Hausa Novels

Tarihin Dr Ahmad BUK

Tarihin Dr Ahmad BUK

 

 

 

 

 

 

 

 

Daga Munir Assalafiy

 

Dr. Ahmad BUK fitaccen malamin addinin musulunci ne, tsohon malami ne a Sashen Larabci a BUK. An haifi Ahmad BUK a Ghana.

 

Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba wanda aka fi sani da Dr. Ahmad BUK da Kala Haddasana. Ya kammala karatunsa a daya daga cikin manyan Makarantun Ghana. Ya yi karatu a Saudiyya.

 

Bayan nan ya dawo Najeriya ya karantar a Jami’ar Bayero da ke Kano inda yayi karatun dakta. Dr. Ahmad BUK. Dr. Ahmad BUK ya auri mata 3. Shi ya sa ya bar mata 3 da ‘ya’ya 30 ciki har da jikoki.

 

Dr Ya karantar da littafai masu dimbin yawa wadanda har ya saukesu tare da Dalibai. Haka zalaika Dr yanada tarin Dalibai masu dimbin yawa wadanda a halin yanzu suma sunada tarin Dalibai da suke karkashinsu.

 

Daga cikin Manyan ayukkan da Dr yayima addini akwai fassara littafin Muwadda Malik zuwa yaren Hausa a ranar 1 ga watan Muharram 1443. Wanda Gerawa Oil ya dauki nauyin bugawa.

 

 

Dr yakasance wani alheri wajen bayas da gudunmawa ga addini a Nijeriya da Kasashen waje. Dr yakasance mutun marar tsoro wajen yada Sunnah tun lokacin da kowa yakejin tsoron yadata.

 

Dr. Ahmad yana da shekaru 82 a lokacin da yabar duniya a shekarar 2022. Dr. Ahmad BUK ya rasu ne a ranar 7 ga watan Janairun 2022 dai da 4_6_1443, a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan ya sha fama da jinya.

 

Allah Ta’ala yajikansa da rahma

 

Wafatin Dr Ahmad BUK

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Dakta Ahmad BUK ya rasu a Kano.

Allah yayiwa fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba wanda aka fi sani da Kala Haddasana rasuwa a yau Juma’a.

‘Yan uwa sun tabbatar wa BBC Hausa rasuwar.

Fashin baki kan cutar corona Dr Mansur Sokoto

Ya kasance mashahurin malamin Hadisi, inda ya kasance yana koyarwa a masallacin BUK amma daga baya a nasa masallacin da ake kira Darul Hadith.

Ya rasu ne bayan gajeruwar jinya a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.

Iyalan sun sanar da cewa za a yi jana’izar ne a masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan sallar Juma’a.

Daya daga cikin ‘ya’yansa Abdul ya shaida wa sashen Hausa na BBC cewa yana da shekaru kusan 82 a duniya, ya bar ‘ya’ya 30.

Kala Haddasana, kamar yadda aka fi saninsa, ɗan ƙasar Ghana ne kuma a can aka haife shi.

Ya dawo Najeriya ne bayan ya yi karatun digiri a Saudiyya inda ya yi koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano.

 

Tarihin Dr Ahmad BUK

4 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!