Taimiyyah Hausa Novel

Taimiyyah Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

: *TAIMIYYAH*

 

©️Ayshat Ɗansabo Lemu

 

*MABUƊI*

 

*Ina me farawa da godia ga Allah subhanahu wata’ala,da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna asama,ina roƙo ubangiji yayi riƙo da hannuna wajen rubuta dai-dai,ya kuma yafe kusakuran da zasu iya kasancewa aciki Ameen.*

 

*SADAUKARWA*

 

*Na sadaukar da wannnan littafin gaba ɗayansa zuwa ga duk wata me nakasa,especially masu matsala irin na TAIMIYYAH,ina roƙo ubangiji yasa nakasan ta zame muku alkhairy da ɗaukaka a rayuwa.*

 

*Page 1*

 

Matashiyan budurwace kwance ƙudundune cikin bargo,jikinta na faman kakkarwa alamun zazzaɓi ne yai mata kamun me kyau,daga gefenta wata dattijuwa ce wacce shekarunta ya fara nisa sosai,don a ƙalla zatai shekaru sittin da biyar zuwa sama,farace tas dattijuwan me tsagen kalangu a fuskanta hagu da dama,kyakykyawace wanda a kallo ɗaya zaka zaci cewa bafulatana ce,sai dai ba hakan bane bahaushiyace ziryan,wanda ubangiji ne kawai yai mata baiwan kyau da farin fata,hannu takai tana janye bargon da budurwan ta ƙudundune aciki,cikin muryan da ke nuni da tsananin kulawa take faɗin “Tashi TAIMIYYAH ki ƙoƙarta kiyi wanka ko zaki daina wannan rawan sanyin,idan kin karya yanzu sai Sani yazo ku koma asibitin watakila waɗannan magungunan kaɗai bazasu wadatar da ke ba sai an haɗa da alluran dai da ba’a so.”

 

Ta ƙare maganan tana ƙarisa yaye bargon da budurwan ta rufa dashi,nan take kyakykyawan fuskan budurwan da aka kira da TAIMIYYAH ya bayyana,tare da jikinta baki ɗaya wanda take sanye da rigan bacci Ash colour me kauri sosai,kamanninta da tsohuwan daya bayyana sosai zai baka tabbacin idan ba ƴarta bace to akwai alaƙa ta jini me ƙarfin gaske dake tsakaninta da dattijiyan matan,abinda kawai dattiyan zata nuna mata shine fuskan manyance ,amma hatta farin fatan nata irin na Dattijiyan ne,TAIMIYYAH ta yamutse kyakykyawan fuskanta tana sake lumshe manyan idanunta,muryanta can ƙasa dake ɗauke da ƴar shagwaɓa take faɗin “Wash! Allah Iya baki ji kaina ba kaman zai cire wallahi.”

 

Iya ta dube ta cike da tausayi da kulawa tana faɗin “Sannu kiyi haƙury zai bari,yanzu tashi ki shiga wankan na haɗa miki ruwan ɗumi sosai da zakiji daɗinsa,Allah ya baki lafiya TAIMI na.”

 

Budurwan ta amsa da “Ameen.” Tana miƙewa tsaye da ƙyar sai lokacin na kula da cewa tana da tsayi dai-dai misali wanda bai cika yawaba,sam bata da jikin ƙiba sai dai jikin a murje yake cike da tsoka da cikan halitta me ɗaukan hankali,ta sake lumshe manyan idanunta sabida ciwan da kanta keyi,kafin a hankali takai hannunta na hagu ta dafa guiwan ƙafanta na hagun tana me fara takawa zuwa toilet ɗin dake manne cikin ɗakin,Dattijiya Iya tabi bayanta da kallo ƙaunar budurwan da tausayinta na sake ratsa ilahirin jinin jikinta,tana matuƙar tausayin TAIMIYYAH sai dai ko kaɗan ba ta nuna mata cewa nakasan da ta samu na ƙafa yana damunta domin ita kaɗaice a kullum take ba TAIMIYYAN tabbacin haka ubangiji yaso ganinta,tashi tayi tana me ficewa daga ɗakin mintoci kaɗan ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da Mug da ta ciko da zazzafan Kunun gyaɗa da yaji madara sabida sanin TAIMIYYAH na matuƙar son sa,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga toilet,tana ɗaure da ƙaton towel da tsayinsa ya sauka har zuwa guiwanta,ƙafafunta nabi da kallo wanda na lura ɗaya ya sirance ɗaya kuma lafiyayye,ta yadda ruwa ke gangara a jikinta kaɗai zai baka tabbacin Allah yai mata baiwa da sulɓin fata,taiwa Hajiya Iya kallo ɗaya tana sakin murmushi,a hankali ta ciga da dafa ƙafanta na hagu tana takowa zuwa cikin ɗakin,da alamu wankan da tayo yasa ta fara jin daɗin jikinta,Iya ta ɗaga kai ta dubeta tana faɗin “Sannu kinji daɗin jikin ko? ga kununki nan saiki daure ki farasha kafin Ladi ta gama soya miki dankalin.”

 

TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta masu haske ta dubi Iya,cikin sanyin muryanta me daɗi take faɗin “Naji daɗi Iya nagode da kulawa,amma ina ga abar dankalin wannan ɗin kaɗai ya isa,amma zuwa anjima don Allah ki min faten tsaki da kanki irin wanda kikeyi yayi ɗan tsamin yakuwannan shi kawai nake son sha.” Ta ƙare maganan da shagwaɓa sosai a muryanta.”

 

Hajiya Iya tayi murmushi me faɗi tana faɗin “To shikenan baki da damuwa za’ayi insha Allah,yanzu dai sha kunun ki sha magungunan,sai a sake kiran Sanin ku koma asibitin,ki tafi da duka magungunan sabida su gani ki kuma buɗe baki kiyi magana agaban likitan bana son wannan miskilancin naki idan kina ciwo ki ƙi magana.”

 

Hajiya Iya ta ƙare maganan da mita,wanda hakan yasa murmushi me faɗi suɓucewa daga face ɗin TAIMIYYAH wacce ta kammala shafa mai tana ƙoƙarin saka rigan da ta ciro,ba tare da tayi magana ba har Iya ta fice ta sanya doguwan rigan atamfa Red wanda akaiwa adon zanen manyan Flawer da milk and black,yayi mata kyau sosai tare da haska kalan skin ɗinta,bata shafa komi a face ɗinta ba sai lip balm me taushi,qamshin Body mist datai anfani dashi ne ya cika ɗakin baki ɗaya domin ita ɗin ma’abociya son qamshi ce na ajin ƙarshe,zama tayi tana ɗaukan Mug ɗin da Iya ta aje tana fara shan kunun ahankali cike da nutsuwa,magungunan ta sha bayan ta shanye kunun,wani zufa ta fara ji na keto mata hakan yasa ta miƙe tana ƙara ƙarfin gudun Fan ɗin dake aiki a ɗakin,tsaye tayi gaban dogon mirrow ɗin ɗakin tana kallon fuskanta da ya rame sosai a kwanaki biyu kacal da fara ciwan nata,sai fararen manyan idanunta ma’abota haske da ɗaukan hankalin mai kallonta,domin wasu irin idanu Allah yai mata baiwansu masu ɗaukan hankali,ƙirjinta ta kalla tana me waro ido waje ganin cewa ta manta bata sanya Bra ba,gashi fita zasuyi sam bazata iya fita babu shi ba,sabida Allah yai mata baiwan cikar ƙirji,sai dai bawai irin sunyi girman da har suka rankwafa bane,kawai dai bata iya fita haka babu Bra dake tare su ajikinta,wannan sabo ne dataiwa kanta tunda ta isa sanya Bra ɗin,don haka kai tsaye wajen da take aje su ta nufa ta ɗakko tana sauke zip ɗin riganta zuwa ƙasa ta sanya,wayanta dake aje bisa gado ya fara ringing,sai ta nufa wajen don ganin me kiran,ganin sunan Sani ya bata tabbacin yazo kenan,ta ɗaga wayan tana gaida shi tare da bashi tabbacin fitowanta yanzu.

 

“Iya ga Sanin can ya iso zamu wuce.”
 

Littafan Hausa Novels Guda 1000 masu dadi

Matar Makaho Complete Hausa Novel

Hotunan Lalle Masu Kyau Kunshin Gam

Matar Yaro Hausa Novel

Hajiya Gwale Hausa Novel Complete

Gyaran Nono a sari data

Tsofaffafin Hausa Novels Watpadd

 

TAIMIYYAH ta faɗi hakan tana kallon Hajiya Iya dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun da suke qawataccen falon nata,Iya ta ɗaga kai tana sauke ganinta akan TAIMIYYAH da ke sanye da dogon Hijab kalan Red da yai mata kyau sosai,ta saki murmushi tana faɗin “To sai kun dawo ki kula ki kuma buɗi baki agaban likitan bana son wannan miskilancin naki,kice ma Sanin idan kun dawo ya shigo ina son ganin sa.”

 

TAIMIYYAH ta amsawa Iya tana miƙewa hannunta ɗaya riƙe da ƙaramin hand bag da ta sanya magungunan da aka ɗaurata akai,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta na hagu,wanda ke bada tabbacin sai da taimakon dafa guiwan shanyayyen ƙafan take iya takawa tana tafiya,a dukkanin cikar halittan ta babu inda ke da naƙasu sai wannan ƙafan na hagu daya shanye ya silance,kyakykyawace da ta mallaki duk wani cikan halitta me ɗaukan hankali,ahaka ta dinga takawa har ta fice daga falon Hajiya tayo waje,idanunta suka shiga ƙarewa haraban sasan Iya kallo kaman me son gano wani abu,kafin ta cigaba da takawa bisa tsarin yadda ubangiji yaso tafiyan nata ya zamo ahaka har ta fito daga sashin Iya baki ɗaya,ta iso ainihin haraban gidan me ɗauke da part guda biyu duk da na Hajiya Iya ne cikon na ukun,tafiya ta cigaba dayi zuciyanta na karyewa a lokacin da idanunta ke hango mata matar da ta fito daga ɗaya part ɗin,bayan matan wani matashi ne ke biye da ita riƙeda da wata ƙatuwar leda a hannunsa,TAIMIYYAH tayi saurin yin ƙasa da kanta tana cigaba da tafiya har ta iso dai-dai inda Hajiya Shuwa suke tahowa,hakan yasa TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan tana jiran ƙarisowan Hajiya Shuwan wacce suke kira da Umma,matar wan mahaifinta ne wacce taiwa TAIMIYYAN wata irin muguwan tsana.

 

“Ina kwana Umma.”

 

Sune kalmomin da suka fito daga bakin TAIMIYYAH a lokacin da su Umman suka iso suna shirin gitta ta su wuce,sai dai gaisuwan da ta aikawa Umman yasa Umman dakatawa tana zubawa TAIMIYYAH ƙananun idanunta,fuskanta babu ɗigon fara’a ko kaɗan,tai mata wani malalacin kallo memakon ta amsa gaisuwan TAIMIYYAN sai cewa tayi “Ikon Allah su gurguwa kenan ance baki da lafiya,ke kuma haka Allah ya yoki irin jaraba ga nakasa ga yawan ciwo da wanne za’aji? kuma a hakan ake so wani yazo yace zai kwashi jaraba,ga gurgunta ga yawan cuta kaman sikila,to mu dai kurwan mu kur kada arasa me so ace wataran za’a cinnama lafiyayyun ƴaƴan mu gurguwa raguwan cuta.”

 

Ta ƙare maganan da jan tsaki tana yin gaba abinta bayan ta kalli ɗan lelen ɗan nata ta maka masa harara tare da yi masa sign da ido alamun ya shige gabanta,ba tare da ta kuma kallon TAIMIYYAH da tai ƙasa da kai zuciyanta na shiga wani irin ƙunci mara misaltuwa ba,manyan idanunta tuni sun fara tara hawaye, ciwan kan da take riritawa taji ya dawo sabo,cikin ɗan hanzari ta dafa ƙafanta me laluran ta fara cigaba da tafiya,sai dai taku biyu tayi taji sassanyan qamshin turaren BENTLEY na isowa hancinta,kaman yadda kafin tayi wani yinƙuri yayi saurin tare gabanta,manyan idanunsa masu kama da nata ya sauke akanta,wani abu na yawatawa cikin maƙoshinsa,cak! TAIMIYYAH ta tsaya still bata ɗago face ɗinta ba don qamshinsa ya gama bata tabbacin ko waye domin kaf gidan shi kaɗai ne mamallakin irin wannan turaren me qamshin da ke kashe jikinta, amon muryansa me cike da ginshira taji cikin kunnuwanta yana faɗin “Kiyi haƙury Sis da halin Umma please! watarana sai labari ko kaɗan bana so kisa wani damuwa a zuciyanki haka Allah ya halicceki kuma yaso ya ganki, mu da ita babu me halitta haka kuma babu wanda isa ya sauya halittan wani face wanda yayisa,ya jikin naki?”

 

Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,hakan yasa TAIMIYYAH yin jarumtan maida ƙwallan da suka cika idanunta,sai dai duk yadda ta so ɓoye halin da zuciyanta ke ciki ƙaramar zazzaƙan muryanta dake rawa ya fallasata,cikin sanyin muryan da ke kashe zuciyansa take faɗin “Naji sauƙi Yah Sadeeq zazzaɓin ne yaƙi tafiya shine yanzu zamu koma wajen ganin likita,ina kwana dafatan mun tashi lafiya.”

 

Ta ƙare maganan da gaida shi tana me ɗago manyan idanunta ta sauke akan face ɗinsa,sai dai ganin ita ɗin yake kallo yasa ta sake ƙasa da kanta,tana jin yadda idanunsa ke cigaba da yawo akanta,kafin ya furta “Okey! Allah ƙara lafiya yi maza kije tunda yana jiranki zuwa anjima zan shigo sasan Iya sai muyi magana,take care Angle.”

 

Ya ƙare maganan da wani karyayyen sauti daya motsa zuciyan TAIMIYYAH,hakan yasa ta gyaɗa kanta tana lumshe idanunta da buɗesu lokaci guda ta cigaba da takawa zuwa parking space inda take hango motan Sani,ya bi bayanta da kallo tausayinta da matsananciyan ƙaunarta na sake kassara zuciyansa.

 

Ko da TAIMIYYAH ta isa wajen motan Sani baya ta buɗe ta shiga don tana buƙatan kwanciyane sabida yadda kanta ke sarawa,sam baiyi ƙorafi ba domin matsayin driver yake bashi da damuwan duk inda zata zauna ɗin,sannu yai mata yana tada motan bayan TAIMIYYAH tayi ƙarfin halin amsa masa,zuciyanta na mata bitan baƙaƙen maganganun Umma wanda inda sabo yaci ace ta saba da yadda Umma ke kyaran halittan ta da kushe nakasanta tamkar itace tayo kanta a hakan,ba haka Allah yaso ganinta ba, hawaye masu ɗumi suka silalo mata ta kai hannu ta share tana son ƙarfafa zuciyanta kaman ko yaushe,don ganin maganganun basuyi tasiri a zuciyanta sosai ba,sai dai har suka isa asibitin ABU da ke zaria zuciyanta babu daɗi,zuciyanta ya sake nauyi tana tambayan kanta wai har sai yaushe ne zata daina fuskanta gorin halitta da cin fuska daga wasu cikin ahalinta akan yadda Allah ya yota? da ƙyar ta lallashi kanta ta samu ƙwarin guiwan shiga cikin asibitin don ganawa da likita.

 

 

A ƙalla ta shafe kusan awa guda kafin ta fito tana faman liliya inda akai mata alluran,domin bayan dukkanin bayanai da taiwa likitan sai ya sanar da ita dole ta amshi allura guda uku wanda zaa jera yi kullum guda ɗaya,ba don rai yaso ba ta amince domin allura na daga cikin abinda family ɗinta suka tsana akira za’aiwa ƴaƴansu tun bayan laluran data samu TAIMIYYAN wanda ta sanadin allurance ta samu wannan nakasan na shanyewan ƙafa ɗaya,wanda hausawa ke kira da shan inna wanda kuma take fuskantan ƙalubale me tarin yawa daga ƴan uwanta da wasu baren daban ma,kai kace itace ta janyowa kanta laluran da kanta ba Allah ne ya ɗauro mata ba…….

 

 

 

Hello! my people gani da sabon salo sabon tafiya irin wanda Ɗansabo bata taɓa zuwa dashi ba,labarin TAIMIYYAH labari ne mai cike da ban tausayi, haɗi da darasi me tarin yawa ga zallan ƙauna da soyayya me motsa zukata,kada ki bari abaki labari a wannan karon kowa ta ƙoƙarta ta mallaki nata akan fara shi me sauƙi da zan faɗi nan gaba kaɗan,ku dai ku cigaba da bibiyata a shafukan da zasu biyo baya don jin ya rayuwan TAIMIYYAH zai kasance.

 

 

 

 

#Ɗansabo ce#

[23/07, 12:20 pm] +234 814 437 4241: *TAIMIYYAH* ❤️

 

©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

 

 

*Page 2*

 

Lokacin da TAIMIYYAH suka dawo gida daga asibitin ana ta kiraye-kirayen sallan zuhur ne,hakan yasa Sani wuce wa masallacin kusa da gidan,ita kuma TAIMIYYAH ta nufo sasan Iya jikinta gaba ɗaya ya saki ga wani zufa da ke keto mata alamun alluran da akai mata ya fara aiki sosai wajen saukar da Zazzaɓin gaba ɗaya,kaman ance ta kai dubanta ga sashen adana motoci na gidan,idanunta suka sauka akan motar Abie ɗinsu,ƙatuwar baƙar LEXUS tuni taji zuciyanta ya fara gudu wani daɗi ya lulluɓe zuciyanta,domin tayi kewansa matuƙa don sun rabu da shigowa garin shi da matansa da qanninta ,ta cigaba da takawa cikin takun tafiyanta wanda take dafe da ƙafanta na hagu,lokacin da ta sanya kanta a sashin Iya shi kuma Abie na shirin fitowa don zuwa masallaci,kaɗan ya rage suyi karo TAIMIYYAH tai baya don bashi hanya,cikin rashin sa’a hannunta dake dafe da ƙafanta me lalura ya zame,tai kaman zata kifa Abie ɗin yayi saurin taro ta yana faɗin “Subhanallah! ki dinga kula Zainab.”

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

 

Wasu littafan Hausa Novels da zaku so Kuma zaku iya download kyauta

TAIMIYYAH da duk murnan ganinsa ya gama cika ta tai murmushin da suka bayyana kyawawan haƙoranta,cikin zallan murnan daya kasa ɓoyuwa take faɗin “Sannu da zuwa Abie,i miss u so much tare da su Ummie kazo?”

 

Alhaji Sameer ya gyaɗa mata kai yana sakin murmushi yake faɗin “We ol miss u too dear,tare muke ya jikin naki hope kina samun sauƙi sosai?”

 

Ta gyaɗa kai da shagwaɓa take faɗin “Naji sauƙi sosai Abie bari in shiga daga ciki na ga masallaci zaka sai ka dawo.”

 

Daga haka ta raɓa shi ta wuce ya bi bayanta da kallo,yana kallon yadda take tafiya wanda shi yake ganin kaman a wahalce take takawa,tausayin ƴar sa da ƙauna irin ta uba da ƴa ke ratsa sa,sai da ta ɓacewa idanunsa sannan ya juya ya fice daga sasan baki ɗaya.

 

A cikin sasan Iya kuwa TAIMIYYAH na shiga falon Iya bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka fara sauka akan qanwarta Nahar,yarinya ƴar shekaru bakwai zuwa takwas,Iya da Ummie da ke zaune cikin falon ne suka amsa sallaman TAIMIYYAH,yayinda Nahar ta rugo da gudu wajen TAIMIYYAH tana faɗin “Oyoyo! Anty TAIMIYYAH.”

 

TAIMIYYAH da tayi saurin jingina da jikin kujera don kar Nahar ɗin ta kadata,tayi saurin sakin murmushi tana ware mata hannuwanta Nahar ta shige,ta rungume yarinyan tana faɗin “Welcome My Baby i miss u.”

 

Raudha yayar Nahar ce ta iso itama tana ma TAIMIYYAH oyoyo,TAIMIYYAH ta rungume su duka sunata murnan ganin juna,Raudha zatai shekaru goma sha ɗaya,kallo ɗaya zakai mata kasan sun haɗa jini da TAIMIYYAH,domin kamansu ɗaya da Iya har farin fatan,yayinda suka ɗakko manyan idanun Abie farare tas,sakin su TAIMIYYAH tayi tana nufan wajen su Iya,Nahar ta biyo bayanta tana faɗin “Anty har yanzu Abie ya kasa sawa a gyara miki ƙafanki ki dinga tafiya irin yanda mukeyi,kuma a daina ce miki gurguwa yadda su Anty Zuhrah ke kiranki.”

 

Ummie ne tayi saurin buge bakin Nahar ɗin a lokacin da ta iso wajen,yayinda TAIMIYYAH tai murmushi tana duban Nahar ɗin da muryanta me raunin daya fallasa cewa maganan Nahar ya taɓa zuciyanta,ta furta “Nahar ba laifin Abie bane domin bashi ne zai iya sawa ƙafan ya gyaru ba,ni haka Allah yaso ganina karki damu kinji,ni Allah bai nufa in dinga tafiya irin yadda kuke yi bane kuma ki daina ɗaukan maganan da su Anty Zuhura ke faɗi kina sawa a ranki kinji ko?”

 

Yarinyan ta gyaɗa kai alamun gamsuwa yayinda TAIMIYYAH tai ƙasa tana gaida Ummie,Ummien ta amsa da kulawa duk da cewa fuskanta babu wani alamun ɗoki ko murnan ganin TAIMIYYAN,domin irin matannan ne marasa sakin fuska,sam bawai ta damu da TAIMIYYAN bane kanta da ƴaƴanta kawai tasani,shiyasa tun lokacin da Abie ɗin ya auro ta ya nuna son ta riƙe TAIMIYYAN ta bijera masa,domin a ganinta zama da irin su lalurace kawai da ɗawainiya duk da cewa babu abinda yake gagaran TAIMIYYAN a hakan babu abinda bata iyawa,hatta da ɗaukar ruwa a bucket da duk wani aikin ƙarfi gwargwado tana iyawa,babu abinda ake taimakonta dashi sai ƙalilan,sannu da dawowa Iya taiwa TAIMIYYAH tana tambayanta yadda sukai da likita,TAIMIYYAH ta sanar da ita cewa allurai aka bata uku anyi ɗaya saura gobe da jibi,Iya tai mata fatan samun sauƙi daga haka ta zame jikinta ta nufi ɗakinta don yin wanka da sallah sabida yadda take jin zufa ya jiƙe jikinta bazata iya komiba ba tare da ta sake wanka ba.

 

Lokacin da ta fito wankan samun su Nahar tayi sunyi ɗai-ɗai a bed ɗinta,suna faman kallon ƙaton photo album dake aje saman Bed side na gado,kallo ɗaya tai musu ta saki murmushi tana wucewa wajen kayanta,doguwar riga mara nauyi ta saka me taushi bata shafa komi ba a jikinta,ta zura Hijab ta tada sallah,bayan ta idar ne ta tasa kan su Raudha zuwa falo lokacin Abie ya jima da dawowa daga masjid,zama sukai gaba ɗaya aka shinfiɗa babban ledan cin abinci wanda aka jera manyan kulolin abinci duk da cewan zuwan bazata sukai bai hana Iya saka Ladi me aiki shirya abincika masu sauƙi ba,tare sukai lunch ɗin gunin sha’awa TAIMIYYYAH na jin farin ciki sosai na ganin ahalinta,duk da cewa sam babu cikakken wani shaƙuwa tsakaninta da Abie ɗin,amma hakan baya hana ta shiga farin ciki a duk sanda zai zo garin walau shi kaɗai ko da su Ummie ɗin,Ummie itace ta fara tashi daga wajen cin abinci tana sanar da Iya cewa zata wuce part ɗinsu,Iya tai mata Allah huta gajiya tai gaba su Nahar ko kallonta basuyi ba bare suyi yinƙurin bin ta suna nane da TAIMIYYAH domin Allah ya ɗaurawa yaran son Yayar tasu,ko don irin kulawa da ƙaunar da TAIMIYYAN ke gwada musu ne Allah masani,lokacin da Abie ya kammala cin abincin yayi hamdala tare da goge bakinsa da tissue,sai ya ɗaura manyan idanunsa akan TAIMIYYAH wacce itama ta gama cin abincin tana gogewa Nahar baki ne,cikin murya me nuna kulawa yake faɗin “Zainab yanzu kin gama NCE ɗinki sai kuma miye plan ɗinki na gaba,aure ko karatun zaki ɗaura?”

 

Kalman aure daya shigo cikin kalamansa yasa TAIMIYYAH saurin waro idanunta,cikin muryan da ke nuna kiɗima take faɗin “Abie aure kuma? Karatun dai zan ɗaura ni bazan yi wani aure ba waye ma zai auri gurguwa kaman yadda Umma ke faɗi.”

 

Ta ƙare maganan tana turo baki alamun shagwaɓa,Iya da ke zaune duk tana jinsu ta ɗago tare da saukewa TAIMIYYAH harara tana faɗin “Ashe ban hanaki irin waɗannan kalaman na banza ba TAIMIYYAH,don Allah ya yoki ahaka sai akace shikenan bazaki samu masoyin da zai aureki a haka ba,to bari kiji wanda suka fiki nakasama sunyi aure har sun haihu bare ke da babu abinda ma yake gagaranki,kije gidan Malam Inuwa ki kallon gurguwan da bata ko iya tashi ta miƙe a nannaɗe take amma tayi aure ƴaƴanta goma sha biyu zar sunanan suna taka doran ƙasa,don haka ki iya bakinki ki kuma daina ƙoƙarin ja da ikon ubangiji,ita wacce kike ji abakin nata tana cewa bazaki auru ba sai ki zuba mata ido ki ga idan itace ta halicceki da zata hana Allah ikon sa,ni a nawa ma babu wani karatun da zaki ɗaura Allah ya kawo me so kiyi aurenki kawai ki huta.”

 

Tunda Iya ta fara magana ko tari babu wanda yai har ta dasa aya cike da sababi da jin zafin Hajiya Saratu a ranta,Abie ne ya dubi mahaifiyan na su yana faɗin “A’a Iya idan har tana son cigaba da karatun kar a tauyeta,abata dama ta ɗaura idan yaso tana cikin yi Allah ya kawo me son sai ayi auren,amma zaman haka bazai yiwu ba,Zainab wani skull ɗin kike so gashi yanzu ana cikin wannan strike ɗin,ni kuma bazan so ki tafi wani gari ba sabida laluranki, karatunki a kusa da gida zaifi,don haka sai dai ajira aga janyewan yajin aikin malaman sai asan abinyi,idan akwai wani plan ɗin da kike dashi ina jinki tell me.”

 

 

Abie ɗin ya ƙare maganan idanunsa akan TAIMIYYAH da daɗi ya cika ta,na jin cewa Abie ɗin bazai hanata cika burinta na son yin karatu me zurfi ba,cike da ɗoki take faɗin “Abie zan fara yin wani Computer Skull kafin a dawo daga yajin aikin,ina so in samu certificate na Computer Training ɗin,kuɗin form da na registration kawai zaka bani,a can wajen Congo ne sai Sani ya dinga kaini yana ɗakko ni ko Abie?”

 

Alhaji Sameer ya jinjina kansa cike da gamsuwa yake faɗin “Eh hakan ma yayi kinyi tunani me kyau,karki damu zan baki kuɗin komi da komi,amma Iya tace an baki allurai uku meyasa kika yadda aka fara,kinsani sarai bana so ko kina manta alluran shine silan laluranki Zainab.”

 

Ya ƙare maganan da faɗa sosai wanda yasa TAIMIYYAH bashi haƙury,tare da sanar dashi magungunnan ne basui mata ba dole sai an haɗa da alluran,tare da su Raudha ya bar sashin zuwa part ɗinsu da suke sauka idan sun zo daga Lagos ɗin.Bayan fitan su Iya ta kalli TAIMIYYAH da ke ta faman murnan zata shiga Computer skull,ta maka mata harara tana mitan faɗin “Ayi dai mugani duk son karatun mutum da ƙinsa da aure indai lokacin mutum yayi dole yai auren ba.”

 

Kafin TAIMIYYAH tace komi suka jiyo amon muryansa,wannan dai muryan nasa me cike da isa yake doka sallama daga bakin ƙofar ɗakin Iyan,Iyan ce ta amsa sallama tare da bada izinin shigowa,qamshin turaren BENTLEY ya riga isowa cikin ɗakin kafin gangar jikinsa ya shigo,idanunsa ya sauke akan TAIMIYYAH da ta miƙe tare da dafe ƙafanta ta fara takawa don komawa ɗaki ta kwanta,baiyi magana ba har ta shige corridor ɗin da zai sadaka da Bedrooms ɗinsu,illa ɗauke kansa da yai ya maida dubansa kan Iya yana takowa cikin falon,a kujeran 2 seater ya zauna yana fuskantan Iya ya fara gaida ta,ta amsa fuska a sake tana faɗin “Yanzu Sadeek ka dawo tun jiya sai yau zaka shigo gaida ni,to kayiwa kanka ne aiko baka shigo ba ka zo don mutuniyar ka dana tabbatar kaji bata jin daɗi ko da yake naga yanzu ƴar wasan ɓuya kuke tunda uwarka bata ƙaunar jituwan da ke tsakaninku.”

 

 

Ta ƙare maganan cike da sababi hakan yasa Sadeeq sake haɗe fuska,yana wani taɓe baki yake faɗin “Ke dai Iya kin faye son nacin magana ɗaya,waya gaya miki wasan ɓuya muke ita ɗince dai bansan meyasa bata son haɗuwan mu ba yanzu ko don taga ta gama zama Big Girl ce oho.”

 

Iya ta taɓe baki itama tana faɗin “kadai ji da ƙaryan turancinka,ya wajen aikin naku ina fata dai komi na tafiya yadda ya dace ko?”

 

Sadeeq ya gyaɗa mata kai kawai,kafin ya miƙe ya nufi wajen cin abinci yana faɗin “Iya akwai abincin da zan iya ci anan,cikin gida tuwon shinkafa akayi ni kuma banso,ai na ga motar Abie ashe sun shigo.”

 

 

Iya ta amsa da “Eh aiko sai ga su babu sanarwa,sai ka duba akwai ragowan shinkafa da miya sai dai mayyan Salad ɗin ta juye shi ta kai fridge.”

 

Tuni ya gane wa take nufi don haka baice komi ba sai nufan hanyan ɗakinta da yai,Iya ta bi bayansa da kallo tana taɓe baki ba yau ta gama gane jikan nata ya kamu da son ƴar uwan nasa ba,sai dai bata ji ko sama da ƙasa zasu haɗene zata bar TAIMIYYAH ta aure shi,sabida ƙiyayyan da uwansa take gwadawa TAIMIYYAN,shiyasa tai biris bata taɓa nuna musu daga shi har TAIMIYYAN tasan abinda suke ciki ba……..

 

 

 

*Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

 

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

 

 

_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻

 

 

*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU

 

*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*

 

*Recharge* – inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

 

*Balance* – Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

 

*Credit/Debit Card* – Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

 

A inda (Enter your amount) za’a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba “Proceed”. Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

 

——–

 

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

 

*Bank Transfer*

*Airtime Transfer*

 

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za’a gansa a Balance.

 

 

*Bank Transfer* – kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.

 

_Account No_ – *1220077999*

_Account Name_ – *Arewa Books Publishers*

_Bank_ – *Zenith Bank*

 

Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:

 

Amount Paid: – Nawa aka tura?

 

Name used for transfer: – sunan da aka saka wajan turowa

 

Transferred time: – lokacin da aka turo

 

Name of bank: – sunan bankin da aka turo dashi

 

Deposit date: – ranar da aka turo

 

Sai ayi SUBMIT.

 

*Airtime Transfer* – muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:

 

MTN,

9Mobile

Glo

Airtel

 

Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.

 

*WANNAN SHINE BAYANAN*

 

 

 

#Ɗansabo ce#

[23/07, 12:21 pm] +234 814 437 4241: *TAIMIYYAH*

 

©️Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

 

*Page 3*

 

Yana sanya kansa cikin ɗakin sassayan qamshin daya kama ɗakin ya doki hancinsa,ya ɗan lumshe idanu yana jinjina tsafta da son qamshi irin na TAIMIYYAH,halayyanta da ke sake saka shi jin ta aransa sosai da yaba ƙoƙarinta akan kula da kanta, duk da laluran ƙafanta sam bata da ƙyuiya da son jiki,kwance ya hange ta tayi ruf da ciki tare da tokare hannayenta da pillow waya riƙe a hannunta,sam bata ji sallamansa ba sai qamshin turaren BENTLEY da ya buɗe ɗakin,hakan yasa ta saurin tashi zaune tana sauke manyan idanunta akansa,fuskanta a sake take faɗin “Yah Sadeeq shigowa kayi,ina yini.”

 

Harara ya zabga mata yana takawa zuwa wajen stool da ke gaban madubi ya janyo ya zauna,idanunsa ya mayar kanta kafin ya buɗe baki cike da ginshira yake faɗin “Wannan yarinyan kin girma da yawa kin fara raina mutane ko? Ba kina kallo na shigo ba amma ki kai tahowanki sabida baki ƙaunar haɗuwan mu yanzu ko? to yau sai kin gaya min yadda akai na zama dodo har da kike guduna.”

 

Ya ƙare magana babu alamun wasa ko sassauci a face ɗinsa,hakan yasa TAIMIYYAH sake dubansa ya sake jefa mata harara,ganin hakan yasa ta tsuke baki tana faɗin “Kayi haƙury ni fa ba gudowa nayi ba,kasan banda lafiya to kwanciya na shigo yi ina jin jiri ne.”

 

“Allah ya sauƙe ya baki lafiya,amma meyasa tun wancen week ɗin dana shigo kika ƙi bari mu haɗu har na koma?”

 

Yadda ya tsare ta da ido yasa ta kauda kanta,ba tare da tace komi har sai da ya sake maimaita tambayansa sannan ta ɗago ido ta dube sa kafin ta shagwaɓe murya tana faɗin “Umma ce fa tace in daina shige maka inba haka ba duk randa ta sake ganina da kai saita ƙarisa ɗayan ƙafan nawa na zama gurguwan me sosai.”

 

Yadda ta ƙare maganan muryanta na ɗan rawa yasa jikinsa yin sanyi,cikin taushin muryansa me kauri yake faɗin “Amma sau nawa zance ki daina damuwa da maganganun Umma,haba Baby meyasa kike son kafa Hujja da Umma ni kuma kina azabtar da zuciyata why?”

 

TAIMIYYAH da tai ƙasa da kanta ta ɗago tana ƙoƙarin danne hawayen da ke son zubo mata,cikin rawar murya take faɗin “Dole in saka maganganunta araina Yah Deeku,Umma bata so na bansan miye laifi na don na kasance gurguwa ba,bani nai kaina ba inda ana ba ɗan Adam zaɓin ya zaɓi yanda yake son halittansa ya kasance bana ji akwai wanda zai zaɓi nakasa,amma ita sam ta kasa gane bani ce na zaɓi zamowa a haka ba,yanzu ba da bane Yah Deeku nasan ciwan kaina a yanzu,maganganunta suna ƙona zuciyata kaman yadda wuta ke ƙona itace,dole in kiyaye duk abinda zai dinga janyo min gorin halitta,kayi haƙury Umma uwace a guna amma zuciyata bazata iya juran yawan aibantani da takeyi ba,shiyasa tunda ta nuna bata son shaƙuwan dake tsakaninmu dole mu koyi nisanta da juna.”

 

Zuwa lokacin da TAIMIYYAH takai ƙarshen magananta tuni hawayen da take dannewa sun ɓalle,suna zarya a saman kyakykyawan face ɗinta,Yah Sadeeq da tunda ta fara magana ya tsura mata ido,ransa yai matuƙar sosuwa da hawayen da take zubawar,ya sani tafi shi gaskiya domin kaman yadda ta faɗi ne babu wanda yasan ciwan kansa da zai so jin yadda Ummansu ke kyaranta tana aibanta nakasanta kai kace TAIMIYYAN irin guragunnan ne da basa ko iya tafiya,cikin muryansa da ya bayyana raunin da zuciyansa shi ma yayi yake faɗin “Yanzu kina nufin sabida Umma ne zaki daina kulani bayan kinsan zuciyata ta riga ta kamu da ƙaunar ki Zainab,ya kike so inyi da wannan sabuwan ɗabi’an da sam bazan iya jure masa ba?”

 

Sanin bazata amsa masa ba yasa shi kai tsaye cigaba da faɗin “Lokaci yayi da zan fito fili insanarwa da Umma ke nake so,so kuma da aure ko hakan zai tabbatar mata da cewa alaƙanmu dake ya wuce shaƙuwa na ƴan uwantaka,zallan soyayya ce mara algus.”

 

Kukan da TAIMIYYAH ta sanya masa ne yasa shi tsura mata ido cike da mamaki,baki buɗe yake kallonta wani abu na yawo a cikin zuciyansa,cikin muryan kukan take faɗin “Ka dubi girman Allah Yah Sadeeq karka faɗawa Umma wannan maganan,wallahi kasheni zatayi nina sani,don Allah karka shigo da abinda kasan bazai taɓa yiwuwa ba,alaƙanmu ta tsaya iya na ƴan uwantaka, ka riƙe girmanka na Yayana wanda nafi so da shaƙuwa dashi,me sharemin kuka na da bani dukkanin ƙwarin guiwa,don Allah kada ka rusa wannan alaƙan ka shigo da batun da bazai taɓa yiwuwa ba illa jefa rayuwata cikin garari.”

 

Kuka takeyi sosai zuwa lokacin domin ita kaɗai zata iya gayawa duniya irin tsanan da Umma tai mata,ba ta ji ko za’a tashi duniya zata iya amincewa da Yah Sadeeq ɗin ya zama abokin rayuwanta,ta sani yana son ta don ya riga ya jima da fallasa mata sirrin zuciyansa,ita ɗince har yau ya kasa jin taƙamaimai miye a zuciyanta game dashi,baya hango kowace irin soyayya a idanunta daya wuce na ƴan uwantaka,irin na wanda shaƙuwa ya shiga tsakani,cikin tsananin ɓacin rai ya daka mata tsawan da yai saurin sata sake rushewa da kuka me ƙarfin gaske,ta kai hannu tana toshe bakinta ganin yadda ya taso yana nufota,ta shiga matsawa da baya-baya tana cigaba da toshe bakinta kuka nacin ta,zama yayi daga bakin Bed ɗin yana kai hannu ya janyota baki ɗaya zuwa jikinsa,kafaɗunta duka ya kamo yana girgizata yake faɗin “TAIMIYYAH me kike nufi da waɗannan kalaman,kina so ki gaya min tuntuni ni kaɗai nake haukata ke zuciyanki bata kamu da soyayyata ba? Ki sanar dani ni kaɗai nake shirme na kome?”

 

Yadda yake magana yana ɗaga murya da sake jijjiga kafaɗunta yasa TAIMIYYAH sake rushewa da kuka,sai dai kafin tayi wani yinƙuri sai shigowan Iya suka ji cikin ɗakin,ta tafa hannu tana salati tana faɗin “Me zan gani Saddeeku dukanta kai bata da lafiya kome,ko kaima ka fara kurɓe kurɓen zamanin nan da samari keyi ne bamu da labari? To sakarta tun ranka bai ida ɓaci ba,ka kuma sanar dani tun farko ma uban mi ya kawo ka ɗakinta?”

 

Sadeeq da ransa ya gama ɓaci sai ya saki TAIMIYYAH yana ballawa Iya harara yake faɗin “Bansani ba miye naki na shigowa nan ɗin kaman an kiraki.”

 

Iya takai hannu ta bige bakinsa tana faɗin “Yi min shiru mara kunya,kuma ka gaya min me tai maka da zaka tasa ta agaba kana jijjiga kaman ka biya sadakinta sabida tambaɗa da fitsara,to ahir ɗinka ka kiyayeta ince dai soyayya ce kakema wannan haukan,to inma son ta kake tun wuri ka cire bazata so ka ba,inma ta fara dole ta daina kowa yai ta kansa,indai ina raye TAIMIYYAH ba zata aure ka ba uwar ka taje can ta zaɓo maka matan aure amma ba dai Zainab ba,wuce ka kabar min sasa tun bansa an kira min uwar ka da uban ka sun maka iyaka daga shigowa nan ɗin ba.”

 

Yadda Iya ta rintse ido tana yayyafin masifa yasa Sadeeq ficewa cikin zafin nama,zuciyannan kaman ya faso ƙirjinsa sabida ɗaukan zafi,Iya ta bishi da tsaki kafin ta koma kan TAIMIYYAH tana lulluɓeta da faɗa kaman zata duke ta,cikin faɗan take cewa “In banda ke ɗinma banza ce uwar sa har nan tazo tai miki iyaka da ɗanta,amma shine zai lallaɓo ya tasaki agaba har da kama jikinki yana girgizawa baki fito kin bar masa ɗakin ba,yo ko dai kema son nasa kike? Aiko da kinyi asaran duniya kin kuma ba mutane kunya me zakici da mutumin da uwarsa bata da aiki saina aibanta halittanki tana kyaranki,to ahir ɗinki wallahi idan kika biyesa har ya yaudari zuciyanki sai dai ku mutu da son juna amma bazaki aure sa ba indai ina numfashi kuma na isa dake,shashashu kawai marasa hankali.”

 

TAIMIYYAH dai kuka kawai takeyi ba tace uffan ba har iya ta gama bambaminta ta fice,sai ta zame ta kwanta tana cigaba da kuka me tsuma zuciya,ita sam bata taɓa jin cewa zata iya son kowani namiji bama bare Yah Sadeeq ɗin,meyasa Iya zata ɗauki zafi da ita har haka? ta cigaba da kukanta zuciyanta na ƙuna ,kiran wayanta da akai ne yasata tsai da kukan bayan ta ɗauki phone ɗin ta ga cewa qawarta Haneefa ce me kiran,basu jima suna magana ba sukai sallama da juna,TAIMIYYAH ta nufi toilet ta wanke face ɗinta ta fito,dogon Hijab ta zura ta ɗauki phone ɗinta ta fito,a falo taci karo da Iya har lokacin bata fasa ƙananun mitanta da ta saba idan ranta ya ɓaci ba,kallo ɗaya taiwa Iyan ta ɗauke kai tana takawa zuwa ƙofan fita falon ba tare da tayi niyyan tankawa Iya ba,ganin da gaske fita TAIMIYYAH zatayi ba tare da ta kula ta ba,ya sanya Iya ɗaga murya tana faɗin “Au binshi zakiyi don na kore sa,ko kuwa gidan ubanwa zaki kina fama da kanki?”

 

 

TAIMIYYAH da takaicin Iya ya gama cika ta,ta juya ta balla mata harara kafin ta furta “Ni part ɗin Abie zani tunda yau abin naki akaina zaki sauke shi.”

 

Yadda TAIMIYYAN tayi magana cike da shagwaɓa da jin haushi yasa Iya sakin murmushi,tana faɗin “Oh’oh’oh me yai zafi daga faɗin gaskiya kuma ƴar nan,dawo kije ki kwanta tunda ba lafiya ne dake ba,ni ina jiye miki ne yadda uwarsa ta tsaneki me zaki ci dashi Allah na tuba,ko da kike a haka ai kinfi ƙarfin ajinsa ke ɗin matar manya ce.”

 

Wani hararan TAIMIYYAH ta ballawa Iya tana juyowa ta dawo cikin falon,kujeran kusa da Iya ta nufa ta kwanta tana faɗin “Nidai Iya wallahi fitinanki idan ya tashi yana bani tsoro,yaushe rabon da kika ga na kulasa amma sabida son ɗauramin laifi har da faɗin ko na fara son sa ne,ni bana son sa kuma bazan so kowa bama bare aje ana min gori,auren ma bazanyi ba ko zanyi kuma zanyi fatane Allah ya bani me nakasa irin tawa ta yadda ƴan uwa da danginsa babu wanda zai min gori,amma Yah Sadeeq bazan taɓa iya bashi zuciyata ba Iya don Allah ki kwantar da hankalinki,ni abinda kawai zakiyi ki birgeni ki samu Abbah da maganan kice masa baki son sake jin shi Yah Deekun ya tada maganan.”

 

Iya da ta tsurawa TAIMIYYAH ido tsananin tausayin ta na faman ɗawainiya da ita,ashe dai TAIMIYYAN na son auren gori take gudu sabida nakasan ta,zuciyan Iya ya motsa da wani irin yanayi me wuyan fassara,ji take da komi nata zai ƙare akan TAIMIYYAN ƙafanta ya dawo dai-dai da zata iya sallamawa,sai dai ita ɗin shaida ce akan irin yawon manyan asibitocin ƙashi da sukai tun TAIMIYYAN na ƙarama har kawo yanzu,amma ba’a dace ba ƙasar waje ne kawai ba’a fita da ita ba,ita da kanta TAIMIYYAN da ta gaji da wahala ta roƙi a ƙyaleta haka ubangiji ke son ganinta,Iya ta furta “To shikenan karki damu zanyi magana da Sanin,ni dai abinda nake so kisawa ranki gorin da ake miki bazai sauya komi ba,akan duk abinda Allah yai nufin kasancewansa,kada kisawa zuciyanki lallai sai me lalura irin taki zaki bawa dama,ina fa lura da dake sarai kina samun masoya kece kike kore su ashe sabida wannan manufan ne dake ranki? To wallahi ki kiyayeni angaya miki sai me lalura ne irin taki kaɗai zaki aura ki samu kwanciyan hankali da soyayya? Wannan shirmenki ne kawai ke dai ki dinga addu’an Allah yai miki zaɓi mafi alkhairy kawai.”

 

TAIMIYYAH kai kawai ta gyaɗawa Iya alamun gamsuwa da kalamanta,daga haka suka kulle wannan babin,Iya ta ɗakko mata zancen aminiyanta Hajiya Juwairiyyah,wacce suka rabu da saduwa da juna,cikin hiran Iya ke sanar da TAIMIYYAH da zaran ta sake samun sauƙi zasu kaiwa Hajjajun ziyara,ita dai TAIMIYYAH jin Iya kawai take yi amma sam a ranta bata son zuwa ko’ina, ita sam tafiye-tafiye basu dame ta ba…….

 

 

 

Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

 

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

 

 

_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_

 

 

*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU

 

*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*

 

*Recharge* – inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

 

*Balance* – Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

 

*Credit/Debit Card* – Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

 

A inda (Enter your amount) za’a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba “Proceed”. Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

 

——–

 

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

 

*Bank Transfer*

*Airtime Transfer*

 

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za’a gansa a Balance.

 

 

#Ɗansabo ce#

[23/07, 12:21 pm] +234 814 437 4241: *TAIMIYYAH*

 

©️Ayshat Ɗansabo Lemu

 

*Page 4*

 

Kwanaki biyar da suka biyo baya TAIMIYYAH ta samu sauƙi tayi garas,don ta gama amsan alluranta har tana harkokinta,tun safiyan yau da ta tashi tana jin cin Meat pie,sai dai basu da nama ya ƙare dole sai ta aika an siyo gashi Nura almajirin Iya kwana biyu bai zuwa ya tafi gida,bayan tayi wanka ta shirya wajen ƙarfe sha ɗaya har da rabi,ta samu Iya a ɗaki don sanar mata zata fita cefanan yin Meat pie ɗin ta dawo,don kuɗi sosai take dashi a hannu,sabida duk idan Abie zai koma yana barin mata kuɗi sosai a hannunta,gefen gadon Iya ta samu ta zauna ganin Iyan akan dadduma alamun idar da sallan walhan ta kenan tana addu’a,wayanta da taji yana ring acikin ƙaramar jakan hannunta ta ciro,ganin sunan Mubarak yasa ta share kiran tare da maida wayan silent,Mubarak wani course mate ɗinta ne da sukai NCE tare,shi a dole son TAIMIYYAH yake da gaske sai dai ita kuma bai taɓa birge taba,mutuncinsa da take gani da irin taimakonta da yake yi akan karatu yasa ta kasa blocking ɗinsa,Iya ta waiwayo ta zubawa TAIMIAYYAH idanu,wacce ke sanye da Hijab kalan Pusha Pink daya haske farar fatanta,tayi kyau ƙwarai duk da cewa babu komi akan face ɗin illah manyan fararen idanunta da ta sanyawa kwalli,sai bakinta da sai ka kalla da kyau zaka gane ta goga lip gloss,wani kuma zaiyi zaton pink ɗin janbaki ta saka domin pink lips gareta.

 

“Sai ina kuma da hantsinnan TAIMIYYAH?”

 

Iya ta jefa mata tambayan har lokacin idanun Iyan na kan TAIMIYYAH,TAIMIYYAH ta dubi Iya tana sanar da ita inda zata da abinda zai kaita,Iya ta gyaɗa kai tana faɗin “To shikenan sai kin dawo ki kula da kyau,ni bana son yawan zuwa kasuwan da kike da Nura na nan ma babu inda zaki gaskiya,ga ɗari biyu can saman madubi idan kinga Goro me kyau ki siyo min.”

 

TAIMIYYAH da ta miƙe tana me dafa ƙafanta ta fara tafiya take cewa”Bar shi Iya akwai kuɗi sosai a hannuna bayan Goran ma har Gautan Yalo idan na gani duk zan siyo miki.”

 

“To Allah yayi albarka TAIMI na,Allah fito min da suruki nagari.”

 

Cewan Iya tana bin bayan TAIMIYYAH da kallo,cike da so da ƙauna haɗi da tausayinta me zurfi,a ciki TAIMIYYAH ta amsa addu’an Iya tana cigaba da takawa har ta fice daga ɗakin,lokacin da ta fito haraban gidan sai ta dubi part ɗin Abie da ke kulle,ta cigaba da tafiya tana jin kewan su Nahar na ratsata don kwanaki biyun da sukai ba ƙaramin ɗebe mata kewa da sanya ta farin ciki sukai ba,sam bata kula da fitowan su Zuhura daga Sashin su ba,sai da ta kusa fita daga gate ɗin gidan sai ji tayi kawai an janyo Hijab ɗinta ta baya,ta waiwayo tana sauke idon ta akan Basma,kafin ta buɗe baki don musu magana Zuhura ta riga ta da faɗin “Dallah! Malama bamu waje mu wuce sauri muke kinzo kina wannan shegen tafiyan naku na guragu,salon a bangajeki ki faɗi ki janyo ma mutane masifa,yanzu gaba ɗaya na ga wani tashen girman kai kike ji tunda Yaya ya zubda ajinsa yace ke yake so,ko mai zaici da gurguwa bansani ba,ko da yake kila kyawu da dirin jikin yake mawa,inma hakan ne banda abinsa idan Kyan da nonuwan ke ruɗansa ga lafiyayyun ƴan mata nan da suka haɗa komi mitsuww!”

 

Zuhura ta ƙare maganan da jan dogon tsaki,Basma na taya ta yayinda TAIMIYYAH da suka ja gefe tayi saurin durƙusawa ƙasa,tuni hawaye sun fara zarya a face ɗinta,har suka fice daga gate ɗin ta kasa koda motsawa,kanta na duƙe tana ji zuciyanta na mata wani irin zafi kaman ya kama wuta,ko kaɗan bata fiya ganin laifin su Zuhuran akan duk irin cin mutuncin da suke mata ba,tafi ganin laifin Umma domin a wajenta suka fara gani,itace ta koya musu hakan duk da cewa TAIMIYYAN age mate ɗin Zuhura ne watanni biyu kacal ke tsakaninsu,amma ace har Basma da take qanwan bayanta ta san taci zarafinta akan kawai ta kasance me nakasa,wasu hawayen masu tsananin zafi suka sake wanke face ɗinta,tayi saurin buɗe jakanta tana ciro hanki da ke ciki ta shiga share hawayen ,tana rarrashin kanta kaman yadda ta saba,don wannan ba shine karon farko ba,idan zasu haɗu so dubu to tana da tabbacin sai sun goranta mata sunci fuskanta,taso fasa fitan kawai ta koma amma sai tayi tunanin Iya zata tsare ta da tambaya,da zaran ta gaya mata yadda sukai da su Zuhuran kuma to abin bazai kyau ba domin Iya wanke ƙafa zatai ta je taci mutuncin Umma da su kansu su Zuhuran,wanda hakan bakomi yake sake janyowa TAIMIYYAN ba sai tsantsan tsana,don haka kawai ta miƙe duk jikinta yayi sanyi ta cigaba ta kawa har ta fice daga gate ɗin gidan,idanunta sun rine sabida kukan da tayi amma bata da zaɓi haka ta cigaba da tafiya bisa yadda Allah ya nufeta da takawa,ta miƙo layin nasu sosai tana cigaba da tafiya,wasu yara da suka zo wucewa ne suka zuba mata ido suna kallonta,ƙaramin cikin su ne ke cewa “Laah! Gurguwa ce kunga yadda take tafiya.” Ya ƙare maganan yana kwatanta ma ƴan uwansa yadda TAIMIYYAH ke dafe guiwanta tana takawa,TAIMIYYAH da ke cigaba da tafiya duk tana jinsu yadda suka biyo bayanta suna ta kwaikwayon tafiyanta,idan tace zuciyanta baya shiga ƙunci to tayi ƙarya ,sai dai babu yadda ta iya haka ubangiji ya nufe ta da kasancewa,kuma bata isa ta hana a kwaikwayeta ba,sai dai tunawa tayi da cin mutuncin da ƴan uwanta na jini sukai mata a yanzu yanzu,yasa takaicin yaran raguwa a ranta domin tana ganin gara su yara ne masu hankali ma sunyi bare su,har ta iso bakin layin su inda zata iya samun abun hawa zuciyanta a cinkushe yake babu daɗi sam,bata wani jima a tsaye ba ta samu abin hawa tai gaba abinta.

 

___________

 

*GRA,Zaria.*

 

Babban gida ne wanda tun daga nesa me kallo zai san gidan na manya ne masu hannu da shuni,tsananin haɗuwan ginin da tsaruwansa zai sa me kallo yasan cewa ƙwararru a harkan ginin zamani ne suka zana asalin taswiran ginin,ginin upstairs ne da tsayawa misalta tsaruwansa ɓata lokaci ne,daga cikin ƙaton parking space na gidan motoci manya guda uku ne aje,za kai tafiya me nisa kafin ka isa asalin main entrance na shiga cikin gidan.

 

Daga ciki gidan babban falo ne a ƙasa,mai ɗauke da ɗakuna guda uku kowanne manne da toilet a ciki,an zuba kaya na alatu wanda ƙwararrun Interiors ne suka tsara komi bisa muhallin daya dace,yanayin yadda aka tsara falon da irin kujerun dake cikinsa da sauran kayan decor na ɗakin,zai tabbatarwa me kallo ba ƙananun kuɗi aka narkar ba, daga hannun hagu wanda nan ne aka aje 3 Seater,wani kyakykyawan magidanci ne ma’abocin kyawu da cikar haiba,Black Beauty ne wanda fatarsa ta rine da hutu da jin daɗin rayuwa,hakan ya haifar ma lafiyayyan fatansa da wani irin fresh,yana da dogon hanci zar tare da manyan dara-daran idanu,abinda ya ƙarawa kyawunsa armashi shine gashin giransa baƙi siɗik wanda suke a cinkushe,kame yake cikin kujeran ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya,a shekaru bazai gaza shekaru talatin da bakwai zuwa da takwas ba,daga saman cinyansa ƙaramar laptop ne yana faman latsawa,dukkanin nutsuwansa yana ga aikin da yake a cikin computern,sanye yake cikin wata Farar Jallabiya,wanda kana kallo zaka san manyan kuɗi aka aje kafin a ɗauke ta,dukkanin wajen ya cika da qamshin turaren RALPH LAUREN,takun takalman dana fara jiyowa daga ɓangaren matakalan benan dake kallo cikin falon yasani kai dubana wajen,idanuna suka fara hango min fuskan matar da ke sakkowa daga stairs ɗin sanye cikin kayan bacci riga da wando da suka fiddo suranta a fili,baƙace sai dai tana da matsakaicin kyawun fuska,don kai tsaye bazaka kirata kyakykyaba,haka kuma bata da muni akwai ta da cikar halitta me ɗaukan hankali,ko kaɗan bata da makusa,matashiyace da bazata gaxa shekaru ashirin da takwas ba a duniya,amma duk wanda yai mata kallo ɗaya zai iya bata shekaru ashirin da biyu sabida yanayin kula da gyara da jikin ke amsa a kowani lokaci,gaba ɗaya tunda ta doso tsakiyan falon qamshin turarukan da tai anfani dasu masu sanyi da daɗin qamshi suka cika wajen,abinda yasa magidancin tsayawa cak! daga latsa Cumputern da yake ya ɗago manyan idanunsa masu cike da kwarjini ya zube akanta,fuskansa babu yabo ba fallasa yai mata kallo biyu yana me ɗauke kai ya cigaba da aikinsa,ita kuma ta cigaba da takowa cikin takun da ke nuna yanga da kwarkwasa don janyo hankalin wanda akeyi dominsa,ko da ta iso inda yake kai tsaye ta zauna kusa dashi tamkar zata shige jikinsa,gaba ɗaya gangar jikinta ya gama mannuwa da tasa,ta miƙa hannu da nufin ɗauke Laptop ɗin dake bisa cinyansa,yayi saurin kai hannunsa yana dafe nata hannun, tare da ɗago ido ya zuba mata,fuskansa na tsukewa hakan yasa ta janye hannun nata,cikin muryanta me cike da iyayi ta fara faɗin “Haba A.Maleek magana fa mu ke daya kamata ace ka bani lokacinka ka saurareni,amma shine zaka sakko nan ka zo ka zauna kana faman sabgan gabanka,meyasa yanzu ni bani da ƙima da darajan da zaka xauna ka saurari matsololina? A gaskiya A.Maleek na fara gajiya da halin ko inkulan da kake nuna min.”

 

Tunda ta fara magana ya tsaida abinda yake ya zuba mata idanunsa dake rikitata,yana jifanta da wani irin kallo da ita kaɗai tasan ma’anansa,kafin amon muryansa ya fito cike da Isa da izza yake faɗin “Suhailah ni za ki zo ki tasa kina ɗagawa murya,si’anki ne ni ko ni ɗin ɗanki ne? karki bari ki fusata zuciyata a wannan karon har kija in ɗauki matakin da ba zai mana daɗi ba,ke kike ɗaukan maganan da kika zo dashi tana da muhimmanci,ni a wajena maganan banzace tunda bazaki bi abinda nake so ba,don haka ki barni inji da tarin matsololi da ciwan kan da kike bani,oya tashi ki bar nan wajen tun raina bai ɓaci ba,kuma wannan ya zama karo na ƙarshe da xaki sake zuwa min da raini makamancin wannan.”

 

Ya ƙare maganan yana nuna mata hanyan inda ta fito,idanunta ta sauke akansa kaman zatayi magana amma yanayin yadda ta ga ya haɗe fuska yana jifanta da kallon da ta fi tsana a wajensa, yasa ta juyawa da sassarfa ta nufi hanyan stairs ɗin,da bibbiyu take takawa har ta haye,ya bita da wani mugun kallo kafin yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa tare da ɗaukan laptop ɗinsa da wayansa ya rufa mata baya zuwa saman,ɗakinsa direct ya nufa yana aje Laptop ɗin da wayansa,ya fara cire jallabiyan jikinsa yai jifa dashi bisa Bed,ɗakin yabi da kallo zuciyansa na ɗaukan zafi,sam Suhailah bata damu da gyaran ɗakinsa ba,abinda kawai tasani ta ciyo wanka tazo ya biya mata buƙatanta su sha bidirinsu ta kakkaɓe jikinta tabar masa ɗakin,sai lokacin da ta busa iska sannan zatai gyaran ɗakin,idan kuma tayi sai ta ɗauki wani dogon lokacin kafin ta sake,sai dai shi idan yana gari ya dage yai gyaran ɗakin da kansa,don bai lamunci wani ƙato ko ƙatuwa su shigo masa ɗaki da sunan gyara ba,Bathroom ya nufa don yin wanka kaman yadda saba baya iya bacci idan baiyi wanka ba,lokacin da ya fito kintsa jikinsa yayi ya sanya wasu kayan bacci masu taushi ya zura slippers ya fito,kai tsaye kitchen ɗin dake nan upstairs ɗin ya nufa,don haɗo shayin da zai sha kafin ya kwanta,da kansa ya tafasa ruwan zafin ya zuba duk abubuwan da yake buƙata,cikin Mug ya juye bayan ya tafasa ya fito zuwa wajen dining ɗin da ke manne da corridor ɗin shiga Kitchen ɗin,Sugar ya ɗiba da slice bread guda biyu ya nufi ɗakinsa,bayan yayi ma ƙofan shiga ɗakin Suhailah kallo ɗaya ya ɗauke kansa,koda ya kammala shan shayin nasa bakinsa ya je ya wanko yazo ya kwanta,ba tare da yana jin cewa zai bi takan Suhailah wajen nemanta zuwa ɗakinsa kaman yadda yakanyi a wasu lokutan ba,don shi yana ɗaya daga cikin irin mazan da sam basa son raba shinfiɗa da matansu koda sun samu saɓani ne,sai dai yana ganin a yanzu lokaci yayi daya kamata ya fara biris da lamuranta ko zata saitu tasan abinda ya dace da ita,addu’an kwanciya bacci yayi ya shafa yana fata yau yayi bacci ba tare da yayi mafarkin da ya saba yi a ƴan kwanakin nan ba,mafarkin dake tsaya masa arai ya kuma rasa gane kan inda mafarkin ya dosa,lumshe idanunsa yayi bayan yaja blanket ya rufe jikinsa……..

 

Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

 

*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*

 

 

_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_

 

 

 

*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU*

 

*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*

 

*Recharge* – inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

 

*Balance* – Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

 

*Credit/Debit Card* – Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

 

A inda (Enter your amount) za’a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba “Proceed”. Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

 

——–

 

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

 

*Bank Transfer*

*Airtime Transfer*

 

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za’a gansa a Balance.

 

 

 

#Ɗansabo ce#

[23/07, 12:21 pm] +234 814 437 4241: *TAIMIYYAH*

 

©️Ayshat Ɗansabo Lemu

 

*Page 5*

 

_________

Ƙarfe goma da rabi na dare TAIMIYYAH ce ke zaune tana kallo a falon Iya,ita da Ladi me aiki ne da yake nan take kwana Ladin tana da ɗakinta daga waje,wayan TAIMIYYAH ne ya fara haske alamun kira na shigowa sabida ta sanya wayan a silent,ta kai hannu ta ɗauki wayan tana ganin sunan Yah Deeku ɓaro-ɓaro kaman yadda tai saving number ɗinsa,ƙaramin numfashi ta sauke kafin ta danna received takai kunni,zuciyanta na sauya bugu domin rabonta da shi tun ranan da yabar part ɗinsu a fusace,muryansa ta jiyo yana faɗin “Hello!” sai ta lumshe ido tana amsawa da faɗin “Hello! Yah Sadeeq ina yini.”

 

Memakon ya amsa sai kawai ya zarce da faɗin “Yanzu Zainab ban isa ki neme ni kiji lafiyata ba,ina kallo zaki buɗe status ɗina amma ban isa ko gaisuwa ya haɗamu ba,kina ganin hakan shi zaisa idan ma zan janye manufata ne in janye eyim?”

 

Ya dakata yana jiran yaji me zata faɗi,TAIMIYYAH da tai kasaƙe rike da waya a kunni sai ta sauke numfashi tana miƙewa tare da dafa ƙafanta ta fara takawa zuwa hanyan ɗakinta,cikin muryanta dai dake kashe gaɓɓan jikinsa take faɗin “Sorry Yah Deeku ba haka bane ina ta so in maka magana Allah ne bai nufa ba,ya kake ya Kaduna ya aiki kuma.”

 

“Duk basu na tambayeki ba malama,kuma bana son wannan sunan kin sani amma bazaki daina faɗi ba ko? Zan kamaki ne bari dai in shigo gobe,yanzu dai sanar dani me zaki dafa min kafin in shigo girkin ki kawai nake jin ci Baby kinji?”

 

Sadeeq ya ƙare magana cikin wani irin salo da shi kansa bai san yanawa TAIMIYYAH illa ba,zuwa lokacin tayi kwance a bed tana tada kai da pillow,hannunta ɗaya dafe da wayan a kunni,yanayin salon da yai maganan kawai ya bata tabbacin rigimansa da neman magana ne kawai ya tashi,inba haka ba ita ta mance rabon daya ƙirƙiri cewa sai girkinta zai ci,sanin idan ta bijire wani sabon rigiman ne yasa ta faɗin “Baka da Matsala Yayana,faɗi me kake son ci ka ga da yin safe sai aje cefanen abinda babu.”

 

Ya saki murmushi daga ɓangarensa,kafin ya gyara kwanciyansa yana jin tasirin muryanta da salon shagwaɓarta na kassara gaɓɓan jikinsa,tuni idanunsa ke hasko masa yadda take maganan ɗan ƙaramin bakinta na motsawa,ya lumshe idanunsa ya buɗe kafin ya furta “Bani da wani zaɓi ai kinsan duka irin abincin da nafi so,yanzu me kike yi yau ki ka kai har to 11pm baki bacci ba?”

 

Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,domin ya santa da baccin wuri wani lokacin tara ma ta daɗe da yin bacci,TAIMIYYAH ta sake yin ƙasa da murya tana faɗin “Kallo nake na wani film da ya ɗauke hankalina.”

 

“Hala film ɗin na soyayya ne ko?”

 

Ya sake jafe mata tambayan,TAIMIYYAH ta waro ido waje kaman tana gabansa,kafin ta wani kwaɓe face cikin shagwaɓe murya ta furta “Kai Yah Deeku ni dai bance ba kawai dai Film ɗin na da kyau ne,kasan Korean Films akwai ɗaukan hankali.”

 

“Shikenan Baby idan na zo kya bani labarin Film ɗin,wannan Old Woman ɗin ta jima da yin bacci kenan,ki gaisheta zuwa da safe kice wallahi idan na iso gobe rigima zamuyi sosai da ita,tunda yanzu ta daina ƙaunata so take ta zama ƴar ta’addan Soyayya.”

 

Cewan Yah Sadeeq da wani irin salon da yasa TAIMIYYAH fashewa da dariya,sai da tayi me isanta yana sauraranta da jin kaman ya rufe ido ya ganshi gabanta,kafin ta tsaida dariyan tana faɗin “Kai Yah Deeku Iyan ce tazama ƴar ta’adda daga faɗin gaskiya.”

 

Ta ƙare maganan da dariya a muryanta,hakan yasa Sadeeq taɓe baki kaman TAIMIYYAN na kallonsa,kafin ya furta “Okey gaskiya ma take faɗi lallai Baby,any way bye karki ɓata mood ɗina yanzu in kasa bacci.”

 

Bai jira cewan komi ba yai hanging up,TAIMIYYAH ta sauke wayan daga kunni tana me taɓe baki,ko kaɗan bata ji duk wani salonsa zata bari yai tasiri akanta,bare ta jefa kanta acikin masifan da bazata iya fita ba,don a ganinta yin soyayyah da shi babban masifa ne a gareta domin Umma ba zata taɓa bari ta sami nutsuwan zuciya ba,aje wayan tayi tana hamma alamun baccin yazo da gaske,sanin Ladi zata kashe kayan kallon idan taji bacci yasa TAIMIYYAH nufan toilet ta ɗauro alwalan kwanciya bacci,already tana sanye da kayan bacci shiyasa tana fitowa ta kashe fitilan ɗakin ta haye bed,bata ɗauki lokaci ba kuwa baccin yai gaba da ita.

 

_________

 

Ƙarfe goma na safe(10:00am) A.Maleek Ibrahim ya fito daga wanka,tunda ya sanyo kansa cikin Bedroom ɗin nasa qamshinta daya shaƙo ya sanar dashi wacece,hakan yasa ya ɗauke kai sam bai kalli inda take ba, ya taka zuwa gaban dogon mirrow ɗin ɗakin,yana cigaba da tsane ruwan jikinsa yana jin tasirin idanunta da ke biye dashi,amma sam yaƙi duban sashin da ta zauna daga bakin Bed ɗinsa idanunta akansa “Darling good morning.” Cewan Suhailah cikin narke murya,amma memakon ya amsa sai yai biris da ita yana cigaba da abinda yake,hakan yasa ta miƙewa ta isa garesa,ba tai magana sai ɗauke man da yake shafawa da tayi,ta lakuta kaɗan ta murza a tafukan hannunta,tana me kai hannu don fara shafa masa amma sai ya kama hannunta ya riƙe,manyan idanunsa masu cike da kwarjini ya zuba mata fuskansa a tsuke yake tsaf babu annuri,cikin muryan da idan yai mata magana dashi take sanin babu alamun wasa ya fara faɗin “Bana so Suhailah,sai yanzu ne kika san ki ɗakko ƙafa ki shigo ɗakina,meya hanaki zuwa ki kwana da mijinki a daren jiya?Bayan kinfi kowa sanin na tsani raba shinfiɗa,look! Suhailah wallahi kinji na rantse na fara kaiwa maƙura da halayyanki da sabbin banzayen ɗabi’un da kike shigowa dasu a zamantakewan auren mu,idan ma sabbin ƙawaye kikai da suke neman canzaki to kisani bazan ɗauka ba,don haka tun wuri ki dawo cikin hankalinki ina nan ban canxa ba daga Maleek ɗin da kika sani abaya ba,karki ga ina nuna miki so ki ɗauka na sauya ne ban sauya ba,kuma zan baki mamaki nan kusa.”

 

Ya ƙare maganan yana sakin hannuwanta,tare da raɓa ta ya wuce zuwa wajen kayansa da ya fiddo zai saka,Suhailah ta bishi da kallo kafin ta fara faɗin “Haba My A.Maleek duk me yayi zafi haka?Ni gaba ɗaya wannan dawowan naka na rasa me ke fusata zuciyanka akaina,ni wani sauyawa nayi don Allah? Gayu iya gayu ina maka ta ina na rage ka,gyaran ɗakinka da girki su kaɗai ne nasan matsalata,kuma nace maka zan samo masu aikin da zasu dinga yi kaine ka nuna baka so,ni kuma kasan na tsani aikin gyara da girki tun ina gida,kuma a hakan idan na samu time da kaina nake zagewa in gyara ko’ina a ɗakinnan,girki kuma kai da kanka ka yaba cewa Ameena ta iya girki,to me kake so kuma dani Maleek?”

 

Ta ƙare maganan tamkar zata fashe masa da kuka,tana tsananin son sa bata faye son ɓata ranshi ba,amma akan wannan matsalan sam bata ji zata iya biye masa ta koma yadda yake so ɗin,bata son girki a rayuwanta sam tafi gane a girka taci ta kwanta,bata son moriya da yawan aikace-aikace amma shi Maleek so yake ta zama ƴar bautansa,komi na hidimansa yace sai itace da kanta zatai masa komi,hatta girki yafi so idan yana nan tayi masa abinci da kanta,ita kuma hakan ne take ganin bazata iya ba,wani irin kallo ya juyo ya watsa mata kafin cikin kaushin murya ya fara faɗin “Okey! Kina iya bani waje tunda baki san me nake so da ke ba,amma ina so kisa a ranki duk randa kika ji nazo da maganan sake aure kiyi kuka da kanki ne,domin na fara ji ajikina dole zan sami wata abokiyan rayuwan da zata iya sadaukar da lokacinta domin yimin hidima,tare da bin dukkanin umurnina.”

 

Suhailah da maganansa ya mugun girgizata,game da zancen sake auren daya shigo dashi tayi saurin kallonsa a razane,za tai magana ya daka mata tsawa yana nuna mata hanyan fita,hakan yasa Suhailah fashewa da kuka tana ficewa daga ɗakin nasa,ya bita da tsaki yana cigaba da shirinsa,cikin mintuna biyar ya gama kintsa kansa cikin wani lallausan farin yadi,da yai masa mugun kyau links ɗin hannun rigan ya gama sawa,ya isa gaban madubi ya ɗauki turarensa na RALPH LAUREN yana fesawa gaba ɗakin ya sake rinewa da daddaɗan qamshinsa,wayoyinsa ya kwasa ya fito zuwa down stairs.

 

A ɓangaren Suhailah kuwa tana fitowa daga ɗakinsa,ta wuce ɗakinta tana ɗaukan waya ta kira Hajiyansa,kuka ta sanya mata tana sanar da ita cewa Maleek aure zai ƙara ya daina son ta da ƙaunarta,bata aje wayan ba sai da Hajiyan ta gama rarrashinta da bata tabbacin wasa A.Maleek yake kawai,sai dai sam ta kasa samun sukuni hakan yasa ta fito ta koma ɗakinsa, ganin baya nan yasa ta san ya sauka ƙasa kenan,sai kawai ta biyo bayansa zuwa falon ƙasa,direct ɓangaren dining ta nufa don tana da tabbacin wannan time ɗin yake zaman karya kumallo indai yana ƙasan ko yana gari,ilai kuwa can ta hangesa riƙe da cup ɗin Tea yana kurɓa,gabansa plate ne daya zuba chips,Suhailah ta ja kujeran dake kusa dashi ta zauna,tana sake duban yadda ya haɗe fuska kaman hadarin watan Augusta,cikin narke murya ta fara faɗin “My Maleek don girman Allah kayi haƙury,insha Allah zan gyara duka kuskurena,amma don Allah karka sake min irin wasan ɗazu wai zaka iya samo wata bayan ni,wallahi zuciyata zata iya tarwatsewa,kai min rai don Allah ka bar shigo da irin wannan wasan,in dai abinda kake son in dinga yima da kaina ne zan dingayi Allah kuwa zan daure kaji Baby.”

 

Ta ƙare maganan tana kwantar da kanta a kafaɗansa tare da kama hannunsa ta shiga murzawa,hakan yasa ya dubi cikin idanunta tare da watsa mata harara,kafin ya sake kurɓan Tea ɗinsa ya aje cup ɗin yana faɗin “Ni ɗin ne nake wasa Suhailah?Wato a wasa kika ɗauki maganan ko Hmm! To maganan Planing ɗin da baki fasa ba kuma fa? Ko kina ɗaukata a sakarai ne bansan duk wani motsinki ba,to ki sani ni bazan iya cigaba da zama da macen da bata shirya haɗa zuri’a dani ba,in karatune ina sha kin ƙare har bautan ƙasan duk kin gama,to ina so kisa a ranki nan da wani lokaci kaɗan komai zai iya faruwa,abinda kike ɗauka wasa zai matuƙar baki mamaki.”

 

 

Kafin Suhailah ta sami ƙwarin guiwan yin magana,wayan A.Maleek ɗin ya fara kiɗa alamun shigowan kira,daga yana yin ringing ɗin yasan Hajiyansa ce,don haka yayi hanzarin ɗauka yana fara gaida ta,memakon ta amsa sai kawai ta shiga tuhumansa akan cewa me zaisa ya fara ɗagawa Suhailan hankali da zancen cewa zai sake aure,ta rufesa da faɗa ba tare da ta bashi daman kare kansa ba,daga ƙarshe ta kashe wayanta ta bar Maleek da bin wayan da kallo,kafin ya maida dubansa kan Suhailah ta dai tsumu alamun rashin gaskiya,ya aika mata da mugun kallo yana faɗin “Bar kallona kinyi da ido kaman Munafuka,zan baki mamaki wallahi domin sai na sanarwa Hajiyan abinda kike aikatawa wanda sai tayi fishi da ke,xanga ƙarshen ji dake da take yi alhali ke ko haɗa jini da ita baki shirya yi ba,sai gayu da ƙaryan kina son ɗanta da kishinsa,haka ake son Suhailah?”

 

Suhailah dai tai ƙus zuciyanta na faman bugawa,idan akwai abinda baza ta so ba shine MALEEK ya tona mata asiri a wajen Hajiyansa ta gane cewa,itace ke anfani da maganin hana ɗaukan ciki,tasani Hajiya tafi kowa tsanan tsarin Iyali,kuma a ƙagauce take da ta samu jika daga gare su,ganin yana shirin miƙewa ya bar wajen don tuni ya kammala cin abincinsa,hakan yasa ta tashi ta ruƙunƙumeshi tana magiyan kada ya faɗiwa Hajiya,ita wallahi ta daɗe da daina anfani da komi na hana ɗaukan ciki,lokaci ne kawai baiyi ba,sam Maleek fuskansa babu sassauci ya zare ta daga jikinsa yana takawa ya bar mata wajen,wayoyinsa kawai ya kwasa a falo da mukullin mota yai waje don barin mata gidan ma baki ɗaya,zuciyansa na tunzurasa akan yaje ya fayyace wa Hajiyan irin rayuwan da yake yi da Suhailah,ko Hajiyan zata daina goyan bayanta da ɗaure mata gindi,hakan yasa ko da ya tada mota ya baro gidan kai tsaye hanyan da zai Kaishi Gonan Ganye ya nufa,inda a nan ne ya tanfatsawa Hajiyan nata ginin………

 

 

 

 

 

#Ɗansabo ce#ce#



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Taimiyyah Hausa Novel]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.