Silar Fyade Hausa Novel Complete

Silar Fyade Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Silar Fyade Hausa Novel Complete

*SILAR FYAƊE*

Free Book

 

 

 

NA

UMMU MAHER(MISS GREEN

 

*MARUBUCIYAR*

 

1 UWAR GIDA NA

3 AUREN DOLE

4 RUHI ƊAYA

5 FAROUK

6 INAYATULLAH

7 ASANADIN ABAYAR SALLAH

8 AKAN AIKINA

9 JAMILA

10 DR NAWWARA PAID BOOK

11 DARASI PAID BOOK

12 SILAR FYAƊE FREE BOOK

 

 

 

Bismillahir Rahmanir Rahim

 

 

 

 

1-2

 

 

 

. . . .Kuka na ke kamar raina zai fita tsabar tashin hankali,wai yau ni ce agaban gawar mahaifiyata ina kallonta bata numfashi,wani irin ihu na sake sakawa ina girgiza Ummana cikin kuka na ke ce wa”Ummana don Allah ki tashi kada ki mutu,in dai da gaske ne kin mutu to nima tabbas mutuwa zanyi”.

 

 

“ke wai wacce irin mahaukaciya ce?saboda uwarki ta mutu sai ki saka mutane a gaba kina wani kukan banza?to wallahi ba a gidannan ba,banza karuwa wacce ta bawa wani ɗa namiji jikinta ya yi mata ciki,ai gashinan yanzu kin kashe uwarki da baƙin ciki kinzo kina wani kukan banza da wofi”.

 

 

Da sauri na jiyo da idanuwa na da sukayi jawur kamar wuta,tsabar tashin hankalin da na ke ciki bai saka na mayarwa da Maman Nusaiba amsa ba,sai ma ba da ƙaimi da na yi akan kukan da na ke yi,don dole suka fita suka ƙyeleni sai da na yi mai isata sannan na yi shiru,ɗan ciki na naji yana ta motsi kamar zai fito wanda tun da na samu cikin baiyi motsi mai ƙarfi haka ba.

Ina ji ina gani aka fita da gawar Mamana,a duk cikin mutanen da suka zo ta’aziyya babu mai rarrashi na, ni kaɗai na ke kuka na ina share hawaye ranar yini na yi banci ba bansha ba,ƴan uwan Mama na suka kawo abinci katan katan suna ta sha’aninsu ɗaura wannan ɗaura wancen,ni dai ina ɗaki ina tunanin rayuwa ta,a shekaruna da basu wuce 15 ba naga rayuwa kala kala.

 

Ina ɗaki naji Baba na yana ƙwala min kira,da sauri na fito jiki na sai kakkarwa ya ke saboda rashin cin abinci ga juna biyu a jiki na.

 

“Ke dan iskanci shine ki ka shige ɗaki ki ka ƙwanta uban waye zai yi miki duk wannan aikin da jama’a su ke maza fito ayi da ke,banza ballagaza kawai yaja wani dogon tsaki ya fita.

Ko da na fara aikin wani irin mugun jiri ne ya dinga ɗiba na ina daurewa don nasan halin Baba yanzu zai dawo,a haka har na gama tatar ƙullin kokon,ina tuno da mahaifiya ta ina ta kuka mai ciwo.

 

 

 

 

 

 

* * *

Karin wasu littafai da zaku so

 

 

“Girke2 ake a gidan kana shigowa zaka ji ƙamshi ta ko ina,masu aikin gidan kowa da aikinsa,gida ne ƙaton gida mai ƙyau d tsari kana ganin gidan kasan gida ne na masu kuƊi sosai.

 

A tsakiyar garden ɗin gidan an saka wata mat ƙatuwa doguwa wacce zata sada ka da cikin gidan mai ɗauke da sunan,WELCOME MY LOVELY SON.

 

 

Hajiya Barakat ce ta ke ta zagaya gidan tana ganin irin decoration ɗin da aka yiwa gidan,wanda ya yi tace ya yi wanda baiyi ba ta ce bai yi ba.

 

 

Da wuri ta saka ƴaƴanta a gaba ƴan mata guda uku masu suna,Zeenat,Rabiat,Aisha,Fatima.

 

 

Suka tafi taro babban yayan nasu sojan sojoji wato admiral Aliyu Muhammad,A.A M.

 

 

 

 

 

 

 

Miss green ce

*SILAR FYAƊE*

Free Book

 

 

 

NA

UMMU MAHER(MISS GREEN

 

Wattpad user name

Rabiatu33

 

 

 

3 – 4

 

 

. . . . .Cikin ta kunsa mai kyau da tsari ya fara sakkowa a jirgin ,fari ne ƙal kamar zaka taɓa sa kaga jini tsabar farinsa,yana da jiki da kuma tsayi, ƙyaƙƙyawa ne shi ajin farko,yana sanye cikin wasu haɗaɗɗun ƙana nan kaya,waɗanda suka amsa sunansu ya cire cort ɗinsa ya riƙe a hannu yana gƴara necktail ɗinsa.

 

 

Ayshe ta fara hangosa ta ce”Hajiya ga yaya cen yana sakkowa,gaskiya yaya ya daɗa ƙyau wallahi gaskiya Hajiya yaya ya fimu Ƙyau”.

 

 

Rabiatu ta ce”ke kuma kina kishi ko?ke dai wallahi aisha kishi ne da ke wallahi,ke ce ki ka yo dangin Papa shuwa arab kishi ne dasu”.

 

 

Hajiya ta ce”kuyi wa mutane shiru zaku fara halin ko?”.suka ja bakinsu suka yi shiru ita daman Zeenat da Fatima miskilanci ne dasu irin Yayansu.

 

 

Zeenat tana da shekara 25,sai Fatima 22,sai Rabiatu shekara 19,sai Fatima auta mai shekara 17.

 

shi kuma babban gogan yana da shekara 35 a duniya,Har hajiya ta fitar da ran haihuwa sai kuma ta dawo ta haifi mata har huɗu.

Da sauri Hajiya ta ƙarasa ta rungume ɗanta cikin so da ƙaunarsa duk da sojojin da ke bayansa,shi kuwa jan zaki Aliyu Haidar kunya ce dashi sosai,don haka cikin kunya ya rungume ta,shi daman tun yana yaro kunya ce dashi,tun yana shekara 4 ya daina yadda mahaifiyarsa na yi masa wanka,sai dai ya rufe gabansa ta yi masa,haka har ya girma shi mai kunya ne.

 

 

 

Yana cikin cin abinci wayarsa ta kama ringing ɗin wayarsa,ya ƙi ɗauka Hajiya Barakat ta ce”haba son ka ɗauki wayar mana kaji ko menene?”.ta faɗi hakan cikin yaran yarbanci,shima cikin yaran ya ce “to momi”.

 

“Haba A/D ka tausayamin ka dinga ɗaga waya ta,kasan dai babu ƙyau wulaƙanta ɗan adam, please ka yadda ina sonka tsakani da Allah”.

 

“oky”.

 

kawai ya ce mata ya kashe wayar.

 

Salimat ta goge hawayen da suka zubo mata don matuƙar ba ta auri admiral ba komai zai iya faruwa,ya zamar mata dole Ƙara Ƙaimi wajen yin addu’ah don komai yazo da sauƙi,tana cikin wannan tunanin ta tashi ta shiga bathroom ta ɗauro alwala ta fara yin sallah tana kai kukanta ga mahaliccinmu subhanahu wata ala.

 

 

 

 

 

 

 

*** *** ***

 

yau aka yi 7 ɗin mahaifiyata dangi duk sun fara tafiya,har yanzu mutuwar mahaifiyata tana cikin ƙoƙon zuciyata,na share wata ƙwallar da ta cukomin ƙwarmin idanuna,na gogesu ina cigaba da ƙara tsanar wannan bawan Allahn da ya yi sanadin rugujewar rayuwar a halin gidanmu.

 

Ƙannena uku ne duk suna bording skull,Salimat,Afra,khadija.

 

 

Har lokacin kuma ba a gaya musu rasuwar mahaifiyarmu ba,ko ya ya zasuji idan suka ji mahaifiyarmu ta cika oho?.

 

 

ina cikin wannan tunanin naji an watsomin ruwan kanzo mai sanyi,don alokacin safiya ce,na waiga don ganin maiyi min wannan izayar,mmn nusaiba ce da kuma Hafsatu,wacce ta kasance ƙanwa awajen mahaifina.

 

Suna ta kumfar baki wai na iya munafunci na shiga ɗaki na ƙi fitowa don nasan na yi abin kunya.

 

 

 

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara fitomin a ƙwarmin idanuwa na,na gogesu na fita don yin aikin da suka ce zuciyata tana yimin ƙuna.

 

 

 

 

 

 

 

*miss green ce*

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.