, ihun ma ta daina yi sai zuciyarta dake ta bugawa.
Ta rufe idanunta a so da take yi na ta daina arba da wannan baƙar leda da take tsorata ta amma sai dai tana rufe idanu za ta ji kamar an sa hannu a buɗe mata su da ƙarfin tuwo.
A hankali hannu ya ɓullo a jikin baƙar ledar, can kuma sai ga ƙafa ita ma ƙwaya ɗaya ta bayyana, ƙafa irin ta gizo-gizo.
Can kuma sai kan wata mace ya bayyana, kai irin na fatalwa, ba a ganin komai sai wasu zara-zaran gashi da suka lulluɓe fuskar fatalwar.
Dariya ta fara yi mata tana zaro mata harshe mai siffar kan maciji har tashi yake yi yana yin kamar yadda macijin ke fasa kai yana kawo mata sara.
“Ba za ki tsira ba Hajiya Malika matar Alhaji Nura!!!”
Da wata irin murya mai amsa amo har sau uku aka yi maganar.
Nan take kuma sai ga wani lafcecen gizo-gizo ya faɗo ƙasa tim daga bakin halittar ya rarrafo a guje ya nufo jikin Hajiya Malika, kafin ya ƙaraso ta fara takure jikinta tana ƙoƙarin tashi ta gudu sai dai tun daga nesa gizo-gizon ya yi mata feshin yana, yanar ta tafi a guje ta nannaɗe ta tamkar hannu aka sa aka yi.
Hajiya Malika ta kasa motsin komai, tana ji tana gani gizo-gizon nan ya haye jikinta ya fara yi mata yawo yana yi mata wata irin tafiya a jiki, wani yarrr take ji a jikinta sakamakon kaushin ƙafafun gizo-gizon da kuma irin tafiyar da yake a jikin nata mai kama da tafiyar tsutsa da ake yi wa mutum a tafin ƙafa.
Tana ji tana gani wannan baƙar leda mai kan fatalwa ta zuro hannun nan ƙwaya ɗaya ta buɗe mata baki da ƙarfin tsiya gizo-gizon ya yi tsalle ya faɗa cikin bakin nata kai tsaye ya wuce cikin cikinta ya fara yi mata ɓarna da ‘yan hanji, faruwar hakan ke da wuya ledar nan ta yi sama tana ɓaɓɓaka dariya sannan ta ɓace, ita kuma jini ya fara ambaliya daga hanci, baki da kunnenta, kai har da sauran duk ƙofofin gashin jikinta ko ina jini ne ke ɓulɓulowa.
Ta faɗi ƙasa tana malelekuwa da ihun neman ɗauki.
Alhaji Nura na faka motarsa ya fara jiyo gunjin kukan matar tasa, ko kashe motar bai yi ba ya tafi a guje zuwa falon, yana shiga falon idanunshi karaf a kan baƙin gizo-gizon da ya bullutso da ƙarfi ya yi fitar burtu daga kofar kunnen Hajiya Malika ya kwasa a guje ya shige wani lungu.
A guje ya ƙarasa kan matarsa lokacin tana gab da ƙarasa sheƙewa.
Magana take so ta yi amma ta ƙasa sai motsi da bakinta ke yi yana ambaliyar jini, lokaci ɗaya kuma ta yi laƙwas alamun ta mutu!
Alhaji Nura ya kurma ihu ya sake ta ya tashi da sauri zuwa inda ya ga gizo-gizon ya shige ya fara watsi da kayan wajen, ƙarshe bai ga komai ba sai wata tsohuwar ruɓaɓɓiyar baƙar leda irin wadda ake tono ta daga cikin ƙasa ɗin nan.
Ya dinga ihun tashin hankali da ɗimauta, bai yarda ta mutu ba don haka ya cicciɓe ta ya nufi asibiti da ita.
Bincike na farko da aka yi aka gano babu komai cikin kayan cikinta tun daga kan hanji da hanta, huhu, saifa, ƙoda, zuciya, har maɗaciya duk babu sai ramin wawakeke ciki kawai tamkar an fafake cikin kabewa.
Alhaji Nura, Alhaji Falalu da Alhaji Badamasi sun gama gigita da wannan lamari, Alhaji Falalu ne ya fara tunanin tun da har abin ta kansu ya fara biyowa to kamata ya yi su yi shiru tun da ba su kaɗai suka aikata laifin ba su bari kowa hukunci ya biyo ta kansa…
Alhaji Nura girgiza kai ya yi ce shi kam ba zai bari ba, tabbas zai gaggauta neman abokansu a duk inda suke don ya ankarar da su abin da ke faruwa kafin gizo-gizon fatalwa ya zo ya yi musu ɓarna.
***
Hisham farkawa ya yi ya gan shi kwance a ɗakinsa mahaifinsa da mahaifiyarsa a kansa suna jiran ya farfaɗo, a tsorace ya farka, ya miƙe a gigice yana shirin zundumawa da gudu, da sauri Abbansa ya dafe shi.
“Kwantar da hankalinka Hisham, a gida kake kana tare da mu ka ji!”
Ya dinga zazzare idanu a tsakaninsu yana sauke numfashi.
“Kun san me na gani jiya Abba? Fatalwa!”
Ba su gamsu da maganar tashi ba don haka suka ce.
“Babu wata fatalwa Hisham, wata shaiɗaniyar yarinya ce ta so yaudarar ka Allah ya tsare su Rabil suka gani, amma babu wata fatalwa mutum ce…”
Tana rufe baki ta ɗaga kai ta kalli can saman ɗakin ta hango saƙar yana tari guda, cikin mamaki ta kalli Hisham.
“Hisham! Me yana take yi a ɗakinka? Kamar ba a gyarawa?”
Da sauri suka kai duban su gurin, tabbas yana ce ga ta nan tsohuwar saƙa curi guda, suna hango wani jinjirin baƙin gizo-gizo a ciki yana ta motsi.
“No! Mom wannan yanar babu ita gaskiya, yanzun nan gizo-gizo ya saƙa ta amma ɗakin nan bai taɓa yin yana ba.”
“Garin yaya ma aka samu gizo-gizo a gidan nan duk feshin da ake yi a kai a kai?” Abbansa ya yi magana shi ma.
Mom ta juya da sauri, “Mu je Alhaji tun da ya tashi mu bar shi ya huta, zan turo Asabe mai aiki ta gyara ɗakin.”
Suka fita a tare, jim kaɗan aka yi sallama aka shigo ɗakin, Asabe mai aiki ce, yarinya ce matashiya da za ta kai shekaru sha shida.
Abin da ya ba shi mamaki shi ne yadda yarinyar ta shigo sanye da shigar Fulani, bai taɓa ganin ta da wannan kayan ba, hasali ma ƙauyen da aka je aka ɗauko ta ba ƙauyen Fulani ba ne, to ya aka yi yarinyar ta yi wannan shiga haka? Kuma sai ya ga ta yi masa ɗan karen kyau a ido.
Littafan Hausa Guda 1000 Download
Abin da ya ƙara ba shi mamaki shi ne yadda yarinyar ta shigo tana ta zuba murmushi, tashi ya yi daga kan gadon da nufin ya fita ya ba ta guri ta yi aikin sai gani ya yi kai tsaye yarinyar ta nufi wajen yanar, duk da yanar a sama take amma ga al’ajabi sai ya ga hannunta ya ƙara tsayi ya tashi sama shuuu ya taɓo yanar, da ɗan yatsa ɗaya ta fara naɗe yanar, nan take sai ga ‘ya’yan gizo-gizo ƙanana ‘yan mitsi-mitsi suna faɗowa, abin da ya fara ba shi tsoro shi ne yadda ta sunkuya ta dinga tsince ‘ya’yan gizo-gizon tana cillawa a baki tana taunewa, faruwar hakan ke da wuya ya ga ta miƙe ta juyo sun yi fuska da fuska, ai sai ya ga fuskar tata tana rikiɗewa da kaɗan da kaɗan tana koma kamannin wannan budurwa ta jiya da ta tsorata shi a gidan rawa.
Leave a Comment