Tag - Siffofin Namiji Hariji Karanta Siffofi guda 10 na Namiji Hariji
Namijin Da Yake Da Wadannan Siffofin Zai Iya Sace Zuciyar Mace Ko Da Sarauniya Ce.
. Turawa mijinki ko saurayinki ya karanta.
A soyayyar gaske wacce babu kwadayi ko jari-hujja a cikinta. Ga irin manyan siffofin da suka fi jan hankalin mace :-
1. Nutsuwa da tsafta (Gentility and Neatness) – Nutsuwa ce ake fassarawa da “basarwa” a bakin matasa. Shashasha shine mara kan-gado wajen magana da mu’amila. Nutsatstsen mutum ba a cika gajiya da zama dashi ba. Mace ‘yar kwalliya ce. Tana son namiji mai kwalliya amma fa bata so ya dinga finta kyau. Tafi so ta fika amma kaima tana so kayi kyau.
2. Namiji jajirtacce (Focus and Hardwork) – irin wadannan mazan har maza ‘yan uwansu suna burgewa. Rayuwa da mutum mai manufa alheri ce saboda ana sa musu rai da cigaba.
3. Wayayyen namiji (Wiseness) – Wayewar kai itace, yin abinda ya dace a lokacin da ya dace. Wayayyen mutum yana da saurin sabo (familiarity). Mace tana son namijin da zai iya sace zuciyar ‘yan gidansu da gaggawa.
4. Namiji mai barkwanci da iya zance (Jokes and Eloquence) – Mata suna son barkwanci. Shiyasa duk mutumin da yake saka mace dariya yana da wahala ta rabu dashi cikin sauqi. Maza masu harshe suna saurin jan hankalin mata saboda suna son hira mai dadi.
5. Qwazo da yabo (Vibrancy and Appreciation) – Namiji mai fasaha yana daukar hankalin mace. Misali, idan har zata shiga cikin 6acin rai tana son mutumin da zai iya kwantar mata da hankali cikin hikima. Wani namijin ya iya abubuwa da yawa. Sannan tana son yabo idan tayi abu ko da kwalliya ce.
6. Kulawa (Caring) – Maza masu baiwa mace kulawa suna da wahalar fita daga zuciyarta. Mace tana so a dinga kula da ita kamar wata jaririya.
7. Kyautar bazata da kamun kai (Surprised gifts and Decency) – Kyautar bazata tana qara wa namiji kwarjini a wajen mace. Kada ka zama marowaci. Matan arziki basa son namiji mara kamun kai saboda kishi da tsoro.
Kudi baya siyan so saidai na qarya. Matarka ta dinga fatan ka mutu saboda dukiya.
Allah Ya Kiyaye.
C. M. K Soron Dinki