Alamomin Mace Mai Dadi – Karanta Wasu Alamomi Da Ake Gane Mace Mai Dandano

Alamomin Mace Mai Dadi – Karanta Wasu Alamomi Da Ake Gane Mace Mai Dandano

Alamomin Mace Mai Dadi

Yaya cikakkiyar lafiyar mutum ta jima’i take?

Kama daga sau nawa muke yi da kuma yadda muke yin jima’i BBC ta yi nazari kan dimbin irin sha’awa da kuma hanyoyi ko dabi’un yadda ake jima’in, domin samun wasu bayanai.

Ga nazarin David Robson

Idan za mu fadi gaskiya maganar jima’in dan adam tana da wuyar sani. Za mu iya cewa yawan ‘yan kananan laifukan jima’i sun kai yawan nau’in dandanon abinci.

Kuma kamar yadda muka bambanta a zabe ko sha’awar dandanon abinci haka ma zabinmu na jima’i ya bambanta daga wannan kasa zuwa waccan, daga mutum zuwa mutum da kuma wannan rana zuwa waccan.

Saboda wannan dalilin, maganar ka ce za ka yi kokarin tantance mece ce cikakkiyar lafiyar jima’i wani abu ne na kamar bata lokaci.

Saboda abu ne iri-iri kuma mai salo daban-daban ta yadda ba za ka iya daukar wasu alkaluma ko wata kididdiga ka yi amfani da ita, ka ce ga yadda yawancin mutane suke ji ba.

A kan haka ne BBC ta duba alkaluman da ake da su domin ta yi kokarin samun akalla wani bayani da zai nuna yadda ainahin jima’in gaba daya yake, kama daga yawan yadda muke son jima’in zuwa yadda muke yinsa.

Ba shakka akwai bukatar yin taka-tsantsan matuka wajen yin wannan nazari. Domin bincike ko alkaluma ko wani kiyasi game da wata dabi’a ta jima’i ba abin dogaro ba ne, wato ba su da tabbas, saboda har yanzu ana daukar yin magana a kan jima’i a matsayin wani abu da ya saba wa al’ada.

Mutanen da za a yi wa tambaya ko bincike a kansu ba lalle ba ne su fadi gaskiya gaba daya, ko kuma ma su yi karin gishiri a bayanansu.

Saboda haka wadannan alkaluma ba wasu bayanai ba ne da za a ce lalle ilalla haka suke, amma dai za a iya amfani da su a matsayin wata alama ta gaba daya, idan aka yi la’akari da shedar da ake da ita zuwa yau ta yadda rayuwar jima’i take a wannan karni na 21.

Ya yawan bukatar mutane ta jima’i yake?

Abu ne mai wuyar gaske ka bayar da wata kididdiga ta yawan masu dabi’a iri kaza ta jima’i, domin misali kididdigar masu neman maza ta bambanta daga kashi daya cikin dari zuwa kashi 15 cikin dari, ya danganta ga wanda ka tambaya, da yadda ka yi masa tambayar, da kuma ko kana lura da yadda mutumin yake da dabi’arsa da kuma yadda ya nuna kansa.

Amma duk da haka wasu nazarce-nazarcen da aka yi a sassan duniya sun nuna cewa akwai mutanen da ba su da wata sha’awa ta yin jima’i (amma hakan ba yana nufin ba su taba yin mu’amulla ta jima’i ba fa).

Kamar dai alkaluman yawan masu sauran dabi’u ko zabi na irin mu’amullarsu ta jima’i su ma masu wannan rashin sha’awa ba za a iya cewa ga ainahin yawansu ba (yawanci na cewa kusan kashi daya nea cikin dari).

Amma dai akwai wasu da suke fitowa masu kungiyoyin irin wadannan mutane da ke alfahari da cewa su ba su da wata sha’awa ta jima’i.

Da wa mutane ke jima’i?

Wata gurguwar fahimta ita ce yawancin jima’i na dama ta samu ya kunshi mutane ne da muka hadu da su kwatsam, a zahirin gaskiya jima’i na kasancewa ta hanyoyi da dama wadanda ba na al’ada ba kuma irin haduwar dare dayan nan a yi a watse ba kasafai ake yinsa ma, kamar yadda wannan binciken na Amurka daga shekara ta 2009 ya nuna.

Ma’ana dai kusan a tsakanin kashi 50 cikin dari na al’ummar abu ne wanda ba a san inda ya sa gaba ba, wanda yake da wuyar fahimta.

Sau nawa mutane ke yin jima’i?

Wannan alkaluma ne da aka samu bisa kididdigar da aka yi ta jima’i ta jima’i ta duniya a Amurka, wadda ta kunshi mutane sama da dubu 50 wadanda sun wuce shekara 18, da aka yi wa tambayoyi.

Ko da ya ke yawan yin jima’i yana raguwa da yawan shekarun mutum, amma ba zai ragu ba kamar yadda kake tunani.

Wani bincike da aka yi a kan tsofaffin mutanen da suka kai shekara 70 a Amurkan ya nuna cewa akalla kashi 50 cikin dari daga cikinsu suna jima’i fiye da sau biyu a wata daya, inda kashi 11 cikin dari cikinsu kuma suke jin dadin yin jima’i sosai a duk sati.

Ta yaya mutane ke yin jima’i?

Wadannan alkaluma ne da aka samu daga binciken da aka yi na mutanen da ba su bayyana kansu ba, su kusan 2,000 masu shekara tsakanin 18 zuwa 59, a Amurka, wadanda aka tambaye su kan irin jima’in da suka yi na karshe.

Tsawon lokacin da ake yi ana jima’i

Ko da ya ke ‘yan madugo (mata) sun nuna ba sa yin jima’i akai akai kamar yadda ‘yan luwadi (maza), ko masu jima’i na namiji da mace suke yawan yi, to amma abin ya nuna kamar abin nan ne na cewa kadan ya fi dadi, kamar yadda binciken da aka yi ta intanet a Canada da Amurka ya nuna

Mutum nawa ne suka taba karyar yin inzali?

Yawanci ana dauka cewa mata ne kawai suke karyar yin izali, amma wani bincike da aka yi a baya bayan nan a Amurka ya gano cewa akwai maza masu yawa da suma suke karyar nuna wa abokan jima’insu cewa sun yi inzali a lokacin saduwa.

Suna yin hakan ne kuwa kamar yadda za ka iya tsammanin, yawanci saboda ba sa sha’awar yin jima’in a lokacin da aboki ko abokiyar saduwar tasu ita kuma take bukata, amma kuma ba sa son su bata mata rai.

Duk da cewa su kansu maza suna yin karyar samun biyan bukatar (inzali), kashi 20 cikin dari ne kawai na mazan suke ganin abokan saduwar tasu (mata) su ma za su yi karyar inzalin, ma’ana kashi 80 cikin dari basu yarda matan na wannan yaudara ba. An kwafo a Bbc Hausa

Powered by: www.mynovels.com.ng

Scroll to Top