Hausa Novels

Sune Sila Hausa Novel Complete

Sune Sila Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

SU NE SILA

Na

Aisha Abdullahi Yabo

 

1&2

 

 

*Marubciyar*

*Amal*

*Mu kula’yan matan zamani*

*Kar ka gujeni*

*Ma’aurata*

*Illar Auren dole*

*Nuraddeen*

*Rayuwarmu*

*Kuskuren waye*

 

 

KAINUWA wRITER’S*

*ASSOCIATION*

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

Karin wasu littafai da zaku so

 

 

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

 

 

*____________________________________*

 

 

Matashiya ce zaune a acikin ɗaya daga cikin tsukakkin ɗakunan gidan yari, tana sanye da kayan gidan yari a jikinta, ta sa kanta a tsakankanin gwuiwoyinta, Ɗaya matashiyar ce da itama take sanyi da kayan gidan yarin ta tasu daga wajan da take a zaune ta matso dab da ita tasa hannu ta dafa ta tana faɗin “tun ɗazun da aka kawo ki gidan yarin-nan kuka kawai ki ke, shin wane irin laifi kika aikata har kika tsinci kanki a cikin wannan yanayin“? Ko motsi bata yi ba daga yanda take a zaune cikin jin haushi ta ce; “koda yake ni miye ma nawa a ciki ai amsar ma a fili take kisan kai kika yi, shi ya kawo ki gidan-nan kamar dai ni ɗinnan, sai dai ban sani ba ko ƙaddararmu iri ɗaya take“? Ko ci kanki bata ce da ita ba hakan ya sa ta dawo gefe ta zauna sai dai zuciyarta na azalzalar ta da son jin labarin matashiyar da tun zuwanta kalma ɗaya bata iya jin ta furta ba kuka ne kawai take. Wasu mata da suke sanye da kayan ‘yan sanda irin na masu tsaron gidan yari su biyu su ka zo suka buɗe ɗakin cikin masifa ɗaya gandurobal ta ce; “oya-oya a fito a fito lokacin aiki ya yi”! Jiki a sanyaye ta miƙe tsaye tana tafiya a hankali domin ko ina na jikinta ciyo ya ke mata ga ƙafafafunta sunyi haushi saboda dukan da tasha a wajan ‘yan-sanda kafin zuwanta nan ɗin kullum sai ta sha duka na fitar hankali, ɗayar tana ganin sun buɗe ƙofa ta falla a guje ta fita dan ta san halinsu ba a masu tafiyar yanga yanzu sai mutum ya sha na jaki da kulaken da su ke hannunsu, da ƙyar take iya taka ƙafanta aikuwa su dinga ingizata da ƙarfi da kai mata duka, cikin tsawa ɗayar ta ce; “ke mu fa ba a mana iskanci anan kina wani tafiyar yanga kamar kina a gidan ubanki“! Kuka ta fashe da shi yayin da take ta ƙoƙarin ɗaga ƙafafunta domin yin sauri amma hakan ya gagareta haka su ka sa ta gaba da duka da hantara har zuwa wani babban fili da ya ke ciki da mata ‘yan gidan yari kowa da irin aikin da ya ke, ma su tsaron su suna biye da su da abun bugu kuskure kaɗan su labtawa mutum, ingiza ƙeyarta suka yi wajan cirar haki da ƙyar ta iya duƙawa tana cira da hannunta suna dukan ta da hantara, azabar da take ji ya sa kukan idaniyarta ya ƙafe, sai ƙunar da zuciyarta take mata. Haƙiƙa rayuwa tattare take da shafukan ƙaddarori wasu takan zo masu da sauƙi wa su kuma gaunin da take zuwa masu da ita ya wuce misali, ita dai tata ƙaddarar har bata san da wace irin suna zata kira ta da shi ba, mutanen da suke tare da ita su ma suna aikin tausayinta ya cika zuciyarsu, ta kusa da ita ta ɗago ta kalli masu tsaron su ta ce; “haba ku kuwa dan Allah ku tausaya mata ku duba yanda ƙafafunta ya yi haushi Allah kaɗai ya san irin azabar da take ji, dukan jikinta a farfashe ya ke da shacin bulala“ laftawa mai maganar bulala ta yi cikin faɗa ta ce; “ke har tausayi kika sani! Banzaye mararsa imani, tana son jikin nata ne za ta je ta aikata rashin imani, maza ku kama aikin gaban ku kar na sake jin waninku ya ce tak“! suka cigaba da aiki suna magana, da ta kusa da ita ta yi magana ƙasa-ƙasa “kema dai da son janyowa kai wahala waɗannan mutanen ai ba su san Allah ba, babu tausayi a zuciyarsu, kawai idan kika ga suna abunsu kawo na gani ki zuba mau“

“Allah dai ya fitar damu daga wannan baƙar izaya, ya rabamu da aikin Da-nasani “

“ami… Dukan da a kai masu ne ya sa ta haɗiye sauran maganar ba tare da ta shiryawa hakan ba. Wuni ta yi ana sanya ta aiki mai matuƙar jigata sai azahar suka je wajan sallah, banɗakunan biyu da a ke zuwa dan yin lalura duk mutane a tsaye suna bin layi sai hayaniya ake wa na ciki a kan suyi su fito sun daɗe, tana tunanin yanda za tayi babu buta duk an ɗauka wasu na tsaye suna jiran ‘yan uwansu su gama su basu, wacce suke ɗaki ɗaya ce ta tsaya gefenta ta bata wani ƙoƙon roba da ya ke da ruwa ta ce; “ga ruwa kuma idan kika ce zaki yi sanya duk wanda ya ke wajan nan sai ya gama lalurarsa ya barki a tsaye“

Miƙa hannu tayi ta karɓa tana takawa a hankali ta ƙarasa wajan layin, ta jima tsaye ƙiris ya rage ta saki fitsarin a wando dan ba ƙaramin matsuwa ta yi ba, ta zo kan layi kenan ta sa ƙafarta ɗaya ciki ɗaya ƙafar a waje wata ɓukekiya ta zo da sauri ta bangajeta tayi taga-taga za ta fadi ta yi saurin dafa ginin banɗakin matar ta shige ta rufe ƙofar kwanon da har ya fara ɓallewa da kuma tsatsa, wacce take alwala ta ce; “gara ma ki je can baya ki yi lalurarki a kan ki jira wannan ɓukekiyar jakkar kashi sai ta yi minti talatin bata fito ba kuma babu wanda ya isa yayi magana, idan ka yi magana ta zaune abin banza su kansu hukumomin gidan-nan shakkunta su ke, waɗancan kuma ba nasiha zasu maki ki shiga ba“ bata ce da ita komai ba, ta sake faɗin “ki yi sauri kije tun kan marasa imanin nan suzo su ganki a wajan, idan kuma baki gaji da tsayuwar ba sai kiyi ta tsayi“! Ta ƙarasa alwala ta bar wajan, bata da mafitar da ya wuce tabi shawarar matar, da sauri ta je baya wajan ƙazanta ga bahaya duk anyi wani ya bushe wani kuma ba a jima da yi ba, da ƙyar ta samu wani wajan da ya fi ɗan sauƙi ta yi fitsari tana gama yin tsalki ta tashi tsaye kenan sai ga ɗaya daga cikin ma su tsaronsu tazo wajan “ke uban waye ya faɗa maki ana fitsari a nan“?! Ta yi wuri-wuri da idanunta “ba tambayar ki nake ba“?! Muryarta na karkarwa ta ce; “kiyi haƙuri yau na zo baƙuwa ce ni“

“sannu raɓa kinji, maza duƙa ki gyara filin nan bana son ganin wata ƙazanta a wajan“! Cikin tashin hankali ta ce; “duk kashi ne fa a wajan“

“sai a ka yi ya idan kashi ne? Maza kisa hannu ki kwashe ki gyara“

“dan Allah ki yi haƙuri ki ƙyaleni wallahi na maki alƙawarin duk rintsi ba zan sake zuwa wajan… Wani irin duka ta kai mata da icce a kan kunkuminta har sai da ta sunkuya ta sake wata irin ƙara mai razanarwa “bana son musu maza ki yi abinda na sa ki idan kuma ba haka ba yanzu sai na karkarya ƙasusuwan jikin ki, kuma hannu za ki sa ki kwashe“! Kallon ƙazantar wajan take cike da tashin hankali ta yanda za’a ce mutum mai rai ne zai sa hannu ya kwashe ya gyara wajan, wayyo Allah ƙaddara me ya sa zata ma ta haka me ya sa ta cillota cikin wannan mummunan rayuwa, a ranta addu’a take Allah ya tasheta daga wannan mummunan mafarkin, ɗaiɗaikun mutanen da su suka yi saura a wajan duk sun tsaya suna kallon su, wasu zuciyoyinsu cike da tausayin ta, wasu kuma dariya su ke suna fadin ai kowa ya so kwana lafiya shi ya so, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan doka, wacce su ke ɗaki ɗaya ta ce; “haba ku kuwa me yasa kuke mata dariya da yada magana haka, dukanmu ƙaddara ce ta cillomu cikin gidan nan ya kamata kuwa mu so juna, mu tausayawa juna“

“hihihi ƙaddara ko san rai, ba wata ƙaddara malama duk wanda kikaga gani a gidan nan san ransa ne ya kawo shi ihin!“

“barta da wani tauhidin ta can, da ta ji me yarinya ta aikata ai da sai ta ta ƙyamace ta da ba zata so ta ganta a kusa da ita ba bare har wani tausayinta ya shigeta, ɗazun ina jin ma’aikatan gidanan suna maganar laifin da ta aikata da ɗebe mata albarka“ shiru ta yi bata iya cewa komai ba, domin dukansu masifaffu ne abu kaɗan zasu hau dukan mutum kafin a karɓeka kaji jiki, tsawa mai tsaron nasu ta daka ma su “ku ɓace min da gani kowa ya kama gaban shi tun kan na waiwayo kanku“! da sauri suka bar wajan sai wacce suke ɗaki ɗaya da ta laɓe ta gefe tana leƙen yanda matar nan take labtawa matashiyar icce cikin rashin tausayi da imani, hawaye su ka ciko idanunta, hango wata daga cikin ma’aikatan ta nufo wajan ya sa ta bar wajan da gudu, yayinda matashiyar ta ke kallon ƙazantar da ba ita ce ta yi ba da ake so asa ta kwasa dole, wani dukan aka mata da ya sata gantsarewa ta buɗe baki tana ihu da muryarta ko fita ba ta yi, “wallahi idan na ƙirga uku ba ki fara ba sai na maki dukan kawo wuƙa“! Ta ya za ta iya kwasar kashi da hannunta….

 

 

Fulani

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Leave a Comment

error: Content is protected !!