Sirrin Mijina Hausa Novels Books
Oyoyo yaya kabeer…,oyoyo yaya kabeer..”
Wannan shine ihun da yaran dake zaune cikin
tsakar gida suna wasa suketa faman yi daidai
lokacin da suka ga shigowar matashin saurayin
wanda ke sanye cikin farar shadda kansa babu
hula sai yar kyakkyawar suma da ya dan ajiye,
Fuskarshi dauke da murmushi ya rungume yaran
wadanda akalla zasu kai su kimanin guda hudu,
Daga inda take acikin kitchen ta sake lab’ewa
saboda bata son ya ganta duk da sanin cewar
dominta yazo gidan, sadadawa tayi ta buya a
bayan fridge gamida leka kanta ta window ta
yadda tasan bazai iya hangota ba,
Ganinshi tayi rike da hannun Amira da waleeda
kannenta sannan ga amir da husna atsaye sai
faman jajja masa riga suke suna tsalle,manyan
chocolate samfarin coconut chocolate ya debo
daga cikin aljihunsa ya mimmikawa yaran,
Sunkuyawa yayi wurin Amira saboda itace babba
tafi su husna wayo,
“Amira ina mama?”
“Tana falon abba?”
“Yaya NADIYA fa?”
“Tana kitchen mama tasata aiki..”
Murmushi yayi ya mike saboda yasan aduk inda
take taji shigowarsa shiyasa ta gudu ta buya,
Yana rikeda hannun su Amira ya bi hanyar da
zata sadashi da falon Abba,
Sai da ya tsaya yayi sallama mama ta amsa ta
bashi izini sannan yasaka kai ya shiga cikin
falon,
Mama yasamu zaune kusa da abba suna yin
hira gefe daya kuma kwanukan abincine da
abban yaci kasancewar bai jima da dawowa
daga wurin aiki ba,
Su walida da amira na biye dashi har cikin falon
sai da suka rakashi ciki sannan suka ruga da
gudu suka fita,wuri yasamu ya zauna kanshi a
kasa saboda kunya da kuma girmamawa,
Ganinsa yasa abba sakin fara,a tareda mikewa
daga kishingiden da yake ya gyara zamansa
yana murmushi,
“Kabeeru yanzu kake tafe? Barka da zuwa..”
Cikin jin kunya da sose sosen keya kabeer ya
daga ido ya kalli Abba,
“Ehh wallahi abba, shigowata kenan dama nazo
ne in gaisheku saboda kwana biyu ban samu
damar shigowa ba..”
Murmushi Abba yasake yi ya kalli kabeer din,
“Haba kabeer har yaushene rabonka da gidan,
nazaci ai jiyane kawai baka zoba amma ai
shekaran jiya ma kazo kodai ka manta ne?”
Maganar da abba ya fadice tasa mama tsoma
bakinta tana dan murmushi amma fuskarta babu
yabo babu fallasa,
“To ai Alhaji tunda yasaba zuwa kullum jiya
kuma baizo ba ai dole yaji kamar yafi sati daya
rabonsa damu”
Dariya abba yayi yakoma ya kishingida yana
kallon kabeer wanda ya gyara zama yafara
gaisar da mama,
Shiru falon ya danyi nawani lokaci saboda shi
kabeer nauyin mama da abba yakeji yanzu sam
baya iya sakewa yayi hira dasu yanzu kamar da,
Ganin yanata zaune shiru sai dai dan lokaci
zuwa lokaci abba yana sakoshi cikin zancen da
suke yi da mama yasashi mikewa,
“Abba bari naje waje..”
“To kabeer tafiya zakayi?” Abba yafada yana
gyara zamanshi,
“A’a ba tafiya zanyi ba waje zanje”
Fita yayi daga cikin falon cikeda kunya, yana fita
abba ya dubi mama yana fara,a,
“Nasan dama ba tafiya zaiyi ba wurin mutuniyar
tasa zaije..”
Shiru mama tayi batace komai ba saboda ita
kwata kwata bata son wannan maganar saboda
wani dalili wanda ta barwa zuciyarta ita daya
amma idan hali yayi zata bayyanar dashi ga
abban shima yaji, ganin taki zancen yasa abba
barin maganar ta hanyar shigo da wani zancen
daban domin ya fahimci duk lokacin da zaiyi
magana makamanciyar wannan wadda ta shafi
kabeer da nadiya mama bata bada goyon baya.
Yana fitowa daga falon abba cikin kitchen
yawuce, a bakin kofar kitchen din ya tsaya
saboda ganinta da yayi tsaye tana mopping
bayan ta kammala share cikin kitchen din,
Yarinyace yar budurwa wacce bazata wuce
shekaru goma sha biyar aduniya ba, tanada
hasken fata amma ba farace can ba, tana sanye
da atamfa kalar koriya dinkin riga da zani, daga
inda yake yana iya hango gashinta dake
nannade cikin dan kwalin dake daure akanta,
“Sannu da aiki..” Yafadi yana murmushi har
lokacin yana tsaye akofar kitchen din,
“Sannu da zuwa yaya kabeer” tafada ahankali
sannan maganar ma tayi tane cike da kunya,
“Yawwa sannu sarki aiki..”
Tunowa da tayi cewar bata gaidashi ba yasata
saurin dan rissinawa,
“Yaya kabeer ina wuni?”
“Bazan amsa ba har sai kin jiyo kin kalleni ido
da ido..”
Murmushi yasaki bayan ya furta mata hakan
saboda yasan ba karamin aiki ya hadata dashi
ba domin kunyarshi da takeji bazai taba barinta
ta iya hada ido dashi ba…
Leave a Comment