Hausa Novels

Tambadaddiya Hausa Novels

*TAMBAƊAƊƊIYA*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*’Yar mutan zazzau Naanarh M Sha’aban*

 

 

TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!

 

*Mata iyayen nagarta*

 

 

 

*1-2*

 

Gudu take kamar zata tashi sama ba ta da wani buri irin ta ga ta isa gidan Mai gari domin ta sanar dashi abin da ta gani gaba d’aya a firgice take jikinta sai rawa ya ke yi tana isa gidan Mai gari ta fad’a gidan ko sallama ba ta yi ba, ta zube a tsakar gida tana kwad’a masa kira tana sauke wani irin numfashi sama-sama “Baba mai gari! Baba mai gari!! Baba mai gari!!!” Fitowa Inna tayi wacce ita ce matar Mai garin tana yi mata wani irin kallo na wulak’anci tare da cewa “Wai ke tambad’addiya kina da hankali kuwa duk kin ishi mutane da ihu kamar wata mahaukaciya”, Yarinyar ta kalleta tare da murgud’a mata baki tana cewa “to ke meye ruwanki da ni, kuma ai ke ce babbar mahaukaciyar, ina Baba Mai gari gurinsa na zo dan kuwa garin nan yana dab da kamawa da wuta” Kallonta Inna tayi cike da rashin fahimtar zancen nata ta ce “Kamawa da wuta kuma? Me zai saka garin ya kamata da wuta Dije?” Dije ta ce “Babban zunubi aka aikata yau kuma har yanzu suna chan suna ci gaba da aikatawa” Inna za ta yi magana sai ga Mai gari ya fito daga d’akinsa, da sauri Dije ta mik’e tsaya jikinta na cigaba da rawa “Baba mai gari ka gaggauta kasa su dogari su je bayan gari domin kuwa garin nan yana daf da kamawa da wuta” Mai gari a rikice ya ce “meya faru Dije?” Dije ta sauke wata muguwar ajiyar zuciya tare da cewa “Larai ‘yar gidan Malam Ado mai sanaye da d’an ladi d’an gidan sarkin fawa ne na zo hucewa na gansu a bayan gari yana saka hannunsa cikin rigarta kuma mazugin rigarta a bud’e yake ana ganin bayanta”, hankalin Mai gari yayi matuk’ar tashi “Yanzu a garin nawa ake yin irin wad’annan mugayen sab’on to wallahi ba zai yi yu ba dole na d’auki kwakkwarar mataki Kuma dole na hukunta su” Ya na gama fad’ar haka ya fita waje a fusace har yana yin tuntube, Inna ta kalli Dije ta ja wani mugun tsaki ta ce ” Ke dai wallahi Dije kin cika tambad’add’iya meye ruwanki da su, saboda tsabar munafurci” Harararta Dije tayi ta ce “Ke Inna wallahi ki kiyayeni ai Baba mai gari ne ya ce duk abun da na gani anyi a garin nan in dai na sab’o ne na zo na fad’a masa, kuma da kike cewa ina ruwana dasu ai in da wannan jakar ‘yar ta ki Indo ce aka kamata tana yin wannan sab’on ai ke za ki san da ruwanki, kuma wallahi ni ba munafuka ba ce ke ce babbar munafuka shashasha dabba kawai” Tana gama fad’ar haka ta d’auki wani farantin roba ta makawa Inna a fuska ta fita tana zage-zage.

******

Larai kuwa tunda ta ga Dije ta gansu kuma ta saka gudu ta dora hannunta a kai tana cewa “Na shiga uku shikenan wannan tambad’add’iyar ta ganmu za ta je tayi ta tambad’amu a gari” Tayi maganar cikin muryar kuka, d’an ladi ya kalleta ko kad’an shi bai dameshi ba dan Dije ta gansu daman ai shi ya saba ba wannan ne farau ba kowa a k’auyen ya san irin muguyen halin d’an ladi “Wai ke dan waccen yarinyar ta ganmu shine zaki hanani jin dad’i to menene dan ta ganmu ta je tai-ta fad’a mana ke fa ki ka ce kin d’aukeni tamkar mijinki to menene dan mata tana biyawa mijinta buk’atarsa wata ta zo hucewa ta gansu” Ya k’arasa maganar yana kok’arin jawota, da sauri ta ja da baya tana girgiza masa kai tana cewa “kasani cewa ni ba matarka ba ce dan ba’a d’aura mana aure ba, kuma indai Dije ta je ta fad’awa Mai gari to kashina ya bushe na san Innata kasheni za ta yi baffana kuwa ban san wane irin hukunci zai d’auka ba dan kuwa ya tsani zina idan kai ka na tunanin wannan ba abun damuwa ba ne to ni abun tashin hankali ne ba ma damuwa ba” Wani irin murmushin mugunta d’an ladi yayi duk da cewa yau bai samu abun da ya ke so daga gurin Larai ba hakan ba zai saka ya k’i yi mata rashin mutunci ba “To sai me dan wannan tsohuwar uwar ta ki zata kasheki dan ta ji abin da ki ke yi ai ita ma kullum sai sun yi da Mahaifin na ki me sanaye kuma ta haka suka same ki, kuma da ki ke wani ja da baya menene a jikinki Wanda ban san shi ba” Larai ranta ya b’aci sosai “ni ka ke fad’awa haka” Tayi maganar cike da d’acin rai, “Eh d’in na fad’a miki me za ki iya ko zaki iya dawo da abin da kika rasa ne wato budurcinki” Jikin Larai na rawa ta saka gudu Dan Kuma tayi Alk’awarin wallahi sai ta wulak’anta d’an Ladi kuma zata San yadda za ta yi ta kare mutuncinta gidan Mai gari ta nufa tana zuwa ta tarar dashi a zaune ya kirawo mahaifinta da Mahaifiyarta ga dogari da sauran dattijan k’auyen zubewa tayi a tsakiyar fada tana kuka tana cewa “ranka ya dad’e ka taimaka min na shiga uku d’an Ladi ya raba ni da budurcina Innata ta aikeni bayan gari nayi Mata itace shine” Sai ta fashe da wani matsanancin kuka, Inna Talatu wacce ita ce mahaifiyar D’an Ladi ta matso kusa da Larai ta Rumgumeta tana cewa “Ranka ya dad’e Daman nasan yarinyata ba za ta iya aikata abin da ake tuhumarta dashi ba, Kuma kaf garin nan babu Wanda bai san d’an Ladi busuru ba ne Dan haka Dan Allah ka taimaka ka hukuntashi a kan abin da yayi wa yarinyata Dan ya gama cutarta” Tayi k’arasa maganar tana kuka mai tsima zuciya.

*******

Zama Mai gari ya gyara sannan ya fara magana “Tabbas d’an Ladi ya addabi mutanan k’auyan nan ba ga Matan aure ba da yammata Kuma hatta yara ma bai kyalesu ba, kuma dole ne nayi masa hukunci a kan abin da yayi wa Larai kamar yadda addini ya ce duk Wanda yayi wa wani fyad’e to za’a yi hukuncin zaman yari na har abada to Amman wannan hukuncin d’an Ladi ya banbanta da sauran domin d’an Ladi har kashe mutune ya ke yi dan haka za’ayi masa hukuncin kisa ta hanyar jifa, Larai ta d’ago da sauri ta ce “Dan Allah ranka ya dad’e ka taimaka min ya lalata min rayuwata, yanzu babu mai aurena Kuma ya ce Indai na fad’a kashe ni zai yi ayi masa hukuncin tun yau” Inna Talatu ta ce “Kiyi hak’uri yarinyata ba zai yi miki komai ba Kuma za’a bi miki hakk’inki kin ji ki yi shuru ki daina kuka” Larai ta k’ank’ame Mahaifiyarta tana jin sanyi a zuciyarta, haka Mai gari ya ba wa Malam Lawal mahaifin Larai hak’uri tare da yi Masa Alk’awarin gobe za’a jefe D’an Ladi, suka tashi suka tafi gida Mai gari Kuma ya ba da umarnin aje a nemo masa d’an Ladi duk inda yake, shi kuwa d’an Ladi Larai na tafiya ya zauna a k’ark’ashin wata bishiya har bacci ya fara kamashi sai ga abokinsa Kalamu ya nufoshi a guje Yana zuwa kusa dashi ya shiga kwad’a masa kira ” ‘Dan Ladi ka yi gaggawar tashi ka bar k’auyen nan idan ba haka ba daga yau kwananka ya k’are dan kuwa gobe jefe ka za’ayi” Dan Ladi ya bud’e idonsa daga kwance Yana yi wa Kalamu kallon mara hankali ya ce “A kan me za’a jefeni kamar wani dabba, Dan Allah idan maular da ka saba zuwa ka yi min ne ka tafi dan yau ban da kud’i” Kamalu ya ce “ni babu wata maula da na zo yi taimakonka na zo yi, Amman tun da ba ka buk’ata ka ga tafiyata d’an Ladi Allah ya jik’anka ya gafarta maka Annabi ya san da zuwanka” ‘Dan Ladi ya kallesa sororo cike mamaki har Kamalu yayi nisa d’an Ladi ya kwad’a masa kira ya dawo ya tsaya a gabansa “ga ni” Kamalu ya fad’a yana kallon d’an Ladi “meyasa ka ke ce min Allah ya jik’ai na mutuwa a ka ce maka zan yi”,”Eh Dan gobe zaka mutu indai ba ka gudu daga k’auyen nan ba” Nan d’an Ladi ya kwashe duk abubuwan da ya faru a fadar Mai gari ya fad’a Masa, d’an Ladi yayi matuk’ar razana “dole na gudu daga k’auyen nan yanzu ma kuwa, Kamalu Allah ya sadamu da alkhairinsa” Yana gama fad’ar haka ya saka gudu ya nufi wani daji, Kamalu Yana ta kiransa Amman Ina d’an Ladi ko waiwayensa bai yi ba, nan Kamalu ya saka dariya “Shege d’an iskan banza kawai” Nan ya juya ya koma cikin k’auyen.

*******

A ‘bangaren Dije kuwa tana fita daga gidan Baba Mai gari, gidansu ta nufa inda kafin ta k’arasa gida ta had’u da k’awarta Lami suna dambe da wata ‘yar makobtansu Zuwaira, nan Dije ta shigarwa Lami fad’an suka had’u su biyu su ka yi wa Zuwaira dukan tsiya har sai da suka fasa mara baki, sannan suka barta kowaccensu ta huce gidansu, Zuwaira ta mik’e ta nufi gida tana kuka kamar ranta zai fita, ita kuwa Dije tana shiga gidan ta ce ” ‘Yan gidan nan gafaranku dai” Mussadam wanda yake zaune a baki kofar d’akinsa yana wanke takalminsa ya d’ago tare da yi mata wani irin kallo da sai da hantar cikin Dije ta kad’a domin tana matuk’ar jin tsoron Mussadam koda tana yin rashin mutuncinta ta ji ance za’a fad’awa Yaya Mussadam daina wa takeyi domin ta san indai aka fad’a masa to dukanta zai yi kamar jaka “Keee! Dan ubanki haka ake sallama, zaki koma kiyi sallama ko sai na zabga miki mari” Dakewa Dije tayi tare da murgud’a masa baki “Ba za’a koma ba d’in” Mik’ewa Mussadam ya yi da niyyar ya mata dukan tsiya, amman kafin ya mik’e Dije ta shige cikin gidan da gudu tana ihu “Wayyo Inna ki fito zai kasheni” Inna tayi saurin fitowa daga d’akinta Dije ta b’uya a bayanta, kallon Mussadam Inna tayi tare da cewa “meya faru Mussadam?” Mussadam cikin muryar fushi ya ce “Wannan shegiyar yarinyar Tambad’add’iya kawai ta shigo gida babu sallama nayi mata magana shine takeyi min rashin kunya” Inna ta ja tsaki tare da cewa “A kan wannan d’an abun shine ka biyota zaka duketa, kai wai meyasa baka kishin ‘yar uwarka kullum cikin dukanta ka ke sai ka ce ‘Ya’Ya kishiya, Dije fa k’anwarka ce uwa d’aya uba d’aya amman ka ke yi mata wannan uk’ubar kamar wata ‘yar kishiyar uwarka” Inna ta k’arasa maganar cikin hargagi da masifa, “Assalamu alaikum Dije ke Dije kina ina dan uwarki ki fito nan” Gaba d’aya suka mayar da hankalinsu gurin mai shigowar Inna Ladidi ce fuskar nan ta ta a d’aure Zuwaira tana biye da ita a baya tana kuka, Inna ta ce “Ladidi lafiya kika shigo min gida kina zagar min yarinya saboda baki san ciwon haihuwa ba” Inna tayi maganar cikin fushi, Inna Ladidi ta ce “Ai shiyasa na ga ke kin san ciwon haihuwa tunda har kika haifo wannan tambad’add’iyar yarinyar wacce da haihuwarta gwara ‘barinta” Dije cikin tsiwa ta ce “Kee! Inna Ladidi wallahi ki kiyayeni wallahi idan ba haka ba zan koya miki hankali, kuma naji ni tambad’add’iya ce ke kuma shashasha ce wacce bata san abin da takeyi ba, kuma idan kun isa ku cigaba da tsayuwa anan ke da ‘yar ta ki sai na koya muku darasi” Duk tana bayan Inna takeyi wad’annan maganganun dan idan ta fito Mussadam zai calikata

 

Mussadam cikin fushi ya nufi inda Dijan take tare da fisgota ya zabga mata mari har sau uku ya ce “To shaid’aniya mara kunya yau zan koya miki hankali wannan tambad’ar da ki ke yi yau zan kawo k’arshenta” Yana magana yana dukanta kamar ya samu jaka ita kuma Dije sai ihu take tare da kiran sunan Inna,Inna cikin zafin nama ta d’aga hannunta tare da kifa masa mari, da sauri Mussaddam ya cika Dije yana kallon Inna fuskarsa tana nuna alamun tsantsar mamakin da yake, dan tunda suke bata tab’a yin yunk’urin dukansa ba, amman yau gashi ita ce ta d’aga hannunta ta mareshi “Inna” Ya kira sunanta yana zubar da hawayen bak’in ciki, takalmansa ya saka ya fita waje a fusace zuciyarsa kamar zata fashe, Inna Ladidi da Zuwaira da suka ga Musaddam ya fita su ma suka fita daga gidan domin kuwa sun san idan suka tsaya to Dije da Inna zasuyi musu rashin mutuncin da suka ga dama, Inna ta kalli Dije wacce ta turo baki tana wata girgiza, wani k’ayatatcen murmushi tayi mata,amman zuciyarta kwata-kwata babu dad’i saboda yadda ta ga Musaddam “Dijena meyasa zaki dinga biyewa wannan k’awar taki kuna tsokanan mutane” Dije ta kalli Inna tana wani yatsine ta ce “Nifa ba tsokanarta muka yi ba, fad’a suke da Asabe ni kuma na shigar mata” Inna ta ce “Ni Bilki na shiga uku, wato har fad’a ki ke shigarwa mutane, meye ruwanki dasu”,” To ba k’awata bace ai dole na shigar mata” Dija tayi maganar turo baki had’e da harara “Au ni ki ke harara? Saboda na………”Ni fa Inna ba harararki nakeyi ba, kawai idona ne a haka” Tayi maganar tare da shigewa d’akinta, ita ma Innar cigaba da yin aikinta tayi.

 

*KANO🙌🏽*

 

Wani had’add’en saurayi ne ya fito daga cikin supermarket rik’e da leda a hannunsa, da alama siyayya ya yi, yana takunsa d’ay-d’ay, kallo d’aya za ka yi masa kasan hutu da jin dad’i sun zauna a jikinsa, fari ne sosai dogon hancinsa ya yi matuk’ar dacewa da d’an k’aramin bakinsa, sajan kan fuskarsa ya kwanta luff a fuskar ta sa sai shek’i yake, idanuwansa manya ne wad’anda suke d’auke da zara-zaran gashin ido, Yana da sumarka da yawa, wanda ya gyarata ta kwanta a kan nasa kuma ta k’ara masa kyau, Shadda ce a jikinsa tsadaddiya white colour, yana isa wajen da aka tanada don yin parking, drivernsa Ado wanda yake jikin wata mota mai numfashi, ni kai na dijartyy sai da na numfasa da na ga wannan motar had’uwa iya had’uwa ta riga da tayi sai dai muce ma sha Allah, “Sannu da fitowa ranka ya dad’e” Ko kallon inda Ado driver yake bai yi ba, barantana yasa ran zai amsa masa,bud’e masa bayan motar Ado ya yi sai da ya d’auki kusan mintina biyu zuwa uku sannan ya shiga motar cikin izza, Ado ya rufe motar tare da zagayawa mazaunin driver ya shiga ya ja motar cikin nutsuwa suka fita daga supermarket d’in, sunyi nisa sosai suna tafi dan har sun kusan zuwa gida sai jin muryar wannan mutum Ado ya yi ya ce “Gidan Hajiya za mu je” Cikin izza ya yi maganar Ado ya ce “To ranka ya dad’e an gama” Anan Ado ya juyar da kan motar ta sa suka nufi gidan Hajiya, suna isa gidan mai gadi ya wangale musu babban gate d’in gidan, Ado ya danna hancin motar cikin gidan, tabbas gidan ya tsaru sosai kuma an zubda naira wajen gina shi, tsayawa nayi muku bayanin irin had’uwar gidan zai d’aukenj dogon lokaci kafin nayi,ya yi parking ya fito daga cikin motar da sauri tare da bud’e kofar bayan, a hankali ya zuro k’afafuwansa fara sal, sannan daga bisani ya fito gaba d’ayansa daga cikin motar, taku uku ya yi sannan ya juyo yana kallon Ado “Ka jirani yanzu zan fito” Bai jira abin da Adon zai ce ba ya nufi cikin gidan, wata babbar kofar glass ya tura ya shiga bakinsa d’auke da sallama “Assalamu alaikum” Hajiya wacce take zaune a kan dadduma ta idar sallah la’asar kenan, ta zauna tana jan carbi “Wa’alaikumussallam Abdulhamid” Ta amsa masa sallamar tana murmushi, shima murmushin ya sakar mata tare da k’arasawa gurun da take ya tsugunna har k’asa yana gaisheta “Ina yini Hajiyata” Hajiya ta yi murmushi tare da cewa “Lafiya k’alau alhamdullahi Ina Abban na ka da Mommynka”,”Suna lafiya” Anan dai ya zauna suka d’anyi hirarsu irin ta jika da Kaka kusan mintina hamsin sannan ya yi mata sallama ya fito, Ado driver yana nan a gurin da ya barshi a tsaye,ya bud’e masa murfin motar ya shiga,shima ya mazaunin driver ya ja motar ya mai gadi ya bud’e musu gate ya fita ya d’auki hanyar gida, “Ma sha Allah! Ma sha Allah!! Abin da nake ta fad’a kenan lokacin da suka isa gidan mai gadin gidan wangale musu gate d’in gidan sakin baki nayi ina kallon ikon Allah ganin wani gate d’in nan ma wani mai gadin ya bud’e musu suka shiga babban gida ne sosai mai d’auke da part hud’u, d’aya na Mummy, d’aya na Abba, d’ayan na Abdulhamid sai kuma d’ayan na masu aikin gidan, Ado yana yin parking kamar yadda ya saba ya fito ya bud’ewa Abdulhamid kofar, ya fito ya fara tafiya duk inda ya gifta masu aikin gidan sai sun zube suna kwasar gaisuwa, hannu kawai yake d’aga musu har ya isa Part d’insa, da kanta kofar ta bud’e ya shiga babban falo ne sosai wanda girmansa zai kai fuloti d’aya komai na falon blue ne da ratsin fari a jiki, bedroom d’insa ya huce shima yana da girma dan kad’an ya rage ya kai girman falon, ajiye ledar da yayi siyayya yay a kan bedsite drower ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet ya kai kusan awa d’aya a toilet yana wanka sannan ya fito d’aure da towel a k’ugunshi, drower ya nufa ya d’auko jallabiyya ya saka sannan ya koma wajen madubi ya d’auki kum yana taje kanshi sannan ya shiga feshe jikinsa da turarurruka, ya koma kan gado ya kwata ya so ya je part d’in Mami amman kuma ba zai yi zuwa ba saboda irin gajiyar da ya yi, ko minti biyu bai yi ba bacci mai nauyi ya yi awan gaba da shi.

 

*’KAUYEN MARKARAWA……*

 

_Wacece Dije?_

 

Dije ‘yar asalin k’auyen markarawa ce mahaifinta Malam Lamiru ya rasu tun tana k’arama, su biyu kad’ai iyayensu suka haifa daga ita sai Yayanta Musaddam, Musaddam ya yi karatun boko kasancewar kafin mahaifinsu ya rasu yana zuwa Kano ya siyar da shanuwa, irin yadda ya ga ‘yan Kano suke karatun boko yasa ya yi sha’awar ya kai Musaddam domin shima ya yi karatun, lokacin da Musaddam ya kammala secondary school mahaifinsu ya rasu hakan yasa Mussadam dawowa k’auye markarawa, saboda irin yadda Inna ta matsa masa a kan ya dawo tunda ya gama karatun, haka Musaddam ya dawo ba dan yaso ba, dan yaso ace shima ya yi karatu mai zurfi, irin yadda Dije bata da rufin asiri kuma duk abun da akayi da ita indai na sirri ne sai ta tona shi, yasa ‘yan k’auyan suke ce mata Dije tambad’add’iya, ko kad’an wannan sunan bai tab’a damun Dije ba kuma ba ta yi yunk’urin hana kowa fad’ar sunan ba, Saboda irin yadda mai garin k’auyen ya ga Dije take fad’ar gaskiya duk abun da ta ga ni mara kyau tana zuwa ta fad’a masa yasa ya nad’ata matsayin ‘yar lek’en asirin k’auyen, Dije ta ji dad’in muk’amin da aka bata don kuwa hakan zai taba damar tsula tsiyarta son ranta, ‘yan k’auyen kuma sam basu ji dad’i ba dan sun san Dije ba za ta tab’a barinsu su huta ba……….

 

 

*Cigaban labarin………….🙌🏽😂*

 

*_Habibaties gani na zo kuyi min sharing kuma kuyi min comments_*

 

*Please👏🏽*

*Share👏🏽👏🏽👏🏽*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*ƴar gidan sha’aban❤️*

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!