Siddabaru Hausa Novel Complete

Siddabaru Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*EPISODE 01

 

 

Busar iska ake mai cike da ni’imar ubangiji,inda kuma sararin samaniya ta gauraya da haduri baki wuluk,kasar wannan haduri ko wata farar haske ce, ta haskake ilahirin gurin,abin gwanin ban sha’awa.

A daidai wannan lokaci kuwa wata farar mota, ta bayyana cikin *high-speed* kai tsaye ta nufi bakin rafi,inda mutane ke zuwa domin shakatawa,But surprisely babu wanda ya kasance a wannan guri ta sanadiyar wannan haduri.

 

Wani santalelen saurayine ya fito daga cikin wannan gabjejiyar mota,bayan motar ta tsaya dap da bakin ruwan,fuskar sa kuwa babu annashuwa ko kadan,fitar sa ya naimi wuri ya zauna sannan yayi tagumi alamar yana cikin damuwa,Soma tuno wasu kalmomi yayi,kalmar ko ta saka shi zuwar da kwalla…

Wannan kalma ko itace *we can’t be more than friends,because I don’t have a filling for you*

 

Hakanne yasaka shi jifa da wayar dake hannun sa,sannan ya saka hannu ya share kwallar dake zubo masa a fuska yin hakan dayayi yana tunanin zata rage masa wani part cikin kuncin dayake ciki, but dadɗa cusashi cikin damuwa hakkan yayi *he keeps on acting like everything is alright* amma kuma yin hakan babu abinda ta ragarmai……

 

Soma zabga ruwan sama akayi babu kakkautawa kaikace da bakin kwarya ake,dukda ruwan saman da ake zabgawa hakan bata saka ya koma cikin motar tasa ba, zama yayi akan ruwa,har daukewar ta 8:22 na dare.

 

Zaune yake sai famar kakkarwar tsiya yake hakwaran sa kuwa na bada sautin kak kak kak,Nan yake sai yajiyo wata kara mai kamada rushewar kayan kwalba abaya sa,nan da nan ya juya ya fuskanci gurin sannan kuma ya cike da mamaki domin dogayen bishiyoyine bila adadun bayan sa,babu alamar wani a kusa amma yajiyo karar rushewar tarkace,hakan ta sakashi cikin fargaba.

 

Nanfa ya mike ya soma waige waige indako ya soma jiyo ana kiran sunan sa cikin rad’a  *Eshan!! Eshan!! Eshan!!*

 

Abinka da mai naiman matsifa,bin wannan sautin yayi tayi har ta kaisa izuwa wata lambu mai cike da al’ajabi…

Cikin wannan lambun al’ajabi dai ko’ina furanni ne masu launin jan hankali sararin samaniya kuma taurarine tako’ina ga kuma farin wata….wanda ya haske gurin.

 

Nan yake yana ta washe hakwara sai yayi arba da wani haske wacce hasken natama abin sa’awa ne,da ganin haka yayi saurin karasawa gurin inda ya tarar da wata *kundin* wacce akayi mata ado da jan karfe sannan kuma aka tsarata irin ta zamanin daa.

 

Da ganin wannan littafi ko yasa hannu ya dauka, nan da nan hasken ta yaye,ya koma normal Kundin….

Da ganin jikin wannan kundin kuwa kasan ba abanza aka tsara ta ba,a jikin nasa anyi rubutun kalmomi biyu wanda shine *KUNDI* da kuma *AL’AJABI* wacce idan ka hadasu biyun zasu baka kalmar *kundin Al’ajabi*

Bayan ya dauki kundin sai damin butterfly suka kewaye sa,hade da jansa izuwa wata kujera wacce aka tsarata da furanni suka kuma zaunar dashi….haka wasu suka zo masa da wata hular fulawa suka daura masa.

 

Nan da nan suka watse suka kyaleshi a gurin shiko ya aje kundin asaman wata teburi wacce akayita da bakin karfe,Nan sai kundin ta bude kanta da kanta,Sannan wata haske mai launi uku ya fita daga cikin wannan kundi hade kuwa dayin wata jawabi……

 

*BARKA DA MALLAKAN LAMBUN AL’AJABI DA DUK ABINDA KE CIKIN TA,KUNDIN AL’AJABI MALLAKAR DUK WANDA YA MALLAKI WANNAN LAMBU,DAN HAKA WANNAN KUNDI MALLAKAR KANE ESHAN*

Cikin Kakkaurar murya wannan jawabi ta fito, Eshan ko cike yake da mamaki “taya hakan zata faru kuma taya na mallake lambun da yanzu nan na shigo cikin ta.” Abinda ke yiwa Eshan Yawo a ƙwaƙwalwa kenan….

 

Aiko bai tabbatar daya mallake wannan lambu mai cike da al’ajabi ba har saida duk halittu dake wannan lambu suka baiyana a gabansa hade kuma da rusunawa gaban sa suna mai kwasar gaisuwa, Eshan ko yana cikin wannan yanayi na mamaki hade kuma da fari ciki tuni ya mance kuncin daya kasance ciki dakikun da suka wuce,Aiko wannan mamaki da kuma farin ciki bata gushe ba har sai daya jiyo karar harbin bindiga, bayan wannan sautin harbi kuwa ya sake juyo wata siririyar murya na ihu.

 

Idan muka dawo da Labarin baya,kafin faru hakan Eshan ya kasance cikin hali na kunci da kuma damuwa ta dalilin hakan yake jan motar sa cikin fushi a wannan uban gudu da yake kuwa ya wuce gefen wata ƴar madaidaiciyar gida wacce a tsakiyar wannan gida kuwa wasu kyawawan ƴan matane biyu suke cirar shayar da suka yi ta sanadiyyar hadiri nan da suka gani,sun kasance suna mai wasa cikin salon burgewa wacce kuma suna hakane ta sanadiyyar wannan kyakkyawan hadiri daya mamaye sararin samaniya,wannan ƴan mata biyu kuwa sun kasance sa’anni juna,domin dacewa sukayi da kawayen juna,Aiko basu daina wannan wasa nasu ba har aka soma zabga ruwa sama babu kakkautawa.

 

“Yusra! Yusra!.”

Kiran wannan suna ake daga karkashin faranda na wannan gida, wacce ke wannan kiraye kirayen sunan ko ta kasance babbar mace ce mai suffar matan manya,gata da diri na a zo a gani,kuma tana da hasken fata,koda Yusran nan da take kira bata ansa mata ba zamu iyya cankar wacece Yusran daga ciki domin kuwa tayo uwar tata,ta Komi.

 

#Yusra ta kasance fara ce fes gashi kuma har gadon baya,gata da kyakkyawan gira da kuma mulmulelen lips, Siririyar ce wacce kyawun nata idan nace zan kwatanta muku sai munyini muna wannan zancen.

 

Jiyo Sunan nata yasa ta Juyo ganinta izuwa gurin.

 

“Yusra! kungan ku da shiririta maimakon ku shigo da kayakin ciki shine kuka tsaya har ruwa ta samo kuna wasannin?.”

 

da juyo hakan ta Kama kunnuwan ta da hannayen ta biyu hade kuma da cewa..

“Mummy Sorry,inaga daga Ruwan ne domin har izuwa yanzu ba sha’awar fita muke ba.”

Bayan ta karashe fadar haka kuwa ta fashe da dariya..

 

“Aikuwa ya zama lallai daku shigo dankuwa ina gudun muku zazzaɓi.”

 

“A’a Mummy kema ya kamata ki shigo muyi wasannin tare.”

 

Suna cikin wannan yanayi kwatsam sai suka jiyo an buge Kofar shigowa wannan gida nan da nan suka jiyo ganin su izuwa gurin,inda suka tarar da wasu mutane uku wacce sukayi shiga ta bakaken kaya kansu kuma pickup 🧢 suka sangama,sun kuma rufe fuskokinsu da Facemask,da ganin Yadda suka shigo gidan nan kasan ba’a banza bane domin shigarsu suka ja kofar suka rufe.

 

Cikin kasaita suke taku suna karasawa inda Yusra da kawar nan nata ke tsaye..

Abin tambayan anan shine suwaye wayennan kuma meye ya kawo su a irin wannan yanayi??

 

Ganinsu yasa Umman Yusra ta zura Idanu hadi da juyawa ta shige ciki ɗaki,suko isarsu inda Yusra ke tsaye suka tsaya cek shugaban nasu ko nace wanda ke jan nasu ya juya Idanu sa izuwa kan Yusra ko kibtawa bayayi haka ya tsaya har baiyanar Umman Yusra tare da abban nata…

 

Da ganin Abban Yusra ya taka izuwa karkashin faranda inda suke tsayen hadi da cewa…

 

“Nasan kasan mai ya kawo mu.”

Iyakan abinda ya furta kenan inda Abban Yusra ya juya suka hada Idanu da matarsa,bayan yayi hakan sai ya sake juyowa hadi da cewa.

 

“Mai kake nufi da hakan?.”

 

Gajeriyar murmushi wannan mutumin yayi hadi da zaro bindiga a kugun sa,aiko babu ɓata lokacin ya harbi sahun Abban Yusra Ganin haka yasa Yusra ta Kwarma bagidajiyar kara hadi da yunkurin karasawa gurin da suke,amma bata iyya yin hakan ba,ta sanadiyyar ji datayi an jata an kuma haɗata da kasa bayan haka kuma aka take mata gadon baya,haka zalika kawarnan nata itama.

 

Wannan wanda yayi harbi tsunkuyawa yayi gefen Abban Yusra yayinda Mahaifiyar Yusra ko rike take da mijin nata tana mai kuka cikin kara ganin haka yasa mutumin cewa…

 

“Shit! Matan nan taka akwaita da ihun tsiya duk tabi ta cike min kunne da koke koke marasa kan gado.”

Cikin sanyayyar murya ya furta hakan bayan nan ya haɗa rai sannan ya juyo ganin sa kanta hade kuma da cewa.

 

“Ki rufe min baki idan ba so kike ki cigaba da kuka na iyyakan rayuwar ki ba.”

Cikin fushi ya furta hakan bayan ya furta hakan saiya sake juyowa kan Abban Yusra..

 

“Ina akwatin take?.”

 

“Wacce akwatin kake magana akai?.”

Tambayan da yayiwa wannan mutumin kenan,shiko ya mike tsaya yayi sannan ya fashewa da muguwar Dariya hadi da tafi.

 

“Kar kayi kamar baka san komi ba,domin yin hakan babu abinda zata tsinana maka illa ta jefa iyalan ka cikin kunci,So karka ɓata mana lokacin whare is the box?.”

 

Box wacce Akwatin suke naima kuma meye a cikin wannan akwatin,babu wanda keda masaniya akan hakan hatta Yusra da kuma kawar nata.

 

Babu irin tursasawar da basuyiwa Abban Yusra da ya basu wannan akwatin ba amma yaki amince da hakan har saida sukayi masa Barazanar sheke Yusra kasarta da kuma matarsa kafinnan ya amince da bukatar su,haka yayi handing over na wannan Box ga wannan mutane suka ansa suka wuce still anan wannan Ruwan saman.

 

Cikin salon Kuka suka kasance yayinda kuma jini yayi ta zuba wa mahaifin Yusra har Tsayawar wannan Ruwa wato 8:22PM aiko 8:30Shep suka yanke shawarar kai Abban nata asibitin domin yana zubar da jini sun gwammace ƴan sanda su rike su maimakon ya mutu a hannun su garin gudun binciken akan raunin da yaji.

 

Haka suka shirya da niyar fita kwatsam sai suka jiyo an sake buge Kofar shigowa gidan nasu,suko a wannan lokaci rige suke da mahaifin nasu suna kokarin fitar dashi izuwa asibitin cikin garin..

 

Aiko still taron Mutane suka tarar wacce sukayi shiga ta bakaken kaya fuskokin su a rurrufe kawunan su ko sun rufe da hula pickup baki, dukkanin su sun kasance cikin wannan shiga illa daya tak wanda nake kyautata zaton shine jagoran su yayi daban da su domin shi shigan nasa bai rufe fuskarsa ba kuma kunnen sa da ƴar *Bluetooth speaker*.

 

Cikin sauri tawagar nasa suka haɗa masa kujera ya zauna.

 

“Well well well,hakan na nuna cewar kun sami labarin zuwan mu kenan,kuma am very sure kunsan Mai mukazo naiman,dan haka ku gaggauta bamu akwatin mu kara gaba.”

 

*Kuttsi ana wata ga wata,idan suma akwatin sukazo naima to su waye wayencen da suka karbi akwatin suka kuma wuce dashi?.* Tirkashi.

 

“Mai kuma kuke bukata daga garemu yanzu, bayan duk abinda kuka aikata a gare mu.”

Tambayar da kawar Yusra tayi kenan inda mafia Boss din Yayi gajeriyar murmushi hade kuma da cewa.

 

“A iyyakan sani na malam Kabir ƴa daya tilo gare sa,ke kuma wacece da zakiyi mini kasa landa cikin aikina?.”

Haka ya furta hadi da zaro bindiga yayi nuni da ita kan kawar nata,ganin haka yasa Yusra ta shige tsakani hadi da cewa.

 

“Wacce akwatin kuma kuke naima Bayan dakiku talalin da suka wuce kuka karba?.”

 

“Oh really,Gaskiya kam masu iyya magana sunyi gaskiya,kyawun ɗa ya gaji ubansa amma ke kuma meye abin sha’awa a halin mahaifin naki da kike kokarin dauka,koda shike ba gyaran tarbiyya bane ya kawoni wannan gurin na zone na anshi akwati na kuma gindayar da rayuwar maci amana.”

Ajiyar zuci yayi bayan nan ya cigaba da cewa

“Amma sai kuma aka sami sauyin wasa, mahaifin ki bazai gajiya da juya mana hankali ba,amma tunda yanzu yayi kurkuren mallaka miki wasan a hannu ina ganin gindayar da rayuwar sa shine tafi dacewa.”

 

Karan Harbin bindiga ne ya tashi aiko saiga Abban Yusra a kwance yayinda alburushi yabi ta cikin kwakwalwar sa ta fice….

Ganin haka yasa Yusra zura Idanu Umman Yusra ko ta bushe guri guda ta gagara motsawa…

 

Haka wannan Mafia Boss ya Mike ya riko Yusra a gashin kanta,dukda raɗadin da ake ji idan an rike mutum a gashin kai haka bata saka Yusra ta koma cikin hayyacin taba haka mutumin nan ya jata izuwa mota sa,ya shige cikin motar aka jasa yayinda yake rike da gashin kan Yusra itako tana tafe da kafafu ta har izuwa bayan gari inda suka tsaye kuwa taku talatin wata ƙatuwar tsauni ne wanda a saman wannan tsaunin wasu samari ne uku wanda nake kyautata zaton sune wanda sukayi basaja har suka anshi akwatin.

 

Fashewa sukayi da dariya yayinda suka yaye wannan kyalle dake fuskar su,aiko Samari biyu ne da kuma wata kyakkyawar yarinya…suka baiyana

 

“Wow Gaskiya munyi aiki mai kyau,babu wani wanda ya gane mu ƴan basaja ne.”

 

“Gaskiya mun yi aiki mai kyau.”

Fadar wannan kyakkyawar yarinya… kenan

 

“Yanzu maiya rage?.”

Tambayan da daya daga cikin samarin nan yayi kenan inda yarinyar ta basa ansa cewa.

 

“Bude ta kawai.”

Haka yarinyar ta basa ansa inda dayan saurayin ya zaro bindiga ganin suna kokarin daukar akwatin…

 

“What Are You trying to do *Malik?*”

Tambayan da suka yiwa wannan wanda ya zaro bindiga kenan.

 

“Babu Wanda zai bude wannan jaka har sai *Jafaru* ya karaso,domin shine wanda ya bamu labarin wannan akwati har mukaje muka ansa.”

 

Aiko da jiyo haka dukkanin su biyu suka zaro bindiga su inda sukayi nuni da ita kan Malik…

 

“Malik bamuso ta kaimu ga haka ba,ka kyale mu mu bude wannan akwatin domin itace kawai mafita kuma tunda mun riga mun san *kason* Kowa ina ganin bude akwatin shi tafi dacewa.”

See also  Gidan Uncle Audio Episode 5

 

“Babu wanda zai bude wannan akwatin, domin babu hakan a cikin tsarin aikin mu.”

 

Ajiyar zuci yarinyan tayi hade da kuma cewa….

 

“Ina ganin Malik yayi gaskiya meye na sauri bayan gamu rike da akwatin?.”

 

“Hakan bamai yuwa bane.”

furta hakan yayi bayan ya furta hakan sai yayi kamar zai dauki akwatin, *Eysha* ta juya bindigan izuwa kansa sannan tace dashi.

 

“Karkayi ganganci domin zaka iyya rasa ranka kuma ba damuwar kowa bane domin kason kowa zata karu.”

 

Aiko da jiyo hakan saiya sauke bindigar hadi da cewa..

 

“Ok na bada Gari.”

sauke bindigar nasu keda wuya ya tura akwatin da kaifin tsiya ta gangaro izuwa kasan wannan tsauni,aiko ganin haka yasa Malik da Eysha suka zura Idanu domin bangaren da akwatin ta gangaro babu hanyar sauka saidai a zaga kuma hakan zata cinye musu lokacin.

 

Haka suka tsaya kallon akwatin har ta sauka kasa kafin Eysha tare da Malik suka Juyo hadi da daga bindigar su sukayi nuni da ita kan *Awais*

 

*ESHAN*

cike da farin ciki yake kwatsam sai yajiyo karar Harbin bindiga,nan da nan ya mike tsaye hadi da juyawa Yana waige waige yana kan hakan sai ya sake jiyo sautin kiran sunan sa cikin Raɗa,haka wannan sauti ta kaisa inda Yusra da tarun mutane nan ke tsaye….

 

Yusra Zube take a kasa yayinda wannan mutumin ke nunata ta bindiga aiko Eshan sake jiyo wata sauti yayi wacce cikin sautin wasu kalmomin yake jiyowa..

 

“Eshan Eshan Tallafa mata.”

 

Aiko lumshe Idanun da zaiyi sai Kawai wata bakar guguwa ta tashi a tsakanin mutanen nan kamar yadda yake gani acikin kwakwalwar sa haka al’amarin ta kasance wannan bakar guguwa dai tayi ta jujjuyawa tsakanin su,kuma sai data saka duk suka rufe Idanu kafin nan ta yaye,Yayewar wannan guguwa keda wuya saiga Eshan ya baiyana a tsakiyar su ganin sa ko yasa mifia Boss din yayi saurin tambayan kansa.

 

“Waye kuma wannan?.”

 

Aiko cikin salo Eshan ya bude Idanu…. yayinda ya ɗaga ta izuwa kansa.

 

*EPISODE 02 PREVIEW*

 

Fadar wata Tsoho

“Dukkanin ku biyu abin farauta ne ga duniya,kamar yadda mutanen Gafur bazasu daina bibiyan rayuwan Yusra ba haka kaima bakaken Aljanu,Mayu,dodoni da kuma bokaye bazasu daina bibiyan kaba.”

 

 

*AKWATI*

Haka wannan akwatin ya gangaro izuwa kasan wannan tsauni,Yayinda suka tsaya kallon sa har dirar sa kasan,kafin nan suka Juyo cikin fushi hade da ɗago bindigar su sukayi nuni da ita kan *Awais*

 

“Babu Abinda zata hana ni fasa maka kai,idan da nasan abinda zaka aikata kenan.”

Fadar Eysha kenan inda Malik yayi sauri cewa.

 

“Munyi da Jafaru karfe Goma shep zamu hade a nan gurin,kunga kenan mintuna Talatin kacel muke dashi na samo wannan akwatin dan haka ya kamata mu gaggauta nemo wannan akwatin tunkan jafaru ya karaso.”

 

Dajiyo wannan batu na Malik sai Eysha tayi ajiyar zuci hade da sauke bindigar ta Juyo ganinta izuwa kan Malik,Haɗa fuska tayi yayinda suke kallon cikin Idanun juna..

 

“Zamuji da Al’amarin Awais later.”

Sake furta hakan Malik yayi itako bata ce dasu komi ba ta Juya ta soma tafiya cikin sauri haka Malik ya biyo ta abaya Awais ma haka…

 

Sauka sukayi izuwa inda suke tsammanin akwatin zai fadi amma suka tarar babu komi aiko Malik jujjuyawa yayi yayinda yake haske guraren da Touch light but still Babu alamar akwatin a kusa….

 

Alama Malik yayi musu da hannu da su zaga su duba ko zasu sami akwatin but still bayan sun zaga babu wanda ya sami akwatin…Haka suka sake hadewa a guri guda.

 

“Shin Akwai wani labarin ko kuma wata alamar?.”

Hakan Malik ya tambaya yayinda ya haske fuskar Eysha da Touch light itako girgiza kai tayi alamar A’a shi ko Awais gajeriyar murmushi yayi sannan yace dasu.

 

“Wata kila fiffige tayi ta fire akwatin.”

Aiko kafin ya rushe baki sai yaji an sharara masa tafi a fuska, aiko ba kowa bane yayi wannan illa Eysha dake tsaye gefen sa,ganin hakan ya sakashi haɗa rai hadi da yunkurin kaiwa Eysha martani,But shiga tsakani Malik yayi yayinda suka soma kaiwa juna suka suna mai zagin juna cikin cacan baki….

 

“Ku daina Wannan shashancin.”

Cikin kara Malik ya furta hakan,aiko tsit sukayi nan Malik ya hau surutun cewa.

 

“Ku wai Maike damun kune eh,meye anfani wannan rigima yanzun?,kowa dai yanzu yasan yayi kuskure amma mai makon mu naimo hanyar magance Wannan kuskure a’a ku ba hakan kuke tunani ba sai bata mana lokaci kuke da wannan fadace faɗacen naku na banza,karku manta dai nine jagora a wannan aikin dan haka ya zamanto dole kubi umurni na domin mession namu har yanzu bata kare ba,and we all know Idan har wannan aiki bata tafi yadda aka tsara ba dukkanin mu makomar mu itace mutuwa.”

 

Aiko da jiyo wannan zance dukkanin su jikin su tayi sanyi nan Eysha ta sauke Idanu hade da cewa…

 

“I’m sorry Malik.”

 

“Why?.”

Tambayan da Malik din yayi kenan inda Awais yayi saurin basa ansa.

 

“we are sorry sabida wauta irin tamu ce masu gajerun tunani take kokarin taɓarɓarar mana da wannan aiki.”

 

Dajiyo haka yayi gajeren murmushi hadi kuma da cewa.

 

“Ba wauta bace Awais,ko nine a wannan matsayi naka da hakan nima zanyi,amma kafin aikata komi ya kamata mu tuno yarjejeniyar da mukayi, wannan aiki mun karbane yayinda mukayi musayar ta da rayukanmu bayan nan kuma nayiwa kowannen ku alkawarin komawa gida cikin koshin lafiya dan haka karmu cire tsammanin da samun wanna akwatin babu inda zataje wata kila makalewa tayi a saman bishiya.”

 

“Alhakin kare rayukan mu ta rataya ne a wuyoyin mu dukka,Malik ka daina daurawa kanka nawin komi,we are all here as a team Dan haka zamuyi aiki tare mu kare kawunan mu tare.”

 

*ESHAN*

 

“Eshan! Eshan! Tallafa mata.”

 

Kalmomin da suka fado masa cikin kwakwalwa kenan nan da nan ya lumshe Idanun,aiko kumshe idanun da yayi keda wuya Kawai sai wata bakar guguwa ta tashi  a tsakanin mutanen nan,bakar guguwa cikin bakar dare wannan abace na azo a gani…

guguwa dai tayi ta jujjuyawa tsakanin mutanen nan, yayinda tayi ta jujjuya tunanin su,kuma sai data saka duk suka rurrufe Idanu kafin nan ta tsaya,Yayewar wannan guguwa keda wuya saiga Eshan ya baiyana a tsakiyar su kamar walkiya a duhun dare,ganin sa ko yasa mifia Boss din yayi saurin tambayan kansa.

 

“Waye kuma wannan?.”

 

cikin salo Eshan ya bude Idanu…. yayinda ya ɗaga ta izuwa kan wannan mutumin hadi da ɗaga yatsa yayi nuni dashi kan mutumin yana wasu maganganu marasa kan gado.

 

Yusra dai ta ƙasance kwancen take yayinda kuma iyakan gadon bayan Eshan take iyya hangowa,amma kuma zuciyarta cike fal da tsoron ganin fuskar nasa dukda tasan yazo wannan gurin ne domin ya cece ta…

 

(“Taya Aljani kuma zai baiyana domin ya ceto rayuwa ta shin Rayuwar tawa wata daraja ce da ita?.”)

Tambayar da take ta yiwa kanta kenan cikin zuciya amma kuma dukda wannan fargaba bata iyya mikewa ta bar gurin ba.

 

Eshan cigaba yayi da nuna wannan mutumin  da yatsa yayinda yake wata aba yadda kasan zombie hakan ya kasance, mutumin ko nace Mafia Boss din bada umurnin yayi da a kawo masa Eshan din domin kuwa da a kwai dan rata tsakanin su da Eshan din amma kuwa da yasan abinda zata biyo baya da banyi gangancin aikata hakan ba.

 

Domin kuwa karasawar wanda aka tura ya taho da shidin keda wuya sai mutumin ya nemi Eshan ya rasa.. mutumin na kan waige waige sai yaji an damkeshi ta baya da kuma hannu daya aka ɗagashi akayi hajijiya dashi aka kuma hadashi da kasa aiko raga raga kasusuwan jikinsa sukayi bayan nan Eshan yayi jifa dashi hadi da juyowa ya sake fuskantan Shugaban tawagar tasu….

 

Aiko ganin haka yasakashi ihun cewa suyi harbi kuma haka sukayi domin soma zazzagar da alburusan su but cikin abinda bai wuci dalilai guda ba Eshan ya bisu daya bayan daya ya warwargazar da bindigogin nasu ya kuma dawo ya tattare alburusan dake kokarin taba Yusra sannan ya dawo matsayar sa,bayan dakika dayan nan sai sukaji bindigogin nasu ya zube kamar tarkace…

 

Eshan kuma tsaye yake ya zuro Idanu sai wata sabuwar guguwa ta tashi ta kuma lullube Eshan da Yusra aiko bayan yayewar wannan guguwa babu wanda kuma suka tarar a gurin..

 

A firgice wani santalelen saurayi ya farka daga bacci yayinda ya soma nishi kamar an shake Masa makogoro yana kuma kakkarwan tsiya,da dukkan alamu mummunar mafarki yayi mai razanarwa hakan kuma ya saka idanunsa suka juye suka dawo fari sal yayinda jijiyoyin jikinsa suka baiyana,yana wannan gaggauran nishi kuwa sai wani dattijo ya shigo dakin cikin sauri domin kuwa tun yana kofa yake jiyo wannan nishi da wannan santalelen saurayin keyi…

 

“Zain! Zain!!.”

Cikin kara wannan dattijo yake kiran wannan suna bayan ya kai inda wannan saurayi yake zaune ko yasa hannu da niyar shafar goshin sa,aiko ji yayi tamkar garwashin wuta ya kama domin har hayaki hannun nasa ta soma…

ihu ya sake hade da riko hannun nasa da dayan, bayan ya jefar da akwatin daya shigo dakin da ita a hannu..

 

Akwati? Aiko wannan itace akwatin da Eysha Malik da kuma Awais ke mutuwar naima a cikin dajin, taya wannan mutumin ya kasance dashi?.

 

Cikin sauri wannan dattijo ya koma izuwa bangaren daya na wannan daki ya dako wata ƙatuwar mayafi wacce aka rataya a jikin bango na wannan daki saiya lulluba kan Wannan santalelen saurayin aiko cikin abinda bai wuci dakiku goma ba sai yajiyo Zain ya fara shesshekar kuka…

 

Cikin sauri ya yaye wannan Kellen hade dajan Zain ya rungume sa…

 

“Zain daina kuka ina nan tare dakai,nasan mafarki ne ko ba haka ba?”

Alama yayi masa da hannu alamar eh…

 

*ZAIN*

Yaro ne wanda ya kasance cikin yanayi na muggan mafarke mafarke tun yana Ɗan shakara Biyar,kafin mutuwar mahaifiyarsa ta kasance takan daukesa izuwa wajajen malamai dan naiman waraka amma kuwa  basu taba dacewa ba har rasuwar ita mahaifiyar tasa,bayan rasuwar ta da ƴan shekaru mahaifin sa ya biyo baya haka yasa dangin nasa sukayi ca akansa suna mai cewa shidin mummunar ƙaddara ce ga ahalinsu,dukda cewar bashi da alaka da mutuwa iyyan nasa amma sukan danganta shi da faruwar hakan… wannan dalili ne yasa kakansa namiji wanda yake zaune shi daya a katafaren gidan sa ya dauke da zumman naimamasa magani.. Gajeren bayani game da Zain kenan.

 

“Zain daina kuka ina nan tare dakai,nasan mafarki ne ko ba haka ba?”

Zain bai ce dashi kala ba bayan ya juyo kalman nasa,amma bayan yayi arba da hannun nasa daya kone saiya janye jikinsa daga runguma da sukayi ya soma cewa.

 

“Ni mummunar ƙaddara ce ga duk dangi na, ban cancanci kulawa daga gare ku ba domin nakasata takan iyya cutar da duk na jikina ya kamata ka kyale ni nace ka kyale ni.”

Haka yayi ta Maimaita kalmar ka kyale ni domin Wannan dattijo na kokarin jawo sa jikinsa…

 

Haka wannan mutumin ya jawosa jikinsa suka sake rungume juya sannan ya soma cewa…

“Zain kaifa jika nane,kuma fadar ƴan uwan ka na cewa kai bakar ƙaddara ce wannan ba haka bane domin laluran ka iyya fata take iyya cutarwa ba Ruhi ba dan haka ka kwantar da hankali ka Insha Allah zamu sami waraka.”

 

Haka Zain Yayi shiru sai faman shesshekar kuka yake…idan kuma muka duba bangare guda na wannan daki akwatin nan da Tawagar Malik ke naima ne a yashe.. toh taya Wannan dattijo ya samu wannan akwatin???

Domin samun wannan amsa sai mun dawo baya da wannan labari…

 

A daidai lokacin da wannan akwatin ya fado daga saman tsaunin dirar yayi a gaban wannan dattijo…

Yayinda yayi arba da wannan akwatin kuwa sai zuciyar sa ta soma raya masa daya kyale akwatin a gurin amma sai wata tunanin ta sake fado masa shin ko warakan cutar dake addabar jikan nashi ne a ciki? Haka yasa ya dauki akwatin izuwa gida…

 

Al’amarin Eshan da Yusra kuwa cikin wata tsohuwar guri mai kama da fada suka tsinci kansu inda da faruwan haka Eshan yanki jiki ya fadi…a sume

Aiko ganin haka yasa Yusra ta mike tsaye hade da rugawa domin Eshan ya tsorata ta sannan kuma zuciyan ta na raya mata Aljani ne wannan…

 

Guduwa take ba tare da sanin inda take sanya kafafun ta ba kuma bata daina wannan gudun ba har saida tayi karo da wani abin ta zube a kasa, soma jan kata da baya tayi domin gujema wannan abin amma sai ta jiyo wata murya na cewa.

 

“Ki nutsu ƴar nan,Ni bil adama ce ba wata abar bane na daban.”

Aiko dukda hakan da ta jiyo bai saka ta tsunu ba,har saidai wannan mai magana ta kunna fitula kafin nan ta kame gurin guda…

 

“Ƴar nan maiya kawo ku wannan guri haka?.”

Tambayar da wannan tsohuwa tayiwa Yusra kenan inda ta soma yi mata nuni da yatsa tana nuna hanyar data fito…

 

“Shin Kin tsora ta ne?.” Bayan nan ta sake da cewa “kina bukata na nuna miki hanyar fita daga nan guri?.”

 

Gyada kai alamar Eh tayi aiko wannan mata ta mika mata fitula hade da cewa “biyo ni muje na cire ki daga nan.”

See also  Hausa Novels Complete Documents Pdf

 

Tafiya sukayi na fitar hankali kafin wannan matar ta soma cewa…

 

“Yusra naji bayanin ki game da wannan wanda kika baro a baya,toh abinda nake so ki sani shine shi din ba jinnu bane bil adam ne kamar ki,kuma abinda nake so na tabbatar miki shine kasancewar ku tare bata da wata anfani domin Dukkanin ku biyu abin farauta ne ga duniya,kamar yadda mutanen Gafur bazasu daina bibiyan rayuwan ki ba haka shima Eshan bakaken Aljanu,Mayu,dodoni da kuma bokaye bazasu daina bibiyan rayuwarsa ba dan haka kasancewar tare ba alheri bane.”

 

Aiko da jiyo hakan tayi saurin yimata tambayan cewa

 

“taya kika san hakan kuma waya gaya miki sunan sa Eshan?.”

 

“Toh wai Yanzu abin mamaki ne idan mutanen boye suka san abinda ke boye?.”

 

Dajiyo hakan Yusra ta kame guri guda ta gagara motsawa aiko wannan tsohuwa ta Juyo ta fuskanci Yusra hade da kyakkyawa da dariya… Wacce tasa hanjin cikin Yusra kadawa…

 

“Eshan Ya kasance abin farauta ga ire iren mu domin shidin ya kasance cika makin iko ne na duk duniya,amma kuma zaki zame min katanga ga cikar buri na toh yanzu mai kike ganin zan aikata kenan ga wannan katanga dake kokarin tare cikar buri na?.”

 

Aiko da juyo wannan tambaya Yusra ta zuro Idanu…

 

Idan muka gangara izuwa wajenda Eshan da Yusra suka baro kuwa jagaban tawaga mai suna Gafur ne ke tsaye yayinda ya cike da mamaki… “Shin wai har yanzu irin wannan abubuwa takan faru a zahiri?.”

 

Tambayar data tsaya masa akai kenan, bayan wasu sa’o’i ya juyo hadi da kirawo daya daga cikin masu taka masa baya da suna Jafaru aiko nan da nan Jafaru ya karasa inda yake tsaye sai yace dashi…

 

“Kaine kadai wanda zan Iyya mallaka wa wannan aiki dan haka zan kyale ka da mutane uku anan ku cigaba da bincike yayinda zan dibi sauran izuwa main House domin sanar da mai gida abinda ke faruwa..”

 

Amince masa Jafaru yayi bayan wucewar su Jafaru ya umurci kowa daga zaga domin binciko ko zasu samo Yusra nan kusa bayan sun wuce ko ya taka izuwa saman tsaunin inda sukayi zasu hade da boyayyen tawagar tasa amma ya tarar babu kowa a gurin illa bakar rigunan da suka sakane ya zube agurin hakan kuwa yasa Jafaru zaro wayarsa ya soma kiran su aiko babu inda wannan waya ta soma kara sai a gidan su Yusra inda Umman Yusra tare da kawar Yusra ke zaune an daura musu bindiga a kawunan su…

 

Wannan wanda aka daurawa Ragamar tsaran nasu ya mike cikin fushi ya karasa inda wayan ke yashe… Ganin Private number ne ke kira ya sakashi take wayar..ta dauke

 

Jafaru Ganin an datse masa kira ya sakashi hada rai hade kuma da sake daura wayan a kunne da niyar sake kiran nasu amma sai yaji wayar a kashe aiko sauke wayan yayi hade da cewa…

 

“Yara dani kuke wasan.”

Bayan ya furta hakan sai ya turawa Gafur sakon cewa *”I found something,ya kamata kazo ka duba.”* Bayan nan yayi gajeriyar murmushi…

 

*EPISODE 03 PREVIEW*

 

“Na ɗebi shekaru da dama ina mafarke mafarke akan ababen tsoratarwa,kuma nakan tarar da mutane da dama cikin mafarke mafarken amma duk cikin su babu wanda ya taba tallafimi ko yayi kokarin ceto ni daga hannun ababen nan sai yau na sami wani mai suna Eshan,yayi kokarin cetoni shin waye wannan Kaka?.”

[

 

 

 

 

*ZAIN*

Cikin yanayin bacci wannan dattijon ya kwantar da Zain yayinda ya jawo barko ya lullube sa da ita.. Bayan yayi hakanne ya mike tsaye hadi da cewa… “Bacci mai daɗi jika na.”

Haka wannan dattijon ya furta Bayan nan ya wuce ya kyale shi kwance,aiko fitar sa da wasu dakiku Zain ya sake komawa a yanayin mafarki hade da shure shure Al’amarin Jafaru kuwa Ganin an datse masa kira ne ya sakashi hada rai hade kuma da sake daura wayan a kunne da niyar sake kiran nasu amma sai yaji wayar a kashe aiko sauke wayan yayi hade da cewa… “Yara dani kuke wasan.” Bayan ya furta hakan sai ya turawa Gafur sakon cewa *”I found something,ya kamata kazo ka duba.”* Bayan nan yayi gajeriyar murmushi… Kai tsaye Gafur ya taho gurin,inda ya tarar dasu,issar sa da tawagar nasa keda wuya Jafar da saura abokan aikin suka rusuna suna mai nuna girmamawa hade da kwasan gaisuwa..

 

“Jafar hakan na nuna cewar wayenda sukayi wannan aika aikan suna kusa,amma bai kamata daga ganin wannan alama mu amince da fadar wancen yarinyar ko kuma mu daina farautar ta ba,tunda na riga na sanar da shugaba kuma ya bada umurnin kawo ta araye,ina ganin yanzu aikin ya rabe mana gida biyu… dole yanzu musan yadda zamuyi mu rabe gida biyu domin tafiyar da wannan aiki yadda ake bukata, inaso muyi kokarin samun wannan akwatin kafin Susan Maike ɗauke acikin.”

Dajiyo hakan sai Jafar yayi gajeriyar murmushi hadi da yin wani batu a kasan ransa… Cewar shine “Yanzu ne zaku fahimci abinda ake nufi da Rayuwa ko mutuwa.”

 

Yusra.

“Eshan Ya kasance abin farauta ne ga ire iren mu domin shidin ya kasance cika makin iko ne na duk duniya,amma kuma zaki zame min katanga ga cikar buri na toh yanzu mai kike ganin zan aikata kenan ga wannan katanga dake kokarin tare cikar buri na?.” Bayan furta hakan datayi saita fashe da dariya wacce tasa hanjin cikin Yusra kadawa

 

“Yusra shin kin tsorata ne,ko kuma dai mamaki kike ne,shin na sake sanar dake wani abin mamakin?.” Tambayoyin da wannan tsohuwa ta jerawa Yusra kenan bayan Yusra ta jiyo hakan sai ta soma kakkarwan tsiya ta kuma gagara bude baki,Haka wannan matan ta sake da cewa

“Yusra kina tsaye ne akan karfin ikona shin ko kin sanda hakan?.” Yusra ruɗewa tayi domin batasan nufin wannan matan ba,haka ta ɗago Idanu tana kallon Fuskan wannan mata yayinda Itako tsohuwar ta sauke Idanuwa kasa alamar tana yiwa Yusra nuni dashi… Aiko sauke idanun da Yusra zatayi sai ta tarar akan iska take tsaye domin ramine mai matukar zurfi a kasanta.

“I’m sorry!.” Kalman karshe kenan data fito daga bakin wannan tsohuwa aiko furta hakan keda wuya sai Yusra taji ta zurme cikin wannan ramin haka ta Kwarma bagidajiyar ihu yayinda take sauka izuwa kasan wannan Rami,wannan tsohuwa kuwa juyawa tayi ta koma ta kyale Yusra cikin wannan hali.

 

MALIK

Idan muka gangara bangaren su Malik kuma yanke shawarar karasawa kauye mafi kusa dasu sukayi ta hanyar bin wata shatin sawu.. kuma sun kasance suna mai kyautata zaton mai wannan sawun shine wanda yayi gaba da akwatin,kuma fa hakane domin wannan sawu shine sawun dattijon nan wanda yake kula da jikansa wato Zain Amma Kuma Taya zasu gane hakan? tunda iyakan sawun kafafunsa kadai suka gani…. Haka suka kasance suna bin wannan sawun kafafu har ta kaisu wannan gari,amma kuwa rashin Sa’an da sukayi shine isarsu kauyen keda wuya aka soma zabga ruwan sama again… Aiko tuni suka naimi shatin kafafun suka rasa. “We are all in Danger now!.” Fadar Eysha kenan inda Awais yayi saurin cewa da ita “Bai kamata muyi saurin karaya ba Eysha.”

 

“Abinda nakeson ka fahimta shine it’s 12 already,Kuma munsan Jafar ko dakika daya bazai kara akan lokacin da ya ɗiba mana ba,a gani na warhaka ya saka a farauto mu.”

 

“Enough Guys ku sani mission namu koda late ne ya kamata mu cika ta dan haka zamu biya gida daya bayan daya mu duba, Lets go.”

Duk cikin su babu wanda ya budi baki haka suka bi Malik din a baya,gida daya bayan daya sukayi ta cajewa suna mai binciko akwatin ba tare da sun tashi Kowa ba, haka sukayi ta naiman wannan akwatin ba tare da sun sami akwatin ba har suka dibe tsawon awa guda suna kan hakan.

 

Ɓangaren Eshan kuma misalin ƙarfe Bakwai na safe ya buɗe Idanu ta sanadiyar Surutun wani dake damunsa a kunne,aiko kafin ya buɗe Idanu jiyo muryan mai shi na cewa “taya muka kasance a wannan gurin,bayan jiya a wani Gurin muke na daban… Gaskiya na gode Allah da ya ceto mu daga hannun wannan hastabibiyar maiyar.” Haka yake jiyowa bayan nan mai wannan magana ya dawo yana waka ta cikin wuya yayinda iyya sautin wakan ake iyya saurara,babu ɓata lokaci Eshan ya bude Idanu,aiko cika yayi da mamaki bayan yayi arba da gurin domin tsintar kansa yayi a tsakiyar sahara wanda iyya ganin ka bazaka iyya ganin karshen sa ba,tsayawa ganin ikon Allah Eshan yayi yana kan hakan kuwa sai ya jiyo an ce dashi

 

“Barka da Safiya,ɗan kyakkyawan saurayi.” Jiyo hakan dayayi ne ya sakashi juyowa inda yake tsammanin zaiga wanda yake wannan batu amma saiya tarar babu wani a kusa,hakan ta sakashi waige waige yana kokarin ganin mai wannan magana, aiko sake rudewa yayi bayan ya jiyo an sake cewa dashi

 

“wai shin wa kake kokarin dubawa ne,shin ka manta mu biyu ne kacal muka fado nan?.”

Karanta Littafin Dogon Yaro

Sake waigawa cikin rudewa da yayine ya saka wai wannan magana ya fahimci tuntuni shi ake kokarin dubawa sai yace dashi “Malam daina wahalar da kanka domin gani nan a tanan gurin.” Duk da fadar hakan Eshan bai iyya ganin sa ba har sai da yaji an ja masa wando hadi da furta cewar “sauke Idanuwa ka kasa.” Kafin nan ya sauke hade da ganin wanda ke wannan magana,aiko bayan yayi arba da mai magana wannan magana ya buga bagidajiyar kara hadi da kamewa gefe guda

 

“Yadai Yau kuma abin tsoro na zama?.” Tambayan da wannan abin yayi masa kenan “Mai kake nufi,kenan munsan juna kafin Yanzun?.” Gwauron nishi wannan abin yayi hadi da salatin Manzo kafin nan yace dashi “kenan babu abinda kake yiya tunowa dame da abinda ka aikata jiyan ko kuma sabon salon rainin hankalin ne kazomi da ita,Eshan yafa kamata ka tuno abubuwan da suka faru da kai domin itace kadai hanyar da zaka komar damu a inda muka fito.” Wannan abin na kan Surutan nashi sai Eshan ya fara wasu batutuwa cikin raɗa yana mai cewa “hakan na nuna cewar duk abubuwan nan da na gani game da lambu da kuma wancen kogon zahiri ne bawai mafarki ba?,kuma nakan iyya jiyo maganar dabbobi hakan ta faru ne bayan daukewar ruwan sama lokacin da na taka izuwa waccan lambu amma bayan nan kuma maiya faru?.”

 

Wannan wanda ke bashi labarin ko ba kowa abane illa farar ɓera 🐀 mai dogon jela,da dukkan alamu wannan ɓera shegen bakine dashi Danko tun dazu yake ta zuba dukda cewan Eshan baya sauraran sa, gaskiya babu shakka shine dalilin da yasa Eshan buga ihu bayan yayi arba dashi.

 

“Shin maike shirin faruwa da nine?.” “Mutuwa!,mutuwa ce wacce take shirin faruwa damu Eshan.” Haka wannan ɓeran ya basa ansa sannan ya sake da cewa “zuwa awani biyu nan gaba dukkanin mu zamu babbage dan zunzurutun zafin rana,Eshan Sahara ne fa muke ka fahimci hakan mana.”

 

Haka wannan ɓeran ya basa ansa shiko Eshan tsunkuyawa gaban sa yayi hadi da ce masa “Toh yakai dakiki kuma abokina ɓera ya kamata na fara tuno abubuwan da suka faru dani jiyan tukun kafin nan nasan meye mafitar, akwai wani abinda ke shirin faruwa dani,da fari lambu sai kuma bindigogi da kuma wata ƴar kyakkyawan rayinya.”

 

Aiko da jiyo batun nasa sai yace dashi “bindigogi da kuma lambu? Babu wanda na sani daga cikin su,meye hakan ke nufi?.”

 

“Shine nima nakeso na fahimci wani abun akai.” Haka Eshan din ya basa ansa shiko ya buɗi baki yace dashi “Ruhin Haske!.”

 

“Ruhin Haske kuma?.” tambayan da Eshan yayi kenan inda ɓerar yayi saurin hayewa kafaɗar sa hadi da ce masa “hastabibiya ce kuma bokanya ce domin babu abinda nake tunowa daga abubuwa data furta na tsoro jiya illa Ruhi da Kuma haske.”

 

Aiko da jiyo wannan wannan furucin sai yayi shiru alamar nazari,haka Eshan ya soma tuno abubuwan da suka faru dashi daren jiya kama daga zama da yayi akan ruwan sama har zuwa lambun da yayi sannan ya tuno kokarin kare rayukan Yusra da yayi aiko cek ya tsaya a lokacin nan daya sume.

 

a lokacin da wannan tsohuwa ta jefa Yusra cikin Ramin kuwa kama hanyar komawa ga Eshan tayi hakan kuwa sai tayi daidai da lokacin da Tawagar Malik suka shige gidan su Zain kasancewar Eysha ce kadai ta shige gidan hakan ya dauke ta lokacin mai tsawo tafin ta gama bincike dakunan gidan banda wanda Zain ke kwance ciki,bayan tayi hakan saita tsaya kallon dakin da Zain din ke kwance ciki,domin tasan idan akwatin bai samu a gidan nan ba toh hakan na nuna cewar akwatin tabar wannan kauyen,haka ta taka ta bude kofar inda take tsaye kuwa tana iyya kallon komi na wannan daki amma da shike akwatin ta fadi wa dattijon ta dayan bangaren gadon ne shine dalilin da yasa ka bata iyya hangowa daga inda take tsayen..

 

aiko niyyar sa kafa tayi sai tajiyo an tabo ta a na’urar dake makale a kunnen ta na dama “We got a accompany.” Abinda ta jiyo ta ciki kenan inda tayi saurin juyawa da baya hadi da cewa “what do you mean by that?.” Awais din yayi saurin bada ansa yayi “Gafur Squad!.” Aiko da jiyo hakan Malik yayi furucin “Bala’i,let move to plan B.” Ciki sauri ta fice daga gidan ba tare da ta bincike dakin Zain ba.

See also  Hausa Novel Wattpad Documents

 

Al’amarin wannan tsohuwa kuwa taku take cikin takama hatta karasa inda Eshan ke kwance da zuwan ta gurin ta fashe da muguwar dariya.. hadi da cewa “daga karshe saiga wanda na ɗibe shekaru da dama ina jiran baiyanar sa ya taho har inda nake ASHRAF _the Protector_ maraba da zuwa duniya ta.” Bayan ta furta hakan saiya sake fashe da muguwar Dariya a karo na biyu sannan ta juya ta wuce izuwa wanta ƙatuwar kofa wucewarta saiga wasu fararen ɓeraye biyu sun baiyana yayinda suke tattaunawa da junan suko Suka tashi Eshan daga sumar da yake tattaunawan suna yine akan sunan nan da tsohuwar ta fadi ne wato Ashraf “shin Dan uwa kana ganin yadda ta hallaka wacce yarin yar haka shima zata hallaka shi?.” “Toh wayasan abinda ke ranta bamu da ta cewa mu namu ido ne.” Aiko kafin wannan ɓera ya rufe baki sai yaji Eshan yace dashi “wa aka kashe kuma wa ake kokarin kashewa?.” Aiko da jiyo haka ɓerayen suka buga uban ihu hadi da Rugawa a guje.

 

Eshan ba tare da ganin wanda ya jiyo maganar daga garesa ba ya mike yayinda yake jin kaman an narka masa uban duka domin duk jikin sa babu kwari yanaji kasala, aiko sai dayayi tafiya mai nisa cikin wannan guri kafin nan yaji an anbato wannan sunan wato Ashraf hadi kuma da cewa “ina ne kuma zakaje dan uwa bayan bamu gama aikin ba?.” Aiko juyawan da yayi saiya tarar da wannan Tsohuwa a tsaye bayan sa da murmushi a fuskanta yayinda take kallon Fuskan Eshan.

 

aiko suna kan hakan sai suka jiyo muryan Yusra na ihun naiman agaji yayinda ta kasance marne jikin ramin,da jiyo hakan sai wannan tsohuwa ta haɗa fuska hadi da cewa “taya hakan zata kasance.” Eshan juyowa da niyyar bin inda yake jiyo wannan kara yayi amma sai wannan tsohuwa tayi Surutan tsafi Nan da nan sai hanyar ta like haka Eshan ya sake kokarin canza hanya amma still hakan ne ya sake faruwa,aiko juyawan da Eshan zaiyi sai taji wata iska mai karfi gaske ta haɗa ta da bango yayinda ta ɗaga idanunta izuwa Fuskan Eshan ko sai ta kalli Idanu sa ta juye izuwa fara wacce babu ɗigon baki a ciki da ganin haka ta mike tsaye hadi da cewa “put it on Ashraf.” Aiko bayan ta furta hakan sai ta sake da cewa “hakan ne ya tabbatar mini wannan shine wanda Duniya ke jiran zuwan sa.” Babu bata lokaci wannan mata ta ɗaga tafukan hannayen ta sama nan da nan kogon tahau girgiza kaikace girgizan kasa ake amma ko Yar karaman yatsa da Eshan ya daga sai hakan ta tsaya cek,yin hakan da Eshan yayi ne ta hassala tsohuwar ta soma kai masa hari da dogayen faratun ta kaikace daga China ta fita,haka suka gwabza na tsawon dakiku kafinnan Eshan ya shige jikin bango Itako ta fasa bangon da karfin tsafi,ta naimi Eshan ta rasa hakan ko ya saka ta haɗa fuska nan da nan ko’ina na wannan guri ya kama ci da wuta haka ta rikiɗe izuwa bakin hayaki yayinda take biya ko’ina tana buda shi,tarar dashi tayi yana kokarin ciro Yusra daga ramin nan ta sake komawa suffar ta na ainahi ta sake kawowa Eshan hari haka sukayi ta zibgar juna a wannan lokacin kuwa Yusra ta iyya kare masa kallo domin lokacin da yake kokarin cirota daga ramin fuskarsa kawai ta zubawa ido..

 

MALIK SQUAD

Zuwa inda suka tsara zasu hadu ne Eysha tayi inda ta tarar da Malik kadai da zuwan ta tayi furucin cewa “ina Awais din?.”

 

“Tunanina tare zaku taho.” Aiko da jiyo hakan Sai tayi saurin kai hannu a kunnen ta inda ta danna wata madanni dake na’uran kunnun nata ta soma cewa “Awais! Awais! Kana sauraro na Awais kana kan layi?.” Bayan ta furta hakan har sau uku kafin nan ta jiyo Awais na magana cikin raɗa yayinda yake cewa “sun Rutsa dani,suna kewaye da gidan da nake ciki.” Aiko da jiyo hakan ta zura Idanu inda Malik yayi sauri anso wayar daga hannun ta ya soma cewa..

 

“New Plan sauya shiga ta bakin kaya ka shige cikin tawagar su yayinda mu kuma zamu janyo hankalin su izuwa wani gun na daban,zamu bika a baya karka damu babu abinda zata same ka.”

Aiko da jiyo hakan Eysha ta kwace wayar dake hannun sa hade da cewa..

 

“You’re risking his life,Malik what are planning to do shin hakan kake kokarin punishing nashi?.”

 

“Calm down I know what I’m doing.” Haka ya Bata ansa inda tayi saurin cewa “You don’t,Taya zaka turo sa cikin tawagar wayenda ke naiman mu sannan kace zamu ceto sa taya hakan zata faru ne wai?.”

 

Haka Eysha ta soma kara tana surutu akan abinda Malik ke kokarin aikata shiko Awais shiga yayi irin tasu wato bakar suit da pick up da kuma face marks da shike tuntuni kayan na jikinsa kawai cire na sama yayi saiga bakar shigan ta baiyana haka ya fito cikin sanɗa ba tare da wani ya gansa ba ya shige cikin tawagar inda yaje dab da inda shugaban zugan ke cewa.. “dukda cewa bakar tsafi yayi amfani dashi wajen kubutar da yariyar ina kwatata zaton bazasu wuce wannan ƙauyen ba dan haka ku naimo ta.”

 

Tirkashi ana wata ga wata shin mai zai faru idan suka tarar da akwatin a gidan su Zain Kuma meye zai faru da Awais shi dayayi basaja a cikin su?

 

Haka suka soma bi gida daya bayan daya yayinda Awais ya ga alamar ba su akazo naima ba sai yayi takaicin karban shawaran da Malik ya basa haka suka wahalar dashi domin kowace gida sai sun shige sun tashi yan gidan.. Karar harbi ne yasa Malik da Eysha suka taka biriki yayinda wannan kara kuma ta tayar da kowa dake wannan kauyen daga bacci,Kuma hakan ta faru ne a wani gida yayinda mai gidan yake kokarin basu Hard time Suka harbeshi.

 

Cikin sauri wannan dattijo wanda yake kula da lafiyar Zain ya fito daga dakin sa,inda yaje dakin zain ya rufe su a cikin,zama yayi gefe guda bayan yayi arba da zain a kwance domin tunda yake bai taba ganin Zain na bacci cikin kwanciyar hankali irin ta yau ba…

Hakan kuwa tayi matukar kwantar masa da hankali ya kuma manta maiya kawosa dakin nashi…

 

Idan muka Laika Ɓangaren su Eysha ko kokarin dawo baya take sai Malik ya rike mata hannu…

“What Are You planning to do Eysha?.”

 

“Zuwa zanyi koba komi na dauko gawarsa, sannan na nisantar da kaina daga makashi irin ka domin kaine wanda ka hallaka shi yanzun.”

 

“Calm down nasan it’s hard but ya kamata ki amince dani domin sauyawar plan failure ne a gare mu…”

 

Dajiyo hakan kuwa ta zaro bindiga hadi da cewa “babu abinda zata saka na sake amincewa dakai saina daukar masa fansa.”

 

Aiko kafin ta harba wannan bindiga sai Malik ya kama bindigar ya daga sama yayinda tayi harbi a sama saiya sareta da hannu a wuya aiko karatu guda ta sume ta fadi kasa,nan da nan ya daurata a kafada suka wuce… Tawagar nan da Malik ke cikin suko jiyo karan Harbin dasukaji ne yasa suka fice a guje izuwa inda suke tsammanin zasu tarar da wayenda sukayi harbin,a wannan lokaci kuma tsayawa Awais yayi suka wuce suka kyalesshi a baya ba tare da ko daya daga cikinsu yasan hakan ba.

 

ESHAN

wuta ne keci ta ko’ina yayinda suke kaiwa juna sakon tsafi nan sai Eshan ya soma jiyo muryoyi masu tarin yawa na bukatar taimako aiko bai fahimci yana jiyo hakan daga dabbobi kuma ɓeraye ba har saida wannan tsohuwa ta haɗashi da kasa kafin nan… Ya fahimci hakan. Ganin yanayi da suke ciki na gobara ne yasa Eshan bude tafin hannayen bayan ya mike tsaye,kamar wani mai addu’a ya bude tafukan hannayen sa sai Ruwa ta soma bubbulo daga cikin kasa kuma kusa da inda kafafunsa ke tsaye.

 

yadda kasan ruwa yayinda yake zubowa daga fumfum haka take bullulowa daga kasan yana kuma tashi sama ya na kaiwa kusa da Fuskan sa ko sai yayi anfani da hannayen sa wajen sarrafa ruwan cikin kankanin lokaci gabakiɗayan gurin ya jike sharkaf yayi ruwan ya kashe wutan kuma yayi anfani da Ruwan wajen daskarar da wannan tsohuwa jikin bango iyakan kanta ne kurun ke motsawa.

 

Aikuwa komi data faru a gaba taru ɓerayen ta faru hakan ko ta faru daddai lokacin da Eshan ya magance matsalolin nan biyu wato tsohuwan da kuma gobaran sai daya daga cikin ɓerayen maia tarin shekaru ya furta cewa.

 

“ASEEM the Guardian jinjina a gare ka.”

Aiko da jiyo wannan suna Eshan ya rude Taya ake kiransa da mabanbata sunaye a daidai wannan lokaci kuma daya daga cikin taron ɓerayen ya ruga izuwa Ramin su Eshan ko a kiɗime yake saiya sake jiyo muryan Yusra na naiman tallafi haka yaje yana kokarin ciro ta sai wannan tsohuwa ta narkar da kankaran da take ciki ta sauka hadi da dauko wata ƙatuwar takobi ta nufi inda Eshan yake,aiko ganin hada da beran wanda ya ruga cikin ramin yayi sai yayi ihun kiraso Sunan Eshan cikin kara, juyawa da Eshan zaiyi saiya tarar da wannan mata na kaimasa sara aiko sa hannu yayi ya tare sannan ya shuri matan da kafa hakan sai tayi daidai da karasawan wannan ɓera izuwa kafaɗar sa hade kuma da baiyanar wata haske mai kamada tsartsatsin wuta yayiwa Eshan ɓerar da kuma Yusra zobe da ganin haka da tayi tasan hanyar guduwa ne Eshan ke naima musu shiyasa ta ruga a guje ta kaiwa Eshan yamusa a Fuska domin takobin dake hannun ta tuni ya narke,kaucewar da Eshan yayine yasa yamusar ta koma kan Yusra wacce jininta ya fesu a Fuskan wannan tsohuwa aiko buga ihu tsiya ta tayi bayan faruwan hakan hadi da rufe Fuskan nata da hannu biyu suko Eshan suka bace kamar walkiya tare da ɓerar da kuma Yusra.

 

Aiko tundaga wannan lokaci bangarorin nan uku wato Eshan, Eysha da kuma Zain Babu Wanda ya farka a cikinsu sai wayewar gari farkawar Eysha tayi mamaki ganin Awais gefen ta farkawan Zain Kuma ya tarar da wannan dattijo ko nace kakansa na bacci a gefen sa inda ya sanar da kakan nasa kamar haka bayan farkawan kakan nasa shima.

 

“Na ɗebi shekaru da dama ina mafarke mafarke akan ababen tsoratarwa kaka,kuma nakan tarar da mutane da dama cikin mafarke mafarken amma duk cikin su babu wanda ya taba tallafimi ko yayi kokarin ceto ni daga hannun ababen nan sai yau na sami wani mai suna Eshan,yayi kokarin cetoni daga hannun su gaskiya inason nasa shin waye ne haka?.”

 

Eshan kuwa shine ya farka a karshe kuma a sahara tare da farar Bera mai Surutun tsiya…

“Bera na tuna komi,hakan kenan ba mafarki bane?.”

 

“Malam saurayi idan da a mafarki ne da acen mafarkin zaka baro Ni ehe,Bama wannan ba ya kamata ka samo hanyar mayar dani ga ahali na domin godiya ma yakama kayimin dan mayar maka abinda kani na ya cire cikin aljihun ka nakeyi amma sai gashi ka jaguboni izuwa wata duniyar.”

 

“Meye abin?.” Tambayar da Eshan yayi masa kenan inda ya mayar masa da cewa..

 

“Wata farar abu mai kanshin tsiya,ya dauko.”

Aiko bai karashe furta hakan ba ya buga ihu hadi da marnewa jikin Eshan, Eshan ko ba tare da ya ga abinda wannan ɓerar ke yima ihu ba ya ruga a guje suna tsakiyan shekawa da gudu sai Eshan yaji kof daya shaho 🦅 yayi gaba da ɓerar dake kafaɗar sa aiko taka biriki Eshan yayi hade da wangale baki dakuwa ca yayi kura ko damisa ɓerar ya gani yayi wannan uban karan koda shike shaho shine Kura ga kananun halittu irin wayen…

 

“Shin wai yanzu Ni zan taimaka masa kenan?.”

Haka Eshan ya futar bayan ya jiyo ihun naiman taimako da ɓerar yake a garesa tuni ya ruga da gudu yana binsu a baya ganin yayi kusa da sune ya sakashi buga ƙasa da ƙafarsa daya tuni ya tashi sama kai kace tashiwar rocket Aiko sai dayayi kusa da ceto ɓerar sai yaji wata jar kelle ta naɗe Masa sawu an kuma jawa sa da karfin tsiya ya fadi kasa..

 

Aiko bayan kura ya lafa saiya tsinci kansa a gaman wasu tarin mutane Yan mata da kuma samari cikin shiga ta jajayen kaya dogayen, hannayen da kuma mayafin wannan riga suna da matukar tsayi wacce nake kyautata zaton dashi aka jawosa kasan.

 

Maza da matan sun kasance sun rufe kawunan su da kuma fuskokin da wannan kelle kuma ana iyya ganin fuskokin nasu ta ciki wannan kelle dan shara shara ne Kellen hakan yasa Eshan ya iyya gane dakwai maza a tawagar tasu amma Banda haka dako zakace duk jansi dayane.

 

Jagaban wannan zuga dake tsaye a baya tattaki tayi har gaban Eshan sannan ta yaye Kellen dake fuskarta hadi kuma da cewa

 

“TANVEER the Rays of light muna maraba da zuwan ka.”

Bayan ta furta hakan tayi gajeriyar murmushi.

 

 

*EPISODE 04 PREVIEW*

“Ka sani bazaka kare rayawan ka wajen tserewa mutane ba domin even if you keep running away millions will find you.”

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top