Taswirar Kaddara Hausa Novel

Wayyo gindina Hausa Novel

Taswirar Kaddara Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

TASWIRAR KADDARA

 

 

 

 

Written by

Mrs A.M🥰

 

Page 1

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

 

 

Ina zaune a matsakai cin tsakar gidan mu ina duba littafina kasancewar Jamb din da zan rubuta wannan shekarar gashi lokaci yana ta kurewa saura sati biyu mu zama jamb din.

 

Hankali na ya kasu kashi biyu, daya yana kan English din dana ke rubutawa daya kuma yana ga tunanin inda *MIMI* ta shiga, tun da akai la’asar ta fita ban kara ganin taba, kwafa nai ina tunanin yadda zan hukunta ta tunda tasan cewa bana son tana fita da yamma haka ita kadai.

 

Wata yarinya mai kimanin shekaru 4 fara kar kamar balarabiya sbd tsabar kyaun da Allah yai mata ta shigo gidan tana sanye da riga yar kanti har kasa duk da rigar tadan kode amma kal take a wanke sai alamun kasa kasa daka kasan rigar da alama yarinyar tayi wasa a kasa ne.

 

Tunda ta shigo na kafe ta da ido ina tasbihi a raina, kullum na kalli Mimi sai nayi tasbihi ga Ubangiji sbd tsabar kyaun ta, fara ce tass mai dauke da zagayayyiyar fuska tana da manyan idanu sosai tubarkalla sai dogon hanci wanda ya dace da zagayayyiyar fuskar ta sai kuma karamin bakinta jajir dashi, maida kallona kan gashin ta nai dake tufke amma jelar har kusan duwawun ta take sbd tsayin gashin ta.

 

Lumshe idona nai jin wani hawaye yana kokarin zubo min, muryar ta mai cike da shagwaba naji a kusa dani tana fadin *”MAA* kiyi hakuri baxan sake ba Hidiya ce tace inzo muyi wasa a garden din gidan su.”

 

Kallon ta nake kawai ina bin kumatun ta da kallo yadda dimple dinta na gefen kumatun ta na dama yake lotsawa sosai, hakan ba karamin kyau yake karama ta ba.

 

Hade rai nai cikin dan fada fada da saurin maganar da nake da shi nace “ban hana ki fita ba amma wato kin fara raina ni koh Mimi shine har zaki fita BA tare da na sani ba”

 

Rau rau tai da idonta daya fara tara hawaye ta kama kunnuwan ta da hannayen ta tace “Maa kiyi hakuri bazan sake bafa kar kiyi fushi dani”

 

Daga bayan mu Umma da ta fito daga daki tayi dariya tace “zo kinji kawata kema kinsan Maa dinki baxa ta iya fushi dake ba”

 

Makale kafada tai tace “toh Umma ai bata ce ta hakura ba”

 

Janyo ta jikina nai cikin tsananin kaunar ta nace “na hakura babyta amma kar ki sake fita ba tare da kin fada min ba kinji koh”

 

Daga kai tai tana kuma kwantar da kanta a jikina sai shagwaba take zuba min ina biye mata, girgiza kai Umma tai kawai tana dauke kwallar dake neman sakko mata a fuska.

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Muna zaune a tsakar gidan Umma da Mimi na kan tabarma ni kuma ina daga kitchen Aysha ta shigo cikin uniform din islamiyya.

 

Fitowa nai hannuna rike da ludayi nace “kinyi saurin dawowa yau Aysha ina su Kamal din”

 

Zama tai akan tabarma tana ajiye jakar hannun ta cikin gajiya tace “suna hanya Ya *BATUL* ai baxan iya jiran suba wallahi duk ba gaji fah kinji kafa ta”

 

Dariya nai nace shiyasa nace “sannun ku ai kun kusa sauka ki dinga hutawa kema”

 

Kallon Mimi tai tace “shine kika ki zuwa islamiyya yau koh ai Malamar ku tace sai ta zane ki gobe”

 

Murguda karamin bakin ta tai tace “ai bani da lafia kaina yake ciwo shine Maa tace nai zama na gobe sai naje”

 

Na bude baki zanyi magana knn su Kamal suka shigo, kallonsu nake da dukkan alamu ba lafia ba don yadda Kamal yake ta hura hanci yana goge gumi.

 

Kallon Khalil nai don nasan yadda kamal yake ko na tambaye sa baxai iya min magana ba, cikin saurin magana ta nace “mai aka masa naga sai huci yake ko fada sukai ne”

 

Goge goshin sa Khalil yai cikin nutsuwa kasancewar sa komai a nutse yake yace “Ya BATUL Manniru din gidan Kawu Nasiru ne sukai fada dashi, wai kawai don Malamar su Mimi tace bata ganta ba a gaishe mata da ita shine da muka fito ya tare mu yana fadin baiga amfanin saka Mimi a makaranta ba tunda *SHEGIA CE* ita Shi kuma khalid ya mare sa shine suka fara fada da kyar aka rabasu” ya karashe hawaye na zubo masa.

 

Tunda ya ambaci shegia naji kirjina na min wani irin zafi cikin masifar dake taso min na shiga dakin mu, hijab na dauko na fito dashi a hannu na ina kokarin sawa.

 

Umma da tai shiru kanta a kasa ta dago ta kalle ni tace “meye haka Batul ina zaki je”

 

Girgiza kai kawai nake don tsabar bala’in dake cina bana Jin ma zan iya magana in da abinda na tsana a duniya shine a dangan ta min Mimi da shegia tabbas nasan gaskia ake fada amma raina baci yake a duk lokacin da aka kirata da haka kuma ko waye ya fada mata sai na gaya masa maganar da nasan zai dade yana jin takaicin ta.

 

Da kyar na hadiyi wani yawu nace “zanje gidan su ne in jawa uwani kunne akan yaranta wallahi Umma duk lokacin da suka kara shegan tamin yarinya sai nasa an karya musu kafafu don uban babansu.”

 

“Mai kuma babana yai haka ake zagin sa Batul”.

 

Juyawa nai ina kallon babanmu daya shigo hannun sa rike da leda wanda wannan dabi’ar sa ce kullum zai dawo daga kasuwa sai ya siyo wani abu komai kankantar sa ya shigo da shi.

 

Turo karamin bakina nai gaba ciki ciki nace “Manniru neh ya cewa Mimi shegia shine zanje na jawa uwani kunne akan su kar nasa su cilla su karya min kafar su ace ban fada musu ba”

 

Zaunar dani baba yai akan dakalin kofar dakin mu yace “don sun ce haka sai ki biye musu, kinsan dama abinda suke so knn suyi magana wani ya biye musu su tada fitina ki rabu dasu wata rana ko ance su fadi haka baxa su fada ba Batul”

 

Nidai Shiru nai kawai ina girgiza kaina tunda Baba yace na rabu da su na kyale su Amma wallahi sai nasa cilla ya zane min yaron nan in da hali na ko yar karamar targade ne ya masa a kafafun.

 

Ina zaune a wajen Aysha ta shiga kitchen don karasa girkin da ban gama ba, su Khalil kuma sun chanja kaya sun fita, Mai da kallona nai gurin su Baba da yake wa Mimi Wasa sai dariya take tana jan gemun sa. Kafe ta nai da ido ina Jin tsoron zuwan ranar da zata tambaye ni *WAYE MAHAIFIN TA* mai zan ce Mata ban san saba ban taba ganin fuskar sa ba banma san ya yanayin sa yake ba abu daya ne nake da shi mallakin mahaifin ta shi kuma bansan ta yadda zai kaini ga mahaifin nata ba.

 

Lumshe idona nai tsanar ko waye baban ta yana taso min tabbas da zan ido hudu da shi da ina da dama saina caka masa wuka a kirji……

 

 

 

 

*************

 

Zaune suke a lafiyayyan palourn gidan daya kasance mallakin mai gidan ko wanne dare anan iyalan gidan suke taruwa suke zama tare suke cin abincin dare.

 

Mami ce ta shigo palourn cikin shigar ta da kowa yasan ta da shi wato lifaya mai tsadar gaske red colour wacce ta haska farar fatar ta kana kallon ta zaka san cewa ita din shuwa arab ce, zata kai shekaru 45 Amma jikin ta bai nuna ba sbd tana da jiki nai kyau.

 

A hankali take tafiya hannun ta rike da kaskon turaren wuta data saka, sai da ta fara ajiye kaskon a kan table din gefen manyan kujerun Palourn sannan ta juya ta kalli Abie da tunda ta shigo ya kafe ta ido yana sakar mata murmushi mai cike da ma’ana, itama mayar masa da martanin murmushin tai tana masa wani kallo na kasan ido kafin ta isa kan kujerar da suke zaune shida Mama ta zauna itama.

 

Gaisar da Abie tai cikin nutsuwa kafin ta juya taiwa mama sallama, ciki ciki ta amsa ta daga kanta sai hura hanci take, itama bata damu ba ta maida kallon ta kan TV tana kallon news.

 

*JUNAID* ne ya fara shigowa cikin nutsuwa sanye da jallabiya as usual hannun sa dauke da carbi yana ja a hankali, kara sowa yai kusa da Abie ya tsugunna ya gaishe su, cikin so Abie ya amsa yana shafa kwantaccen sumar sa.

 

Mami ma murmushi take kafin tace “ina ka baro Samira din yauma baka zo da ita bakoh?”

 

Sosa goshin sa yai yana sunkuyar da kansa don baya iya hada ido da iyayen sa yace “Mami tana gidan su ne ynxu in zan wuce zan biya na dauke ta”

 

Gyada kai tai tace “Allah yai muku albarka ya warware muku dukkan matsalolin ku”

 

Ameen ya amsa yana komawa gefen ya zauna a kasa yana jan charbin sa cikin nutsuwa.

 

Baiyi minti goma da shigowa ba Yusuf ya shigo bayansa Sagir ne sai auta Mufeeda, Suma sai da suka gaishe da Abie dasu Mami sannan suka koma kusa da Junaid suna masa magana kasa kasa.

 

Hade rai Mama tai ta sani kusancin yaran ta da su Junaid tayi yadda zata yi ta raba su Amma abin yaci tura ta zage su ta zuga su amma a banza sudai kome zata yi baza su daina kula Yan uwan suba, kusan kullum ma a part din Mami suke wuni wannan abin yafi komai bata Mata rai.

 

Kallon su Abie yai kafin ya girgiza kansa yace ina *AZLAN* Junaid ne ya amsa Shi da fadin “Abie yana nan zuwa da zan fito ya shiga wanka neh”

 

Gyada kai kawai Abie yai yana maida kallon sa TV, ba’a dau lokaci mai tsayi ba suka fara jiyo fito yana doso palourn gaba dayan su suka zubawa kofar shigowa palourn ido duk da kuwa sun san waye zai shigo din.

 

Cikin takun jarumta ya shigo palourn yana sanye da three quarter brown colour sai armless riga light brown wacce ya bude botir din gaban rigar guda uku hakan ya bayyana kirjin sa, kafar sa sanye da wani takalmi mai kama da silifas, kamar su daya da Junaid don kana ganin su zaka gane Yan biyu neh sai dai Shi yafi Junaid haske kuma ya fisa kyau da kirar jiki mai kyau, cikin takun jarumta ya karaso tsakiyar palourn bayan ya cire takalmin sa.

 

Binsa da kallo Mami tai tana girgiza kai ganin askin kansa ita ynxu ma data sanin ce masa yaje yai aski take, da kansa sumar ce kawai ya tara sosai duk da sumar tasa a kwance take kamar ta larabawa amma tace yaje ya rage ta gashi ynxu yaje an kwashe gefe data an bar masa gefe daya. Mai da idonta kan damtsen hannun sa na dama tai dake dauke da katon tattoo na zaki a jiki, sai gefen wuyansa na hagu kuma da aka masa tattoo na miciji inda aka biyi da jelar micijin har wajen kirjin sa, girgiza kai tai a ranta tace “Allah ya shirya min kai Azlan”

 

Daga tsayen da yaje ya dan rankwafo yana tura hannun sa a cikin aljihun sa cikin muryar sa Mai kaushi da kame wa yace “Evening Abie” ba tare daya jira amsar Saba ya juya gun Mami yace “Evening Mami”, Mai da kallon sa kan Mama yai ya zuba mata manyan idon sa da suka sha kwalli yace “Eve Hajia”

 

Hadiye wani yawu tai a duniya tana tsoron Azlan duk iskancin da zata yi a bayan idon sa take yinsa amma tana matukar tsoron sa, cikin inda inda tace “lafia”

 

Yamutsa fuska yai yana duba apple watch din dake daure a hannun sa na hagu ganin pass 8 yasa shi kallon Abie yace “zan iya ware wa Abie”

 

Girgiza masa kai yai takaici kamar zai kashe sa yace “na fada ma wallahi yau baxa ka fita a gate dinnan ba na gaji da halin Ka in Ka fita shashancin Ka baxa ka dawo ba sa tsakar dare”

 

Girar sa ta hagu ya daga yana shafa gemun sa yace “ta gate nedai Ka haramta min ware koh”

 

Daga kai Abie yai cikin tabbatar wa, juyawa yai ya kalli su Junaid da suka zuba masa ido gaba dayan su, yana juyowa duk suka juya suka maida kallon su kan TV sai Junaid ne kawai ya tsare sa da ido yana masa magiyar ya saurara yaji abinda Abie zaice.

 

Tabe bakin sa yai ya kalli Mami yace “kina bina da addua fah Mami kar wata ta danne miki ni tayi min fyade ta raba ni da budurwarcin dana ke ajiye wa”

 

Sunkuyar da kai su Mufeeda sukai yayinda Abie ya zuba masa ido kawai yana mamakin inda Azlan ya dakko rashin kunya sam bashi da kunya ga kwarjini da Ubangiji yai masa ko shi daya ke mahaifin sa kwarjini yake masa sosai, ita dai Mami addu’ar daya ce tai masa take yi a zuciyar ta tana kuma roka masa shirya.

 

Juyawa yai yana tafiya cikin jarumta, sai da yakai bakin kofar palourn ya juyo ya kalli Abie yace……

 

 

 

 

 

 

Ya kukaji salon book din🥰

 

Littafi ne mai cike ta sarkakiya ku biyo ni don na warware muka duk wata sarkakiyar dake ciki.

 

 

 

Comments Nd share plz🥹

 

 

 

Mrs A.M🥰❤️

[11/08, 3:01 pm] +218 92-2035171: ♠️♠️♠️♠️♠️

 

*TASWIRAR KADDARA*

 

♠️♠️♠️♠️♠️

 

 

Written by

Mrs A.M🥰

 

Page 2

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

 

Sai da yakai bakin kofar palourn sannan ya juyo ya Abie yace “baxan taka dokar kaba,” daga haka yasa kai ya fita.

 

Da sauri Abie ya mike yabi bayansa sanin dayai masa tunda har ya shirya zai fita sai ya fitan kuma ba ta gate zai bi ba, bin bayansa Junaid yai shima da sauri yana girgiza kansa.

 

Azlan yana fita daga palourn bayan gidan yaje ya dakko ladder ta karfe cikin zafin nama, ya rike ta da hannu daya kamar ba abin nauyi ya dakko ba, ware ta yai ya saita a jikin bangon gidan yadda zai mai daidai, su dai masu gadi suna zaune sai satar Kallonsa suke ba halin su bari ya gane suna Kallonsa.

 

Cikin sassarfa ya shiga takawa hana hawa sai da ya Kai karshen sa yadda zai dira daga gidan sannan ya juyo ya kalli Abie da Junaid, shafa gemun sa yai kafin ya saki wani murmushin gefen baki daya bayyana dimple dinsa guda daya na bangaren dama, juyawa yai ya dira daga gidan.

 

Sai da Abie ya dafa kirjin sa yana addu’ar Allah yasa bai ji ciwo ba, maganar da Azlan yake da karfi ne yasa Abie sauke ajiyar zuciya.

 

Shi kuwa yana dira mikewa yai ya karkade jikin sa sannan ya kalli dogon ginin daya diro, shafa gemun sa yai yana lasar lips dinsa iPhone 13 pro max dinsa ya zaro a aljihun sa, wata number yai dialing bata dade tana ringing ba aka dauka.

 

A kausashe yace zo mu hade ina kofar gidan mu, daga haka ya kashe wayar, bai dade sosai a wajen ba wata lafiyayyar mota ta shigo layin, a daidai kusa da shi ta tsaya bai wani tsaya jiran komai ba ya bude gurin mai zaman banxa ya shiga suka figi motar a guje suka bar layin.

 

Abie kuwa girgiza kai yai kawai suka koma palourn, Mami ce ta kalle sa fuskar ta cike da damuwa tace “ya fita koh Abie”

 

Zama Abie yai yana ajiyar zuciya yace “don na ce masa baxai fita ta gate ba shine ya haura katanga ya dira”

 

Lumshe idon ta kawai tai tana binsa da addu’a duk da ya kasance mara Jin magana amma shidin mafi soyuwa a gare tane baya Wasa da duk abinda ya shafe ta kuma baya mata karya.

 

Mama kuwa ajiyar zuciya ta sauke cikin Jin dadi sbd dama ita duk ranar da yazo suka zauna da shi takura mata yake, ta rasa mai yasa yaron ya raina ta tunda take dashi bai taba ce mata Mama ba sai dai Hajia da Yaya ma yake ce Mata saida Abie da Mami suka dinga masa fada sannan ya fara ce Mata Hajia.

 

Haka suka ci abinci kafin su gama aka shiga hira, sai wajen 10 sannan Junaid ya mike kallon Abie yai yace “Abie bara na tafi zan biya na dauki Samira a gidan su”

 

Murmushi Abie yai cikin kauna yace “Allah ya tsare ya cigaba da kare mana ku Allah ya warware muku dukkan matsalolin ku”

 

Fuskar sa cike da murmushi yace”Ameen”

 

Kallon Mami yai cikin nutsuwa yace “Mami sakon samiran tace min kin ce zaki bada sako in taho mata da shi”

 

Mike wa Mami tai cike da tausayin yaron nata ta ce “muje na baka dama dambun naman da nai ne nasan tana so sosai shine na zuba mata”

 

Tabe baki Mama tai tana gwasine fuska itama ta kusa aurar da Yusuf dinta tayi sirikar.

 

Bayan sun shiga part din Mamin Mika masa leda Mai dan girma tai wacce take dauke da dambun naman a cikin, sai da ta kara masa nasiha sosai akan yadda da KADDARA sannan ya tafi.

 

Binsa tai da kallo cike da tausaya wa shekarar sa biyar da aure amma har ynxu matar sa ko bari batayi ba, duk inda suka je kuma matsalar daga gare sa ne amma matar tasa lafiyar ta Lau, da farko da aka gane matsalar daga gurin sane yaso rabuwa da samiran amma ta dage ita akan ta yadda da KADDARA zata zauna da shi ko da baxa ta taba haihuwa ba har karshen rayuwar su..

 

 

 

***********

 

Kallon cilla nai dake zugar sigarin sa cikin kwanciyar hankali, tsaki nai cikin fada fada nace “wallahi cilla in baxa ka rage shan sigarin nan ba zamu raba hanya haba”

 

Yar da sigarin yai a kasa ya murje ta sannan ya kalle ni yana murmushi yace “afuwan aminiya ta xan kiyaye Insha Allah tun safe ban sha ba fa.”

 

Tsaki na kuma ja kafin nace “cilla so nake ka targada min Manniru dan gidan kawu nasir, yaron nan dan baya jin magana shine zai zagi Mimi”

 

Ashar ya saki yana jan kafar sa baya kafin yace “kika ce zagin shalele yai wallahi sai na karya sa don uwataii”

 

Gyada kai nai cikin takaici nace “ba sai ka karya saba kawai kasa amasa shegen duka yadda gobe ko wani ya gani zai zagi Mimi sai ya kwabe sa”

 

Murza kafa a kasa Cilla yai kafin yace “an gama aminiya ta kuma abokiyar shawara ta muje in taka miki ki karasa gida sbd yan jagaliya”

 

Jera wa mukai muna tafiya yana ban labarin yadda zai casa Manniru har muka karasa kofar gidan mu, sallama nai masa na shiga gidan, ba kowa a tsakar gidan hakan yasa na nufi palour don nasan suna zaune ynxu tunda an kawo wuta.

 

Da sallama na shiga palourn duk suka amsa min, Zama nai a gefen kafar baba ina cire hijab din jikina.

 

Kallona Umma tai tace “kin biya gurin cilla neh koh don nasan yadda kika dade din nan sai dai in kun hadu dashi”

 

Sosa keya ta nai nace “Umma a kofar gida muka hadu fa shine kawai muka gaisa”

 

Girgiza kai Umma tai tace “ni na rasa me yasa kike Kula wannan yaron wallahi sam baya ji tubarkalla”

 

Abba ne ya ce “A’a Umman Aysha ki bisa da addu’a kawai shima dana Allah ya shirye sa da dukkan zuri’ar musulmai baki daya”

 

“Ameen” muka hada baki gaba daya muka ce, mike wa nai ina fadin “sai da safe Baba gobe da school kuma ina son na fara shiga school din su Mimi”

 

Khalil ne yace “Ya Batul zan raka ki in zaki kaita”

 

Harara na sakar masa sannan na juya na nufi dakin mu nida Aysha, akan katifar mu 6 by 6 na ga Mimi tana sanye da rigar baccin ta kanta sanye da hula, murmushi nai na karasa gurin wardrobe dinmu, kayan bacci nasa na hauro kan katifar addu’a na fara ma Mimi kafin nima nayi, janyo ta jikina nai na rungume ta hawaye masu dumi suna zubo min a fuska tabbas a duniya Mimi ce rauni na ita nake kallo nake tuna *TASWIRAR KADDARAR* data same mu shekaru 5 baya.

 

Lumshe idona nai ina ina tuna abubuwan da suka faru shekarun baya lokacin ina da shekara 14 gashi ynxu ina 18 amma abun kamar ynxu ya faru……

 

 

 

**********

 

Kallon Haidar Azlan yai yana tabe jajayen lips dinsa yace “in baxa ka kaini club dinba sauke ni in karasa ai ina da kafa”

 

Girgiza kai Haidar yai yace “Azlan kayi ma kanka fada Kai ynxu ya dace ma ace kullum kana hanyar zuwa club gurin Yan mata”

 

Shafa gemun sa yai yadan lashi jajayen lips dinsa kafin yace ina ruwan Ka Mata ai abin nishadi neh kuma don naje AI ba budurcina zan basu baaaa…….

 

 

 

 

 

 

 

 

Comments Nd share plz🥹

 

 

 

 

Mrs A.M🥰❤️

[11/08, 3:01 pm] +218 92-2035171: ♠️♠️♠️♠️♠️

 

*TASWIRAR KADDARA*

 

♠️♠️♠️♠️♠️

 

 

Written by

Mrs A.M🥰

 

Page 4

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

 

Kallon Junaid Azlan yai ya saki wani killer smile sannan ya juya kansa gefe yana shafa gemun sa, girgiza kai Abie yai kawai kafin yace “wallahi Azlan kar ka kara kwana a waje in ba haka ba sai na Saba maka wallahi”

 

Lumshe idonsa yai kafin ya bude su a kan Abie din, cikin kasa kasa da murya yace “insha Allah” daga haka Abie ya mike ya bar palourn.

 

Kallon sa Junaid yai yace “me yasa baka Jin magana ne wai Azlan kai kafison kullum Ka dinga batawa Abie da Mami rai koh, ynxu sbd tsabar rashin kunya a gaban su kake cewa mace na kwanciya akan kirjina..”

 

Zakudowa Azlan yai daga kan kujerar da yake ya kalli Junaid yana kankance idonsa daya sha kwalli rambadadau don shi baya ware idonsa gaba daya shiyasa ake masa kallon rikakken dan iska, tsuke karamin bakin sa yai kafin yace “ai gani nai ba karya nai ba koh abinda kuke yi knn masu auren kullum matan ku suna kirjin ku shiyasa naga nima zan maida hankali nayi auren nan ko naji abinda kuke ji”

 

Girgiza kai Junaid yai yana kallon Azlan kawai don shikam dama tuni Azlan yafi karfin sa, mikewa Azlan yai yana gyara wandon sa daya sassako sannan ya kalli Junaid yace “Ka gaida Mai dakin Ka ni zan wuce gurin tsoho”

 

Da ido Junaid ya bisa har ya fita kafin shima ya mike ya nufi part din Mami don yana son magana da ita akan tafiyar da yake son yi India akan matsalar rashin haihuwar sa…

 

 

********

 

Ban koma gida ba sai bayan Isha’i don Saida na gyara wa Yakumbo bangaren ta tsaf duk da ba wani datti kasancewar Yakumbo macece mai tsafta, bayan mun koma gida ban samu Umma a Palour ba nasan maybe tana daki hakan yasa nima na kwantar da Mimi da tai bacci a daki, addua nai mata sannan na fita zuwa kitchen don dora zobo na so nake nayi shi tun da daddare nasa a fridge kafin safe yayi sanyi.

 

Nida Aisha ne muka shiga kitchen din muna hada zobon muna hira tana bani labarin school dinsu fadan da akai yau akan wani saurayi, girgiza kai kawai nai cikin takaici ina mamakin yadda mata suke zubar da ajinsu da kimar su ta diya mace suna fada akan namiji, tabe baki nai takaici kamar zai kashe ni don haushi cikin saurin magana ta nace “ke ni ki daina bani labarin nan haba bakomai a ciki sai kayan takaici”

 

Dariya tai tace “dama nasan haka zaki ce ai Ya Batul don ba a gaban ki sukai damben bane ba wallahi nasan da sai kin kusa kuka kinga yadda suka yagawa juna hijab kuwa, kuma abin takaicin Wanda suke damben akansa yana zaune yana kallonsu amma ko uhm bai ce ba daga karshe ma mikewa yai ya tafi ya barsu agun irin su kashe junan nan nasu ma”

 

Cije lips dina na kasa nai cikin takaici nace “taya suke tunanin ma zai ga darajar su ita mace ai MAI DARAJA ce ynxu alal misali ko da ace a cikin su yana son wata wannan zubar da mutuncin da sukai a bainar jama’a ai dole ma yaji baya ra’ayin su”

 

Gyada kai Aisha tai tace “kuma a haka fah wai su basu yadda ba sun burge sbd sunyi fada akan abinda suke so sai hura hanci suke nidai banga karshen yadda aka kare ba na taho kar Umma tai min fada tace na dade Amma wallahi Ya Batul Allah Allah nake gobe tayi naje naji yadda ake kare”

 

Tabe baki nai nace “anan kika fi kauri ai son Jin gulma da munafurci”

 

Turo baki tai tace “ynxu ya batul nice nake da son gulmar”

 

Kallon ta nai nace “toh in bason gulma ba ina ruwan ki da son sanin yadda fadan ya kare”

 

Gyada kai tai tace “Hmm Ya Batul knn”

 

Kamal ne ya shigo hannun sa rike da leda yar madaidaiciya, kallona yai yace “Ya Batul yau tun da muka dawo daga school ban ganki ba ina ta tambayar Umma tace kina kin je babban gida”

 

Zobon dana kulla a a leda na ajiye nace ina can naje duba Manniru sai kuma na tsaya gurin yakumbo daka sani ai daka shigo gurin nata tana ta min mitar baka zuwa wai khalil ne kullum sai yaje amma banda Kai”

 

Dariya yai yace “rikicin tsufa ne kawai yake damunta Allah amma ko ranar Monday fa sai da naje na gaishe ta nine ma na kai mata abincin da Umma ta bayar a kaimata”

 

Miko min ledar yai yace “gashi inji Mansur Mai shago wai cake din ya kare nan kudin cinikin ne dubu Biyu da dari 3 shine yace na kawo miki in ba damuwa wai ki yi gobe da wuri sbd ana siya da safe sosai”

 

Karbar kudin nai na ciri dari ukun kai na mikawa Aisha naira dari, dari biyun kuma na bawa Kamal nace “gashi Kai da Khalil ku raba”

 

Godia suka fara min suna murna don dama haka nake musu in har nayi ciniki toh ina basu dari dari wannan ina ragewa Abba kudin kashewar sune tunda in na basu kudin basa tambayar Abba kudin makaranta har sai ya kare.

 

A gajiye na mike bayan mun gama jera Zobon a fridge nace “gaskia Kamal Ka fadawa Mansur ba lalle nayi cake din gobe ba, kaga gobe kamun Khadija kuma ni ta bawa In Mata cake da donut ga kunun Aya da zobo zanyi jibi na yini gaskia ba lallai wannan satin nayi cake ba kuma fa Monday zamu fara waec”

 

Marairaice fuska Kamal yai yace “Ya Batul zamu taya ki don Allah ko a cake din goben da zakiyi ki kara kayan hadin kawai sai kiyi duka hadda Wanda za’a Kai shagon”

 

Aisha ce tace “laaaa kuma haka ne basa banba sumu munzo da shawara mai kyau”

 

Harara ya sakar mata sannan ya juyo ya kalle ni yace “ko Ya Batul zamu taya ki Allah gobe Friday muna dawowa daga school in baki gama ba sai mu tayaki ko Aisha”

 

Harara Aisha ta sakar masa tace “wai sa’ar kace ni shekara biyu na baka amma Ka raina ni don wulakanci baxa ka dinga cemin Ya Aisha ba sai wani Aisha kana ganin yadda Khalil yake cemin duk zai kira ni sai yace Ya Aisha Amma Banda kai banza mara kunya”

 

Zai yi magana na janyo hannunsa na tura sa palour nace “wuce muje toh ka taya ni duba abinda Banda Shi na cake din sai Ka siyo min tunda ga kudi sun shigo”

 

Shiga palour mukai yana fadin “me yasa baki ce su Khadijan su baki kudi ba kafin ki musu Ya Batul”

 

Dariya nai nace “kawai na fison sai na gama maka abinka tsaf in kazo dauka Ka ban kudina cas kaga wannan kudin da aka ban zan ware ribata nasa a banki ragowar kuma na kara siyo kayan flour”

 

A Palour muka zauna muna lissafi har Abba ya shigo gidan anan aka hau hira kowa na bada labarin abinda ya faru daya basa mamaki ko wani Abu da yai Wanda Abba zai gyarawa mutun yai masa in na fada ne yayi, haka muke muna da fahimtar juna sosai mun dauki iyayen mu matsayin aminan mu da ba wani sirrin mu da muke boye musu shiyasa ko lokacin da KADDARA ta fada mana akan samuwar cikin Mimi sosai iyayen mu suka fahimci zancen kuma suka karbi KADDARAR da hannu bibbiyu duk irin bakaken maganganun da suka dinga ji suka toshe kunnen su har Mimi tazo duniya komai Abba ne yake mata sai dana fara Sana’a nema komai na samu akan ta nake karar da shi gurin siya mata sitiru masu kyau daidai talaka mai rufin Asiri.

 

Sai karfe 10 sannan Abba ya kashe TV yace kowa yaje ya kwanta dama haka dokar sa take tun muna kananu karfe goma kowa yake shiga daki ya kwanta sbd school sai in ranakun daba makaranta ne ma yake barin mu wataran mukai 11, dakin mu muka shiga nida Aisha su Kamal ma suka tafi dakin su dake jikin dakin mu, sai dakin su Umma dake kallon dakunan mu, koda muka shiga daki sai da muka sha hira sosai nida Aisha kafin mu kwanta bacci.

 

Washe gari da kaina na raka Mimi makaranta bayan tasa nai mata alkawarin zan koma na dauko ta da kaina, ina komawa gida na fara aikin cake dina tunda da wuta Allah ya taimake ni kafin 11 har na gama don da toaster biyu nake yi da toaster daya ce dani da aka fara bani order din cake na biki ko suna sai na tara kudina na siya wata toaster din sbd na rinka sauri, doughnut din na kwaba na ajiye a rana, hijab dina na zumbula har kasa dark blue nai ma Umma sallama na tafi school din su Mimi dake cikin Unguwar mu.

 

A compound din school din na same su itada Hidaya suna zaune suna wasa da kasa, suna gani na suka taso a guje suka taho suka rungume ni, dariya nai ina shafa kansu ina son Hidaya sbd ita kadai ce kawai Mimi mutane sun jahilci Kaddarar data same mu basa son yayansu suna kawance da Mimi duk da kuwa yadda yarinyar take da farin jini amma banda cikin layin mu don duk Wanda yasan ta yadda aka same ta kyamar ta suke banda gidan su Hidaya.

 

Riko hannun su nai sai murna suke nazo daukan su, sai da na tsaya na siya musu awara ta goma goma da ice cream sai murna suke suna tsalle, har gida na kai Hidaya kasancewar gidan su a jikin gidan mu yake mamarta ba wata babba bace Aunty Zainab tana da kirki sosai Hidaya ce yar ta kadai sai ynxu da take dauke da wani cikin.

 

Muna shiga gida wanka nai ma Mimi na sa mata atampar ta ta sallah powder da kwalli na samata sai vaseline dana shafa Mata a lips dinta, dankwalin ta na daura mata, abincin da Umma ta dafa na Rana na zuba mata na koma gurin aikin doughnut din da nake, kafin karfe 2 na gama doughnut din na ajiye a gefe, kafin na mike daga gurin kanwar Khadija da yayar ta suka shigo, gaisawa mukai bayan sun gaishe da Umma, a tare muka kirga cake da doughnut din sai da na tabbatar ya cika iya adadin Wanda suka ban na jera su a cikin kwali, dubo Goma Yayar Khadija ta miko min tace “ga kudin nan Batul mun gode sosai sai gobe insha Allah kinsan yini da wuri ake yi don Allah kafin karfe daya muke son zobon da kunun Aya.”

 

Karbar kudin nai na mikawa Umma sannan nace “Insha Allah zaku samu da wuri sai dai ku kawo kulolin da zan sa zobon a ciki tunda kinga sai na zuba kankara akai yadda zasuyi sanyi koh”

 

“Insha Allah goben da safe za’a kawo mun gode sosai”

 

Kati ta mika min guda biyu tace”gashi na kamun ne karfe 4 ne za’a yi don Allah kuzo keda Aisha”

 

Kallon Umma nai ganin bata kallona ma yasa na karba nace “zan Kira Abba na tambaye sa in ya bari mai zai hanani zuwa”

 

Har kofar gida na raka su sannan na shigo na gyara gurin Aisha da dawowar ta knn ta tayani muka kintsa inda na bata, cake din da nai na zuba a Bokitin fenti na ajiye a gefe ina jiran khalil ko kamal wani ya shigo na basa ya kaiwa Mansur, Zama nai gurin Umma muna lissafin yadda za’a yi da kudin sai murna muke sbd wannan ne order da aka taba bani mai tsoka ragowar duk basa wuce na 5k koh 7k Amma ynxu gashi 10k zuwait ga gobe ma Insha Allah zan musu zobo da kunun Aya na 5k.

 

Kasancewar inada banki da nake tara kudi kodan university din da nake son shiga in na gama waec, sbd na ragewa Abba wani abun yasa Umma yanke shawarar a ajiye 10k din duka a bankin nawa,

 

Kallon Umma nai nace “a’a Umma keda Abba kudai dubu biyar kusa albarka ko Umma”

 

Girgiza kai tai tace “A’a basai mun dauka ba ke da kike Tara kudin ki”

 

Damun Umma nai dole sai da ta dau 2k tace “zamu raba wannan nida Abban naku Allah ya karo kasuwa mai albarka yai muku albarka gaba dayan ku”

 

Nida Aisha muka hada baki gurin fadin “Ameen Umma”

 

Wayar Umma na karba don kiran Abba na gwada tambayar sa zuwa bikin Khadija ko Allah zai sa ya barmu

 

 

 

*********

 

Gyara zaman sa yai yana kallon Baffa yace “toh kai tsoho meye damuwar ka da aure na”

 

Kallon sa baffa yake yana gyara zaman glass din idonsa yace so nake kaima kayi aure kamar yadda da uwan Ka yai kana kallo dai shekarar Dan uwanka biyar da aure amma kana zaune Kai baka da aiki sai zuwa gidan casu kuna juya mazaunai”

 

Murmushi Azlan yai har saida jerarrun hakoran sa suka bayyana yace “tsoho kaima fa Ka iya vawulence fah ynxu meye na cewa mazaunai”

 

Salati Baffa ya saki yace “ynxu Azlan nine na iya vawulence din”

 

Gira daya ya daga yace “yesss tsoho”

 

 

 

 

 

 

 

Comments are share plz

 

 

 

 

Mrs A.M🥰

[11/08, 3:01 pm] +218 92-2035171: ♠️♠️♠️♠️♠️

 

*TASWIRAR KADDARA*

 

 

 

 

Written by

Mrs A.M🥰

 

Page 3

 

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

 

Assalamu alaikum Fans ina muku albishir din mai da Book din Taswirar kaddara free Book, Allah y bar kauna🥰

 

Tsaki Haidar yai yace wallahi gaba dayan Ka dan iska ne, ynxu kai sbd takadari ne baka da aiki sai maganar budurci daga anyi magana sai kace kana tattala budurcin Ka.

 

Dage gira daya Azlan yai kawai yana tsotsar lips dinsa hayaniyar ta ishe sa shiyasa kawai yaja bakinsa yana tsotsa, kallon sa Haidar yai ganin yana tsotsar lips dinsa hakan ya nuna masa cewa baxai sake magana ba kuma yan miskilan cin sun hawo knn, shima Jan bakin sa yai yai shiru ya maida hankalin sa kan titi.

 

Tafiya mai dan nisa sukai kafin Haidar yai parking motar juya wa yai ya kalli Azlan daya kwantar da kansa a jikin kujerar motar yana gyada kai a hankali, bai yi magana ba sai bude motar yai kawai ya sauka ya tafi don tarar Keke napeo ya mai da shi gida.

 

Sai da Haidar ya fita tukun ya bude idonsa a hankali yana lasar lips dinsa, fitowa yai ya shiga gurin driver sit yana tabe baki, a guje ya fisgi motar yana sharara gudu a hanya ikon Allah ne kawai ya kaisa club din lafia.

 

Parking motar yai a cikin katon compound dn club din tun daga yanayin motocin dake fake a gurin zaka San cewa club din sai wane da wane ne suke zuwa gurin, cikin tafiyar sa ta jarumta ya nufi cikin club din dake tashin Kida kamar zai tsage ginin Amma su wadanda suke ciki ba abinda ya dame su harkokin su kawai suke…….

 

 

 

************

Da safe ina tashi bayan nai sallar asuba wanka na shiga nai ina fitowa Aisha ta shiga itama don da asuba dukan mu muke wanka, bayan na shafa mai doguwar riga na zira na fito kitchen gas na kunna na dora ruwan tea don hakan ya zamar mana al’ada kullum sai mun sha tea da safe.

 

Ina gama fada tea din na juye a flask doya na dafa mana fara na dauki ragowar miya dake fridge na dumama, sai da na gama duka na kai palour sannan na shiga daki don dauko Mimi nai mata wanka.

 

A zaune na same ta tana hamma sai murza idonta take alamun ynxu ta tashi, murmushi nai da ya fito da wushirya ta na karasa gurin ta zama nai akan katifar mu na janyo ta jikina, cikin kaunar ta da baya boyuwa a fuskata nace “Morning My baby”

 

Murmushi tai dimple dinta na gefen kumatun ta na dama yana lotsawa, kwantar da kanta tai a jikina tana fadin “Good Morning MAA dita”

 

Dariya nai na girgiza kai ganin in na tsaya biye mata zamu iya makara yasa na mike na cire mata kaya, towel dinta na sa Mata naja hannun ta zuwa toilet dinmu dake tsakar gida, wanka nai mata kafin na bata ruwa na sata tai alwala.

 

Daki muka shiga na shirya ta cikin uniform dinta Riga da wando light blue sai karamin hijab dinta dark blue, socks na sa mata muka fito Palour karya wa mukai muna yi muna hira har muka gama na sa mata takalmin ta, Nima daki na shiga na shirya cikin uniform dina ringa da wando sai hijab Wanda ya kusa zuwa min har gwiwa ta, jaka ta na rataya na dakko ma Mimi jakar ta itama.

Ina fitowa naga Abba da Umma a zaune suna Shan tea gefensu su Khalil ne a zaune Suma suna karyawa, gaishe su nai na janyo Mimi ina samata hijab dinta, kallon Abba nai nace “mun tafi Abba”

 

Murmushi yai cike da dattako yace “ynxu dai sai kin je makarantar su Mimi din”

 

Turo madaidaicin baki na nai gaba nace “Abba in ban je ba haka malamar nan tasu zata dinga ma Mimi maganar meye ma’anar sunan da take using gwanda naje nai reporting in ba haka ba tun Mimi bata damuwa har sai abin ya soma damun ta tunda ynxu tace har classmate dinta sun fara tambayar ta Suma”

 

Daga kai yai yace “kuma hakane amma bar ya ni sai naje na musu magana kinga kema student ce ba lallai su baki wani muhimmanci ba amma In suka ga babba yaje zasu fi saurara koh”

 

Murmushi nai ina sakin hannun Mimi nace “Haka ne Abba Allah ya kara arziki da wadata ya Kara muku lafia”

 

A tare suka amsa da Ameen, sunkuya wa nai nayi ma Mimi kiss a kumatun ta sannan na mike na fita don na kusa makara ma karfin hali ne irin nawa kawai yasa ni cewa sai na fara raka Mimi school din su don na fara gajiya da tambayar da Aunty dinsu take mata akan meye ma’anar sunan babanta sbd tana Amfani da Khadija B ne a school shine Auntyn su kusan kullum sai ta tambaye ta meye B din yake nufi, ni kuma inaso naje na yi reporting wa headmaster dinsu tunda ai ba dole ne sai ta san ma’anar B dinba…

 

Ban dawo ba sai karfe 4:30 na yamma a gajiye na shigo gidan jakata a hannu na saukin tama daga yau na daina zuwa makarantar mun gama lesson ranar Monday zamu fara waec, a tsakar gida na samu Umma da Aysha suna hira sai Mimi dake zaune a cinyar Umma suna hira.

 

A gajiye na zauna a gefen tabarmar ina gaida Umma, a dakile ta amsa ni tana kauda kanta gefe, hannu nasa na tallafo kumatuna ina kallon ta kafin na kalli Aisha dake dariya tana kauda kanta.

 

Marairaice fuska nai nace “Ummana me kuma nayi ko Aisha ce ta hada min bom a gurin ki don taga bana nn”

 

Dariya Aisha tai tace “ba ruwana wallahi Ya Batul dazu ne aka aikowa Umma wai Manniru ba Shi da lafia machine ya kade sa ya samu targade a hannu shine fa Umma tace tasan aikin cilla ne kuma ke kikasa Shi yai ma Manniru targade tunda an hana kisa a karya sa”

 

Zaro madaidaitan idona nai nace “Umma ni kuma ina ruwana da wani Manniru ai kince kar nasa a karya sa kuma Umma ai Shi Mannirun bai ce cilla bane naji Aisha tace machine ne ya kade sa”

 

Kallona Umma tai kafin ta girgiza kai tace “Allah ya shirye ki in kin huta sai ki leka ki duba sa don dama Yakumbo tana min mitar ynxu kin dena leka ta”

 

Dariya nai nace “Ameen Ummana anjima sai na leka din Insha Allah”

 

Janyo Mimi jikina nai ina fadin “babyn wace wannan” dariya ta kalkale da shi da suka fito da jerarrun hakoran ta tace “babyn Maa ceh”

 

Murmushi nai ina jan kumatun ta daga kanta nai daga cinyata na mike don zuwa watsa ruwa gashi yunwa nake ji sosai, bayan nai wanka na chanja kaya dama nayi sallah a makaranta, kitchen na shiga na zubo shinkafa da wake nasa salad akai, Kan tabarma na zauna ina ci muna hira da su Umma har na gama, wanko hannuna nai na shiga daki nasa Hijab dina har kasa, hula na Sawa Mimi na shiga palour na dakko wa Yakumbo robar zobo guda daya da robar kunun ayar da nake na siyarwa, don Alhamdulillah ina Sana’a ta daidai gwargwado ina siyar da zobo da kunun Aya Allah yamin baiwar iya hada zobo da kunun Aya sosai shiyasa nake na siyar wa kuma Allah yasa ma abin albarka ana siya sosai wasu ina zubawa a roba wasu ina kullawa a leda har fridge Dan karami ne dani Wanda Abba ya siya min nake sa kayan zobo na a ciki, ga kuma cake ina yi shima don na iya sarrafa flour.

 

Fitowa nai hannuna rike da ledar dana Sama Yakumbo zobo, hannun Mimi na rike mukai ma Umma sallama muka fita daga gidan, cikin nutsuwa muke tafiya muna hira da Mimi tana ban labarin school dinsu har muka karasa Babban gida, ba nisa tsakanin mu da gidan a farkon layin mu gidan yake.

 

Muna Kiran sa babban gida ne sbd family house ne anan Yan uwan Abban mu suke zaune da matansu, muma da a bangaren da Yakumbo take ynxu anan muke da Zama da lokacin da nake da shekara goma Abba ya bar gida sbd sam Umma bata Jin dadin zama a gidan sbd Uwani matar Kawu Nasiru da kuma Hama matar Kawu Kabiru, su uku yakumbo ta haifa Kawu Nasiru ne babba sai Abba sai Kawu Kabiru.

 

Da sallama na shiga dogon soron gidan ina hade fuskata direct bangaren Kawu Nasiru na nufa hannu na rike da na Mimi, sallama na karayi a kofar bangaren nasu da ba kofa, shiga nai a tsakar gida na gansu zaune a kan tabarma Manniru yana kwance daga shi sai dogon wando, hannayen sa an dora akan pillow, a tsaye na tsaya ina kallon uwani dake bina da wani mugun kallo, Nima kallon da take min shi nake mata kafin na dauke kaina a kanta na maida kan Manniru da yai kalar tausayi, karkace kaina nai nace “ya jikin naka ashe hatsari Ka samu ALLAH ya kiyaye gaba”

 

Cikin rawar murya yace “Ameen Ya Batul” kallon Mimi yai yace “Mimi ba magana”

 

Murguda karamin bakin ta tai tana fari da ido tace “ai dukana kake yi wani lokacin shiyasa baxan ma sannu ba”

 

Karya wuya yai yace “baxan sake ko hararar ki ba Mimi ai ni ynxu kin zama kanwata ko Baki so na dinga siya miki alawar madara”

 

Washe kananun hakoran ta tai zatai magana na katse ta gurin fadin “Allah ya kiyaye gaba Uwani” daga haka naja hannun ta muka fita daga sassan zuwa sassan Yakumbo.

 

A Palourn ta muka same ta tana zaune a kasa ta mike kafafun ta da dukkan alamu iska take sha duba da rigar dake jikinta, anan muka shantake da hira don jinin mu yazo daya sosai da yakumbo duk cikin jikokin ta munfi dasawa da ita muyi fada muyi dadi haka muke lokacin da muke babban gida yawanci a dakin ta nake kwana ma sai da muka bar gidan sannan na rage zuwa gunta sbd Umma bata son muna yawan fita…

 

 

 

***********

 

Kallon Abie yai kafin ya lashi jajayen lips dinsa yace “A gidan su Haidar na kwana”

 

Cikin bacin rai Abie yace “ban hanaka amma kwana a waje ba na fada ma ba so daya ba ba so biyu ba duk daren da kai Ka tabbatar Ka dawo gida Ka kwana a gida”

 

Karkatar da kansa yai yace “Amma abie Shi Junaidu ai a waje yake kwana daki daya da mace ma watakila ma a kirjin sa take kwana me yasa shi baxa kace masa ya dawo gida ya kwana ba”

 

Sunkuyar da kai Junaid yai cikin tsananin kunya baisan yaushe Azlan zai nutsu ya daina iskanci ba.

 

Girgiza kai Abie yai duk da shima maganar Azlan din tasa shi jin kunya amma kuma ya saba da yanayin maganar sa haka yake bashi da kunya.

 

Girgiza kai Abie ya kuma yi yace “Ka fara mantawa cewa Shi Junaid yana da aure koh Kai kuma gwauro ne dole zai kwana a gidan matar sa kai kuma tunda baka da matar ai sai Ka kwana a gidan ubanka koh”.

 

Dage gira yai kafin yace”nima aure xanyi na dinga kwanciya akan kirjin matata kawai” ya fada yana lumshe idonsa.

 

Mikewa Mami tai kawai ta shige dakin ta tana girgiza kai lokaci daya tana murmushi.

 

Kallon Junaid Abie yai yace duba min yaron nn ko ya sha wani Abu kafin ya shigo gidan nan…..

 

 

 

 

 

 

 

 

Comments Nd share plz

 

 

 

 

 


‚Äč


Name: [My Novels (www.mynovels.com.ng)]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na TelegramPowered by: www.mynovels.com.ng

Mrs A.M

Leave a Reply

Your email address will not be published.