Tarihin Aisha Najamu Izzar So Hajiya Nafisa
Aisha Najamu Izzar So wanda akafi sani da Hajiya Nafisa cikin shahararren shirin nan wanda tashar Bakori TV take kawowa wato Izzar So, wannan jaruma ta shahara sosai cikin kungiyar Kannywood saboda yadda mutane suke kaunar wannan shiri akoda yaushe.
Tarihin Aisha Najamu Izzar So (Farawa)
Wannan rubutu munyi shine domin tsakuro muku wani sashi daga tarihin Aisha Najamu a takaice, muna fatan zaku karanta wannan post cikin nutsuwa domin sanin wace ce Hajiya Nafisa Izzar So.
Wacece Aisha Najamu?
Aisha Najamu wata sananniyar jarumar kannywood ce wanda aka haifa a garin Jihar Jigawa a ranar 12 ga watan Agusta a shakarar 1997 kuma tayi karatun Sakandire a cikin Jigawa, daga nan jarumar ta dora karatu a Jihar Maiduguri inda ta karanci harkar kasuwanci domin samun abin dogaro dakai.
Aisha Najamu Izzar So tayi Aure bayan wani lokaci inda allah ya albarkace ta da samun ‘ya ‘ya har guda biyu, lokacin da take bayyana yadda tayi Aure, Aisha tace tayi aure da wuri saboda mahaifinsu mutum ne mai saurin aurar da ‘ya ‘yansa da zarar sun zama yan mata.
Aisha Najamu Izzar So
Yaushe Aisha Najamu Tafara Film?
Bana shekara biyu kenan da Aisha Najamu ta fara film, wato ta shigo kannywood a 2019 zuwa 2021 kuma anfara shirya wakokin hausa ne da ita kafin daga baya ta samu shiga shahararren shirin Izzar So wanda Bakori TV suke kawowa a tasharsu dake Youtube.
Jarumar a lokacin da ake sanyata a wakokin hausa tayi suna sosa domin masoyanta dadama daga nan suka fara sonta saboda yadda ta iya hawa waka cikin salo mai burgewa, tayi videon wakokin hausa da manyan jaruman kannywood irin su Garzali Miko, Abdul M Shariff, KB International, da sauransu.
Wacce Matsala Aisha Najamu Izzar So Tasamu A Kannywood?
Kamar yadda jarumar ta bayyan a hirar ta da BBC Hausa tace bata taba samun wata matsala ba cikin shirin film din da take yi a Kannywood, sai dai tace wata rana ta wallafa wani rubutu a shafinta na Instagram domin tunawa da ranar da aka haifi Sayyadina Aliyu (alaihissalam) kawai sai mutane suka fara ce mata ‘yar shi’a.
“Mutane suka fara surutu akan rubutun da nayi kuma suna ce min ni ‘yar shi’a ce” Inji Aisha Najamu, wannan shine matsalar da jarumar tace tasamu tun sanda ta shiga harkar shirya fina finan Hausa.
Mecece Alakar Lawan Ahmad Da Aisha Najamu?
Kamar yadda muka fada a farko Aisha Najamu tafara yin videon wakokin hausa ne kafin daga baya ta shiga shirin Izzar So, alakar da ke tsakanin Lawan Ahamd (Umar Hashim) da Aisha Najamu (Hajiya Nafisa) kawai abokan sana’a ne kuma sun kasance cikin girmama juna akoda yasuhe,
Kuma ta bayyana abin dayake sata farin ciki duk lokacin da ta tuna cewa yanzu tana iya daukar nauyin kanta dana iyayenta akoda yaushe, Aisha Najamu tace tana alfahari da hakan kuma tasamu wannan abu ne sanadin fara shirin Izzar So.
Aisha Najamu Izzar So
Shin Aisha Najamu Tana Da Aure Yanzu?
Aisha Najamu tayi aure a baya kuma har tana da ‘ya ‘ya maza guda biyu amma a halin yanzu bata da aure, jarumar tayi aure tun tana yar karamar Budurwa kamar yadda tafada a tattanawar ta da BBC Hausa.
Amma da aka tambaye ta, Yaushe zaki kara Aure? jarumar tace duk lokacin data samu wanda yadace zatayi aure, ya zuwa yanzu dai ana ganin Aisha Najamu tauraruwar ta tana kan haskawa kuma kullum kara yawan masoya takeyi.
Tarihin Aisha Najamu Izzar So (Karshe)
Aisha Najamu Izzar So ta kasance cikin shirin Bakori TV yanzu wajen shekara guda kenan, wannan shiri na Izzar So ya haska jarumar wanda yanzu haka tana cikin jaruman Kannywood yan mata da akafi yayi, kuma hakan yasa jarumar ta rage fitowa cikin shirin wakokin hausa da ada aka santa tana yi.
Yanzu haka Izzar So shine shirin hausa film na kannywood da akafi nema a cikin Qasar Nigeria da Niger.
Wannan shine karshen Tarihin Hajiya Nafisa Izzar So wato Aisha Najamu, muna fatan wannan rubutu ya gamsar da ku kuma idan anga kuskure cikin wannan post muna rokon a sanar damu zamu gyara cikin gaggawa.
Umar Hashim Na Murnar Cika Shekaru 13 Da Aurensa
Ku kasance da Izzar So Website domin samun abubuwan da suka shafi shirin akoda yaushe, Muna fatan zakuyi Sharing din wannan post a shafukan sada zumunta domin bamu gudummawa. Mungode
A
[…] Tarihin Sugaban Nijar Bazoum […]
Tambayata anan itace yanzu tanada aure ko babu
BABU
AISHA WAI DAMA A FILI BAHAKA KUKEBA? DA FILMNE TO (ALLAH)YAKARA DAUKAKA. !!!!
GIADE