Hausa Novels

Siradin Rayuwa Hausa Novel Complete

Siradin Rayuwa Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Siradin Rayuwa

Malam bilyaminu usman,haufaffen bafulatanin nijer a haihuwa da yare,ta wani fannin kuma d’an qasar *KAISA* kuma bahaushe magidanci mai halayya da dabi’u da al’adu irin na wasu daga bara gurbin hausawa,wadanda basu gama fahimtar abinda addini yayi magana akai ba kan iyali da haqqoqinsu dake bisa wuyan dukkan wani magidanci,walau saboda jahilci ko kuma sun take ne da gangan bisa son zuciyarsu da soye soyen rayuka.

 

Haifaffen agadez iyayensa dukkaninsu suka kasance xallar fulanin niger,fatauci da neman kudi yakawoshi qasar kaisa,wanda a yanzun ita tazame masa mazauni na dindin.

 

 

Shiga da saninki kusan shine laqabin da mutane suka yiwa gidansa bayan da halayyarsa tafito qarara na auri saki,mutum ne ma’abocin aure aure,wanda har hakan yazame masa jini da tsoka,bai kuma daukeshi a wani abun aibu ko abun Allah wadarai ba,ya auri mata aqalla da suka doshi goma,wanda mafi yawa daga cikinsu kowaccensu tana da yara a gidan,walau maza ko mata.

 

 

Yana da tarin yara da suka kusa su ashirin da biyar,wanda dukkaninsu warin takalmi ne,mutum biyu uku uwarsu daban,harda masu mutun d’ai d’ai da uwarsu ta haifesu su daya tak cikin wannan gurguxu zuga da harqalla ta gidan,kamar yadda BILKISU take ‘ya daya tilo da mahaifiyarta tahaifa cikin gidan.

 

 

Kusan dukka wadan nan tarin yara nashi yara mata sunfi yawa,saidai mazan da aka soma haifa masa na farko farko mutum uku daga ciki sun tasa,babu wani batun samun sauyi salama ko tallafi daga tasawar da sukayi,domin suma kowannensu takanshi yakeyi,ci sha sutura ko muhalli mai kyau bai cikin tsarinsa bare akai ga jigo kuma uwa uba ilimi,hasalima za’a iya cewa baisan kwana da tashin wani cikin iyalinshi ba,kowa yana riqe ne da kanshi.

 

 

Saidai kash,dukka wadan nan halayen nasa hakan bai hana a bashi aure ba,a duk sanda tabusa mishi,ko ranshi ya raya masa,yayi katari da budurwa ko bazawarar da ranshi ya kwanta mai da ita,tofa bazaiyi qasa a gwiwa ba wajen zage qwanjinsa da qarfin aljihunsa koda qarfin aljihun wasunsa ta hanyar cin basussuka yakashe mata kudi yakawota gidanshi.

 

 

Dukkan matar daya aura takan fantama a lokuttan da take cikin amarci,takanyi yadda takeso,takumayi yadda taga dama,saidai kuma da zarar wannan dama ta subuce daga hannunta shikenan itama zata shiga sahun ‘yan ci dakai da neman na wanki da wanka,wanda hakan kan sanya wasu kasa jurewa,wasunsu sukan kai harsu haihu,yayin da masu zuciya a kusa,masu qarancin haquri kan tafi da ciki su haife a gida,bayan wani lokaci su dawo masa da yaro ko yarinyar da aka samu.

 

 

Cikin dukka matan daya aura mutum biyu ne tak suka iya jumurin xama dashi,mace tafarko itace kattume,wanda itace matarsa uku daya aura,tana da yara a gidan balaifi,hakanan takama sana’a ka’in da na’in,tana daukan nauyin kanta dana yaranta,hakanan cikin yaran takan yiwa wanda taga dama,hatta shi kansa malam bilyamun wani lokaci yakanci cikin arziqinta,hakan yasanya babu ganin girma girmanawa ko ganin mutunci tsakaninsa da kattume,idan ta hadosu babu wanda bazaiji kansu ba,bata shakka ko shayin zazzaginsa,ko lafta mishi baqaqen maganganu,hakanan yake zaune da ita shima saboda wataran yakan jingina da ita,sa’annan tazama tamkar wata kujera a gidan,duk wani harqallarsa da auri sakinsa a gaban idanunta yakeyi,hakanan za’ayi zaman a gama yasallami mace yasake jajibo wata.

 

Karanta Kuruciya Hausa Novels Complete

Mace ta biyu data juri zamanta a gidan kuwa itace maimunatu,maimunatu macen da bai taba auren matar dayaji sonta cikin jiki da zuciyarsa ba irinta,macen dayaso har zuwa randa tabar duniya,macen da haryau yake marmarinta duk da qasa tarufe idanunsa,macen da bata taba daga kai ta kalleshi ba duk da mugunyar halayyarsa.

 

 

Yakance maimunatu tayi!,saboda ta soshi,ta qaunaceshi,takuma zauna dashi,duk da banbancin ahalin,daraja,nasaba,kyau arziqi da dukiya dake tsakaninsu,tazarace mai yawa tsakaninsa da maimunatu,amma duka bata duba wannan ba,a zamanin tanunashi takuma zabeshi cikin dubban samari masu kyau dukiya da aji da take dasu a zamanin.

 

 

Mahaifinta dan kasuwane da yayi suna,hakanan ya shahara wajen arziqi,kamilin mutum mai managartan halaye,nagartarsa tasanya bai duba matakin arqizin bilyaminu ba a wancan lokacin yadauki maimunatu yabashi,duk da cewa su biyu tak Allah ya azurtashi dasu a duniya.

 

 

Duk da tarin wahala da fama da take a cikin gidan bata taba fasa halin da take ciki ba,tun mahaifanta suna da rai har Allah yadauki abinsa,hakanan taci gaba da zama dashi,sam babu jituwa tsakanin bilyaminu da qanwar maimunatu mai suna zuhriyya saboda yadda take ganin yana gasa ‘yaruwarta,ita kuma bata daga kai bare ta nuba mishi bacin ranta,tsabar sanyin halin maimunatu yakawo hakan,tun zuhriyya na budurwa idan tazo gidan bata kwana,iyakarta awa biyu uku tayi tafiyarta,don tace ba zata iya ganin baqinciki da takaici ba,kusan har tafi maimunatu jin zafin abun,don ko gaisuwa bata hadata da bilyaminu,hakan yasa ya shina yake cike da haushinta,yakance

“Duk abinki dai baki isa ki raba qaunata da maimunatu ba”

“Dana isa din ai da tuni na raba wallahi da baka kai warhaka tare da ita ba”.

 

 

Haihuwarta tafari tasamu Bilkisu,yarinyar data fita daban cikin ahalin gidan da ‘yanuwanta gaba daya,hakan kuma baya rasa nasaba da dangin mahaifiyarta data dauko wadanda suke jinin fulani,kakarta mahaifiyar maimunatu kuma shuwa ce.

 

 

Yadda komai na halittar bilkisu yake daban tun tana qanqanuwarta,saiya zamana komai nata ma daban yake,tsafta kwalliya da ado kullum cikinsu take,maimunatu tana da tsafta gason gayu da ado,uwa uba alokacin takan samu kudi cikin gadonta da mahaifinta yabari,na gidajen da ake mata haya da sauransu.

 

 

Duk wanda yakalli bilkisu saiya kuma dubanta,komai nata tsaf gwanin birgewa,uwa uba ga kyau da Allah yayi mata,sai hakan yasake zame mata ado da qawa.

 

 

Bilkisu nada shekara shida Allah yayiwa mahaifiyarta maimunatu rasuwa,duk dacewa a sannan tana da qarancin shekaru amma ta koka sosai,har hakan yabaiwa mutane mamaki,kukan nata saiya zama wani gwanin tausayi.

 

 

Zuhriyya kusan tafi kowa jin mutuwar ba kadan ba,tayi kuka tayi kuka har taji babu dadi,mutuwar ‘yaruwarta daya tilo datake gani taji dadi ta girgizata matuqa,a lokacin saura watanni aurenta,amma babu yadda ta iya hakanan ta dangana.

 

 

A sannan taso daukar rainon bilkisu,amma bilyaminu ya qeqashe qasa yace sam bazai bata ba,dama can shiri suke na,bata taba nadamar rashin jituwarsu ba irin wannan lokacin,sai taji dana sanin bata aikata dukkan abinda ta aikata din ba sabida rasa damar daukar bilkisu datayi,ta wani bangaren kuma saita sake qullatarsa dajin takaicinsa,saboda duk sanda tatuna rayuwar da ‘yar uwarta tayi duk da wadatarsu wanda shine sila saita sakejin qinsa a zuciyarta.

 

 

Ta fannin dangi ma bata samu goyon baya ba,kasancewar bata da aure itama riqonta ake, hakanan bikinta gab yake,tilas ta tattara ta haqura,duk da yadda taso daukar bilkisu kamar mutuwarta,saidai kullum tana hanya tana jelan ganin bilkisun,duk da tarin wulaqanci da take gani daga wajen bilyaminu amma tashanye,ita bilkisun kawai take kalla.

 

 

A sannan yarinyar bata gamu da wata matsala mai yawa ko.matsatsi ba,saboda zuhiryya kusan kwana a gidan ne kawai batayi,idan tayi nawar duniya ta tsallake kwana daya bata je ba,duk sanda taje zata mata wanka ta gyarata,ta siya mata duk abinda ranta yakeso,tawuni da ita,ta sanyata taci abinci sosai,a haka aurenta yatashi.

 

 

To yanayin aure bazaiyiwu tadinga sakaraftu ba kullum tana kan hanya,saiya zamana duk sati take zuwa ganin bilkisun,a sannan ta fuskanci akwai ‘yan matsaloli na rashin kula daga matar uba dashi ubanma gaba daya,sai tasake ninka kulawarta akanta.

 

 

Ganin haka yasanya mijin zuhriyya sake shiga maganar karbo bilkisu,nan ma bilyamu yace Allah ya kasheshi shi bazai bada diyarsa ba,a sannan har duqawa zuhriyya tayi tana roqonsa kan hakan amma yace sam,haka tanaji tana gani ta haqura,saidai taci gaba da kulawa da bilkisun har zuwa tsahon wasu shekaru,wanda a sannan bilkisun takai shekara goma sha biyar.

 

 

A lokacinne yanayin aiki yadauke anty zuhriyya da mijinta zuwa qasar brazil,wanda zasu kashe shekara shida a can.

 

 

Ba qaramin tashi hankalinta dana bilkisun yayi na gaba dayansu,saida maigidanta ya kwantar mata da hankali,yakuma tayata shiryawa bilkisu duk abinda tasan zata iya buqata na tsahon lokaci.

 

 

To,ta hadu da uba mai son abun duniya,kusan duk abinda aka aje matan shida matarsa akaci,hakan yasanya kayan basuyi wani tsahon rai ba suka taru suka qare,abinda yarage mata kawai school fees dinta,wanda shima don anty zuhriyyan taje tabiya na shekarun da suka rage mata,hakanan islamiyya an mata total ta biya na shekarun.

 

 

A sannam bilkisu ta sake tantance tsakanin aya da tsakuwa,tasake gane dacin maraici da rashin uwa,ta gane ranar anty zuhriyya,saboda cikin qanqanin lokaci tasoma tagayyara,hatta da sitturunta zuwa wasu abubuwa nata masu daraja tasoma adabo dasu saboda ba ita kadai ke amfana ba.

 

 

Dalili kuwa shine,yarinyace da tunda tabudi idanu ta fahimci rayuwar gidan nasu Allah yazuba mata qauna da tausayin qannenta,kusan dukkaninsu suna qarqashin kulawarta ne,idan ka gansu saika rantse da Allah uwarsu daya ubansu daya,zata iya hana kanta tabasu,zata iya hana idanunta bacci su suyi,zata iya yadda ta wahala su su huta,saidai a wannan lokacin dukka wani qoqarinta yagaza,saboda bata da matallafi,sa’annan bata da wani sana’a ko aiki da takeyi.

 

 

Kafin wani lokaci tsanani yayi tsanani,wanda yasa tasoma tunanin wacce sana’a zata kama?,duk da bata da komai bata da kowa,saita soma wankau,lokacin da malam bilyaminu ya fahimci haka nan yadinga surfa ruwan bala’in ba za’a maida masa gidansa gidan tsummokara ba,duk da gidan na wani kyaune dashi na azo a gani ba,hasalima yana buqatar gyare gyare saboda tsufa daya soma yi,tanaji tana gani ta watsar.

 

 

Daga bisani tasamu aiki a maqotan unguwarsu,gidan wata mata da ake kira da umma luba.

 

 

Takan fita wajen aikinta tun safe har dare,wani lokacima takan kai goma kota kwana a can,Idan tatashi a aikin saita biya gida wajenta ta amsa,duka duka albashin nata dubu biyu ne da dari biyar,hakan yasa baya kaima tarin qannen dake gareta ko ina bare tasamu ta tsinanawa kanta wani abu.

 

 

Babban tashin hankalinta a rayuwa taga qannenta cikin wani mayuwacin hali na buqata,kuma bata da abinda zata basu ko tayi musu,wannan yasa tasake dagewa wajen daukarwa kattume tallan abinci ranakun da babu makarantar boko da safe kenan,kusan sana’arta kenan,wanda a ciki take ci tasha ta yiwa kanta da yaranta sutura,harma wani lokacin shi mai gayya mai aikin ya rabo yaci a jikinta randa yatashi bashi dako asi.

 

 

Ko daya kattume bata da mutunci ko tausayi musamman akan kudi,akan kudinta zata iya yin komai,bata da lamuni bare daga qafa ko misaqala zarratin,tana iya dafa abinci ta hana dukkan wani yaro dake gidan sai wanda taga dama ko kuma yaranta,takance

“Ubanku mara zuciyar bai kawo ba,don haka bazaku karyani ba,duk maiso yamiqo kudinsa yaci abinci” abun na matuqar baiwa bilkisu mamaki da daure mata kai,hakanan takan shiga tashin hankali duk lokacin da irin hakan tafaru babu kudin da zata baiwa kattumen ta bawa yaran abinci,idan ‘yan mutuncin na kusa duk sanda ta dawo daga talla zata zuba mata maidan dama,anan ne zasu hadu duka suci,idan wannan bata samu ba,saita karbi bashi idan aka bata albashinta tabiya ta,tana kuwa rubuce da adadin abincin nawa ta karba din,hakanan tana ankare da lokacin biyan bilkisun albashi,da zarar lokaci yayi zata nemi kudinta.

 

 

_wannan itace BILKISU da salon nata rayuwar. Ko yaya nata SIRADIN RAYUWAR YAKE?,ku biyo ‘yar mutan huguma,itake dauke da amsoshinku_

 

 

****** ******* **********

 

 

*2005*

 

 

 

K’arfe takwas na dare take takawa a hankali cikin layukan unguwar tasu,iskace irin ta sanyi ke kadata hagu da dama,tana kuma kada dan yalolon hijabin dake mannewa a jikinta kasancewarsa na roba,uwa uba tsufa da shan jikin da yayi wanda ya rage kaso hamsin cikin dari na kaurin asalin yadin.

 

 

Kusan hankalinta bai jikinta,tayi nisa qwarai cikin tunani wanda har hakan yasa ya bata damu da wanda ke gabanta ko bayanta ba bare gefanta,tunanin nata dukka yana kan qannenta data bari wuni guda sur yau a gida,batasab me sukaci ba yaudin,ko umna kattume ta basu abinci?,ko yauma tayi musu irin halin nata data saba,da yunwa suka kwanta ko kuwa sun qoshi?,duka ire iren abinda yake damunta kenan tunda ta fito daga gidan umma luba takamo hanyar gidan nasu,wanda duk da yake cikin unguwa daya suke amma akwai ‘yar qaramar tazara a tsakaninsu.

 

 

Hannu tasa tadan share kyakkyawar fuskarta da takejin qurar hazo samanta,wanda hakan ita bai dameta,takan dauki lokaci mai tsaho kafin ta sanya mudubi gaban idanunta takalli fuskarta,duk wata halitta takyau da Allah yayi mata baiwarsa saidai tajita daga bakin mutane,bata taba tsaiwa ta kalla ba bare ta tantance,hasalima bata da wannan lokacin ko kadan a rayuwarta.

 

 

“Yammata daga ina haka?” Ta tsinci muryarshi daga bayanta,gabanta ne yayi wani mummunar faduwa,tun kafin tajuya tasan waye,ko kusa ko alama ta tsani duk wani abu da zaya hadata dashi,bata qaunar tarayyarsu ko alaqa dashi,hakanan ta tsani irin abinda yake mata,ita kwata kwata bata sanya kanta cikin jinsin mata bare har wani yace zai damu da rayuwarta da sunan soyayya,a wannan halin da take ciki?,tana ganin babban zaluncine a gareta wani dan adam ya takura mata da kalmar so ko qauna.

 

 

kalmace dako sau daya bata taba magana akanta ba walau a zuci ko a fili,a karan kanta ko ita da wani,towai dawa ma zatayi zancanta?,wa take dashi,bata da kowa bata da abokin magana shawara ko tattaunawa,bata da wanda zata gayawa shawara ko damuwarta face ‘yan qannenta,wanda su kansu basu gama fuskantar rayuwar ko matsalarsu ba bare su fuskanci ta wani.

 

 

Koda tana da wani gata ko wani tsayayye,tana ganin babban zunubine a shekarunta qwalli goma sha biyar kacal ta jefa kanta a wannan layin.

 

 

Tana tsaka da wannan tufka da warwara yasha gabanta,yaja birki yana kallonta,tsantsar baiwar kyawun da Allah ya mata ta bayyana tarwai a dan ragowar hasken farin wata wanda hazo yayi nasarar dakushe kaso mafi yawa na hasken nashi,qare mata kallo yaci gaba dayi yana jin yadda yake sonta cikin zuciyarsa,bilkisu nada wani irin kyau mai sanyi da shiga zuciya,hakanan komai nata mai kyaune,kama daga kallonta,tafiyarta da maganarta,hatta da shurunta ma,komai nata abun burgewa ne,duk da tarin talauci da fatara daya musu katutu kuwa,yasha rayawa a ranshi wannan da a gidan wadata take ba shakka ba qaramin haddasa fitina kyawun nata zaiyi ba,matuqar yasamu dukkan wani abun buqata da zai bayyana kanshi yadda ya kamata,ba kamar yanzu daya tabbatar da cewa duk da yadda yake ganin kyawun nata fatarar da suke ciki ta wawashi kaso mai yawa ta boye ba.

 

 

Da wannan damar tayi amfani ta kewayeshi cikin matuqar sauri da wani irin hanzari tawuce,to ba ma’abociyar iya saurin bace ita,hakan yasa baiyi wani taku mai yawa ba ya cimmata,yayin da zuciyarta taci gaba da bugun uku uku,Allah Allah kawai take takai gida wannan qaramar alqar tasu ta yanke.

 

 

Dab da dakalin qofar gidansu yake a zaune,shi daya da alama yaudin babu ‘yan tayin hirar nashi duk dare da suka saba zaman kisan dabe,masu matattar zuciya kusan irin tashi,kuma ‘yan amshin shatar nashi,hakan yasanya tasu tazo daya dasu sosai

“Ke bilki,bilki!,zo nan” ta tsinci muryar mahaifin nata a sanda yana kwado mata kira a sanda take gab da shigewa soron gidan nasu.

 

 

A matuqar sanyi ta sauya akalar tata zuwa inda yake zaune,ta gefen idanu tana iya hango sabi’u wanda yasamu wani waje ya lafe bai qaraso inda suke ba sakamakon ganin mahaifin nata da yayi zaune a qofar gidan nasu.

 

 

A ladabce ta isa gabanshi kana ta durqusa da dukkanin gwiwoyinta,kanta na kallon rairayin dake shimfide gabanta

“Gani baba” sai yatashi yazauna sosai daga kashingidar da yayi,ya gyara hularshi dake niyyar zamewa tazauna sosai a kanshi

“Yauwa” yafada yana sake gyara zaman rigar wuyanshi kamar wanda ya qwaci kanshi daga hannun ‘yan dambe

“Dama cewa nayi zan samu wani abune a wajenki?,yau natashi bani dako sisi wallahi,waccar kafirar kuma yau tsiyarta ta motsa ganin na tada sabon ginin dakuna,ta hanani abincin daren ma kwata kwata” wani dunqulallen abu mai tauri taji yazo mata iya wuya ya tokareta.

Leave a Comment

error: Content is protected !!