Hausa Novels

Tantiriya Complete Hausa novel

Tantiriya Complete Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

Alhamdulillah alhamdulillah dukkan yabo da kirari gami da godiya sun tabbata ga ubangijin talukai maiji mai gani, mamallakin sammai da k’assai da abin dake tsakaninsu mahaliccina gareka nake mik’o godiyata.*

 

*Ya Allah ya Rahmanu ya Rahimu Allah kayi salati da sallama ga annabin mu shugabanmu kuma jagorarmu MUHAMMADUR-RASULILLAHI S.A.W, da sahabbanshi da iyalanshi da Wanda sukayi imani dashi har izuwa ranar sakamako.*

 

 

 

*Masoya kubiyoni domin littafina cike yake da ilimintarwa fad’akarwa kai harma da nishad’antarwa, na tabbata zai saku nishad’i fiye da littafin KILALLU domin wannan nashi salon na dabanne.*

 

*Fatana da addu’ata shine yacce na fara wannan labari na TANTIRIYA lafiya ubangiji yasa nagama shi lafiya, kusani comments d’inku shine k’arfin gwiywata a ko da yaushe masoyana.*

 

*SHAFI NA 1📖* “Boka so nake a jefeta da bak’in jini mai k’arfin gaske Wanda zaija kowa ya gujeta, ta daina haskawa ta daina burge uban kowa ta fita aran kowa kowa yaji ya tsaneta, soyayyar da mutane ke mata ajuyar da ita izuwa bak’ar k’iyayya, samarinta su koma mata kallon Bunsurin cikin je-ji, k’awayanta sukoma mata kallon karyar kan ti-ti, malamanta sukoma mata kallon Ballagaza, danginta suke mata kallon do-do, mutanan gari suke mata kallon abin k’yama, haka zalika iyayanta suke mata kallan almajira ko y’ar rik’o mak’ask’anciya.

 

Acireta daga zuciyar kowa akashe tauraronta muris har lahira, a firgita rayuwarta a tsorata tunaninta a rud’amata lissafinta kazalika a wargatsa wannan natsuwar ta-ta.

 

Inaso Kare ya fita daraja, maciji ya fita samin wajan fakewa, sannan mushe ya fita daraja wajan mutane.

Sam bansan mutuwarta so nake a jirkitarmin da rayuwarta sama ta koma k’asa k’asa kuma ta dawo sama, a koramata bak’ak’en aljanu Wanda zasuke bibiyarta dare da rana har saita zama mahaukaciyar da babu wani gidan mahaukatan dazai iya rik’onta.

 

Boka ko kad’an ko da wasa banaso a sassautamata so nake taita mutuwa a tsaye tagama wulak’anta tagama jigata kafin mummunar mutuwa da mummunar k’arshe su risketa.

 

Ni kuma a koremin zazzafin farin jini asani aran kowa ta yadda zan sami damar shiga ran duk Wanda nakeso.

A haskakamin duniyata a fad’ad’amin duniyata a cikata dajin dad’i marar Yankewa, a tashi taurarona na zam Zinariya cikin mata.

 

“Idan har kamin haka Boka nasami cikon burina domin Sam bansan Fa’izarh taci gaba da walwala a rayuwarta.”…

 

Dariya mai k’arfin gaske matashiyar budurwar ta saki wacce a k’alla bazata rufe shekaru ishirin ba.

Zaune take gaban k’aton wani basamuden shirgegen Mutum Wanda a zahiri bai kala da Bil-Adam ba.

 

Wata zazzafar iskace ta kad’a mai k’unshe da sautin bak’ak’en aljanu, yayin da guguwa mai k’arfin gaske ta tashi a saitin gaban wannan bokan.

 

Kankace maye fuskokin bak’ak’en aljanu masu tsananin muni wajan kama suka fara bayyana cikin wannan guguwar ta gaban boka.

 

Dariya ce ke tashi ga k’arar guguwa data cike ciki da wajan bik’in jejin da suke ciki Wanda ba hasken farin wata Dana taurari balle na lantarki sabo da tsananin duhu da bak’in ciyayin wajan.

 

In few m wani k’aton babban aljani bahaushe ya bayyana gaban wannan bokan yana dariya da tafi kukan karnuka k’arfi da tsoratarwa.

 

Cikin Indian language Bokan yayiwa aljanin magana ta tsawan 2m.

cikin k’ank’anin lok’aci bak’in aljanin ya juyo da ganinshi gaban wannan matashiyar dake zaune tan k’washe da k’afa gaban boka wacce har zuwa lok’acin take dariya batare da tsoro ko alhinin ganin wata halitta wacce bata D’an Adam bah gabanta.

 

Cikin wata murya mai munin gaske aljanin yace.

 

” yarinya kinyi tafiya mai tazarar gaske tun daga k’asarki Nigeria izuwa wannan k’asa ta India, ko da kika zo Indiar mah sai da ki kayi tafiya mai tsayin gaske gami da had’ari mai girman gaske, k amma kika murje ki kayi fuska duk akan muguwar buk’atarki, kin taho tundaga Mumbai izowa garin Banghulu sannan daga nan kika kutso kanki cikin wannan jejin sanda ki kayi tafiyar kwana d’aya da yini d’aya kafin isowarki nan.

Batare da gazawa ba ko wani tsoro kika zuba gwiwyoyinki kika tan k’washe k’afa gaban bokan da Aljanun duniya ke gwabzawa dashi kuma da yawan wasu aljanun ke shakkarshi gami da mugun tsoranshi dan dayawama akwai Wanda suke kamar bayi a gareshi sabo da k’arfin Pawer shi.”…

 

Dariya ya k’ara bugewa da ita saida yayi mai isarshi sannan ya d’ora da.

 

” madalla da wannan k’wazo naki, madalla da wannan Jan aiki naki, hak’ik’a Boka FURTAB ya amshi buk’atunki, ki fad’o sunan mahaifiyar yarinyar wacce ta haifeta da ranar da aka haifi yarinyar.”…ya k’arashe magana still yana dariya.

 

Wani irin farin cikine ya rufeta tare da fara magana baki na rawa.

 

” sunan yarinyar Hassina mahaifiyarta kuma.”…

 

Wata razananniyar tsawa Aljanin Boka Furtab yayi wacce duk da k’arfin hali da rashin tsoran yarinyar saida ta razana, nan ya gargad’eta dayin abin da aka umarceta na fad’in iya sunan Mahaifiyar yarinyar da ranar haihuwarta dansu basa wani buk’atar sunan yarinyar.

 

 

Nan tafad’i baki na rawa duk da tsoran da taji cikin farin ciki take magana.

 

Nan take fuskar Hassina ta bayyana a cikin wannan guguwar ta gaban boka Furtab , hannu Aljanin yasa tare da shafar wuyanta yana dariyar mugunta.

 

Nan take bokan dashi da aljanin suka fara dariya mai hargitsa k’wak’walwar Bil-Adam.

 

Cikin d’aga murya wannan Aljanin ya fara kiran sunan bak’ak’en aljanu har guda hud’u, nan take suka bayyana cikin mummunar suffa.

 

Wani garin magani ya mik’awa na farkon Nan take ya fara fad’in.

 

” rub’ab’b’un kayan cikin gawar wani tantirin Boka da yake garin Mumbai, da rub’ab’b’un kayan cikin gawar alade da kuma Rub’ab’b’un kayan cikin gawar karya aka shanya suka bushe sannan aka had’a wannan maganin, Furutu idan har kasa cikin ruwan wankan yarinyar tayi wanka dashi to tamkar tayi wanka da ruwan wankan gawane cikin kwanaki kad’an duk mutanen da take mu’amala dasu zasu mance da ita, ba iya Bil-adam dai-dai da wata halitta saita mance da ita, a zahiri dai matacciyace a bad’ini kuma rayayyace kai d’aici kawai sai yayi silar ajalinta domin babu Wanda zai kusanceta.”…

 

” kai kuma Zubur da Ranchai zakuje ne Ku firgita rayuwarta ku tsorata tunaninta Ku rud’amata lissafinta, sannan Ku wargatsa natsuwarta dukanta kamar yanda ta buk’ata , Ku tabbatar ta rasa duk wata natsuwa ta-ta kamala k’ima duk Ku zubarmata dasu.”….

 

” phauger kai kuma zaka bibiyetane iya tsayin rayuwarta duk Wanda kaga yana da niyya ko k’ok’orin taimakonta ka hallakashi, wanda hakan zai k’aramata bak’in jini k’warai da gaske.”…

 

Batare da tawaya ko canzuwar Suffa ba zata munana k’warai da gaske idon mutane.”…

Wata gigitacciyar dariya su duka aljanun sukasa da Bokan ciki ko harda matashiyar budurwar *Diya* .

 

” ke kuma sharad’i biyune a kanki, na farko daga yau mun haramtamiki sake yin sallah ba’iya na wani lok’aciba na iya duka tsayin rayuwarki bazaki sake yin sallaba, sannan zamu had’aki da Yaronmu Bungdur shidai Mutum ne amma a zahiri zakiga kamar aljani ne zaiyi tarayya dake na tsawan kwana uku , a kwana ukun al’adarki ko ta kusa zuwa koda saura zadai tazo idan harkinyi aikin da yaja kika kwantamashi a rai har yasha jinin al’adarki toh fa kin more domin duniyarki zata haskakane zakiji dad’i zakiyi nishad’i za kuma kifantama mutane zasuyi dake kema kuma zakiyi dasu zaki shiga ran Mutum da aljann Deeyarh sunanki zai shahara abakin masu mu’amala dake lalle tauraronki zai haskaka, hahahaha hahahaha.”…. Yafad’i yana mai bugewa da dariyar da saida dajin ya amsa tako ta ina.

 

Wani sanyi gami da daddad’ar iska Deeyarh taji yayin da tuni tasamu ya k’ini gami da natsuwa akan abin da Aljanin Furtab yace mata, tabbas ita ji take ko a yanzu tabar duniya ta cika burinta domin bata da burin daya wuce ganin Hassinarh ta wulak’anta ta tozarta ta k’ask’anta ba.

 

Dariya itama ta fashe da ita tamkar aljana yayin data kwance ribom d’in kanta tana karkad’a kanta gami da rawa dashi cikin kakkaifar murya tamkar ba itaba tace.

 

” Boka babu damuwa zanyi duk abin da kuka cemin daman ni duniya ce a gabana Burina tunanina da lissafina a kullum bai wuce yadda za’ayi na sami duniya da jin dad’in cikin taba kuma a b’agas, nidai burina Ku bani zazzafin farin jini ta yadda zan mallaki zuciyar Wanda nakeso, ita kuma Hassinarh ta dawwama cikin bak’in jini da mutuwar rayuwa, tabbas Idan zan sami haka zanyi fiye da abin da kukace, hahahahah.”… Ta fad’a Tamkar bokanya yayin da take kara rawa da kanta.

 

Nan take itama suka buk’aci ta fad’i sunan mahaifiyarta da mahaifiyar mamanta wato grandmother and date of Barth of her.

 

Bayanta fad’amusu Aljanin Yace.

 

” tabbas zaki samu jin dad’in rayuwa ita kuma zata haukace tarihinta ya shud’e duk da tana raye amma sai ta gwammace gwara mutuwa fiye da rayuwarta, amma ki sani muddin kinyi kuskure wajan fad’in sunan mahaifiyarki da kakarki ko shekarun haihuwarki to lalle ki kuka da kanki domin mu ba’amana kuskure kamar yadda bama son gyara,hahahaha hahaha.”…

 

Itama cike da nishad’i tace.

 

 

” tabbas boka banyi kuskureba domin Deeyarh Sam bata kuskure, hahahaha hahah.”…

 

Nan su duka suka dunga dariya yayin da guguwa ta ninku sama da wacce ke kad’awa abaya yayin da bushiyoyi ke kad’awa tun k’arfinsu inda duhu ya k’ara tsananta a dajin babu abin dake tashi, face sautin dariya Aljanu da boka da kuma Deeyarh.

 

Niko ina daga gefe nace lalle Diya a gaisheki.

 

 

 

*Mujezuwa*

 

 

 

*Comments, like, vote & share*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wattpad:- *GaskiyaWritersAsso.*

*Gmail:*

-gakiyawritersassociation@gmail.com

Youtube Channel:-

*Gaskiya Hausa Novels TV.*

Bakandamiya:-

*GASKIYA WRITER’S ASSOCIATION.*

 

*Our Motto:*

_{Gaskiya ɗaya ce daga ƙinta sai ɓata, burinmu mu faɗakar da Al’umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_

 

 

*Alƙalamin Dr Fayeex✍🏼*

Leave a Comment

error: Content is protected !!