Hausa Novels

Sihirtaccen Ikoh Hausa Novel Complete

Sihirtaccen Ikoh Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SIHIRTACCEN IKOH

 

_PAID BOOK_

*300*

*_VIP 500_*

Katin waya:

*09133307121*

Account number:

*9303372002*

Domin nema k’arin bayani

09133307121

 

“`WRITTEN BY:“`

*_NANA KHADIJATU KHADMAH_*

*_(K_SHITU🦋)_*

 

_Assalamu Alaikum_

_Masoyana Gsky naji dad’in yanda kuka karb’i Littafin sannan Zakuga nasanya nanakhadijatu KHADMAH eh Da k_shitu din duk nice so koda kunga KHADMAH nice amma sai idan akwai nanakhadijatu._

 

_*FREE PAGES*_

_D’AND’ANO_

 

“`GARGAD’l:“`

_Banyar da wani ko wata ta saura mun littafina ta kowace siga ba batare da izinana ba._

 

_Bismillahir rahmanur rahim_

 

Chapter:

*1_2*

 

*_________________*

“Mafarin k’addarar ya farane, tun sanda kakata ta d’auki tulun ta fasa”…..tun daga wannan lokacin shed’anu ke bibiyar rayuwar mu ,Anci galaba akan kaka ta sai mahaifiya ta,saini _ZOYA_ wacce ake bibiyar rayuwata,Anchi galaba akan kakata da mahaifiyata, saini _ZOYA_ ina da shekara 17 wacce ake bibiyar rayuwata, mahaifiyata tayi nasarar hambud’e wani shaid’ani, bayan shekara 4 Fatalwar sa ta dawo d’aukar fansa A ranar da ta haife ni ranar ta mutu.IKUNAN sun Kasance kwaya ukku Ikon sharri na biyu shine ikon dake dauke da wani zobe acikin tulu, Ranar da kanaka taga tulun ta fasane, Wani babban malami ya tabbatar mata da cewa,Tabbas wannan tulun data fasa akwai ikoh n abiyu Aciki, saidai k’arfin ikon ya hana bayyanar zoben, don ahalin yanzu zaben yabar tulun saidai abund tayi shine ta k’ona b’aren tulun. Nan take taje ta k’ona amma dayake, Abun bauta yariga da yace dole saita bar wannan duniya Sai tabar b’urb’ushin tokar Wani Shaid’ani yazo daga wata duniya ya KAWO mata farmaki, tunda ya Kawo mata wnn farmakin, ba’a sake ganin ta ba Mahaifiyata kuma ta kasace cikin bak’in ciki da damuwa, abunda bata saniba shine shed’anin nan yana bibiyar rayuwar ta itama, Wata Rana taje Majami’a yin Addu’a taji wani babban malami yana fad’in shed’ani na bibiyar rayuwar ta dandanan cikin yayi sanyi tace to ngd bbn mlmi amma miye abunyi, daganan yabata wata hodar sirri yace duk sanda ya bayyana gare ta tayi gaggawar watsa masa.

 

….….……

Daga nan ta amsa ta dawo gidan kwatsam rannan ta zaune taji dariya Saita mik’e cikin gaggawa tace “Waye kai idan ka isa ka bayyana kanka na ganka” Wata guguwa ce mai had’eda isa suka rikid’e suka zama wata mummunar, halitta Cikin gaggawa ta watsa masa hodar srrin nan danan jikinsa yafara k’onewa yana ihu saidai Abu d’aya daya fad’a ya girgiza ahalin mu don dama sunsan komai ta musu bayani, yace “Tabbas! kunyi kuskure kunyi kuskuren hambad’e ni Amma kusani Tunda sannan ahalin kukayi kuskuren fasa tulun tsafi toh Ku zaku kammala wannnan Aikin” Yana gama fad’a haka yaza toka Aka tattara guri d’aya aka yi rami d‘akin addu’a aka ajiye….

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

Tun daga wannan lokacin mutane suke rad’erad’in wai mahaifiyata shed’aniya ce, bayn shekara 4 hud’u ta haife ni ta mutu, daga nan muka tatara muka bar k’asa zuwa wata ta daban. Tak’aitaccen tarihina knn.

 

IKUNAN sun kasance, Duk Wanda ya mallake su zai iya mulkar duniya gabad’aya Ikon sharri na FARKO ya kasance wata hulace ta IKOH,wani shaid’ani shiya fara mallakar, hular…IKON sharri na BIYU ya kasance Wani zone ne Mai D’auke da sirri ka Zoben Ya kasnce, hannun wasu shed’anu IKON sharri na UKKU ya kasance wata Sarauniya Ce mai Wata Sark’a….Bayan wani lokaci akayi fad’a kowane IKOH ya b’ace anata Neman su, saidai dukkan ikunan bazasu iya Zama SIHIRTATTU ba face ansamu _DAIWAN_ Shine mahad’in IKUNAN…… Yayin da Ni Tunda ahalin my suka bar Ainahin k’asar mun don samun kwanchiyar hankali duk wannan labarin na sameshi ne ta hanyar Kawu na don Ahalin mu babu Wanda ke sha’awar a tado lamarin… Firgitt ta dawo daga duniyar tunanin data shiga sakamakon, wata mata data zauna kusa da ita, kallon ta tayi tace ”Yarinya kema _MAHYAN_ kika nufa ne?” D’aga mata kai tayi tace “Eh” Daganan ta maida idon ta Cikin ruwan don Tunda suka hau kwalakwalan take jin k’ishirwa don jiya tashanye ruwan ta Kamar wannan matar tasan abunda me ranta tace “Ga ruwa idan zaki sha” Da sauri ta dube ta tare da sannu ta karb’i ruwan…..bayan ta sha tace “Nagode Sosai” Murmushi ta sakar mata tace Amma baki fad’amin sunan ki ba” Y’ar dariya tayi tace “sunana _ZOYA_” Kafin ta rufe baki mutane suka zazzagaye, ta sunata hayaniya ’Gaskiya kina da kyau sosai ki d’an k’ara yin dariyar’ A dole suka sakata taita kwasar dariya sukuma sunata tattab’e mata fuska……

 

KHADMAH CE

SIHIRTACCEN IKOH

 

 

WRITTEN BY:

*_K_SHITU🦋_*

 

*_GAMJI WRITERS ASSOCIATION_*

_Home of exceptional writers_

 

Paid book

_300 VIP 500_

_*09133307121*_

 

 

CHAPTER:

*3_4*

 

*_________________*

Da k’yar tasamu, suka rabu da ita don har ta farajin wani iri sakamakon hayaniyar da sukeyi, da dare Ta kwanta kenan wani mutumi shima yazo ya kwanta kusa da ita hatta mai Tafiya da jirgin ruwan yana yi yanai mata surutu…WASHEGARI ta tashi cikin tsantsar farin ciki don kuwa sun iso k’asar su Dan tsabar d’oki ko Abinci ta kasa ci burin ta kawai taga mahaifin ta da Ariya, Dai-dai Bakin wani k’aton Ruwa suka tsaya mutane kowa ya fara fiffitowa, Allah ya sani tana son zama gidan yayan nata Amman tana son tazo taga gida shiyasa…Fitowa Itama tayi dai² kakar baban ta da su baban ta da dai sauran Ahalin su baki d’aya suka k’araso,Cikin Tsananin murna ta k’araso, ta rungume jikar tata, cikin murna tace “Tsohuwa adai Bini A hankali kar a kakkaryani ko?” Dariya duk sukayi banda tsohuwa wacce ta had’e fuska tace..”Amma lallai yarinya ki dubeni duka dukana Ina ni ina karya k’atu irin ki”….dariya tayi tace “Amma ya Akayi banga _Ariya da Y’ar’uwa janki_ ba?” dafe kai tsohuwa tayi zatayi magana mahaifin _ZOYA_ Yace, “y’ata lallai ba kiyi kewar mu ba don tunda kika iso ko gaisuwa bamu samu ba kin biyewa tsohuwa kin barmu tsaye ko?” da sauri tace ”A’a baba ba haka bane kasan mun dad’e bamu had’u da tsohuwa ba shiyasa” daga haka Suka Hau dawakai suka nufi hanyar gidan su….

 

Suna shiga ta bud’e murya tace “Ariya Ariya”! Janki Ce tafito tasa wani mayafi ta rurrufe fuskar ta tace ” Wa nake gani kamar zoya!” Rungume ta ZOYA tayi tace..”.Ita ce yar ‘uwa nayi kewar ki da yawa””Nima haka yasu yayan naki da fatan duk suna lfy ko?” Eh lafiyan su k’alau duk sunce A gaishe Ku “Y’ata zaki fara cin Abinci ko wanka zakiyi tukun?” Tsohuwa tace “Bacin rashin tsafta irin naki Ai gwara ta fara wanka ko, Ku Kuma Ai zoyar ta dawo sai Ku kama gaban Ku” Girgiza kai tayi tace ”kina nan dai da halin ki Ashe tsohuwa” tsohuwa zata sake mgn Janki taja Hannun ta suka nufi Wani d‘aki Suna Shiga _ZOYA_ ta fad’a bisa gado tace “Y’ar uwa Janki ki ajiyemin jakar kayana anan bari nayi wanka”…..

 

Fita Janki tayi don kawo mata abinci taci, Tana shiga madafa ta d’ibo mata Abinci kala² Ta Ajiye knn taga wani littafi ya fad’o daga cikin jakar kayan _ZOYA_ Hannu tasa ta d’auka da k’arfi tace “Littafin _SIHIRTACCEN IKOH?_” ‘Eh shine miya faru, ‘yar’uwa?” cewar _ZOYA_ d’an saita kanta tayi tace “babu komai amma a ina kika same shi?” Cikin basarwa tace “Wata k’awata ta bani shi.” daga haka taja bakin ta tayi, shuru ita Kuma ta fita cikin sauri tabar d’akin.…………

 

Bayan taci Abinci ta huta ,janki ta shigo ta sameta Da wannan littafin A hannun ta saidai wannan karon, karantawa takeyi, k’arasowa kusa saita tayi tace

“Ya kin huta ko?” d’aga mata kai tayi alamun E zama tayi sai sannan ZOYA ta kalleta tace….

 

“y’ar uwa idan babu damuwa inaso na d’an tambaye ki”

 

”babu damuwa ki tambaye ni‘‘

 

…..’’dama inaso naji shin daman, A lokacin da kakata ta b’ata Anyi kyakykyawan bincike akai?.‘‘ dubanta tayi A zuciyar ta tana mai kokonto anya zoya CE wannan amma saita basar tace…”E Tabbas Anyi bincike sosai Amma ba’a gano ta ba Dan haka muka hak’ura.’

 

“Toh amma daga nan miya faru da Ahalin mu?”….

 

Nisawa tayi kana ta kalli bakin k’ofa don San gane ko ba kowa “A lokacin da ta b’ata munyi iya bakin k’ok‘arin mu amma ba’a ganta ba Dan haka muka hak’ura, bayan mutuwar mahaifiyar ki muka tattara muka dawo nan da zama harzuwa lokacin yayan ki yayi Aure ba’a sake jin d’uriyar ta ba nayi bincike sosai har na hak’ura Dan malamai sunce idan muka matsa da bincike shaid’anu zasu iya dawowa ciki, rayuwar mu, Dan haka aka rude wannan labarin, kuma aka gargad’i kowa kan fad’a miki”..nima abunda yasa na fad’a miki nasan kin Riga da kinsan komai shiyasa…..

 

“Toh amma.”

 

”Karki ce Komai wani zai iya zuwa ya tarar damu.”

Bayan fitar zoya ta shiga nazari don ta karanta cewa mamallakiyar SIHIRTACCEN IKOH na ukkun sarauniya ce wacce take amfani da mutane musamman ma k’anana yara ta mayar dasu k’adan garu…Haka dai taita saqa da warwara har ta yanke hukuncin bari sai gobe,tasamu mafita, A ranta tana tunani anya Janki zata taimake ta……

 

comments nd shareMuna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Sihirtaccen Ikoh Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!