Zaman Aure Sai Hakuri Sirrin Mata
Zaman Aure Sai Hakuri Sirrin Mata Kashi na 1
“Idan namiji bai ji daɗin aure ba zaiyi tunanin kara mata ne don ya samu jin daɗi. Idan kuma ya ji daɗi zai yi tunanin ƙarawa don ya ƙara jin daɗi. Mata ku yi hakuri. Ƙarin aure ɗabi’a ce a cikin mazajen mu
IDAN KIN GANE SAIKI ZAUNA LFY!
Haka ne tabbas, kuma duk mace mai son Allah da Manzan Sa zata yi hakuri, sai ta ɗauki namiji abokin rayuwa, aboki kuma yana kuskure yana son rai sannan baya da tabbas, Allah kaɗai yake da tabbas, mai zai hana muyi hakuri mu mata
DA MUN HUTA DA ZAFIN KISHI
A lokacin da kika ɗauki son duniya kika tattara kika ɗora akan namiji tabbas, zaki halakar da rayuwar ki, domin Allah kaɗai Ya cancanta da wannan soyayyar.
IDAN KUNYI TUNA NI
A lokacin da kika ɗauka sai kina ɗasawa da namiji zaki kyautata masa, da kuma biyayyar aure Hakika kina wasa da shiga aljannar ki
WANNAN HAKA YAKE
A lokacin da kike banzatar da mijinki dan ya ɓata miki rai koh ya ƙaro kishiya zaki yi da na sani marar adadi, domin ba shine ya baiwa kansa iznin ƙarin aure ba, Allah ya umarce shi
INA MAFITA
A lokacin da kika ɗauka duk biyayya, kyautatawa, ihsani, kyautatawa, farantawa, sadaukarwa da miƙa wuya da kike yi ga mijin ki domin shi kike yi ai kuwa sai in baza ki cigaba da yi ba, idan kuma baki yi ba Allah zai bashi dubun ki masu yi fiye da abinda kike masa, muddin dai mai riƙo da gaskiya ne.
BABU JA AKAN HAKA
A lokacin da kike bibiyar sahu da ƙwaƙƙwafin miji don kisan abinda yake ciki koh abinda yake akai, koh wata alaƙar da yake da wasu matan waje, lallai kuwa zaki samarwa kanki hawan jini. Domin a ƙarshen zamani namiji ɗaya tal na iya jiɓantar al’amurran mata masu yawa
WANNAN HAKA YAKE
Amma abinda ya fiye maki alkhairi shine dai, ki so namiji tsaka – tsaki domin zai iya canja maki nan gaba, sannan ki rika masa biyayya da kyautatawa domin Allah; ta hakan baza ki gajiya ba, kuma kada ki sanya shi a ran ki, domin rayuwa ɗaya kike da ita koh yau kika mutu, gobe wata zai auro,ya ci kaza ya sha maltina
Leave a Comment