Ta Fita Zakkah Hausa Novel Complete
Ta Fita Zakkah Hausa Novel Complete
Ki biya ki karanta cikin Salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba kada ki karanta sannan kuma kada ki yad’ashi..Pay N500 via jamila Umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan Lambar 09069067488*
Karfe hudu na asuba ya farka kamar yadda ya saba,Kwata kwata bai ji dadin barcin ba akan kujera sannan zuciyarsa tana cunkushe ne ya dade bai samu barci ba kuma kasala ya rufeshi ya kasa tashi yayi ko nafila ne.
Sai da asuban ya shiga dakin nasa yayi wanka ya dauro alwala Jallabiya mai ruwan madara ya saka da Hula ya Dau cashabahansa ya fice zuwa masallaci ko ta kan Sakina bai bi ba ballatana wata Amina.
Sai shidda saura ya shigo gidan,yana shigowa tsakiyar falon suka ci karo da Sakina ta fito daga dakinta yarkace yarkace da ita idanuwanta sun kumbura sannan kanta ba dankwali kanta ba kitso gashinta ya baje kansa tana sanye da rigar barci mai taushi iyakarta gwiwanta ayanayin yadda yaganta sai da ya kara kallonta ganin yanayinta.
Kamar zai mata mgana sai kuma ya fasa ya dauke kansa zai shiga Dakinsa Da hanzari ta daga kafa zata bisa jin takunta yasa ya Dakata bai juyo ba taji muryansa yana fadin”Ina zaki..?
Cak ta tsaya jikinta yayi sanyi kanta ta maida kasa kafin tace”Da..Dama zan gaisheka ne Habibi..!
Shuru yayi mata bai yi mgana ba taga yana shirin shigewa ya barta yasa tayi saurin cewa”Ina kwana Habibi..!
Kamar bazai tankata ba sai kuma ya amsata kamar baya so da Lafiya Lokaci daya ya shige dakin nasa ya banko mata kofa saman fuskarta baya taja Hannunta Dafe da kirji tana fadin
“Na shiga uku ni Sakina..!
Kasa tsayuwa tayi kamar mahaukaciya haka ta kwashi gudu zuwa Dakinta saman gadonta ta koma ta Zauna gabanta na fadi meta aikata kenan .?Jiya ko barci batayi ba in ta tuna Kalaman Umar zuwa gareta.
Taso ta kira Anty tun jiyan sai ta kasa Tasab Halin Anty in taji abunda ta aikaata sai ta Zageta saboda haushi Saboda sai da ta tausheta akan kada tayi wani abu sai ta tambayeta yanzu in ta Kirata ta fadamata abunda ya faru ta tabbata sai Anty ta mata fada sosai.
Sai dai bata da wata mafita Anty zata kira ta fadamata abunda ke faruwa ko zata samamata mafita.
Wajen shidda da rabi ta dokama Anty Amarya kira tun da taga kiran tasan ba Lafiya cikin Tashin hankali ta Daga kiran tana fadin”Sakina kada ki fadamin kin kara aikata sakarcin naki ..?
Sakina tafara Fiki Fiki da ido tana fadin”Anty…!
“Don ubanki ki fadamin abunda ya faru..!
Sakina cikin sanyi ta fara fadamata Duk abunda ya faru jiya har zuwa yau Anty Amarya ta mike Har hijabin jikinta datayi sallar asuba na neman Hardeta ta fadi ta Dafe jikin gadonta Cikin Firgici tace”Kikace Umar da kansa yace baki Chanchanta dashi ba..!?
Sakina tace”Wlh haka yace Anty..!
Anty Amarya bakinciki suka kusa kasheta alokacin cikin Tsawa tace”Sakina na rantse da wanda Raina ke hannunsa in kishin ki na banza yayi sanadiyar Tono Abunda muka Binne da Dadewa babu ruwana..zan zame kaina ne na barki ke kadai..Kin kuma Tabbatar ma kanki wannan kokawar tafi Karfinki..!
Jin haka yasa Sakina ta kara Rudewa kawau sai ta saki kuka tana Fadin”Anty don Allah kiyi hakuri..Ba laifina bane..Kishi ne ya rufemin ido kinsan ina son Umar bazan juri ganinsa da wasu matan ba..Sannan Aliya tacemin kada na barta ta zauna Dakin Mijina..!
Bakar Inuwa Hausa Novel by Billyn Abdul
Anty Amarya ta lailayo Ashar ta saki kafin tace”Aliya Burauban ki Sakina..Ina ruwanta da wannan mganar ban fada miki kada kiyi wani yunkuri sai nace ba..?
Da kika kwantar da hankalinki Lokacin Sakaryan balarabiyar nan ba gashi yanzu muke da riba ba..Itama in kin kwantar da hankali kamar haka zata zama nayi alkawarin ko zan rasa komai Amina bazata yi zaman kishi Dake ba Sakina ammh shegen Taurin kan ki yana neman jawo mana matsala..!
Sakina na sharan kwallah tana Fadin”Nidai Anty ki fadamin ya zan yi..?Wlh ko son ganina bai yi ina mgana Dakyar yake amsa mun..!
Anty Amarya tace”sai kin bata komai kizo kina Damunna da kukan banza..Yanzu ina ita Aminar..?
Sakina ta tabe baki kafin tace”Tana chan Dakin Sarood..Tun jiya bansan isalinta ba..!
Anty Amarya tace”Shi kuma fa..?
Sakina tace”Ya dawo daga masallaci ya shiga Dakinsa ya kulle..!
Anty Amarya tace”To ki tashi ki shiga kitchen ki hada breakfast ki yi wanka da kwalliya kije ki tasosa ki basa Hakuri..Mganar Amina kuma kada ki shiga mganarta ki koma gefe ki zama yar kallo kawai a na nan ana aiki akanta kin ji ko..?
Sakina ta gyada kai kafin tace”Anty Dakyar ya Saurareni fa..!
Tsaki Anty Amarya taja kafin tace”To Tunda bazai Saurareki ba..ki Zauna..!
Daga haka ta katse kiran tana Huci ita Kadai adaki Sakina fa Bata san ciwon kanta tasan kudin data kashe kafin Umar ya kalleta da sunan so..?
Tasan wahalan data sha kafin Umar ya kalleta da kalmar aure..?
Batasani ba shiyasa take son bata komai ba bazata yi wannan saken ba in abubuwa suka fara Lalace mata bata samu Cikar Burinta ba anyi ba ayi ba kenan ko zata rasa komai sai Sakina ta zama Tauraruwa awajen Umar da danginsa gabadaya Wata mace bata isa ba kuma tayi kadan.
Ashe Sakina duk zaman data ke yi batayi sallah ba,Sai da suka gama waya da Anty tatshi ta Dauro alwala tayi sallah sama sama ta Daura Zani saman rigarta ta fita zuwa Kitchen,Sakina ta iya girke girke Anty Amarya bata barin ya”yanta haka tasan duk cikar ya mace in bata iya Girki ba Saura ce shiyasa ba wacce bata koyama girki ba hatta da Sa”adatu da Sabeeha..!
Cikin Hanzari take aikinta Cikin Lokaci ta kamallah Doya ta Dafa sai tayi miyar kayan miya ta yayyanka mai kwai,Sai ta Dafa Ruwan tea ta soya Buredi da kwai saman Dinning ta jera komai kafin ta gyara Kitchen din sannan ta koma Daki ta shiga wanka.
Bayan ta fito ta shirya Cikin Doguwar rigarta ta atamfa ta gyara gashinta tayi Daurinta na Maryam babangida..!
Gabanta fadi yake bata san wani Tarba Umar zai sake mata ba ta zata Ya kulle kofar ne sai da ta Tura taganta a Bude Cikin Takunta na Takama ta shiga Dakin da sallama sanin Halinsa yanzu sai ya maidata waje.
Yana zaune a kasa saman Darduma yana karatun Qur”ani a hankali cikin Sautinsa mai Dadin Sauraro Dakin tabi da kallo komai neat,Gado ne kawai sai wardrope sai ma”ajiyar takalma sai cafet babba da ya malale Dakin gefen gadon ta zauna tana Jiransa ya idar da karatun ammh wajen Minti Goma sha biyar bai rufe karatunba sai ta fahimci in tayi shuru to sai rana ta Dago zai tashi daga wajen nan.
Gyaran Murya tayi kafin tace”Ina kwana..Wajen ka fa nazo Habibi..!
Ta karishe Fada Cikin shagwaba.
Yana jinta yayi kamar bai ji ba sai da ya kai inda yaga damar Tsayawa sannan ya rufe Qur”ani ya Daga hannu Sama yana addu”a tare suka shafa ya mike ya ijiye Qur”anin saman Side drower din gadon,Yana kokarin Ninke Darduman ne tayi saurin mikewa ta karba bai hanata ba ya sakarmata Ta ninketa ta maidata wajen zamanta tana gani ya hau saman gado ya kwanta harda juya mata baya.
Bata damu ba ta Durkusa saman kafafunta tana fadin”Don Allah kayi hakuri Habibi..Da abunda ya faru sharrin Shedan ne da kuma Kishi..
Ammh nayi alkawarin bazan kara ba..!
Kaji..!
Kamar bazai tanka ba sai chan taji yace”Zaki kara Sakina..!
Da sauri tace”Allah bazan kara ba..!
Ajiyar rai ya sauke kafin ya juyo yana kallonta Lokaci daya yace”Ya wuce..!
Mirmishi ta saki kafin tace”Nagode..Ga breakfast chan na gama Hada maka ka taso muje ka karya..!
Lumshe ido yayi kafin yace”Am ok..Bana jin yunwa..!
Marairaicewa tayi tana fadin”Haba Habibi..Ko baka hakura bane..?
Da Sauri yace”Bani da riko kema kin sani..!
Jin haka yasa tace”To in hakane ka taso muje..abunda kafi so na Dafa maka Doya..!
Muskutawa yayi ya mike zaume yana Fadin”Naji..Zan yi wanka ne ganin nan fitowa..!
Taji dadi sosai ta mike tana Fadin”Bari na taimaka maka Habibi..!
Duk yadda yaso ya yakiceta bata yarda ba Tun yana kin sakin mata har ya sakarmata ita ta taimakaima ya Cire kayansa ta hadamai ruwan wanka ya shiga yayi wanka daya fito ta taimakamai ya shirya Cikin Riga da wando na pakistan sannan ta Tarosa Hannunta Cikin nasa zuwa Falon har saman Dinning jikinta na rawa ta yi Sarving dinsa kallonsa tayi tana zubamai Ruwan tea din dayaji Ganyen shayi masu kamshi tace”Kana so da yawa ne Habibi..?
Kai ya girgizamata kafin yace”Rabin kofi..!
Haka kuwa ta sakamai ta Turamai gabansa baya son madara siga ya kara kadan ya fara sha Bai san yana jin yunwa ba sai da ya gansa gaban abinci Rabonsa da abinci tun jiya da rana..
Ita Tea ta hada maa kanta tana Hadawa da Buredi da kwai shi kuma yana cin Doya daman mutuniyarsa ce.
Ranta yayi mata Fes ganin ya sauko har suna dan mgana jefi jefi Shine ma yace mata”yana da kyau in ana cin abinci a Dakata da mgana har sai an kamallah..!
Daman sai yayi mgana bai cika son tana mai mgana in suna cin abincin ba yasa tayi shuru tana kurban tea tana kallonsa shima kuma in ya Dago suka hada ido sai yayi mata Yake kawai.
Sai da ya kusa gama cin abinsa sannan Amina ta fadomai arai kamar ya Tuna da wani abu ya Dakata da komai yana kallon Sakina Cikin wani yanayi yace”yarinyar nan ta fito kuwa..?
Wani irin Kallo tayi mai kafin tace”Wata yarinya kenan..?
Yadda ya kalleta ne yasa tayi Saurin gyara mganarta da cewa”Bansani ba..Nidai ban ganta ba..!
Tsam yayi yana wani Tunani bata ci abinci ba,Ba domin yadda Hajiya da maallam suka saka shi a Tsakiya ba da sai yace ta Dauwama adakin ai yunwa ba”a mata iskanci sai dai in ya kyaleta Allah zai kamasa kuma Hakkin mallam da Hajiya na wuyasa..!
Tuna haka yasa ya kalli Sakina kafin yace”je ki kiramin ita..!
Ido ta Zaro kafin tace”Ni kuma..?
Kai Tsaye yace”Eh ko bazaki ba..?
Jin haka yasa tace”ban ce ba..!
Tashi tayi tana Tura baki ta wuce ya Bita da kallo daman yasan lambo Tayi Sakina ai bazata Daina Halinta ba.
Afusace ta Buga kofar ta shigo Tana bin Dakin da kallo lokaci daya tana wani yamutsa Fuska nan kasan Cafet ta Hango Amina ta Dunkule waje daya acikin Hijabinta,Ga ghanas dinta nan inda ya ijiyemata ko kauda su batayi ba Ranta ya kara baci Cikin kufuluwa tace”Kee…!
Cikin Tsswa Amina bata jita ba Domin barci ne na wahala ya kwasheta bata sani ba Jiya yadda taga rana haka taga Dare bazata kwatanta kwana awajen da ba Hanne ba Hamida ba bata taba tsamanin wannan ranar ba ballatana ta Shiryama zuwanta Tunda ta shigo Dakin ta zube anan kasan Cafet ko motsi bata karayi ba tayi kukan har ta gaji ga Tsoro Daki ita kadai abunda bata saba ba,Bata iya barci ba Tsoro da Fargaba da kewa basu barta ba Dakyar ta Rarrafa da Asuba ta shiga Toilet din Dakin tayi alwala tazo ta Rama Sallar Isha”in da ake Binta jiya da kuma Sallar asuba shine fa tana nan zaune bata ma san barci ya kwasheta ba.
Sakina jin tayi banza da ita kuma taki Motsi yasa ranta ya baci a Tunaninta da gangan tayi mata yasa ta isa kusa da ita ta saka kafa ta Shureta daya sa Firgigit Amina ta farka Daman a Tsorace take cikin muryanta da Bata Fita sosai saboda kuka tace”Wayyo..!
Sakina ta saki Tsaki kafin tace”Baki ce wayyo ba sai nan gaba..Badai kin ce dani Zaki kishi ba yarinya..Ai wayyo Salamu Alaikum..!
Amina ta bita da kallo da kumburarrun Idanuwanta Hancinta ya Toshe da majina sai ja take ga kuka ga sanyin Dakin Domin A.C a kunne kuma fanka ma haka ita kuma bata yi Hausan tashi ta kashe su ba.
Sakina ta koma da baya tana mata wani kaskantattacen kallo kafin tace”Kazama kawai..Sai ki taso yana kiranki..!
Amina ta kalleta da mamaki kafin tace”Shi wa..?
Cikkn Shakewar murya Sakina ta ga tama raina mata wayau yasa ta juya tana fadin”Uban ki ba..!
Amina ta bita da kallo har ta fita itafa bata gabanta ita yanzu kokuwa take da wannan Sabuwar rayuwar shiyasa Zagin Sakina bai ma Dameta ba kamar bazata je ba Domin jiri take gani in ta mike ammh Tuna Kalaman ya Danmallam yasa ta mike jiri na Dibanta ta fice Daga Dakin zuwa Falo Daidai sanda Sakina taja kujera ta Zauna Dammallam na zaune bai ce mata komai ba sai ga Amina ta fito tana Layi Cikin hijabinta kamar zata fadi Daga nesa ta Tsaya tana kallonsu kafin tace”Gani..!
Daga sama har kasa yake kallonta alamu sun nuna ko mai yarinyar nan batayi ba tunda ga jiya kenan ganin yadda Fuskarta ta Kumbura ne ya bashi mamaki Sakina kuwa Kamar ta yi Tsaki haka taji da taga yana kare ma Amina kallo bata ma lura da kallon kyama yake binta dashi ba..!
Saboda mugunta sai da tafi minti Goma a Tsaye tana neman faduwa sannan yace”kizo ki ga abun kari nan.!
Amina da Tagaji da Tsayuwa tace”Ni na koshi..!
Ko kallonta bai yi ba ya maida hankalinsa wajen cin Doyansa Sakina ta juya tana kallonta ta Harareta bata ma ganta ba ta juya tana Faman Kama Hijabinta ta koma inda ta Fito nan inda ta baro ta koma ta zauna ta Hada kai da gwiwa ta fara Rera sabon kuka Allah sarki sai yanzu ta kara Tabbatama da kanta da cewa tayi maraici tazo inda ba mamanmu ba Hamida ba Hanne,Wadanda sune ita in basu Rayuwar Amina bazata taba cika ba Aminu ne ya fado mata arai ko wani Hali yakeciki..?
Tasan da shi ta aura ta tabbata zai lallasheta zai mata komai Saboda yana sonta ammh kalli inda Kaddara ta kawota inda ba”a san Darajanta ba Daga megidan har matan gidan basu da Imani Allah ya isanta wlh bazata taba yafe musu ba mugaye kawai..!
Tun daga Lokacin Amina ko motsinsu bata sake ji ba tun tana Daurewa har ta kasa Cikinta ya kulle yunwa take ji ga jiri ga rashin barci sai mulmula take saman cafet dafe da Ciki tana faman kuka ita kadai Zata mutu acikin wannan gidan wayyo ita Amina..!
Umar kuwa agida ya wuni bai Fita ba sai da yammah da ya kira Jafar yazo suka hadu shima iyakarsa haraban gidan bai shiga b,Mganar Visa dinsa sukayi so yake cikin satin nan ya koma Madina bazai iya sake wasu kuma kwanaki ba,gabda mangariba Jafar ya tafi shi kuma Daganan masallaci ya wuce sai da akayi sallar Isha”i ya dawo ya iske Sakina tayi sabon wanka bayan ta gama girki ta gyara gidan yana tashin kamshi Sai ransa yayi fari,Yana son Sakina saboda Tsabtarta,sannan uwa uba kuma kwalliya,yau din ma ta tsuke cikin Riga da wando,ko Dankwali bata saka ba gayu take ji yau din,Ko bai yi mgana ba tasan ya yaba tunda yana ta kallonta yana mirmishi.
Abincin mara nauyi tayi musu Faten Dankwalin Turawa da hanta sai Coffea data hada musu tare suka zauna suka ci abincin su kafin su dawo Falo su zauna Sakina ta Dora kanta saman cinyar Umar shi kuma yana wasa da gashinta,Hankalinsa na wajen kallo a tashar Sunna Tv Qur”an,sakina kuma har ta fara barci bata damesa da mgana ba sanin Halinsa hira in ya sota suna yi bai so ba kuma baya son ana damunsa Duniya ta mata sabuwa yadda taga ya manta da Halittar Amina acikin gidan
Kamar wasa wayarsa ta Dauki Sautin kidan Larabawa Sakina ta Bude ido tana fadin”Habibi kamar ana kiran wayarka fa..!
Chan saman dinning ya barta da sukaci abinci,Yasa ya Daga kansa yana Fadin”itace..!
Mikewa tayi tana fadin”Bari na Dauko maka..!
Sanda ta karisa ta Dauko wayar sai da gabanta ya fadi ganin sunan mallam,sai da Annurinta ya Dauke tsayawa tayi har wayar ta katse jin ta Shuru yasa ya dago yana kallonta kafin yace”Waye ke kirana..?
Sakina ta kariso ta mikamai tana Fadin”Mallam ne..!
Gabansa sai da ya fadi ya karba da Sauri Lokaci daya yana fadin”Dauke min karar nan..!
Ba musu ta Dauki Remot tayi kasa da Volume din shi kuma yabi bayan kiran Mallam
Da sallama mallam ya daga Kiran Umar ya zamo daga kan kujera kamar yana gabansa yace”ina yini mallam..?
Mallam na zaune afalonsa Gefensa Hajiya ce yaa amsa yana fadin”lafiya lau Umaru ya wajen iyalan naka..?
Ya amsa da lafiya kalau kansa na kasa kamar yana gabansu Sakina na kallonsa ta gefen ido a duniyar nan Umar na bala”in ji da mutanen nan guda Biyu mallam da Hajiya na ukun su kuma wannan Mayen Baba Sa”idun inyana mgana dasu kamar ya kwanta musu saboda Biyayyah..!
Mallam yace”Masha Allah..lafiya yau baka shigo anguwan namu ba..?
Nace to bari na kiraka naji Allah yasa ba Rigiman me sunan mamana bane har yanzu bata bari ba..Domin yanzu nan yan”uwanta suka tashi daga nan tun jiya suke kuka ko makaranta ba su je ba suna ta koke koke sai da na kira su yanzu nayi musu nasiha na lallashesu da cewa su bari tayi ko sati Daya ne sai suje su mata yini..!
Danmallam yayi shuru bai yi mgana ba Mallam ya gyara zama yana fadin”Ina ita maman tawa..?ina fatan ta Daina kukan ko..?
Danmallam kansa na kasa yace”Eh ta bari Baba..!
Runtse ido yayi yayi karya Domin bai san ko ta bari ba..
Mallam yace”Madallah Sai kayi hakuri Umaru kaji ko..?Mamana yarinya ce karama yanzu bata da kowa sai kai..Kai zaka zama mai mata Tarbiya Tunda ta bar karkashinmu..In tayi ba Daidai ba kamata nasiha cikin jan hankali,Duka ko Tsawa basa gyara Tarbiya jan mutum ajiki da nuna mai so shi ke sa ya rage wasu abubuwan..Don Allah Umaru ka kula da Mamana..itace karama acikin matan ka ba lalle ta kai su wasu abubuwan ba..ku rika mata uzuri in ta aikata wani abun Umaru..!
Kansa na kasa ya gyada kai kamar Mallam na ganinsa kafin yace”Insha Allahu..!
Mallam ya cigaba da fadin”Ina ita abokiyar zaman nata..?fata dai ba wata matsala..??
Cikin Ladabi yace”Babu mallam..!
Mallam ya jinjina kai kafin yace”Dakyau itama Saratun nayi waya da Mahaifinta namai bayanin komai har ita nace abani nayi mata Nasiha sosai..ina rokin Allah ya hada kanku..Sannan kai kuma Allah ya baka ikon yin Adalci..!
Umar ya amsa da Ameen Ameen daganan yayi shuru kafin yaji mallan yace”Ina ita maman tawa..!
Ko tayi barci ne..?
Umar ya runtse ido murya kasa kasa yace”Eh..!
Mallam yace”To shikenan Allah ya zaunar daku lafiya..ga Hajiya nason mgana Dakai..!
Bai gama zufan karyan daya yi ma maallam ba Hajiya ta karbi wayar suka gaisa kafin tace”In fatan Amina taci abinci kafin ta kwanta..?
Dakyar yace”Eh Hajiya taci..!
Kai ta kada kafin tace”Shikenan ka kula da ita kaga dai yarinya ce..Wlh ban yarda ka hada kai da matanka ku cutar da ita ba..Domim ba sa”ar su bace..!
Yana jin Hajiya bai iya mgana ba ta cigaba da fadin”Ina mganar mu ta kwana..?
Sannan yaushe zaka koma..?
Kai Tsaye yace”Ina so cikin satin nan Hajiya Visa na nake jira..!
Hajiya tace”Kake jira..?Ita Sakinar fa..?
Kai Tsaye yace”Nan zan barta..Sai na Sake dawowa..!
Hajiya ta bude baki tana kallon mallam shima yana kallonta kafin tace”to ka dai samar ma