Tag - Kwarton Anti Cikakken Labari Kwarton Anti

Kwarton Anti Cikakken Labari Kwarton Anti

Kwarton anti

Kwarton Anti Cikakken Labari Kwarton Anti

 

 

 

Page 1

 

Ranar bakwai,ga watan d’aya,shekara ta dubu biyu da goma sha shida,ita ce ranar da littafin k’addarata ya fara bud’ewa,ranar da na shiga cikin damuwar da ba na tunanin zan fita har abada!

Zaune na ke a cikin adaidaita sahu,kan hanyata ta komawa briged daga gidan yayata da ke unguwar hotoro,kaf hankali na ya na kan wayar da na ke amsawa ta masoyina,wanda yau watanni biyu ya rage auren mu.

“Y’an mata don Allah zan shiga nan,na kar’bawa maigidana sak’o”

Na ji muryar mai adaidata sahuna

Sai na kai duba na ga laundry (wurin wanki)d’in da ya ke nuna min,na ce”ok”

Tsautsayi ba ya wuce ranar sa,da na san zan ga abin da na gani yanzu me zai fito da ni yau? Wata bak’ar mota ce ta ke k’ok’arin fakin a wurin,duk da ban san tsadar motoci ba na san wannan dai ba k’arama bace,ya yi minti uku da fakin ga shi dai ya bud’e murfin motar amma bai fito ba,haka ne ya sa ni sake tattara duk hankali na wurin ganin wannan mashahurin.

A kan idona ya fito daga cikin motar,gabana ya fad’i daga yi masa kallo d’aya tak!

Fari ne tass,mai manyan idanuwa ,farare tas kamar bai ta’ba yin kuka ba,ba wani dogon hanci ne da shi ba,madaidaicin bakinsa ya hau sosai da zagayayyiyar fuskarsa,
Bak’ar riga ce a jikinsa da bak’in wando iya k’wauri,ga wani bak’in agogo da ya yi wa farin hannunsa kyau sosai

Ba k’aramin tafiya da imanina ya yi ba,nan take na ji wani irin yanayi a zuciya da gangar jikina,na yi wata kasalalliyar ajiyar zuciya,ina kuma k’are masa kalllo

Yamutse fuska na ga ya yi,tare da kai hannunsa kan gashin kansa da ke ta shek’i da alama ya sha gyara har ya gaji,ya wani hautsina sumar wanda na ji kamar da gayya ya yi,don kuwa wani irin kyau na ga ya k’ara,kai ka ce ba d’an Nijeria ba ne,wallahi ban ta’ba zaton a kwai irin kyawawan nan a garin Kano ba

Mota ya koma,ko shiga ciki bai yi ba hannu kawai na ga ya mik’a ya ciro wata jar facing cap ya saka.

Wanda ya yi daidai da dawowar mai  adaidata sahu na,hannunsa d’auke da wata jaka

Ina kallo matashin ya shiga wurin,ya na ta b’ata rai.

“Yi hak’uri hajiya,na ‘bata miki lokaci” Mai adaidaitar ya fad’a

Na yi guntun murmushi lokacin da mu ke wuce wurin na ce”babu komai”

Sai da mu ka d’an yi tafiya,na ji muryarsa”sunan shi Salim,shi ne mai wurin wankin nan,kuma shi ne me wurin cin abincin nan na sabin sati(seven thirty) ba shi da kirki,kuma ya na shan sigari,an ce ya na da kamfani a sharad’a,wanda da kan shi ya ke kula da shi,kuma gidan su ma a can ya ke”

Ban yi mamakin maganganun sa ba,don na san ba ya rasa nasaba da irin kallon da ya ga ina yi wa wanda ya kira da Salim d’in

“Hmm!” Na sauke ajiyar zuciya kafin na ce

“Ba ka san wani abun ba game da shi bayan wannan?”

“Abin da na sani kenan” Ya fad’a

“Ba ka da number shi?” Na tambaya zuciyata na bugu

Ya yi dariya ya ce”tabb! Wane ni?”

Cikin zak’uwa na ce”to don Allah maida ni wurin, idan ya fito ka bi min bayan sa”

Mai adaidaita ya yi wata irin juyowa ya zaro ido kafin ya ce”ki rufa min asiri,ban shirya mutuwa ba,y’an mata ina da iyali”

Ni ma y’ar dariya na yi na ce”don ka bi bayan shi sai ka mutu?”

Ya ce”to me zai hana? Ko ban mutu ba na san zan sha wuya,ke watak’il ma na k’are rayuwata a gidan yari”

Dariya kawai na yi na ce”hakane”.

“Amm…ka ce ya na shan sigari? Ta ya ka san da hakan?”

Na yi tambayar da zumud’in jin amsar da zai bani.

Mai adaidaita ya ce”eh,sau biyu ina ganin shi a wurin nan ya na zuk’a,da alama ta bi jikinsa don ya na sha a gaban kowa”

Na jinjina kai kafin na ce”Allah ya shirye sa”.

Har mu ka k’araso unguwar mu ban kuma magana ba,na fad’a duniyar tunanin Salim.

Da sallama na shiga gidan,na tadda Mama Saude ta na tsintar shinkafa,ga wutar murhun da ta kunna sai hayak’i ta ke yi,gidan duk ya kaure da k’auri
.Mama Saude matar mahaifina ce,bai jima da auro ta ba,sakamakon rabuwar su da mahaifiya ta,wanda ni ce silar rabuwar,a duk lokaci da na tuna da haka na kan shiga damuwa,wata rana ma har hawaye na ke yi.

Mama Saude ba ta da kirki,sam ba ta k’auna ta kullum cikin ganin ta had’a ni da mahaifina ta ke,gashi shi kuma duk abin da ta fad’a masa yarda ya ke yi,ya hau kai ya zauna ya yi ta surfa min masifa. Ko da ya ke ban cika ganin laifin sa ba,tun da nawa laifin ya fi yawa,ba na jin magana ko kad’an,shi ya sa ma a k’a k’agauta na yi auren kowa ya huta.
Hmm! Nan gaba dai za ku ji ko wacece ni.

Ban ko kula Mama ba,na shige d’akina da ba wani tarkace ne a ciki ba,wulli na yi da jakata ina fad’awa kan katifa ta.

Kiran sallar la’asar ne ya tashe ni daga guntun baccin da na tafi,kai tsaye wanka na shiga na fito na d’aura alwala,ina dab da shiga d’aki na ji sallamar Mama ta shigo cikin gidan,ban amsa ba sai tsaki da na ja,ina mamakin irin halin Mama Saude,wai ta san sarai bacci na ke yi amma sai ta yi ficewar ta,ba ta ko karo k’ofar gidan ba,yanzu idan wani ya shigo ya yi min sata kuma fa?

“Allah ya kyauta” Na fad’a ina k’ok’arin shigewa d’aki

Ban kai ga shiga ba na jiyo muryar ta”ke! Uban wa ki ke fad’a wa hakan?”

Banza na bawa ajiyar ta na shige d’aki,don idan na kula ta sai mu kai magriba mu na yi,ko kad’an ba ta gani ta kyale,kuma ba ta gajiya da mita ni ma yau d’in Allah ya sa ba y’an rashin kunya bane a kaina,da haka zan biye mata mu yi ta yi,wannan ya zama jiki kusan kullum sai mun yi,kamar kishiyoyi ko facaloli haka mu ke ni da ita,shi ya sa ma ban fiya zaman gidan ba na gwammace na fita yawona,idan na dawo na sha fad’a a wurin mahaifina.

*Zinatu* kenan,matashiyar budurwa mai ji da kanta,y’ar kimanin shekara ashirin cif,ta kammala secondary tun shekaru uku da su ka wuce,islamiyya kuwa tun tuni ta ajiye ta a gefe,babu yanda ba ta yi da Baban ta ba kan ya bar ta,ta cigaba da karatu ko y’ar digiri ta samu,amma ya ce sam ba zai yi wu ba,a rashin jin maganar ta bai ga dalilin da zai sa ta je makarantar gaba da sakandari ba,don kuwa ya na jin tsoron had’uwar ta da maza,da kuma gogaggun mata,saboda Zinatu ba ta jin magana.Allah ya yi wa Zinatu farinjinin masoya,don duk inda ta shiga sai wani ya k’yasa,ita kuma mutum ko kad’an ba ta sauraron maza,don duka ma ba ta yarda da soyayya ba,wahala kawai ta d’auke ta,haka ne ya sa ta dad’e ba ta tsaida mijin aure ba.

Ba ta da k’awa ko d’aya,sai abokai maza sun fi a k’irga,ita kowa nata ne in dai namiji ne,hakan ne ya sa mutane su ke yi mata kallon ballagaza,wasu ma har su na zargin ta da wani mummunan halin.

Ban gama tsinkewa da lamarin Salim ba,sai da dare ya yi na zo bacci,don kuwa yau duk saurin bacci na sai na neme shi na rasa,hoton fuskar Salim ya yi ta dawo min kamar dai maza bak’ina ne? Sai da na tashi na d’akko k’ur’ani na fara karatu,kafin na fara jin baccin.

Kiran sallar asuba a kunnena,na tashi na yi sallah na koma na kwanta,don baccin yau bai is he ni ba.Shuuu! Na ji Baba ya kunna rediyon sa me hanani komawa baccin safe,na ja tsaki ina shirin sake yin juyi na jiyo muryarsa

“Zinatu! Ke Zinatu!”.

“To fa! Babu lafiya,Allah ya yi dare gari ya waye”. Na fad’a a bayyane ina tashi na saka hijjabi na fito

Zaune na tadda shi a k’ofar d’aki,Mama kuma ta na ta gyare-gyaren wurin sana’arta,da ya ke ta na saida wainar shinkafa da k’uli kullum da safe.Na gaisheta ta amsa a d’ak’ile,na kalli Baba da ya ke nuna min gefen sa,alamar na zauna.

“To ni Zinatu! Allah ya fitar da ni!”. Na fad’a a zuciyata,don kuwa in dai ka ga Baba ya min irin kiran nan da zai bani wurin zama to akwai magana,ko dai zai min fad’a ko kuma nasiha,ille kuwa! Ban gama tunanin laifin da na yi ba,na tsinkayi muryarsa

“Yanzu Zinatu irin rayuwar da ki ka za’bawa kanki ki na ganin za ta kai ki tudun tsira?”

“Subhanallah! Baba me na yi kuma? Ko dai an sake had’ani da kai ne?”. Na yi maganar ina yiwa Mama kallon gefen ido.

Tuni Baba ya tsuke fuska,ya fara magana” yanzu a masallaci a ke fad’a min an ganki jiya wai maza su na koya miki keke,haba Zinatu! Ke me yasa ba kya gudun bakin duniya wai? Kullum burinki ki jawo min abin magana ko,a yi ta nuna ni a gari a na ga mahaifinki ko? Don Allah ki rufa min asiri na aurar da ke lafiya,sauran y’anuwanki dai ba mu yi haka da su ba”.

Yanda ya k’are maganar da sanyin murya sai ya bani tausayi,don ni kaina ina tausayin Baban yanda ya ke ta k’ok’arin ganin na nutsu

“Ka yi hak’uri Baba,zan daina in sha Allah, sai a yi ta saka ni cikin addu’a”.
Na fad’a ina tashi na koma d’akina,ba tare da na jira abin da zai ce ba.

“Kar ma ki daina! Ni kam shi ya sa na matsu ki bar gidan nan ko na huta,da ganin takaicinki”

Mama Saude ta yi maganar ta na jan tsaki.

Katifa na fad’a ina murmushi,tunowa da Anas da ya ke fad’a min tunda na fad’i sau uku ba zan ta’ba iya keken ba.

“Allah ya shiryi y’an gulma” Na fad’a ina rufe idona,tuni bacci ya sureni.

Powered by: www.mynovels.com.ng

error: Content is protected !!