Taj Mahal Hausa Novel Complete
Gudu take na fitar hayyaci tana k’wala masa kira da iya k’arfin ta bata da burin da ya wuce ta cimmasa tana zuwa gaff dashi wata gagarumar iska me had’i da guguwa ta fara kad’awa.
Hakan yasa yayi taga-taga k’afar sa ta zame yayi baya ya fad’a k’asa.
Cikin ihu ta furta sunan sa tana k’ara waro gwara gwaran idanun ta, cikin sanyin jiki da wani irin taku ta k’arasa wajen tana lek’awa, ganin da gaske ya fad’a d’in yasa ta dafe k’irjin ta tana wata irin shak’uwa idanun ta suka k’ara firfitowa ko k’yaftawa basayi,, zubewa tayi a wajen kamar sumammiya ta durk’ushe akan k’afafunta.
Wani mutum ne ya zagayo ta bayan ta ya kama damtsen Hannun ta ya fara janta k’irrrr kamar ba mutum.
Babbar Harabar TAJMAHAL PHURLA.
Cike take da mutane iri daban daban bayi da hadimai haka ma dogarai mawak’a da masu bushe bushe.
Ko ina kid’a ne ke tashi da wata irin busa me d’auke da wani take da wani kyakkyawan salo da k’warewa.
Rukunin y’an mata sun sha ankon riga da wando burguza burguza sunyi k’awanya a tsakiya suna rawa da karairaya cike da k’warewa da kuma sabo.
Gefe guda kuwa sai watsi ake da furanni da garin fure da kuma kaloli.
Da alama ana gudanar da wani babban shagali ne a wannan masarauta.
A cikin Mahaal a hawa na bakwai.
Wani k’ayataccen d’aki ne wanda yaji ado irin na sarauta ta ko ina, acan ciki,
Zaune take bisa wani katafaren lilo yana lila ta cike da isa gami da izza ba’a iya ganin fuskar ta sakamakon juya baya da tayi.
Gefen ta kuwa wata kyakkyawar Hadima ce tsaye kanta a k’asa tana wasa da yatsun Hannun ta, cikin sanyi da kuma zak’in murya tace, “Hazoor Ki yafe ni, amma masarauta ta cika ta ko ina ke kawai ake jira”
Ba ta ce komai ba sai mik’ewa da tayi cikin wani irin salon mulki da gadara.
A take fitinanniyar surar ta ta bayyana kanta. Budurwa ce me ji da lokacin ta,
Kyakkyawa ce ta azo a gani jajur da ita kamar ka ta’ba jini ya fito jikin ta ko ina kayan ado ne na gwal da azurfa sark’ok’i duk wani sassan jikin ta babu inda babu su hakan yasa duk wani motsin ta sai kaji k’arar su bare kuma idan ta taka, ta had’e cikin wani Saarie ruwan ganye, kore, yayi matuk’ar kwanciya a jikin ta tayi kyau kamar ba gobe kasancewar ita d’in kyakkyawa ce, babu wata kwalliya a fuskar ta sai kwalli da yaji bajau a idanun ta hakan ya k’ara musu kwarjini da wata irin barazana.
Wannan hadimar ta kalla, take ta sako wani shu’umin murmushi ta kauda kai cike da izza, a hankali ta lumshe idanun ta tareda motsa bakin ta alamun magana, cikin dadd’ar muryar ta ta furta Arjulaa???
Wata tsuntsuwa fara tass ce ta nufo inda take suuuu,, itama kanta tsuntsuwar kyakkyawar gaske tana zuwa ta sauka akan kafad’ar ta tana wani kuka tareda karkad’a jela, hakan yasa ta saki murmushi.
Kamar me tsoron k’asa ta fara takawa a hankali idan tayi taku d’aya sai ta girgije sannan zata k’ara d’aya a haka tayi gaba, Hadimar tabi bayan ta kanta a k’asa.
Hannun tasa ta janye tufafin jikin ta ta d’anyi sama dashi sakamakon jan k’asa da yake sannan ta sako k’afar ta a wajen d’akin.
Tin daga k’ofar d’akin sojojin masarauta ne rerass baka iya gano iyakar su, suna ganin ta na farko yayi wata irin busa, daga can ma wani ya k’arayi haka abun ya d’auka har ya fito harabar masarauta wane gayawa wane, ai kuwa take Salo ya k’ara canjawa yanayin kid’i da busar da akeyi ya canja zuwa wani salo me bala’in d’aukar hankali.
Da takunta irin na wahainiya har ta fito harabar duk inda ta ratsa zubewa suke kan guiwoyin su tareda sunkuyar da kansu k’asa su k’ame kamar abu mara numfashi har sai ta wuce tabar wannan sashin sannan zasu mik’e, mata da maza manya da yara haka sukeyi.
daga can wani d’an bene aka tanadin gurin zaman ta ita da na kusa da ita, kai tsaye can ta nufa kafin ta zauna ta d’aga musu hannu a take gurin yayi tsittt kamar ba sune suke hayaniya ba.
Sihirtaccen murmushin ta ta sakar musu.
Hakan yasa kowa da yake gurin murmusawa sannan suka dunk’ule hannayen su na dama suka d’ora kan k’irjin su gami da d’an rank’wafawa, kansu a k’asa.
Jinjina kai tayi taja wani yalwataccen numfashi.
Wanda yake da alhakin sanar da umarnin ta yayi busa hakan yasa kowa ya d’ago, masu kid’e-kid’e suka fara kid’a da busa me sautin taken ta.
Zama tayi ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya, tana kallon ko ina da fararen idanun ta,, bayan wani lokaci ta tuna da Hadimar ta da take a tsaye kallon ta tayi fuska a sake tace, ” Farhanaa zauna”
Wadda aka kira farhanaa ta sadda kai k’asa cike da ladabi tace, “ina godiya Hazoor”
Bata sake kallon inda take ba taci gaba da kallon mutanen ta, wato mutanen masarautar Phurlaasirie.
Bayan an d’auki lokaci ana wannan sai aka tsagaita.
Yayin da idon kowa kuma ya dawo kanta.
Wata kuyanga ce ta turo wani abun saka jarirai na gargajiya wanda yasha ado ganyayyaki kala kala jaririn sai baza ido yake yana kallon kowa, a gaban ta aka ajiye shi kuyangar tayi gefe tana me sunkuyar da kanta k’asa.
Wasu mace da namiji ne suka k’araso duk kansu yana k’asa suka kwashi gaisuwa ta musamman sannan sukayi gefe suka tsaya, cike da ladabi namijin yace, “ranki ya dad’e wannan d’an mu ne nida matata wanda a dalilin haihuwar sa ne kika shirya mana wannan gagarumin shagalin, mun gode da wannan karramar Hazoor, wannan d’a mun sadaukar dashi gare ki duk abunda kika yanke a kansa mun amince ba dan kanmu muka haifeshi ba sai dan ke mun mallaka miki shi ranki ya dad’e.
Kyakkyawan murmushi tayi tareda mik’ewa tayi tsaye akan jaririn,, ido ta zuba masa shima ya zuba mata ido suna kallon-kallo har wani lokaci kafin tasa hannu cikin nutsuwa ta d’auke shi ta rungume, kallon iyayen sa tayi cikin k’asaitacciyar muryar ta tace, ” menene Lak’abin sa???
Uwar yaron tace, “ranki ya dad’e yanzu ba namu bane naki ne duk hukuncin da kika zartar akan sa ya zama dai-dai ko da kuwa yanka shi zakiyi ki sadaukar da jinin sa ga abun bauta”
Baban yaron yace, “ranki ya dad’e mu mun kasance bayi ne a wannan masarauta tin iyaye da kakannin mu kuma har yau bazamu gajiya da hidimta muku ba bakin rai bakin fama nayi alk’awari ga abun bauta zan mutu ina me bautawa wannan masarauta”
Murmushi tayi ta d’an yi taku biyu kafin ta juyo, girgiza kai tayi tace, “na k’aunaci yaron nan dan kuwa yana da k’warin zuciya tamkar mahaifin sa bazan bawa kowa shi ba shi d’in mallaki na ne kamar yadda kuka mallaka min shi dan haka zan rad’a masa suna yanzu.
Share hawaye mahaifiyar yaron tayi har cikin ranta tana jin kewar d’an ta wanda ba lallai ta sake ganin sa ba.
Ita kuwa lumshe ido tayi tana motsa baki da alama addu’a takeyi bayan ta kammala ta hura masa iskar bakin ta a kunne,, hakan yasa yaron ya k’ara zazzaro ido tareda k’ank’ame jikin sa, bud’e idon ta tayi ta zubawa yaron su, tana murmushi tace, ” AbdulKareem”
Da sauri baban yaron ya d’ago kai yana wani irin murmushi tareda k’walla jikin sa har rawa yake ya mai-mai-ta AbdulKareem??
Zubewa yayi kan guiwoyin sa yana kuka yana cewa, “mata ta na gode miki da kika haifa min AbdulKareem, Ranki ya dad’e kin biyani ubangijin AbdulKareem ya saka miki da mafificin Alkairi.
Uwar d’an kuwa jin sunan da d’an ta yaci yasa ta dena sharar k’wallar bak’in cikin rabuwa da shi , farin ciki ya wanzu a tattare da ita itama ta zube a k’asa tana mik’a godiyar ta.
Fure ta dank’a ta watsa musu tana murmushi tace, ” ina muku fatan samun wani d’an bayan wannan kunyi babbar sadaukarwa bayan tarin shekarun da kuka samu ba tareda kun samu d’a ba kuma kun haifa kuka sadaukar dashi gare ni tabbas kun cancanta da komai a gareni Udday”
Mik’ewa Udday yayi cikin d’aga murya yace, “ku saurara kowa ya maida hankali,,, ni Udday d’aya daga cikin bayi kuma y’an bayi na wannan masarauta na sadaukar da d’a na da na haifa ga Uwar wannan masarauta, Uwa me adalci ta sanyawa yaro suna AbdulKareem!!!!!!!!!!!
Sai da wajen ya girgiza gaba d’aya saboda fad’ar wannan suna take wasu suka fara zubda hawaye wasu kuwa razani da firgici gami da rud’ani ya d’arsu a zukatan su, wasu kuwa jikin su har kakkarwa.
Wani tank’amemen faranti wanda aka lullu’be da wani k’yalle me ado da Hatimin Phurlaa Mahaal ta kar’ba a hannun wata baiwa tana murmushi ta mik’owa Udday sannan ta kar’bi d’ayan ta bawa matar sa.
Farin ciki da murna ba kama hannun yaro,,, ba su kad’ai sukaji dad’in wannan kyauta ba har da sauran jama’ar wajen,, take aka k’ara rud’ewa da fad’in, ” Godiya ta musamman da jinjinar ban girma ga Uwar Masarauta”
Shagali akeyi sosai ko gajiya basayi.
Mik’ewa tayi da zummar komawa tana rungume da AbdulKareem, ta fara tafiya kenan wata murya ta dakatar da ita, cikin d’aga murya ba tareda tausasawa ba ya kira sunan ta.
“Mahalakhshmie???????
Juyowa tayi tana waro masa idanu cikin wani mugun zafin nama ta d’auke shi da wani gigitaccen mari, cikin tsawa da kuma kwarjini tace,
” MAHARANIE MAHALAKHSHMIE ”
sassauta murya tayi tak’ara cewa, “ka sai ta harshen ka ba’a kiran sunan Uwa haka kawai”
K’asa yayi da kansa zuciyar sa na rad’ad’i kafin yayi wani yunk’uri yaji an sark’e k’afafunsa da wasu mazajen sark’ok’i ido ya zazzaro yana kallon mahaifiyar sa wadda itama idanun ta suke warwaje.
Da sauri dattijuwar matar ta k’araso ta durk’ushe a gaban ta cikin k’ask’antar da kai tace, “kiyi hak’uri ki yafi d’a na k’uruciya tana damun sa shiyasa kiyi hak’uri Mhaa”
Da hannu tayi musu alamar su sake shi.
suka kwance shi suka ja baya.
Nuna shi tayi da yatsa tace, “RamRaj shine kawai sunan ka rik’e matsayin ka”
K’ara yin k’asa da kai yayi tareda cewa “zan kiyaye”
(Kuci gaba da bibiya ta a cikin wannan k’ayataccen labari domin jin ya abun ze kasance. Wacece
Maharanie mahalakshmie?? Shi kuma RamRaj waye shi?? Meyesa baya girmama sunan ta kamar kowa?? Shin meye yasa ta kasance uwar masarauta duk da kasancewar ta k’aramar yarinya budurwa?? Wannan sunan da ta rad’awa yaron Udday sunan waye?? Meyesa wasu suke farin ciki dashi wasu kuma suka razana?? Waye shi in ya girma??? Duk amsoshin suna cikin gundarin labarin sannu sannu bata hana zuwa,ku biyo ni domin jin yadda zata kasance..)
Taku.
INDO Ce
Leave a Comment