Hausa Novels

Sun yi min illah Hausa Novel Complete

Sun yi min illah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: SUN YI MIN ILLAH

 

 

 

 

*SUMMY M NA’IGE*

 

 

*FIRST CLASS WRITER’S ASSO…*

 

 

 

 

*SHAFI NA ƊAYA*

 

 

Da ma ashe haka duniya take mai halin ɗan mangwaro? Me na yi musu ko sun manta kowa da ƙaddararsa a tsarkakken allo. Ban san inda zan saka raina na ji sanyi ba. Ya zan yi na sauya ƙaddarata ko zan kasance yar adam kamar kowa lallai sun yi mini babbar illa wadda har duniya ta naɗe ba zan daina cin gajiyar raɗaɗin ƙonar zuci ba.

 

Cikin sauri ta shiga gidan, bayan matar gidan ta karɓa mata sallama sannan ta fito. Gani ta da ta yi ne lokaci ɗaya ta ɓata fuska haɗi da jefa mata tambaya, “me ya kawo ki gidana?”

 

Ƙasa ta yi da kanta sai da ta yi raurau da ido kamar mai koyon magana ta ce,

 

“Daman na zo ne ko akwai aikatau?”

 

Kallon ta ta yi a walaƙance sannan ta ya tsuna fuska ta ce,

 

“Za ki iya wankau na yara kala naire goma!? idan ba za ki iya ba bi ta inda ki ka fito.

Ta faɗi haka haɗi da nuna mata ƙofar fita da yatsa.

 

Kanta ta yi ƙasa da shi, haɗi da tunanin baya, gashi baya bata dawo wa bare ta yi ƙoƙarin gyara kaddarata, dama duniya haka take me halin ɗan magoro, yaranta da ta tura makaranta ta tuna da su, kuma gashi sun tafi makaranta ba abin da suka ci, sanin suna kan hanyarsu ta dawo wa ne ya sa ta ɗago kanta cikin hanzari ta ce,

 

” Zan iya Hajiya”.

 

Tsaki wannan matar ta yi sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko kayan yara masu muguwar dauɗa, kamar waɗanda aka yi wasan tsere da su.

 

Haka ta duƙa ta fara wankau har sai da hannuta ya ji ciwo, sosai ta sha wuya kafin ta kammala, tana idarwa ta gayawa matar, dubu ɗaya ta ɗauko ta bata, ta ce,

 

” Ƙuɗinki ɗari uku ne, ki cire kuɗinki ki kawo min sauran canji”.

 

Sai da ta rusunan kamar maroƙi ya je bara sannan ta karɓa haɗi da yi mata godiya. Cikin hanzari ta nufi mai shago, garin kwaki ta sayo iya na kuɗinta sannan ta shiga ta bawa Hajiya canjinta, gab da za ta fito gidan ƙofar gidan ta riƙe ledar garin ya zube ƙasa gaba ɗaya. Lokacin da idonta suka sauka kan abin da ya same ta ba ta san lokacin da hawaye suka sauka a idonta ba, zazzaɓin da take ji ne tun safe ya sake rufeta, da ƙar ta iya tashi ta koma gida cikin tashin hankali. yaran ta tuna me za su ci idan sun dawo? Musamman Afiyya da bata da haƙuri, sosai ta san Afiyya ba ta da hakuri, don halinsu ya babbanta da na Husnah, kamar yadda sararin samaniya ya yi hannun riga da ƙasa, to haka ta san halin su ya babbanta. duk da wannan halin da take ciki ta yi alƙawarin ba za ta nemi taimakon kowa ba, bale har a koma yi mata lllah.

Littafan Hausa Novels

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Tana cikin wannan halin ta ji sallamarsu, cikin hanzari ta miƙe da ga kwanciyar da ta yi haɗi da goge hawayen da ke mata kwaranya.

 

” Ammi! Ammi! Ina abincinmu yunwa nake ji ?”

Abin da ta ji Afiyya na faɗa kenan tun kafin ta ƙaraso cikin ɗakin da take.

 

Cikin ƙarfin hali ta tashi haɗi da faɗar,

 

” Kun dawo?”

 

Husnah ta ce,

 

“Mun dawo Ammi”.

 

Tun kafin Afiyya ta sake buɗa baki ta yi magana Ammi ta ɗau mayafinta ta ce, “zan je na karɓo muku abinci, kar ku fita kun ji”.

 

Haka ta faɗa jikinta sai rawar zazzaɓi yake kamar wadda ta ji tashin gangar makiɗi. Tun kafin su yi magana ta fice gidan, ko da ta fita ta jima tsaye ta rasa ina zata dosa, wa zai taimaka mata ya kawo mata a gaji, duk da ita aka yi wa illah amma kowa ya gojeta, ko sana’a ta kasa ba mai saye ina zata sa kanta ta ji daɗi. Tafiya take tana tunani har ta kusa fita unguwarsu, a haka aka fara kiran sallah magarb waje ta samu ta rakuɓe ko zata samu ta gabatar da sallah.

 

Hankalin Husnah ya tashi lokacin da ta ga Afiyya ta fara rera mata kuka yunwa take ji, kuma gashi har duhun dare ya kama amma Ammi har yanzu babu ita babu labarinta.

 

Suna cikin haka sai suka ji sallamar Ammi, da hanzari suka isa gare ta, ledar da ke hannuta suka karɓa, tun a tsaye suka fara ci, hannu baka hannu ƙwarya, da ƙyar Ammi ta samu suka zauna suka ci gaba da ci.

 

Dankali da ƙossi ne, haka suke ci suna korawa da ruwa kamar mayunwata daji. Kallonsu take cike da tausayi, numfashin ta ne ya fara yin sama-sama, ƙoƙarin jawo shi take amma ta kasa, basu ankara da halin da take ciki ba har ta kai kwanci. Husnah ce ta kai duba wajan da take, jinin da taga yana fita ta hancinta ne ya ankarar da su halin da take ciki, da hanzari suka yi kanta suna faɗar,

 

“Ammi! Ammi Kar ki mutu!.

Haka suka riƙa faɗa suna jijjigarta suna kuka.

 

Amma shuru ko mutsi bata yi ba bare su sa ran zata farka. Suna cikin haka sai wata mata ta shigo gidan sai sababi take, ta shanyata kamar kayan wanke zata karɓar mata ƙosai da dankali ta ce ta jira ta….bata ƙarasa maganar ba ta ankara da ita kwanci jini sai fita yake a ƙofar hancinta, irin yadda ta ga yara na jijjigarta yasa ta fahinci da matsala. Ƙoƙarin guduwa ta fara yi, sai kuma taga haka ba shi ne ma fita ba, ba ɓata lokaci ta kira mai adaidaita aka sakata har yara suka nufi hospital.

 

Irin yadda a shigo da ita ne likitoci suka karɓe ta, ba ɓata lokaci aka fara bata taimako, lya mai ƙosai na ganin haka ta sulale ta bar asibitin gudun kar ace a saye wani abu.

Afiyya da Husnah kawai ke zaune suna jiran ko Ammi zata fito ɗakin da suka ga anshiga da ita?

 

Takarda magani aka rubutu, ko da nurse suka fito neman ƴan uwanta ba kowa sai Afiyya da Husnah, tsaki suka yi haɗi da faɗar,

 

“Duk lakacin da ƴan uwanta suka zo za a dubata idan sun sayo magani.haka Ammi take halin mutuwa ko rayuwa har sa’a biyu.

Haka suka cigaba da aiki ba wanda ya bi ta kanta. Suna cikin haka wata likita ta shigo cikin azama don ta duba wata marasa lafiya da ta bari, sosai ta ga jikin matar da sauƙi don haka ta kama hanyar da zata fita ganin dare ya yi mata kan hanya, har zata fito ɗakin idonta suka sauka kan wannan matar da ke halin rai ko mutuwa, gabanta ne ya faɗi haɗi da sake duba gyafin da take, sosai hankalinta ya tashi ganin mara lafiya na neman taimakon gaugawa amma ba ko wani likita akanta, wajan da likitoncin suke ta ƙarasa ta fara musu masifa, irin yadda suka ga ranta ya ɓace ne suka yi mata baya ni ba kowa nata wanda zai sayo mata magani ko ya je a yi mata test , cikin ɓacin rai ta dube wata Nurse ta ce,

 

” Ina sauri zan tafi gida, amma duk abin da ya kamata ayi mata ayi mata”.

 

“In sha Allahu Aunty”.

 

Tun bata fita ba suka fara bata taimakon gaugawa, duk abin da ya dace sun yi mata, cikin ikon Allah numfashin ta ya dawo daidai, duk wani gwaji anyi mata, typhoid da older ce suka yi mata mugun kamu wanda sanadin haka jininta gaba ki ɗaya ya ƙone har sai da suka yi mata ƙarin jini. Duk wani maganin ko allora sun yi mata, cikin ikon Allah kafin safe ta farfaɗo.

 

Afiyya da Husnah ta fara cin karo da su agyfinta, godiya ta yi ma Allah sannan ta fara tunanin ya aka yi ta zo asibiti, waya kawo mata su Afiyya da Husnah? Ta san ita tunda mai ƙosa ta bata bashin ƙosai da dankali bata san inda take ba, mi suka ci?. Hawayen da taji suna ɓuɓɓugowa a fuskarta ta goge, duniya ke nan wanda bai zo ba ma jiranshi take.

 

Tana cikin haka likitoci suka zo aka bata magani sannan aka duba lafiyarta. Nurse ɗin da ke kula da ita ta sa wata ma’aikaciya ta gyara su Afiyya haɗi da kawo musu abin kalaci, bayan sun ci har Ammi ita ma ta ci sannan wannan Nurse ta yi musu sallama ta yi tafiyar ta.

 

Sai da rana ta fito sannan ta shigo asibitin ta duba marasa lafiya da dama sannan ta zo wajan wannan matar da nurse ke ƙoƙarin sauya mata wasu drip , irin yadda ta ga suna yi mata, alamo sun nuna tana jin zafi haka yasa ta yi sauri ta ƙarasa wurin don karɓa ta sama ta, wata razananiyar ƙara taji an yi mata haɗi faɗar,

 

“dakata! Kar kubari wannan yarinyar ta taɓani!”.

 

Cikin hanzari ta kai kallonta ga wannan matar wadda muryarta ke mata amo a dudun kunnuwa, saboda ko mutuwa ta yi aka tasheta bazata manta wannan muryar ba.

 

Yatsun hannuta ta sa tana nunta da shi, bakinta sai rawa yake amma ta kasa magana.

Ganin Ammi na ƙoƙarin kwanci ruwa da aka ɗaura mata, kuma haka daidai yake da taɓa lafiyar ta, cikin hanzari wannan likita ta fice da ga wannan ɗakin gabanta na dukan uku uku. Iya ruɗuwa ta ruɗe da ma ashe Ammi na raye? Tabbas duniya ta nuna mata cewa yaro da babba duk tana daidai da su!.

 

 

 

_Wannan labarin ciki yake da sarƙaƙiya, ban tausayi da wata rikitacciyar soyayya mai wahala, labarin nan ya kunshi abubuwa da dama musamman rayuwar da muke a wannan zamani, amma ba za ga ne haka ba sai ka biyo ni sannu ahankali zaka yi katari da illah da aka yi._

 

 

_Littafin kuɗi ne idan akwai mai buƙata 300 ne ta account 3191016467. Sumayya Almustapha, first bank. za ki turu shaidar biyanki ta wannan Number 07062118047 only whatsapp, idan katin ne 300 MTN._

 

 

 

 

*UMMU JA’AFAR

Leave a Comment

error: Content is protected !!