Hausa Novels

Tattalin So Complete Hausa Novels

Tattalin So Complete Hausa Novels

************************

 

More Novels at https:/mynovels.com.ng

 

************************[8:06AM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞TATTALIN SO-1  PG-1    Kanal Aliyu Gwarzon jarumin soja kenan, Alhaji Yahuza shi ne mahaifinsa, matansa biyu da ‘ya’ya biya. Hajiya Habiba ita ce uwargida, da ‘ya’yanta uku. Aliyu shi ne babba, sai Sani da Sa’adiya. Sai Hajiya Talatu me ‘ya’ya biyu, Ni’ima da Hamza. Dukkaninsu kansu a hade ya ke, da ya ke sun sami tarbiya sam babu yan ubancin nan bare nuna banbanci a junansu. Alhaji Safiyanu kanin Alhaji Yahuza ne, uwarsu daya ubansu daya, matarsa daya Hajiya Saude, da ‘ya’yansu uku, maza biyu Faruq da Sadiq, sai karamar su mace mai suna zainab. Babban gida ne kowanne da bangarensa, gaba dayansu akwai kyakkyawar dangantaka da son juna a tsakaninsu. Mahaifiyarsu Hajiya Babba, ita ma a gidan ta ke bangarenta daban. Dattijuwar arziki ce me addini da ibada, ga ta da kokarin zumanci, du inda ta ji dan’uwanta wanda ko kaka dangantaka ta hada su, sai ta jawo shi jikinta ya ci arzikinta da na ‘ya’yanta. Hajiya kyaftin kenan dattijuwar arziki, ko yaushe jikokinta suna tare da ita tana hada kawunansu, tana yi musu nasihohi da tattausar murya, ta rinka yi musu tarihin Annabawa da abubuwan da ta san za su karu dasu, su kara samun fahimta ko da a makaranta ne.

[1:15PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**2

 

Yace, kai hajiya, kin matsanta min da maganan auren nan, wai ke bakya kishina ne?

Tace ni ai indai akan wannan ne banayi, ka samo min abokiyar zama, idan kuma kai bazaka iya ba ni na samo maka.”

hajjaju kenan, za’a nemo in Allah ya yarda. Tace dakai wani ne saika samo a hadaka da ‘yar uwarka sadiya, tunda kaga ansa rana data yi candy za’ayi aure insha Allahu.”

yace kai hajiya, kedai kina son hada sabgata da yaran nan so kike su rainani ne?

Tace, “ai kaji sha’anin naka, sai son girma kamar gyambo, yo meyesa baka nemo tuni kayi ba? To bari kaji na fada maka, ko ka nemo yarinyar da kake so ayi auren kafin bikin sadiya, ko kuma ayi auren lokaci daya da sadiya.”

Ni da Yaya Arman Hausa Novel Complete

yamike yana dariya, “hajaju kenan, kin taba ji anyiwa namiji auren dole? Tace za a fara shi kuwa daga kanka.”

hajiya dai da gaske take lamarinta, don ta matsu taga Aliyun yayi aure, tana so ya kara samun daraja da mutunci a gun iyayenshi, saboda Aliyu yaro ne nutsatse mai hankali da nutsuwa, yana da biyayya. Du abunda iyayensa suke so shi za yayi.

Du da karancin shekarunsa yanada halin ya kamata, shiyasa ya zama abokin shawarar iyayensa.

Karfe shidda na yamma direba ya kwaso ‘yan makaranta tun safe. Da yake zainab a firamare take, karfe daya ake tashinsu, to saita shiga lesson na awa daya, karfe biyu take fitowa sannan antashi su sadiya da ni’ima da suke ‘yan sakandare. To sai suyi sallah direba ya kawo musu abinci suci, sai kuma shiga islamiya data ke duk a cikin makarantar. Karfe hudu zasu fito sallar la’asar, suyi dan ciye-ciyensu su kuma komawa aji, sai karfe shidda za’a tashesu suyo gida.

Yau direba yana tsayawa zainab ta bude ta fito tayi bangarensu, kicin ta nufa don tasan mamanta tana kicin ita da ‘yan aikinsu don gudanar da girkin dare.

Hajiya saude ta tari ‘yarta da murna tana cewa, “sannu da zuwa auta.” ta rungumeta suna dariya ta cika uwar tata ta nufi firiji tana cewa, wallahi mama yunwa nake ji.” ta bude firij tace kai mama ina vanilla ice-cream dina?

Mama tace a’a zeey bana son rigima, ba tun jiya kika gama shanye naki ba?

Tace “to mama bana sa ragowar dayan a firij ba.” tace to ai kuwa dashi sadik ya tafi makaranta da safe.

Zainab tanajin haka ta yarda jaka ta hau tsalle da ihu tana kuka, “wallahi saiya biyata ice-cream. Faruk da sadik suka shigo duk da goyon jakunan su, suma nasu direban ya dauko su, don makarantar matan daban ta mazan daban aka sakasau.

Tace “wai ice-cream dinta tasa a firij waye ya daukar mata a cikinku. Faruk yace “mama ai sadik ne ya tafi dashi makaranta.”

sadik yace ai banaki bane ragowa ne na dauka da zaki kama yiwa mutane kuka.”

tace “to bani nasa shi a firij ba kaje ka dauka min ba, wallahi sai biyani abuna.” taci gaba da kukanta tana tsalle. Aliyu yana dakinsa ya ringa jiyo ihunta, ya shigo da sauri yana cewa lafiya?

Me akayi mata mama? Tace rigimar data saba ne kawai, ice-cream ne du sunsha roba dai-dai, ragowar daya ne wai ta dauka tasa a firij shikuma dan uwan dayan abokin yin nata ya dauke ya tafi makaranta dashi ya shanye, shiya kawo wannan rikici nata.” ya daka mata tsawa, “tashi zaune.” ta mike a razane tayi daki da gudu. Dai-dai lokacin ni’ima take shigowa take cewa “wallahi yaya ko abinci bata ci a makaranta ba sai youghot me sanyi ta rinka siya tana sha wuni guda, yaya sadiya tai ta mata fada ta kwace youghot din ta siyo mata meat pie da yambos, saida taga zata daketa sannan taci.

Aliyu yace a’a ba akai muku abinci bane?

Tace, “ankai mana mana, bata cin abinci sai kayan zaki dana sanyi take sha.”

ya kwada mata kira da karfi, “zainab kina ina? Ta fito daga falon da sauri ta rabe a waje daya. Yace maza ni’ima shiga kicin ki zubo mata abinci ina zaune ta cinye shi.

Ni’ima ta zubo mata abinci ta dire a gabanta, Aliyu ya daka mata tsawa dauki ki cinyeshi. Taja filet din ta fara cin abincin, tsoronsa take ji sosai, don tasan baya wasa.

Yace ki cinye shi du idan kika rage ko kaka nida kene. Ya juya ya fita, ya sami direba a waje ya bashi dubu biyar, yace yaje bakori ya siyo masa ice-cream da youghot masu sanyi, da gashashiyar kaza guda biyu.” ya wuce dakinsa. Zainab kuwa tana zaune tana kuka tana tura abincin, saida ta cinye tas sannan ta tashi tayi daki ta kuka, me aikinsu ta bita tana rarrashinta, ta hada ruwa a baho, ta cuda ta sannan ta kyaleata ta karasa wankan da kanta ta dauro alwalar sallar magariba, tana cikin shiryawa taji sallamar direba da yake kaisu makaranta. Mama ta amsa masa, ya shigo ya durkusa yace, “gashi mama inji yaya Aliyu, na zainab ne.

Maman ta karba tana budawa, tace “Aliyu kenan, ai shine ma ja gaban sangartar da zainab, don daman can shiya koya mata irin wannan cimar bata damu da abinci ba, gashi ta fara girma abu yana nema ya zame mata jiki.

ta kwala mata kira, ta fito da sauri tana cewa “mama me yayan ya kawomin. Ta tura ma kayan, gashinan ‘yar lelen yaya. ta fito ta kama dubawa, robar yght guda shida, ice-cream guda shida, gasassun kaji guda biyu, ta dauki robar ice-cream da nono dai-dai ta saka a firij, tace wlh mama kada ki bari sukuma daukar min.

 

surayya

[1:16PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**3

 

MAMAN ta bata kaza daya da youghot guda uku, ice-cream guda uku, gashi nan saii tafi gidan hajiya ki hadu keda ‘yan uwanki mata da mazan tunda suna can kuci, wannan kuma in na nashiga wajen su hajiya cin abinci maci acan.”

zainab ta dauki ledar tayi bangaren wajen hajiya, ta shiga da sallamarta, ni’ima ta tarota tana dariya tare da cewa, “sai ‘yar gidan daddy, me kika samo mana.

Tace, “ai bazaki ciba tunda kika sa aka sani cinye abinci.” tace haba yi hakuri ‘yar kanwata, kinsan tsakaninmu bata baci.”

sadiya ta karbo kayan tace, bawanin kunyi fada da ita dani take shiri.” gaba daya suka hadu suna cin kazar da youghot din da ice-cream din. Ahaka Aliyu ya shigo ya sami kujera can nesa dasu yana duba jarida. Zainab tasa jummai mai aikinsu ta dauko mata jakarta ta islamiya tana son yin hadda, don gobe malaminsu yace su zo masa da haddan Arrahaman izu bakwai.

Ta bude Qur’ani ta bawa hajiya, tace hajiya rikemin nayi hadda, gobe malam yace muzo masa da hadda, du wanda bai iya ba zai sha bulala.

Hajiya ta rike mata Qur’ani ta fara karanto Arrraman cikin kwararen larabci irin wanda ake koya musu a islamiyasu, da yake tana da zakin murya, gashi ta iya fitar da kowane harafi, ta iya rera karatun da kome kake yi in kaji saika tsaya ka saurareta.

Aliyu ya lumshe ido yana mai jin dadin karatun nata, a ransa kuwa fassara suran yake yi yana fasalta mata ‘yan aljannan da Allah ya yiwa rahama. Tana kaiwa karshen suran tace Alhamdulillah, na haddace a kaina.”

hajiya tace “barakallahu fik, kin wuce dukan malam.” hajiya tace shiyasa nake sara miki mutuniyata

shagwabarki bata damuna tunda akwai ki da kwakwalwa mai kyau, du abunda aka gaya miki kya dauke shi a kanki.

Sadik yace “iyayi dai da neman suna wai ita ace mata mai ilimi.”

zainab tace toh ilimi karyane? Ai ilimi shine kan gaba a rayuwar dan Adam. Ilimi lallai ne mace ya kasance tana kula dashi, ilimin addinin ta da kuma ilimin rayuwa.

Misali, bari na baka misali da kowanne. Ilimin addini don tasan yadda hukunce-hukunce sallah, tsarki, jinin al’ada, jinin biki da dai sauransu.

Ilimin rayuwa kuwa, don kanta ya waye ya kasance tasan abunda yake faruwa a duniya, koda ta sauraron ko radiyo, kada ace mace bata san sunan gwamnan garinsu ba, ko shugaban kasa. Kinga akwai karancin wayewa a wajenki kenan.

Ilimi wani abune da yake karawa mutum daraja, Allah mai girma da daukaka yace “Allah ya shaida lallai babu abun bautawa da gaskiya sai shi.” kuma mala’iku ma’abota ilimi sun shaida yana tsayar da adalci mabuwayi mai hikima. Kaga saboda muhimmacin ilimi a wannan aya, sai Allah ya ga hada shaidarsa data mala’iku da kuma ta masu ilimi.

Ashe du wanda ba malami ba, ba kuma mai neman ilimi ba, toh bai cika cikakken mutum ba. Haka kuma annabi ya fada acikin wani hadisi, “duk wanda Allah yaso shi da Alkhairi, saiya fahimtar dashi Addini.” haka kuma yana cewa, “neman ilimi farilla ne akan kowane musulmi namiji ko mace.

Kuma Darajar farko idan ance ilimi shine ilimin addinin musulunci,sai kuma ilimi na rayuwa, kamar su ilimin likita, injiniya, siyasa, mu’amala da dai sauransu.

Daraja da kimar ‘ya mace tana karuwa gwargwadon yadda ta kula da iliminta, kamar kuma yanda darajar da kimarta take lalacewa a wulakance sakamakon yanda taki yin ilimi.”

mace ta gar itace wadda kunya bata hanata neman ilimi, ilimi na addini kona rayuwa. Ka duba ka gani, nana Aisha matar manzon Allah (S.A.W) du da yarinya ce karama, domin har annabi ya bar duniya shekarunta sha takwas ne, amma tayi gwagwarmaya da maza wajen haddace hadisan Annabi (S.A.W), domin itace ta hudu a cikin mutane bakwai da suka fi kowa haddace hadisai annabi acikin sahabbai.

Kaga wannan yana nuna kulawar mata da ilimi kenan.

To kada kuma yi min zargin son gwaninta ne yake sani yin karatu, a’a inason yin koyi da nana Aisha ne, don nima inaso na zama mace ma wadatatcen ilimi.

Hajiya tace Allahu akbar, Allah ya baki ikon yi.

‘yan’uwan suka sa mata dariya, tare da cewa sai auta.

Aliyu yarinyar yaji ta burgeshi, ta kara shiga ransa sosai, yanda take da kyakyawar kwakwalwa ya kamata abarta tayi ilimi mai zurfi don ta zama wani abu gaba. Iliminta ya amfani sauran al’umma.

Washe gari yaya Aliyu sammako yayi ya koma kaduna bakin aikinsa. Cikin hukuncin ubangiji sai ga mama da ciki, don ita harta fitar da ran sake haihuwa, to ta ga zainab shekara bakwai harda wata uku. Sannu a hankali hajiya tana matsawa aliyu da maganar aure, shifa ya gaya mata bashi da lokacin da zai tsaya duba matar da zai aura, ita tace “to ta nemo masa, don ita tanada lokaci.

Du da akwai gidan makocinsu Alh haruna, ‘yar gidan mansura ita take mutuwar son Aliyu, du sanda yazo tai ta shige da fice kenan a gidan, ayi masa soye-soye na kayan dadi akawo masa, amma baya kulawa saidai kannensa su cinye, hajiya ta zuba tukuici.

Duk yanda mansura taso taja ra’ayinsa don ya sota, ya rinka sauraranta bata isa ba, ko kallonta ba yayi saboda miskili ne.

Ita kuwa hajiya taga tayi tayi dashi ya samo matar da zai aura ya kasa, suka nema masa auren mansura.

 

Surayya Abubakar

[1:16PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**4

SUKA nema masa auren mansura. Alh

haruna mahaifinta yaji dadi, inda yace a

hade sa ranar data yaya sadiya ayi biki

gaba daya.”

da mansura taji wannan labarin kamar ta zuba ruwa a kasa tasha don zumudi da

murna. Shikuwa yaya Aliyu ya hakura ne

ya yarda don bashi da yanda zaiyi, tunda

iyayensa da kakansa sunfi karfinsa.

Yaya sadiya sunyi candy a ranar suka yi

fatin candy, kawayenta da ‘yan makarantar sun shayin hotuna harda

bidiyo caset don dai tarihi. Sun kakkarbi

adireshin junansu da lambobin waya,

don dai su rinka tunawa da juna suna

sada zumunci a junansu.

Satinsu biyu da candy yaya sadiya ta fara rabon katin bikinta. Inda itama mansura

ta ke raba nata katin bikin ga kawayenta

da ‘yan uwa.

Haka yaya Aliyu anbawa sani ya kai

masa katunan can kaduna, yanata

rabawa abokan aikinsa da abokan arziki. Ranar alhamis akayi kamun mansura,

ranar jumma’a akayi kamun yaya sadiya.

A ranar yaya Aliyu ya dira daga kaduna,

da wasu tawagar abokanan nasa da yayi

musu masauki a daya daga cikin gidajen

iyayensu. Washe gari ranar asabar akayi daurin

aure, gaba daya ankon galila shadda

suka matsa, da hadadden dinki yi mata

na aikin saa. Du ita suka sa, saida akaje

gidan su mansura aka dauro auren yaya

Aliyu, sannan aka daura auren yaya sadiya, daga nan maroka suka shiga

busa da kade-kade, su Alh suka shiga

rabon kudi ana watsawa maroka kudi.

Haka abokanan yaya safiyanu mijin

sadiya, sukai ta watsawa maroka kudi.

Karfe hudu dai-dai aka shirya walima, kawayen yaya sadiya da kawayen

mansura, abokanan yaya Aliyu da

abokanan yaya safiyanu, du sun ci

kwalliya ta kece raini, hadaddun ‘yan

mata gogaggu, wannan ta wace wannan,

wannan tana wace waccan, sun sha ado da kwalliya.

A harabar gidansu akayi da yake

farfajiyar katuwa ce, an kafa rumfuna

aciki an zuzzuba kujeru farare acikin

rumfar.

An ware gunda Aliyu da mansura, safiyanu da sadiya zasu zauna.

Anyiwa wajen ado da fulawoyi da roba

balan-balan, an wadata wajen da amare

da angwaye, sunyi kyau kamar fulawa

aka dasa dan kyau.

Ni’ima ‘yar shekara sha hudu ta fara zama budurwa, domin makerin budurci

har ya fara kerata. Tayi kyau ta ratso

cikin tsakiyar filin gurin da lasfika take, ta

dauki lasfikar tace, “ansuturillah.” ta fada

sau uku, jama’ar sai kowa sukayi shiru

suka zuba ido. Ni’ima ta kalli inda iyayenta suke taga

daddyn zainab da Abbansu, shigarsu iri

daya. Haka iyayen su mata duka su ukun

shiga iri daya suka yi.

Ta kalli jama’a taga kowa yayi shiru ya

nutsu ya zuba mata ido. Saita ce “muyi salati ga annabi.” gaba

daya suka ce (s.a.w).” bayan an gama

karantawa tace, “ya shafi sha biyu, Allah

ya shafe du wata fitina da zata kunnowa

ma’auratan nan.” gaba daya akace

ameen.” bayan angama tace Ayatul kursiyu kafa

uku, Allah ka karemu ga mugun ji, mugun

gani, sharrin mutum dana Aljan, da

sharrin duk wani abunki.

Allah ya basu zaman lafiya, Allah ya basu

zuri’a dayyiba saliha, Allah yasa anyi wannan aure a sa’a.

Ta cika da fatiha, ta daga hannunta tana

addu’a ana amsawa da Amin. “waman

yattikillah yaja’allahu makraja, wa

yarzurku min haisu lah ya tasiri, waman

tawakal alallahi fa huwa hasbun, innallaha baligul amri kadija’Allahu li kulli

shai’in kadira. Amin.

Yayinda kowa ya shafa.

Tace to Alhmdllh, jama’a muna yi muku

barka da zuwa, mungode da hallartat

taronmu da kuka yi don ku taya mu murnar auren ‘yan uwan mu.

Bari na kira muku autarmu dan tazo tayi

mana ‘yar fadakarwa kadan kafin

malaman namu da zasu yi wa’azizzikan

su gama karasowa, tace “zainab zeey

daddy bismillah.” zainab ‘yar shekara takwas ta taso cikin

nutsuwa tana murmushi daya karawa

fuskarta kyau, tana sanye da dan dan

datsetsen yelow les da yake ta walwali,

dambara-damran dutsuna ajiki kamar

madubi, tasa gwagwaro yelow, ta yafa dankwalin les din. Tasa fashion azurfa

mai yalayen dutsuna wuya da kunne, da

zobensu, tasa warwaraye suma yaleye.

Yarinyar tayi kyau sosai, tsarin kwaliyarta

kamar wata babba. Shiga iri daya sukayi

da ni’ima komai da komai. Ni’ima ta mika mata lasfikar suna yiwa

juna murmushi, yayinda masu hotuna

suke basu flasha, masu filet din dvd da

cd suke ta dauka, ni’ima ta koma wajen

zamanta, zainab cikin zakin muryarta

tace “Aslm ‘yan uwa musulmi.” gaba daya kuwa suka amsa mata da “wslm.

“hakika ina taya ‘yan uwana murna da

wannan rana ta aurensu, Allah ya basu

zaman lafiya dauwamamme, yaya sadiya

da aunty mansura, yanzu Allah ya kaiku

wani matsayi da rayuwarku zata canja ba kamar sanda kuna gida ba. 1- abu na

farko da ake so ‘ya mace ta gane ta

fahimceshi shine, hakkin mijinta akanta,

ta gane cewar miji shine shugabanta, ta

rinka jin hakan a ranta.

Saboda Allah ubangiji yace, maza masu tsayuwa ne da shugabanci a kan mata,

kuma maza suna suke da fifiko wajen

girma da daraja akan mata.”

wadanan dalilai su zasu mace ta dinga

jin cewa, namij fa shugabane, kuma ta

dinga jin haka a jikinta, kuma tasan yana da hakki akanta, domin tasan bazata fita

ba saida izninsa, kuma duk inda zata je

saita san ransa bazai baci ba.

Manzon Allah (s.a.w) ya fada a cikin

hadisi ingantacce

[1:17PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**5

 

YA fada acikin hadisi ingantacce, saboda girman hakkin miji akan matarsa, “da za’a umurci wani yayi sujjada ga wani, dana umurci mace tayiwa mijinta sujjda. Koda miji zai bukaci amfani da matarsa, ita kuma tana kan sirdin rakumi, to kada ta hanashi.

A wata ruwayar ta bukhari, manzo Allah (s.a.w) yace, “idan mij ya kirawo matarsa zuwa ga shimfidarsa ita kuma taki har ya kwana yana fushi da ita, to mala’iku zasuyi ta tsine mata har sai an wayi gari, bukhari ne ya ruwaito.

Idan mace ta gane hakkin miji akanta, kuma tayi masa da’a akan abinda ba sabon Allah bane, to hakan zai taimaka kwarai wajen gyara zuciyarta.

2- abu na biyu shine amana, anaso mace ta zamo mai amana bata  cikin abunda ya shafi dukiyarsa, kuma bata ha’ince shiba akan karan kanta.

Ha’intar miji wajen dukiyarsa daukan wani abunsa batare da iznin sa ba.

Ha’intar miji aka karan kanta kuwa, shine ta bada kanta ga wani namiji. Ko kuma tayi kawance da mijin da banata ba. Du matar kirki bazata yi haka ba.

Toh macen kirki itace wadda bata ha’intar mijinta daga dukiyarsa ko kuma akanta. Salihan mata masu da’a ne ga mazajensu, masu tsare mutuncinsu ne da dukiyoyin mazajensu, basa ha’intar mazajensu alokacin da basa nan.

Manzon Allah (s.a.w) ya fada cewa babu yanda za ayi mace ta dauki wani abu a dakin mijinta ba tare da izninsa ba, to bai halatta ba,

sai sahabbai suka tambayi annabi cewa “ko abinci ne? Sai annabi yace “wannan shine mafi daraja acikin dukiyoyin mu, ba a yarda mace ta dauki abincin mijinta tayi kyauta dashi ba.

 

Kuyi hakuri plz yau bazan samu daman pstn ba, wannan wanda nadan soma rubutawa jiyane, amma gobe insha Allahu zanyi muku 3 times pr day, kuyi hkr

[1:17PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**6

 

BA AYARDA mace ta dauki abincin mijinta tayi kyauta dashiba saidai in dafaffe ne in tayi, gudun kada ya lalace, to sai a sadaukar dan gudun kada ya zamo almubazaranci. Shima idan miji ya dawo saiki sanar masa, ko gidanku zaki aika da abinci saiki sanar masa, bare ki bawa wani can daban. Wannan yana cikin cin amanar miji.

Manya mutane suka rinka mikewa suna yiwa zainab kyautar kudi, saboda yanda yarinya karama ta burgesu, Abba da daddy sai washe baki suke yi don jin kokarin ‘yar tasu da kwazonta.

Mamanta kuwa tayi hamdala acikin ranta, tana mai jin dadin baiwar da Allah yayi wa ‘yarta tun tana karama, kowane tebir mutum hudu ne a zagaye dashi, akayi umurni da masu sabis su fara rabon abinci, shinkafa ce fara da taliya itama haka, sai soyayyun kaji da gasashen nama, sai mitfy, samosa, sopringros, haka kowa za a tsira katon filet a dire a gabansa, mata masu wa’azi sun zo, wajen yayi shiru an nutsu ana cin abinci, yayinda aketa kwararo wa’azi akan zaman aure ga ma’aurata.

Washe gari akayi yini, ranar litinin akayi fati, a ranar kuma aka kai amare dakunansu. Burin mansura ya cika, yau ta auri gwarzon namiji cikakke, wato Aliyu.

Tasan sarai Aliyu miskili ne bai fiya

wasa da dariya ba, shi hasalima magana wahala take masa yi masa, don inzaka daka ta tashi sai dai kuyi ta zaman kurame dashi.

Aliyu mutum ne mai tsafta, dan gayu ne mai son kamshi, baya damuwa du tsadan turare zai saya indai kamshin shi yana da dadi. Aliyu yana ji da kansa, akwai iya jan aji, yana da tsananin iyayi da gwalli kamar mace, ya fiya kasaita da son girma kamar wani basarake.

Washe gari ranar talata gajiyar biki bata bar ni’ima da zainab zuwa makaranta ba. Tun asuba da aka tashe su suka yi sallah, suka sake komawa gado suka nade cikin bargo suna bacci. Karfe bakwai masu aikinsu sukayi ta tashinsu don su shiry su tafi makaranta, amma du sunki tashi.

Dole sai rabuwa suka yi dasu.

Karfe goma dai-dai Aliyu ya shigo gidan don gaishe da iyayensa. A farfajiyar gidansu mai gadi da direbobi suna ta risinnawa suna gaisheshi. Aliyu ya cewa malam idi direba, “ina ‘yan makaranta , i ce kodai basu makara bako?

Malam idi yace ai basu fito ba, yau ban kaisu makaranta ba.” a zuciye Aliyu ya shiga gidan, kafa kawai yasa ya daki kofar ta bude garam.

Ni’ima da zainab suka tashi a firgice, suna mitsike ido. Suna dago kai suka ganshi. Kafarshi daya akan gadon, dayar tana kasa, fuskar nan tayi kirtif da ita kamar bai taba dariya ba.

Zumbur suka mike suka diro kasa daga gadon, suka durkusa can nesa dashi, suka kama cewa “yaya ina kwana? Bai amsa musu gaisuwar ba, sai tambaya daya jefo musu cewar “meya hanaku zuwa makaranta? Gaba daya jikinsu ya hau bari suna in’ina da kame-kame abunda zasu ce, ya daka musu tsawa “ku tashi ku saka uniform dinku, ina jiranku a falo.” suka mike da sauri kowacce ta nufi kwaba. Shikuma yayo falonsu yana tsaye. Mintuna kadan suka fito sanye da kayan makaranta da jakunkunansu a rataye, ya sasu a gaba har farfajiyar gidansu, ya kwalawa malam idi direba kira, ya taho jikinsa na rawa. Yace “daga yau du ranar daka kara kin kaisu makaranta abakacin aikinka.”

malam idi ya rikice jikinsa yana bari, yace “kayi hakuri yallabai, wallahi ba laifi na bane sune basu fito ba.” yace “daga yau idan kaga basu fito ba kayi min waya kawai ka gaya min. Yace “to yallbai.” suka shiga motar direban ya jasu. Shikuma Aliyu yayi cikin gida. Zainab tace, “inbanda abun yaya, daga yin aure saika fito da sassafe. “ni’ima tace, “ai gwandake bangarenku ma na ‘yan firamare ne, ni ‘yar sakandare nasan wallahi sai an dake ni, daya kyalemu gobe basa muzo ba.”

gidan Aliyu yana nan daga bayan gidansu ba nisa. Amma tunda aka kai mansura basu je gidan ba, saboda basu da wani lokaci sai dare, sukuma ba fita suka yi da dare ba.

Yau alhamis ana tashi daga boko gida suka yo, dan ba islamiya. Ni’ima da zainab tuni sun gama shiri, anko sukayi na wani dandatsesen material baki, ni’ima tana rike da hannun zainab suka tafi.

Suna zuwa gidan suka shiga, ‘yan aikin gidan sai sannu da zuwa suke yi musu. Suka karasa babban falo inda matar gidan take, sukayi sallama, saida akayi musu izni sannan suka shiga. Mansura ta taresu da murna, a’a sai yau zaku zo, nayi fushi.” suka rike hannunta suna cewa, “tuba muke aunty, kinsan kullum da makaranta.

Tace, “to amma gaskiya yau anan zaku kwana.” suka ce wai kwana aunty? Ai baza a barmu ba a gida.” tace haba don Allah, ya ya zasu hanaku kwana a gidan babban yaya.” yayinda take kwalawa mai aikinta kira talatuwa, “na’am ranki ya dade, ta amsa da saurinta, ta durkusa a gabanta, mansura tace “bakya ga munyi bai ne baki kawo musu komai ba, nifa bana son shashanci, kirinka kula da aikinki fa.”

talatuwa tace kiyi hakuri aunty. Ta fita da sauri ta shiga kicin ta hado musu lemuka da snacks taje ta durkusa a gbansu ta ajiye. Zata mike zainab ta bude jakarta ta dauko dari biyar ta mika mata. Talatuwa tasa hannu biyu ta karba tana godiya. Inna laraba tashigo ta durkusa a gaban mansura tana tambayarta hajiya me za’a girka?

 

Surayya Abubakar

[1:19PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**7

 

TA YAMUTSA fuska tana tsara mata abunda zata girka. Harta mike ta fara tafiya zainab tabita tasa mata dari biyar a hannunta, tsohuwa laraba tace, “auta me za a sayo miki? Tace a’a ki rike baki nayi. Laraba ta washe baki tana murna tana godewa zainab.

Yaya Aliyu ya shigo, da sauri zainab da ni’ima suka yi masa sannu da zuwa tare da gaishe shi. Ya wuce bangarensa. Mansura ta kwalawa talatuwa kira, tazo da saurinta. Mansura tace, “ki hadawa Aliyu abinci kikai bangarensa.”

zainab kanta data ke yarinya tayi mamakin abun, bare ni’ima data fara zama budura. Sun san haka bai kamata ba, don ba haka ake yi a gidan su ba.

Wata mata ce da goyon ‘yarta ta fita da hayyacinta kamar almajira, ta durkusa tana gaida mansura. Mansura ta hade rai tana ya musta, da kyar ta amsa gaisuwan matar.

Ni’ima da zainab suka gaishe da matar, zainab tace kwanto yarinyar, bata da lafiya ne? Matar tace “wallahi zazzabi ne da amai da kashi na hakori.” yayinda take kokarin sakkota. Zainab ta mika hannu zata karbeta, mansura tayi karaf tace “ke zeey auta yarinyar ba lafiya kokarin daukarta kike? Saita yo miki amai ajiki.” zeey tace to kije ki sai mata magani ta sha mana.

Matar ta girgiza kai cikin yanayi na tausayawa, tace, “aiba kudin ne, magani har dari tara da hamsin, banida kudin dazan sai mata, kudin yayi yawa, ko dari da hamsin bani da’ita bare har dari tara da hamsin.” zainab ta bude jakarsu ta zaro gudan dubu daya ta mikawa matar, “ungo kije kisai mata maganin.” matar ta karba bakinta yana rawa.

Mansura tace, “ke zeey kudin wa kika samu kiketa rabarwa haka? Zainab tace daddy ne ya bamu da zamu zo ko zamu sai wani abun.

Mansura tace to shine kike rabar da kudi baku sai komai ba.” zainab tace aunty ai muna da komai me zamu saya? Ba gwanda mu bayarba.” matar nan dai tanata sawa zeey albarka harta fice ta tafi.

Ni’ima ta fuzge jakar daga hannun zainab, ta bude ta leke bakomai aciki, ta harareta to kin rabar mana da kudin, to yanzu dame zamu sai ice-cream din? Ni shiyasa wallahi bana so nabar kudin mu a hannunki, du saiki rabarwa da mutane mu ki barmu haka. Nidai kawai kirinka bayar da iya naki, kada ki kuma bayarmin da nawa kudin.”

zainab tayi murmushi, tace “haba yaya ni’ima, abunki ai nawa ne, zan iya iko da komai naki, Allah ya bamu rai da lafiya, muna da kudi a gida, ko an bamu ma tarawa muke yi idan bamuda abun siya. To ga masu bukata saimu hanasu.” ni’ima tace, “to amma ai bakya bayar du ba, ai kinsan zamu sai ice-cream.”

zainab tace bakomai yaya ni’ima, zaki ga Allah ya bamu wasu, don ranan malaminmu yace, “anaso mutum ya rinka ya waita sadaka, saboda tana juyar da bala’i.

A zamanin annabi sulaiman (a.s) akwai wani mutum a gidansa akwai wata katuwar bishiya, tsutsuwa tayi ‘ya’ya akai. Sai wata rana matar ta gaya wa mijinta cewar, ya hau kan bishiyar nan ya debo musu ‘ya’yan wannan tsutsunwar zasu ci suda ‘ya’yansu.

Mutumin nan ya kwaso ‘ya’yan, suka gashe shi, shida matarsa da ‘ya’yansa suka cinye. Sai tsunsuwar nan takai karar wannan mutumin gurin annabi sulaiman (a.s), shikuma yasa aka kirawo mutumin yayi musu tsakani da wannan tsuntsuwar, mutumin yayi alkawari bazai sake ba.

Ana haka sai wata rana matar nan ya kuma gayawa mijinta ya hau bishiya ya kuma debo musu ‘ya’yan tsunsuwa, mutumin yaki, yace “annabi sulaiman ya hana shi ya sake dibar mata ‘ya’ya.” sai matar tace kana ganin annabi sulaiman zaiyi maka wani abu danka kwashe ‘ya’yan tsunsuwa, alhalin shima me shagaltuwane da mulkinsa? Matar dai tai ta rudarsa har ya hau ya debo.

Sai tsuntsuwar nan tasake kai kararsa wajen annabi sulaiman, annabi sulaiman yayi fushi, ya kirawo shaidanu guda biyu, daya daga gabas daya daga yamma. Yace sutafi kan bishiyar nan su zauna, idan mutumin nan ya sake zuwa wajen ‘ya’yan tsunsuwar nan su rike kafafuwansa su watsoshi kasa.

Shaidanu suka je kan bishiya suka zauna. Shikuma mutumin ganin ya debo wa’yancan ba ayi masa komai ba, don haka sa wannan karon ma ya sake komawa domin ya debo ‘ya’yan. Har ya taka kafarsa zai hau, sai yaji almajiri yana bara a kofar gida, saiya umurci matar nan data bawa almajirin nan wani abu. Sai matar nan tace bakomai awajenta.

Sai mutumin nan ya dawo ya samu lomar abinci ya bawa almajirin nan, sannan ya koma bishiya ya debo ‘ya’yan tsuntsuwar nan, saita sake dwowa ta gayawa annabi sulaiman, sai yayi fushi mai tsanani, ya kirawo shadanun guda biyu daya tura kan bishiyar. Sai suka ce bamu saba maka ba, muna kan bishiyar koda yaushe, lokacin da mutumin zai hau kan bishiyar sai wani almajiri yayi bara ya koma ya bashi lomar abinci, sannan ya dawo ya hau. Zamu kama shi kenan sai ubangiji ya aiko da mala’iku guda biyu, daya ya kamani ta wuya ya jefar dani inda rana take bullowa, daya yakama abokina ya jefar dashi inda rana take faduwa.

To kinga dalilin sadakar da yayi ya kubuta daga sharrin shaidanu. Aliyu yana daga dakinshi yana jinsu, ya sake jinjina hankalin autarsu, yasan hakika akwai bawar da Allah yayiwa autarsu na musamman.

Ya fito daga dakinshi.

 

Surayya abubakar

[1:19PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**8

YA FITO daga dakinshi, yayi gyaran

murya, ya ciro dubu biyar a Aljihunsa ya

mikawa zainab, yace “zeey auta ga kudin

ice-cream.” ta rissana ta karba tana

godiya. Yaya Aliyu ya wuce ya sake fita. Zainab tace yaya ni’ima kinga abunda

nake fadamiki ba, inka bayar da kadan

sai Allah ya baka mai yawa.” ni’ima tace

nagani, amma bani su nan kada ki sake

bayar mana.” ita kuwa mansura a

zuciyarta cewa takeyi, “wannan yarinyar da shegen iyayi take. Wajen mangariba

suka isa gida. Bangaren hajiya suka nufa

sukayi sallar mangariba, zainab ta mike

tayi bangarensu, saita tarar da mamanta

kwance tana juyi. Ta tafi da sauri ta

rikota, tana cewa menene mamana, meya sameki? Maman tace banida lafiya

zaina, marata da bayana ciwo suke yi.

Nan da nan sai zainab tasa kuka tana

cewa, “mama tashi muje asibiti kinji?

Mama don Allah tashi mu tafi asibiti ko

kya samu lafiya. Maman tace da kyar, saboda ta fara

galabaita “zainab asibiti babu abunda

zasu iya yi min, Allah ne kadai zai bani

lafiya. Ki kirawomin hajiya da umma da

ummi, tayi cikin gida da sauri, du ta gaya

musu gaba daya suka taho, a lokacin Aliyu yana gidan. Maman ta galabaita

sosai, ko hannunta bata dagawa.

Umma tana ta hado kayan haihuwar a

dakin. Umma tana rike da maman, hajiya

tana mata tofi a ruwa a kofi, zainab din

taje ta rike maman tana jijjigata tana kuka, tana cewa mama! Mama!! Ki bude

idonki kiga hajiyan fa na kirawo miki ita.

Ki bude idonki kifa tofi take miki, don

Allah mama ki bude idonki kiga umma da

ummi., kefa kika ce nakira miki su, don

Allah ki tashi.” ta kama jijjigata tana gwale mata ido, tana cewa mama!

Mama!!. Aliyu yace “umma ku kamata mu

tafi asibiti.”

a lokacin Aliyu yaiwa abba da daddy

waya, suka ce to suma sun wuce

asibitin.” a can suka tarar dasu Abban har sun riga zuwa, aka shigar da mama dakin

haihuwa, zainab sai kuka take yi, ta tafi

ta rungume daddynta tana kuka tana

cewa daddy kana ganin mama bata da

lafiya sun shigar da ita can, daddy kazo

mu bita. Ya rungumota yana rarrashinta, “kiyi

hakuri zainab, ki kwantar da hankalinki,

mamanki haihuwa zatayi. Ko bakya so

tasamar miki kanwa? Tace ina somana

daddy.” to kiy shiru ki daina kuka,

mamanki haihuwa zatayi kinji ko? Kita yi mata addu’a kinji? Tace “to daddy

zanyi mata. Abba yace, hajiya su koma

da zainab gida a ar umma da ummi a

gurinta.

Abba ya taho da hajiya da zainab gida,

zainab sai kuka take yi, suna zuwa gida suna ni’ima da sadik su ni’ima suka tare

su da cewa ta haihu? Hajiya tace musu

a’a ta dai kusa. Du rarrashin da hajiya

take yiwa zainab ta kasa yin shiru, sai

kuka take yi.

Su kuwa can asibiti sun kasa samun nutsuwa, saboda jikin mama da yayi

tsanani. Wajen karfe uku na dare ta haifi

‘yarta mace, su umma da ummi suka ta

hamdala suna yiwa Allah godiya.

Karfe bakwai na safe gaba daya ‘yan

gidan sun hallara, ganin yanda jini ya tsinkewa mama, hankalin kowa ya tashi.

Daddy mijinta yana rike da ita yana

salati, yayinda likitoci suketa iya bakin

kokarinsu. Sunyi mata allura jinin ya

tsaya, du ‘yan uwa sun zagaye ta, harda

sadiya amarya da mansura, su sadik da ni’ima du suna wajen. Zainab kuwa

hajiya ta janye ta suna falon dakin da

aka kwantar da maman nata. Saboda

kuka da zainab din take yi.

Ita kuma mama jikin nata yayi tsanani,

sai wasiya take bayarwa, sai cewa take cikin dakushashshiyar murya, “ina zainab

autata, ki kirawo min zainab dina.

Sadik ya fita da gudu yana kuka ya kira

zainab, ta taho da gudu ta rike hannun

maman nata ta jijjigawa, tana cewa “gani

mama, tashi gaya min abunda zaki gaya min, kinji mamana?

Ta kwantar da kanta akan ruwan cikin

maman nata tana kuka, maman data ke

fitar da nishi da kyar ta dora hannunta

kan zainab din tana shafawa, a hankali ta

rinka motsa bakinta tana karanto kalmar shahada ‘yan uwa sunata amsa mata,

tana ta shakewa. Su sadiya da ni’ima

kuwa gaba daya sun rikice da kuka.

Can mama tayi shiru, hamza cikin firgita

yace, “ta mutu! Iyayen suka dauki salati

ga daya da hawaye, yayinda yaran suka cika daki gaba daya da kururuwar kuka.

Zainab kuwa tana yin baya ba’a ankara

ba ta sulale ta fadi kasa ba numfashi.

Aliyu ya sunkuce ta aguje ya shiga office

din likitan da ita. Likitan ya karbe ta da

sauri ya dorata kan gado yana kokarin ceto rayuwrta. Aka tafi da mama gida

akayi mata sutura aka binneta, kowa yaji

ciwon mutuwar mama. Mama mutuniyar

kirki me kawaici da hakuri, daddyn zainab

karfin hali kawai yake yi, domin yasan

yayi rashin da da wuya ya mayar da’ita. Don rashin hajiya saude ba karamin gibi

rayuwarsa tayi ba.

Anata amsar gaisuwa shikuwa sai yayi

jigudin yana tunani, ga ‘ya’yanshi ‘yan

mazan faruk da sadik suna manne da

jikinsa, yaran sun kasa manta mutuwar, sai dai kawai kada suna sharar hawaye.

Faruk shine sa’a ni’ima mai shekara goma

sha hudu, sadik kuma shekararsa sha

daya. Kwana daya da rasuwar mama aka

sallamo zainab suka taho, da yake ummi

ce a wajenta. Yarinyar tayi wata irin rama sai kace wacce ta dade da ciwo.

[1:22PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**10

 

ABBAN yace “toh shikenan Aliyu, Allah ya tayaka riko.” Aliyu yace amin Abba, nagode, Abban yace to ka gayawa daddyn naku? Yace “eh, saida na fara zuwa nayi shawara dashi tukunna.”

yace, “to ai shikenan komai yayi dai-dai, Allah ya tayaka riko.” ya amsa da Amin. Ya yiwa mahaifinsa godiya ya tashi ya nufi gidansu, ya gayawa kakarsu.

Hajiya murna tayi takara karfafa masa gwiwa daya rike ‘yar uwarsa dakyau, ta hakane zumunci zai kara karfi a tsakaninsu.”

don ita hajiya mace ce mai zumunci, tana so taga kan zuri’ar ta a hade, yayiwa hajiyar alheri, hajiya tanata godiya dasa masa albarka, ya fice ya nufi bangarensu. Ya tarar da umma da ummi a babban falo suna hira.

Yace musu, “ku hadamin kayan zainab da daddare zan zo na tafi da ita.” gaba daya suka hada baki cikin razana suka ce, “zaka tafi da ita ina?

Gidana zata koma zan cigaba da rikonta.

Umma ta mike ta kama yi masa fada, ” wato mu ka raina irin rikon da muke yi mata, shine zaka ce zaka dauketa saboda kafi mu sanin darajarta, ko iko zaka nuna mana akanta?

Yayi murmushi yace “kuyi hakuri, umma ba haka bane.” iyakacin maganar kenan yayi musu shiru. Sun riga sun san bai fiya yawan magana ba, sai dai yayi atakaice. Inkin ji shi yana hira mai tsawo, to da iyayensa ne maza.

Ya mike yana ce musu, “umma bari na karasa gida.” umma tace “saboda maganar tamu bata da amsa ko? Yayi murmushi ya dire musu kudi a gabansu, yace ummi kwasai goro.” tace “to, mungode, Allah yayi albarka.”

yana fita umma ta kama baki, tace, “ki gane min yaro, wai shi babba har ya fimu sanin abunda ya dace. Ummi tayi dariya tace “Aliyu kenan gadanga kusan yaki. Shifa zuwan da yayi yaga dazu bata je makaranta ba, gani yake kamar zamu kara sangartar da ita mu rika biyewa shagwabarta.”

Aliyu yana isa gidansa yayi fakin ya shiga, a falo ya zauna yana karkade kafa. Mansura ta fito daga daki, tace “sannu da zuwa Aliyu, ga break dinka can, koda yake rana ma tayi kaine kayi fitar safe.”

yace “nayi break a office din daddy bana tare da yunwa.” yace kisa a share wancan dakin, zan dawo da zainab gidan nan zata zauna acikin dakin can.

Ta dafe kirji tace “haba Aliyu, ya zaka ce zaka dawo da zainab? Ai zaka takurawa rayuwarta. Don Allah ka kyaleta a gidanku, wannan shagwababiyar yarinyar in zamu iya da ita anan?

Ya doka mata harara yace ba shawararki nazo nema ba, idan zainab tazo kada ki barta ta zauna ki koreta.”

tace, “haba Aliyu kai ka fiya zafin zuciya, daga ‘yar wannan maganan saika hau tari, ba nufi na haka ba, ita da gidan wanta “ai ban isa na koreta ba.” yamata shiru bai sake ce mata komai ba daman tasan ba zai sake magana ba, don ya fiya miskilanci, baya son yawan magana.

 

***                ****

karfe shidda ‘yan makaranta sun dawo, suna cin abinci ba dadewa akayi mangariba, suna idar da sallah hajiya ta rungumo zainab jikinta tana shafa kanta, tace “zainab yanzu fa yayanki zai zo zai tafi dake gidansa, zaki ci gaba da zama acan.”

zainab tasa kuka tace, nidai hajiya bazan jeba nace, yai tamin fada koma ya dokeni, hajiya tace bazai dokeki ba, kuma fada ma ya daina yi miki. Kije ki zauna kinji zainab? Ta make kafada, um-um, ni ba zanje ba.”

suna haka taji yo sallamarsa, da sauri ta tashi da gudu tai cikin dakin hajiya. Aliyu ya shigo ya sake gaida hajiya, hajiya tace masa “zainab dai tace baza taje ba, ka ganta can harda kuka.”

ya kwala mata kira ta fito a tsorace, tazo ta durkusa a gabansa

yace “shine kika ce bazaki gidana ba? Ta girgiza kai alamar cewa, a’a yace to meye nayin kukan? Yi min shiru. Tasa hannunta ta toshe bakinta ta hadiye kukan.

Yace ki goge hawayenki kije, kiyi wa Abba da daddy sallama.” tace to, ta goge fuskarta. Ta shiga bangaren su umma ta tarar da Abba da umma da ummi suna falo, Abba yace yaki ‘yata tazo ta zauna a jikinsa.” yace menene naga idonki alamar kinyi kuka? Tace bakomai, Abba sallama nazo inyi muku zan koma gidan yaya.”

Abban yace “zainab bana son abunda zai takuraki, in bakya son zuwa ni zansa ya kyaleki kiyi zamanki.” tace a’a Abba zanje.” yace to shikenan zainab, Allah yayi miki Albarka, kici gaba da maida kai da kokari a makaranta, tanan ne zaku fi shiri da yayan naki kinji ‘yata?

Tace “to Abba nagode.” ta mike ta shiga wajen daddynta, ta daura kanta akan cinyarsa tana kuka. Yasa hannunsa yana shafa kanta yace “kiyi hakuri zainab, nasan bakya son tafiya. Zainab ko yaushe kina raina, dana ganki saikin tunamin da mamanki. Zainab du ina tausaya mana ni dake na rashin mamanki.

Kiyi hakuri zainab kiyi zamanki, nasan zai rikeki da amana kamar ni. Kiyi masa biyayya shida matarsa, banda rashin kunya kinji? Tace “to daddy zan kiyaye.” ya bude firij ya dauko rubutu a roba ya bata, ungo shanye rubutunki maganin tsari da kariya daga shaidanu.” ta karba tayi bisimilla ta shanye, ya karba yasa ruwa ya dauraye mata, ta karba tasha, ragowar ya zuba a hannunsa ya shafa mata a kanta da fuskarta.

Yaita mata nasiha mai shiga jiki, yace ta daina kuka ta tashi taje su tafi.” hajiya dasu ni’ima su sadik har gindin mota suka rakota suna hawaye tana hawaye.

 

Surayya

[1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**11

 

HAJIYA tana rungume da ita tana rarrashinta suka bude mata gaban mota ta shiga, ta dunkufar da kanta akan gwiwoyinta tana ci gaba da kukanta kasa-kasa, Aliyu ya sallame su du yaraba musu kudi, yace su koma gida, suna tunanin ‘yar uwarsu wai anrabata da gidansu kenan.

Ya kalleta au baki daina kukan ba? Tayi saurin hadiye kukan nata, ta goge idanuwanta. Tafiya kadan suka isa gidansa, suka fito har daki ya kaita, “nan shine dakinki, talatuwa zata rinka taya ki kwana.” dakin yayi kyau, a yau dinan ya sayo mata gadon silba da madubi, sai kwaba ta jikin bango, sai labuye da jan kafet, shikenan ba wani shirgi, sai toilet aciki dake gefe, tace “to yaya.” ya fita ya nufi sashinsa, zainab itama ta shiga dakin aunty mansura.

Zainab ta kwantar da hankalinta tana zaune a gidan yayanta, tsakaninta da abinci saita ga damar ci, ko yaushe yayan nata yana cikin siyo musu ice-cream, youghot su biskit da cakulet, da yake abinci bai dami zainab ba, ita hakan saya fiye mata dadi.

Ita kuwa mansura ta fiya lalaci da sangarta, bata wani iya girki ba, shikuwa Aliyu dan gaye ne mai aji, gashi da kyankyami, don haka bazai iya cin abincin mai aiki ba.

Don haka inya zo garin ma saidai yaje gida yaci abinci, don a gidansa inna laraba ita take yin girki. Babbar mace ce amma da kwarinta, don bata wuce yin aure ba, sai ‘yar budurwa wato talatuwa, ita take yi mata shara dasu goge-goge da gyaran gado, inta yi baki ta kula dasu. Don wata wauta ta mansura dai-dai da mijin ma inya nason wani abu sai dai ta kira talatuwa.

Don haka ma ko meye ya gwammace yayi da kansa, abinci kuwa saiya je gidansu sannan yaci. A gidansu su umma har fada suke yi masa, don me zai rinka baro girkin matarsa baya son ci.

Sai dai yayi murmushi kawai yace musu bakomai. Bama yanzu da mansura take fama da laulayi. Da safe yana zaune a falo da wando iya gwiwa da farar shirt, yana lumshe idanuwarsa kamar mai jin barci. Mansura tana zaune kusa dashi tana cin wainar kwai da dankalin turawa, ta zuba shayi a kofi yana ta turiri, gashi yayi kauri da hadin madara da naskofi da dai sauransu.

Zainab ta fito sanye cikin shirin makaranta, ta durkusa ta gaishe da yayan nata da mansura. Ta mike a gurguje take, dan takusa makara. Ta dauki shanyin gaban auntyn nata tadan kurba, tace “wai aunty wannan kaurin ai yayi yawa, bakya tsoron ya kulle miki ciki?

Mansura tayi dariya tace, laifin babynku ne ba ruwana. Zainab tayi dariya tace ai, “ai gwanda ki dinga ci sosai don ki haifa mana katon baby in rinka daukarsa da kyar.” ta nufi firij ta dauko ice-cream da youghot da cake, tazo ta wuce su da sauri saboda yayan nata, tace aunty natafi makaranta.” kafin tayi magana Aliyu ya kirata “zainab.”

tayi saurin juyowa tare da amsawa, a sanyaye tace na’am yaya.” zo nan. Ta dawo ta durkusa a gabansa. Yace haka zaki tafi makaranta baki karya ba? Tace yaya zanci cake da ice-cream da youghot a mota.” yace wato har yanzu kina nan dakin cin abincin ki ko sai kayan kwadayi? Ke wace iri ce ne? Da safe ma sai kin sha sanyi bazaki ci abinda zai dumama miki ciki ba?

Mansura tace wallahi haka nake fama da ita, bata son cin abinci, daga shan kayan zaki sai shan kayan sanyi.” yace ina break din nata? Mansura ta kwalawa talatuwa kira, tace mata ina break din zainab? Talatuwa ta shiga dakin zainab da sauri ta dauko break din data kai mata, yanda ta ajiyeshi haka yake, ko budawa bata yiba. Ta ajiye a gaban zainab din.

Aliyu ya kalleta yace to maza ki cinye shi yanzun nan.” idonta yayi rau-rau alamar sonyin kuka. Shikuwa sai ya jingina da kujera ma ya lumshe shanyayyun idanuwansa kamar zaiyi barci. Ba yanda zata yi, haka ta rinka tura dankalin nan da kwai tana shan ruwan shayin.

Cikinta ya cika taji kokarin yin amai take yi, tace a hankalin cikin sanyin muryanta, “yaya ya dago kai yayi mata wani kallo, bata iya fada masa komai ba, ta sake sunkuyar da kanta, ya sake lumshe idonsa.

Haka taci gaba da ci tana hawaye, saida ta cinye du. Dakyar ta iya tashi tsaye, tace yaya na cinye, na tafi? Ya bude ido daya yayi mata alama da hannu wai ta tafi. Ta fice inda direba yake jiranta ta shiga ta tafi.

Mansura tace gaskiya Aliyu kana matsawa yarinyar nan, da nice saika bata min rai kace ina takurawa kanwarka.” ya bude ido daya yace karki manta shekaranta goma sha daya, yanzu ta shiga sakandari aji daya, har yanzu ita yarinya ce, idan bana matsamata taci abinci sai yunwa ta kamata.”

ta tabe baki tana gunguni, “in rashin cin abinci ne ai a wurinka ta gado, tunda kaima baka cin na gidanka.” ya kwanto akan cinyarta yace, kiyi min da kanki mana, du rashin dadinsa ai zanci. Amma zaki rinka sa tsohuwar mutane wahalar girki, sannan kisa wata yarinya daban itace mai bani abinci, kallon yarinyar nan kadai tayar min da zuciya yake.”

ta zumburi baki bata ce komai ba, ya shafa cikinta yana cewa, “i luv u baby, yaushe zaka iso kaga daddynka? Tace ai kuwa zai jima baiga daddyn ba, sai nan da wata biyar.” ya gyada kanshi, Allah kawo minshi lafiya.”

tadan rankwafo kanshi tace, “Aliyu dan Allah zaka danyi min tausa?

 

Surayya

[1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**12

ALIYU dan Allah zaka danyi min tausa?

Yace nikuma me zakiyi min? Tace

bakomai.” yace to kyaleni bacci nake ji.”

ta ture masa kansa akan kujera, tace to

dagani naje na kwanta.” yau alhamis karfe biyu direba ya dauko zainab daga

makaranta, saboda yau basuda islamiya,

shiyasa basu kai shidda ba. Ta shigo

tana jan jakartata, ta zube a falo tace

“wash! Aunty sannu da gida, ya

bybynmu? Mansura tace gashi nan dai yana ta min

zillo.

Aunty ki bashi abinci yaci yunwa yake ji,

inya ci zai daina yi miki zillo.” ai naci

abinci zeey, kin zata ni irinki ce sai anyi

min dura ina kuka? Zainab tayi saurin mikewa, bari na tashi kada ya shigo ya

ganni anan ya kuma sani cinye abincin

daya fi karfin cikina.” tayi dakinta suna

dariya.

Da mangariba ni’ima tazo gidan, sukayi

tsalle suka rungume juna suna masu jin dadin ganin juna, kamar ba dazu suka

rabu a makaranta ba. Suka zauna a falo

suna dariya. Ni’ima tace auntyn mu ina

wuni, ya babyn namu?

Lafiyarsa kalau gashi nan yana jinki.”

ni’ima tace zainab kinsan gobe ne fatin zara’u yusuf shidda na yamma, ya zamuyi

wajen tafiya, don yanda muke da zara’u

dole ne mu fasa fatin nan?

Zainab tace, wallah yaya ni’ima ina so in

rakaki, to amma ya zamuyi da yaya, dama

ya tafine da sauki, to shi sai ranar littinin da safe zaiyi sammakon tafiya kaduna

kan bakin aikinsa.” ni’ima tace, “ai dolene

ma kije zainab, tare fa nayi mana ankon

fatin, har gwagwaron, har takalimin da

not din iri daya ne. Kuma yanda zara’u

take sonki, ke wallahi kin fiya tsoro, ba sai kice masa zaki zo gida ba sai muyi

tafiyar mu ta gida.” mansura tace amma

ni’ima anyi saurin yiwa zara’u kawarki

aure da wuri, shekararki sha bakwai fa?

Koda yake daga ganini zara’un nan ta

girmeki, Allah ne dai ya hada kaunarku.” ni’ima tace shekara biyu fa ta bani, yanzu

da ita fa zamuyi candy, wai mijin zai

barta ta karasa a gidansa.”

to saurin na meye? Inji mansura, saura

wata shidda fa kuyi candyn, da ya kyaleta

ta karasa ba shikenan ba.” ni’ima tayi dariya tace tsoro yake yi kada ayi masa

kwace, tafiya samari daya wa.”

talatuwa ta shigo tana jera musu abinci,

ni’ima ta bude jalof din taliya ce da

farfesun kifi. Ni’ima tace zubamin jalof

din kadan da farfesun.” talatuwa ta zuba mata.

Zainab kuwa farfesun kawai ta diba, ta

debo musu fantar gwangwani a firij.

Ni’ima tace, zainab wai ke wace iri ce?

Ban taba ganin makiyin abinci ba sama

dake, yanzu kuma inkinci wannan shikenan saida safe ko?

Tace “a haba yaya zai taho mana da

cake da icream. Ni’ima tayi tsaki tace,

shikenan abincin naki.” tace don Allah

aunty ki rinka yi mata fada, shiyasa

kullum gata nan kamar a busheta ta fadi. Mansura tace ai tasan karonsu da

yayanku, saina shiga gaya masa

tukunna.” talatuwa ta dawo da tangaram

a rufe, da gasasshiyar kaaza aciki da

mansura tasa agasa mata.

Ni’ima tace kai aunty ni aida nasan da wannan ai bazan ci farfesun ba, ba

ruwanki aunty, abinda kike so kici shi zaki

ci. Muma dai Allah ya aurar damu, ina

daga kwance aita yimin komai.” mansura

tayi dariya tace, ke kuma abunda yake

baki sha’awa kenan. Suka fara cin kazar suna hirarsu, zainab ta fara cire

hannunta waita koshi, ni’ima da mansura

kuwa har kashi saida suka taune.

Ni’ima ta kwalawa talatuwa kira tazo,

“gani. Kije ki gayawa direban gidan nan

gani nan fitowa zai kaini gida.” talatuwa ta fita da sauri. Ni’ima ta mike tana yafa

mayafinta da jaka, zainab ta rike

hannunta tace, “don Allah yaya ni’ima ki

bari sai anjima kya tafi kinji?

Tace a’a zainab gwanda na tafi, kinsan

yanzu yaya yana kan hanyar dawowa gida, kada ya gane ni nazo najaki ya

hanaki zuwa goben.” tace to shikenan

saina zo goben. Ta rakata har mota ta

tafi. Sannan ta dawo ciki ta wuce dakinta,

alwala tayi ta tayar da sallar ishsha. Aliyu

ya shigo ya wuce dakinsa, sai da ya watsa ruwa ya dan shafa lotion a jikinsa,

yasa kananan kaya, ya fito falo yana

kallon tashar zee-aflam, suna wani

tsohon film mai kyau.

Mansura tana gefensa tana cin tufa,

zainab ta fito daga daki ta durkusa a gabans, tace, yaya sannu da zuwa.” ya

amsa a hankali. Taci gaba da

tsugunnawa tana so ta tambayeshi zuwa

gida gobe ta rasa ta ina zata fara.

Ya kula da ita yasan akwai abunda take

so ta tambaye shi, don haka sai yaci gaba da kallonsa ya dauke kansa daga

bangaren tana zaune tana zaune tana

wasa da yatsun hannunta, tace “yaya.

Yace “uhm! Ba tare da ya kallo taba.

Saita yi shiru ta kasa cewa komai.

Shikuwa yana jingine da kujera ya lumshe ido yana kallo kamar ma baisan

da zamanta a wurin ba, ta sake cewa,

yaya don Allah gobe zanje gida. Yace me

ake yi a gidan? Tace bakomai. Yace to

bazaki jeba.”

ta sunkuyar da kanta sai hawaye kawai itada bata da wahalar yin kuka. Mansura

tace don Allah ka kyaleta taje.” yayi mata

shiru kamar baiji abinda tace ba.

Mansura tace, ni tsiyata dakai kenan, sai

ayi ta ma magana kayi shiru kana jin

mutane kamar wani kurma. Ko motsi bayyi ba balle yasan dashi take. Zainab

ta mike a hankali zata wuce daki, ya

kirata “zainab.” ta juyo da sauri tare da

amsawa na’am yace “don nace bazaki

jeba shine kike kuka?

[1:23PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**13

TA juyo da sauri tare da amsawa na’am.

Yace “don nace ba zaki gidan ba kike

kuka?

Tayi saurin girgiza kai. Yace bakida baki?

Tace a’a ta koma ta durkusa a gabansa tace, “yaya dama bikin kawar yaya ni’ima

za’ayi, shine zan rakata.”

yace “to me ya hanaki ki gaya min

gaskiya? Tace, “don Allah yaya kayi

hakuri ba zan sake ba.” ya jinjina kai.

Tace yaya naje goben? Ya daga kai. Amma kada kiyi dare.” tayi murmushi,

“yaya nagode, Allah ya saka da Alheri.”

tamike ta shige dakinta tana murna. Da

safe a makaranta zainab take gaya wa

ni’ima yaya ya barta zata zo. Ni’ima tayi

murna, tace “to ki taho da wuri dai. Bayan sun tashi daga makaranta, karfe biyar na

yamma ni’ima ta bugo wayar mansura

tana neman zainab.

Zainab din tana karba ni’ima tace, “haba

zeey, ki sauri kizo man biyar fa tayi.

Zainab tace, “nayi wanka na gama kwalliya, yaya nake jira ya fita nasa

kayana na taho. Tace baya barki ba ki

fito ki taho kawai mu tafi.

Tace mata, cewa fa yayi kada na dade, to

kinga gwanda yasan ban taho da wuri ba.

Tace eh to gaskiya hakane. Yauwa kingan shi can ma ya fitarsa,

yanzu direba zai kawoni.

Wajen fatin ya hadu, ango da amarya

sunyi kyau kamar fure, sai walwali suke

suna sheki. Ni’ima sai kaiwa da komowa

take a matsayinta na babbar kawa, du inda tayi kuwa zaki ga idanuwan samari a

kanta, saboda ni’ima ta zama budurwa

kyanta ya kara fitowa, ga gwalli ga iyayi.

Su masu sabis da aka dauka sunata

kaiwa mutane abinci dasu swan, lemon

kwali dana gwangwani. Jama’a suna cin abinci Ali jita ya saki kida, tuni zakin

kidansa yasa jama’a suka fara kada kai.

Amarya da ango suka shiga filin rawa,

nan fa kawaye da abokan ango ‘yan

uwan amarya da ‘yan uwan ango, aka

shiga filin rawa aka rinka watsi da naira kamar ba a san zafin nema ba.

Hankalin zainab ya tashi ganin har

takwas na dare tayi, ta rinka damun

ni’ima ta taho su tafi gida. Ni’ima tayi

tsaki, waike meye hakane? Ki bari agama

basa mu tafi ba. Zainab tace um-um yaya ni’ima, kinsan

halin yaya, kizo mu tafi, ni’ima tace ke

wallahi kin fiya matsala, saika ce wata

matar aure, kita faman jin wannan

tsoron, bafa abunda zaiyi miki. Tace um-

um, nidai kizo mu tafi bana son bacin ran yaya, wallahi du saina ji na damu.” dai-

dai lokacin da Ali jita ya saki cashiyar

karshe ni’ima ta riko hannun zainab suka

fice suka shiga motarsu, direba ya kawo

su gida. Saida aka sauke zainab sannan

ya wuce da ni’ima gida. Yana zaune a falo yayi zaman nasa na

kasaita kamar wani basarake, ya lumshe

ido daga gani tunani yake yi, mansura

tana kwance da littafi tana karatu, zainab

tayi sallama ta shigo, mansura ta amsa

sallamar tare da cewar “kun dawo? Tace mun dawo aunty.” tace yaya sannu da

gida.” ya bude ido daya yace sai yanzu

kuka ga damar dawowa? Bance ku dawo

da wuri ba? Ta marairaice, “don Allah

yaya kayi hakuri bazan sake ba.” ya daga

kai “shikenan tashi kije. Ta mike tana hamdala a ranta da abin yazo da sauki.

Ranar littini da asuba Aliyu ya nufi

kaduna bakin aikinsa, sai kuma ranar

jumma’a da yamma zai dawo. Kwanci

tashi asarar mai rai, cikin mansura ya

shiga wata tara harda kwanaki, tana zama dakyar tashi da bisimillah.

Ranar jumma’a da mangariba Aliyu ya

iso, bai samu wata tarba ba, sai dai

mansura ta langwabe masa bata da

lafiya, sai kuka take yi masa. Shikoma du

ya wani rikice, don shi kukan yaro ma baya so bare na babba.

Ya kwasheta suka nufi asibiti, raki take yi

da ihu tana murkususu acikin motar.

Zainab kuwa sai hawaye take yi, tana

cewa aunty kidaina ihu salati zakiyi.

Tun a motar Aliyu yayi waya gidan su mansura da gidansu. Suna isa asibiti aka

shigar da mansura dakin haihuwa, Aliyu

yayi tagumi yana sauraron ikon Allah,

yayinda zainab ta dukufar da kanta acikin

gwiwarta tana kuka kasa-kasa. Tana

tuna lokacin da suka kawo mamanta acikin irin wannan halin, wanda

haihuwarce sanadiyar mutuwarta,

‘yan gidan su mansura sun zo. Yart da

kishiyar babarta. Can saiga ummi tazo,

zainab ta tafi ta kankame ummi tana

kuka, ummi ta rinka shafa kanta tana rarrashinta. Wani ihu da suka ji mansura

tayi shine dai-dai da dan ya fado. Nurse

din ta garzayo da gudu tazo ta

kwantsama musu labarin haihuwa, tuni

kowa ya washe baki ya daga hannu sama

yana yiwa Allah godiya. Sun shiga dakin anata yiwa juna barka

da yaba kyan yaron. Aliyu ya rungumeshi

a jikinsa yana maiyi masa addu’a da

fatan Allah ya raya shi.

Washe gari da safe ka sallamesu

kasancewar mai jego kalau da ita da babyn. Gidan ya cika da ‘yan barka ‘yan

uwan Aliyu dana mansura.

[1:24PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**14

GIDAN ya cika da ‘yan barka ‘yan uwan

Aliyu da ‘yan uwan mansura. Sadiya ta

taho tinkis-tinkis dana ta tsohon cikin,

ni’ima da zainab suka rungumota suna

murnar ganinta. Dakin mai jego sai kamshi yake. Kowa yazo barka zainab ce

zata karbeshi da farin cikinta, ta dakko

masa jaririn. Ko yaushe yaro yana

rungume ajikinta, kamar kada ta bawa

kowa.” ranar kwana hudu aka kawo

kayan barka a katuwar akwati, kayan jariri ne tsala tsala masu kyau, da dan

jeans da shet na yara, takalma, safofi,

fidoji, saitin shawul da tawul, barguna

masu laushi.

Kaya ne masu kyau da tsari duk ‘yan

waje. Sai karamin akwati kayan mai jego ne, turmin super holllan biyu, leshi biyu,

shadda galila mai tsadar guda daya,

kowanne da mayafinsa, sai takalma da

jaka kala bibbiyu.

Ya bawa ni’ima da zainab da sadiya

super holland biyu su uku, ya karawa zainab da galila anyi mata haddaden

dinki aikin sama mai tsalelen kyau.

Da mangariba Aliyu yana dakinsa,

mansura ta shiga da jaririn, Aliyu ya

karbeshi yana murmushi, sai shafashi

yake yana murmushi. A zuciyarsa kuwa godiya yakewa ubangiji daya bashi

kyautar da duk duniya babu wanda ya isa

ya baka kyautar da sai Allah.

Mansura tace Aliyu nazone akan

maganan shirye-shiryen suna. Yace uhm!

Me da me zaku yiyyi? “inaso da yamma ayi walima, da daddare

mu fita fati a daula hotel, sai bokitai da

manyan robobi da kalanda, du za’a

rarraba a wajen.

Yace za’ayi komai amma banda fati.” ta

wani harzuko, haba don Allah don Annabi, wallahi ka fiya yawa, ya zaka ce

ba za’ayi fati ba, alhali ni inaso na burge

saboda kawayena zamu kakko makadi

don kawata fatin, kuma zaka kawo min

matsala.

Yace albarka nake nemarwa ‘ya’yan, bana so su taso akan harkar shaidanci.

Ta mike ta kama masifa, kai dai kawai

kana so ka wulakantani a gaban kawaye

na, haka wai haihuwar fari dan kwaya

daya amma bazaka saki kudi ayi

bushasha ba, don kasan bakai kasha wahalar haihuwan ba.

Ya daga mata hannu yace, ya isheni

haka fita ki bani waje.” ta fito tana

kunkuni tare da bakaken maganganu. Ya

dafe kai don jin kansa yana sarawa,

mansura zata haddasa masa ciwon kai, shi baya son hayaniya.

Ta dawo daki tana kunkuni da fadar

maganganunta. Saratu yayarta tace,

meye kuma?

Mansura tace kinji wai baza ayi fati da

kida ba. Saratu tace, ai wannan wulakanci ne, ya

mayar damu kananan mutane bayan ni

har na buga kati na fara rabawa?

Lawisa kawar mansura tace, kawai inba

zai bari mu tafi ta nan ba, ba saiki ce

masa zaki je kiyi sunan a can ba, inyaso da daddare muyi tafiyarmu fatin, ai mun

riga munyi dai ai shikenan.” saratu tace

ita wallahi jeki ce masa zaki tafi gida

zamuyi sunan acan.

Mansura tace wallahi yace na fice na

bashi waje, idan na koma nasan halin zuciyarsa, sai ya iya marina.

Saratu tace tabdi ya mareki? Ai kuwa

wallahi daya mari aurensa.

Lawisa tace, tunda kuwa kika nuna kina

jin tsoronsa kinsha wulakanci iri iri.

Nan suka hadu sukaita aibata shi, suna fadar maganganu son ransu. Zainab

kuwa ranta ya baci, kawai saita sa kuka.

Saratu da lawisa suka hau yi mata

masifa. Kinji yarinya da munafunci, dan

uwanki yayi ba dai-dai ba zaki hanamu

fadane munafuka? Kiyi kukan jini bana hawaye ba.” zainab ta mike tayi dakinta

tana kuka. Lawisa ta rike baki, tace ahaka

kike zaune da wannan yarinya mai

miskilancin tsiya, har wani kuka take don

anfadi laifinsa.

Mansura tace kuma wallahi baki ga yanda yake takura mata ba, ni har

tausayi ma take ban, don inyana gari

bata da sakewa” saratu tace “ai wani irin

mutum ne, shiko fuska baya saki don

kada akawo masa raini.” ranar suna dole

mansura ta hakura da maganar fati, akayi taron suna da yamma akayi walima ta

burgewa da bajinta, mai jego sai shiga

take tana fita tasa wannan ta cire tasa

wancan ta cire.

Yaro yaci suna Ahmad, sadiya da ni’ima

da zainab, les din da Alh ya dinka musu suka saka, da yamma a wajen walima

suka sa super ta wajen Aliyu. Can

jimawa zainab ta canjo da shaddar da

Aliyun ya dinka ma, sadiya tayi mata

daurin gwagwaro akanta, tayi kyau,

kamar ka saceta ka gudu. Sadiya da ni’ima sun cancanja shiga,

suma dai shadda ce amma kalar ta kowa

daban. Sadiya ta rinka raba kalanda mai

hoton zainab tana dariya rungume da

jariri, kaandar tayi kyau

kowa ya karbi kalandar ya kalla saiya yaba da ita.

Haka su saratu da lawisa su kaita raba

robobi da ‘yan kananan bokitai. Da haka

taro ya tashi lfy, kowa yana san barka.

Kayan barka da atamfofi data samu, da

rigunan jarirai kamar wadda zata bude shago.

Ba ruwanta kibarta kawai take yi, taci mai

kyau tasha mai kyau, ta hau gado ta

mimmike ba ruwanta da harkar Ahmed,

yana wajen masu rainonshi su zasu hada

masa madara su bashi yasha, su bashi ruwa, idan ya koshi su goya shi.

Shan nononsa sai lokaci lokaci, saidai

idan ta jiyo kukansa ta kirawo ‘yan aikin

nata ta balbalesu da masifa, mai suke yi

masa yake kuka? Suyi ta faman rantse

rantse cewar, wallahi basu yi masa komaiba, sannan zata karbeshi ta bashi

nono, tasa su goya shi suyi ta faman

jijjiga har sai yayi barci.

[1:25PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**15

TASA su goya shi suyi ta faman jijjiga shi

har sai yayi barci.

Sai dai fa du sanda zainab ta dawo daga

makaranta, tana yin sallah zata karbo

ahmad daga wajen masu rainonsa, taita yi masa

wasa tana tarairayarsa, tai

tayiwa mansura naci da magiya dole

saita karbe shi ta bashi nono ya sha ya

koshi.

Ahmad yayi wayo sosai, yayi mugun sabo

da zainab, don har yafi ganeta akan mamanshi

don zainab har ta iya yi masa

wanka, ta shirya shi cikin kaya masu

kyau, tasa mishi turare yaita kamshi. Har

mansura taita sha’awarshi, abinda ita

lalacinta da son jikinta bazai barta ta iya

ba. Du da zainab din ba wani lokacine da ita

ba, inta fita tun takwas na safe sai shidda

na yamma take dawowa, idan sun taso

data dawo gida inta ci abinci tayi sallah,

tayi wanka tasa kayanta, saita dakko

yaronta ahmad taita yi masa wasa tana

lallabashi, har lokacin bacci ta kaiwa

mansura shi ta bashi nono yasha ya

koshi ta taho dashi dakinta ta kwantar

dashi a gado, ta canja kayan barci tayi

musu addu’a taja bargo ta rufe su, ta

rungume ahmad a jikinta suyi barcinsu. Talatuwa

data ke tayaa kwana idan ya

farka cikin dare, ita zata dakko shi ta

bashi madara da ruwa, tasa shi shi

akafada ta jijjiga shi yayi gyatsa ya koma

baccin shi, saita shimfida shi a gaban

zainab ta rufe su. Itama ta koma baccinta du

sanda Aliyu yazo weekend, yana kula

da abinda yake faruwa da yaronshi da

yake kokarin zama marayan karfi da yaji.

Sun sha fada da mansura akan sakarwa

masu aikin dansa data keyi. Yasha korota

intaje kwana dakinshi, yace saita dakko mishi

dansa. Saita rabu dashi ta tafi

dakinta tayi kwanciyarta.

A hankali ya fuskanci tsananin son da

zainab take yiwa ahmad, ya gano zainab

ce take kwana da ahmad ba yan aiki ba,

sai ya samu nutsuwa a ransa, yayi wa Allah

godiya, don yasan zainab tafi

mansura tarbiya da sanin ya kamata,

yasan danshi zai taso da tarbiya matukar

yana tare da zeey autarsu.

Yau asabar, Aliyu yana gida, zainab babu

makarantar boko, wajen tara na safe tayi wa

ahmad wanka a bahon shi, Aliyu yana

kallonta yana yaba baiwar da Allah yayi

wa yarinyar, ‘yar da har yanzu bata cika

shekara goma sha uku ba, amma tana da

nisan hankali da tunani wanda ‘yar

shekara ashirin da biyar bata dashi, wato

mansura.

Ta gama yi masa wanka, ta nade shi a

tawul tana yimi shi wakar data ke yi masa

inyana rigima. Wayar falonce tayi kara,

zainab ta daga tace “hello yaya ni’ima.”

daga can ni’ima tace yau ne fa yinin kawata

murja sule, kizo da wuri muje.”

zainab tace don Allah yaya ni’ima kiyi

hakuri, ba zan samu damar zuwaba.”

ni’iman tace saboda me?

Zainab tace, yaya ni’ima wallahi ban

tambayi yaya ba, kuma kinga yau nadan samu

hutu ba boko, ina so na wuni da

ahmadina, ba zan iya fita waje na barshi

ba.

Ni’ima tace kinfiya shirme zainab, ina

uwarsa ko zaki zama mai rainonta ne? Ita

ba unguwa take ficewa ta barshi ba, sai ke zaki

zauna ki rinka yi mata wahala

dashi? Tace “haba yaya ni’ima kada ki

manta ahmad dana ne gudan jinina ne,

don wallahi basu da maraba da abunda

zan haifa, tunda dan yaya nane. Ina

ruwana da halin uwarsa, tsarina daban nata

daban. Kiyi hakuri wata rana na

rakaki, kinji yaya ni’ima?

Tace to shikenan auta, ba komai ki

shafamin kan ahmad ki sumbace shi, kice

masa inji momynshi.”

zainab tayi dariya tace, “to bar kiji ma nayi masa

kafin ki kashe wayar.” ta

suabcin kumatun ahmad tace yarona

momynka tace nayi maka, tana kuma

gaisheka, inta dawo daga gidan biki zata

zo ganinka.” ta ajiye wayar tana dariya.

Ta zauna ta gama gogewa Ahmad danshin

jikinsa, ta shafa masa manshi, ta

shafa mashi farar hoda, sannan ta daga

wuyarsa da hammatarsa ta zazzaga

masa, ta shafa masa kasan wuyansa da

hammatarsa, tasa masa kwalli, tasa mai

pampas, tasa masa farar ves, tasa masa safa da

dan takalminsa, ta shafa masa

turarensa. Shirin yaron yayi kyau, gashi

yana ta kamshi.

Ta dama mishi madararsa a fida daidai

cikinsa, tasa masa abaki ya kama zuka,

ya shanye tas, ta bashi dayan fidar mai ruwa a

ciki ya sha, ta dora shi a kafadarta

tana shafa bayanshi, yaron har yayi

gaytsa.

Ta dago shi tana yi masa wasa yana

dariya, daga bayanta taji ance ” bani

yaron naki na taya ki raino.” ta juyo da sauri tace

“lah! Yaya yanzu ka shigo?

Don ita kwakwata dazu bata ganshi ba,

don ita inta na tar da Ahmad bata

tunanin komai sai yanda zata kula da

yaronta. Ta durkusa ta mikawa Aliyu shi,

ta gaisar da Aliyun ta mike tayi dakinta itama ta

shiga wanka. Tana fitowa ta

goge jikinta da tawul, ta zauna gaban

madubi tana kalkale jiki.

Zainab tun tana karamarta ‘yar iyayi ce

da son kwalliya, gata da son kamshi, da

kudinta ma sayan turaruka take yi bare yaya

Aliyu yana sai mata, hakama

Abbansu ko daddynsu suna bata.

Ta tsara kwalliyarta cikin wani fine les

mai fulawoyi, bashida nauyi, riga da siket

ne filet, ta kafa daurin dan kwalinta daya

kara fitowa da kyanta, ta fesa turaruka sai

kamshi take zubawa.

Ta fito falo har yanzu Aliyu yana zaune

yana lallaba Ahmad da yayi barci, tace

yaya yayi barci kawo shi naje na

shimfede shi. Ta dan marairaice masa

cikin shagwabarta tace….

Next episode by 6pm

via #Justice_hamxat

[1:26PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**16

TA DAN marairaice masa cikin

shagwabarta, tace don Allah yaya

kabarni naje gida.

Yace meyasa kike so ki koyi karya ne, ba

inaji ni’ima tayo miki waya zakuje gidan biki

bane?

Tayi kasa da murya cikin shagwaba tace,

wallahi yaya ba gidan biki zanje ba, aina

gaya mata bazan jeba, tunda ban gaya

maka ba. Daman su hajiya zan kaiwa

Amadina su ganshi.” ya gyada kanshi, “kuje

direba yana waje sai ya kai ku.” tayi

murmushi, yauwa yaya nagode.” ya

gyada kanshi ya jingina da kujera yana

ta kallonta, tana ta hada fidar Ahmad ta

ruwa data madara, da dan fulas dinshi na

ruwan zafi, ta debo masa kaya kala biyu da

pampas guda biyu ta zuba acikin jakar

goyonshi.

Wannan page ya dan samu matsala yayi

baki

kwanci tashi ba wuya, zainab ta zama

budurwa, tana da shekara goma sha bakwai,

yanzu tana aji shidda a

sakandare. Zainab kyanta ya kara fitowa,

tana da iyayi da kwainane, akwaita da

tsabta dason gayu, don du wata saita je

salon, bata gajiya da kunshin tafin

kafanta ko zanen fulawa ta lalle. Ta fiya sanyi

magana da marairaita; saiki

zata sangarta ce da shagwaba tayi mata

yawa. Idan tana magana mace ma

burgeta take yi bare namiji, akwaita da

iyayi da yauki da yanga.

Abinda yafi fisgar maza da hura wutan sonta a

ransu, inhar zata shiga waje

saita samu maza masu sonta. Amma

bata iya tsayawa ta sauraresu, domin

tana tsoron yayanta, tana gudun abunda

zai bata masa rai, bata so tayi masa laifi.

Don waya ma ya hanata rikewa, sai wata rana

data je gida Abba ya bata wata mai

kyau, amma ta rinka dari-dari da tsoron

gaya masa. Sai Ahmad ne ya dauka da

gudu ya kai masa yana gaya masa

Abbanshi ya bawa aunty maminshi waya.

Saida ya mata gargadi sosai akan in ta sake yaji

ta bawa wani saurayi numbar

wayarta sai ranta yayi mummunan baci,

don haka take kiyaye wa. Ni’ima anzama

babbar budurwa sosai, tana karatun

diploma har ansa mata ranar aure har ma

ankusa bikin. Aunty sadiya tanada ‘ya’ya biyu,

hafiz da

sajida. Mansura kuwa tun daga Ahmad

bata sake haihuwa ba, tace dama saiya

shekara biyar, toh gashi yanzu ya

shekara biyar din. Zainab yarinya mai

hakuri, ga hankali da nutsuwa, tana da kwazo,

don tayi saukar qur’ani yanzu ta

juya hadda. Yau asabar tana tasowa a

daga islamiya ta ware kitson kanta tana

son zuwa salon, harta fara tunanin ta

yanda zata tambayi yayan nata fita, bata

son yayi mata fada. Zainab tayi murmushi tace

don Allah

aunty gayawa yaya zanje salon. Tace

“bazan je inda yake ba munyi fada.” tace

haba aunty, don Allah kije ki lallabashi ki

bashi hakuri, ki tambayo min nidai na tafi.

Ta tabe baki tace hakuri? Hakuri fa kika ce? Don

ya kara wulakantani.” zainab ta

kalleta cikin mamaki, Ahmad ya fito da

gudunshi da hijabin nata a hannunshi

yana cewa “aunty mami gashi mu tafi

kinji. Tace jeka gayawa Abbanka cewar

zanje salon. Dai-dai lokacin Aliyu ya shigo,

Ahmad yaje ya rike hannunshi

yana gaya mishi “Abba inji aunty mami

wai zamuje salon. Ya dago kai ya kalleta,

“saida kika dauki mayafin tafiya sannan

zakice a gayamin.”

ta durkusa cikin marairaice warta, tace don Allah

yaya kayi hakuri, tun dazu nake

jiran fitowarka, ba mayafin tafiya

nadauka ba.”

ya gyada kanshi kuje Allah kiyaye.

Tace yaya na gode. Ya bawa Ahmad

kudin salon din, suka tafi direba yakaisu. Suna

yin fakin a gaban shagon salon din,

suna fitowa daga kanta da zata yi karaf

idanuwanta suka hade dana wani dan

kyakyawan saurayi daya zuba mata ido,

tayi saurin kawar da kanta, taja hannun

Ahmad suka shiga ciki, a gurin suka wanke mata

kai suka gyara mata shi,

suka yanke mata farce, suka goge mata

kafa, du da karfa tata sumul take kamar

ta jarirai. Ta fito da youghot da biski ta

bawa Ahmad don kada yaji yunwa.

akayi mata kunshi kunshi sarka a hannu da kafa,

nan da nan ta canja ta kara yin

kyau kamar tauraruwa. Tana fitowa daga

wajen idanunsu suka sake haduwa, yayi

mata murmushi ta dauke kanta da sauri,

ya taso ya tari gabanta. Yace “don Allah

ki taimakamin ki saurareni ki gaya min inda

gidanku yake nazo na sameki a

gida.”

ta mika masa katin yayanta, tayi saurin

shigewa motar direba yaja suka tafi.

Saurayin nan ya sumbaci katin data

bashi yana mai jin dadi da farin ciki haduwarsa

da wannan beb

din.

Suna tafe tana tunanin saurayin data

gani, gaskiya ya hadu, itace da tsayawa

yau harda bawa saurayi katin yayanta,

wyarta ce tes ya shigo, tayi mamakin waya turo

mata tes. To kodai ni’ima ce?

Ta bude tes din, bakuwar lambace bata

san mai lambar ba, ta fara karanta sakon

kamar haka.

“i ‘ve been lucking 4 a chance to tell u my

message, i luv u.” mamaki ya kamata bata

ankara ba ta

kuma jin shigowar wani sakon, ta bude ta

fara karantawa.

This secret has been in my heart enough

now i want to make it.

Ta bude dayar da suka shigo tare, i told you that

i want u to be my wife” a’a

wannan wane irin kalamomi ne masu

rikitar da zuciya, waye wannan? Ta sake

dubawa ta maimaita karantasu gaba

daya. Ba suna to waye wannan? Ita dai

tasan ba wanda suka hadu dazu bane, donshi

bata bashi lambar wayarta ba.

Kuma tasan ba wani namiji data bawa

lambar wayarta, to ko waye?

Next episode by 9pm

via #Justice_hamzat

[1:26PM, 04/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 1**17

Har suka karaso gida zuciyarta tana cike

da tunane-tunane, waye wannan?

Meyasa ya boye mata kanshi bai fadi

sunanshi ba?

Ahmad yayi barci, ta saboshi akafada ta kwantar

dashi kan kujera. Mansura ta

kalleta tace ammafa kinyi kyau, saide kin

dade.” ta zauna tace “hum! Kedai ki bari

aunty, saurayi fa nayi a wajen, kuma

harna bashi katin gidan nan, ina tsoro

kuma kada yazo yaya yayi min fada. Mansura

tace a haba wane irin fada

kuma? Ai yanzu kin wuce wannan ajin.

Don ma keba wayayyi bace kanki a duhu

yake, amma yanda kike kyakyawar nan

gaki danyar budurwa shine dai-dai fara

wankar samari, toke sai rashin waye wa, kullum

kina like a gida, idan zaki fita ki

zurma hijabi saika ce gyatuma. Don Allah

ki waye.

Tace, to aunty wai ya kike so nayi ne,

wace iri ne ce wayewar?

Haka dai ta ringa ce mata tanasa matsatsun

dinki ita kuma zainab tace ba

haka Allah yace ba, ka waye akan

addininka shine wayewa, aunty sadiya ce

ta shigo da sallama da kanwar mijinta

yasira, a’a auntyn mu barka da zuwa.

Zainab taje ta rungumeta, tace yasira rabon goron

harda aunty kuke yi ne?

Tayi dariya tace to ya zanyi tace da ita

za’a kawowa zeey autarsu na fati.

Zainab tace fati yasira, anya zan dai zo

miki yini, yaya bazai barni naje miki fati

ba. Sadiya tace haba don Allah, ke bari zakiyi

yasan zakije? Kice masa gidana

zaki zo, ni’ima ma nan zata zo saimu tafi

tare, nayi muku ankon fati da

gwagwaronsa, harda takalmi set din

kayan.”

zainab tasa ihu, “sai auntyn mu, kedai kina son

fito da ‘yan kannenki.

A to inbanyi muku ba wa zanyi wa, ku

kenan fa kannen nawa mata, ai dole na

gyaraku.

Mansura tace, “ai wannan autar taku

saikin dage mata don taki wayewa, kullum kanta

a duhu yake.

Sadiya tana dariya tace ai laifin mijinki

ne, bakina kallo yke takura mana auta ba,

ki rinka hanashi kin barin ta da yake ta

sake.

Mansura ta kama baki tace rufamin asiri da

yayanku, idan nayi magana tawa ce

take yin zafi, ranar jumma’a wato ranar

fatin, mansura ta shigo dakin zainab

tace, “bazaki je ki fada masa maganar

fatin ba saiya fito? Tace don Allah aunty

gaya masa.” tace kinsan in ni na gaya masa cewa

zaiyi inason koya miki yawo.

Ta mike bari naje, aunty kiyi min addu’a

Allah yasa ya barni.” tace “to Amin.”

yana shirin fita mansura ta kawo masa

jakarsa, zainab ta fito ta durkusa tace

“yayana. Bai kulata ba yace “uhm! Ya akayi?

Yaya dan Allah zanje gidan aunty

sadiya? Me akeyi a gidan?

Bikin kanwar mijinta ake yasira, shine

nake neman alfarma dan Allah yaya

kabarni naje. Ya daga kai kada ki dade. Tace to

yaya

nagode.” yana fita ta tafi gidan sadiya,

direba ya kaita. A can ta tarar da ni’ima

suka rugume juna suna murna. Kinyi sa’a

‘yar uwa ya barki.”

kinganni dai, yayan namu ne sai a hankali. Amma

yau ba laifi fuskar tasa a

sake take. Hu! Aunty wannan material din

fa? Tana daga su tana yaba kyansu.

Tace Abban yasir ne ya kawomin su

tsaraba, amma naga sun zo akaya zan

sai muku. Yauwa auntyn mu kina burgemu fa.

Suka

gama tsra shirinsu na zuwa fati, wani

hadadden material ne da aka sake fito da

kyansa da wani dinki mai kyau.

Gaba daya su ukun sunyi kyau amma ba

kamar zeey da kamar don ita aka yoshi. Suna

bayan motar sadiya da mijinta suna

gaba. A gidan fatin suka bi bayan amarya

da ango suka rakata har mazauninta.

Yaron sa’adu bori yanata kida da waka

‘yan mata sunata rawa daga baya aka

tsaya da kidan, babban kawar amarya tazo ta yi

addu’a tareda yiwa bakin da

suka zo barka da zuwa. Daga nan ango

da marya suka tashi suka ja zugar

kawaye da abokai suna biye da bayansu

har wajen masu sabis. Kowa shiyake

sabis din kansa. Zainab duk inda tyi idon mutane

ne akanta, ita kallon ya isheta,

don bata saba da irin wannan shiga ba,

ta saba kullum tana hijabi, to ita abunda

yafi damunta ma sha daya har tayi, tana

jin soron yaya fa.

Amma yaya sadiya da mijinta sunce har dakinta

zasu rakata su bawa yaya

hakuri.. Wata kawarta tazo taja

hannunta, dole saita yi rawa. A hankali

take juyawa, kusan maza hudu ne suka

rufa kanta suna mata liki.

Kamar daga sama yaya Aliyu ya diro wajen, saiji

tayi an damki hannunta. Ta

juyo a tsorace dan ta razana, ganin

yayanta ya hade rai kamar wanda bai

taba dariya, saita firgice ta tsorata. Ya

funciki hannunta yayi waje da ita, ya

bude mota ya turata ciki shima ya shiga. Ta

takure a tsorace take, saboda tasan

halin yayanta sarai, akwai zafin zuciya.

Aliyu ransa ya baci sosai ganin maza

suna yiwa zainab liki, ba dai sonta suke yi

ba? Wani abu ya soki kirjinsa, ya rinka

ganin bibbiyu a idonsa, yayin da motar ta fara

tangal-tangal kamar zata kifa.

Zainab ta fara salati ta baro kujerarta ta

rungume Aliyu tana ihu tana salati.

Tirkashi! Mu hadu a littafi na biyu,

waishin menene ya soki zuciyar Aliyu?

via #Justice_Hamzat

[9:14AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**1 &  2**2

 

A hankali ya dawo hayyacinsa,

yaci gaba da maimaita salatin daya ji zainab tanayi. Saida

taji ya samu nutsuwa sannan itama tafita daga tsoron data

shiga, tayi saurin komawa

wajenta. Yaci gaba da tukin a hankali cikin nutsuwa, zainab

ta fashe da kuka tace, “don Allah yaya kayi hakuri bazan

kuma ba. Don Allah ka yafe min.” da kyar ya iya bude

bakinsa yace,

zainab meya hadaki da wa ‘yannan maza da suka

rufu suna yi miki liki? Tace “wallahi yaya ban san su ba, ban

taba ganinsu ba sai yau. Kuma ko magana bata hadamu

dasu ba, wallahi ina zaune

wata kawata tajani gurin rawar, kawai sai gani nayi anamin

liki. Kayi hakuri kaji yaya bazan kuma ba. Ya daga kai, yace

shikenan ya wuce.”

da sassafe aunty sadiya tayo mata waya tana tambayarta,

“ince kodai yaya bai dake kiba? Tace

baiyi min komaiba.” ta bata labarin abunda ya

faru, suka yi dariya gaba daya. Bayan sun gama

hirarsu, ni’ima ta bugo ta tambayi abunda yaya

yayi mata. Itama ta bata labarn yanda suka yi.

Ni’ima tace, “dadina da yaya akwai zafin zuciya,

amma inka bashi hakuri shikenan komai ya wuce.

** ** ** ** *** ni’ima ce ta shigo, suka rungume

juna, suka zauna talatuwa ta shigo musu da

abinci, ni’ima tace, aunty sadiya fa tace muje

goben ta sai mana material din, kala uku ta dibar

mana. Zainab tace sai auntynmu, gaskiya mun

gode, kawai daga can sai mu wuce gurin dinki.

Ni’ima tace daman mama ma zata karba mana

kudin dinki awajen Abba.” ta mike, tafiya zanyi.”

haba yaya ni’ima tun yanzu? Wallahi inkin zo

bana so ki tafi.” ta dafa kafadarta, kiyi hakuri

zainab, na baro yaya a gida, kinsan yanzu zai

taho, idan ya sameni anan, gobe inkin tambaye

shi zuwa gidan aunty sadiya cewa zaiy ni nake

zuwa nake saki yawo. To shikenan yaya ni’ima

sai goben.” sha biyun dare ta tashi tayi na filla,

tai ta addu’o’inta tayiwa mahaifiyarta addu’a tare

da mahaifinta, da fatan Allah ya bashi zaman

lafiya da matar da ya sake aura. Ta gama

shirinta, ta gama tofa addu’o’inta ta kwanta, taja

bargonta zata rufa. Yayinda ta jawo wayarta zata

kashe, dai-dai lokacin da zata kashe, sakkonni

suka shigo. Mamaki ya sake kamata, ta fara

budewa ga abunda yake ciki. “wah! Zeeytah

tsananin sonki da kaunarki kullum yakan hanani

bacci. Zeeytah yaushe zaki ban dama na

bayyana gareki, na matsu na aureki. Na jini

manne a kirjinki ina bacci kona ji sauki da

radadin sonki. Wayyo zeey kece rayuwata.”

subhanallahi, waye wannan? Na shiga uku! Allah

yasa dai ba aljani bane. Ta sake bude sakon ga

yanda yake. “zeeytah kaunarki takai makura a

zuciyata, dab nake da rasa rayuwa saboda zugin

sonki. Wai yaushe mafarkina zai zamo

gaskiyane? Na jiki kan kirjina ina lallaminki ina

riritaki, na dameki da soyayyata mai hanani

bacci. Ta cillar da wayan tana cewa na shiga

uku! Waye wannan? Waya ke son rikitamin

zuciya? Mutumne ko aljan? Allah gani gareka,

Allah ka kawomin sauki. Dakyar tunani ya barta

tayi barci. Ranar alhamis da yamma bakonta

yazo, saurayin da suka hadu a kofar wajen salon.

Ahmad ne ya shigo da gudunsa yana cewa,

“aunty mami kizo inji wani dan gayu a mota mai

kyau. Tace “dan gayu a mota mai kyau? Yace ka

kirawo ni? Eh, aunty mami, yace nace wai

mutumin da muka hadu dashi ranan.” mansura

tace mutumin da kikace kin bawa katine. Saiga

talatuwa ta shigo tana dariya, tace “don Allah

aunty mami. Yanda Ahmad yake gaya mata, tace

don Allah yau dai kije kada ki kori wannan, ki

taimaka kije. Mansura tace kai mata kujera

farare guda biyu harabar gida, yanzu zata zo.

Mansura tace kije ki shirya, ba kyau fa

wulakanci.” ta mike ta shiga dakinta ta sako

hijabinta ta fito. Mansura ta kalleta tayi tsaki,

meye haka? Yanzu zance ma saida hijabi zakije?

Wallahi kedai gidahuma ce kije ki yafo karamin

mayafi.” tace don Allah aunty ki kyaleni, yaushe

zanje gaban wani kato da dan karamin mayafi ya

karewa halitta na kallo ya cuce ni? Mansura tace

saiki tayi ‘yar kauye kawai.” tayi murmushi ta

wuce ta tafi harabar gidan. Yana zaune akan

kujera, ya rinka sakin murmushi dan yaga ta taho

gareshi. Ta zauna tace barka da zuwa.” ya amsa

“yauwa zainab ya gida, kun dawo? Ta amsa da

“lafiya lau. Yace “to dama gaskiyar abunda yake

tafe dani, na ganki kuma gaskiya naji ina sonki,

ina kaunarki, ina matukar son na aureki. Shiyasa

nake neman amincewarki, daki amince ki aureni

dan mu zamo abokanan rayuwan juna nan gaba.”

tace mishi, bakomai Allah ya zaba mana mafi

Alkahiri. Yace Amin. Kin amince naci gaba da

zuwa kenan? Ta daga masa kai. Yace naji dadi,

ubangiji Allah ya tabbatar mana da alkahairi.”

talatuwa ta kawo mishi ruwa da lemo, zainab ta

zuba masa ruwa da lemon a kofuna, tace masa

bisimillah mana, kasha.” ya dauka yana sha suna

ci gaba da hirarsu, yayi mata bayanin kansa.

“nidan garin nan ne, muna zaune a unguwar

gandu. Mahaifina Alh sani yana da mata biyu da ‘ya’ya

tara, nine na uku a gidanmu sunana nura.

Nayi karatu na firame da sakandare a garin nan, inda nayi

jami’a a dubai. Ina kan harkokin mahaifina na bangaren

kamfanin motoci.” ta jinjina kai, tace naji labarinka, Allah

yayi mana jagoranci na Alheri.

 

ALLAH yayi mana jagoranci

na Alheri, sukayi sallama zai tafi ya bata rafar kudi taki

karba. Yaita mata magiya data karba, tace don Allah yayi.

Hakuri bazata karba ba. Ta wuce gida. Tes ne ya kuma

shigowa wayarta, ta

bude ta karanta kamar haka. ” i luv u zeey, luv is like d

music of the nature the note ‘re heard by the loving heart

that is tender nd pure, i care 4 u,

i miss u, na i luv u.” ina sonki, ina sonki, na dade cikin

sonki. Ki soni zeey shine samun kwanciyar

hankalina. Zeey yaushe zaki amince dani na

bayyana gareki.” ranta ya kuma dagulewa, wai

waye wannan ne yake damunta da kalamai?

Maye nufinsa? Ta mayar masa da amsa kamar

haka. “dan Allah waye kai? Me kake nufi da

rayuwata? Don me zaka boyemin kanka? Nifa

marainiyace dan Allah ka rabu dani kada ka cuci

rayuwata. Tana tura tes din mintuna biyu da

tafiya waya ta shigo ta kama ringin, tana dubawa

lambar da ake yo mata tes da itace. Tsoro da

fargaba suka kamata, ta kasa daga wayar harta

katse. Aka sake bugowa ta sake katsewa, sai

akaro na uku sannan ta iya dagawa, muryanta

can kasan makogoro tace hello! Wake magana?

Cikin taushin murya da kyakyawan lafazi yace,

“salamu alaiki ya hasken ruhina. Sanin

muhimmacin sallama shiyasa ta amsa, amma a

zuciyarta tana cike da tsoro da fargaba. Ya ce,

“haba zeey, kada ki taba mugun tunani akaina,

zainab ni masoyinki ne na usuli mai burin gina

miki ingantacciyar rayuwa. Zeey ta na dade cikin

tafarkin kaunarki, tun kina kankanuwa zainab

Allah ya jarabceni da azababbiyar sonki. Zainab

ki amince da soyayyana kona samu dadadden

burina ya tabbata, wato ya zamo na aureki.” to

waye kai? Aina kake? Ya sunanka? “to ni sunana

haidar, kuma ni haifaffen garin nan ne, sai dai

aikina daya sa bana zaune anan din dindindin.”

to taya akai ka sanni, kuma waya baka lambar

waya ta? to nasanki ne idan nazo garin ina ganin

sanda ake wucewa dake a mota zuwa makaranta

da safe, ina ganin sanda direbaku yake daukoki

shidda na yamma. Lambar wayarki kuma wata

rana na tsaya zan sai kati a wajen wani me dan

kes din katuna waya da wayoyi, saina ga wata

mata, ina ganin mai aikinku ce tazo da wayarki

wajen. Saina ji tace bari taje ta dawo kafin yasa

mata katin. To tanan na samu dama na dauki

lambarki. Shikenan bayanin da kike sonji? Tace

a’a meyasa ba zaka fito na gankaba kake yomin

tes? Yace haba zeey ina yo miki tes ne danki san

dani kada nazo miki gaba gadi ba tare da saninki

ba, shiyasa nake yo miki tes dan nasamu

amincewarki tukunna kafin nazo. Da fatan kin

gane? tace na gane. Sannu a hankali soyayya da

shakuwa ta shiga tsakaninsu, don yanzu zainab

ta saba da soyayyarsa, sai sukai sha biyu na

dare suna hirar soyayya, amma har yau basu ga

junansu ba, daga waya sai tes ke hadasu. Saidai

har yau ta kasa gayawa yayanta Aliyu maganan

saurayinta haidar da yake neman amincewarsa

daya fara zuwa zance wajenta, sai dai har yanzu

suna tare da saurayinta nura, du sati ranar

Alhamis yake zuwa wajenta, basu taba haduwa

da yayanta Aliyu ba. Yau ma nura ne yazo, ta fita

harabar gidan, yana zaune kan farar kujera da

tebur fari zagaye a gabanshi, dayar kujerar tana

kallonshi. Zainab tayi masa sallama ya amsa da

fara’arsa, taja kujera ta zauna suka gaisa fara

tambayar ya bayan rabuwa. Talatuwa ta kawo

masa lemo da cin-cin da meatfay yana ci yana yi

mata hira, har yanzu bata wani sakewa dashi ba,

amsarta daga um sai a’a sai dai kuma tayi

murmurshi. Wayarta tayi kara tana dubawa tayi

ta amsa da hello! Mazaje ya akayi ne? Zeey ta

inakan hanya yau na taho gida, na gaji da

tunaninki, inaso zan zo muga juna.” kai amma fa

naji dadi mazan jiya.” yauwa zeeytah, nagode,

shigowar safe zan miki dan ki ganni sosai.”

bakwai da rabi zanzo gidanku, nizan kaiki

makaranta muna tafe muna hirarmu mai dadi, na

jira tunda jumma’a ce ba dadewa ba zakuyi a

tasoku, mu sake tahowa tare muzo gida mu wuni

muna hirar soyayya.” Allah mazan jiya? Allah

zeeyta, saina iso. Ok mazaje, bey.” nura ya

kalleta yace dama kina hira haka? Ko donni

bakya sona ne, naji har sunaye kika rada masa

mazaje dan mazan jiya. Tayi murmushi tace ba

haka bane, bazan iya fadar sunan sa bane

saboda sunasu daya da yayana, shiyasa nake ce

masa mazaje. Inace masa mazan jiya ne saboda

yanayin aikinsa. Ta tsiyayo lemo ta miko masa

ungo yi hakuri karbi kasha. Yace saidai ki bani

abaki in kina so nasha. Tace “a gaskiya baza

iyaba, ka karba kasha da hannunka kawai.” ta

miko mishi. Shikuma ya kawo baki yana so ya

kurbi lemon. Dai-dai lokacin Aliyu ya shigo get

din gidan idonsa ya gano mashi. Yayi wani irin

kogi da motar. Tsoro yasa zainab ta saki kofin

lemo ya fadi. Aliyu ya bude motar ya fito kamar

namijin zaki, ransa abace fuskarshi a daure

kamar bai taba dariya ba, da kakinsa ajikinsa na

soja ajikinsa. Yana taku cikin kasaita ya nufo

inda suke, tuni zainab ta hankade tebir din

gabanta tayi cikin gida a guje. Cikin kakkausar

murya ya nunawa nura dan yatsa yace “waya

baka iznin kula kanwata? Zoka fice kada na sake

ganinka da ita. Zoka fice. Nura yana so yayi masa bayani

ya daka masa tsawa tareda

[9:14AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**3 &  2**4

 

NURA yaba so yayi masa bayani ya daka masa tswa tare da

nuna masa kofa, da sauri nura ya fice ya shiga motarsa

yaja. A fusace ya

shiga

gidan, zainab duta gigice ta rukunkume

mansura

tana cewa “aunty ki ceceni, ki ceceni aunty. Mansura tana

ta tambayarta meye? Ta kasa gaya

mata saboda rudewa da gigita da take ciki. Cikin takunsa ya

shigo, ta saki mansura tai daki da gudu ta turo kofar, da

kafa ya daki kofar

dakin ta bude, ya zari wayar radio, ta rude, tana

bashi

hakuri yace “uban waye ya baki iznin zance

da

wani?

Harda bashi lemo a baki. Dama abunda

kikeyi

kenan in ba na nan? Ya tsula mata wayar, ta

gigice ta rukukume mansura. Mansura ta

tareshi tana masa magiya yayi hakuri. Ya hankade ta,

yace ina nan zuwa kanki, zaki san kinsata

zance. Mansura tayi saurin barin gurin danta san

halinsa. Ya sake tsulawa zainab, ta

rukunkumeshi

tana ihu, “don Allah yaya kayi hakuri, wallahi

bazan sake ba kaji yaya, kayi hakuri yayana, wallahi dukan

da zafi. Allah zankiyaye bazan sake

ba.” ya cillar da wayan, tayi saurin cikashi,

yayi dakinsa. Zainab ta zauna tana kuka. Mansura ta

dagota tayi dakinta da’ita tana rarrashinta.

Wallahi bansan zai dawo yau ba, shida baya dawowa sai

jumma’a da mangariba, to me ya kawoshi gida yau

Alhamis?

Ya kwalawa mansura kira, ta fito da saurinta.

Ya rinka gaya mata maganganu, yaci mata mutunci.

Yace wallahi wannan shine na karshe, du

sanda

ta sake barinta ta fita zance wajen wani sai ranta yayi

mummunan baci.

Ya fice ya bar gidan, mansura tace,

masifaffe,

kada ka barta tayi zance ta samu mijin aure, saika

kwadantata kaci.” zainab tana daki tana sheshekar kukanta

taji wayanta na ringing.

Ta duba, saita daga tace hello! Mazaje. Yace a’a zeeyta

yana ji haka? Du yanda akayi akwai

damuwa, gaya min zeeyta meyake faruwa?

Cikin sanyinta tace lafiya lau mazan jiya ba komai.

A’a daga jin muryar nan ba kalau ba, bazan

iya hakurin zuwa gobenba, bari yanzu nazo naji

ko meye.” tayi saurin cewa a’a mazaje kada kazo ka bari

tukunna saina gayawa yayana.

Haba zeeyta ki bari nazo mana muga juna, yanzu du donki

da nake bazaki bari nazo ba?

Tace, “kabari sai wani lokacin.

Yace don bakya sona baki damu dani bako? Ya kashe

wayar tasa.

Ta dafe kanta, “ya Allah sharrin soyayyar kenan, da da bata

kula kowa tayi zamanta lafiya, yanzu

kuwa daka fara soyayyar tata gashi ta fara cin karo da

matsaloli.” ita dai gaskiya tana son

haidar, don bata taba ganinshi ba amma yanda take jin

muryarsa da lafazinsa tasan cikakken

mutum ne me mutunci da kamala

baza taso ace ta rabu dashi ba dan bata san wa zata hadu

dashi agaba ba.

Ta dauki wayarta ta buga masa, ringin daya ya dauka, yayi

shiru. Cikin sanyinta da marairaita tace “mazaje fushi kake

yi? Yayi mata shiru

cikin shagwaba tace, “mazan jiya, kada kayi fushi

dani, baka sani bane wallahi ina cikin matsala shiyasa.”

cikin sanyi rai yayi ajiyar zuciya, yace wacce irin

matsalace? Ki gaya min mana.” dazu yayana

yazo ya sameni ina zance, baka ga yanda ransa ya baci ba.

Yaita mana fada nida aunty na.

To idan kazo ya ganka kaga bansan abunda zai kuma

faruwa ba.

Wallahi bana so naga ran yaya abace,

ballantana kuma ace nina bata masa, wallahi raina yaki dadi

duk nadamu da fushin da ya keyi, don ni

yaya shine uwata.

Haidar yace gaskiyane na gane, tunda ina sonki dole na

tayaki biyayya ga iyayenki da ‘yan

uwanki, zan nemi yayan naki na gaya masa ina

sonki, ina so ya amincemin na fara zuwa zance

gurinki kina ganin hakan yayi?

Tace, yauwa mazaje nagode.

Yace kada ki damu na gaya miki, i care 4 u, i miss u, i luv

u.”

tace, “nima haka” tayi saurin kashe wayar tana dariya.

Shima daga can dariyar yayi yana mai farin ciki yanda ya

samu karbu awajen yarinyar.

Sai goma na dare sannan Aliyu ya koma gida, yana zaune a

falo, Ahmad yazo ya zauna a jikinsa

yana dan lallbashi har yayi bacci. Mansura tana

jin shi bata fito ba, ita a dole fushi takeyi

akan fadan da yayi mata akan zainab.

Zainab tana sanye da kayan bacci kwance akan

gado ta kasa bacci, tunaninta yana kan

yayanta da yake fushi da ita.

Ta mike ta daura zani tasa hijabinta akanta, ta

rufe jikinta. Ta bude dakinta ta fita falon, tayi

sallama cikin sanyinta da yanayi na tausayi aciki,

ya amsa sallamar, ta zauna akasa kusa da kafarshi, tace

yaya don Allah kayi hakuri, Allah ya

huci zuciyarka, don Allah yaya ka yafe min bata maka

danayi.

Yace, zainab kin batamin rai, daman inba na

nan zance kikeyi? Meyasa kike kula samari?

Don Allah kayi hakuri yaya bazan kuma ba. Yace, “gaya min

da mutum nawa kike yin zance.

Wallahi yaya shikadai ne yake zuwa.” to

kuma suwa kike waya dasu? Wallahi yaya shima shikadai

ne.” gaya min sunansa?

Tayi murmushi sunkuyar da kai. Yace kina sonshi? Ta rufe

idonta bata ce komaiba. Yace “nida burina naga kinyi digiri,

ashe hakan bazata

samu ba, samari bazasu barki kiyi karatu ba, ko auren za

ayi ne?

Yace ga maganin na dauki kisha kada jikinki yayi ciwo.

Tace to yaya nagode. Ta dauka tayi dakinta. Ya bita da

kallo yana kissima abu a zuciyarshi, yayi murmushi ya

lumshe ido yana tunani abunda yake tabo ranshi. A daure

ayi like da comments don hakan ke kara mana kwarin

gwiwa

 

ZAINAB sunyi candy, ita dai bata samu hutu ba ta fada

kacaniyar bikin ni’ima. Ranar Alhamis akayi

kamu, kuma dije ya cashe musu da kida, ranar

zainab ta ajiye ustazancinta tasha rawa. Da

daddare yunwa ta isheta, gata ba gwanar cin

abinci, daman ga abun ya hade ma da hidimar

biki. Tana cikin kawayen ni’ima da zasuyi kwanan

biki anata hira da ita, kowa sonta yake yi, suna

son hira da ita, don sha’awa take basu. Gata fara

kal kyakyawa, gata da fara’a ga ladabi, don

kowacce aunty take ce mata. Tace yaya ni’ima

nifa yunwa nake ji.” tace baga tuwon shinkafa ba

da zafinsa? Tace tuwo yaya ni’ima, ai ba zan iya

ci ba.” ta dauki wayarta ta buga, “hello, yayana

yunwa nakeji.” ya hauta da fada, “don me zaki

zauna da yunwa? Cikin shagwaba tace, “to yaya

su basuda komai sai tuwo.”

mintuna kadan sai gashi a gidan da youghot da

ice-cream, da kaji uku manya ya kawo mata. Ta

bude tana ci, ni’ima tace ‘yar gatan yaya kenan.”

sakina cikin kawayen ni’ima tace, yarinyar nan

kinaji da gata, irin wannan cima da kikeyi dole

kiyi ta faman kyalli, baki da matsala.”

zainab tayi dariyarta mai ban sha’awa tace,

yayana ai shine babata, baya barina cikin

damuwa, suna cin nama da youghot da ice-cream

tana basu labarin yayanta da yanda take tsoron

shi da gudun bacin ransa. Da safe ta shiga gurin

babanta ya bata rubutun tsari da magani a dame

da kindirmo, da tsumi da zuma. Tun tana ‘yar

shekara sha uku babanta yake tsumata da

magani, shi tausayinta yake ji, yana ganin tunda

ta rasa uwa ba mai kula da ita ta wannan

bangaren.

Kullum addu’arsa Alah ya bata miji na gari wanda

zai kula da ita, ya tallafi maraicinta. Washe gari

suka tafi gyaran amare, akayi musu dilka da

halwa, jikinsu ya rinka tsantsi da sheki.

Suna gidan kunshi haidar yayo mata waya, “hello

mazaje ya akayi ne? Nifa na matsu zeeytah so

nake kawai na aureki, zainab kaunarki tayi min

yawa, zainab yaushe zamu hadune? Yaushe zamu

ga juna?

Karka damu mazan jiya gobe kazo daurin auren

yayata saimu ga juna.” yauwa zeeytah zan zo

miki cikin farar shadda da bakar dara, da farin

takalmi. Zansa babbar riga, zansa farin agogo na

azurfa da farin gilas. Tara da rabi zanzo, sannan

saura rabin awa a daura auren kenan, tunda

goma za a daura.

To naji dadi wallahi sai goben.

Ranar daurin aure zainab tagama tsara

kwalliyarta cikin wata dakakkiyar shadda mai

tsadar gaske da yayanta yayi mata biki, ta nada

dan kwalin kamar nadin gwaggwaro, tayi kyau

sosai.

Haidar yayo mata waya cewar ya iso yana dakin

saukar baki na gidansu, ta kara feshe jikinta da

turare ta fice tayi dakin baki. Tayi sallama cikin

sanyinta, ta hango bayanshi cikakken mutum mai

zati dakyan kira, irin mazan nan masu wahalar

samu. Kamar yanda ya gaya mata zaiyi shigarsa

haka ta gani. Tayi sallama tare da cewa hello,

haidar barka da zuwa.

Yana juyowa hanjin cikinta ya hautsina, nan da

nan ta dabarbarce ta nemi nutsuwarta ta rasa,

bakinta ya dabarbarce. Dakyar ta iya hada

sunansa ta fada, tace, yaya Aliyu!”

ta juya cikin gida aguje ta fada daki tasa kuka

tana jimamin meyake shirin faruwa da ita? Karfe

goma dai-dai taji an daura auren ni’ima da

hamza saurayinta. Dai-dai lokacin da aka sake

daura auren Aliyu da zainab.

Zainab bata karasa jiba ta yanke jiki ta fadi, inda

mansura ta sheko da gudu dakin data ga zainab

ta shiga tana cewa, “ni zaku yaudara ku ciwa

Amana? Yau zainab koni ko ke, saina kasheki

nayi maganin maciya amana.” inda ta shaki zainab.

Zainab ta rinka kakari. Sadiya da ni’ima suka yo

dakin da gudu, suka cakumi mansura suka cillar

da ita gefe suna cewa, ke kada kiyi mana hauka,

‘yar uwar tamu zaki shaka kina kokarin kashewa?

Umma ta shigo a guje ta dago zainab ta

rungumeta tayi dakin da ita. Mansura ta rinka zage-zage,

“ni za ayiwa rashin mutunci da tozarta na rike yarinya tun

tana ‘yar shekara

takwas, sirrina babu wanda bata saniba, na riketa

kamar ‘yar cikina, amma cin amanar da zai biyo

baya kenan ku aurawa mijina ita?

Ta rinka deban kayan wajen tana watsi dasu.

Sadiya tace mudai kiyi mana shiru kada ki bata

mana taro.” ta kawowa sadiya duka, mutane

suka tare suna bata hakuri, amma tijara take tana

zuba ruwan rashin mutunci. Saida ummi tayi

waya gidansu babarta da yayarta suka shigo

suna tambayar meya faru? Mansura ta fada jikin

babarta tana kuka, tana cewa hajiya kinga

abunda suka yi min, kina kallon irin sakayyar da

sukayi min, du kyakyawan rikon dana ma zainab

yau sunga ta mike ta zama mutum, shine suka

aurawa Aliyu ita.” ta karasa tana kuka. Hajiya da

saratu suka saka salati tare da cewar, amma

Aliyu da zainab sunci amanarki sun tozarta ki, sun

wulakantaki, amma kansu sukayi wa, yanda

sukayi miki Allah ya tozartasu, taho mu tafi, aure

ne bakya yi su rike dansu. Bayan zainab su kara

aura masa mata uku su zama hudu.

Daman munafunci daya sa aka kai miki zainab

din don ta gama ganin sirrin gidan, ta riketa

Amana tamkar uwarta, amma sakayyar da zakuyi

mata kenan. Don kanku ku rike Aliyu, Allah ya

bata wanda ya fishi, suka jata suka nufi nasu gidan sunata

sababi.

Tofa Littafi ya canja salo

[9:15AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**5 &  2**6

 

SUKUWA maza ‘yan daurin aure, ana gama daurin

aure suka nufu daula hotel, don cin abincin daurin

aure, wato walima ta zama kadai ‘yan daurin

aure.

Aliyu ba abunda ya dame shi sai washe baki

yake, yana ta gaisawa da mutane. Da yawa

mutane sunata mamaki, don sun san miskilanci

da rashin yawan dariya irin na Aliyu, amma yanzu

ya kasa rufe bakinsa saboda fara’a da amsa

gaisuwar jama’a da masu sanyawa auren nasu

albarka.

Cikin gida kuw, masu gidan yaransu da manyansu

cikin farin ciki suke da wannan aure na Aliyu da

zainab, saboda kawunan su a hade yake.

Su sadiya dasu ni’ima kuwa sai murna suke suna

zuba shewa da tafi.

Zainab kuwa tana dakin umma kudundune cikin

bacin rai, duniyar tayi mata zafi, ta rasa mai yake

mata dadi. Ita bata ga laifin auntyn ta ba, dole

tace taci amanarta. Mai auntyn ta rage ta dashi?

Ta dauketa kamar ‘yar cikinta, amma yau

sakayyar da zata yi mata kenan ta aure mata

miji? Ta sake fashewa da kuka.

Meyasa haka? Meyasa yaya Aliyu mata haka?

Tana ganin yaya Aliyu mai rikon gaskiya da

amana, ashe shima zai iyabin son zuciyarsa. Ya

aureta yaci amanar matarsa? Wayyo ni Allah!

Kaico da wannan rayuwar, ranta ya rinka kuna,

makogwaronta ya rinka daci, ta rinka jin wani

yuuu a kanta. Ta dafe kan tana jin wani sara

mata da yake yi, wasu duhu suka gifta ta idonta,

idanuwanta suka rufe tayi baya ta fadi

numfashinta ya dauke.

Umma da ummi suka shigo dakin a lokaci daya,

suka ganta a wannan halin. Gaba daya sukayo

kanta suka dagota suna salati, umma ta

rungumeta tana salati tare da nanata kalmar

innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.”

yayin da ummi tayi falo da sauri tana salati,

mutane suka yo caa akanta suna tambayarta

lafiya? Ta rude sai fadi take ku kirawo mana

direba, zainab ce ta suma.”

sadiya da ni’ima suka saka ihu suka yi cikin

dakin. Dakyar aka samu direban aunty sadiya a

waya, don duka direbobin sun kwashi mutane

suna can daula hotel.

Aka dauki zainab bata san inda kanta yake ba,

suka tafi asibiti. Sunata neman wayar Aliyu gaba

daya wayoyinsa a kulle suke saboda jama’a.

Haka ta Abba da daddy ma du ba’a samu.

A asibiti kuwa gaba daya matan sun cika daki

sunata koke koke, su umma da ummi kuwa da

mama matar baban su zainab, sunyi jugum-

jugum sai salati suke suna hailala a zuciyarsu,

tare da nemawa zainab lafiya cikin zukatansu.

‘yan nurse din duk suka korasu falon asibitin,

sannan likita ya fara yiwa zainab taimakon

gaggawa.

Cikin ikon Allah ta farfado, sai likitan yayi mata

allurar bacci donta samu nutsuwa.

Sai sha biyu aka tashi daga walima, sannan aka

samu lambar wayar Abba da daddy. Suna jin

zainab a asibiti suka ce subhanallhi, meya faru

kuma haka? Umma tace, “shidewa tayi ta zube a

sume.” to Allah sauwake gamu nan zuwa.” Abba

ya binciko Aliyu cikin abokansa yace kaifa muke

jira ka gama sallamar abokanka kazo muje wata

‘yar anguwa. Aliyu ya amsa musu cikin

girmamawa, bai tsaya tambayarsu ina zasuje ba.

Aliyu yana gaba kusa da direba, Abba da daddy

suna baya. Direba ya kaisu asibiti, tunda suka

shiga gaban Aliyu yake faduwa, yake tunanin me

kuma ya faru?

Direba ya tsaya suka fito, suka nufi falon asibitin

jikin Aliyu a sanyaye,

yana hango su umma da ummi, ni’ima da sadiya

da hajiya ya fara karanto kalmar “innalillahi

wa’ina ilaihi raji’un.

Daga nan ya rinka tsintar bayanin da ummi take

musu, na abunda ya samu zainab, ran Aliyu ya

baci hankalinsa ya tashi. Bai tsaya sauraron

ummi datake gaya masa likita yace kada a shiga

inda take ba, da saurinsa ya nufi dakin da aka

kwantar da zainab din.

A hankali ya murda kofar ya shiga

da sallamarsa aciki.

Nurse din data ke gadinta tana zaune gefe daya

tana sauraron farkwanta, tana ganin Aliyu tasan

shi sarai, don haka ta mike ta fito.

Aliyu ya tasaya gaban zainab yana kallonta,

yarinyarshi zainab mai kyau da nutsuwa, lallai ta

shiga tashin hankali, yau daya kawai ta rame

haka. Yasa hannu ya shafi fuskarta, tayi fiyau da

ita. Saiya ga takara fari, dan bakinta lebenta

jajaye, siririn dogon hancinta mai tsawo, ga zara-

zaran gashin idonta, baki lafiyayyen gashin girarta

daya kwanta das kan girar.

Ya zame dan kwallin kanta, bakin gashinta mai

tsawo da sheki wanda kullum yake kasancewa

cikin gyara, yaita walwali yana sheki, shiyasa bai

taba hanata zuwa salon ba, yanzu du sati biyu

take zuwa salon, dan ya fuskanci bata damu da

kitsoba saide kalba.

A hankali ya rankwafa kanta ya hada fuskarsa da

tata, cikin kyakyawan lafazi muryansa can cikin

makogwaronsa yace “zeeyta

ki soni don Allah ki kaunaceni, bani da buri

kullum saina yanda zan mallakeki. Zainab kece

rayuwata, tun ranar da kika fado duniya ina

ganinki Allah ya dasa min kaunarki a zuciyata,

kullum kwanan duniya karamin kaunarki akeyi.

Zeeyta ba kya ceto rayuwar yayanki ba, ki

tsamoni daga cikin damuwa ba? Haba zeeyta, ke

kadaice farin cikin rayuwata.” aka taba kauren

kofar ya dan ja baya. Likita ne zai shigo, yayi

saurin gyara mata dan kwalinta ya rufa mata

maya fi, wai don kada yaga jikinta.

Likitan yayi sallama, yace, ta farka ne? Yace

mishi a’a ya mika masa hannu suna gaisawa..

 

YACE kada ka damu idan ta farka normal zaka ganta.

Sai dai don Allah adinga kiyaye wa abunda zai bata mata

rai.”Aliyu ya gyada kai, yace “insha Allahu za’a kula.

Abba da daddy suka shigo suka tsaya akanta

suna yi mata addu’a da fatan Allah ya bata lafiya.

**** *** ****

saratu da lawisa sun saka mansura a gaba

sunayi mata fanfo zuga iri-iri, lawisa tace, “don

haka nake gaya miki, ki kula da yarinyar nan,

mutum mai shiru-shiru abun tsorone, kinga yanzu

ta kaiki ta baro. Ta gama sanin sirrinki kaf gashi

yanzu ya aureta ta zamo kishiyarki, wallahi ko

kadan kada ki saurara mata, kada ki barta ta

zauna don ba gidan zama tazo ba.

Kuma wallahi ki fito da kudi mu shiga malamai ki

samo kansa, ki mallake shi tsab. Dai-dai da

uwarsa da ubansa ki rabasu dashi, ya zamo babu

wanda yake gabansa saike da yaronki.

Mansura tace, “um! Wannan uban ‘yan taurin kan

zai mallaku ne, tun kwanakin baya fa na kashe

kudi akansa, amma inda kika san dutse haka

yake, kwata-kwata baya lankwasuwa. Kuma

halinsa ne bawai ni kadai yake yiwa hakan ba, ita

kanta yarinyar baki ga yanda yake takura mata

ba. Inta jin tausayinta. Ashe shidai akwai abunda

yake kullawa ransa.

Kiga mutum kullum kicin-kicin dashi ba fara’a shi

ba zai zauna ayi wata hira mai dadi dashi ba

ballantana kiga dariyarsa. Wallahi na gaya miki

sai muyi kwana biyu dashi bama magana, don

haka ma tsani naga yazo garin gwanda yana can.

In nayi magana yace wai dan Allah na rabu dashi

ban iya soyayya ba. Du wayewata yana cewa ban

iya soyayya ba, yanzu daya auri wannan

gidahumar kifin rijiyar aina ga ta yanda zasuyi

soyayyar.

Saratu yayarta tace, to inbanda ke da abunki

wannan ai du shi zai koya mata.” mansura tace,

tabdijam wannan, wannan dinne zai zauna yana

koya wa mace wani abu, ai shi inbanda isa da iko

da gadara babu abunda ya iya. Shifa ason ransa

komai saide kayi masa yana daga kwance, tunda

naga sangartar tasa tayi yawa kai tsaye inya ce

inyi masa abu nake cewa bazan iya ba.

Lawisa tace wallahi na gaya miki namiji ba dan

goyo bane, ko uwarka ka yanka ka bashi inya

tashi mantawa zaiyi ya zuba ma rashin mutunci.”

saratu tace to ba gashi ya mata ta gani, ta rike

‘yar tamkar cikinsu don yankan kauna ya tashi ya

aureta.

Mansura tace shekara takwas ina rikon ‘yar nan,

ko shekara banyi gidan miji ba ya tattaro min

rikon ‘ya, karshe abunda ya sakamin dashi

kenan? Ai duk zasu ci buhun ubansu, mun saka

kafar wando daya dasu. Wallahi saina rushe

zamansu, basu bajin dadin rayuwar, mu zuba su

gani.

**** *** ****

kwanan zainab biyu a asibiti, tayi bacci ta huta

sosai, don data farka take komawa baccin

zuciyarta ta huta ta samu nutsuwa, ta manta da

abunda ya faru.

Dakin cike yake, da mutanen gidan, zainab ta

farka ta yunkura zata mike, umma ta dagota a

hankali tana yi mata sannu. Zainab tayi salati

tace, “umma meye na ganni a asibiti? Tace ishiru

bakida lafiya ne, zo muje ki wanke bakinki.”

ta kamata takaita toilet ta wanke mata bakinta

da fuskarta. Ta dawo da ita ta zauna a bakin

gado ‘yan uwanta da iyayenta suna mata sannu.

Ummi ta hada mata shayi mai kauri tana bata da

kofin, mama ta zubo mata farfesun kaza ana bata

tanaci, taci dayawa.

Aliyu ne ya turo kofa ya shigo da sallamarsa, tayi

kur ta zubo masa ido tana so ta tuno wani abu,

shikuwa murmushi yake yi, ya daga hannunsa

sama yana yiwa Allah godiya.

Ta kura masa ido tana kallonshi ko kiftawa

batayi, a hankali abun ya fara taro mata cikin

kwakwalwarta, tabbas abunda taji ba mafarki

bane gaskiya ne, yanzu ita matar yayanta Aliyu

ne da gaske? Hawaye ya fara zubowa a idonta,

ta mike a hankali tana takawa sannu a hankali ta

nufi inda Aliyu yake a tsaye, ta durkusa a

gabansa cikin kuka, ta rike kafafuwansa tasa

kanta ajiki tana kuka, da sheshsheka tana cewa,

yaya, haba yayana yaza kayi min haka? Haba

yaya kaine fa uwata? Yaya yaza ka rikide ka

zama mijina? Yaya du abunda uwa take yiwa

‘yarta tunda na rasa mamana kai ka fansheta, ka

juye ta a wajena, ka hanani maraicin rashin uwa,

ka zama kaine uwar tawa. Ya zakayi min haka

yayana? Kaifa mijin auntyna ce, matar da na

dauketa kamar ‘yar uwata da muke ciki daya, ta

rikeni da gaskiya da rikon amana, zumunci ne mai

karfi tsakanina da ita.

Yaya ya zakayi sanadiyyar rugujewar wannan

zumuncin? yaya don Allah, yaya don girman zatin

Allah ka taimake rayuwata ka sauwakemin

aurenka ka bani ko waye kaga dama.”

dakin shiru yayi bakajin motsin komai sai

kukanta, mahaifinta ya taso yazo ya dagata, yace

“haba zainab ina ganinki da hankali da ilimi, ashe

sun zamo na banza tunda zaki iya cewa mijinki

ya sakeki.” tace kayi hakuri daddyna

bazan iya zama da auren nan ba, naci amanar

auntyna, da wani ido zan kalli auntyna? Na

yaudareta naci amanarta, naso kaina daddy,

bazan iyaci amanar auntyna ba.”

daddyn yace yau, “zainab yau zan gaya miki

abunda baki saniba, tun kafin Aliyu ya san zai

san mansura mahaifiyarki ta bawa Aliyu ke.” ta

juyo a razane ta kalli mahaifinta. Ya daga mata

kai yace kwarai hakane.

Bazan taba mantawa bayan mamanki ta haifi

sadik da

banda lpia ina fatan zky hkri

[9:15AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**7

 

Bazan taba mantawa ba bayan mamanki ta haifi sadik da

faruk, tana so ta haifi ‘ya mace, ita da Aliyu har nafilan dare

sun sha yi da rokon Allah ya bata ‘ya mace mai hankali da

nutsuwa da hakuri da baiwar ilimi.

Saboda tunda na auri mamanku Allah ya hada jininsu da

Aliyu, komai nasa a gurinta yake.

Shawararsu daya bakinsu daya. Lokacin da mamanki ta

samu ciki kusan tare sukayi laulayin cikin nan, idan tayi

amai shi zai kwashe ya gyara

wajen, du abunda take son ci shine dan aiken

sayowa.

Ranar da aka haifeki kuwa kiri-kiri Aliyu ya hana

daukanki wai kada asa miki datti da ciwon jiki, du

sanda akace Aliyu ya samu hutu bashida wajen

tarewa sai wajen mamanki yana rainonki. Kina da

shekara daya ya shirya miki birthday. Kina kan

kafadarsa yana yawo dake. Lokacin da ya yanka

cake din yasa miki abaki aka dau tafi, yace Allah

yasa na miki na aurenmu watarana.”

mamanki tace, “haba Aliyu, yaushe zakayi jiran

karamar yarinya haka? Yace wallahi mama tun

ranar da aka haifi zainab Allah ya dasa min

kaunarta araina, ni dai dan Allah mama inaso

kimin Alkawari zaki auramin zainab inta girma.”

mamanki tace na dau alkawari, in dai har Allah

yayi kai mijinta ne, to ba mai aurenta sai kai, na

baka zainab tundaga yanzu ta zama taka.

To kinji yanda mahaifiyarki ta bawa Aliyu ke, tun

kina ‘yar shekara daya. Abunda ya tashi aurenku

kuwa yanzu, yazo mana ne ransa a bace yace

“shidai dan Allah a taso da alkawarin mamanki a

aura masa ke, don yana tsoron samarin da suke

yi miki tururuwa, yaga har kin fara zance. Shiyasa

ya nemi alfarma a hade aurenku data ni’ima.

To yanzu mahaifiyarki tana karkashin kasa ta

rasu, baza kiyi kokari ki cika mata alkawarin data

dauka ba, kinfi so kita barinta da nauyi akanta?

Ta dago kanta tana kuka tace, daddy ko wane

irin alkawari mamana ta dauka akaina zan iya

cika mata shi, na hakura daddy. Kayi hakuri ka

yafe min bata maka da nayi.” yace bakomai

zainab, tsakanina dake kullum sai albarka.”

***** ****** ****

kwananta uku a asibiti aka sallameta, don taji

sauki. Amma du shigowar da Aliyu zaiyi tana

asibiti nan bata iya dago kanta ta kalle shi bare

tace zatayi masa magana kota gaisheshi,

kunyarsa take ji sosai. Bama inta tuna haidar

shine Aliyu, du tes din kalamomin soyayyar da ya

rinka turo mata da wayar da suka rinka yi ashe

du yayanta ne Aliyu, ita ya zata yi da wannan

abun kunya?

Ita kuwa mansura data ji zainab tana asibiti,

addu’a ta rinka yi Allah isa kada taji sauki a fasa

aurenta da Aliyu.

Da Aliyu yaje dadadare gidansu mansura zai

dauketa su tafi gida, sai tace ai ita ta gama

zaman gidansa, mayaudari maci amana, Allah ya

isa tsakanina dakai! Tunda kaci amanata.”

abun ya konawa Aliyu rai, yace ni kike gayawa

wannan maganar? Tace ana gaya maka din

azzalumi! Yace to ya isheki, kada ki sake bakinki

ya kuskure ki zageni, zaman gidanku kuwa kiyi

tayi, randa kika gaji kya dawo.” yaja motarsa ya

tafi ya barta nan tsaye.

Saboda kwanciyar zainab a asibiti, an fasa bikin

da kaisu acikin wannan satin sai asabar mai

zuwa za’ayi wuni akaisu dakin mazajensu.

Zainab ta zamo bata da sakewa ko yawan

magana, ko yaushe ka ganta tayi shiru tana

tunane-tunane. Aliyu daya fuskanci kunyarsa take

ji sosai, saiya daina shigowa inda take. Sai dai da

safe d daddare yayo mata tes yace kici abinci fa,

kinsan bana son zama da yunwa.

Ya karashe mata tes din da kalaman soyayya

masu sanyaya zuciya. Takan girgiza kai tace, “kai

namiji, ba ruwanshi da kunyar abunda yake so.

Wai yayanta Aliyu shine yake mata irin wannan

kalaman soyayyan, baya jin nauyinta bare

kunyarta.

Yaita aiko mata da cimarta ko yaushe, abubawa

da yasan tafi so,

suna zaune a falo ita da ni’ima, wayarta tayi

kara, ta duba ta gani saita kyaleta taita burarinta

harta gaji ta tsinke don kanta, amma sai aka

sake bugowa.

Ni’ima ta dago kai ta kalleta, tace ki dauka mana

dan Allah, nasan bazai wuce yaya ba.” ta girgiza

kai tace bashi bane.” ni’ima tace to ki dauka

mana.”

ai ban san mezan ce masa bane.

Ni’ima tace ki gaya masa abunda ya faru kawai

kada yaga kin yaudareshi.”

tana daf da katsewa ta dauka, a sanyaye tace

“hello! Daga can nura yace ai dole kiki daga

wayata, kunya ma ai ta isheki.

Wato zainab ina ganinki simi-simi kamar ma

hankali, ashe azzaluma ce ke, kin yaudareni.

Kinsan saurayinki ne aurenki zaiyi kika binneni a

cewar yayanki ne a hannunsa kike, ashe

masoyinki ne.

Zainab idonta ya fara zubar da hawaye, tace ba

haka bane, don Allah nura ka saurareni kaji.

Karaf a kunnen Aliyu daya shigo dakin a yanzu,

tuni hanjin cikin zainab ya hautsina, tuni ta rikice

ta kasa cewa komai, wayar tana manne a

kunnenta tanaji nura yana gaya mata

maganganu.

Aliyu ransa ya baci, ya rinka wani huci ya karaso

inda hankalinra ya tashi, ta rintse idonta tana

jiran saukar mari. Yasa hannunsa akan nata

hannun da yake kange a kunnenta, ya zare wayar

, ya daka masa tsawa kai wawa shasha! Kana

sane da matar aure kake waya? Wallahi kayi na

farko kayi na karshe…

 

Bakwa comments ko likes don haka zanyi daina wahalar da kaina may be littafin bai muku bane shiyasa nayi typing kadan ma.

[9:16AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**8,  2**9 &  2**10

 

DU sanda ka sake yiwa matata waya saina daureka bbu

beli. Kuma yanzu ma ka saurari zuwan kana nan sojoji,

zasu zo su koya maka

hankali.” ya cire wayar da kunnansa yayi cilli da ita ta daki

bango ta tarwatse, ya karasa gurin ya ciro sim card din ciki

ya kakkarya shi gutsi-gutsi ya

watsar a wajen. Ya dago kansa yana mata wani

irin kallo, yace wannan ya zamo na karshe, idan

na kuma gani kina waya ko kina magana da wani

sai ranki ya baci.” ya juya ya fita.

Ta dafe kanta tana kukanta. Ni’ima ta dawo

dakin da tun shigowar yaya Aliyu data ga sababin

da yake yi ta zame jikinta ta gudu, don kada ya

huce akanta.”

ni’ima ta zauna kusa da ita ta dafa ta, tace meye

na kuka, ke matsalarki kenan saurin kuka.”

tace, haba yaya ni’ima, kin san sarai yaya Aliyu

ya fiya saurin fushi da zafin zuciya, ni kuma bana

so naga bacin ransa balle kuma ace ni na bata

masa, taya za ayi zaman aure a haka?

Ni’ima tace haba zainab kefa mai hakuri ce zaki

iya zama da yaya Aliyu, don kinfi kowa iya gudun

bacin ransa. Ni sai yanzu ma na fahimta ashe du

tsanani da yaya yake yi miki soyayya ce da

kishinki da yake yi, ni wallahi ban taba ganin

amarya da ango da suka dace da juna ba irin ke

da yaya.”

idonta yayi narai-narai hawaye ya sake zubowa

tace, “ke yaya ni’ima haka zaki rinka yi min?

Ta fashe da kukanta. Ni’ima ta rungumota tana

rarrashinta, “to shikenan kiyi hakuri na daina, ba

zan kuma ba.”

du wayanci kawayen zainab ta gayyace su bikin

ni’ima, to da abun ya zamo haka ya hade da

nata, sai babbar kawarta hauwa Rabi’u ta rinka

yiwa kawayensu waya tana sanar musu tare da

basu hakuri na rashin ganin kati. Du da haka

saida Aliyu ya sanar a gidajen radio, saboda na

nesa kawayenta da basu sani ba.

Ranar jumma’a akayi mata kamu, kamun da ya

bada mamaki saboda cikar kawayenta da ‘yan

uwanta suka yi, sai da aka fara saukar Qur’ani

sannan aka kamata.”

daga nan wata malama ta bude filin da dan

wa’azinta (kusan hakkin miji akan matarsa ne

wa’azin kuma inaga munyi a baya basai na

maimaita ba).

Malamar nan tai ta wa’azi da fadakarwa akan

aure, wanda tunda aka fara zainab take kuka, dan

jikinta har rawa yake yi. Du da tasan hakkokin

miji akan matarsa babu abunda malamansu na

islamiya basu koya musu ba, amma wa’azin

malamar nan ya shigeta.

Yanzu taya zata hada jiki da yayanta Aliyu harta

kwanta gado daya dashi? Ya salam! Allah kaika

san abunda kake nufi da auren nan, Allah ka bani

ikon biyayya ga mijina.

Ranar asabar tun asuba akayi wa zainab da

ni’ima gyaran jiki, inda jikinsu ya fara laushi da

tsantsi, fuskarsu kuwa kamar kwan lantarki dan

kyau.

A wajen walima shiga iri daya akayi musu, wani

dankareren abu me kyalli da walwali pink, da

gwagwaro pink, dutsen da suka sa a hannu da

wuya duk pink, takalmi da jaka duk pink, sunyi

kyau sosai.

Walimar ta tara kyawawan ‘yan mata gogaggu

masu takama da ayar Allah.

Domin ayau ma wani wa’azin aka kuma yi mai

shigarwa, daga nan wani babban malami yayi

lakca wadda ya ladftar da zuciyar mai saurare, ya

dasa tsoron Allah a zukatan wanda suka saurara.

Daga karshe aka rufe da addu’a, aka yiwa

angwaye da amare addu’ar Allah basu zaman

lafiya. Amaren suka rinka zagaye tebir-tebir suna

gaisawa da kawayensu, suna yi musu godiya da

damar da suka samu ta hallartar bikinsu.

Aunty sadiya tana ta raba manyan bokitai da

farantai, da kofunan shayi na tangaram. Sun so

yin kalanda, Aliyu ya hana wai baza aje a lika

masa hoton matarsa a wani waje ba, wani gardin

ya kalleta yayi sha’awarta ba.

Da mangariba daddyn zainab ya kira Aliyu ya

tambayeshi ya maganar mansura? Aliyu ya gaya

masa yanda sukayi, yace randa ta gaji da zaman

gidan nasu saita dawo.

Daddy yace, “ashsha haba Aliyu yaushe zaka

daka shirme na mata, ai hakuri zakayi ka

rarrasheta tunda kai ka tabota, kayi mata laifi

babba, don su mata wannan shine babban laifi da

zakayi wa matarka.”

don haka ni yanzu zanje wajen babanta mu

tattauna na bashi hakuri kai kuma da daddare

saika je ka tafi da matarka.”

Aliyu ya rissina ya amsa masa tare da yi masa

godiya.

Daddy yayi sallama gidan Alh haruna, alh ya fito

da fara’arsa, ya bude dakin saukar bakinsa suka

shiga, bayan su gaisa daddy yake cewa, “nazo

bikon mansura ne, na tambaya dazu aka cemin ai

har yanzu tana gida bata koma dakinta ba.”

Alh haruna mutumin arziki, yace kasan halin mata

sai hakuri, hauka tayi masa yace tayi zamanta a

gidansu. To in banda rashin hankali ma ya za’ayi

da hukuncin ubangiji. Allah ya kaddara hakan tun

fil azal, towa ya isa yaja da hukuncin ubangiji?

Daddy yace”hakane fa don wallahi naso na sa shi

ya hakura da auren zainab ya rinka yi min

magiya dana hakura na kyaleshi, to ya za ayi da

hukuncin ubangiji. Don Allah kuyi hakuri Alh, in

ajima Aliyu zai zo ya duketa su tafi gida.” Alh ya

washe baki yace, wallahi bakomai saiya zo din.”

da Aliyu yazo Alh ya hadasu da mansura yayi

musu fada. Ya dauko mansura suka taho gida.

Tunda suka taho take yi masa kuka, yace “haba

mansura, kin san bana son kuka, laifi ne kince

nayi kuma na baki hakuri ba sai ki yafe minba.”

 

LAIFI ne kince nayi kuma na baki hakuri basai ki yafeni ba.”

niba wani wallhi, ai kasan ka zalinceni, haka kawai saikoyo

aure bakamin kayan fadar kishiya

ba, kuma baka canjamin kayan daki ba.” yace kiyi hakuri,

idan nagama ginina wanda zan

hadeku waje daya saina canja miki, kayan fadar

kishiya kuwa ga akwatuna biyu can da kudi dubu

dari suna dakinki na ajiye miki.”

sannan tayi shiru tana Allah-Allah suje gida taga

irin kayan da yake cikin akwatunan. Suna zuwa

gida shiya bubbude mata akwatunan ta gani,

kaya masu kyau da daraja da tsada, kala goma,

super, holland,leshi, shadda,ingila, diamond,

takalma uku, mayamayai da turaruka da

sauransu.

Ta zumburi baki tace ita kala nawa kayi mata?

Yace, “ba abinda ya shafeki bane wannan, tace

dama mana kace haka, kaci amanata na rike

yarinya ta gama sanin sirrina ka aureta.” ya daga

mata hannu yace, “ki rinka yiwa bakinki linzami,

tun kafin nasan zan hadu dake nake son zainab,

tanada shekara daya aduniya mamanta ta bani

ita. Shiyasa lokacin da mamanta ta rasu na dawo

da ita gidana gabana don nasa ido sosai akanta

kada wani ya hure mata kunne. Yayi ficewarsa ya

barta ta dora hannunta aka tana zunduma ihu.

Ranar lahadi akayi wuni ni’ima taci kwalliyarta,

tna cikin kawayenta sunata hotuna da bidiyo.

Zainab kuwa tana cikin dakin hajiya tana

kudundune tanata aikin kukanta, sadiya ta shiga

ta dagota, “haba zainab wai miye hakane, yanzu

du kaunarku da yaya don an aura miki shi kike

kuka irin haka?

Tace, yaya sadiya aunty mansura fa marikiyata

ce, kuma saina juye na zama kishiyarta.”

to meye ba haka Allah ya shirya ba. Ta lallabata

tayi wanka, ita ta shiryata ta dandasa kwalliya

cikin wata dakakkiyar galila da akayi mata dinkin

bubu, ta aikatu da surfani ta nada mata dan

kwalin shaddar kamar nadin gwaggwaro.

Tasha gwal tanata sheki, ta fito da ita zuwa

babban falo, mutane sai guda suke suna binta,

maroka kuwa sai wasata sukeyi. Sadiya ta fito da

kudi tana watsa musu, ta zaunar da ita. Ni’ima

tazo ta rungumota tana cewa, “haba my sister ko

kefe. Kawayenta du sunzo sun zagayeta ana yi

mata shekiyanci, bata iya cewa komai sai

hawaye.

Jikinta kuwa ya dumame da zazzabi, aunty

sadiya ta bugawa Aliyu waya, yana dauka tace,

“hello yaya, dama cewa nayi zainab ce ba lafiya

take fama da zazzabi, shine nace ko zaka bari a

barta a gida inta samu sauki akwota? Yace dan

Allah gafara can, inkun ajiyeta a gidan me zakuyi

mata inbanda ku dameta da sannu-sannu. Kunga

ku kawo min matata na bata kyakyawan kulawa.”

tace “a yaya haka za’ayi?

Yace ku bata waje ta kwanta ta huta kada kusa

mata ciwon kai, bana so kudameta da hayaniya.”

‘yan wajen suka sa ihu da dariya.

Zainab kuwa ta dafe kai data ji yana sara mata.

Da daddare akayi jerin gwanon motoci, sai aka

raba jama’ar biyu, rabi zasu kai zainab da

kawayenta rabi kuma zasu kai ni’ima da

kawayenta.

Ankai ni’ima janbulo kabuga, gidanta babba mai

kyau ita kadai abunta, zainab an kaita nasarawa

G.R.A gidanta mai kyau zaman mutum daya,

fadan kyaun gidan bata lokacine. ‘yan kawo

amarya sun zagaye ko ina kowa sai santin gidan

yake. Da yanda aka tsara komai, gashi ba wani

babba bane tsarin turai ne komai, ‘yan kawo

amarya zasu tafi zainab ta kankame aunty sadiya

tana kuka.

Sadiya ta rasa yanda zatayi mata saboda yanda

taga jikinta yana karkarwa, yayi zafi zau, zazzabi

ne mai zafi. Sadiya tayi mata dabara tace “zauna

anan na samo miki magani da ruwa a kicin.

Ta zaunar da ita a bakin gado ta fice da sauri

tana kuka, bata ankara ba taji gidan shiru alamar

kowa ya fashe kenan. Ta dora kanta kan filo taci

gaba da zubar da hawaye, kanta yanata sara

mata, ta dora hannunta akanta ta dafe shi.

Aliyu yayi sallama cikin sanyi muryarshi, du da

tasan muhimmacin sallama amma saita kasa

amsawa, saboda wani irin rudani data shiga, itace

yau da yaya Aliyu a daki daya, daga ita saishi a

matsayin matarsa ta aure. Ko ina auntyn nata?

Yanda dai taji anata zugugun gidan tasan ba

gidan da auntyn take ya kaita ba. Yazo ya zauna

a bakin gadon, ta zame kasa tace, yaya ina wuni?

Ya dagota “lafiya lau zainab ya taro? Tayi shiru

tana sheshshekar kukanta. Yace zainab kiyi

hakuri nasan bakya sona, kada kiga na takuraki.

Zainab tsananin kaunar da nake miki bazan iya

bawa wani aurenki ba, saina ga kaman zai cutar

min dake. Kiyi hakuri zainab kidaina yawan kuka,

bana so ki jawowa kanki matsala, a sannu a

hankali wata rana zaki soni, kinki zeeyta?

Ni jininki ne dan’uwanki ne, ki daina damuwa

akaina kinji babyna.”

yana dan bubbuga bayanta na rarrashi, ya shafa

cikinta, “kinga cikinki kwalam kina zama da

yunwa, bana son zamanki da yunwa kada olsa ta

kama minke.

Ya jaeo ledar kusa dashi yana zaro katon nadin

takarda, gasassun kaji ne guda uku, sai robobin

youghot da ice-cream, ya yago naman zaisa

mata abaki ta kauda kai, cikin sigar rarrashi yace

kinga, “kinsan bana son gaddama, ki karba kici.”

ya rinka bata tana ci, a zuciyarta kuwa tunani

take yi, wai dama yaya Aliyu zai iya rarrashin

mutum da lallabashi haka? Yau babu wannan

fadan da hargagi na yaya,..

 

YAu babu fada da hargagi irin na yaya, sai wani ji

yake da ita. Lallai namiji kenan.

Ta kifa kanta a jikin gadon saboda yanda taji

yana sara mata kamar zai rabe biyu, yace zeeyta

mene ne? Ya dagota yaji jikinta zafi zau, yace, ya

ilahi. Yanzu zeeyta bazaki daina sama kanki

damuwa akaina bako? Ta rinka lumshe idonta

yana kokarin rufewa, saboda azabar ciwon da

kanta yake yi, Aliyu hankalinshi ya tashi, ya

kwantar da ita ya mike ya shiga kicin ya debo

ruwa awata a silba, ya taho da hankicif.

Ya kwantar da ita a cinyarsa ya cire mata rigar,

sai farar shimi mai kyau a jikinta, ya rinka tsoma

hankicin a ruwa yana goga mata jikinta. Sannu a

hankalin zafin jikin nata ya fara raguwa, ya bata

magani tasha, ya barta daga ita sai bes da siket,

ya shimfideta a gado ya mike ya koma kicin don

ya mayar da kayayyakin ciki, ya jere ice-cream

din da youghot din a firij, ya shiga dakinsa ya

fada toilet yayi brush, ya saka kayan bacci ya

koma dakin bayan ya rufe ko ina, ya tofe ko ina

da addu’o’i ya hawo gadon. Tuni ta dade da fara

bacci, ya dagota ya dorata akan kirjinsa ya

rungumeta, a zuciyarsa ya ringa jin wata irin

nishadi, wai yau shine rungume da zainab dinshi,

ashe zaiga wannan rana? Ashe wannan lokaci

yana nan zuwa gareshi? Yaso suyi sallah raka’a

goma sha biyu don nuna godiyarsu ga Allah, to

matsalar rashin lafiyar zeey dinshi hankalinshi ba

akwance yake ba.

Zainab ta dan motsa, ya rinka jijjiga ta yana

lallabta kamar yarinyar goye, da yake zazzabi ya

sauka baccinta take yi sosai.

Sai wajen asuba ta farka, tana jinta rungume

ajikin yayanta Aliyu du kunya ta dame ta, tana

kokarin zame jikinta daka nasa sai ji tayi ya sake

kankameta, dole ta hakura amma du kunya ta

isheta, ta kasa wani kwakkwaran numfashi.

Saida akayi assalatu sannan ya shimfideta a

gadon, ya rada mata akunnanta, “ki tashi kiyi

sallah ni zan tafi masallaci.

Ita kunyarsa take ji sosai, bata iya amsa masa

ba, ya fita ya nufi dakinsa ya shiga toilet ya

daura alwala, ya fita masallaci.

Ta mike tana mamakin yaya Aliyu, daman haka

yake? Tayi alwala tayi raka’atul fijir, ta tashi tayi

sallar asuba, ta gama laziminta ta daga hannu

sama tana addu’a, Allah ya basu zaman lafiya,

Allah ya hada kanta da kishiyarta yaya Aliyu Allah

ya kara buda masa, Allah ya bashi ikon yin adalci

a tsakaninsu. Ita kuma Allah ya bata ikon yin

biyayya ga mijinta.

Tana cikin yin addu’a yaya Aliyu ya shigo, sai ya

huce dakinsa. Tayi sauri ta shafa addu’ar ta

koma dakinta saita rufe kure kofofi, don ita a

tunaninta da wani ido zata kalli yayanta.

Daya taba kofar tata yaji ta rufe, sai yayi

murmushi kawai ya koma dayan dakin ya kwanta,

sai sannan ya samu bacci mai karfi ya daukeshi.

Karfe takwas ta tashi ta shiga wanka, ta shirya

cikin riga da siket na shadda ruwan goro dinkin

stayil ne, anyi mishi hawa-hawa kamar asabari,

an zuba dutsuna aciki yana ta walwali. Farar

fatarta tayi das aciki, ta hade kananan kalabar

kanta tasa ribon ruwan goro ta daure, ta feshe

jikinta da turare tana ta zuba kamshi.

Ta rinka jin ana kwankwasa kofar falon, taje ta

bude. ‘yan gidansu ne hamza da sadik suka kawo

musu abun karyawa. Ta basu hanya suka shige.

Hamza ya kama tsokanarta, “amarya kinsha

kamshi, don Allah du kukan da kika sha jiya harda

su zazzabi amma kalleki yanzu shar dake kinsha

kwalliya.

Yace kin hakura kenan? Tace “ban hakura ba,

yanzu zan biku mu tafi tunda ku kuka fara zuwa.”

sadik yace kibi su wa?

Na biku mana.” hamza yace rabu da ita fade

take, ina zata iya zuwa, data sha bulalan Yaya.

Sadik yayi dariya, yace irin wacce tasha data yi

zance ba. Gaba daya suka sa mata dariya.

Tace to ya isa, tunda kun kawo aiken da akayi

muku kuzo ku tafi. Sadik yace zamu tafi bamu

gaisa da yaya ba? Tace to bacci yakeyi.

To ki taso mana shi mana.

Ya zan taso shi yana bacci aiba haka akeyi ba.

Hamza yace, “wati har kin fara rowarsa ko? Tace,

“kai ka sani.

Suka fice suna mata dariya. Ta bude taga

shiryayyun break din da akayo musu ta girgiza

kai tasan iyayensu mata ne zasu yi ba

‘yan aiki ba.

Ta shirya komai a tebir, tuni ta gyara falon tasa

turaren wuta mai dadin kamshi. Daga bayanta taji

motsi, tasan Aliyu ne, saita kasa juyawa, a haka

ta durkusa tace, yaya ina kwana?

Sai shima ya durkusa ya dora kansa a bayanta

yace, “haka akeyin gaisuwa a juyawa miji baya?

Yace “zeeyta ya jikin, meyasa kika rufe min kofa

da asuba?

Du ya saukar mata kasala ta kasa wani katabus,

wai shi yaya baisan kunyarsa take ba, meyasa

yake yi mata hakane? Ya kama shafa

wuyantayana cewa “zeeyta zazzabi ya sauka ko?

Ta rasa yanda zatayi, du ya kanainayeta,

kunyarsa da nauyinsa ya isheta, gashi ta gaji da

tsugunan.

Ta zame zata zauna ya tallafota jikinsa a hankali

yana shakar ni’imtaccen kamshin jikinta,

muryanta can kasa cikin marairaita tace “don

Allah yaya ka bari, kunyarka nake ji.

Cikin kunnanta ya rada mata, kidaina jin kunya ta

nifa mijinki ne, kin taba jin inda mata take jin

kunyar mijinta? Kefa malama ce kinsan hakkin

miji akanki, kada kunyata tasa ki sabi dokokin

ubangiji, ki saki ranki ki saki jikinki.

[9:16AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**11, 2**12 & 2**13

 

ALLAH NE ya shirya aurenmu, kodai akwai haramci aciki?

Ta girgiza kai alamar a’a ya dagota, taso muje muyi break,

dura zan ringa yi miki bana son

zamanki da yunwa.”

ya riko hannunta zuwa kan tebir din, yana bude abincin

yana shirin zuba musu, ta rike hannunsa,

ka bari yaya na zuba mana.

Yace, yauwa ko kefa, ai gwanda ki fara aikin lada.” ta zuba

masa farfesun da soyayyen dankali

da kwai, ta hada masa tea mai kauri, ta tura masa

gabanshi.

Yace to sannu, muci.” ta girgiza kai tace, bana jin yunwa.”

yace, “kinfi so na miki dura kenan?

Ta hada tea kadan tana sha a hankali. Ya zuba

mata ido, shi yarinyar sha’awa take bashi, komai

nata a nutse cikin hankali da nutsuwa. Suna

gamawa ta kwashe kayan ta kai kicin. Shikuma

ya zauna akan doguwar kujera. Tazo zata huce

ta shiga daki, ya jawota ta fada jikinshi, yace

mata a kunnenta in zaki je kibar mijinki? Zo muyi

hirar soyayya, nine fa haidar dinki kin manta da

hirarmu da mukeyi mai dadi? Ta boye fuskarta.

Yayi murmushi wayarshi tayi kara, ya dauka da

sauri ya kara a kunnensa, ya rissina tare da cewa

hello, umma ina kwana?

Lafiya lau, ya jikin zainab din?

Yace, dasauki umma gata nan ma

ya nana mata wayar a kunnenta, ga umma zata

yi miki ya jiki.

Ta noke um-um, nidai kunyarta nake ji. Yace au

yau kunyar umman taki kike ji, bazaki amsa mata

wayarta ba?

Cikin sanyinta tace, hello, umma ina kwana?

Lafiya lau zainab ya jikin naki? Da sauki umma.

“kiyi hakuri zainab kinji, yanda nasanki da hakuri

da biyayya ki kara akan da, kada kisa kunya a

harkar aure, saita jawo miki halaka kinji zainab?

Cikin sanyita tace to umma, nagode, don Allah

umma ku daina wahalar da kanku wajen girki don

Allah umma kada asake kawowa zan girka da

kaina.

Anya zainab, ki bari ki kara hutawa mana ba zaki

iyaba akwai wahala. Tace bakomai umma zan

iya. To shikenan zainab Allah yayi miki albarka.”

amin umma.

Ta kashe sannan Aliyu ya cire mata wayar daga

kunnenta, yace, “nifa kada kije ki kone ko ki

yanke, zaki ce zaki iya girki da kanki.

Tace yaya niba mace bace, ai dole nayi girki, zan

bar iyayenmu suna wahala ne? Ai saidai mu muyi

musu don su huta mu kuma samu lada ko? Ya

daga mata kai kawai saboda shi yana yabawa da

hankalin zeey din tashi.

Tace, yaya kaje ka gano aunty da Ahmad kaga

yasuka kwana? Au har korata kikeyi?

Tace ba haka bane yaya, gwanda kaje kaga yanda

suka kwana.

Ya gyada kanshi zanje, daganan zan wuce office

din daddy da Abba na gaishesu.

Sha biyu dai-dai ya fita ya nufi gidansa, yayi

sallama falon mansura tana zaune bata amsa ba.

Ya shiga ya zauna bata juyo ta kalleshi ba.

Yace yau bakisa su talatuwa sunyi shara da

wanke wanke ko ina kaca kaca haka? Tace, tunda

kazo ai saikai kasa suyi.

Ina Ahmad kinsa ankaishi makaranta daiko?

Tace nidai kada ka dameni, ka damu da

rayuwarsa meyasa baka tafi dashi can gidan naka

ba? Wai don Allah ko kunya baka ji ka riki yarinya

ka aureta yau ka kwana gado daya da ita har

wani abu ya faru a tsakaninku? Wannan abun

kunya da yawa yake, wallahi idona idon yarinyar

nan saina raunanata.

Ya daka mata wata irin tsawa data firgitata, yace,

wallahi ki kiyaye, du ranar da kika sake kika dora

hannunki akan matata saikin gane kurenki wallahi

sainayi maganinki. Bissimillah kije ki tabata.

Abunda yasa kenan nakasa bawa kowa auren

zainab, don kada wani ya cuceta, shiyasa na

aureta don nabata kulawa, sannan ke kuma kice

zaki daketa. Wallahi da sai kin raina kanki.” ya

mike ya fice ya bar mata gidan, yayi office din

iyayensa.

Zainab kicin ta shiga, inda duk aka jere mata

kayan amfanin kicin kamar a turai, du wata

na’ura da zata dafa abu kota gasa abu cikin

sauki an sa mata aciki.(nan yanda za ayi

abincine nasan basai na rubuta ba)

Ta gama abinci ta shiga wanka ta dauro alwala,

tayi sallah tashafa mai, ta shafa farar hoda du da

ba wata kwalliya tayi ba saida ta kara kyau tasa

atamfa holan baka, dinkin karamine yayi das

ajikinta, ta fesa turaruka tanata kamshi.

Ta jona abun turaren wuta, mintuna kadan gidan

nata ya dumame da kamshi. Tana so taji

mutuniyar tata yayarta ni’ima, to bata tunda yaya

ya fasa mata wayarta batayi wata ba. Koda yake

bawa zai ba tunda shine me sayen?

Yaya Aliyu yayi parking motarsa ya fito a harabar

gidan, daddan kamshi daya ji yana tashi shiya

shaka ya ratsa masa zuciyarsa, saiya ji ya

sanyaya masa rai. Yayi murmushi ya shige ciki,

ya tura kofar falon ya shiga da sallama. Tana

zaune akan kujera ta amsa sallamar kanta a

sunkuye.

Yazo ya zauna kusa da ita, saita zame kasa ta

durkusa, “yaya sannu da zuwa.” ya dagota ya

karata ajikinsa yace, “zeeyta meyasa baki taso

kin tareni ba kina oyoyo sannu da zuwa yaya?

Tace, “a da girmaba?

Wane girma kike dashi? Kefa babyna ce. Ta rufe

idonta, yaya kana sani jin kunya.

Zanyi kokari na cire miki kunyar nan dai ta daina

takura mana.” don Allah yaya ka bari, ga

abincinka can a tebir.” a lallai yau zanci girkin

amaryata, to taho muje ki bani. Ya riko hannunta

suka jere harkan tebir din, ta jawo masa kujera ya

zauna, tana bude abincin kamshi ya bugesa ya

lumshe ido…..

 

TA loda masa abincin ta rinka tura masagabansa, tasa

masa cokali, ta zuba masa hadinlemo data yi masa. Tace

yaya kaci mana.” yazaunar da ita kusa dashi, ya debo a

cokalin yanufo bakinta, tace dn Allah yaya kaci, nasan

fabaka ci komai ba tunda safe. Nikuwa nasha ice-

cream.”inbanda ke wa yake maida ice-cream abinci. Yabata

ta karba cikin kunya taci, shima yaci yceum-um carkwai,

waya koya miki girki haka?Tayi murmushi ta sunkuyar

dakai, ya rinka cinabinci yana santi, saigashi yaci dayawa.

Ta rinkamamaki ashe yaya yana cin abinci? Ita saita gaidan

aunty ta ajiye masa, idan yazo kokarinsayayi cokali biyu ya

ajiye.Intayi magana yace yakoshi. Saidai suyi ta ciye-ciye,

da yamma kuwa ya tafi gida yaci acan.Kodai daman rashin

dadi ne yake hanashi ci?Yana tafiya sallar isha ta rufe

dakinta ta kwanta,daya dawo ya taba kyauren yaji shi a

rufe, saiyakoma dayan dakin yayi kwanciyarsa.Da asuba

daya fito sallah ya buga mata, saidayaji motsin tashinta

sannan ya tafi masallaci.Yana dawowa dakinsa ya shige ya

koma bacci.Itama baccin ta koma, sai karfe takwas ta

miketa shiga kicin, tana gamawa ta kwashe komai tajera a

tebir, ta gyara kicin din ta share ko ina, taturare shi da

turaren wuta.Ta koma dakinta ta shiga wanka, tana fitowa

tashirya cikin wani jan les riga da siket, dinkinkaramine yayi

das ajikinta, sai kamshi take.Tana jera kayan kwalliyarta

akan madubi yashigo, ta durkusa da sauri tace yaya ina

kwana?Yace bazan amsa.” ta marairaice, haba yayasaboda

me bazaka amsa min gaisuwata ba?Kinyi min laifi jiya kin

rufe min kofa.” kayi hakuriyaya kunyarka nakeji.To zeeyta

me zanyi miki, na sani ke yarinya ce,nima ina tausayinki, ki

saki jikinki ba abundazanyi miki, rainonki zan tayi har sai

kinyi wayo,kada ki kuma rufe min kofa ina tsoro kada

waniabu ya sameki a daki ke kadai, gwanda munatare a

waje daya.Saiki yi kwanciyarki a gado, ni saina

kwantaakasa. Kinji zeeyta? Ta daga kai, kayi hakuriyaya

bazan kuma ba.To shikenan na hakura.Yaya ga break

can.Zeeyta harkin gyara waje haka kinyi wanka?Zainab aiki

yayi miki yawa, kodai asa umma tasamo miki mai aiki?

Haba yaya zan iya komai, wallahi malaminmu yagaya mana

du abunda kayi a gidan mijinka ladane, idan ka bawa wani

yayi maka, to shi yake daladan ba kai ba. Nikuwa yaushe

zan yardalahirata mu rinka rabawa da wasu?Ya gyada kai,

haka akeso zeeyta, mutum ya rinkaamfani da abunda yake

karanta.Akan tebir inda ta shirya masa break ya rinka

ciyana santi yana sa mata albarka. Saida yacidayawa ya

koshi yayi hamdala, yace zeeyta zokigaya min waya koya

miki girki ne? Naga a gidanauntyn naki bata fiya yi ba bare

nace gani kika yitana yi kka koya.Yaya a makaranta mana

ai har fanni koyon girkiakwai, shiyasa in mun tafi tun safe

sai shidda nayamma za a tashi. Yaya Aliyu yace ai

makarantartana da kyau, daddy baya wasa a harkar

ilimi.”wayar tasa tayi kara, ya dauka yace, ke ina kikabar

mijin naki kika bugowa mutane waya dasassafe? Kayi

hakuri yaya, wallahi inaso injizainab shine na bugo a

taka.Ta gaisheshi. Ya mikawa zainab wayar, ni’imatana

jinta tace mutuniyar ya akai? Ina taso najiyo ki saina tuna

kefa kurmace yanzu tundabakida waya. Wai ya yayan ne,

komai ya faru ko?Zainab tace oho! Ke kika sani. Yaya ni’ima

inakika barshine?Yana kicin yana soya mana

break.A’uzubillahi, kiji tsoron Allah kina zaune mijinkiyana

kicin.”ni’ima tace, ai shiya jawo, bashi ya dora mingajiya ba,

a wahale nake ba abinda zan iyayi. Aiya kuma shiga

kicin.”ke yaya ni’ima wace irin gajiya ce da zata

hanakishiga kicin?Ni’ima tace ‘a daga jin bayaninki

bakisankomaiba. Wai yaya kallonki ya tsaya ne haryanzu

baiyi miki komai ba?Tace “don Allah yaya ni’ima ki bari ni

bana sonirin wannan maganan.Zainab da wahala fa, nima

nasha wahala bare keda kike yarinya.Zainab tace don Allah

kidaina min irin wannanmagana, Allah zan ryfe

wayar.Ni’ima tace wai yaya na wajen ne koya tashi?Tace

mata, oho ke kika sani, ni dai ki bari banaso.”to shikenan

naji matsoraciya, wata rana da kankizaki zomin da zancen

bazan saurareki ba.Tace, eh naji na yarda. Ta rufe wayar

tana dariya.Yaya Aliyu yace, me take gaya miki kike

cewabakya son ji? Gaya min ni.”tace kai yaya nidai ba

ruwana. Ta tashi zatagudu daki ya rikota, zeeyta ba zaki

gaya minba,ni inason ji gaya min kinji.Ta boye fuskarta, don

Allah ka bari ni bazan iyaba. Wata wayar ce ta sake

shigowa, da yayi birisda ita saida yaga numbar mai

bugowan sannanya daga.Hello mansura ya akayi?

 

Hello! Mansura ya akayi? Jin yaambaci mansura tasan

auntynta ce,kawai saita mike zata bar wajen, yazuba mata

ido yana kallon yanayinyanda take tafiyarta kamar bata

sontaka kasa, yarinyar ta shige ransadayawa, yanda yake

jin kaunarta tarinka azalzalar zuciyarsa, dole sai yaganta

koya ji muryanta, inba hakaba baya iya rintsawa. Son

gaskiyakenan, ko yaushe yana ranka. Yaugashi zeey dinshi

a matsayinmatarshi ta aure, ko yaushe mafarkinnasa zai

tabbata ya ganshi manneajikinta suna faranta ran juna?

Tace baka jinane? Yace inajinkimansura ya akayi? Dama

yar lawisakawata ce ta haihu, shine zamujesuna.Yace a’a

bazaki ba.Saboda me? Kana ganin irinamintakar da take

tsakaninmu dalawisa, amma kace bazan je sunanyarta

ba.Eh nace bazaki ba, kada kuma ki sakekiyi min

maganar.Ta kama maganganu, “haka kawai adakeka a

hanaka kuka, ka gama cinamanata ka auri ‘yar dana rika

kumani ka rinka takurawa rayuwata kanagallaza min. Haka

kawai kai ba’agidan kake ba kuma ka hanani fita,zanta

zama ne ni kadai kamarmayya?To ya isheki haka, ina gaya

miki kirinka iya bakinki, ki rinka saninkalmar da zaki gaya

min.Ya kashe wayar.Lawisa ta kalleta, tace, to ya ya,

yabarki? Ta tabe baki, ya hananizuwa.” lawisa tace mugu,

dayakyaleki muka je wurin malamin nandu taurin kansa sai

yayi laushi, donsaiya lankwasa mik shi, saikin juyashi a

tafin hannunki. Amma yanzuma ba zama za ayiba, ki bani

kudi ninaje miki.” tace to. Ta mike ta shigedaki, ta fito da

kudi ta bawa lawisa.Yauwa kin gani ba, ai Aliyu dazainan

sun shiga uku, sai sun sansunci amarki.”yauwa aminiyata,

don Allah kikokarta, kada kiji komai kawata.***** ****

*****da daddare ta bar yayan nata a faloyana kallo, tayi

shiri kwanciya bacci,saita rasa ya zatayi saboda yayanyace

kada ta sake rufe kofa takwanta bacci ita kadai a daki. To

yazatayi?Ta dauko bargo da filo takudunduna a kasa kan

kafet, tayiaddu’o’inta ta shafa, ba jimawa bacciya

dauketa.Du da har yau ‘yar uwar tashi takisakin jikinta

dashi, saboda tsaninkunyarsa data keji, shidai yana so

yakasance tare da ita, don inya kalletasaiya ji farin

ciki.Intayi magana kalamominta sai sunsanyaya masa

zuciyarsa, yana sonyanayin maganarta cikin shagwabada

sanyi, bata son yawan hayaniyaamma baza a kirata miskila

ba,saboda akwaita da fara’a da kumafaram-faram da

jama’a.Tunda ta mike yaji du zaman kadaiciya isheshi, shi

kadai awajen. Donhaka ya kashe komai ya rufe ko ina.Ya

tofe ko ina da addu’o’i, sannan yashiga dakin ya rufe kofar,

ya ganta akudundune akasa cikin bargo tatakure waje

daya.Yayi murmushi ya tsugunna kasanya janye bargon a

hankali, bacci takesosai. Yasa hannu ya shafikumatunta.

Yasan shidai maikyaune, du inda ya shiga ana yabashi. ‘yan

uwa suna zuzuta kamaninsada zainab. Amma ina, shidai

yasanzeey dinshi tafi dhi kyau, yarinyamai hakuri da

nutsuwa, shidai Allahya barshi da zeey dinshi.Ya dauketa

cak ya daurata akangado, ya tofeta da addu’o’i, sannanshi

ya sakko kasa ya kwanta. Shidahakan yafi mashikwanciyar

hankali, da ace zeey dinshitana wani daki shi yana wani

dakidaban.Cikin dare ya manta bai kashewayarsa ba, tai ta

damunshi da karahar zainab ta farka, tayi mamakinganin

yayanta akasa ita kuma akangado, alhalin ba anan ta

kwanta ba.Yayi tsaki cikin yanayin bacci yadaga wayar,

daga can dayanbangaren amininsa, abokin aikinsadaga

kaduna, kanal faruk yayi yomasa wayar, cikin magagin

bacciyace waye ne?Faruk yace, magagin amarci kakeyine

shiyasa baka gane lambarba?Aliyu yace “shegen gari maye

nayomin waya cikin dare haka?Ai tun dazu naso nayo

maka, sainace dai kada na katse maka hanzaribari na bari

ka gama samun untsuwatukunna.”Aliyu yace, dan

ganganci, autar tamudanake ji da ita a rayuwata, aiyarinya

ce karama saita wahala.Faruk ya kwashe da dariya,

yacekaidai ko gudunka take yi, yandanasanka da kaunar

zainab anya zakasaurara mata?Ba dole ba tunda ina

tausayinta, waimeyene ka tasheni cikin dare haka?Yanzu da

idon zeey biyu ai da kafirgitamin ita.Faruk yace, ai ya zama

dole nanemeka, aiki aka turamu kasarbayelsa tafiyar

gaggawa jibi-jibnnan.Aliyu yace haba dan Allah, kumadole

saidani basu san inada sabuwaramarya ba? Ina zan tafi na

barta?Faruk yace ai anan zaka tafi ka barta,ai tasan

cigabane yazo ai bazata kicigabanka ba.Aliyu yace, wai

daga ina tafiyar tataso haka?Daga can sama takardar ta iso

manaa dazun nan office, kamata yayigobe ka taho nan

kaduna, jibi dasafe jirginmu zai daga.”Aliyu yace innalilahi

wa’inna ilaihiraji’un, banso tafiyar nan ta sameni awannan

lokacin ba, ya zanyi dazeeyta?Faruk yace, kaji ka, saika ce

wanimace, kai ba namiji bane. Kakarfafawa iyalanka gwiwa

har mujemu dawo. Bari na barka sai gobeninka iso.”da safe

tun wuri ya tashi, zainab tanakicin tana hada break, tana

fitowataga yayi zugum alamar tunani. Takawo break din ta

jere, tazo tadurkusa agabansa tace, yayamenene?Ya rike

hannunta zainab tafiyace tasamemu ba shiri.”

 

A daure ayi likes da comments

[9:19AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**14,  2**15

 

YA rike hannunta, zainab tafiya ne ta samemu bashiri.Toh

don Allah yaya meye abun damuwa? Bakasaba tafiye-

tafiyen nan ba, zaka sawa kankadamuwa. Don Allah ka cire

komai daga ranka zomuyi break din.Ya biyota kan tebir, ta

rinka jan ra’ayinsa yanatura abincin aciknsa, har yaci mai

yawa. Yacemata zaije wajen mansura yanzu zai

dawo.”yana fita zainab murna ta rinka yi sosai, zatakoma

gidansu kafin yaya ya dawo.Aliyu yana shiga falon

mansura yaji shiru, yashiga cikin dakin tana kudundune

cikin bargo, yazauna gefen gadon ya zanye bargon, ta

budeidonta, tana ganinsa tayi zumbur ta tashi tace,lafiya

yanzu da sassafen nan?Yace lafiya lau ke baki san ma

garin ya waye bako?Karfe goma kina kwance. Kaduna zan

tafi yanzu.Tace au har amaryar ta ginsheka ka fasa yi

matakwana bakwai, yau fa kwananku hudu.Yayi tsaki ya

harareta, ki rinka sanin kalmar dazaki gayamin.Yau zan

koma kaduna zamuyi asubancin tafiyabayelsa aikin

gaggawa.Tayi dariya da shewa, Alhamdulillah, Allah nagode

maka, ai gwanda ka tafi. Ya bude baki yanamamaki, au har

so kike ma na tafi bakya sonzamana kusa daku.”tace

wallahi bana so, aini tafiyarka tafi komaikwanciyar hankali

awajena. Ya daga mata hannuto naji, ya kuma isheni haka

kafin ki fara fatannabar duniyar. Kiyi min lis din abunda

kukebukata keda Ahmad. Sito dai cike yake da

kayanabinci.Tace “zaku dade ne?Ya mutsa fuska, eh to

zamu iya yin sati hudu kozuwa sama.Ta hau lissafe-

lissafemai dalili da mara dalili. Yabata damin kudi kamar

yanda tace ya kara matawasu ma akai.Ya mike zai fita yace

mansura kiyi min addu’a,anason addu’ar mace zuwa ga

mijinta, Allah yanaamsawa zan biya makarantar su Ahmad

yanzumuyi sallama, don Allah ki kula da komai, kijagirmanki

da mutuncinki, don Allah kada kuyiabunda zai daga min

hankali.Kinga yaki zamu tafi, ko mudawo da rai koakawo

gawarwakinmu, laifin da kike ganin nayimiki kiyi hakuri ki

yafemin.Jikinta yayi sanyi tace, amma kasani baka

kyautamin bako?Na riki yarinya ka aureta.Yace haba

mansura, ba zaki yarda da kaddara bakinsan bana son

mita. Kiyi hakuri don Allah kibarmaganan nan.Tace to

shikenan naji, Allah ya kiyaye hanya.”yace Amin, nagode.Ya

shiga motarsa ya nufi makarantar su Ahmad,har sun fito

break, yana ganinsa ya rungumesayace Abbana har yau

aunty mami bata dawoba.kuma naje gidan Abbanka ban

gantaba, in natambayi mama ina aunty mami saita doke

bakinatace kada na kuma zancenta.Abba zaka kaini wajen

aunty mami? Ya shafakanshi, zan kaikaamma kayi hakuri

kaga yanzu tafiya zanyi wajenaikina, sainayi kwanaki

dayawa zan dawo, karinka kula kana maida kai akan

karatunka kaji.Ya rike hannunsa zuwa wani dan kes na

cikinmakarantar, ya saya masa mitfy da kek da

lemonkwalba, ya zaunar dashi ya cinye indomi da kwaidin,

ya shanye lemon kwalbar yace ya koshi.To sai ya saka

masa mitfy din da kek a jaka,yace ya koma aji.Shikuma ya

tafi gida.Zainab tun bayan fitarsa ta gama share-

sharentada goge-gogenta, ko ina yayi tas yana kyalli,

tayiwanka ta gyara kanta cikin wani material bakimai

gwaldin da gashi-gashi ajiki. Dinkin yayimata das dai-dai

jikinta, farar fatarta ta karamata kyanta da kwarjini acikin

kayan, ta feshejikinta da turararuka.Haka kawai take jin

nishadi, yau zata komagidansu du da dai tasan dole ta rinka

jin kunyarsu umma da ummi, ai saitai ta zama abangarensu

wajen babanta.Yaya Aliyu ne yayi sallama, ya katse

matatunaninta, ta mike tsaye tana yi masa sannu dazuwa,

ya nufo wajenta ya zaunar da ita, ya zaunakusa da ita yana

amsa mata da yauwa. Ya shafikuncinta kinyi kyau

zeeyta.”ta mike ta nufi firij ta dauko mishi lemo da ruwa,ta

shiga kicin ta dakko masa gasashen nama takawo masa.

Yace yauwa zeeyta nagode.Yana ci yace, yanzu zeeyta

yanda kika farasangartani da wannan girki naki masu dadi

badole nayi maraicinki ba, wa zai rinka kula daniidan na

koma can?Gashi da yamma zan tafi.Tace yaya inka tafi da

yamma nikuma saida darezan tafi? Yayi saurin cewa ina?

Har yana kokarinkwarewa. Cikin sanyin murya tace, “yaya

gidamana.Kije gida kiyo me?Yaya ba a gida zan zauna

saika dawo ba?Ya girgiza kai, a ina kika taba ganin anyi

haka?Zamanki zakiyi a gidan mijinki har saina dawo.Nan

da nan hawaye ya wanke mata fuska, tadurkusa kasa

agabanshi takama kuka, “don Allahyaya ka mayar dani gida.

Idan ka dawo na dawo.Wallahi yaya tsoro nakeji bazan iya

zama ni kadaiba, kaji yaya.Ya dafa kanta yana rarrashinta,

kiyi hakuri za akawo miki wa’yanda zasu tayaki zama ko

mutumnawa ne a ‘yan uwanmu, amma bazan iya

mayardake gida ba, gwanda kina inda na ajiyeki.Nidai nafi

son ka mayar dani gida.Ta kifa kanta a jikin kujera, kuka

take yi masasosai.Ransa du ya baci shi kwata-kwata baya

sonkuka.Bare kukan mace, ballantana kuma zeey

dinshiwanda tun tana yarinya baya kaunar

ganinkukanta…….

 

Wadda tun tana yarinya baya kaunar ganinkukanta, yanzu

yaji hankalinshi ya tashi, sai yanemo mata komai take so

sannan yake samunnutsuwa, bare yanzu data zama

mallakinsa.Ya sanyaya murya can kasa kamar zaiyi

kuka,yace “zainab so kike ki daga min hankali ko?Bakya

son kwanciyar hankalina zeeyta? Ya kikeso nayi da

rayuwata? Zainab tafiyarki gidaawajena ba karamin tashin

hankali bane. Habazeeyta kiyi hakuri ki zauna agidan ki

rikeminamanar kanki da dukiyata da gidana. Yanzu inkika

tafi bakya nan gidan ai kango zai zama.Ya zauna dirshen a

kasa ya jawota jikinsa yanararrashi, kiyi hakuri zainab ki

kwantar dahankalinki ko na samu nutsuwar zuciyata.Zainab

yaki fa zamu tafi, ko muyi nasara ko akashemu . Tayi

firgigit ya dago kanta daga jikinsacikin razana. Tace yaya

mutuwa? Ya maida kantaya kwantar jikinsa. Yace kada ki

damu, ai hakamuke, nasara tana wajen ubangiji mun

dogaradashi zai karemu, cikin hukuncin ubangiji, Allahzai

bamu nasara akan abunda muka jeyi.kita yimin addu’a kinji

kada ki kuma damuwa.Ta dago kanta tace “yaya kayi hakuri

in na batamaka ka yafe min kaji.Bakomai zainab na hakura

na yafe miki ki dainadamuwa ki taimaka min da addu’a.To

yaya na dau alkawari zan tayi maka nafilfili daaddu’o’in

neman nasara. Yauwa kanwata,nagode. Bari naje gida

nawa su Abba da daddymaganar tafiyan, wa kike so akwo

miki ta tayakizama?Hajiya.”yace, hajiya babba?Ta daga

kai. Yace babbar magana, bari na gayamusu, ai ‘yar gatan

hajiya ce ke zata zo.Yana fita ta mike ta shiga kicin zata

tanadarmasa abunda zaiyi guziri dashi.Tana gamawa ta

shiga tayi wanka, tayi alwalatayi sallar la’asar, ta tsala

kwalliyarta da orangedin shadda, ta kafa daurinta tayi kyau

tanatasheki kamar ba ita bace tasha kuka dazu ba. Tajeta

bude jakar tafiyar ta zuba mishi kunshin ledamai kyalli guda

hudu, daya hadadden kek ne datayi masa mai kwakwa,

dayar kuma mitfy, dayarkuma kwallon kaza, sai soyayyen

cincin maisugar data ke dashi, ta dibar masa. Daya

kena’uroro sun zo mana masu saukaka mana aiki,shiyasa

nan da nan ta gama.Aliyu kuwa daya jewa iyayensa

maganar tafiya,nasihohi suka yi masa kamar yanda suka

saba,suka yi masa addu’ar samun nasara da

fatanalkhairi.Daya zo wajen hajiya yake fada mata

sakonmuniyarta, hajiya tace “Allah sarki, ai zainab cesaina

zo na tayata zama, yarinya mai hankali danutsuwa, ka gaya

mata ta kwantar da hankalintakana tafiya direba zai

kawoni.”Aliyu yace yauwa hajiyarmu, kakarmu ta kanmu,ya

bata kudi mai yawa taita masa godiya, yabawa su umma

suma sukaita masa godiya da saalbarka.Ya amsa da Amin,

ya shige motarsa ya tafigidanshi, yana ganin gimbiyar sai

yaji hankalinshiya tashi daya tua tafiya zaiyi ya barta har

nawani lokaci.Ta tare shi tana murmushi tare dayi masa

sannuda zuwa, ya zuba mata ido da irin kallon nan

maibirkita kwanyar masoyi, ya nufi wajenta, ya

warehannunshi ya rungumeta yana sumbatarta ahankali

kamar zai hadiyeta.Du kunya da nauyinshi ya isheta,

kokarin zamewatake daga jikinsa amma yaki ya bata

damarhakan saima ya kara matseta ajikinshi.Sannan ya

zauna akan kujera yana shafa kanta,du ta noke ajikinsa

kunyarsa take ji sosai.Ya rada mata a kunnenta yaushe zaki

daina minkunyar nan ne Amma zanyi kokari na rabaki

dakunyar nan.ta rufe fuskarta ta zame daga jikinsa tana

maitsananin jin nauyin abunda ya fada mata.Yace baki bani

abinci bafa taso muje ki baniabinci yunwa nake ji.Da kyar

ta mike tayi gaba yana biye da ita harzuwa tebir din, ta

bude abincin kamshinsa yabugeshi. Malmala biyu ta cire

daga ledar sunataturiri ta zuba kan filet din tangaram, ta

zubamiyan cikan tagaran din ta zuba masa kunun aya,ta

rinka tura masa gabansa. A hankali tace kacimana.Ya

jawota ya zaunar da ita acinyarsa, yace waihar yanzu

kunyarce ne? Don Allah ki cire kunyarnan ki bani abaki.

Tace um-um, nidai bazan iyabadon Allah ka kyaleni.Ta mike

da gudu tai cikin daki, yabi ta da kalloyana murmushi, saida

ta shige ciki ya girgiza kaiya kama cin abincin yana mai jin

dadinsa sosai.Ya rinka shan kunun ayar nan da yaji

madararruwa yana santi.Saida ya gama ci, ya shiga

dakinsa ya fadatoilet, yaga ta tara masa ruwan wanka a

baho, yashiga yayi wanka ya fito.Ya shirya cikin kakinsa, ya

fito ya shiga dakinta.Tana zaune abakin gado tayi tagumi,

ya zaunakusa da ita ya cire hannun tagumin yace babukyau

ki daina, ya ciro sabuwar waya akwalinta yamika mata. Ga

waya zainab kullum zamu kasancetare awaya kinji.Ta daga

kai tace nagode.Ya fito da kudi masu yawa ya mika mata,

ungowannan kirike a hannunki ki rinka ‘yan bukatunki.Ta

bude baki cike da mamaki, tace ai yaya kudinsunyi yawa,

me zan siya? Komai fa da akwai asito.Ta karba ta raba

kudin biyu, tasa masa rabi aaljihunsa, don Allah yaya ka

barsu wa’yannan masun isa nagode Allah kara budi.Yace

Amin nagode nji dadin addu’arki. Ya mikezainab zan tafi?

Ta dago kanta a sanyaye yayatafiyar zakayi? Sai kuma

hawaye. Ya dawo yazauna, ya jawota jikinsa, sai kuma ta

sakar masakuka……kawaisai tausayinta ya kamani na

tsaya da rubutun ina kallonsu

 

Bakwa komai

[9:20AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**16 &  2**17

 

Ya dawo ya zauna, ya jawota jikinsa, sai kuma tasakar

masa kuka.Ya rinka rarrashinta yana lallaminta

kamaryarinyar goye dake jikin mamanta, kiyi shiruzeeyta

kiyi hakuri bazan dade ba zan dawo, mekike so na siyo

miki? Ta girgiza kai bakomai.” yadago kanta yana share

mata hawayen, to kiyishiru bana son kukan nan, yana daga

minhankali.Ta hadiye kukan tana ajiyar zuciya, ya

rinkararrashinta yana lallaminta tare da dan

bubbugabayanta, sanyin iskar data rinka ji ta cikinkunnenta

shiya saukar mata da kasala jikinta yasaki kawai sai bacci

ya dauketa.Ya lallaba a hankali ya shimfideta, sadaf-sadaf

yafita ya shiga dakinsa, ya dauki jakar kayansa yafice ya

fada motarsa, ya sallami mai gadi yayiwaje da gudu ya

dauki hanyar kaduna.A zuciyarshi yana tunani zeey dinshi

saita tashitaga ya tafi.Kai zeey da rigima take, du ta daga

masa hankali,inba dole ba yaushe zai tafi wani waje ya

barta.Ya zari wayarsa ya bugawa hajiya,yace dan Allah

hajiya direba ya kaiki yanzu fanabar zeey ita kadai a

gidan.Hajiya tace ai kayana ma ake sawa a mota

yanzuzamu tafi.Yauwa hajiyata nagode. Ya kashe wayar.

Lokacindaya isa kaduna ya tarar da abokinsa faruk

yanajiransa, suka rungume juna, ya dakkowa Aliyutakardar,

Aliyu ya bude ya karanta yaji bayananda suke ciki.Aliyu ya

ninke yace to Allah ya taimaka mana.Faruk yace, bari na

karasa gida na barka kadanhuta kayi shirye-shiryenka.

Tafiyar asuba zamuyigwanda ka kwanta da wuri. Aliyu yace

badamuwa. Ya rakoshi wajen motarsa ya tafi.Aliyu ya shigo

cikin gida ya wuce dakinsa, yafada toilet yayi wanka yayo

alwala yayi sallah,yayi addu’o’insa ya shafa.Ya shafa

cikinsa daya ji yunwa ta fara matsamasa, yasan yayi

maraicin zainab ko don yandatake kula dashi wajen abinci,

yanzu dole saide yahada shayi yasha, don ya gaji bazai iya

fita gidanwani abinci ba.Gashi yaronsa maiyi masa girki

shima yaje ganingida bai dawo ba. Ya bude wayarsa ya

dannalambar zeey dinshi, ringin daya tayi ana biyu

akadauka, “hello yaya.” saita sa masa kukanshagwaba. Ya

kama rarrashi, yi shiru yi hakurizeeyta, daina kukan gaya

min meye? Mene nezeeyta? Gaya min kinji babyna.Yaya

shine kayi min wayo kasani bacci ka guduko? Yaya kuma

kudin dana raba biyu na dau rabinace maka sun isheni na

baka rabin shine kaajiye min ko?Oh! Sorry zeeyta, bazan

kuma ba nadaina kinji,daina kukan kina tsiyayar min da

hawayenki maitsada a kasa, gashi bana kusa bare na

tsotse.Tace, ka gani zaka fara ko?To na daina, hajiya tazo

ko?Hajiya tazo tuntuni, suna falo ita da hamza dasadik

suna hira.Yace, yauwa ai nasan bazasu barmin ke

cikindamuwa ba zasu rinka zuwa suna tayaki hira. Keko dai

kinci abinci? Bana so ki rinka zama dayunwa fa, ki rinka cin

abinci sosai kinji?Tace, to yaya ai kaima baka ci ba.To ni

wa zai bani zeeyta? Yanzu ma zan jonahita na tafasa

ruwan shayi nasha, don yunwanakeji.Ya marairaice masa

tace, haba yaya da kanka?Yace to ya zanyi zeeyta, wa zaiyi

min? Tace yayaka duba cikin kayanka da akwai sako.Sakon

me?Um-um nidai bazan gaya maka ba, ka budeyanzu inka

kashe wayar.”yace to.Ya kashe wayar ya jawo jakar kayan

nasa yanabudewa, yaga nadi-nadi na leda har kashi

hudu.Ya rinka warewa ganin abubuwan da suke cikiyasa shi

tsananin mamaki da al’ajabi, a yaushezeey tayi wannan

aikin? Kai wannan yarinyaubangiji Allah yayi mata albarka.

Hakika yaji dadita faranta masa sosai, ya daga hannunsa

yanayiwa Allah godiya. Allah na gode maka da

wannanbaiwa dakayi min nasamun nutsasiyar mace

maihakuri da sanin ya kamata.Ya ware komai ya rinka ci

cikin nutsuwa danishadi, saida yaci ya koshi yasha lemo

yayigyatsa yayi hamda ga ubangiji, yaita shiwazainab

albarka a zuciyarsa.Yayi waya gida ya sanarwa mahaifansa

ya isolafiya, ya bugawa mansura itama ya gaya mataya iso

lafiya, taba shi Ahmad sukayi hirarsu yanagaya masa

abunda zai sissiyo masa.Mansura ma ta karba ta gaya

masa abubuwandatake bukata, sukayi sallama. Yana kashe

wayarzeey dinshi ya sake bugawa.Tana dauka tace, hello!

Yayana ka koshi?Nakoshi zeeyta Allah yayi miki

albarka.Amin yaya nagode.Yace, wai zainab ba zaki rinka

gayamin sunayendana ji kin radamin ba, mazan jiya da

mazaje?Tace “kai yaya nidai ban zan iyaba, da dinma

danbansan kai bane ba.To yanzu me zaki rinka gayamin?

Honey ko myluv?Tace, kai yaya dan Allah ka bari.Yace, au

bazaki gayamin kalmar da zata sanibacci cikin nishadi ba?

Sai ya kashe wayar.Ta dafe kai tace kai yaya da saurin

fushi yake,toni yanzu ya zanyi masa? Ta dake ta bugamasa

wayar, ya dauka yace uhm! Ina jinki. Cikinsanyita tace yaya

fushi kayi? Don Allah kayihakuri kada ka kwana kana fushi

dani kaji.Yace to naji na hakura, amma saikin cemin I

luvu.Tace, kai yaya don Allah….Au bazaki fada ba?Saika ce

mai koyon magana ta fada da dai-dai, iluv u, tayi saurin

kashe wayar. Yayi dariya yanamaijin dadin hankalin zeey

din tashi dakuruciyarta.Da asuba yayi sallama da iyayensa

da iyalansa,jirginsu ya daga zuwa bayelsa….

 

Da asuba yayi sallama da iyayensada iyalansa, jirginsu ya

daga zuwabayelsa.Zainab suna tare da hajiya bata dawata

matsala, hajita macece maibarkwanci da sanin ya kamata.

Tai tanusar da ita yanda zata zauna damijinta, da yanda

zata rinka yi masabiyayya.Ga ‘yan gidansu su sadik, faruk,

dahamza, sun riga sun saba hirarsu awajen hajiya, to dole

wajen hajiyansuke tahowa nan gidan zainab dindon haka

zainab take cikin nishadi,kullum tana ganin kamar a

gidatake.Aunty sadiya ta sai musu littafankaratu, tunda ta

karanta matar so,saita ji lallai itama tana so tayi huldada

aunty hadizan nan, ko don tabata shawara ma kan nata

auren,gaskiya zata nemeta dan ta samushawar wari da

zasu tallafa mata garayuwar auren su.Ta jawo wayarta ta

buga mata,ringin daya biyu ana uku ta dauka,”hello wake

magana?Aunty hadiza bakuwace ina wuni?Lafiya lau.”ya

gida ya harkoki?Alhamdulillah.Aunty ina karanta wani littafi

matarso, sai naji matsalar khadija, wallahinima ina cikin

matsala.Matsala kamar ya ya? Mijin ne bayasonki? A’a

yana sona, auren namu nenake ganin kamar na cin

amana.Daga nan ta bata labarin komai dayanda akayi

auren.Aunty hadiza tayi dariya tace, zainabkika ce sunanki

ko?Tace, eh.Aunty hadiza tace Allah sarki gaki dasunan

‘yata zeey auta, haba zainabkada ki bada mata mana akan

watasaiki ki farantawa mijinki alhali bawaje daya kuke da

ita ba.To ki saki jikinki ki farantawamijinki rai, du abunda

kika san zaisashi farin ciki kiyi masa, ki kyautatamasa,

abokiyar zamanki ki riketa dadaraja da mutunci, kada ki

bari wataharkar raini ta shiga tsakaninku.Kada ki sake kiyi

mata rashin kunyako ki wulakantata, yanda kike

ganinmutuncinta da darajar a da, to kikara ninkawa akan na

da din.Amma zainab na fuskanci ke yarinyace baki san

komai ba, don haka zangyaraki, zan koya miki yanda

akegyara jiki, na koya miki yanda akehada turare na ruwa

dana wuta, fararhumra da baka da kulacca, hadinman

gashi da zaiyi tsantsi da tsawo,ya rinka sheki da yana

daukan ido.Sannan na koya miki yanda akehadin lallen

kunshi wanda aketurarawa jiki yana kamshi, sai yayiwata

biyu a kafarki bai fita ba.Tayi caraf tace, don Allah

auntyyaushe zaki koya min? Wallahi inason kunshi da

gyaran jiki, kumawallahi inason turarunkan nan masukama

jiki da kama daki.To shikenan zainab, zan rubuto mikisu na

turo miki.Yauwa aunty nagode, Allah ya sakada alkhairi.

Don Allah aunty sainajiki.Uhm! Karki damu.”to aunty, ki

huta lafiya.To nagode.*** *** *******lawisa bayan kwana

uku tazo,mansura ta tareta da murna, ya akayimutuniyar,

kinje?Ai naje, ga abubuwa ya bayar ta fitoda kulle-

kullentq,wannan gashi aruwan wanka zaki zuba

masa,wannan ki barbada a shimfidar dazai kwanta,

wannan kuma kiyi kokarikisa musu acikin abunda zasu

ci.Gaba dayansu ita dashi zasu tsanijunansu, baza taba

jituwa ba har saian raba auren.”yauwa aminiyata nagode,

gaskiyikinyi min kokari, amma kuma wanihanzari ba gudu

ba kinsan Aliyubaya gari kuwa? Ta dafe kirji, ina yatafi?Yau

kwanansa biyu da tafiyakaduna, jiya kuma sun tafi

bayelsa,zasu yi sati hudu.Lawisa tace ba yanzu maganin

zaifara aiki bama kenan, to da ita yatafi?Mansura tace,

haba ina zashi da ita,tana can inda ya ajiyeta.To mu shirya

muje gidan muci matamutunci, mu tsorata ta mu fakiidonta

mu zuba mata maganin aabincinta ta tsane shi kafin ya

dawo.Daya dawo ta burkice ta zuba masarashin mutunci,

ke kuma saikiyi masaamfani dana wajenki, shima yatsaneta

ya burkice ya saketa, kingashikenan mun samu aiki a

saukake.Mansura tace, ai dole sai dai mu barisai ya dawo,

don bata yanda zanyinaje gidanta.Saboda me? Lawisa ta

tarinumfashinta.Ai hajiya kakarsu tana gidan.Lawisa tace ai

kaji, munafukai kawai,wato har gadinta akeyi, ki nemi

wajeki boye, kawai idan ya dawo din saiayi amfani dashi.To

shikenan lawisa nagode**** *** ******da safe suna yin

break sadik ya shigoda sallama, ya gaida hajiya

sannanzainab ta gaisheshi, sadik yace hajiyakin gama

mutafi? Don nayiwa likitawaya yana asibitin.”hajiya tace,

nagama mana, nida nakeshiri tun asuba. Zainab tace,

donAllah hajiya zan biku asibitin, hajiyatace, waya gaya

miki mace tana fitaba tare da iznin mijinta ba? To donAllah

hajiya na buga masa wayar kigaya masa?Sadik yace a’a

wallahi bazata gayamasa ba, ba mijinki bane ki gayamasa

da kanki mana.Zainab tace, kai don Allah, yayasadik wai ina

ruwanka ne? Don Allahhajiya kinji, kinga ni kadai zaku baria

gidan shiru bazan ji dadi ba.Hajiya tace saika ce wanda

zamushekara a can, naga dana gamaganin likitan nan zan

taho ba indazan biya.Ta zumbura baki cikin shagwaba,nidai

hajiya bazaki tafi ki barni nikadai ba, inma bazaku je

asibitindani ba, to ku ajiyeni gidan yayani’ima, inku dawo

saiku biyo ni mutafi.Hajiya tace banki taki ba amma

farabugawa mijinki waya, abunda yaceshikenan.Sadik yace

hajiya kema kin wanidaka ta tata, sai wani lallabata kikeyi,

ki kyaleta ki taho mu tafi, hajiyatace ai dole….

[9:22AM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 2**18

Hajiya tace, ai dole na lallabata,

mijinta amana fa ya barmin ita.

Sadik haushi ya cika shi, don shi

yana da wajen zuwa su kuma gashi

suna bata masa lokaci.

Sadik ya fito da wayarsa ya buga,

can Aliyu ya dauka, hello sadik kun

isa asibitin ne? Yace, wallahi zainab

tana ta bata mana lokaci.

Yaya Aliyu yace bani zainab din.

Ya mika mata wayar. Tace hello,

yaya, yace zeeyta ya akayi su hajiya

basu tafi bane?

Tace, don Allah don Annabi, yaya

mu tafi tare na rakasu, tsoro nakeji

ni kadai a gidan.”

haba zeeyta, ko zaki fita ai saina

dawo mu fita tare, yaushe zan bari ki

fita ni ina nan wani gaular ya kallar

min ke. Yanzu ma munyi yanda

zamu bullowa mutanen, damun

gama zanyo miki waya muyi hirar

mu har su dawo, yanzu ki bawa sadik

wayarsa, kiyi wa hajiya bye-bye kice

sai sun dawo, Allah ya kiyaye hanya,

kinji zeeyta? Amma fa kada ki damu,

kiyi hakuri kinji?

Tace, to yaya na hakura.

Yauwa zeeyta Allah yayi miki

Albarka. Amin yaya.” ta mikawa

sadik wayar ya kashe yasa a aljihu

yace hajiya mu tafi.

Zainab ta rakosu har kofar falo da

dariyarta, tana musu Allah kiyaye

hanya.

Hajiya taji dadi a ranta ta yaba

hakurin zainab da biyayyarta.

Suna fita tasa mukulli a kofar falon

ta rufe, ta shige daki ta fada

gadonta, ta jawo wayarta ta buga.

Ringin biyu aka dauka, hello, aunty

hadiza kiyi hakuri kada kiga na

dameki. Lah haba bakomai wallahi,

ai irinku muke so masu son gyara

aurensu.

To aunty dan Allah ki fara gaya min

sirrikan turarukan.

Kin shirya na fara gaya miki.

Eh na shirya aunty (so wajen yanda

ake hada turarukan na tsallake bt

inkuna son yanda akeyi zan rubuta

muku bayan mun gama). Zainab ta

shiga tunanin irin nasihar da

malamansu suke yi musu game da

zaman rayuwar aure, ta tuna irin

burin da suka rinka ci na yanda zasu

kyautatawa mazajensu, to ita gashi

yanda nata auren ya kasance mata,

dole ta share komai ta rufe idonta ta

nunawa mijinta kulawa ta

musamman.

Tun daga lokacin ta kasance bata

bacci da dare, ta kara kusanta kanta

ga ubangiji tana yawan yin nafilfili,

tai ta kirari ga ubangiji tana

rokonshi daya bata ikon yin biyayya

ga mijinta, Allah ya tsaresu ya kuma

karesu dukkan wani sharri da bala’i

da zai tunkaresu. Allah ya hade

kansu da abokiyar zamanta.

Mijinta kuma, Allah ya karesu, aikin

da suke yi Allah ya basu nasara, ya

kuma dawo dasu lafiya.

Kullum saita yi tashin dare tayi

nafila da wa’yanan addu’o’in, hajiya

ta rinka jin dadi tana kara karfafa

mata gwiwa data ci gaba dayin

hakan, hanya ce ta tsira, alamomi ne

kuma daga mace tagari.

Ta sake bugawa auntynta waya

cewar, don Allah duk turaruka data

lissafa ta hado mata, harda man

gashi da turaren tsuguno na jiki

dana dakuna.

Aunty tace kada ki damu zan kawo

miki harda hadin kayan itatuwa da

zakiyi amfani dashi na karin ni’ima.

Tayi ‘yar dariya, tace kai aunty har

kin bani kunya.”

kwana hudu a tsakani auntynta ta

hado komai ta kawo mata.

Cikin lokaci kankani zainab ta canja

tayi wani irin kyau, fatarta ta goge

sosai saboda turaren jiki data keyi,

kamshi ya kama jikinta ko yaushe

tana cikin kamshi mai dadi.

Dakunanta kuwa duk wanda ya shiga

baya so ya fito saboda fitinan

kamshi da mutum yake shaka, gaba

daya gidan nata kamshi yake mai

dadin shaka, du saida ta dibarwa

‘yan uwanta aunty sadiya da yaya

ni’ima.

Kwanci tashi ba wuya a wajen Allah,

yau Aliyu satinsu biyar kenan a

bayelsa, sunyi kokari su dawo a sati

biyu da suka ce zasuyi

to abun ya ci tura, gashi har sunyi

sati biyar, yau da mangariba hajiya

tana daki tana lazimi, don intayi

sallar magariba bata tashi daga

wurin sai tayi sallar isha.

Zainab tana falo tana shan romon

kaza da aka dafa mata da

magangunan karin ni’ima, irin cikin

kayan da auntyn nata ta hada mata.

Wayarta tayi kara ta dauka, tace

hello, yayana, kaki ka dawo yaya sai

yaushene?

Yace, au zeeyta kina so na dawo ne?

Ina so mana, yaya nafi so ka dawo

gida.” to gaya min me kika tanadar

min? Me zaki bani? Zaki shayar dani

madarar soyayya? Kai dan Allah yaya

ni bana son irin wannan maganar.

To gaya min wani iri kike so?

Tace nidai kawai so nake ka dawo

to kin yarda in na dawo zamu rinka

kwana gado daya tare na jiki manne

a jikina, ina ririta ki inayi miki

lallamin kauna?

Tace don Allah yaya kabari.

To shikenan tunda bakya so na

dawo. Yaya inaso mana, yaushe zaka

dawo? Yace insha Allahu yau saura

kwana shidda na dawo, amma ki sani

dana dawo zan yaye miki wannan

hijabin kunyar, don ni take cuta.”

tace, yaya nidai don Allah saida

safe.” yace, au abin ma hakane,

shikenan mu kwana lafiya.

Da safe zainab take gayawa hajiya

maganar dawowar yaya Aliyu saura

kwana biyar, hajiya ta rangada guda

tace, ina baiwar Allah nan data miki

turarrukan nan tazo ta gyara minke,

bani lambar wayarta na kirawota da

kaina.

Washe gari auntyn suka zo da aka

fara gyaran amarya zainab, kwana

uku ana gyaran jikin zainab, ranar

kwana na hudu akazo akayi mata

kunshi, akayi mata sarkar kafa data

hannu. Ana gamawa aka wuce da ita

salon, aka gyara mata gashi suka

dawo gida, zanso kuga yanda

wannan tauraruwar mata take.

Saimun hadu a littafi na uku      Sai night  kuma😜😜😜

[9:16PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**1

To yanzu mai kika shirya na tarar

angon naki?

Cikin jin kunya tace “aunty me kike

ganin za ayi masa?

Ina ganin ayi masa girkin zamani.

Karfe nawa yace miki zasu iso?

Tace, karfe hudu zasu iso gida.

To gobe saiki tashi da wuri sai kiyi

masa satisfishal din girke-girke,

dakko littafi da biro na koya miki

wasu girke-girken.

Ta dakko da sauri ta rurrubuta mata

wasu, tayi mata sallama ta tafi. Da

safe tasa aka turo mata mata guda

biyu ‘yan aikin gidansu don su

tayata aiki.

(zan wuce wajen grike-girken nan).

Ta gyara tebir din ta shimfida leda

me cin bakin les da adon fulawoyi,

akan tebir din ta jera saitin filas din

akai guda uku, daya farar shinkafa,

daya jalof din makaroni, daya miyar

kaji.

Sannan ta jere saitin tangarayen nan

guda biyar, daya soyayyan kwai cikin

nama, daya kuma samosa, daya

spring rolls, daya kuma gasasshen

nama me romo ta dasa fulawa a

tsakiyar tebir din.

Su jimmale suka gyara mata gidan

suka share ko ina, suka goge yana ta

zuba kyalli.

Hajiya data ga yanda aka gyara tebir

din aka cikashi da kayan abinci, ta

rinka gyada kai tana murmushi, tana

cewa ma me cikin zani yanda zaiyi

da wannan kayan abincin. Ko giwa

ne shi ai ba zasu ciyu ba awajensa.

Hajiya tace, jimmale tunda kun

gama kunci abinci, ku zo mu tafi

tare daku. Zainab ta rike hajiya ta

marairaice mata, don Allah hajiya

kiyi zamanki kada ki tafi.”

hajiya tace, ke baki da kai ne, yanzu

sadik suka gama waya dashi jirginsu

ya sauka ya za ayi na zauna har ya

sameni?

Haba hajiya ki zauna mana mu duk

ba jikokin ki bane?

Hajiya tace, uhm kyayi kya gama

jummale ku shige muje.

Zainab tace, hajiya ai baki cinye

abinciccikan naki ba.

To taya zan iya cinye wannan girke-

girken haka? Jimmale kwashi ki saka

min a mota, in munje gida naci.”

zainab ta rike hajiya tana kuka,

hajiya tace, to ai ke kinga halinki,

bakya so kenan inya kuma tafiya

inzo in zauna miki ko? Tace a’a

hajiya inaso, don Allah ki dawo, tace

to zan dawo, amma sai kinyi shiru,

kije ki shiga wankan.

Tace to, ta tafi dakinta ta shiga

toilet ta fara wanka, hajiya dasu

jimmale suka yi saurin tafiya kafin ta

fito.

Yaya Aliyu kuwa karfe uku suka

sauka da abokansa su bakwai da

faruk, usman, hafiz, Anas, Amir da

bashir sai Aliyu na bakwai.

Gaba daya suka ce, sai sun biyo Aliyu

sun gano amarya tunda yayi aure su

suna nesa, bai gayyacesu ba.

Yace, to kuma ba sai ku bari sai wata

rana kwazo ba, sai yau mun dade

bamu ga juna ba, ina dokin ganin

‘yar kanwata kuma saiku bini ku

katsemin hanzari?

Usman yace, kaji zancen banza, yana

wani kanwarsa wa ya sani ma ko tuni

ya gama aiki? Faruk yace tun yaushe

kai ma kasan rawar kan nan da yake

yi kasan ba haka kawai bane, ya

dandani zumar amarci.

Aliyu yace, don Allah ku bari ita fa

karamar yarinya ce, wallahi yanda

nake son zainab nake tausayinta,

bazan iya yin abin da zata wahala

ba, aini rainonta zanta yi sai nan da

wasu shekaru.

Gaba daya suka sa masa dariya suna

tafa hannu, tare da cewar, maji

magani, faruk kaine na kusa dashi ka

bamu labari.

Ita kuma mansura tana ta shiri ita da

Ahmad suka shiga mota, suka shiga

mota sukayi filin jirgi tarar Aliyu,

suna isa filin jirgi suka hangoshi

cikin abokansa, Ahmad ya tafi da

gudu yana kiran daddy! Daddy.”

Aliyu ya juyo da sauri ya daukeshi ya

rungumeshi suna dariya su duka

biyu.

Mansura ta karaso inda suke tana

dariya tace, barka da sauka, Aliyu

yayi dariya ya riko hannunta ya

sumbata, barka dai uwar gida

sarautar mata, mun sameku lafiya.

Lafiya lau.”

ya nuna mata abokansa du da dai

tasan wasu daga ciki, ta gaishesu

suka amsa cikin fara’a, suka rinka

tsokananta mun biyo ango zamu ga

amarya.

Tayi dariyar yake tace, so ni ba zaku

je nawa gidan ba, sai gidan amarya?

Suka ce a’a mu mun isa? Ai sai mun

fara zuwa gidan uwar gida tukun.

Tayi dariya tace, to kun fitar da

kanku.”

gaba daya suka shiga motoci suka yi

gidanta.

Zainab tana fitowa wanka tayi sallar

la’asar, gaba daya gidan ta turareshi,

sihirtaccen kamshin jikinta kuwa sai

tashin fitinanun turarukanta yake yi.

Dai-dai da gashin kanta saida tayi

masa nashi turaren.

Ta saka sabuwar super acikin kayan

lefenta. Tayi kyau sosai, fatarta tayi

wani sulbi da santsi, sai wani shnin

take, tana wani daukan ido, ta lika

kati ajikin kofar shigowa falonsu,

dole du wanda zai shiga falon sai ya

gani.

Katin me kyau ne, yanata kamshi fari

me fulawa, anyi rubutu da hausa da

ruwan gwal, ga abinda yake jiki.

BARKA DA DAWOWA YAYANA INA

TAYAKA MURNA DA SAMUN

NASARA AKAN ABUNDA KUKA JE.

tana lika wani katin akan tebir din

data jera kayan abinci taji tsayuwar

motoci, taji gabanta ya fadi, ta

runtse idonta ta karanto addu’o’i na

yiwa Allah godiya, da isowar yayanta

lafiya.

Ga abunda yake jikin katin tebir din

kamar haka.

GODIYA ME YAWA TA TABBATA

GA ALLAH DAYA DAWO DA

YAYANA CIKIN IYALANSA LAFIYA.

tayi saurin shigewa daki, yaya Aliyu

daya taho da tawagar abokansa

akafar falo yaci karo da katinnan, ya

kalli abokansa sukayi dariya tare da

jinjina masa.

Suna bude falon fitinan kamshinan

ya dakesu, gashi ya hade da sanyin

A.C sai ya rinka feso musu kamshi

mai dadi.

[9:16PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**2 &  3**3

 

Kowa ya shaka sai ya lumshe ido.

Abun bai kara rikitar dasu ba, saida suka shiga falon suka

rinka taka canis cafet, kafarsu tana nitsewa cikin taushi

babu wani datti ko ina a gyare kal-kal yanata sheki. Ga

falon

ya tsaru, dole ko kai ka gani ya baka

sha’awa, gaba dayansu suka zube a

kujeru suna ware gajiya, kusan du a

galabaice suke saboda yunwa.

Faruk ya hangame baki yana ina

matar gidan ne, baza tazo taryar mai

gida ba?

Aliyu yace, bari mana kada ka

tsoratata da wannan muryar taka.” ta

sako hijabi ruwan atamfar dake

jikinta, a hankali ta turo kofar tana

murmushi, tayi musu sallama, tace

don Allah kuyi hakuri. Gaba daya

zuba mata ido sukayi, suna kissima

kyawun zainab da hankalinta, Aliyu

kuwa wasi-wasi yake a ransa, anya

zeey dinshi ce takoma haka? Tabbas

du yanda zeey dinshi takoma, bazai

taba mantata ba.

Ta durkusa a gabanshi, tace “yaya

ina wuni, kun dawo lafiya?

Yayi firgigit kamar wanda ya tashi

daga bacci, yace zeeyta mun sameku

lafiya, ya kike? Ya na dawo na

sameki zeeyta?

Tayi murmushi kawai, ba tare da

tace komai ba, ta gayar da abokan

nasa, suna ta zolayarta da tsokanarta

ita kuwa kunyarsu take ji da

nauyinsu.

Tace yaya kuzo kuci abinci a tebir

mana kona kawo muku nan?

Yace zeeyta har yanzu baki daina

shiga kicin yin girkin nan ba? Ni dai

ina tsoron kada ki kone ko ki yanke,

nasa a nemo miki mai aikin girki.

Ta dan marairaice, tace haba yaya

meye amfanina, in banyi ma girki

ba? Allah yaya bana iya cin abincin

‘yan aiki, saina tajin kyankyami,

koma tashin zuciya.

Usman yace gaskiya kin burgeni,

inason mutum mai iya tattalin

lafiyarsa. Faruk ya mike yace nidai

kuzo muje ga tebir din nan don

yunwa nakeji. Nasir yace badai koshi

zakayi ba, abunda aka shiryawa

mutum daya mun debo jiki har mu

bakwai kowa yadan taba mu bar

mishi abincinsa.

Zainab tace, haba don Allah ku

cinye, ni wallahi saina shiga kicin na girka muku wani, ai ba

wahala.

Aliyu ya riko hannunta, kyalesu

zeeyta, sa karata a hotel ba zasu

wahalar min dake ba.

Usman yace, ai aci har dakai a hotal

din.

Zainab ta musu ja gaba har inda

tebir din yake, suka jawo kujerun

duk suka zauna. Tana fara bude

abincin cikar kamshi ya rinka

bugunsu, suka rinka hadiyar yawu.

Tana bude musu abincikan suka ga

uwar dinar kamar awajen walima

zata fara sabis dinsu Aliyu ya kirata, zainab jeki daki ki

huta, tace to.

Cikin sanyinta.

Shikuwa Aliyu kishintane yasa yace

tabar wajen, saboda lafiyayyen

kunshi daya hango a hannunta, sun shagala suna cin dinar

sunata santi,

Aliyu ya silale yayi daki wajen

amaryarsa.

Ya tabata yana sansanar kamshin

jikinta, cikin sarkewar murya tace

yaya bazaka ci abinci ba, ka taho

nan?

Yace, zeeyta kin rikitani dayawa, wai kece kuwa zeeyta, me

kike ci kika canja haka, bana kusa bare nace

abune ya karbeki, gaya min zeeyta

meye sirrin wannan kyau da kika

kara? Ba ruwanki kinyi kyau kin kara fari abunki bakya

tunanina, ko

zeeyta? A hankali, tace haba yaya wa ya gaya maka?

Gashinan kuwa na gani kin kara kyau da murjewa, ni kuwa

ina can

tunaninki ya hanani sukuni, kullum

saina yi mafarkinki. Ya kamo

hannunta ya rinka sha’awar kunshi

ya rinka sa zara-zaran yatsunta

abakinsa ya tsotsa, yana lumshe ido.

Ya rinka shafa tafin kafarta yana

yaba kyan kunshin, ga laushin

fatarta da wani tsantsi da yaji tana

yi, dadadan kamshi daya yake shaka a jikinta du yasa shi

ya birkice. Ya

taba nan ya taba can, ita kuma du ta rasa yanda zatayi da

kunyarsa du ya wani birkice mata kaman ba yayanta ba.

Taji yana kokarin wuce gona da iri,

ta rike hannunsa tace don Allah yaya

kabari, yayi kasa da muryarsa yana

cewa me zan bari zeeyta, wa yayi

miki wannan kunshin?

Ya zame dankwalin nata, ya rinka

yamutsa gashin nata yana tura kansa

cikin gashin nata, ya ilahi, wannan

wane irin kamshine me dadi da saka ka shiga wani hali na

yanayin

sha’awa da shaukin bege? Wai shin

yaya zaiyi da zeey dinshi ne, anya zai

iya hakuri da yarinyar nan har zuwa

wasu shekaru daya ambata?

La a ina! Irin wanan jiki haka mai tsantsi da laushi, kamar

tufa.

Ta rike hannunshi cikin shagwabarta

tace, yaya kabari, banaso. Idonsa

yana lumshe ya marairaice mata,

yana cewa, ni mijinki nefa zeeyta

kike gaya min haka, bakya son

aljanna? Cikin sanyita tace kayi

hakuri yaya.

Wayarsa tayi kara, yana dagawa yasa

dariya, yana cewa aini na manta

daku ma, gani nan fitowa.

Yana fita suka haushi da tsiya,

usman ya kwala mata kira amarya

zamu tafi. Ta sako hijabinta ta fito tana dan murmushi,

suka ce amarya fa mun gode, kin cika mana ciki da girki

masu dadi, kin hada mana

walima tunda bamu samu zuwa ta

aure ba ko, amma ma hadu ata suna, nan da wata tara ko?

Taji kunya sosai ta sunkuyar da kai,

Aliyu kuwa ya zuba mata ido, don

yaga yanayin da zata nuna.

Suka dire mata dubu goma-goma,

cikin sanyita tace don Allah ku

barshi ku debi kudinku.

A’a amarya kar muyi haka dake sai

gani na biyu inmun kawo iyalanmu.

Tayi musu godiya suka tafi, ta shiga toilet ta hada masa

ruwan wanka, ta zuba turaren wanka, nan da nan ruwan ya

dauki kamshi.

Yana shigowa ya fada toilet, yaji

dadi daya samu ta hada..

Fitinannan kamshin danaji shiyasa ni tsayawa da rubutu

batare dana shirya ba, amma dai bari naci gaba

 

Yana shigowa ya fada toilet, yajidadi da yaga ta hada masa

ruwayana ta tashin kamshi, ya rinkatunanin irin wannan

kamshi iri-iri dayake jin a wajen zeey din tashi, yanawankan

cikin nishadi kamar kadaruwan ya kare.Ya fito ya shirya ya

fito kan tebirdin, ya kwala mata kira ta fito ahankali cikin

nutsuwa salon yangartatana tafiya das-das kamar bata

sontaka kasa.Ya zuba mata ido yana kare wakwalliyarta

kallo, amma tunaninyanda akayi ta kara samunsihirtaccen

kyau na ban mamaki.Tace, yaya gani, yace zauna.

Yayindaya gyara mata kujera, ta zauna tasunkuyar da kanta

tana wasa dayatsun hannunta.Yace, bisimillah muci

abincin, taceyaya na koshi.Yace, a’a zeeyta kada muyi

hakadake, ‘yar kanwata nasan wannanhidimar da kikayi

mana bata barkikinci abinci ba, kisa hannu mucikona yi miki

dura…um-hum.Ya karasa taji kunyarsa tasan tanajin

yunwa, amma yaushe ammayaushe zata iya cin abinci a

gabanshiyanda ya tsareta da kallo haka, batayi aune ba taji

abinci a bakinta tace,don Allah yaya kayi hakuri zaci

dakaina.Yace, to ci.Ta fara ci a yangace.Ya rinka ci yana yi

mata santi, waidama zainab makarantar koyon girkikika yi

ne?Tayi murmushi yana ta cika bakiyana yi mata santi, har

ya koshi.Ya mike akan doguwar kujera yana,wash nafa gaji,

kamata yayi karnakuma fita saida safe.”wayarsa ta

dameshi da burari, yadaga “hello mansura.Tuni zainab ta

bace daga wajen,haba Aliyu wulakanci zakayi minkadawo

daga tafiya ko zaman rabinawa baka yi damu ba, ka fice

kayitafiyarka, kayi zamanka?To naji gani nan zuwa, ya

kirazainab a waya ta fito, ya mika matahannu saita noke ta

zauna akasa kankafet.Yace bari naje wajen auntynki

yanzuzan dawo.” tace adawo lafiya, Allahya kiyaye.A

gidanshi mansura ta taho masa dalemo daya sha magani

maimakonkaji kamshi sai baurin maganin.Tasan sarai Aliyu

yana da kyankyamikamar likita yake, wajen

tattalinlafiyarsa.Ahmad ya taho da gudu ya fadacinyar

babansa yana murna, kafarsata zunguri jug din lemon ta

bare,mansura ta zuba masa uban dukandaya gigita shi.

Ahmad ya kwalawata irin karan kuka ya rukunkumeAliyu.

Shikuma Aliyu ya rinkararrashinsayana shafa masa wajen

ransa yayimasifar baci, ya zuba wa mansurawata irin

harara data sata nutsuwa,ya doka tsaki yayi bal da jug din

yatarwatse, ya dauki dansa yayi wajedashi.Mansura tayi

tsaki, uban ‘yan bakarzuciyar tsiya. Yaro ya jawo min

asarakace bazan hukuntashi ba.Zainab tana zaune a falo

tajisallamar Aliyu, ta dago kai tanaamsa sallamar, karaf

suka hada idoda Ahmad, da gudu Ahmad din yataho ya

rugumeta yana dariya, auntymamita ina kika tafi na dade

banaganinki?Ta rungumeshi tana shafa kansa,Ahmad dina

ka kara girma, yakaratu, kana zuwa islamiya ko? Inazuwa

mana, jiya ma saida malam yadakeni, wai ban iya komai

ba, yacena gaya masa sharrudan sallah, dafarilla sallah da

watanni musulunci,du ban sansuba shine ya dakeni.Ranta

ya baci data ji zancen duka,tace to malamin bai rubuta

muku, yakoya muku ba?Yayi mana, ni kuma na manta,

danazo gida na dakkowa mamana, naceta biya min, tace,

na kyalleta baccizatayi. Aunty mami dama kece mekoya

min bakya nan to ya zanyi?Shiyasa malam yake

dukana.Tayi tsaki, kayi hakuri yarona,zamuyi zaman mu

tare dakai anannai ta koya maka kaji.Yauwa aunty

mamena, nafi sonzama wajenki, mamana fadane daita ga

duka.Du Aliyu yana kwance kan duguwarkujera yana jinsu,

ta fara koya mishiyana nanatawa, saida taji ya rike yaiya

tukunna ta shiga kicin ta hadamasa abinci da lemu, ya rinka

ciyana santi, aunty mami kin iya girkimai dadi, anan zanyi

zamana, naitacin girki mai dadi.Tayi dariya Allah Ahmad

dina? Kacedaddynka ya kawo ma kayanka kadawo nan

kaji.Aliyu yana kallon yanda take tatattalinsa, koda daddare

ma dayakoma gidan mansura yi matasallama ta

tambayeshi ina ahmad,banza yayi mata, bai kulata ba, to

bafuskar da zatayi masa fitsara, donhaka taja bakinta tayi

shiru.Lokacin da ya dawo tuni sunyi bacci,suna gado daya

ya kallesu cike dasha’awa yayi murmushi, sai ya

yayebargon ya shiga tsakiyarsu.Daya fita sallar asuba ya

wucedakinsa, da safe yana jinkwaramniyar Ahmad da

zainab akicin ta gama komai ta jera akantebir, tayiwa

Ahmad wanka, ta shafamasa hoda tasa mai kwalli,

tasamishi dan pant, tunda ba kayansa, tatura shi tace yaje

gaida daddynshi,ita kuma ta shiga wanka. Aliyu yabude

cikin kayan tsarabarsu ya fitomasa da t.shit masu kyau,

Ahmad yasaka yana ta murna.Suna kan tebir suna break,

wayarAliyu tayi kara, Ahmad yayi saurindauka.Mansura

tace, Ahmad kana ina?Ina wajen aunty mami, tana banidadi

dadi.Tana ina zainab din?Gata nan.To bata wayar.”Ahmad

yasa mata wayar a kunnantaaunty ga mamana.Zainab ta

rikice ta tsorata, cikinrawar murya tace aunty ina wuni?Ta

wani daka mata tsawa dalla canyi mun shiru

munafuka.Aliyu yayi saurin karbar wayan yasaa kunnansa,

ba tare da yayi maganaba.Mansura taci gaba

munufaka……

[9:16PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**4 &  3**5

 

Aliyu yayi saurin karban wayar yasaa kunnensa, ba tare da

yayi maganaba.Mansura taci gaba, munafuka,annamimiya,

ki dawomin da dana,ko shima za ayi min iko dashi ne?Ki

karba kun hada munafuncinku kinauri Aliyu dama ashe duk

abundamukeyi idonki yana kaikina sha’awar Aliyu, to kin

aureshimatsiyaciya, kuma ki sani kedasamun kwanciyar

hankali har abadaa gidan Aliyu.Shiya katseta da cewar, to

naji nakuma gode, ba zainab kika zaga bani kika zaga,

tunda iyayenmu daya.Kuma ki sani, wannan shine na

farkokuma na karshe, du sanda kika sakeyin kwatankwacin

haka, sai kin rainakanki, tace to naji amma a kawomindana,

don ba ita ta haifa min shi ba.Rawar kan da kake yi da

zirgillo kadaasa ma da yanzu saiku jira ta haifatukunna.”ya

wani daka mata tsawa acikinwayar, daya sa tayi saurin

kashewayar, ba shiri.Ya kira direba yace, ya kai

Ahmadislamiya, ya biya ta gidansa yadaukar masa

jakarsa.Zainab da tunda Aliyu ya karbawayar a hannunta ta

shige daki.Ya bita dakin, tana zaune a bakingado tayi

tagumi, ya janye taguminyace, meye haka, bana gaya miki

kidaina babu kyau ba?Tace, to yaya nadaina.”ya riko

hannunta, meye zeeyta fushikike yi? Gaya min menene, me

akayimiki?Tayi murmushi bakomai yaya bafushi nakeyi

ba.Taso muje na baki tsarabarki, ya rikohannunta har

dakinsa ya jawojakunkunan daya zo dasu, ya zugejakar ya

ringa fito da kananan kayamatsatsu yana buda mata, tana

ganiyana yaba kayan, har kala 20 yace,kinga irin kayanan

su zaki ringasamin dagani saike. Tace yaya yazansa

wadanan kayan kanana nefa.Toni ba mijinki bane? Na fita

dagasahun yaya na koma mijinki, kikwasa kije ki saka daya

ajikinkiyanzu, kizo muyi hira yau ba indazanje, jeki canja

kayan. Tace yaya…Ya daka mata tsawa, bana

songardama. Da gudu ta kwashi kayantayi waje.Ta tsaya

gaban madubita, ta sakawata damammiyar riga iya

cinya,tana da hannun breziya, adon les nea gaban kirjin

rigar, rigar ta lafeajikinta, tayi mata kyau, ta juya tasake

juyawa agaban madubi tayitsaki, ya ya za’ayi na saka

wannanrigar na tsaya a gaban yaya?Karar wayarsa ce ta

katse masatunani wai ta sameshi a sama.Ta dauko after

dress ta daura akankayan, ta yane janta da siririnmayafin ta

karawa jikinta humra tafice ta haura sama.Ta shiga falon

baya ciki, ta budefilin shakatawarsu, yana gurin kuwakan

katifar ruwa, gabanta ya fadiyanda ta ganshi daga shi sai

shimifara kal da ita, ta dame masa jiki dagajeren wando iya

cinyarsa, tatsorata da yanda da yanda ta ganshidon ita bata

taba ganin babba haka,saidai yaro kamar su Amadi.Ya

mika mata hannun yauwa zeeytazoki bani labarin abunda

ya faru daina bayelsa.Ta marairaice fuska kamar mai

shirinyin kuka, ya tashi ya tako a hankaliyazo har inda take,

ya cire after dressdin ya ga yanda rigar tayi mata

kyaukamar ‘yar budurwar baturiya, yashafa kanta, ta saki

kuka mara sauti,ya rinka rarrashinta yana bubbugabayanta,

na rarrashi.Haba zeeyta nine fa mazajenki, ninefa mazan

jiyanki, duk kin mantaalkawrinka da kika yi min.Kinki sakin

jiki dani, ko hira bakyasonyi dani. Zeeyta mena miki

bakyasona?Ta daga kanta, yaya ina sonka manakunyarka

da nauyinka nake ji, yayakaine fa yayana dana

daukekatamkar uwar data haifeni.” nasan dahaka zeeyta,

shiyasa nake tattalinkinaga bazan iya bawa wani ke ba.Don

kada ya cutar min dake, ki sakijikinki zeeyta bazan cutar

dake ba,kuma ni ba wani abu zanyi miki ba,ko wani abu zai

shiga tsakanina dakesainan da shekara uku, sannan

kinshekara 20 nasan kin danyi kwari,yanzu kuwa

makaranta zan mayardake.Tayi dariya tace yauwa yaya

nagode,kullum makarantar itace araina.Nasani zeeyta na

dade da saninburinki.” ya zaunar da ita a cinyarsayana

shakan ni’imtaccen kamshinjikinta, yana bata tufa

abaki.Zainab ta saki jiki da yayanta,saboda abunda take

gudu yace,bazai kusanceta ba sai nan dashekara uku

sannab tayi kwari, lallaiyayanta mai kaunarta ne

datausayinta.Yanzu ta riga ta saki jiki dashi sosai,ya riga ya

koyar da ita salonsoyayyarshi mai tsaya ma ta araibasu da

abun sawa sai kananan kaya,to daga ita saishi, ba wani

wandayake shigo musu har bata so taji zaifita, don bata so

taji zaiyi nesa daita, ko yaushe tana makale ajikinsatana

zuba masa shagwaba, shikumadu ya wani sukurkurce

akanta, donshi yana tunani anya zai cika wnnanalkawari

daya dauka nan da shekarauku? Yarinyar tana birkita

masakwanya, da lallausan jikinta dashamararren

kamshinta.Du sanda suka kwanta gaba dayakarfin hali

yake yi.Sai ya manneta gam yake samunsauki, to yau gashi

kwanansa uku dadawowa, da kafin ya tafi ya matakwana

hudu, yanzu ya cika kwanauku in an hada kwana bakwai

kenan,a bisa ka’ida yauce ranar da zai komagidan

uwargida. Du ya damu ya rasaya zayyi da zeey dinshi,

shidaigaskiya ba zai iya barinta a gidan itakadai ba.Yayi

nisa cikin tunani, yayinta yajikamshinta, ya dago kai

yanakallonta, tana sanye da dogonwando na jeans da farar

bes ta tsukeda bel, ta lumshe idanuwan nannata,…

 

TA lumshe idanuwan nan nata, mekamar jin barci, ya miko

mata hannutazo ta shige jikinsa ta kwantaacinyarsa,

lallausar fatarta dakamshin jikinta shi yake karadimautar

dashi, ya kara hura wutarkaunarta, da sha’awarta a ransa.

Yashafa lafiyayen bakin gashinta metsawo da sheki da

yake ta kamshi medadi.Mansura ce tayo waya, zainab

zatatashi ya kara matseta a jikinsa, yaamsa wayar, hello,

tace Aliyu najikashiru ko harda nawa kwanakin zakahada

mata? Gashi har biyar tayi,kasan na shiga aiki ita kuma ta

fita.”yace, ai ina sane, yanzu, zan taho, yakashe

wayar.Yace, zainab talatu zata zo taci gabada zama dake,

kin gani yau a gidanauntynki zan kwana.Ta makale kafada,

um-um ni bazankwanta ni kadai ba ka kaini gida.Ya dafe

kanshi yana jin rigimar zeeydin tashi, yace zeey rigimarki

yawane da ita, ina kika taba jin aurehaka? Ta zumburo baki,

to yaya nikadai zan kwana adakin. ya sumbacikuncinnta, ya

lallabata, taso mujemuyi ball.Tana sanye da karamar riga

singileti,da gajeren wando iya cinya, suka fitaharabar gidan

suna ball, sunatakokawa ya hanata bugawa, data zozata

buga, sai ya gara ball din dakafarsa, tayi wani wajen, ta bita

dagudu, ya kuma sa kafa ya janye balldin ta rikeshi tana

tsalle tanayunkurin gara ball din.Motar mansura ce ta shigo

gidan,tana ganinsu ranta yayi mummunanbaci, tace dama

wannan dan raininhankalin wannan yarinyar yake kwa-kwar

so? Shiyasa ni kullum yakedaure min fuska, ko hirar

arzikibama zama muyi dashi?Yanzu kuwa dubi irin shigar

da sukayi, suke ta wasa cikin nishadi. Tuni tasaki kan motar

tayi kansu a guje.Zainab bata kula da motar datashigo ba

saboda ball din ta daukemata hankali, tabi ball din da

dangudunta, tana so ta kamota indaAliyu ya sake

garawa.Aliyu yayi wani tsalle don ya daukezainab, ganin

mansura tayi kanta damota. Amma ina kafin ya karasoharta

bugeta da motar.Ya kwalla kara, tare da kiran

zainab.Zainab ta fada kan gaban motar tagangaro ta fadi

kasa. Aliyu yadurkusa gabanta ya dagota, yarugumeta a

jikinsa, ransa yayimasifar baci, ya dago kai yayi wamansura

wani mummunan kallo.Sai ya shimfide zainab gefe

daya,yayi wani irin tashi kamar namijinzaki, yayi kan

mansura.Du yanda taso ta dake ta kasa,domin bata taba

ganin bacin ransakamar haka ba.Tana ganin ya tinkarota,

tayi saurinmurza siterinta tayi baya, tuni ta ficedaga get din

gidan, ya kaiwa bayamotar wata irin dukagun saida ya dan

loba, ya busar dawani hucin zafi abakinsa, ya komabaya ya

dauki zainab tana yi mishikuka, yaya cikina zafi yake yi

min,wayyo yayana cikina zafi.Ransa ya kara baci, baya so

abundazai taba masa yarinyar nan. Ammatazo ta buge

masa ita harta gogemata fatar ciki. Gashi gurin yayi

jini,dole ya dauki tsattsauran matakiakan mansuradon

bazai dauki wulakanci ba. Bazaiiya sa ido a cutar masa da

zainab ba.Ga zainab din tana kara daga mishihankali da

kukanta, wanda yakekamar a ransa.Wayyo yayana cikina

zafi, ya kamararrashinta, yi shiru zeeyta yanzu zankaiki

asibiti, asa miki magani, kinjizainab kiyi hakuriyi shiru.Yaya

karka kaini ayimin allura, banaso yaya da zafi, yace yi shiru

bazanbari ayi miki allura ba.Magani za a sa miki a wajen

yadaina yi miki zafi.Tace, to, ya canja kayansa da

shaddame tsada, yasa ma zainab after dresstare da

hijabinta, ya daukota kamarjaririya, a hankali ya jingineta

kankujerar, wai du dan kada ta famaciwon, ya shiga motar

ya rinka tuki ahankali, har ya isa da ita wanitsaddaden

asibiti na kudi.Wani baturen likita shi yake yi matadiresin

din wajen. Aliyu yana zaunea gefen gadon kan zainab

yanajinyarta, tana ta raki, wayyo yaya kahanashi tabamin,

zafi yaya, kace yadaina yayana zafi.Ransa ya kara baci

tunanin irinhukuncin da zai ma mansura yakeya kama

shafa kanta yanararrashinta, sannu zeeyta kiyi shiru,yanzu

zai gama miki, ki bari yakarasa miki zeeyta, yi shiru kinji,

yihakuri zeeyta sannu, yana shafakanta yana rarrashinta,

har likitan yakarasa yi mata diresin din. Ya daukoallura zaiyi

mata,ta kankame Aliyu tana kuka, yayabana so, kada yayi

min.Ya rinka rarrashinta, yana shafabayanta, likitan yayi

mata alluran takankame Aliyu tana kuka, ya rinkalailaya

mata gun yana hura matakunanta, yana rarrashinta, sannu

ahankali bacci ya dauketa, sannanAliyu yayi ajiyar

zuciya.Ya ciro wayarsa ya bugawaummansa, tana dauka

suna gaisawa,tace ina zainab? Yace umma

munaasibiti.Lafiya meya kaiku asibiti?Wallahi umma

yarinyar nan ce tashigo da mota har gida ta

bugezainab.Umma ta dafe kai tana salati. Tajiciwo daya

wa?Eh, umma ta kwale a ciki, saida likitaya rede fatar

wajen.Zainab tanata kuka saboda zafi,Allah umma saina

dauki tsattsauranmataki akan mansuratace a’a kayi hakuri

ni zan daukimataki da kaina, idan kaine nasanabun baci

zaiyi, kayi hakuri zanyimaganin abun.Yace to shikenan

umma na kyaleta.Umman ta fito ta shiga dakin ummi,ta

zauna take labarta mata abundaya faru.Ummi ta kama

salati, tana cewakinga yarinya da rashin mutunci..

[9:17PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**6 &  3**7

 

UMMI ta kama salati, tana cewa,kinga yarinya da rashin

mutunci,lallai har yanzu bata san Aliyu akanzainab ba,

yarinyar da tun kafin yaaureta baya kaunar bacin ranta ko

yaganta a cikin damuwa, amma shineyanzu zata nemi

nakasta masa ita?Wallahi in bata yi wasa ba indai

dangidanane ya sallameta, ya koretadaga gidan

nasa.Umma tace ai shiyasa nace yayihakuri ya bar

maganar a hannuna,don inna kyaleshi nasan abun bazaizo

da sauki ba.Ummi tace ai gara da kika yi hakabari na

gayawa Alhj naje gidan sumansuran da kaina.Umma tace

to gara kije din, suyiwa’yarsu fada sosai, inba haka ba

watarana zata dauko musu abunda yafikarfinsu.”(nayi

missng wannan page din).Saratu ta shigo tace, a’a ‘yar

uwasaukar yaushe?Ta kara hade rai, tace, yanzu nazolafiya

meye na ganki rai abace? Taceum raina min hankali zasuyi,

nikumanaje gidan na gansu cikin nishadi,har sun manta da

kuncin da sukasakani.Don wani rainin hankali, sunyi

shigarkananan kaya, sunata ball a harabargidan, ni kuwa na

saki motar nayikanta, na bigeta, na fito nayitahowata, shine

yayo min tes waikada yazo ya sameni a gidan, nataho saiya

nemeni.Saratu tace, to saime, don yace kitaho? Allah yasa

kinada gidan zuwaba kwararo zakije ba, indai akanwannan

yarinyar ne, wallahi sai yaraina kansa, saiya zo har inda

kikeyana baki hakuri.Mansura ta kwashe da dariya

Allahyayata? Tace Allah ai mu bana wasabane.**** ****

****A asibiti kuwa gaba daya ‘yangidansu sun hadu harda

sadiya daamarya ni’ima, sai tattaunawa sukeyiakan abunda

ya faru suna cewazasuyiwa mansura rashin mutunci,

suumma suna tausar kan cewa ai sumazasu dau

mataki.Gaba daya suna falon asibitin, suumma da su

mama da ummi dasusadik. Sadiya da ni’ima ne kawai

adakin, sai Aliyu daya ke gefe dayakan darduma, yana

sallar mangariba,zainab ta farka tana cewa washyayana.

Sadiya da ni’ima suka tasosuna yi mata sannu, ta bude ido

takallesu, tace aunty sadiya yayani’ima ina yaya? Suka ce

sallah yakeyi, sannu zainab ya jikin? Tace dasauki aunty

sadiya, sau daya kikataba zuwar min, yaya ni’ima ke

kumabaki taba zuwa ba, sai yau zaki zomin asibiti.Tace ke

Abba ya hanashi ya barni nafito, ko gida fa ban taba zuwa

ba.Sadiya tace ba kunjejje unguwadashi ba.Munje bikin

kanwarshi, na kuma jegidansu sau biyu, mun kuma jegidan

yarshi, fitata fa hudu kwata-kwata.Ya taso ya zo bakin

gadon yacezeeyta kin tashi? Ta shagwabe fuskatace

yayana.Ya dagota zaune ya zauna a bakingadon ya

jinginata da jikinsa, yacesannu zeeyta, ya kike jin ciwon

nakihar yanzu da zafi? Ta girgiza kai yadaina yaya, ba zafi

yanzu.Yace yauwa Alhmdllh, yace sadiyahado min shayi,

ni’ima zubo minfarfesun can.Ta rissina ta miko masa

shayin datafirfita sosai, ya karba ya rinka batashayin a

hankali tana sha, har saidata shanye.Ni’ima ta miko masa

farfesun yakarba ya miko mata, ta kauda kaitare da cewa

na koshi.Yace a’a ban yarda ba, karbi kici,tace don Allah

yaya, wallahi nakoshi.Yace kinfi so nayi miki dura ko,

bazaki karba kici ba, saina dura miki?Tana langabe a

jikinsa, yana bataabaki harta ci dayawa.Cikin sanyita tace,

yaya na koshi.Ya gyda kansa kawai, yasa tisue yagoge

mata bakinta, likita ya shigo yababbata magunguna tasha,

ya fesamata magani akan ciwon na busarda ciwo ne,likitan

ya fita, Aliyu yace zaki yifitsari ko? Kin dade a kwance,

kadaya kullar miki da mara.”ya sako mata kafafuwanta

kasa dagagadon ya mikar da ita tsaye yanarike da ita, suna

tafiya a hankali, yarakata har toilet ta gama abundazatayi,

sai ya daukota kamar watajaririya, ya dire ta a gadon

nata.Ya daga mata gira tare da cewa “reu okey? Tace “yes

sir”yace bari na gaya ma su ummakintashi.Ta daga mashi

kai, ya fita falonasibitin.Ni’ima tace ‘yar uwa kin ware

yanzuba tsoron yaya dajin kunyarshi, kinsaki jiki kunata

soyayyarku.Sadiya tace aini nasan wallahi komaidaren-

dadewa sai yaya ya aurizainab, saboda kaffa-kaffa da yake

yimata, da kulawa kasan kauna ce dasoyayya zalla.Ai

hauka mansura take yi, idan tacehaka zatayi wallahi ba

karamarwahalar da kanta zatayi ba, ta kumazubar wa da

kanta mutunci a idonkowa, ni’ima tace aita ma

zubarmutunci da ake ganinta dashi da,yanzu wa yake

ganinta dashi?Zainab tace, don Allah kuyi hakuri,kada ku

tsaneta, wallahi bana sonabunda zai jawo mana

kiyayyardangin miji.Kishi nefa ai ita tayi da

sauki,shekararsu tara da mijinta, wayataba jinsu, ta riki

yarinya shekaratakwas a hannunta, lokaci dayamijinta ya

aura mata ita, ta zamakishiryata.Ai tyi tawakkali ma, in

wata ce aisaitayi hauka, yanzu ni yanzu ba fatanake yi ba,

yanda nake jin yayaaraina yace zai yo min kishiya,

auntysadiya ai saikun mike kaina daaddu’a, don saina

zare.Gaba daya suka sa dariya, su ummasuka shigo gaba

dayansu, ta rinkagaishesu tana murnar ganinsu, sukuma du

tausayinta suke ji, sunatajajanta mata, tare da addu’ar

Allahya bata sauki.Zainab tace ina hajiya bata zoba?Umma

tace ai hajiya bata sani ba,Alh ne ya hana a gaya mata,…

 

Alh ne ya hana a fada mata dan kada hankalintaya

tashi.Cikin shagwaba tace ummi dake da mama daumma

duk kunki zuwar min. Suka ce kiyi hakurizainab daga ke har

ni’ima du bamu je muku ba.Alh ne ya hanamu zuwa yace

kadamuzo mu daga muku hankali.Tace, nidai don Allah

umma kuzo, umma ta dafata, kada ki damu ‘yata, zamu zo

ai munji dadi damuka ga kinyi kyau dake, munsan kin

kwantar dahankalinki kenan, kinga ai mafi jin dadin

zuwa.Abba da daddyn zainab suka shigo. Abba yacesannu

‘yata ya akayi haka ta faru?Tace wallahi Abba banji

shigowarta ba, da bazantsaya ba Abba, saina gudu

daki.Abba yace “hukumullahi ta’ala, yace kiyi hakurikinji

‘yata kada kice zaki dau fansa ko ki rainatakici gaba da

bata girmanta kamar yanda kikasaba, wata rana sai labari

kinji.Tace to Abba nagode.Kwanan zainab uku a asibiti,

kullum ni’ima dasadiya sai sun zo sun wuni a asibitin, haka

ummada mama da ummi, har hajiya data samu labaridaga

baya.Har yau samarin gidan du anan suke wuni, Aliyukam

dama tarewa yayi, danshi yake jinyarta,komai shi yake

mata.Ya kara wani sangartata da shagwabata.Zainab ta

samu lafiya, ciwon du ya kame yawarke sai dan abunda ba

a rasa ba, Alhmdllh tasamu saukia ranar aka sallamesu

gaba daya, gidanta sukadunguma suka yi mata rakiya, har

gidanta.Gidan fes dashi, ba wani datti ko kura,

dakunankuwa suna manne da daddan kamshinta data

kebadawa.Bayan sallar mangariba, kowa yayi musu

sallamasuka tafi suna me addu’ar Allah ya kara

matasauki.Ta kwanta lamo akan kujera Aliyu ya shigo

dagarakiyar su hajiyaya tabota, ya akayi ne babyna? Ta

lumshe idoyaya bacci nake ji.Yace daure kiyi wanka zaki fi

jin karfin jikinki,taho muje nayi miki.Ta makale kafada, um-

um yaya da kaina zanyi.To taso muje kiyi, saida ya rakata

har toilet, yace,inkin gama kizo dakina mu kwanta.Ta daga

kai sannan shima ya nufi dakinsa yafada toilet. Tana gama

wanka tayi alwala, tayisallar isha’i tare da shafa’i da wutri,

ta tsayagaban madubi goge nan, shafa nan, ta shafejikinta

da manta me sihirtaccen kamshi.Farar hoda kawai ta shafa

a fuskarta, sai manlebe data sakata shafa farar kulaccarta

ta shafa humrarta, tasaka wata riga mara nauyi iya

cinyarta ta doraafter dress da mayafin akanta, ta tafi dakin

yayannata.Yana sanye da rigar baccinshi yana tsaye

yanadaure madaurin rigar kamshinta ne ya fara

mishisallama, ya shaka cikin annashuwa ya lumshe idoyana

mai cike da farin ciki, don shi babu abundayafi sashi

nushadi a duniyar nan irin turare, donhaka ko nawane zai

iya kashewa turare, shiyasadu turarukansa ‘yan dubai ne,

masu tsadar gaske,da dadin kamshi.Don haka yake

mamaki wane irin sihirtaccenturare me ni’imtaccen kamshi

take amfani dashi,tunda dai shi yasan iya kashe kudi yana

kashewaturare, amma sai yaji nata kamshin da

bambanci.Cikin sanyin muryanta tayi sallama, ta shigo

yaamsa mata sallamar yana murmushi, ya dagomata

hannu ta taho, sannu a hankali ta shigejikinsa, kamshin

jikinsu ya gwauraya ya badawani nau’in kamshi mai dadi,

da sanyaya zuciya.Ya cire mata after dress din, yaga

surarta cikinshedaniyar rigar data sa ya kara, a

zuciyarsakuwa hamdala yake yiwa ubangijisa da

yayiwazeey dinshi tattausan jiki da laushi.Ta langabe a

jikinsa tana lumshe ido ya radamata a kunanta baccin ne?

Ta daga kanta, zomuje na baki nama da fresh milk kici

saikikwanta.Tace yaya kasan fa naci abinci tun su

hajiyasuna nan, a koshe nake. Yace kadan zaki ci, banason

ko kaka ki zauna da yunwa ne, kinji zeeyta,ta daga kai

kawai.Tana manne ajikinshi yake bata naman da freshmilk,

saida ya tabbatar da lallai ta koshi, sannanya rabu da ita.Ta

kara wanke bakinta a toilet ta matsa mouthfreshna a bakin

nata.A hankali tana jin dadin tausar tana lumshe ido.Ya

jawo filo ya kwanta ya mannata ajikinshi,yana shafa

bayanta yana wani lallabata kamarwata jaririya, da haka

bacci mai dadi ya daukesu.Ranar littinin da safe Aliyu ya

tura direba gidansumansura yace, ya dauko masa dansa, ya

kaishimakaranta, in an tashi ya kaishi gidansu

wajenumma.Mansura tun tana daukan lamarin abun

wasaabun har ya fara damunta, domin ta shafetsawon sati

biyu a gidansu, amma Aliyu baiwaiwaiyeta ba.Kawarta

lawisa da yayarta saratu sai kudi sukekarba suna zarya

suwa mata wajen malamai dona karkato hankalinsa, ya

nemi ta koma ita kumataja masa aji.Amma lamarin shiru

kamar an shuka dusa.A wannan lokacin ne kuma aka

karawa Aliyugirma tare da wani kereren gida mai suna

aljannarduniya a Abuja. Lokacin da takardar ta samuAliyu

zainab tafi kowa nuna farin cikinta.Ta kankame Aliyu tana

murna, ta cewa yayana”cngrtl yayana na tayaka murna naji

dadi sosai,Allah ya sanya Alkhairi Allah ya kara

daukakaka.Ya shafa kanta Amin zeeyta.Ita tai buga wa ‘yan

uwansu wayacikin murnarta da dokinta, tana gaya

musuankarawa yayanta girma, ‘yan uwansu suna tazuwa

tayasu murna.Haka abokansa wasu na zuwa wasu nayo

masawaya, suna taya shi farin ciki.

[9:17PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**8,  3**9 &  3**10

 

SUNA waya da Abbansa yake gayamasa gobe zaije abuja

fadarshugaban kasa zaiyi godiya ya ganokuma gidan,

amma kwana biyu zaiyiya dawo.Ta taso ta haye cinyarsa

tana shafafuskarsa tace, yayana kaida wa zakutafi?Ya

shafa kanta ni kadai zan tafizeeyta. Tace um nidai gaskiya

banyarda ka tafi kai kadai ba, sabodame? Nidai gaskiya

yaya inka tafi kakadai ‘yan mata zasu zata baka daaure

wata tace tana sonka.Yana dariya, zeeyta wannan fa

kishine, kin iya kishi zainab.Tayi murmushi ta boye

fuskartaajikinshi tace, yaya ba haka bane.Yace to yaya ne?

Tace nifa yayabazan iya barin mijina, ya tafi waniwaje har

ya kwana shi kadai ba nafiso ko ina na kasance tare da

mijina.”yayi dan jim a zuciyarsa yana tunaniirin baiwar

hankali da Allah yayi wazainab shi.Yarinya karama tasan

darajarmijinta, abunda mansura bata iya bakenan, don ita

har Allah-Allah matake kada ya zauna a garin, don itagani

take zamansa kusa da ita takurane don baya barinta ta

sake dayawan fice-ficen unguwa.Yace, zeeyta na tafi dake?

Ta dagakai yaya inaso in bika.To idan na tafi dake wacce

irinkulawa zaki bani?Tace yaya zan ringa yi maka girkime

dadi, yace ita kenan kulawar dazaki bani?To yaya me kake

so inyi makawanda yafi hakan?Yace zeeyta nasan ke me

ilimi ce, kinsan hakkin miji akan matarsa, ni danuwanki ne,

nasan zaki guje minfadawa gararin rayuwa tunda harkina

kishina, kina so ki kasance tareda ni, don ki rika bani

kulawa.Zainab nakai kololuwa wajenkaunarki, sonki yana

neman illatamin zuciyata, zainab ki bani damarda zan nuna

miki cikakkiyar kaunarda nake miki. Tace kamar ya

yakenan yaya?Yace, zainab inaso ki bani hakkina.Cikin

razana da tsoro ta dafe kirjitace “yaya nifa yarinya ce,

kaminalkawari sai nan da shekara uku zakakusanceni,

amma yaya daga yinwannan magana, wata shidda

zakanemi karya alkawarin?Yace, bazan iya barinki har

shekarauku ba zainab, wata shiddan nan maa daddafe nayi

su,ki bani hakkina zeeyta. Ta mike dagajikinsa tana

hawaye, tana ja da baya,tace bazan iya ba yaya.Ya mike a

fusace ya wani daka matatsawa, tayi saurin durkushewa

kasajikinta yana rawa, yace don na gayamiki ina bukatar

hakkina, shine zakice min baza ki iya ba?To kije ki rike

abinki. Ya tashi yanufi dakinsa, ta koma ta zauna sosai,ta

dafe kanta, ya ilahi, ta kama rantainnalillahi wa inna ilahi

raji’un yaya!yaya!! Yaya meyasa yaya zaiyi minhaka?Yaya

ya manta abunda ke tsakaninadashi, shine babban

yayanmu, shi yadauki kulawa ta musamman yakemin, nake

ganinsa tamkar uwata.Yaya fa shine uban rikona, yanzu

yazamo mijina, ta ya ya zan iyawannan al’amari dashi?Ai

da kunya, bazan iyaba.”lawisa tayi sallama dakin da

mansuratake, dakin da yayarta saratu takezawarci, shiru

taji ba a amsa ba,alhali ance mata mansura tana ciki,don

haka lawisa ta danna kai cikindakin.Ta samu mansura tana

zaune tahada uban tagumi. Lawisa ta dafatatace lafiya?

Mansura tayi firgigit tadawo hayyacinta, tace,

lawisaabubuwa ne suka taru suka yi minyawa, tace

abubuwa wane iri?Tace “kina kallo kashe kudin da nakeyi

wai don Aliyu yazo da kansagidannan bikona, amma shiru

balabarinsa, wai ya ma manta danikwata-kwata.To jiyan

nan labari ya sameni, ankarawa Aliyu girma tare

datanfatsetsen gida a Abuja dadankareriyar mota.Lawisa ta

hau salati tace kada famuna zaune anan yarinyar nan

tamallake shi, yazo yana mikiwulakanci daya fi

wannan.Mansura tace, nifa yanzu yarinyarnan bata gabana,

burina kawai nagaAliyu yazo ya maidani, domin niwallahi

nasan halin Aliyu sarai, bakaramin miskili bane.Wannan

yarinyar bata da wayewanda zata iya jan hankalin Aliyu,

waiharta mallakeshi domin gidahumacena karshe.Kuma

tana da sanin da bata so tacuci wani kota danne hakkin

wani,bare nace zata bi malami don cutardani, kota mallaki

Aliyu.Idan har zatayi hakan, to waye zaiyimata, ita ba fita

zai barta ta rinka yiba.Ita ba ya ba, ba kanwa ba, ita bawata

‘yace da ita kanwa ce da itada suke uwa daya uba daya

ba.Ita ba dagin uwarta ne akusa da itaba, bare suyi

mata.Don nasha jinsu idan muna tare,idan kanwar Aliyu,

yayarta ni’imatazo, idan tana ta dokin aurenta,tana gaya

mata ita harta kagu akaita gidan mij, saboda

kawayentasuna bata labarin ana kaza da kaza,saiki ji

zainab din tana mata magiya,da ta daina mata irin

wannanzancen, wai ita wallahi tsoratar da itatakeyi, don ita

cewa tayi, ko karaminyaro ta gani tsirara tsoro yake

bata.Lawisa tace anya kuwa ba aljanineya aureta ba?

Mansura tace Allahyasa shi dinne ma, inga ta karyar

so.Nifa lawisa abunda yafi damuna,rashin kudi, kinsan ni

ba wani abunake sayarwa ba, karyata ta Aliyu ce,bani da

wata takama saita Aliyu, kinsan shi akwai sakin kudi, ga

cima maikyau, wallahi yanzu duna raina cimargidanmu,…

 

Wallah yanzu duna raina cimar gidanmu, shinkafa da miya

dayankan nama biyu, da daddare tuwoda miya, da safe

shayi da biredi dadan dankali.Kya hada da gidan Aliyu da

akewatandar kaji, kwai, farfesu, saina gadama fa nake girki,

na gwammace ahadomin take away a

hadaddenresturant.Gashi Aliyu baya jin kudi ko nawakikace

ya baki bazai rage ba, saidaiya kara miki ma. Shifa abun

duniyabai dameshi ba, burinsa kawai yawadata iyalinsa da

komai.Bare yanzu da aka kara masamukami nasan wasu

ninkakunkudine zasu sake shigo masa.Ga harkar

kasuwancisa, kullum Allahkara buda masa yake, nifa

gaskiya sonake kota karfi kota tsiya na komagidan mijina,

don kinga iyayenafushi suke yi dani.Da zasu yiwa Aliyu

magana wallahida zai maidani, don Aliyu yana damutunci

baya ketare maganar nagaba dashi, indai yasan

maganarbata banza ce.Ki kawo kudi na koma miki

wajenmalam, to ai kinjiki, ina naga wanikudi, du ba kun

karbe ba, kun kaiwabokaye sun cinye a banza ba? Lawisata

kwantar da murya tace mata, “menema fa baya gajiya,

acikinyarirrikanki ki bada wannan karaminyarin gwal dinnan

naki a siyar a jemiki gidan malam da kin koma zakimayar

da mafiyinsa, mansura tacehaba dai, du kudin dana fito

dasu,sun kare ace har na fara fitar dakaddarata.Lawisa

tace to zauna son duniya,kwazama ku biyu zawrawa a

gidan,ai gaki ga yayarki saratu ni kingatafiyata.Ta mike

zata tafi mansura ta riko ta,tsaya lawisa bari na dauko

mikita dauko mata yarinta, bata kiyasinkudinsa zaiyi dubu

tara.Lawisa ta karba tace, zan aiko mikida yanda mukayi

da bokan abundaya bani na kawo mikizan bawa kanwata ta

kawo mikidon kada hajiyarku taga zuwannawa yayi yawa ta

zargi wani abu.Inyaso sai nayo miki waya, nayi mikibayanin

komai, tace to shikenannagode.Lawisa tana fita tasa yarin a

kunantatana cewa, matsiyaciya tare mukataso dake, Allah

ya rufa miki asirinki,kina gidan mijinki kina cin daulararziki,

ni kuwa ina rabe har yanzumiji yaki samuwa tsakanin

kyautarda zakimin basa wuce dari biyar, saikuma kwacen

sutura, yanzu tundaAllah ya kawo hanya mafi sauki aidole

naci ba wani wajen malamin dazanje.Don suma malaman

ci suke yikwanciyarsu. Sai daf da mangaribasannan lawisa

tayiwa mansura waya,take gaya mata yanzunan ta

dawodaga wajen malamin ta tsara matakaryayyaki akan

tace malamin yacezaiyi aiki akansa ya bata hakuri yanemi

ta koma dakinta. Mansura taringa murna tayiwa kawarta

godiya.**********kwana daya kawai da ‘yarhatsaniyarsu

amma zainab ta kasasamun sukuni.Don tuntuni bata son

bacin ranyayanta bare kuma ace akanta yakefushi, du saita

shiga tashin hankali.Bare yanzu da ya sangartar da ita,

yasabar mata da dumin jikinsa, lallaiyayi mata sabo mai

wuyar bari, jiyadai du da agado daya suka kwanaamma da

kyar ta iya bacci, sabodabe jawota jikinsa ya dorata a

kirjinsaba.Amma a jiya akai da kafa ma

sukakwana.Shikuwa Aliyu du abunda yayi mata,yayi mata

ne don ta gane kurenta,domin har yafi shiga damuwa

darashin jin dumin jikinta.To ya riga yakai kololuwa

tasha’awar zeey din domin yarinyarkullum kara cika take yi

da wanifresh.Da safe ma da suka zo yin break bawani

lallbata din nan da yake yi nataci sai takura mata dayayi ta

cinye,kamar yanda yake yi mata sandatake gida.Gashi wuni

gida yaki zama a gidan,yana can wajen iyayensu ya barta

itakadai a gidan.Ita abunda yafi damunta ma kadagobe tayi,

yayi tafiyarsa ya barta.Ta mike daga tunanen data keyi,

tafada toilet ta tsalo wanka dahadadden sabulunta, ta

rinkamitsitsike jikinta da turaruka.Ta gama tsara

kwalliyarta, tasa watairin karamar shimi ta dame

matajikinta, amma fa bata rufe matacibiya ba, tasa wani

dan mini siketiya cinya, ta karawa jikinta turare,tayi kyau

tanata ambaliyar kamshi.Ta jiyo motsinsa a falo, ya gama

cinabinci yau ko nemanta baiyi ba.Ta dafe kanta tana cewa,

yaya yayifushi da ita, da yawa, ta dauki afterdress zata

saka, sai kuma ta fasasawa, saboda shi yafi so ya ganta

ahaka kawai, ya ringa kiranta dabebynshi.Ta gyara gashin

kanta, ta dan sakoda kadan gaba tayi turaren gashi, tahada

ta daureshi a baya da ribom.A hankali ta tako zuwa falon,

yanajiyo kamshinta ya kishingida akankujera, ya lumshe ido

yana shakarkamshinta, tana karasowa ta ganshiya lumshe

ido, a zuciyarta tace, Allahka taimakeni na samu na

gyarakomai.Tana zuwa ta kwanta a cinyarsa, baisan sanda

yasaki ajiyar zuciya ba,don ya gasu jiya kawai da be

jidumin zeey din tashi ba.Ya bude idonsa ya kalleta, sai

kacewata ‘yar tsana, shigar data yi tayimasa kyau sosai,

yasa hannu yanashafar wajen.Ya dagota ya dora a kirjinsa,

yanashakar ni’imtaccen kamshinta, taceyaya don Allah kayi

hakurikaji yaya naga ranka ya baci, yayanakayi hakuri.Ya

taba cikinta, zeeyta baki ci abinciba, kina son zama da

yunwa ko?Cikin shagwaba tace, to yaya bakaikaci abincinka

baka nemeni ba?Ya dagota zo muje na baki abaki,sakwara

ce da miyar agushi, ya rinkabata abaki,….

 

YA rinka bata abaki tana ci ayangace, shikuwa

yangartatabirgeshi take, don haka suka daukilokaci kafin ta

gama cin abincin.Harta gama, cikin shagwaba taceyaya

baka ce fa ka yafe minba.Yace, zeeyta ai bazanso Allah

yakamaki da hakkina ba, na yafe miki,tace yaya

nagode.Allah ya saka maka da alkhairiyayana.Ta

marairaice fuska tace, yaya zuwaabujan fa?Yace a’a

bazanje dake ba, kiyizamanki a gidan nan har na dawo.”ta

kuma marairaita da magiya, donAllah yayana kaje dani.Ya

mike tsaye yana tafiya, yace um-um ba inda zanje

dake.Yayi shigewarsa dakinsa, yayi shirinkwanciya ya haye

gadonsa, yayiaddu’a ya shafe jikinsa, ya rufeidonsa yana so

yayi bacci, don yasaninya tashi sallar asuba bazaiyi

baccinsafe ba.Ta shigo cikin wata shedaniyar rigarbacci,

‘yar karama, me siririn hannushimi daya, komai na jikinta

abayyane yake, ta fada kansa tana yimasa kukan

shagwaba. Ya ilahi!Yarinyar nan so take ta zautar dashida

kaunarta yaushe zai iya fushi dazeey?Ai bazai yiwu ba,

yarinyar ‘yarkarama da ita ta san yadda zatafaranta ran

mijinta, lallai samunmace ta gari shine mafi alkhairi jindadin

duniya.Shi yasan yanzu bazai iya tafiyanwuni guda ba tare

da zeey dinshi ba,bare wajen da zai je ya kwana.Ai dole ne

yaje da ita, don inbatakusa dashima bazai iya bacci ba.Ta

dameshi da kukan shagwabarta,kukan da ba hawaye, ya

bude idonsadaya, yasa hannu daya yana shafakanta daya

kuma yana dan bubbugabayanta alamar rarrashi.Yace

zeeyta kinsan bana son kuka,kiyi shiru ki kyaleni nayi bacci,

kadakisa na makara gobe wajen tafiya.Ta marairaice masa

don Allah yayakayi hakuri ka tafi dani tsoro nakeji,bazan iya

zama a gidan nan ni kadaiba, kaji yayana? Ya daga kai

najizeeyta, zan tafi dake shikenan? Tashiga jikinsa ta

kankameshi sosaitana murna.Ba jimawa bacci ya dauketa,

saimunsharinta take yi a hankali, tanabaccinta cikin

kwanciyar hankali baruwanta, ba abunda ya

dameta.Shikuwa ya kasa baccin, ya rasa inazai cusa zeey

din tashi, ko zaijisa’idar zogin sonta, ya addabeshi

azuciya.Suna yin break suka daga zuwaabuja, tafkeken

gidan da aka bawaAliyu katon gaskene, fadan tsaringidan

bata lokacine, sun gamazagaye gidan Aliyu ya

jawohannunta, ta fada jikinshi sosai sunamasu farin ciki,

tace dashi yaya najidadi na tayaka murna sosai, Allah

yakara daukaka.Amin zeeyta.”yace “zeeyta zaki zauna dani

anangidan? Tace yaya aunty fa? Yaceita zata cigaba da

zamanta a kano,tace “to yaya ai zata ci ga anyi matarashin

adalci.Yace bazata ce ba, tun ina kadunana taba cewa zan

tafi da ita can, tanuna bata so, tafi son zama a kusada

iyayenta da ‘yan uwanta, kingakuwa ai ke bazaki ki zama

dani ananba, tunda ni dan uwanki ne ko? Taceyaya ko aina

ne zan zauna dakai,koda cikin tandun mai ne. Karkadamu

yayana zan zauna dakai.Dakyau zeeyta nagode,**** ******

****daga cewa kwana biyu, shiru balabari, ita kanta lawisa

bata kumazuwa gidan su mansura ba, gashi satibiyu kenan,

ba wata magana dagagidansu Aliyu, gashi Aliyu ya

daukezainab sunyi tafiyarsu sunyi zamansushiru.Ga

iyayenta sun watsar da ita, bawanda yake mata maganar

komawagidan Aliyu, ita yanzu abun tsoroyake bata, tana

gudun kada watarana Aliyu ya aiko mata da

takardarsaki.Lallai data yi muguwar asara, donina zata

samu gwarzon namijikaman Aliyunta? Wai ya zatayine

tadawo da Aliyu gareta?Ita yanzu abunda ya dameta

kusankullum sai sunyi fada da yayartasaratu.Ita fa ta gaji

da zaman gidan nan, sotake kawai ta koma gidan

mijinta.Saratu ce ta shigo ta doka tsaki, tace,wai dan Allah

malama uban waye zaiwanke miki wadancan wanke-

wankeda kika bari guda yana bi?Dubi yanda kikayi kaca-

kaca da daki,kinsha shayi kudaje sai bin kofi dawaje

sukeyi.Mansura tace haba saratu ki rinkatausaya min

halinda nake ciki mana,a gidan mijina tsinke bansan

yandazan kawar dashi a wajen ba, ammayanzu kuta hadani

da shara dawanke-wanke, inayi kinayi minmasifar ban

iyaba.Haba kefa ‘yar uwata ce, yanzubazaki taimakamin na

koma dakinaba?Saratu, tace me zanyi miki, rashinhakurinki,

tunda mijinki yayi niyyaraure ko ba zainab, sai ya aura

mikikilaliyar mata gogaggiya, wacce zataiya fitar dake

lokaci daya, amma donya auri wannan karamar

yarinyar,doluwa, mara wayo, du kinbi kindaga hankalinki

har kina nemankashe musu ‘ya, to kadan ma kikagani,

donma ba aurenki ne, ya mutuba da bakin cikin da zaki

gani, saiyafi haka.To yanzu yaya saratu ya zanyi?Nifa nayi

nadama.Ki kawo kudi naje miki wajen wanishararren

malami, aikinsa kamaryankan wuka.Haba yaya saratu, ni

na gaji da binwasu malamai, kudina du sun kare,na fara

fitar da kaddarata ama dubabu wani ci gaba, nina

gaji.Saratu tace, saiki ta zama, zamangidan ne baki gaji

dashi ba.Tace, to me zan bayar ki siyar? Tace,kayan da ya

baki na fadar kishiyabana ga baki dinki supern kiba, kibayar

asiyar, biyan bukata ai yafidogon buri.Mansura ta bude

akwati ta daukosuper ta mika mata.Saratu tace, to kinga

inada kudidubu koma sha biyar,

[9:18PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**11

Saratu tace, to kinga inada kudi

dubu goma sha biyar, zan sai super

nan taki dasu, tunda ta zama ta

hannu, saina je miki gidan malam da

kudin.

Mansura tace, to shikenan.

Saratu ta fita da super ta kaita dinki,

tana cewa a ranta.

Me shegiyar rowar tsiya, inba da

hakaba bazaka ci komai nata ba.

Tace, na fara jin tausayinki, yanzu

zanje nayi miki taimako daya, don ta

hanyar ne kawai Aliyu zai saurareta,

wannan uban zuciyar.

Daga nan saita wuce ofis din daddyn

zainab, yace lafiya saratu kika zo

nan?

Cikin ladabi tace, wallahi daddy

daman akan abunda mansura tayiwa

zainab ne nazo kara baka hakuri,

wallahi mansura tayi nadama sosai,

don Allah daddy kayi hakuri, kasa

Aliyu ya mayar da ita dakinta.

Daddy yace banganeba, kina nufin

wai mansura bata gidan Aliyu?

Tace wallahi daddy tun sanda tayiwa

zainab abun nan ya korata gida. Har

yanzu tana nan.

Iyayenmu kuma sunce ba ruwansu,

donsu kunyarku suke ji.

Ba zasu tunkareku da maganar ba.

Daddy ya rinka salati yana cewa,

wallahi daga shi har iyayensa basu

san haka ba.

Abu wajen wata uku, ace tana zaune

a gida, Aliyu yayi kuruciya, yace kije

saratu yanzun nan zan nemi Aliyu a

waya, a satin nan mansura zata koma

dakinta.

Saratu ta taso tanata godiya.

Tana zuwa gida ta cewa mansura ai

malamin yace, ta kwantar da

hankalinta, acikin satin nan ALiyu zai

zo da kansa bikonta, tace, yace

amma daya zo kibishi, idan kika ce

zaki tsaya jan aji, to kuwa ajin zai

tsinke miki, ke kika jiyo wannan

kuma ba ruwana.

Mansura tace, um ni abun mafa ya

fara bani tsoro, Allah yasa dai yazo

din.

Can kuma Saratu na fita daddy ya

kira Aliyu, ringin daya tayi Aliyu ya

dauka, da saurinsa ya rissina yana

gaishe shi, saika ce agabanshi yake.

Yace haba Aliyu kai danake ganin

hankalinka, zakayi wannan danyen

aikin? Ka ajiye mace a gidansu

tsawon wata uku, baka waiwaiyeta

ba?

Kuma dagani har yayana bamu sani

ba, ai sai a rinka zarginmu ace don

mun aura maka tamune muka sa ka

wulakanta ‘yar mutane.

Banji dadin abunda kayi ba Aliyu

kwata-kwata. Aliyu yace kayi hakuri

daddy, Allah ya huci zuciyarka.

Yace na hakura Aliyu, amma kazo da

kanka, kaje kayo bikon matarka,

yace to Abba zanzo.

Kazo fa acikin satinnan, bana so a

kuma daukan lokaci.

Yace “to daddy insha Allahu jibi

karshen sati zanzo.

To Allah kaimu.

Sukayi sallama yana yi masa godiya

suka kashe wayar.

Kanta yana kan cinyarsa tana so tayi

bacci, ta bude idonta tace, yaya me

kayiwa daddy, du yanda kuke shiri

dashi yake cewa yau baka kyauta ba?

Yace akan maganar auntynki ne

yake min fada, naje na dawo da ita

gidana.

Yaya wai ina ta tafine?

Gidansu na turata, take ta zama, tace

kai yaya auntyn tawa? Ni wallahi

dana san tana gidansu da tuni naje

da kaina nayo bikonta.

Meyasa yaya kayi mata haka.

To ya zanyi mata zeeyta? Ta

tabamin tauraruwar matana, ai dole

in nuna mata kurenta.

Amma kuma yaya saika barta a

gidansu kowa yasan tana gida?

To zeeyta ai bani da abinda zan

mata daya fi hakan, don in nace

dukanta zanyi bansan wani irin

mugun duka zanyi mata ba.

Kuma in na daketa mutane saisu

manta abunda tayi min, ace na

daketa akan kanwata, yanzu kuwa

kinga ba duka ba zagi, nasan ta

horu.

Tayi dan murmushinta mai kashe

zuciya tace “yaya jibin da wuri zamu

tafi ko?

Yace ina? Keda fita ai sai ranar da

kika zama mace.

Yaya yanzu ni ba mace bace?

Yanzu ke muna mace ce, baki zama

cikakkiyar mace ba tukunna.

Yaya to yaushe zan zamo macen?

Du ranar da kika so zaki zama.

Tayi shiru tana tunani me kalmar

tasa ke nufi, sai kawai ta share

maganar, bata kuma zancen zata

bishin ba.

Sai da safe bayan sun gama break,

yake ce mata, sadik tuntuni sun taho,

suna kan hanya, zai kawo miki talatu

nan zata ci gaba da zama dake,

kwana uku zanyi na dawo.

Ta zumbura baki ta mike tsaye tana

bubbuga kafa, ta tafi wajen labule

zata bude ta fita.

Ya kirata, zeeyta meye haka?

To yaya kai kadai zaka tafi, ni

bazaka tafi dani ba, naga su Abba da

dady ba?

Don Allah yaya ka tafi dani kaji?

Ya girgiza kai, kiyi zamanki a gida,

kwana uku kawai zanyi. Ta juya ta

hada kanta da bango ta kama kuka,

ya taso ya jawota jikinsa, yana

rarrashinta, yi hakuri zeeyta keda

kike ‘yar gatana, ga sadik nan shida

talatu zasu zauna dake, har na dawo,

tunda sadik yana cikin hutu zai

zauna idan nadawo, sai ya tafi, talatu

kuwa anan zata zauna ta ringa

taimaka miki.

Ko bakya son zuwan sadik din? Tace

inaso.

To yi shiru share hawayenki, bazan

dade ba kinji zeeyta.

Ta daga masa kai, to yi dariya.

Tasa dariya, yauwa zeeyta. Dai-dai

lokacin da ake kwankwasa kofa ta

bude da sauri, wadanda take zato su

dinne, ta kankame sadik tana murna,

ta riko hannun talatu tana yi musu

sannu da zuwa.

Lokaci kankani ta cika musu gabansu

da kayan ciye-ciye, sannan ta zauna

suna gaisawa, ta tambayi wannan ta

tambayi wancan.

Sukuma sunata cin abubuwa data

kawo musu, suna gamawa suka mika

suna zaga gidan.

Sadik ya rinka santin gidan, gskya

yaya ka gama hutawa wannn

tanfatsetsen gidan, gashi yaji kayan

kawata gida kaman a turai? Aliyu

yayi murmushi yace Allah sarki sadik,

to idan ka tashi aure irinsa zan gina

maka.

[9:19PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**11, 3**12 &  3**13

 

Saratu tace, to kinga inada kudi dubu goma shabiyar, zan

sai super nan taki dasu, tunda ta zamata hannu, saina je

miki gidan malam da kudin.Mansura tace, to

shikenan.Saratu ta fita da super ta kaita dinki, tana cewa

aranta.Me shegiyar rowar tsiya, inba da hakaba bazakaci

komai nata ba.Tace, na fara jin tausayinki, yanzu zanje nayi

mikitaimako daya, don ta hanyar ne kawai Aliyu

zaisaurareta, wannan uban zuciyar.Daga nan saita wuce

ofis din daddyn zainab, yacelafiya saratu kika zo nan?Cikin

ladabi tace, wallahi daddy daman akanabunda mansura

tayiwa zainab ne nazo karabaka hakuri, wallahi mansura

tayi nadama sosai,don Allah daddy kayi hakuri, kasa Aliyu

ya mayarda ita dakinta.Daddy yace banganeba, kina nufin

wai mansurabata gidan Aliyu?Tace wallahi daddy tun sanda

tayiwa zainab abunnan ya korata gida. Har yanzu tana

nan.Iyayenmu kuma sunce ba ruwansu, donsukunyarku

suke ji.Ba zasu tunkareku da maganar ba.Daddy ya rinka

salati yana cewa, wallahi daga shihar iyayensa basu san

haka ba.Abu wajen wata uku, ace tana zaune a gida,

Aliyuyayi kuruciya, yace kije saratu yanzun nan zannemi

Aliyu a waya, a satin nan mansura zatakoma

dakinta.Saratu ta taso tanata godiya.Tana zuwa gida ta

cewa mansura ai malaminyace, ta kwantar da hankalinta,

acikin satin nanALiyu zai zo da kansa bikonta, tace, yace

ammadaya zo kibishi, idan kika ce zaki tsaya jan aji, tokuwa

ajin zai tsinke miki, ke kika jiyo wannankuma ba

ruwana.Mansura tace, um ni abun mafa ya fara banitsoro,

Allah yasa dai yazo din.Can kuma Saratu na fita daddy ya

kira Aliyu,ringin daya tayi Aliyu ya dauka, da saurinsa

yarissina yana gaishe shi, saika ce agabanshi yake.Yace

haba Aliyu kai danake ganin hankalinka,zakayi wannan

danyen aikin? Ka ajiye mace agidansu tsawon wata uku,

baka waiwaiyeta ba?Kuma dagani har yayana bamu sani

ba, ai sai arinka zarginmu ace don mun aura maka

tamunemuka sa ka wulakanta ‘yar mutane.Banji dadin

abunda kayi ba Aliyu kwata-kwata.Aliyu yace kayi hakuri

daddy, Allah ya hucizuciyarka.Yace na hakura Aliyu, amma

kazo da kanka, kajekayo bikon matarka, yace to Abba

zanzo.Kazo fa acikin satinnan, bana so a kuma

daukanlokaci.Yace “to daddy insha Allahu jibi karshen

satizanzo.To Allah kaimu.Sukayi sallama yana yi masa

godiya suka kashewayar.Kanta yana kan cinyarsa tana so

tayi bacci, tabude idonta tace, yaya me kayiwa daddy,

duyanda kuke shiri dashi yake cewa yau bakakyauta ba?

Yace akan maganar auntynki ne yake min fada,naje na

dawo da ita gidana.Yaya wai ina ta tafine?Gidansu na

turata, take ta zama, tace kai yayaauntyn tawa? Ni wallahi

dana san tana gidansuda tuni naje da kaina nayo

bikonta.Meyasa yaya kayi mata haka.To ya zanyi mata

zeeyta? Ta tabamin tauraruwarmatana, ai dole in nuna mata

kurenta.Amma kuma yaya saika barta a gidansu

kowayasan tana gida?To zeeyta ai bani da abinda zan mata

daya fihakan, don in nace dukanta zanyi bansan waniirin

mugun duka zanyi mata ba.Kuma in na daketa mutane

saisu manta abundatayi min, ace na daketa akan kanwata,

yanzukuwa kinga ba duka ba zagi, nasan ta horu.Tayi dan

murmushinta mai kashe zuciya tace”yaya jibin da wuri

zamu tafi ko?Yace ina? Keda fita ai sai ranar da kika

zamamace.Yaya yanzu ni ba mace bace?Yanzu ke muna

mace ce, baki zama cikakkiyarmace ba tukunna.Yaya to

yaushe zan zamo macen?Du ranar da kika so zaki

zama.Tayi shiru tana tunani me kalmar tasa ke nufi,

saikawai ta share maganar, bata kuma zancen zatabishin

ba.Sai da safe bayan sun gama break, yake ce mata,sadik

tuntuni sun taho, suna kan hanya, zai kawomiki talatu nan

zata ci gaba da zama dake,kwana uku zanyi na dawo.Ta

zumbura baki ta mike tsaye tana bubbugakafa, ta tafi wajen

labule zata bude ta fita.Ya kirata, zeeyta meye haka?To

yaya kai kadai zaka tafi, ni bazaka tafi daniba, naga su

Abba da dady ba?Don Allah yaya ka tafi dani kaji?Ya girgiza

kai, kiyi zamanki a gida, kwana ukukawai zanyi. Ta juya ta

hada kanta da bango takama kuka, ya taso ya jawota

jikinsa, yanararrashinta, yi hakuri zeeyta keda kike

‘yargatana, ga sadik nan shida talatu zasu zaunadake, har

na dawo, tunda sadik yana cikin hutuzai zauna idan

nadawo, sai ya tafi, talatu kuwaanan zata zauna ta ringa

taimaka miki.Ko bakya son zuwan sadik din? Tace

inaso.To yi shiru share hawayenki, bazan dade ba

kinjizeeyta.Ta daga masa kai, to yi dariya.Tasa dariya,

yauwa zeeyta. Dai-dai lokacin daake kwankwasa kofa ta

bude da sauri, wadandatake zato su dinne, ta kankame

sadik tana murna,ta riko hannun talatu tana yi musu sannu

dazuwa.Lokaci kankani ta cika musu gabansu da

kayanciye-ciye, sannan ta zauna suna gaisawa, tatambayi

wannan ta tambayi wancan.Sukuma sunata cin abubuwa

data kawo musu,suna gamawa suka mika suna zaga

gidan.Sadik ya rinka santin gidan, gskya yaya ka

gamahutawa wannn tanfatsetsen gidan, gashi yajikayan

kawata gida kaman a turai? Aliyu yayimurmushi yace Allah

sarki sadik, to idan ka tashiaure irinsa zan gina maka.

 

Sadik yayi dariya yace, yaya nan dashekara sha biyar fa.”au

kace saika kusa zama tuzuru,sannan zakayi auren?Dai-dai

lokacin da suka shigo boyskwatas yace to ga inda zaka

zauna.Aliyu ya gama shirinsa, zainab taratayo jakarsa ta

taho zata yi masarakiya, har zuwa wajen mota.Ya shiga

motar ya zauna, ta sakomasa jakar idonta yayi rau-rau

tanakokarin zubo da hawayen nata.Ya jawota kan cinyarsa,

haba zeeytabazaki yi min addu’a ba, sai kuka,kina so ki

daga min hankalina, nakasa tukin? Tace yi hakuri

yaya,Allah ya kiyaye hanya ya dawo dakailafiya.Yace

yauwa zeeytah, maza tafi gidadon bazan iya tafiya na barki

aharabar gidan nan ke kadai ba.Ta juya tana dan gudunta

da tsalle-tsallenta, tana dariya tana daga masahannu,

alamar bye-bye, ya dauko yawayarsa ya ringa daukarta a

bidiyo,tana ganin yana daukarta, tasadariya ta juya tayi

cikin gida tanacewa yaya saika dawo.Yayi dariya ya kashe

wayar yasata aaljihu.Yaja motar ya tafi.A hanya ya tsaya

yayi musu uwartsaraba. Yana isa gida, ya samu suAbba da

daddy dasu mama, sunatahiransu cikin nishadi.Yayi

sallama cikin falon, suka amsamama da ummi suna ga

Aliyu gaAliyu.Ya rissina ya gaishesu, daddy yaceAliyu jeka,

ka nutsu ka dan huta inanijima kaje ka dawo da matarka.To

daddy nagode, ya mike ya fitayasa me gadinsu dame wanki

sukashishigar da kayan.Ya shiga motarsa yaja sai gidansu

dazeey.Yana shiga gidan, wannan dadadankamshi yana

nan, ya rasa wannansirrin kamshi na zeey dinshi.Ya fada

toilet yayi wanka yayi sallah,yana fitowa ya tarar hamzaya

kawo masa abinci daga gida.Yaci ya kwanta a gado don ya

danhuta, yana so yayi bacci, amma sai yakasa rintsawa

tunanin yaji zeeydinshi a manne a kirjinsa yadameshi.Ya

jawo wayarsa ya buga mata,ringin daya ta dauka, hello

yayanakaje lafiya?Nazo lafiya, gashi har naci abinci,nayi

wanka, nayi sallah na kwantawai don na dan huta, tunaninki

yahanani bacci.Cikin shgwaba tace, um ba kainekayi

tafiyarka ka barni ba?Yaya ka jawo min sai nayi awasaba’in

da biyu ban ganka ba, yacezeeyta ke rashin ganina ne

kawai, nikuwa rashin jin dumin jikinki yafikomai daga min

hankali.Zeeyta wai yaushe zaki bani dama nakusanceki?

Tace yaya me kake so nayi maka, mekake so na baka

yayana? Komai kakeso yaya zanyi mka.Matsayinka da

darajarka a wajenakafi karfin komai yayana.Yace zeeyta

ina matukar so ki banihakkina na jikinki, amma fa sai

kinara’ayi, don wallahi in zamu shekaragoma a haka bazan

taba takura mikiba, ko nayi miki dole.Kuma kada kiyi

tunanin kina dahakki a wajen ubangiji, a’a tsananinkaunar

danake yi miki bazata bari nakullace ki ba.Kona yi fushi

dake ba, na yafe mikizeeyta.Kayi hakuri yayana, na amince

maka,na baka dama du sanda kaso kayira’ayi yayana, ka

karbi hakkinka,yace dagaske zeeyta? Kada kisa nayitsuntsu

na taho yanzu.Tace a’a yayana kada ka dawo yanzu,ka

zauna ka kula da auntyna ka batahakkinta, ka rarrasheta, ka

batahakuri kan abunda kayi mata.Ina jiranka yayana nanda

kwanauku, kamar yanda kace, Allah yadawo min da kai

lafiya. Ka kulaminda auntyna ka bata hakuri, kararrasheta

ka lallbata harta huce, kashafamin kan Amadina. Kayi

hakuriyaya, don Allah kada ka damu, zankashe kada na

cinyewa auntynalokaci, don nasan yau sabon amarezaku

zama, kayi mata kalamai masusanyi da tausasa zuciya, ka

nunamata tattalin so yayana saida safe.Dif ta kashe wayar,

ya rinka juyawayar a hannunsa yana murmushi,yarinya

karama ta iya kalamai maisanyaya zuciya.Ya kunna bidiyo

wayar ya rinkakallonta sanda tayi masa rakiya, dangudun

data keyi tanata tsalle-tsallenta, tana dariya, du dai dontasa

shi nishadi ta kuwa shashi, donkifa wayar yayi a fuskarsa,

yana jinzuciyarsa wasai, cike da nishadi bacciya rinka

fusgarshi ya kashe wayar yakwanta.**** ***** ***mansura

taga shiru har mangaribaba Aliyu, tace yaya saratu anya

kuwaAliyu zai zo, kinji shiru har yanzu?Saratu tace ke

kinfiya wutar ciki, dukudin da kike kashewa wanne

kikasamu nasara kamar wannan?Kina gani kanin babanshi

yazo yaitabawa Alh hakuri, yana cewa basu sanhakaba.To

ko Aliyu baizoba idan daddynzainab ya sake zuwa basai ki

komadakinki ba, inya ji ya dawo dake aidole yazo inda

kike.Bayan sunyi sallar isha’i suna cinabinci, hajiya ta shigo

take gayamata, taje falon baki inji babanta.Mansura ta tashi

da saurinta tawanke hannunta, ta yafa mayafinta,ta nufi

falon babanta.Wani mayataccen kamshine taji yadaki

hanncinta, a hankali tayisallama, ta zauna ta cewa

babantagani. Ya mike tsaye yace, game songaninki nan sai

a sannan ta dagakanta ta ga bakon da yake zaune.Aliyunta

ne cikin shiga na alfarma,ya kara murjewa da kyau, ya

karahaske da kwarjini, fatarsa har wanidaukan ido yake

yi.Yana ta zuba kamshi mai dadi,idonsa yana sanye da

farin glass.Du saita raina kanta taga ta muzantaa gabanshi,

me Aliyu yake ci dayakara wannan kyan, da kwarjini?Lallai

Aliyunta ya kara samun canjinrayuwa, ma’ana kudi sun

sake zamamishi.A hankali tace masa ina wuni?

.

 

A hankali tace masa ina wuni?Ya dago kai ya kalleta, du tayi

baki ta rame, takusan fita daga hayyacinta.Yace lafiya lau

ya zaman jin dadi? Tayi shiru,yace so ya kika gani, zaki

tafine yanzu ko bakigama hutawa ba?Tace zan tafi, yace to

sai kiyi sauri ina jiranki amota, ya bata dubu dari yace, ta

bawa hajiya daAlh su sai goro.Alh ya mata fada, ta durkusa

a gabansu tayimusu sallama, ta tafi, ganin mota ta

bawamansura mamaki, tasan tabbas motar manya ce,a

ranta, tace daula tazo, tana neman tayiwakanta.Tukinsa

kawai yake yi baice mata komai ba,itama bata ce masa

komaiba, sai satar kallonsadata keyi, suna isa gidan tayi

mamakin yanda taganshi gyare, ya zube mata ledoji a

gabanta, yawuce dakinsa, wanka ya sakeyi yasa kayan

bacciya fita falo, ya tarar itama tayi wanka, tasakayan

baccinta, yace baki bude ledojin bane?Tace a’a na bude kai

nake jira.Ya zauna ta dauko plate ta juye gasassun kaji,

tazuzzuba musu fresh milk a kofuna.Sunaci har ya koshi.Ta

nufi toilet yin brush shikuma ya nufi dakinsa,yayi brush ya

rinka feshe dakin da turaruka kusankala biyar amma sai

yaji baiyi masa irin kamshindakunan zainab ba, yana

kwance yana karantaaddu’o’in tsarin jiki, yana shafawa ta

shigo dasallamarta ta rufe kofar ta jingina a jiki, ya

mikamata hannu ta tashi ta miko masa nata hannun,ya

jawota ta fado jikinshi,yayi saurin cikata ya dagota yana

tambayarta,mansura meya sameki naji kin rame, rashin

lafiyakika yi?Ta girgiza kai saita fashe da kuka, ya kwantar

daita a jikinsa yana dan bubbuga bayanta, yi shiruya isa

haka, kinsan bana son yawan kuka,fadamin meye?Ta kama

fada masa irin wahalan data sha nashara da wanke-

wanke.Aliyu yace “O sorry mansura, na godewa suhajiya da

suka tayani horonki, kinga gobe idankika sake kwatan-kwan

abunda kika yi, idan nayimiki horon da yafi wannan, suma

wanda zasu yimiki sai ya fi wannan da suka yi miki.Tace

Aliyu ai bazan kuma ba, na gane kurena,yace a to dakin

samawa kanki lafiya.Don kinsan halina bana daukar raini,

bare kumayanzu da girma ya sake hawa kaina.****

*****bayan tafiyan Aliyu sadik ya shigo suna hira

dakanwarsa, tanata tambayanshi daddy da faruk,yace mata

du lafiyarsu lau.Yace gashima abunda daddy yace na kawo

miki,ya bata jakar hadadden tsumi da jakarhadaddiyar

zuma ta mata, harda su cukudi,gumbar matam haddaden

dakar gari na karinni’ima.Hadadden kayan karin ni’ima dai

mai kyau nasakkwato, don da kanshi daddynta yaje har

canya hado mata su, don yana ganin tunda ta rasauwa

bame gyarata tanan bangaren, shiyasa yakeiya bakin

kokarinsa yana so ya maye matamaraicin rashin uwa.Tace

Allah sarki daddyna me sona.Sadik yace wai magangunan

meye wannan ne?Tace, kaidai ina ruwanka? Cikin farin ciki

danishadi sukaita hira da yayanta sadik, sai da yajiya fara

hamma sannan yayi musu sallama ita datalatu.Zainab ma

tayiwa talatu sallama ta fada dakintadon ta kwanta, sai taji

kwanciyar ta gagareta saijuyi take a gado.Taita faman tsaki

du dundumiyar katifar dake kangadon, da lallausar bargo da

zanin gadon da yakekai, sai take ji kamar akan kaya take,

saboda yauba kirjin gwarzon mijinta.Data ga ta kasa baccin

saita mike ta shiga toiletta dauro alwala tai ta nafula tana

musu addu’a.Tana kwanciya taji karar wayarta, tayi

saurindauka tace yayana, cikin sanyita yace zeeyta,meyasa

bakiyi bacci ba, har yanzu sha biyu darabi?Ta danyi

karamin tsaki tace Allah yaya ban sandalili ba, tun dazu na

kasa bacci.Sai yaji dadi a ransa, yasan lallai zeey dinshi

tadamu dashi, kiyi bacci bana so ki samu matsalarciwon

kai. Tace to yaya zanyi, ina auntynagatanan tana bacci

kona tasheta na bata wayarku gaisa?A’a yaya kyaleta tayi

baccinta ta huta. To kemakiyi baccin kada kizo kina ciwon

kai.To yaya saida safe.Tun a ranar bayan tafiyan yayantata

hada kwastan da madara da kwanduwar kwaida manja ta

dama, ta shafe jikinta gaba dayata jika jar dilka da ruwan

dumi ta rinka mitsesikejikinta iya karfinta.Har kwana uku a

ran na ukun ne da safe ta hadalallenta da ma’ul kal da lalle

da tacecciya humra,lipton, kar-kar, mahalbiya, turaren S.S

mai maiko,garin sanda madaran turare, ta hada tayi

kwabinlallen sannan ta dura a kwararon yin kunshi.Ta

zauna ta zana sitayel a kafarta da biro tabawa talatu lallen

tayi mata kunshin, ta kuma yimata zanen fulawa hannu da

kafa.Tayi mata a saman ‘yan yatsun hannunta.Daddy yayo

waya da safe yace sadik ya taho gidazasu je gaisuwa dashi

da sauran ‘yan gidankanwar kakarsu ce ta wajen uwa ta

rasu donhaka ya tafi bai jira zuwan yayan ba.Sha biyu

zainab ta wanke kunshindu inda tayi talatu na binta da

kallo.Aliyu ya yo mata waya, yace sun taho tuni tamike ta

shiga kicin.Talatu ta bita ta sata yanka wannan

gogawancan. Jajjaga wancan shikenan abubuwandata ke

sata amma dai-dai da juya miya batayarda tayi mata ba,

tace girkin yayanta bata soasa mata hannu talatu tana

tsaye tana kallontamasa jalof din makaroni dasu dankali,

da pepechiken, tayi miyar nikaken kaza da koren wake.

[9:20PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**14,  3**15 &  3**16

 

Tayi masa miyar nikakkiyar kaza, ta dafa masahinkafa da

zaici dashi, tayi masa hadin kos nakabeji, tayi masa lemon

kwa-kwa da madara, tayimasa lemon abarba, du tasaka a

firij yayi sanyi.Tasa talatu ta fito mata da wasu hadaddun

fulassabbi kar a sito, aka wankesu kal, komai tazuzzuba

taje ta jeresu a tebir yasha ado dafulawoyi masu kamshi,

tace talatu ta gyara makicin din, ita kuma ta sake sharo

dakunanta danaAliyu, ta sake goge ko ina yayi tas tasa

turarenwuta nan da nan gidan ya canja, ta bawa

talatuabincinta dana mai gadi, tace ta mika masa.Zainab ta

fita ta kulle ko ina ta fada toilet, tashiga wanka, tana fitowa

tayi alwala ta tayar dasallar la’asar.Goge nan, goge can, sai

uban kamshi data kezubawa.Ta bude kwabarta ta zubawa

suturunta ido, tadauko wani les a ciki na lefenta da yake

bata tabasashi ba.Riga da zani ne, ta daura dankwali daya

kara fitomata da kyaunta, tasa fashion yari da sarka,

daabun hannu du kalar kayan nata.Yayo mata waya, ya

karaso cikin murna dazumudi take yiwa Allah godiya.Suna

kashe wayar taji bude get.Tana jin tsayuwar ta bude kofar a

hankali tarinka wani irin taku kamar hawainya.Ta cikin

gilashin motar ya ringa hangota.Yarinyar ta rikide masa,

kamar aljana, anya kuwazeey dinshi ce? Kamshinta daya

jiyo shiyatabbatar masa da zey dinshi ce tafe gareshi.Yana

zaune cikin motar ya kafa mata ido ya kasahasala komai.Ta

rinka yi masa dariyarta mai ban sha’awa takama murfin

motar ta bude, ta zura jikinta cikinmotar ta zauna a

cinyarshi, ta kwantar da kantaa kirjinshi.Yasa hannu biyu ya

tura kansa cikin jikinta yanashakar ni’imtaccen

kamshinta.Tace yaya nagodewa Allah daya dawo

dakailafiya.Yace zeeyta hakika Allah shine abin godiya,

dayasake canja minke, zeeyta Allah ya bani kyakyawardiya

mace me kama da ke sak.Ta boye fuskarta a jikinshi, tace

yayana zaka sanijin kunya.Yace haba zeeyta ai kunya ta

kare, ko kin mantakalaman da kika gaya min ta waya?Ta

kara cusa kanta cikin kirjinshi.Daukota yayi cak yayi falonsu

da ita, yasa kafaya tura kofar falon nasu.Ta mike daga

jikinsa tana murmushi, ta ballemasa madaurin takalmansa,

ta cire masa, tazame masa safar kafarsa, ta cire masa kwat

dinjikinshi, ta jawo hannunsa zuwa dakinsa.Ta shiga toilet

ta hada masa ruwan wanka,yanata kamshin turaren wanka,

ta ajiye masahadin sabulunta data ke amfani dashi.Ya

shiga wanka kafin ya fita ta ninke kayan dayacire, ta

adanasu a ma’ajiyarsu. Ta fito masa danashan iska du ta

feshe su da turare ta fita dagadakin.Ya gama shirinsa ya

fito falon, ta tashi ta taryoshi, tayi masa rakiya har kan

tebir.Tsarin data yiwa wajen ma ba karamin birgeshitayi

ba.Ta zauna tana zuba mishi abinci, kallonta kawaiyake yi

yana kallon tsarin ado da kwalliya.Ta rinka tura mishi

gabanshi, tace yaya kacimana? Yace zeeyta ki karasa

ladanki ki baniabaki mana.Tayi murmushi bazan iyaba

yayakunya nakeji, ya kashe mata ido daya, yace inamijinki

kike kunyan bani abinci abaki?To ni zona baki. Ta

marairaice don Allah yayakaci, ni ta taka nake kaida ka

dawo daga tafiya.Ya dauki cokalin ya fara ci, yana cin

abincin yanagyada kai, yana santi yaci abincin nan da

yawa,komai saida yaci, saida ya gama ya jawotacinyarsa,

ya rinka bata abaki tana ci.Yaya don Allah ka kyaleni haka

na koshi, ya shafacikin nata, kullum cikin ki a dame saboda

bakyason cin abinci ko dagowa ba ya yi, ko saimunsamu

baby ne zai taso?Ta mike da gudu tayi dakinta, ya bita da

kallonsha’awa yayi murmushi.Sai da ya shigo daga

masallaci, bayan sallarisha’i sannan suka gaisa da talatu da

yarangidansayana shiga falon yaga bai ganta ba, a

cikindakinta ya sameta, ta kanannade a gado hardarufa da

bargo, ya dafa kanta lafiya zeeyta meyafaru kika kwanta?

Tace yaya bacci zanyi, yace yanzu zeeyta zakiiya bacci ba

tare da kin jini a jikinki ba?Tayi shiru bata ce masa komai

ba, don yau atsorace take dashi, tunda taga alamunsa,

yakamo hannunta taso muje muyi nafila.Ta biyoshi zuwa

toilet, sunyi nafila raka’a biyu,ya dafa kanta ya dade yana

musu addu’a, sannansuka shafa.Ya wani kunshin gashin

hanta da koda ya rinkabata tare da fresh milk me sanyi, du

ta marairaicemasa, tace ta koshi, bazata iyaci ba. Lallabata

yarinka yi tana ci, yana fito mata da ice cream saitaware ta

karba tana sha katuwar roba saida tashanyeta.Ta mike tayi

dakinta yaya saida safe. Ya bita dakallo kawai, ya tashi ya

rurrufe ko ina ya tofe daaddu’a, yana shiga dakinta wani

kamshi ya dokihancinsa, ya hangota a tsakiyar gado

takanannade. Ya hau tsakiyar gadon ya janyebargon. Tsoro

ya sake kamata.Zeey dinshi ta rikitar masa da zuciya a yau

daibazai iya mata hakuri ba.Lebenta jajir mai taushi, yasa

hannu yana zagayeleben nata da dan yatsan shi daya, tana

jinsasaita juyar da fuskarta dayan gefen ya kwantoakan

bayanta yana shafa fuskarta sai yaji hawayeya mirgino da

ita gabansa yasa harshensa yanalashe hawayen da haka

yayi dabarar.A yanda yake azabtuwa da kaunarta zai

iyahakura da zeey dinshi kuwa?

 

A yanda yake azabtuwa da kaunar zeey anya zaiiya hakura

da ita kuwa?Zainab ita kadai ce macen da ya mace akanta,

yazube tarin kaunar da yake yi mata, tun tanajaririya bazai

iya barin zeey dinshi ba, domin tatafi da zuciyarsa kamar a

mafarkinsa daya sabayi. Ko da yaushe.Yasha shgawabar

zeey tana yi masa kukansangarta, da marairaita, wanda ya

rinka karamasa kaimin abunda yake yi.Ya kara sanyashi

cikin yanayin kaunarta, da wanidumbin farin ciki da

annashuwa, daya tsincikansa, ta rinka yi masa kuka tare da

magiyar yakyaleta, yaya kaine fa yayana, mai sona,

maitausayina, yayana ka daina bani wahala. Yanajinta,

amma ya kasa kyaleta, sai dai yabi da ita ahankali, don

kada tasha wahala sosai amma tawahalar,sanda ya tashi

yayi wanka, yayi alwala, kasa fitamasallaci yayi, yayi

sallarsa a daki, ya dade yanayi musu addu’a, yanata nuna

godiyarsa ga Allahtare da sawa zeey din tashi

albarka.Kujera yaja ya zauna, a gaban gadon ya zubamata

ido yana mai jin tsantsar farin ciki dakaunarta data ke kara

ratsa shi.Yayi murmushi komai na daren jiya yana

tunashi,yana son wannan daren yana sashi nishadi.Ya ware

masa fili guda acikin zuciyarshi bazaitaba manta shi

ba.Yana can tunaninsa na daren jiya yaji motsinta ahankali

yana dubawa yaga ta farka.Du ta marairaice tana son yin

kuka. Ya kamohannunta zeeyta tashi kiyi wanka kiyi sallah,

nabaki break kinga rana tayi.Ta kasa hada ido dashi, don

tana tsananin jinkunyarsa, tace ni ka kyaleni bazan iya tashi

bajikina ciwo yake yi.Taja bargonta ta dada lulluba.Zeeyta,

ya janye bargon, wayyo yaya ni ka kyalenitasa masa

kuka.Oh! Zeeyta sorry auta, yau na taboki ko? Yadagota

yana matsa mata jikinta a hankali, yanawani lallabata ta

langwabe ajikinsa, tana zubarda hawaye, yafi kowa sanin

laifinsa dan yasanshagwabar zeey bata kaunar abunda zai

tabajikin nan nata, ko yaya ciwo yake taita kukakenan.Kiyi

shiru mana zeey.Yayana jikina ciwo yake yi.Kiyi hakuri

zeeyta zaki koma dai-dai, bana sonkukan zai haddasa miki

ciwon kai.Tayi shiru tana langwabe a jikinshi tamkar

tayibacci, ya dauketa yayi toilet da ita, ya hada mataruwa

mai dumi, ya rinka gasa mata jikinta, saidayaga tadan ware

sannan ya ba waje, tayi wankantsarki tayi alwala.Ta lallba

tayi sallah ya fito da break din, ya rinkabata kadan taci ta

kauda kai, ya bata maganitasha, da yake lallabata yake yi

bai kuma matsamata saita kara ba.Ta langwabe masa yaya

bacci zanyi, ya kwantarda ita yana mammatsa mata jikinta,

tanata yimasa raki da shagwaba, da haka bacci

yadauketa.Yayi ajiyar zuciya ya rungumeta suka ci gaba

dabacci, bacci mai dadi ya rinka yi, sai karfe dayaya farka a

hankali ya zare jikinsa daga na zainab,wai gudun kada ta

farka.Yayi wanka ya shirya cikin shadda da akayi

matadinkin boda, yayi kyau sosai aciki yayi aurinficewa, ya

nufi gidan wani abinci don yayi wazeey take away tunda shi

bai iya girki ba bare yagirka mata.Lokacin data farka taga

baya nan, saita mike tashiga toilet ta sake yin wanka, ta

dauro alwalatayi sallah. Ta tsaya gaban madubi ta

tsarakwalliayarta ta saka wani jan material mai kyalliriga da

siket dinkin du sun matseta.Ta saka yari da sarka da abin

hannu, du jajayetayi daurin dan kwali daya kara fito mata

dakyaun fuskarta.Ta kara turare dakunansu da falon da

gidan takunna a.c.Yayi sallama ya shiga tana kishingide

akandoguwar kujera tana kallon tashar zeey arabiya, aciki

ta amsa sallamar, yazo ya zauna kusa da ita,ya ajiye ledojin

hannunsa.Ya kamo hannunta yace “zeeyta abun ma kotarya

babu, ya jikin naki?Ta sunkuyar da kanta kasa tace ni

lafiyatakalau.”yace haba zeeyta kefa kika ce min jikinki na

ciwokinata kiran daddy da Abba.Ta durkusa kasa tana boye

fuskarta, tace kaiyaya don Allah nidai ka bari.To naji na

bari, ai yanzu du abinda bakya so nadaina gimbiyar

zuciyata.To taso kici abinci, yana fitowa dashi, tace

yayameyasa baka tasheni nayi girki ba, ka siyo

abinci.Zeeyta ai yau ranata ce, bazan bari girki yawahalar

min dake ba.Sai kinyi sati kina hutawa daga kwanciya

saibacci, sai sallah, sai cin abinci sai kula dani.Cikin

shagwaba tace a’a nidai yaya zan rinka girkina, bana so ka

rinka fita sanyan abinci, dadarajarka, yayana zan iya maka

komai, don nafaranta maka, ina kwadayin samun ladan

aure.Yace zeeyta ai kin gama samun ladan aure, tundanake

ban tabajin farin ciki da nutsuwa irin na jiyaba.Allah yayi

miki Albarka zainab, Allah ya barmutare har karshen

rayuwarmu.Allah yasa na sama mana baby, ko kuma

inanjima mu samu. Tace um-um nidai yaya baza akuma ba

bana so.Yace kash zeeyta kada ki kuma fadan hakabakyau,

ta kwantar da kanta cikin raunin murya,tace yaya nadaina

bazan kuma ba, ka yafe min.Yasa hannu ya shafa kanta, na

yafe miki zeeyta,kowane irin laifine da wanda na sani da

wandaban sani ba, du na hada na yafe miki kinji zeeyta.Ta

daga kai nagode yayana, bani ice cream dinda kec din naci.

 

ta daga kai na gode yayana, bani ice cream dinda kec din

naci.A’a zeeyta ki fara cin abinci, ga mutuniyarki

kazagashin inji.Ga youghot da fresh milk a frij gasu tufa

kiciabinci kadan du saiki ci abunda kike so.To yaya du

zanci, dan bani ice-cream din na farasha, ya bude mata

yasa dan cokalin yana batatana sha, zeeyta kin farantamin

sosai bazangajiya dasa miki albarka ba.Allah yayi miki

albarka ubangiji ya miki tukuici dagidan Aljanna, kinsamin

nutsuwar da ban tabasamu ba.Zeeyta ki gaya min me kike

so nayi miki? Komekike so ki zanyi miki, gaya min me kike

so.Yaya ni bana bukatar komai, don komai kayi minyaya,

inada komai bani dawani abu dayagagareni.Nidai yaya

karatuna shi nake so naci gaba. Yarinka shafa kanta, kada

ki damu zeeyta karatu kintayi kenan, har sai kince kin gaji

dashi, gobe nanzan sayo miki form ki cike, kwanan nan zaki

farazuwa makaranta.Yauwa yayana nagode.Aliyu da

zainab sun kara shakuwa da mannewajunansu kamar tif da

taya.Da safe ita take shirya musu break dinsu mai raida

lafiya, idan da lokaci suci tare, idan sunmakara ta zuzzuba

masa a fulas ya tafi ofisdashi.Yana ofis bini-bini yayo waya

shidai yaji ya take,yaji muryanta yasan kalau take, kafin

yamma yadawo ta sake shirya musu wata dinar.Ta gyara

gidan ta baje kamshin nata, cikin gidada falon da jikinta

gaba daya ko ina da nau’inkamshin da yake daban ne.Du

da talatu tanayi musu girki da ita da sojojinbiyu da suke

gadin gidan, da yaron gidan maishayar da fulawowi da

share-shareamma du abunda zainab tayi sai zuba

musutabawa talatu ta raba musu, saboda sanin hakkindan

adam.Ta tsara kwalliyarta ta gani ta fada, tayi shigarkece

raini.Ta zauna zaman jiran yayan nata.Da taji karar

motarsa zata fito cikin yauki dayanga ta taroshi ya

makaleta yana mai jin farinciki da ganinta.Yaita yaba

kwalliyar data yi masa.Shiyasa ko kadan baya son yayi

nesa da ita, dusanda sai tafikano weekend da kyar suke

rabuwa,tana kuka yana aikin rarrashi.Dakyar yake iya tafiya

ya barta, amma ko yausheyana manne da waya, suna hira

cikin shaukin soda tsantsar kaunar juna.Tuni ya siyo mata

form ta cike, harta fara zuwamakaranta.Tare suke fita, ya

sauketa a makaranta, intagama laccarta direbanta yazo ya

mayar da itagida.Watanta shida a abuja bata taba lekawa

kano ba,kuma tana son zuwa don dai yaki kaitane,

intayimagana yace karatunta.Zainab ta kara canjawa tayi

wani irin kyau naban mamaki tayi fresh da ita, sai wani

shekitakeyitayi dumi-dumi da ita, jikinta a murje ta

karahaske.Haka Aliyunta da yake yanzu shima da

hadinsabulunta yake wanka, da turarukanta shima

dasuyake amfani, don haka komai nasu iri daya, duinda

akaji kamshinsu ansan sune.Mansura tasan Aliyunta farine,

me kyau yanakuma da son kamshiamma tana mamakinsa

yanzu, yanda ya wanicanja ya kara kyau da haske, fatarsa

take wanitsantsi da shainin wanda ita data ke mace manata

baya tsantsi haka.Tana mamaki yanda yanzu yake dan

sakin fuska,kamar zafin zuciyar tasa ya ragu, amma ita

kumarashin sabo da hakan bata wani sakin jikinta.Bata yi

masa maganar zainab, ko tace masa yatake, shima kuwa

baya yi mata zancenta.Ba kamar zainab dinba da bata da

zance sainaauntynta da Amadinta.Yau litinin yayi sammako

daga kano zuwa abuja,a jirgi yana zuwa ofis ya wuce, don

bashi dalokacin da zai fara biya wa ta gidalokaci ya

kure.Yana tayiwa zeey dinshi waya yana lallbata,tunda yaje

ofis din bai samu zama ba, ayyuka neagabansa, sai shidda

ya samu kansa, ya isa gida.Yana shiga gidan yaji zuciyarsa

ta cika da farinciki, ya dawo zai kasance da zeey

dinshi.Yana tsaida motar ya hangota ta taho tana yaukida

yanga, kamar hawainiya, yarinyar kullumkamar canjata ake

yi, kyanta kara karuwa yake,to ta samu kulawar gwarzon

namiji, ya kasadaurewa ya fito da sauri ya tareta, cak!

Yadauketa, suna farin cikin ganin junansu.Ya shiga falon da

ita, ya zauna akan kujera tanakwance ajikinsa, ta dago kai

tana shafa fuskarshi,tace yayana daganin ka yau kasha

wahala, yace”wallahi fa zeeyta, tunda naje ofis yau ban

hutaba, jikina sai ciwo yake yi.Ta marairaice fuska cikin

tausayawa tace, Oh!Sorry yayana, sannu don Allah ka rinka

hutawa.Ta mike ta cire mishi kwat din jikinshi da fararrigar

ciki ta barshi da bes.Ta cire masa takalmi da safa, du da

e.c datawadata falon da sanyi, saida ta rinka yi masafirfita,

ta dauko masa sanyaya kunun aya dayasha madara da

kwa-kwa da filebo, yayi dadisosai, ta rinka bashi abaki, ta

marairaice fuskaalamar tausayi karara a fuskarta, sai

wanilallabashi take yi, shi kuma du ya wani langwabemata,

ya kwanta mata ajiki, tana dan mammatsamasa jikinsa. Da

kyar ya barta taje ta hada masaruwan wanka, me zafi, ya

sha turaren wanka.Yana shiga ya mimmike a ciki, sannu a

hankaligajiyar ta rinka rabuwa dashi, yaji jikinsa ya

ynrmlYana fitowa ya sameta a tsaye a kofar toilet dinda

karamin tawul a hannunta, ta rinka goge masaruwan

jikinsa, ta zaunar dashi akan abin zama,hadin manta ta

dauko tana shafa masa.

[9:20PM, 05/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 3**17,  3**18 &  4**1

 

Hadin manta ta dauko tana shafa masa a hankali,shikuma

yana wani lumshe ido don ji yake kamartafiyan tsutsa take

yi masa.Ta gama shirya shi cikin kananan kaya, ta

shafamishi turaruka kamshinsu ya gauraye, suna fitarda

kamshi mai dadi.Ta leka fuskarsa tana murmushitace

yayana kayi kyau.Ya jawota jikinshi yana jin wata nutsuwa

da farinciki du sanda ya rungumi zeey dinshi, don hakako

yaushe yake so yajita manne dashi. Du sandayaje kano

abunda yake wahalar dashi kenan.Babu irin wannan

tarairaya daga wajen mansura,babu irin wannan tattalin

son, da daddan kamshi,babu irin girke-girken da zeey dinshi

take shiryamasa.Yace zeeyta Allah yayi miki albarka, zeeyta

mekike so nayi miki yanda kike faranta min nimazanso inta

faranta miki.Gaya min me kike so?Yaya so nake naje gida,

naga iyayenmu da ‘yanuwanmu.Ki kwantar da hankalinki

zeeyta zaki je kano dandazu da safe da zan taho, umma

suka tafi kaini’ima asibiti, dazu ina ofis suka yo min waya

tahaihu.Ta wani doka tsallen murna ta rukunkumeshi,yaya

ni’ima ta haihu? Yayana meta haifa?Ta haifi danta namiji

yana nan kato akace.Wayyo yayana gobe zamu tafiyadan

bugi bayanta kin fiya zumudi zeeyta.Aikin nawa fa wa zaiyi

min.Sai karshen sati zamu tafi muje ki bani abinci.Ta gama

zuzzuba masa komai ta tura masagabansa du da sanyi a.c

saida tadau mahuccitana dan fifita masa abinci wai don

kada yakonashi.Ta dauki wayarsa ta lalubo sunan ni’ima

tadanna, ringin biyu ni’ima ta dauka, tace helloyaya.Ihun

zainab taji tanata murna, yaya ni’ima kinsama mana

baby.Ni’ima ta kyalkyale da dariya, ni kada ki kashemin

dodon kunne, yaushe zaki zo autamu?Sai karshen satihaba

zeey har sai kin kwana hudusanan zaki zo, kiga babyn naki?

I, wallahi to ya zanyi. Kinsan bazan iya tahowana bar

yayana ba shi kadai anan, dole saikarshen satin mu taho

tare.To shikenan zeey kin san kawai ni na matsu dana

ganki ne, tun safe gidan nan cike yake damutane.Kowa

yazo sai yace ai yanzu zeey kam zata zotunda na

haihu.Auta mun matsu fa da muganki.Tace wallahi nima

yaya ni’ima kuna raina.Tun sanda yaya zai taho inaso ya

taho dani donna ganku sai yakisaboda makaranta, bakomai

autarmu sai kunzo.Kafin tace wani abu, Aliyu ya karbi

wayan yakashe.Ya jawota cinyarsa taho kici abinci.Ya fara

bata ya taba cikinta “yaushe zaki baninawa babyn ne?Ta

langwabe a jikinsa nidai ba yanzu ba yayana.Nikuma yanzu

nake so zeeyta.Yaya da wahala fa, kana kallo wajen

haihuwamamana ta mutu.Ta saka kuka, yana rarrashinta

ya rinka radamata a kunanta, kada ki kuma yiwa mama

kuka,addu’a zaki rinka yi mata. Ki taya mama farin cikitana

aljanna ta manta da kacaniyar duniya.*** *** ****Ranar

jumma’a tun asuba zainab ta gama musushirinsu, tana ta

murna da doki, yana dawowadaga ofis kuwa, suka bi jirgin

shidda na yamma,harda talatu suka tafi, a filin jirgi

direbansu yazoya daukesu, taga an nufi hanyar gidanta.Ta

kalleshi tace yaya ba gida zamuje ba, tundayaya ni’ima tana

can? Yace a’a saimun je gidakin huta. Tayi shiru kawai bata

ce mishi komaiba.Suna zuwa gidan taga komanta fes, yana

ajiyeinda ta barshi, yaushe rabonta da gidanta

tsawonwatanni, amma babu wani kura ko datti a gidanga

kamshinta na nan ciki. Ko du sanda yaya yazoyana zaman

gidan?Sallah suka yi ya hau kan kujera ya mike,

yanalumshe ido son yayi bacci. Tazo ta zaunaajikinshi ta

dan marairaice masa, yaya don Allahka tashi muje gidan

yanzuya bude ido daya yana kallontazeeyta bazaki barni na

danyi bacci ba? Kayihakuri yaya yanzu aunty sadiya tayo

min wayanace mata mun sauka yaya gaba dayansu fasuna

gida sun hallara, don Allah yaya mu tafi.Ya mike tsaye tashi

mu tafi.Tace yaya kayi hakuri idan ranka ne ya baci,haba

zeeyta ba raina bane ya baci,watanni da kikayi ba kiga ‘yan

uwa ba ai nasandole kiyi zumudi,ya kamo hannunta ya

dagota, taso mu tafi.Suna shiga gidan wani ihun da suka sa

suka zosuka rungume zainab kowa murna yake yi, dafarin

cikin ganinta.Hajiya ta rinka taba jikinta tana cewa,

“Aliyuwankan inji kayi mata? Suka sa dariya, zainabtace

hajiya me kika gani?Kin canja kinyi kyau, kin kara fari,

gashinki yakara tsawo da baki.Kinyi bul-bul dake.Aunty

sadiya tace in a hanya muka hadu, ai bazamuyi saurin

ganeki ba.Yaya ni’ima tace autarmu, hutu ya kara

samuwada jin dadi.Zeey anya kina cin abinci kuwa?Du

yanda akayi daga madara sai youghot sai icecream dasu

cakulet, cimar hutu dai da jin dadikina kwance komai sai

anyi mikizeey auta canjawar taki tayi yawameye sirrin, ko

yayanmu yayi ajiyane?Tace ke kika sani, ina babyn namu?

Du nafidokinshi da murnar son ganinsa.Ta dauki baby fari

tas, kato dashi, ta rungumeshitana jin kaunar yaron.Ta

rungumeshi tayi dakin Abba, umma ta tashi dasauri ta

rungumota tana cewa ‘yata zainab najidadin ganinki, kin

kwantar da hankalinki kinyikalau dake.Abba yace “yaki

zonan ‘yata.Umma ta tafi da ita gaban Abba, ummi

tacemasha Allah dana ya iya kulawa ta musamman,Wai

zainab saita samu kanta da jin kunyarsu.

 

Wai Zainab sai ta samu kanta da jin kunyarsu, tarinka sun

kuyar da kanta, ta kasa dago kaitakallesu.A hankali ta bude

bakinta ta gaisheshi, yarinyarta kra birgeshi da shiga

ransa.Ta gaishe da umma da ummi, Aliyu yana kasagefen

kafar Abba yana mamakin irin kunyar dazainab take ji, du

yanda ta matsu tazo ta gaiyayensu, amma ta kasa sakewa

yanzu.’yata zainab ya zaman abuja, ince dai ko

bawatamatsala?Tace bakomai Abba.Yauwa zainab haka

nake sonji, Allah yayi mikialbarka.Amin Abba.Ta ajiye masa

turaruka manyan kwalabe masutsada yaita juyasu yana sa

mata albarka.Ta ajiye umma da ummi nasu harda humra

dakulacca, suma sukai godiya suna sa mataalbarka.Da kyar

ta iya mikewa rungume da jariri tayibangarensu.Ta tafi

gaban babanta ta zauna, yana lazimi, yayisaurin sallamewa,

yana murmushi.Zainab haka kika koma.Tayi murmushi,

babana naji dadi da nazo naganka lafiyanka kalau.Kullum

kana raina Babana, ina wuni?Lafiya lau zainab kin

kyautamin da kika kwantarda hankalinki.Gashi kinyi kalau

dake.Mama ta fito da fara’arta tana yi mata sannu dazuwa,

ta gaisheta ta bata tsaraban turarukan, babawa mahaifinta

kamar yanda ta bawa Abba.Sukai godiya suna sa mata

albarka.Ta mike baba bari na koma wajen su

yayani’ima.Yace to zainab.Ni’ima tana kwance a gado,

aunty sadiya tanaamsa wayar mijinta, tana gaya masa

zuwanautarsu, yace ai yana kan hanyar zuwa daukanta,ya

ga yanda zeey dinta suka koma.Ni’ima tace gaskiya zainab

kin canja da yawa,lallai ruwan aure ya karbeki.Zainab tace,

me kuma ruwan aure?Sadiya tace, ai kinsan ita bata

sanshiba, yaya maitausayinta ne, saita cika shekara ashirin,

sannanzata fara sani ko?Zainab tayi murmushi tace ku kuka

sani. Suka samata dariya, ta zauna suka fara hiran

yaushegamo.Aliyu ya shigo dakin ni’ima da sadiya suka

gaisheshi.Yazo ya zauna kusa da zainab, ya dauki babyn

dayake jikinta, ya rinka sumbatarsa yana yabayaronya

kalleta, zeey tashi mu tafi gida, tayi kasa damurya tace don

Allah yaya ka bari na kwanaanan.Yace ya za ayi na barki, ki

kwana anan nakigidan fa?Yaya bafa a gidan zaka kwana

ba, kafi so kabarni ni kadai na kwana.Kafin yayi magana

tes ya shigo wayarsa, wayartana hannun zainab saita bude

tes din, tunda tagaba lambar mansura bace, ta karanta tes

dinkamar haka.barka da zuwa yallabai, naji labarin

saukarka,kaida madam,ka iso lafiya?Kirjinta yayi wani irin

mummunan bugawa,gabanta yana fadi ta dafe kirjinta tana

haki.Yayi saurin cewa lafiya zeeytah?Meya faru?Ta

sunkuyar da kanta, ta dafe kanta da hannunta,ya ciro

hannun ya daga kanta, yace, zeeyta meyafaru?Ta

marairaice hawaye nason zubo mata, taceyaya wacece

tayo ma tes yanzu?Yace tes me akace acikin tes din?Ta

mika masa ya karanta, ya ajiye wayar, yacegaskiya ban san

ko wacece ba, don ni banma sanlambar ba, bare nasan

wacece tayo tes din.(page nan ya balle).Ranar suna sai da

yamma aka fita hotel da zaayi fatin sunan.Jama’ar suna yi

musu murna samun karuwa jaririda aka samu yasa masa

sunan babansa anakiransa da hanif.Suka zauna a

kwataccen wajen da aka tanadarmusu, gaba daya wajen

anyi shiru sabodaaddu’ar da ake yi. Sannan wani hadadden

motarAliyu ya sawo kai.Hankalin mutane gaba daya yayi

kan motar, zubaido kawai suke yi suga isasun da zasu fito

dagacikin motar, du da dai wasu sun san motar waye,suna

isa wani soja ya fito daga wajen tukin, yabude dayan

bangaren na baya, sannan ya budedayan bangaren.A tare

suka fito Aliyu da zainab kamar taurari,gaba daya

kamshinsu ya cika wurin, suka jerosuna tafe suna hirarsu

da dan murmushi, dukawajen saida suka birgesu, tare da

basu sha’awa.Banda mansura data diririce ta dabarbarce,

itatambaya ma take wacece wannan take manne damijinta?

Saida yayarta saratu ta rikota ta mayarda ita kujerarta ta

zaunar da ita, tace ki kula kisaisaita hankalinki, kada kiyi

wata gigiwa anan,don kada ki manta abunda Aliyu ya miki

akanzainab, kinsan ya gaya miki zai iya yin

komaiakanta.Sannan mansura ta kawo ajiyar zuciya,

yanzuwannan zainab ce, ‘yar da nake kiranta dagidahuma

itace ta koma haka, ta waye?Aliyu ya cuceni daya barni a

kano, saidai ko nimaya mayar dani abuja, ko kuma ayi du

wacce zaayi.Saratu ta tabe baki, tace sai kiyi kin manta

sandaya koraki gida, yanzu kuma naga alamar kina soki

yanke igiyar aurenki, me wannan cikakkiyarmata ‘yar

kwalisa ‘yar gayu, don rabu dake mezai dameshi.

 

Zainab ta dan mika bakinta dai-dai kunnen Aliyutace, don

Allah yaya ka amince min naje na gaidaaunty?Yace okey

bakomai kije.A hankali ta rinka keta jama’a suna

gaisawa.Kamshin data keji a jikin Aliyu mai dadi shi taji

tadago kai.Tana dago kai zainab tana mata murmushi,

saitaji gabanta yayi mummunar faduwa.Zainab ta rissina

sannu aunty ina wuni?Da kyar ta iya amsawa, ta kuma

rissina ta gaidayaya saratu.Ta dan doki kafadar hauwa,

mutuniyar ba aganinku ko?Hauwa tayi dariya tana rike da

hannunta, taceAllah zainab kin canja, sam ban ganeki ba,

saikace bakuwar baturiya.Tayi murmushi hauwa bana son

sharri fa.Zainab tace aunty yaya yace kizo mu koma can.Ta

kalleta ta doka mata harara, tace dan Allahcan matsa ki

bani waje, banza munafuka, bazanjeba din.Zainab tace kiyi

hakuri aunty, don Allah kizomuje.Bazan jeba munafuka

Aliyu dai kin aureshi kinjiabunda yake min mun zama

matsayi daya dake.Hankalinki ya kwanta ko?Zainab tace da

ita subhanallah aunty me yayi zafihaka? Allah ya zuci

zuciyarki.Tayi murmushin karfin hali tace hauwa yayasaratu

sai anjima.Suka ce to zainab yaya saratu ta riko

hannunta,don Allah zainab kiyi hakuri da abunda ta

miki.Tace, lah wallahi bakomai yaya. Ta juya ta tafi.Dai-dai

lokacin sabis suke raba abinci, Aliyu yarikota yace mata a

kunnenta, kika yi zamanki kikabarni ni kadai ko?Tace kayi

hakuri yayana, bazan kuma ba.To shikenan na

hakura.Ni’ima da sadiya suka zo wajensu, anata

hotuna.Sadiya tace, sadiya tace dan Allah yaya kadanara

mana zainab mintuna kadan kagakawayenmu ne ke son yin

hoto da ita.Yace, to bakomai, amma kada a wahalar da

ita.Tasa dariya, yaya daga yin hoto sai mutum yawahala?

Suka tafi da ita, sunata hotuna da kawayensu.Yana shan

lemo hankalinsa yana kan zeey dinsa,tana tsakiyarsu anayi

musu hotuna, dukkansubabu wanda ya kama kafar zeey

dinshi wajenkyau.Yaji anayi masa sallama, ya dago kai ya

kalleta,zulaiha ce, kanwar abokinsa yarinyar data keneman

takurawa rayuwarsa, a dole sonsa take,du da hade mata

ran da yake yi.Ya dan hade fuska yace ya lafiya?Tayi masa

murmushi ta zauna, tace yallabaikenan, kwana uku kenan

ina yo maka tes baamsa, ko sau daya nayi call dinka kaki

dagawa,haba yallabai ina laifin mai sonka?Zainab ana

shirin daukansu a hoto, kamar walkiyata hango mace kusa

da Aliyu tana yi masamurmushi.A hankali ta rinka yo

takunta, tazo ta zauna kantebir din da yake gabansu.Bata

ce komai ba, tadai juya musu keya, yacezeeyta, tayi masa

shiru kawai.Yace lafiya zeeyta me yake faruwa?Taki

waiwayowa bare tace masa wani abu.Ya taso ya rankwafo

gabanta, yayi kasa damuryarsa, gaya min meye zeeyta?

Kawai saihawaye ya gani ya kokarin zubowa

dagaidanuwanta.Yace, “O shit zeeyta.Ya kamo hannunta,

taso mu tafi.Sojan yayi saurin bude musu bayan motar,

sukashiga ya rufe, zai shigo ya jasu Aliyu ya dagamasa

hannu, tare da cewar ba tafiya zamuyi ba.Yace ok sir, ya

tafi can wajen shuke-shuke yayizamansa.Ya dubeta, yace

zeeyra menene?Meya daga miki hankali kike hawaye?Ta

marairaice masa, tace yaya daman ‘yan matane dakai?

Yace zeeyta wace irin magana ce wannan? Ainakika taba

ganina da ‘yan mata?Yaya gani nayi ranar da muka zo,

wata tayomaka tes, tana yi maka barka da sauka,

yanzukuma gashi kuna ta hira da wata, tana tayi

makamurmushi.Oh! Sorry zeeyta, ya rungumota yana

rarrashinta,yayi murmushi wai zeey dinshi ta iya kishi.Ya

rada mata kunanta zeey kinsan bani dara’ayin tara mata,

da ina da ra’ayi shekarun damukayi da mansura a baya

danayi aure.To da yake bani da wani buri sai naki

shiyasawata ‘ya mace bata taba burgeni ba, bare ta

banisha’awa. Shiyasa na zauna zaman jiranki HarAllah ya

kawomu na aureki, yanda kike auta agidanmu, to a wajena

ma kene autar mata, dominkece gimbiyar zuciyata ba wata

bayanke. Tasadariya Allah yayana?Allah zeeyta.Ta

rungumeshi tana dariya.Satinsu biyu a kano suka koma

abuja, kuma batasake haduwa da mansura ba, tun a wajen

fatinnan, bata kuma gayawa Aliyu cewar, ga abundatayi

mata ba.Tana kicin tana girki, ta rinka jin kanta yanajuyawa,

jiri yana dibanta, ta kasa hassala komaita zauna a kicin din

dirshan, ta matsa kararrawarkiran talatu ta shigo da

saurinta, tana fadin ganiaunty mami,halin data ganta ciki ya

bata tsorolafiya aunty mami.Ta rinka nuna mata kanta tana

lumshe idosaboda jiri.Talatu ta gigice ta daukota ta

shimfide a falo, kandoguwar kujera.Ta dauki wayan zainab

din ta laluba numbarAliyu, ta danna, tana ringin daya ya

dauka, hellozeeyta.Cikin dabir-dabir tace, ba ita bace talatu

ce, yacecikin rikicewa, talatu lafiya, ina zeey din tawa ne?

Tace bata jin dadi ne gata a kwance.Yayi zumbur ya mike

da wayan a hannunsa yafito, ya hau motarsa, bai tsaya

kiran direba bayayo gida cikin mintuna kadan.Talatu tayi

mamakin saurin zuwansa.Ya dagota zeeyta lafiya meya

sameki haka?Ta rinka nuna masa kanta, ya rike kan yana

yimata addu’a, ta rinka jin tashin zuciya, tanakokarin amai,

ta yunkura, tana so tabar jikinsa,

[7:59AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**2

Tana kokarin amai ta yunkura, tana so tabar

jikinsa, don kada ta bata shi, amma sai ya sake

rungumeta, ta rinka yunkurin aman kasancewar

bata ci komaiba sai ruwan shayi kawai data sha

ta amayar.

Ya rinka shafa kanta yana yi mata sannu, idonsa

shima yayi ja kamar yayi kuka don tausayin zeey

dinshi.

Saida ta gama aman ta kwanta luu a jikinsa

saboda rashin kuzari.

Ya dauketa ya kaita toilet ya wanke mata jikinta,

ya cire mata kayan jikinta, ya sake yi mata

wanka ya nadeta a tawul.

Ya cire kayansa yayi wanka ya canja kaya, yasa

mata wasu kayan, ya dauketa ya nufi mota, ya

sata ya figi motar da gudu.

Don du ta galabaita aman data yi ya rafkar da

ita.

Abunka da asibiti na kudi, na manya mutane, nan

da nan aka karbi zeey, likita ya fara yi mata

aune-aune da taimakon gaggawa.

Aka debi fitsarinta da jininta.

Suka jona mata karin ruwa da allura, tana ta

baccinta, Aliyu yana zaune gefenta, du ya damu

ganin yanda ta rame lokaci daya.

Bayan lokaci kadan likita ya dawo da gwaje-

gwajen tes din da yayi mata.

Ya mikawa Aliyu hannu cngrtln soja mata tana

dauke da cikin wata biyu.

Wani irin nishadi da farin ciki ne ya kwarara a

zuciyar Aliyu, ya washe baki yana murna ya daga

hannu sama yana godiya ga ubangiji.

Yace nagode likita, ka duba min madam sosai,

inaso ka kure tunaninka, ka rubuta mana

maganguna masu kyau, wanda zasu kara mata

lafiya da kuzari ita da baby.

Likita yayi murmushi yace, kada ka damu, du

maganin da nasan zai taimaka musu zan rubuta

muku, amma laulayi dole sai kunyi a hankali, da

cikin yayi kwari zata samu yanda kake so.

Ka rubuta min abubuwan da zata rinka ci da sha

da zai kara mata lafiya da babyn.

Ok zan rubuta muku, Allah ya kara sauki, amin.

Likitan ya fita Aliyu yayi waya ofis dinsa yake

gayawa sakatariyarsa du wanda yazo nemansa

yana asibiti, madam dinshi ba lafiya.

Ta jajanta masa tare da fatan Allah bata lafiya.

A hankali ta bude idonta tana kallon karin ruwan

da akayi mata.

Ya kashe wayar tare cewa sannu zeeyta.

Tace, yaya kasa akayi min allura, a cire min

wannan bana so.

Ya rinka shafa kanta yi hakuri barinsa su cire

miki,

ya dagota zaune, tana rungume a jikinsa, likitan

ya shigo Aliyu yace, yauwa cire mata karin ruwan

naga ya kare.

Tana noke hannun, tana wash-wash, tana

langwabe ajikin yayan nata, da haka likitan ya

zare mata allura yana tsokanarta raguwa me raki.

Aliyu ya rinka rarrashinta yana bata youghot da

kaza.

Kwananta uku a asibiti ta samu sauki, ta ware,

abokan Aliyu da matansu kullum suna turuwar

zuwa dubata, taji sauki an sallameta ta koma

gida.

Aliyu kullum yana manne da zainab har hutu ya

dauka, yake zaune a gida, don dai kawai kulawa

da ita, bashi da magana sai cikin dake jikinta

kamar bai taba haihuwa ba.

Tana kwance akan kujera tayi matashin da

cinyarsa yana karanta mata jarida.

Talatuwa ta kwankwasa kofar akayi mata iznin

shigowa.

Tace aunty mami, me za a girka miki?

Tace kiyi min pepper chicken, sai kiyi min hadin

salad. Shikenan

tace, to yaya fa? Tace a’a haba talatu girkin

yayan nawa zan baki kiyi?

Ki bari kawai na samu sauki zan mishi da kaina,

na hotel dinma an daina siye.

Talatu tayi murmushi, tace to uwar dakina, ta fita

Aliyu yace nifa bana son abunda zaki wahala ki

bari naci gaba da siyo a hotel din.

Tace, haba yayana kamarka ka rinka shiga hotel

siyan abinci.

Ni dai bana so, ka bari zan rinka yi maka nafa

samu sauki.

Ya shafa cikin nata, to ai ni babyn nawa kada

yazo yana kara saki amai, wahala kike yi zeeyta.

Bari dai nayiwa su Abba waya na gaya musu

albishir tunda kin samu sauki na gaya musu mun

samu ciki.

Tayi saurin damke wayar cikin shagwaba, nidai

yaya gaskiya kada ka gaya musu, so kake su san

abunda muke yi, da wane ido zamu kallesu? Nidai

kunya nake ji.

Haba zainab haka zamuyi ta zama bazamu gaya

musu abun farin ciki da ya samemu ba?

Um nidai yaya kada ka fada kunya nakeji.

To shikenan bazan fada ba.

Cikinta yana wata hudu aka karawa Aliyu girman

babban matsayi a soja, a lokacin ne kuma ya

gama musu tamfatsetsen gida da yake musu gina

a kano, ginin da aka farashi tun kafin ya auri

zainab.

Kowa da bangarensa fadin tsarin gidan bata

lokacine,

lokacin suka taho kano don zasu tare a sabon

gida.

Sannan zainab ta ciko tayi fresh, yaron cikin dan

wata hudu yayi mata kyau, yadan tasa kadan,

amma ba kowa ne zai iya ganewa da cikin ba, sai

me kula.

Lokacin da suka sauka ‘yan gidansu sun

zagayeta kamarsa cinyeta, kowa dada sonta

yake, Abba da daddy sunfi kowa jin dadi da

alfaharin auren ‘ya’yan nasu.

Umma kuwa kamar ta lashe zainab saboda

tsananin jin dadi, bama data hango dan matashin

cikin da yake jikinta, tana ganin kuma ta samun

jika daga wajen yaron kirki.

Ni’ima da sadiya suna zuwa suka rungumeta,

suka yi saurin cikata suna taba cikin, zeey ciki?

Ta kwalalo ido “bani da komai, suka yi dariya,

“um mun gani dai.

Ranar akayi walimar tarewansu a sabon gida,

kowa ya yaba da tsarin gidan da kyansa makeken

gida unguwa guda, ga wajen wasan buga ball,

wajen basket ball, lilina na yara, ga lambu da

swiming ful a ciki. Da dai abubuwan kawata gida.

 

TATTALIN SO 4**3

.

Yarinka lallaminta yana jijjigata kamar karamar yarinya,

harta koma bacci, sannan ya mike ya tafi. Be dade da jan

motarsa ya tafi ta farka da wani gigitaccen ciwon baya da

mara, ta farka tana salati, ta matsa kararrawar kiran talatu

shiru bata shigo ba ta tuna fa ashe tun dazu ta tafi gidan

yarta. Ta taso a hankali tana dafe da kugu, tana salati ta

fito babban falo. Mansura tana zaune tana kallo, ta jiyo

salatinta da nishinta, ta juyo tana kallonta, ta tabe baki ta

juya taci gaba da kallonta. Zainab ta durkusa a gabanta ta

daura kanta akan cinyarta, tana salati. Aunty dan girman

zatin Allah ki taimaka min ki tallafawa maraicina, ki dubi

girman Allah aunty kinsan abunda nakeji. Saita ji jikinta yayi

sanyi, taji tausayin yarinyar ta tuna irin gigicewar dayi

sanda tana nakudar Ahmad, da yanda yarinyar tai ta kuka.

Ta juyo ta kalleta, ta murkususu a jikinta, ta dauki waya ta

bugawa direban gidan, tace maza ya fito da mota. Ta

taimakawa zainab din, saida suka shiga direba ya dauki

hanyar asibiti data ke zuwa awo. Mansura ta fito da

wayarta tana neman layin Aliyu amma bata sameshi ba, har

suka isa asibitin, ana kokarin shigar da ita dakin haihuwa,

ta samu lambar Aliyu ta shiga. Ringin uku ya dauka, hello!

.

Aliyu muna asibiti da zainab ba lafiya. Kafin ta karasa cikin

kara yace mata what? Tayi saurin cire wayan daga

kunnenta, don jin yana barazanar tsorata mata dodon

kunne. Daga nan ya hawo motarsa ya nufo asibiti, ya tarar

da ni’ima da sadiya dasu umma sunata zarya a kofar dakin

data ke ciki. Yana zuwa bai tsaya ba ya banka dakin

haihuwar tayi wujiga-wujiga tana salati, wata likita tana

tsaye a kanta. A galabaice ta rinka miko masa hannu, tana

cewa wayyo yayana zan mutu, yaya ka yafemin, yaya haka

mamana tayi shiyasa ta rasa ranta. Yazo ya zauna a gefen

gadon ya rungumeta, yana rarrashinta kiyi shiru zainab, kita

addu’a Allah zai saukeki lafiya kinji? Ya rinka murza mata

bayanta, yana karanata addu’o’i ya tofa a ruwa ya bata

tasha. Taji ciwon ya lafa mata, ta bingire a jikinsa ta fara

bacci, can wani gigitaccen ciwo ya farkar da ita, cikin lokaci

kankani ta rikice da salati ta kankame Aliyu likitan tana

taimaka mata, katuwar ‘yarta ta fado fara tas da ita. Wata

irin dariya Aliyu ya saka, tare da jerawa ubangiji kirari, yana

nuna godiyarsa ga Allah. Ya dauki ‘yar ya rungumeta,

yanata aikin kallon babyn, likita tana gyara zainab, kamar

wanda aka mutsina yayo waje da gudu yana kiran umma,

mama, ummi, gaba daya suka yo kansa suna masu farin

ciki.

.

Ummi ta karbeta, kai tubarkallah masha Allah. Su ni’ima da

sadiya sai lekenta suke yi a hannun ummi, su naso su

dauketa, amma Aliyu ya hana, wai kada a jagwagwalaa, ko

ya manta suma sun a haihune. Likita ta fito cikin kalmar

turanci take ce masa likita baka tsoro bebyn tayi mura ne,

ka fito da ita take shakar iska? Aliyu yace ato ku kawota. Ya

karbeta da sauri yayi cikin dakin da ita. Su umma duk suka

bishi don ganin jikin zainab din. Zainab tana ganin su umma

ta rufe idonta wai kunyarsu take ji, ni’ima da sadiya sunata

yi mata dariya. Mansura kuwa tana tsaye a gefe tana

mamakin irin murnar da Aliyu yake yi, kamar wanda bai

taba haihuwa ba. Mansura ta fito daga dakin, don bazata

iya kallon takaici ba. Ya wani zauna dirshan a gadon zainab

din, jikinsa yana gogar nata, kamar zai rungumeta, sai wani

dariya yake. Ta dauko wayarta ta buga, hello yaya saratu,

yarinyar nan fa ta haihu yanzu, haba dan Allah meta haifa?

Um du wannan iyayi da akeyi ta bige da haihuwar mace.

Saratu tace “A me bambacin mace da namijin,kema ai yaya

saratu kinsan mace da namiji akwai bambanci.

.

Ai namij shine magajin gida bare ahmad shekara takwas fa

kenan, a hada da ‘ya mace ta mintuna amma kinga yanda

shida kannensa da iyayensa yanda suke ta wani murna da

farin ciki. Saratu tace gaskiya mansura sai anyi miki uzuri,

wannan hali naki sai an taimaka miki da addu’a, ni kinga

bazan iya sauraran wadanan kananun maganganu naki ba,

ta kashe wayar. A ranar aka sallamesu saboda mai jego da

baby lafiyarsu kalau. Ummi itace a gun zainab. A ranar da

dare saida ta kori Aliyu bangarensa, da asuba talatu ta girka

garwa kan kuka gas, ruwan ya tafasa ta kwashe, ummi tayi

wa zainab cikakken wakan jego, tana zillewa tana wash a

haka aka gama. Zainab tana shiryawa ummi tana yiwa

baby wanka talatu tana goge lokaci daya du suka gama.

Me jego da baby sun fito dagwas shar dasu, gaba daya

bangaren nata ya rikice da kamshi me rikita zuciya. Karfe

takwas Aliyu ya shigo, ya durkusa ya gaida ummi, ya karbi

babyn a hannunta, yace ummi zeey din tana ina? Tana daki.

Ya mike da babyn a hannunsa ya shiga dakin , sai yaji

kamshin da dakin yake yafi na ko ina dadi. Tana zaune a

gefen gado ya shiga da dariyarsa, me jego kinsha kamshi.

Tayi murmushi yazo ya zauna kusa da ita. Ta durkusa kasa,

yaya ina kwana? Lafiya lau, yaya babyn ta kwana? Gata

nan ka ganta. Ya dago zainab din ta zauna a jikinsa, zainab

kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni?

.

Zainab kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni? Saboda

me yaya? Wallahi tunani babyn nan tawa ‘yar kyakywan nan

ta zauna min daram a rai, tunda na taso ranar da aka

haifeki, na ganki kika zauna daram a zuciyata, ban taba

tunanin za a samu abunda zai kuma shiga zuciyata ya

zauna min irin haka ba, sai gashi kin haifa min kyakyawan

diyata da tafi komai shiga zuciyata. Zainab ta kalleshi cikin

shagwaba tace, yanzu yaya kafi sonta dani? Yayi murmushi

ya shafi fuskarta, yace ai ke dabance zeeyta, kaunar

danake miki bata da misali, amma kinga bebyn nan tawa

ma ta maye ruhina gaba daya. Zainab kin gama min komai

da kika haifomin bebyn nan, bani da bakin da zan miki

godiya, bani da abunda zan baki. Babbar addu’a da zan

miki Allah ya miki tukuici da gidan Aljannah amin yayana.

Bebyn ta dan motsa, ya balle marfin swan water, ya tsiyayo

kadan a kofin azurfa ya bata tasha. Yace bata nononta

tasha. Yaya wallahi data kama jiya, baka ji zafi ba. Yi hakuri

ki bata a hankali zai daina zafin. Zainab din taba bata tana

cije baki tare da cewar wash. Lallabata yakeyi yana cewa,

yi hakuri zeeyta, tasha ta koshi, yauwa bata dayan. Da haka

babyn tasha ta koshi, ya karbeta ya dorata a kafada, yana

shafa bayanta har tayi gyatsa taci gaba da baccinta. Zainab

ta dora kanta akan cikinsa, yana tambayarta me da me take

so ayi shagalin suna? Suka jiyo karadin ni’ima da sadiya

suna buga kofa yace su shigo. Suka shigo, sadiya tace

yaya ka hade zeey din da bebyn du ka rikesu anan ga

jama’a ga jama’a can sunata zuwa barka ba me jego ba

beby. Yace nifa bana son yawan daukan nan fa, saboda shi

yake kawowa yara ciwon jiki. A fitar da kan gadonta falon a

sakata a ciki, a rufe da net din, du wanda yazo ganinta ya

ringa lekata kawai, a ganta haka basai sun dauka ba. Ranar

kwana hudu aka kawo kayan barka akwatuna shidda uku

na beby akwatuna uku na mai jego fadan kayan da suke

cikin akwatin bata lokacine.

.

Mansura ta mike fuu tayi bangare Aliyu, ta banko kofar

dakinsa, babu sallama ta tsaya masa tsegege aka, yana

kwance akan gado yana kallonta. Tace Aliyu nagaji da

wannan rashin adalci naka, ni bazan iya zama ba, kana

nuna min iyakacina, ka dubi uban kaya daka jibgawa zainab

da jaririyarta, ni wallahi bazan yarda ba saide kome zai faru

ya faru, ya daga mata hannu ki saurara kada kiyi min

hayaniya aka, fita ki bani waje. Ta fito ta kwashi akwatunan

daya bata ita da Ahmad tasa aboot din motar da ya bata da

akwatunan ta tafi gidansu. Mansura tana isa gida, tasa

kannanta suka shigo mata da akwatunan, iyayenta suna

falo da saratu da hauwa, suka tareta da lafiya? Tace

wallahi Alh na gaji da rashin adalcin mutumin nan, ka dubi

‘yan kayan da ya bamu nida Ahmad, amma ita ya hada

mata akwatuna shidda ita da ‘yarta kuma ya bata irin motar

da ya canja min. Saratu ta bude kayan tana gani, super da

holland da les da material da shadda ganila ga takalma

jaka da sarkar gwal. Akwatin Ahmad ma kananan kaya

masu tsada, sai shadda da boyel masu tsada sun sha aiki,

kala goma sha daya, ga takalma da huluna masu kyau da

tsada, harda glas mai ruwan gwal suka gama gani, saratu

ta rufe kayan, hajiya tace mun gani Allah ya saka da

alkhairi, ubangiji ya kara buda masa. Mansura tace, hajiya

nifa na taho gida, ku kirashi kuyi masa fada bazan iya zama

da wannan rashin adalcin nasa ba…. Kafin ta rufe bakinta

Alh ya wanke mata fuska da mari, hajiya ta rufeta da duka.

Dabbar yarinya mara hankali, dazunan ya kawomin

makullin mota sabuwa kar. Ya aikowa da mahaifiyarki

katon injin kankara don ta rinka sana’a dashi shine kike

kokarin tozarta kanki, da yake bakisan abun arziki ba, to du

ranar da kika sake zuwa gidan nan kika kawomin karar

mijinki, saina karyaki, bare kuma kiyo yaji, wannan kasheki

zanyi murus har lahira. Fita ki bani waje, ya biyota tayi waje

da sauri,

.

kananta suka mayar mata da akwatunan cikin mota, taja ta

koma gida tana hawaye, fuskarta da yatsun babanta daya

mareta. Tazo ta wuce ta babban falo tana kuka Aliyu yana

zaune yana kallo, ko kallonta baiyi ba, ta wuce bangarenta.

Ranar suna aka sawa jaririyar sunan maman zainab, suna

kiranta da ihsan. Taron suna yayi kyau angama lafiya aka

watse. Kyaututuka da zainab ta samu baza su lissafuba,

daga kawayenta, abokan Aliyu ‘yan uwa da abokan arziki,

kayan kamar a bude sito dashi. Yaya ni’ima tace, kinsan

kuwa yau shekarar ku uku cif da aure da yaya. Shida yayi

alkawari saikin shekara uku sannan zai kusanceki, sai gashi

shekara uku tazo da ‘yar diyarku ko? Zainab tace ke kika

jiyo, ni ba ruwana. Suka sa mata dariya. *** ***** kwanci

tashi rayuwa ta mika, zainab tuni sunyi arba’in, harta koma

abuja, taci gaba da karatunta. ‘yar diyarta saida daddynta

ya nema mata tsari sosai, saboda kyan Ihsan du wanda ya

bude baki, sai yace hu! Wannan yarinyar da kyau take.

Ihsan watanta shidda kenan tayi ‘yar kubibi abun sha’awa

da ‘yan hakoranta biyu abakinta, tayi sabo da Aliyu du

sanda ya dawo gida, yana tare da ita, don haka data ganshi

tana bayan talatu zata rinka zillo. Ya karbeta ya rungumeta,

yana murnar ganinta…

[8:01AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**4

Tabbas badan tasan zafin zuciyar Aliyu ba, ba

zaiyi mata ta dadi ba, da sai ta barar da abincin.

Fuu! Ta tashi tayi daki, kamar kububuwa, su

kuwa basu kula da ita bama.

Sati yana cika suka koma Abuja, Aliyu yaci gaba

da rainon zainab da cikin da yake jikinta, taci

gaba da zuwa makarantarta, Aliyu shi yake dada

ganar da ita gun da ya shige mata duhu, don

haka kwakwalwarta ta sake budewa, take da

kokari sosai.

Don ma yanzu cikinta yayi nauyi, wani abun yana

yi mata wahala, tana daurewa ne, don saboda

Aliyu kokari yake ya hanata zuwa makarantar,

wai tana wahala.

Ga hajiya tanata damunsa da waya ya kawo

zainab ta haihu a gida, du sanda yazo wkend

hajiya ta sashi a gaba kenan tai ta mita.

Dole sai ya kawo zeey din ko kuma tasa a

kawota, har abujan ta taho da ita.

Yace hajiya kiyi hakuri, exam suke yi, yanzu saura

sati biyu su gama, suna gamawa zan dauki hutun

shekara saimu taho tare, tace to yanzu naji

magana.

Suna gama jarabawa kuwa, da sukayi hutun wata

biyu suka taho gida kano.

Du wata siyayyar haihuwa ta kayan baby da mai

jego Aliyu ya wuce dubai zaiyo musu acan.

Satinsa daya acan ya dawo ya tarar cikin zeey

dinshi ya kara girma, don komai a wahale take

yinsa, da kyar take daga kafa.

Har baya so yaga ta tashi don sai yaga kamar ya

ciro cikin ya dawo dashi jikinsa.

Da ta tashi zai dawo da ita, menene ne, ina zaki?

Yaya lemo zan dauko maka, ya kwantar da kanta

a kafadarshi yana lallaminta kamar karamar

yarinya, ki bari zan dauko da kaina, don Allah ki

daina wahalar da kanki, ni nake jin ciwon ajikina.

Sai kuma ta langwabe a jikinsa ta kama kuka ya

rinka jijjigata, yana rarrashinta, ya rada mata a

kunanta menene, gaya min me akayi miki?

Yaya ba kaine kayi tafiyarka ka barni ba, har

kwana bakwai?ya rinka shafa bayanta, shikenan

yi shiru, bazan kuma tafiya na barki ba. Shikenan

yi shiru kada kanki yazo yana ciwo.

Mansura tazo kansu tana huci, tace, ai saika

mayar da ita ciki, karewar shagwaba da sangarta,

ko kuma ka sakata a jaka, ka rinka yawo da ita

du inda zaka je.

Kuma wallahi rashin adalci da ake yi min na

daina yarda, bazan kuma zama anan ka dauketa

ku tafi abuja ba, kana tura mata kudi kana kashe

mata kudi acan, taci abunda du ranta yake so, ka

kalli yanda kuka canja kamar masu rayuwa a

turai.

To wallahi ko mu rinka tafiya abujan gaba daya,

ko kuma wananan intaje tayi watanni wannan ma

taje.

Ya daga mata hannu ya isheni, tunda ke baki iya

sannu da zuwa ba, sai kananan maganganu kika

iya.

Ta tafi tana kunkuni a dakeka a hanaka kuka,

nidai bazan yarda da zalunci ba, ko gware kuka yi

kuka fito karewar ‘yan uwantaka.

Ta bar wajen. Aliyu ransa ya baci, ya rinka huci

yana kokarin tashi, zainab ta sake langabewa

ajikinsa, tana shafa kirjinsa, yayana menene dan

Allah?

Ka huce kada damu yayana.

Da safe zainab tasha kwalliyarta da wata ganila

shadda bulu tayi kyau, Aliyu ma yasha wata

lallausar farar shadda, sai kyalli takeyi kamar

boyal, sai tashin kamshi suke yi, kamshin da yake

tsoratar da mansura, ta rasa wani irin kamshine

dasu.

Du da ya hanata yin komai amma ranar girkinta

bata iya hakuri saita yi masa girki.

Yau ma ita ta hada break din suna kan tebir din,

shida mansura suna ci amma ita ta kasa cin

komai.

Aliyu yace zeeyta kici mana.

Tace, yaya bazan iya ci ba.

Nasa talatu ta gasa min hanta ita kawai zanci.

Ya ajiye kofin tea din, yace, bakya jin dadi zeey,

tun jiya ina kula dake, taso na kaiki asibiti.

Tace, yaya bana jin ciwon komai

bakina ne kawai ba dadi.

Mansura ta tabe baki ta yamutsa fuska, tace

kyaji da gulmarki, haihuwa dai ba abar wasa

bace, in kin tsaya iyayi kyasha wahalarki ke

kadai.

Aliyu yace Allah zai rabata da wahala, lafiya lau

zata haihu, na samu jaririn dana dade ina

mafarkin samu.

Mansura tace Allah sarki wane dare ne jemage

bai gani ba? Ai sai daran mutuwarsa.

Talatu tayi sallama ta shigo ta kawo mata gashin

hantarta, Aliyu ya karba ya yanka yasa wa zainab

a baki, ta rinka tauna tana yamutsa kamar mai

cin magani.

Shi kuma du ya damu, sai lallabata yake yi da

taci, mansura kuwa ta kumbura tayi tim, haushi

da takaici suka cikata.

Ni’ima tayi sallama ta shigo tana dauke da

yaronta hanif, zainab ta kama dariya, Oyoyo ‘yar

uwa naji dadin zuwanka, bani yarona naji

duminshi.

Aliyu yayi saurin karbarsa yana cewa, zeey ai

bazaki iya daukansa ba, tubarkallah yayi nauyi.

Aliyu ya rinka yi masa wasa yanata dariya, ni’ima

ta gaishe da yayan nasu.

Ta juya tana gaishe da mansura, ta amsa a ciki,

ni’ima ta shareta don intana cikin wannan

yanayin bada sauraronta.

Ni’ima ta fito da atamfar super hollan da les

masu kyau, tace zainab ga ankon suna mun fito

dashi.

Zainab tace yaya ni’ima har wani anko za ayi?

Tace ke kada kimanta dan autarmu nefa da

babban yaya, ai dole muyi abubuwan da zasu

kayatar masa da taron sunan dan dangi (kuji

ni’ima da tsokana)

zainab ta debi kayan ta mikawa mansura, aunty

ga ankon suba nan su yaya ni’ima sun fitar.

Ta watsar da kayan ta doka mata tsaea, dan

Allah can yimin shiru kwaji da munafuncinku,

maga dai abunda za a haifa ko dan gwal ne ma

gani.

[8:02AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**5

Aliyu ya dago kansa yayi mata wani mummunan

kallo, ya rinka wani huci na bacin rai, mansura ta

juya ta shige bangarenta.

Aliyu ya mike zai bita zainab ta rikoshi ta

marairaice fuska, kamar me shirin yin kuka, tace

yaya don Allah kayi hakuri, kaji ka huce, bani

break din zanci.

Ya koma ya zauna, yayi ajiyar zuciya, ya rinka

bata break din du da ba dadinsa takeji ba, amma

ta daure taci sosai, don ta kwantar masa da

hankali.

A yangace tace, yaya na koshi, yayi murmushi, ai

naji dadi ma da kika ci wannan din, hankalina har

ya kwanta.

Ya mike ya dauki makullin mota, bari naje ofis, na

tabbatar da kayan da suka iso jiya, an gama

jibgesu a sito.

Ta mike a hankali ya riketa, kiyi zamanki ki huta,

ta makale kafada, tace um-um nidai saina

rakaka.

Ta dauko masa jakarsa, suka jera suna hira cikin

nishadi, suna murmushi, suna zuwa kofar falon ya

karbi jakan yace, ta koma ciki, ta rinka daga

masa hannu yana daga mata, har ya shige mota,

ita kuma ta dawo falon, ni’ima ta mike suka yi

bangarenta.

Ni’ima tace wai ke zainab ke wacce irice? Ta

rinka yi miki abu iri-iri bazaki dau mataki ba,

kuma ki rinka hana yaya yi mata komai.

Tace haba yaya ni’ima, Allah du abunda take yi

baya sakamin bacin rai, ko daya a zuciya.

Kuma in na mace zan ringa biyeta, ai kullum yaya

bazai samu kwanciyar hankaliba, du inda yaje

yana tunanin halin da gidansa yake ciki.

Yanzu kuwa ko ina yaje hankalinsa kwance,

yasan bazan saurareta ba, kuma dan habaici tai

tayi mana, nasan ko giyar wake tasha bazata kai

hannu ta dake ni ba. Hayaniya kuwa taita yi,

wata rana zata gaji ta daina, dan karfe daya baya

amo.

Ni’ima tace hakane.

Suka ci gaba da hirar abunda ya shafesu.

**** **** *****

mansura tana shiga dakinta ta dauki wayarta ta

bugawa tayarta saratu.

Hello! Mansura ya akayi ne?

Tayi tsaki hum yaya saratu, gaskiya matsalolin

gidan nan sun fara isata.

Tace menene kuma meya faru?

Tace, um mutumin nan du ya wani rikice akan

cikin yarinyar nan, saika ce wanda bai taba

haihuwa ba, zaita lallbata tana wani yanga da

yamutsa ga shagwabar tsiya (komai girman

namiji wani lokacin yana son ana masa

shagwaba), ta kama kukan gulma ya rikice

yanata rarrashinta, sai kace wata ‘yar kwai.

Yarinya ina ganinta gidahuma kamar ba

wayayyiya ba ina ganin bazata iya aikata abunda

take yi ba, kinga yanda take zama dakyar ta tashi

da dakyar amma du ranar girkinta, ita zata yi

masa du wani abun da kanta.

Kuma shima da yake munafikine, ranar girkina

idan kuku yayi girkin iyakacinsa yaci cokali biyu,

ko uku ya ture. Ranar girkinta kuwa ta sashi a

gaba tana loda masa abinci yana ci yana santi

tana dariya, sai yaci dayawa.

Baki ga yanda yake daukin cikin nan ba, kullum

addu’arsa da fatansa ta haihu lafiya inda kika san

ba a taba yi masa haihuwa ba.

Gashi ya mayar da Ahmad din irin makarantar

dasu zainab din suka yi, bazai dawo ba sai shidda

na yamma wannan ai zalunci ne.

Gashi ya debi yayunta ya dorasu akan dukiyarsa,

wannan kamfanin nasa fa a hannunsu yake, daya

darakta daya manaja.

Saratu ta katseta to ina ruwanki ba ‘yan uwansa

bane? To idan ‘yan uwansa ne ni bazaiyi min

kara ba?

Kamfaninsa na motoci ya daura kannensa, da

suke uwa daya uba daya da ni’ima su biyu da

nasa kannen biyu. Shi kenan arzikinsa saide suci

su isu? Ni banda nawa dangin kenan?

Saratu tace kedai mahaukaciya ce wallahi, ki

jawowa kanki abunda zai sakeki, kizo mu sake

zama.

Kina kallona gashi miji yaki samuwa, kuma kice

yana yiwa danginsa banda naki.

Kina ina ya dauki rabi’u da hamisu

ya kaisu kamfanin nasa ya basu aikin yi. Ko kin

manta da zaman banza suke yi.

Gashi yana zuwa yana gaida iyayenmu, ya kawo

musu kudi da kayan abinci. Du ya dauke wasu

sabgogin gidan nan ba tare da kin sani ba ko yayi

shawara dake.

Nidai bazan gaji da baki shawarar ki rike mijinki

da kishiyarki ku zauna lafiya.

Mansura tace, kai yaya saratu abunda nake nuna

miki daban abunda kike hange daban.

Sai anijima tunda kinki ganewa.

Bayan sati daya da dawowan Aliyu daga dubai,

ranar a dakin zainab ya kwana. Da safe ya

taimaka mata tayi wanka, da kwalliyarta ya bata

break taci.

Ta langabe ajikinsa, ya dago kanta, menene zeey,

tana limshe ido tace bacci, yace bai isheki ba

baccin?

Ta daga kai alamar amsawa.

Ya kwantar da ita a hado a hankali ya rinka

matsa mata jikinta, da bayanta data fi yawan

kuka dashi saboda ciwo ya rinka murza mata shi,

sannu-sannu tayi bacci, yayi ajiyar zuciya ya

mike ya fara shiri ya gama shirinsa yana fesa

turaruka.

Wayarsa tayi kara ya dauko yana amsa wayar ta

bude ido tana kallonshi.

Ya gama wayar yasa a aljihunsa, ya dauki

makullin motarsa yazo ya durkusa a gabanta,

yasa hannu yana shafa kanta, yace, an

shammaceni anyo min waya, kararta ta tasar min

dake, da nasan za a yo wayar nan da falo zan

fita.

Da baki tashi ba, bana so ki samu matsala kanki

yazo yana ciwo.

Tace yaya bakomai, normal nake jina, tace yaya

ina zakaje?

Ofis din su Abba znje kona zauna?

A’a yaya kaje Allah kiyaye hanya, ya dawo dakai

lafiya.

To koma baccinki ya rinka lallaminta yana jijjigata

kamar karamar yarinya harta koma bacci

[8:03AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**6

Yarinka lallaminta yana jijjigata kamar karamar

yarinya, harta koma bacci, sannan ya mike ya

tafi.

Be dade da jan motarsa ya tafi ta farka da wani

gigitaccen ciwon baya da mara, ta farka tana

salati, ta matsa kararrawar kiran talatu shiru bata

shigo ba ta tuna fa ashe tun dazu ta tafi gidan

yarta.

Ta taso a hankali tana dafe da kugu, tana salati

ta fito babban falo.

Mansura tana zaune tana kallo, ta jiyo salatinta

da nishinta, ta juyo tana kallonta, ta tabe baki ta

juya taci gaba da kallonta.

Zainab ta durkusa a gabanta ta daura kanta akan

cinyarta, tana salati. Aunty dan girman zatin Allah

ki taimaka min ki tallafawa maraicina, ki dubi

girman Allah aunty kinsan abunda nakeji.

Saita ji jikinta yayi sanyi, taji tausayin yarinyar ta

tuna irin gigicewar dayi sanda tana nakudar

Ahmad, da yanda yarinyar tai ta kuka.

Ta juyo ta kalleta, ta murkususu a jikinta, ta

dauki waya ta bugawa direban gidan, tace maza

ya fito da mota.

Ta taimakawa zainab din, saida suka shiga direba

ya dauki hanyar asibiti data ke zuwa awo.

Mansura ta fito da wayarta tana neman layin

Aliyu amma bata sameshi ba, har suka isa

asibitin, ana kokarin shigar da ita dakin haihuwa,

ta samu lambar Aliyu ta shiga.

Ringin uku ya dauka, hello! Aliyu muna asibiti da

zainab ba lafiya.

Kafin ta karasa cikin kara yace mata what? Tayi

saurin cire wayan daga kunnenta, don jin yana

barazanar tsorata mata dodon kunne.

Daga nan ya hawo motarsa ya nufo asibiti, ya

tarar da ni’ima da sadiya dasu umma sunata

zarya a kofar dakin data ke ciki.

Yana zuwa bai tsaya ba ya banka dakin haihuwar

tayi wujiga-wujiga tana salati, wata likita tana

tsaye a kanta.

A galabaice ta rinka miko masa hannu, tana cewa

wayyo yayana zan mutu, yaya ka yafemin, yaya

haka mamana tayi shiyasa ta rasa ranta.

Yazo ya zauna a gefen gadon ya rungumeta, yana

rarrashinta kiyi shiru zainab, kita addu’a Allah zai

saukeki lafiya kinji?

Ya rinka murza mata bayanta, yana karanata

addu’o’i ya tofa a ruwa ya bata tasha.

Taji ciwon ya lafa mata, ta bingire a jikinsa ta

fara bacci, can wani gigitaccen ciwo ya farkar da

ita, cikin lokaci kankani ta rikice da salati ta

kankame Aliyu likitan tana taimaka mata, katuwar

‘yarta ta fado fara tas da ita.

Wata irin dariya Aliyu ya saka, tare da jerawa

ubangiji kirari, yana nuna godiyarsa ga Allah.

Ya dauki ‘yar ya rungumeta, yanata aikin kallon

babyn, likita tana gyara zainab, kamar wanda aka

mutsina yayo waje da gudu yana kiran umma,

mama, ummi, gaba daya suka yo kansa suna

masu farin ciki.

Ummi ta karbeta, kai tubarkallah masha Allah. Su

ni’ima da sadiya sai lekenta suke yi a hannun

ummi, su naso su dauketa, amma Aliyu ya hana,

wai kada a jagwagwalaa, ko ya manta suma sun

a haihune.

Likita ta fito cikin kalmar turanci take ce masa

likita baka tsoro bebyn tayi mura ne, ka fito da

ita take shakar iska?

Aliyu yace ato ku kawota.

Ya karbeta da sauri yayi cikin dakin da ita. Su

umma duk suka bishi don ganin jikin zainab din.

Zainab tana ganin su umma ta rufe idonta wai

kunyarsu take ji, ni’ima da sadiya sunata yi mata

dariya.

Mansura kuwa tana tsaye a gefe tana mamakin

irin murnar da Aliyu yake yi, kamar wanda bai

taba haihuwa ba.

Mansura ta fito daga dakin, don bazata iya kallon

takaici ba.

Ya wani zauna dirshan a gadon zainab din, jikinsa

yana gogar nata, kamar zai rungumeta, sai wani

dariya yake.

Ta dauko wayarta ta buga, hello yaya saratu,

yarinyar nan fa ta haihu yanzu,

haba dan Allah meta haifa? Um du wannan iyayi

da akeyi ta bige da haihuwar mace.

Saratu tace “A me bambacin mace da

namijin,kema ai yaya saratu kinsan mace da

namiji akwai bambanci. Ai namij shine magajin

gida bare ahmad shekara takwas fa kenan, a

hada da ‘ya mace ta mintuna amma kinga yanda

shida kannensa da iyayensa yanda suke ta wani

murna da farin ciki.

Saratu tace gaskiya mansura sai anyi miki uzuri,

wannan hali naki sai an taimaka miki da addu’a,

ni kinga bazan iya sauraran wadanan kananun

maganganu naki ba, ta kashe wayar.

A ranar aka sallamesu saboda mai jego da baby

lafiyarsu kalau.

Ummi itace a gun zainab.

A ranar da dare saida ta kori Aliyu bangarensa, da

asuba talatu ta girka garwa kan kuka gas, ruwan

ya tafasa ta kwashe, ummi tayi wa zainab

cikakken wakan jego, tana zillewa tana wash a

haka aka gama.

Zainab tana shiryawa ummi tana yiwa baby

wanka talatu tana goge lokaci daya du suka

gama.

Me jego da baby sun fito dagwas shar dasu, gaba

daya bangaren nata ya rikice da kamshi me rikita

zuciya.

Karfe takwas Aliyu ya shigo, ya durkusa ya gaida

ummi, ya karbi babyn a hannunta, yace ummi

zeey din tana ina?

Tana daki.

Ya mike da babyn a hannunsa ya shiga dakin ,

sai yaji kamshin da dakin yake yafi na ko ina

dadi.

Tana zaune a gefen gado ya shiga da dariyarsa,

me jego kinsha kamshi.

Tayi murmushi yazo ya zauna kusa da ita.

Ta durkusa kasa, yaya ina kwana?

Lafiya lau, yaya babyn ta kwana?

Gata nan ka ganta.

Ya dago zainab din ta zauna a jikinsa, zainab

kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya daukeni?

A daure anayin comment please

[8:04AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**7

Zainab kinsan kuwa jiya da kyar bacci ya

daukeni?

Saboda me yaya?

Wallahi tunani babyn nan tawa ‘yar kyakywan nan

ta zauna min daram a rai, tunda na taso ranar da

aka haifeki, na ganki kika zauna daram a

zuciyata, ban taba tunanin za a samu abunda zai

kuma shiga zuciyata ya zauna min irin haka ba,

sai gashi kin haifa min kyakyawan diyata da tafi

komai shiga zuciyata.

Zainab ta kalleshi cikin shagwaba tace, yanzu

yaya kafi sonta dani?

Yayi murmushi ya shafi fuskarta, yace ai ke

dabance zeeyta, kaunar danake miki bata da

misali, amma kinga bebyn nan tawa ma ta maye

ruhina gaba daya.

Zainab kin gama min komai da kika haifomin

bebyn nan, bani da bakin da zan miki godiya, bani

da abunda zan baki.

Babbar addu’a da zan miki Allah ya miki tukuici

da gidan Aljannah

amin yayana.

Bebyn ta dan motsa, ya balle marfin swan water,

ya tsiyayo kadan a kofin azurfa ya bata tasha.

Yace bata nononta tasha.

Yaya wallahi data kama jiya, baka ji zafi ba.

Yi hakuri ki bata a hankali zai daina zafin.

Zainab din taba bata tana cije baki

tare da cewar wash.

Lallabata yakeyi yana cewa, yi hakuri zeeyta,

tasha ta koshi, yauwa bata dayan.

Da haka babyn tasha ta koshi, ya karbeta ya

dorata a kafada, yana shafa bayanta har tayi

gyatsa taci gaba da baccinta.

Zainab ta dora kanta akan cikinsa, yana

tambayarta me da me take so ayi shagalin suna?

Suka jiyo karadin ni’ima da sadiya suna buga

kofa yace su shigo.

Suka shigo, sadiya tace yaya ka hade zeey din da

bebyn du ka rikesu anan ga jama’a ga jama’a

can sunata zuwa barka ba me jego ba beby.

Yace nifa bana son yawan daukan nan fa, saboda

shi yake kawowa yara ciwon jiki.

A fitar da kan gadonta falon a sakata a ciki, a

rufe da net din, du wanda yazo ganinta ya ringa

lekata kawai, a ganta haka basai sun dauka ba.

Ranar kwana hudu aka kawo kayan barka

akwatuna shidda uku na beby akwatuna uku na

mai jego fadan kayan da suke cikin akwatin bata

lokacine.

Mansura ta mike fuu tayi bangare Aliyu, ta banko

kofar dakinsa, babu sallama ta tsaya masa

tsegege aka, yana kwance akan gado yana

kallonta.

Tace Aliyu nagaji da wannan rashin adalci naka,

ni bazan iya zama ba, kana nuna min iyakacina,

ka dubi uban kaya daka jibgawa zainab da

jaririyarta, ni wallahi bazan yarda ba saide kome

zai faru ya faru,

ya daga mata hannu ki saurara kada kiyi min

hayaniya aka, fita ki bani waje.

Ta fito ta kwashi akwatunan daya bata ita da

Ahmad tasa aboot din motar da ya bata da

akwatunan ta tafi gidansu.

Mansura tana isa gida, tasa kannanta suka shigo

mata da akwatunan, iyayenta suna falo da saratu

da hauwa, suka tareta da lafiya?

Tace wallahi Alh na gaji da rashin adalcin

mutumin nan, ka dubi ‘yan kayan da ya bamu

nida Ahmad, amma ita ya hada mata akwatuna

shidda ita da ‘yarta kuma ya bata irin motar da

ya canja min.

Saratu ta bude kayan tana gani, super da holland

da les da material da shadda ganila ga takalma

jaka da sarkar gwal.

Akwatin Ahmad ma kananan kaya masu tsada,

sai shadda da boyel masu tsada sun sha aiki,

kala goma sha daya, ga takalma da huluna masu

kyau da tsada, harda glas mai ruwan gwal

suka gama gani, saratu ta rufe kayan, hajiya tace

mun gani Allah ya saka da alkhairi, ubangiji ya

kara buda masa.

Mansura tace, hajiya nifa na taho gida, ku kirashi

kuyi masa fada bazan iya zama da wannan

rashin adalcin nasa ba….

Kafin ta rufe bakinta Alh ya wanke mata fuska da

mari, hajiya ta rufeta da duka.

Dabbar yarinya mara hankali, dazunan ya

kawomin makullin mota sabuwa kar.

Ya aikowa da mahaifiyarki katon injin kankara

don ta rinka sana’a dashi shine kike kokarin

tozarta kanki, da yake bakisan abun arziki ba, to

du ranar da kika sake zuwa gidan nan kika

kawomin karar mijinki, saina karyaki, bare kuma

kiyo yaji, wannan kasheki zanyi murus har lahira.

Fita ki bani waje, ya biyota tayi waje da sauri,

kananta suka mayar mata da akwatunan cikin

mota, taja ta koma gida tana hawaye, fuskarta da

yatsun babanta daya mareta.

Tazo ta wuce ta babban falo tana kuka Aliyu

yana zaune yana kallo, ko kallonta baiyi ba, ta

wuce bangarenta.

Ranar suna aka sawa jaririyar sunan maman

zainab, suna kiranta da ihsan.

Taron suna yayi kyau angama lafiya aka watse.

Kyaututuka da zainab ta samu baza su lissafuba,

daga kawayenta, abokan Aliyu ‘yan uwa da

abokan arziki, kayan kamar a bude sito dashi.

Yaya ni’ima tace, kinsan kuwa yau shekarar ku

uku cif da aure da yaya. Shida yayi alkawari

saikin shekara uku sannan zai kusanceki, sai

gashi shekara uku tazo da ‘yar diyarku ko?

Zainab tace ke kika jiyo, ni ba ruwana.

Suka sa mata dariya.

*** *****

kwanci tashi rayuwa ta mika, zainab tuni sunyi

arba’in, harta koma abuja, taci gaba da

karatunta.

‘yar diyarta saida daddynta ya nema mata tsari

sosai, saboda kyan Ihsan du wanda ya bude baki,

sai yace hu! Wannan yarinyar da kyau take.

Ihsan watanta shidda kenan tayi ‘yar kubibi abun

sha’awa da ‘yan hakoranta biyu abakinta, tayi

sabo da Aliyu du sanda ya dawo gida, yana tare

da ita, don haka data ganshi tana bayan talatu

zata rinka zillo.

Ya karbeta ya rungumeta, yana murnar ganinta…

via # Abdul azeez muhammad

Ina ‘yan gidan nan kowa ya fito ya bani Happy

sallah nah

[8:05AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**8

Ya karbeta ya rungumeta, yana murnar ganinta,

yasata a gaban mota, yaita yawo da ita.

Tanada wata takwas ta fara takawa, dadi ya ishi

Aliyu, komai ya gani sai ya siyo wa ihsan.

Ihsan tana sanye da dan jeans din dogon wando

da ‘yar riga yalo ta dan kama mata jiki, anyi

mata indomie akanta, ansa mata kananan ribon

yalo. Da takalminta yarinyar tana ta kamshi, tana

tura ‘yar motarta a falon, tana binta.

Aliyu yayi sallama ta taho da gudu tana cewa

Abba! Har tana kokarin faduwa.

Ya sureta ya rungumeta ta Abba.

Zainab ta fito cikin kayataccen kwalliyarta ta

kananan kaya, ta sake komawa yarinya sharaf,

saboda hutu ya kara samuwa.

Ta taryeshi ta rungumesu gaba dayansu yana me

jin farin ciki, da nishadi a zuciyarsa.

Ta karbi jakansa ya zauna kan kujera yana

rungume da ihsan, zeey ta cire masa takalman

kafarsa da safa ta cire masa kakin jikinsa, ta

barshi daga shi sai ves da gajeren wando. Ihsan

tanata tsallenta a jikinshi. Zainab ta kai masa

kayansa dakinsa.

Ta dawo ta dauke ihsan, tare da cewa, daga Abba

yaje yayi wanka.

Ya shirya ya fito cikin kananan kaya suka nufi

tebir, sai da suka gama cin abinci suka nutsu,

suna kan kafet suna wasansu, Aliyu ya daure ido

da farin kyalle yana bin ihsan da rarrafe, tana

gudu tana dariya.

Zainab ta taboshi yayi saurin juyawa baya, yana

lalume zai kamata, ta zille dayan gefen tanayi

masa dariya.

Ta rankwafo gabansa taja masa hanci, tayi saurin

zillewa, yakai hannunsa bai kamata ba, zata gudu

yasa mata kafa ta fado kansa, yayi saurin shafa

kanta yauwa na kamaki. Tace “a wlh ban yarda

ba wayo kamin.

Ihsan ta fado kansu tana gwarancinta, gaba daya

suka sa dariya.

Ya bude idonsa duk suka zube kan kafet din suna

maida numfashi.

Tace Abban Ihsan, yace na’am maman Ihsan.

Tace don Allah tunda na gama diploma, kafin na

fara karatun digiri, muje gida kano mu huta, yaya

rabona da gidan tun bayan arba’in din Ihsan.

Wallahi inason zuwa gida.

Yace haba zainab du fa sati ina zuwa, kuma ina

gaya miki sakon gaisuwar da suke yi miki.

Ga waya kullum kunayi kuna hira dasu kuna jin

dadi, ko yaushe fa kuna tare dasu a waya.

Ta langabe masa tanayi masa magiya, Abban

Ihsan don Allah kayi hakuri ka amince mana

muje, wallahi suna son ganin Ihsan, sunce

hotunan ta baya gamsar dasu, yaya kada fa Ihsan

ta tashi bata san dangita ba.

Yace “I gaskiya hakane da wannan ku shirya

wannan satin zamuje tare.

Ta rungumeshi tana mai cike da murna da farin

ciki, nagode yaya Allah ya saka da alkhairi,

ubangiji ya kara maka budi da son zumunci.

Amin zeeyta.

Ranar da suka sauka ‘yan uwa sunyi farin ciki

sosai da ganinsu, kowa sai daukan Ihsan yake yi.

Ahmad ya rungumesu, yana cewa barka da zuwa

aunty mamina, nagode da kika kawomin ‘yar

uwata.

Ta shafa kansa Amadina naji dadi dana sameka

lafiya ka girma ka kara wayo da hankali.

Gidan nasu ya kasance kullum a cike saboda ‘yan

sanda zuwa.

Ranar da suka yi sati biyu da zuwa

sukayi wanka sukayi kwalliya ita da Ihsan, ta

shiga motarta ita da Ihsan da kanta tajasu zuwa

gidansu.

Ihsan tana da shekara biyu kenan, amma

wayonta da surutunta saika zata tayi shekara

hudu.

Ni’ima ce ta sake haihuwa, suna gidan sunan

Aliyu yayo wa zainab

waya, Ihsan tanata rigima ta hanata amsa wayar,

yanata yi mata fada wai ta shiga cikin jama’a da

ita zafi ya dameta.

Y kashe wayar mintuna kadan ya isa gidan

ni’ima, ya yowa zainab waya yace ta fito ta kawo

masa ‘yarsa.

Ihsan tana ganinsa ta rungumeshi, tana murna,

Abba ka daina tafiya kana barina in ban ganka ba

kuka zanta yi.

To na daina Ihsan dita, dake zan rinka zuwa ofis

ko?

Ta daga kai. Yauwa bebyna.

Yai tafiyarsa da Ihsan din sai mangariba ya koma

gida, Ihsan tana rungume a jikinsa tayi bacci.

Mansura tayi sallama, ta shigo ya amsa mata

sallamar yace ina Zainab?

Tace, kajika da wani zance, motata daban tata

daban zance taho mu tafi ne, tare dai muka fito

daga gidan ni’ima, ban san yanda akayi ba nura

tsohon saurayinta yasan ana suna, sai ganinsa

mukayi a zaune akan motarsa yana ganin zainab

ya kama washe baki, ta tsaya suna gaisawa

nikuma nayi tahowata.

Yayi wata irin zabura ya mike yana huci, dai-dai

lokacin da zainab din tayi sallama ta shigo, a

fusace yace mata daga ina kike?

Cikin sanyita tace yaya wace irin tambayace

wannan?

Kafin ta karasa maganan ya dauketa da mari,

tuni ta dafe kuncin nata, ta wani durkushe a kasa

saboda gigitaccen zafin marin.

Ya nunata da yatsa uban waye ya baki damar

tsayawa da nura, har ku gaisa dashi?

Kanta yana sunkuye, tana jin haka da sauri ta

dago kanta ta kalli mansura, tace aunty kiji

tsoron Allah, wai me na tare miki a doron kasa ne

kike so kiga kinsani bala’i?

Ya kamata ku sani wannan duniyar ba matabbata

bace.

Aunty idan kin kashe aurena da yaya me kikayi

tunda dai kinsan dole a gabanku zanci gaba da

zama, har lokacin da zangama idda na samu

wani mijn da zan aura, kuma duk matsalar data

faru dani dole ku zan kwaso na gayawa.

Aunty duk matan arziki bazata bari mijinta yayi

fushi da ita ba, ni gashi kinsa ran nawa mijin ya

baci dani, yana fushi dani alhalin bada hakkina

ba.

Via #Justice_Hamzat

[8:05AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**9

kiyi hakuri aunty, gaba kike dani, kuma ke

auntyna ce, bazan taba bari wani batanci ya

shiga tsakaninmu ba, amma dan Allah ki rinka jan

mutuncinki da girmanki.

Tace, yaya kayi hakuri, amma ban aikata abunda

kake zargina dashi ba, rabona da nura tun ranar

da ka koreshi, ko labarinsa ban sake jiba bare na

ganshi.

Ta mike tsaye zata nufi dakinta jiri ya kwasheta,

tayi baya zata fadi, Aliyu yayi saurin tareta ta

fado hannunsa, ta shide, numfashinta ya dauke a

gigice sukayi asibiti,

saida likitoci sukayi ta gwaje-gwajensu, suka jona

mata karin ruwa ta farfado, sai dai takoma bacci.

Mansura kukan nadama takeyi, tana bawa Aliyu

hakuri, shi bakin cikin marin da yayiwa zainab yafi

komai daga masa hankali.

Likita ya shigo yace, yallabai saika kula da

madam sosai, ka daina bata mata rai, don tana

da karamin ciki na wata biyu a jikinta.

Wani irin farin ciki ne ya lullube zuciyar Aliyu, ya

rinka dariya yana nuna farin ciki da godiya ga

Allah.

Mansura ta rinka mamakin irin farin cikin da yake

yi, wai yana son haihuwa haka amma bai hanata

planin din data keyi ba, du da dai bashi yasa ta

tayi ba.

Amma ai wataran yana ji tayi waya asibiti, tace

zato zo allura, bai ce mata komai ba, to me yake

nufi da itane, ko bai dauketa wata tsiya ba?

Tayi waje da saurinta, ta zaro wayarta ta bugawa

yayarta saratu

tana dauka tace, hello kinji yarinyar nan ciki ne da

ita, kinga murnar da Aliyu yake yi kamar wanda

akayiwa bushara da gidan Aljanna, yanzu dama

mutumin nan yana son haihuwa ya barni inata

faman planin.

Au dama planin Aliyu ya saki kiyi shiyasa baki

sake haihuwa ba tsawon lokaci?

Tace wlh yaya saratu gaskiya ba Aliyu ne ya

saniba, don na taba gaya masa zanyi tsarin iyali,

yace ba ruwansa, kuma bada yawunsa ba, idan

kuma nayi bai yafe ba.

Ni kuma naga shi dan gayu, ga son ya huta, sai

nake ga kamar tara ‘ya’ya zai iya zame masa

matsala, yaga baya samun yanda yake so

watarana yayo min kishiya, sai duk da haka ban

tsira ba. Amma tunda naji labarin zainab tana da

cikin Ihsan, na daina planin din, amma gashi

harta haihu ta kuma samun wani cikin, ni kuma

ba labari.

Saratu ta daka mata tsawa tare da cewa, ke kika

yiwa kanki, kin cuci kanki abanza a wofi.

Ga dukiya nan yana samu kamar kasa, ita kuma

taita tara masa ‘ya’ya kya zama ‘yar kallo ai,

yanzu ma ya fara baki kujerar makka biyar, kin

kawowa Alh, to gaba muka san me zaiyi mana,

bare ace kin cika gidan da ‘ya’ya, ni bazan iya

sauraran takaicinki ba sai anjima.

Ta kashe wayar.

Mansura ta dawo dakin a sanyaye da ita.

Zainab ta farka Aliyu yace sannu zeeyta.

Ta dago kanta cikin sanyita tace yaya kayi hakuri

dan Allah ka yafemin, wallahi ba wani namiji dana

gaisa dashi.

Kayi hakuri yaya zuciyarka ta huce.

Ya shafa kanta zainab ki daina tuna wannan

magana dakin san yanda raina ya rinka suya da

tukukin bakin ciki, ina tuna ni na mareki da

wannan hannun nawa

sai nake tunanin irin hukuncin da zanyiwa hannun

ko zuciyata ta huce.

Zainab nayi abunda Allah ya hana, yanke hukunci

cikin fushi.

Zainab ba laifina bane, shirin mansura ne kawai

don ta bataki awajena.

Kiyi hakuri zeeyta.

Tayi saurin sa hannu ta toshe masa baki tana

murmushi, don Allah yaya ka daina bani hakuri,

wlh na yafe maka, ka gayawa aunty ma na yafe

mata.

Babban jin dadi na da zuciyarka ta huce, bakayi

fushi dani ba.

Zainab jiyan ma bacin raine da zafin kishinki, wai

har na mareki.

Tace don Allah yaya kadaina tuna zancen marin

nan, kaifa yayana ne, kayi min marin ne a

matsayinka na wana, ba miji ba ko yayana?

Mansura tana tsaye a gefe daya tayi shiru tana

jinsu. Aliyu kamar baisan tana wajenba, bare

zainab da bata san tana nan ba.

Zainab tace, dan Allah yaya kayi hakuri kada

kayiwa aunty wani abu, kasan dan adam ajizine,

kowa zai iya kuskure kayi hakuri yaya ka yafe

mata.

Ya daga kai shikenan naji na yafe mata, mansura

kawai saita juya ta fita daga dakin.

Likita ya rubuta musu maganguna na karin jini da

lafiyar dan tayin cikinta.

A daren suka dawo gida wani irin tattalin so da

sabuwar kulawa da yakeyi, kamar zai mayar da

ita ciki

ita kuma sai sangarta take zuba mai da

shagwaba ga cikin nata mai tsurfa ne du

daurewar data keyi, amma abu kankani sai ya

daga mata hankali yasata amai.

Hankalin Aliyu ya kasa nemansa akeyi awajen

aikinsa, ga zeey dinshi bata cika lafiya ba.

Amma dole ya dauketa su tafi Abujan, ta karasa

warware wa acan.

Yace wa zainab ki hada abunda zaki tafi dashi

don jibi litinin zamu tafi.

Yana fita yayi bangaren mansura, yace mata kiyi

lis din du abunda zaku bukata, don jibi zamu

koma abuja.

Tace, kaida wa?

Yace dawa muke tafiya?

Tace, kana nufin wai da zainab din zaka kuma

tafiya ne?

Yace ya wuce wai.

Ta mike tsaye tana tafa hannu, to wlh abunda

bazai taba yuwuwa ba kenan, na gaji da yi muku

gadin gida wlh, wlh bazan zauna ba, na gaji da

rashin adalcinka, ka rinka kwasar wadanda kake

so kuna tafiya.

Ya daga mata hannu, tare da cewa ya isheni,

kada ki kawomin maganar banza, haka nayi niyya

baki isa ki canjani ba.

Ya fice ya doka mata kofar, ta tabe baki dan

rainin hankali zaka gane kurenka.

Via #Justice_Hamzat

[8:07AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**10

Dan rainin hankali zaka gane kurenka, tauraruwar

taka dole ka barta, ko kuma ka tafi damu gaba

daya, don wlh bazan zauna ba, sai na bika.

A bangarenta ya kwana da safe ya sake yi mata

maganar ta bada lis din abunda zasu bukata.

Tace masa saidai ka nemi lis a wajen zainab, don

ni kaga akwatuna na can nagama shirin binka.

Ya daka mata tsawa ke baki isa ki raina min

hankali ba.

Ga cek nan ki rubuta abunda kike bukata a karbo

miki a banki, idan kinga zaki zauna ki zauna, idan

kinga bazaki zauna ba to ki tafi gidanku.

Ta dafe kirji ni zaka yiwa wannan wulakancin

Aliyu?

Ko kallonta baiyi ba ya fice ya bata waje, tana jin

fitarsa itama ta shirya ta fice, gidansu Aliyu.

Da suka gaisa da umma, sai tayi bangaren ummi

ta gaisheta, sannan ta shiga bangaren su zainab,

ta gaisar da maman sannan tace mata, don Allah

daddyn zainab yana nan?

Mama tace “I yana ciki.

Tace don Allah mama inason magana dashi.

Tace, to bari nayo masa magana.

Ta mike shiga bangarensa ta gaya masa.

Yace mansuran ta shigo, mansura ta rissuna ta

gaisheshi, saita fashe da kuka daddy yace, lafiya

menene, me suka yi miki, wani abu ne ya faru?

Tace daddy wai dan Allah Aliyu yace zasu koma

abuja da zainab, sai nace ya rinka kwatanta

adalci a tsakaninmu, mu ma yaje damu abujan

nan, shine ya hauni da fada wai bazamuje ba,

anan yaga damar ajiyemu, in zan zauna na zauna,

in bazan zauna ba na fice na tafi gidanmu.

Dady yace subhanallahi, me yayi zafi haka? To

kiyi hakuri ki koma gida kici gaba da shirinki, zai

tafi daku kinji.

Tace to dady nagode Allah ya saka da Alheri.

Yace bakomai tashi ki koma gida.

Ta fito tayi musu sallama ta koma gida.

Dady yayi waya ya kira Aliyu, ya zo da saurinsa,

yace dady gani.

Bayan sun gaisa, yace haba Aliyu

kaifa yaro ne, amma me halin manyan mutane.

Haba Aliyu kada rudin duniya ya debeka, ka

kaucewa fadin Allah, kazo kana fadawa halaka.

Yata masa nasiha daga karshe yace to yanzu

tunda bata amince ba, to an shiga hakkinta, don

haka ka tafi da mansura abuja ka bar zainab

anan kano.

Aliyu ransa ya baci wato mansura kararsa ta

kawo kuma tasan inda bai isa yayi musu ba.

Yace to dady na tafi da itan.

Yace yauwa ko kaifa dana, nagode.

Aliyu ya taho gida ransa a bace saboda abunda

mansura tayi masa.

Magoronsa ya rinka daci na tukukin bacin rai, sai

yaji zazzabi yana neman rufeshi.

Ya shiga falon zainab ya zauna ya zuba tagumi

zainab ta fito daga kicin ta ganshi, ta karaso

gabansa da sauri tace lafiya yayana, meya faru,

meya sameka kayi tagumi?

Tasa hannunta ta cire mishi tagumin, ya akayi

yayana menene?

Ya danyi tsaki yace bana jin dadin jikina, ina jin

dan zazzabi ajikin nawa. Oh! Sorry yayana sannu,

ta dafashi tana lallaminsa kamar yaro.

A hankali ta zame masa kayan jikinsa, daga shi

sai gajeren wando.

Ta shiga kicin ta kawo mishi ruwa mai sanyi, da

lemu ta zuba a kofi tasa masa a bakinsa kadan

ya iya sha saboda bacin rai.

Ta debo ruwa a tasa ta dauko karamin tawul tazo

ta rinka dangwalar ruwan tana daddana masa

ajikinsa, yana lumshe ido a hankali ya fara jin

yana watsatsakewa, saida taji jikinsa ya huce

daga dumin, sannan ta bashi magani yasha.

Ya kishingida akan kujera, ta rinka yi masa tausa,

sannu a hankali yana lumshe ido tare da cewar

wash.

Bacci mai dadi ya ringa fisgarsa, ya kwantar da

zainab ajikinsa ya rungumeta, bacci ya daukesu a

haka.

50 min suka kwashe suna bacci, a haka zainab ce

ta fara farkawa, ta runkura a hankali zata zame

tabar jikinsa, ya kara kankameta, ya bude ido ya

sumbaci lebenta, dariya, yayana ka farka.

Tunda zaki bar jikina ai dole na farka.

Yaya lokacin sallah yayi hudu saura.

Ya mike da sauri, ta shiga toilet ta hada masa

ruwan wanka, ya shiga yayi wankansa a nitse ya

fito zuciyarsa wasai, ya manta da wani bacin ran

mansura, yayi saurin sa kaya ya fita masallaci

don sallar la’asar.

Lokacin daya dawo daga masallaci ya tar zainab

ta canja masa shiga ta kananan kaya, irin shigar

da yake so.

Ta tare shi tana murmushi, ta riko hannunsa suka

wuce tebir don cin abinci.

Ta rinka tattalinsa, tana bashi abinci abaki, sai

kace yaron goye.

Suna ci cikin nishadi da faranta ran juna, sai

santi yake zuba mata, yana sata kyalkyala dariya.

Tasa shi cikin farin ciki da walwala

kwata2 ya manta da bacin rai da mansura ta

dasa masa.

Ya dauki waya bari na bugawa ni’ima ta kawo

min Ihsan dita, bana jin dadi idan bana jin

karadin bebyna.

Zainab ta rike wayar don Allah yaya ka bari, tace

saida daddare idan zasu zo yi mana sallama zasu

taho tare.

Yayi wani dif saboda yanda zuciyarsa ta buga da

ya tuno fa bada zeey dinshi zai tafi ba.

Gashi du ta hada kayansu da abunda tasan

zatayi amfani dasu.

Ta kula da halin da yake ciki, tace wayyo yaya

don Allah kayi hakuri idan ranka ne ya baci bari

na tura direba ya dauko maka ihsan din kaji

yayana.

Ta mike ya riko hannunta dawo ki zauna, ba fushi

nayi ba, dani da ni’ima ai duk daya ne.

Tace to meye yayana nafa duk ka canja?

Yace kiyi hakuri zainab bada ke zan tafi abuja ba.

Ta dafe kirji yaya me nayi maka, saboda me

bazaka tafi dani ba?

Ya kwanto da ita jikinsa.

Via #Justice_Hamzat

[8:08AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**11

Ya kwanto da ita jikinsa yana rarrashinta, kiyi

hakuri zainab ba a son raina ba, mansura ce ta

kai karata wajen dady yace na tafi da ita.

Tace shikenan yaya, saikun dawo Allah ya kiyaye

hanya.

Ta mike tayi cikin dakinta ta kwanta tana

hawaye.

Ya taso ya biyota, ya dagota “zeeyta menene

fushi kika yi? Kiyi hakuri nasan dole ranki ya baci,

amma ni nafiki cutuwa da rashinki kusa dani.

Zainab kici gaba da shirinki, saimu tafi gaba

daya, kinji.

Ta tashi tace haba yaya ya zanki jin maganar

mahaifana?

Dady abunda ya fada gaskiya ne, hakan shine

adalci yaya kuje Allah ya kaiku lafiya, zan tayi

muku addu’a daga nan.

Ta tashi ta shiga toilet shiru-shiru yana jiranta

bata fito ba, ya dafe kansa tabbas yasan zeey

dinshi fushi tayi, ya tashi ya fita daga dakin.

Lokacin ni’ima da sadiya suka zo musu sallama,

sannan Aliyu baya nan, zainab bata gaya musu

cewar ba tare da ita za a tafi ba.

Sai goman dare suka tafi, sunyi mamakin rashin

dawowan yayan nasu gida da wuri.

Sha daya na dare zainab ta kasa bacci, tana

tunanin ina Aliyu ya shiga ne?

Tayo alwala ta shimfida dadduma tana sallar

nafila, tana addu’a Allah ya bata hakurin jure

rashin mijinta kusa da ita.

Ya kuma hade kansu da mijinta da kuma abokiyar

zamanta, ya kuma kare su daga sharrin

mahassada da makiya.

Ihsan ta farka da kukanta tana kiran dadynta,

bata ganshi yau ba ta taso ta kwanta abayan

zainab tana kuka, tana cewa aunty mami ina

Abba na, ki kaini wajen Abba kinji aunty mami.

Zainab tana kan addu’a tana hawaye tana jin

ihsan a kwance a bayanta tana kuka.

Ya dade da shigowa yana tsaye yana kallonsu,

tsananin tausayinsu ya gallabi zuciyarsa.

A hankali yae ya durkusa a gaban ihsan ya shafa

kanta, ta dago ta ganshi, ta fada jikinsa tana

dariya

Abba na ina ka tafi ka bani?

Ya rungumeta sosai yarinya ta rinka ajiyar zuciya

ya rinka shafa kanta.

Tayi lamo a jikinsa har tayi bacci ya shimfideta

ya dawo wajen zainab.

Yace yanzu zainab haka zakiyi min kiki sakin

ranki ku rinka shiga kunci keda ihsan.

Keda zaki rarrasheta amma ke kina kuka ita

tanayi, a haka kike so na tafi na barku, taya

zuciyata zata samu nutsuwa, bayan nasan bakwa

cikin kwanciyar hankali.

Kayi hakuri yaya wlh ni ba haka bne, ni abunda

ya daga min hankali naga har sha dayan dare

baka dawo bane, yaya ba dole na damu ba?

Yaya ina kaje ka kai sha daya baka dawo ba?

Yayi murmushi yace ina zanje kuwa, ai kinsan

bazan iya fita wani waje a wannan lokacin ba, ina

falon saukar baki muna lissafi da su sadik yanzu

nan suka tafi.

Tayi murmushi ya kamo hannunta zo muje na

kwanta kada na makara.

Da safe ya fito falo shida zainab yana dauke da

ihsan, sunci kwalliya kamar masu shirin zuwa fati,

sunata murmushi da fara’a ke ba kyace da wani

kunci a ransu ba

mansura suka shigo falon ita da Ahmada sunci

kwalliya tana taunar cingam, Ahmad yayo wajen

zainab yana cewa aunty mami mu tafi gaba daya.

Ta shafa kansa kada ka damu yarona idan mun

gama shirinmu zamu biyoku, inkaje ka kula da

karatunka, kaga za a canja maka makaranta

saika kula sosai.

Yace to aunty mami naji.

Mansura ta kallesu ta tabe baki, takaicinsu da

bakin cikinsu ya isheta, wato du yanda taso ta

kuntatawa zainab donta ga bacin ranta, yarinyar

taki nuna damuwarta.

Har mota ta rakosu, Aliyu ya mikowa zainab

ihsan ta karbeta, ya shiga motar suna daga musu

hannu, direba ya fara jan motar tana tafiya, Ihsan

ta kwala wata gigitaccen kuka tana zamewa daga

jikin zainab.

Motar tana kokarin fita daga get Aliyu yacewa

direba ya tsaya, ya fito da sauri ya karbi ihsan ya

rungumeta, ta rinka cewa Abba jani.

Yaya to ku tafi da talatu, ta taho da ita.

To shikenan turo talatun.

So kuyi hkr wllh banda lpia ne

[8:08AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**12

To shikenn turo talatun. Ta shige gida da sauri

talatu ta fito ta shige gaban mota kusa da direba,

ihsan na kwance jikin babanta, yana lallashinta

Ahmad yana tsunkuninta suna dariya.

Mansura takaici ya cikata, wai me zainab take

yiwa Aliyu ne da yake musu irin wannan kauna?

Kafin su karasa airprt Ihsan har tayi bacci. Suna

fitowa daga mota talatu ta karbeta, ta koma

motar direba yasu suka tafi.

Mansura kanta ya kwance da ganin gidansu na

abuja, du da dai na kano da suke ciki yafi shi

girma da kyau, amma tsarin wannan din ya

burgeta sosai, kamar gidan turawa.

Tuni Aliyu ya fice cikin sauri ya nufi ofis. Mansura

da Ahmad sun zagaye ko ina, bangare daya ne a

kulle, ta tabbatar wajen zainab ne, tunda bai bude

musu ba.

Sai dare Aliyu ya dawo abun haushi ga yunwa ga

wahala, amma yana zuwa ya tarar da mansura da

Ahmad du sunyi yaushi, wai yunwa suke ji basu

ci komai ba.

Ya hauta da fada dan me ga kayan abinci nan

bata girka ba? Tace ai babu gas kuma ta masa

waya taji ta a rufe.

Yace baki bude jakunan da akwatina da muka zo

dasu kin jere kayan ba?

Tace ai bata yi komaiba, yayi tsaki matsalarki

kenan har yau baki san yanda zaki kula dani ba.

Ya tashi da kanshi ya bude kayan ya fito da

soye-soyen da zeey ta musu, dambun nama, kec,

meat fy, samosa, cin-cin da wainar shinkafa, da

sinasir da fukasau da soyayyen miya.

Kawai sai mansura tayi turus, lallai zainab tayi

nisa wajen siye zuciyar Aliyu, ita yaushe tayi

tunanin haka ma bare tayi, abu daya tasan tana

da yaji.

Aliyu yasa Ahmad ya shiga kicin ya dauko filet da

cokala, ya bawa Ahmad shima ya diba. Yaja gefe

ya fara ci, yace wa mansura ki debi abunda zaki

iya ci, ki zuba ragowar a firij. Ki debo mana ruwa

da lemu tunda komai sai ance kiyi.

Ta zumbura baki, ta tashi tayi yanda yace, ta

zuba nata abincin ta zauna tana ci.

**** ***** ****

zainab ta shiga damuwa sosai, na rashin

tafiyarta, tana son zaman kano saboda iyayensu

da ‘yan uwansu.

Amma gaskiya tafi son zaman abuja, saboda tafi

kusa da mijinta, tasan halinshi tasan damuwarsa.

Tasan yayanta mai son a kula dashine wajen

cikinsa da biya masa bukatarsa to tasan

auntynta tun tana ita kadai ta riga tayi sakaci da

hakan.

Ta kalli Ihsan data gama rigimar neman abbanta

tayi bacci. Ta mike ta shiga toilet ta dauro alwala

tazo ta kama nafila tana musu addu’ar neman

zaman lafiya a tsakaninsu da cikawa da imani.

Tana shafa taji nutsuwa ta saukar mata, taji

zuciyarta wasai, babu kunci ko damuwa.

Tahau gadonta ta kwanta, wayarta kamar jira

take tahau burari, ta dauka da murmushinta, tace

“hello gudan raina, ya kake? Ina auntyna da

dana?

Yayi wata irin sanyanyar ajiyar zuciya, yace

rayuwata ina Ihsan dina tayi bacci kota nata

rigimar nemana?

Um-um ta hakura tayi bacci.

To saka min naji munsharinta don na tabbatar da

lafiyanta.

Tasa a wayar a hancin Ihsan, yaji numfashinta

yana sauka a hankalo, tasa a kunanta kaji ko?

Um Alhdllh naji bebyna kalau take. To ya dan

bebyna baya tare da matsala ko?

Kinsan tunda nayo miki waya mun sauka, to tun

daga lokacin ban samu kaina ba sai bay isha

inata aiki.

Cikin tausayawa tace, wayyo yayana, ka wahala,

sannu yayana, koda yake ai ka huce gajiyar yanzu

dan nasa aunty ta gasa ma jikinka da ruwan zafi,

kuma tayi maka tausa, nasan gajiya ta gudu sai

wacce zaka sake dauka yanzu ko yaya?

Yace, don kinga bana kusa kika samu bakin gaya

min haka ko?

To bashi du ranar dana dawo na ware gajiyar

akanki.

Tasa dariya tace yaya kayi hakuri bazan kuma ba

kaji?

Yace nasan ranki ya baci sosai rashin tahowarmu

tare.

Amma don ki kwantar min da hankali kika dake,

kika nuna min bakomai kina goyon bayan nayi

adalci a tsakaninku, don kina so ranar lahira na

tashi cikin maza salihai, masu adalci a tsakanin

matayensu, baki nuna son zuciya ba.

Tace yaya dare fa yayi, kada mu shiga hakkin

auntyna, yaya saida safe. To Allah ya tashemu

zeeyta.

Kwana hudu ranar jumma’a da azahar ya baro

ofis ya taho yayi shiri, ya taho kano.

Zainab kuwa tana cike da doki anata yi masa

girke-girke da soye2 da lemuka.

Taci kwalliyarta ita da Ihsan.

Ihsan tana cikin ‘yar shimin riga ruwan hoda me

adon les, a kirjin da hannun rigar sai dan jeans ga

dan takalminta me madauri kasansa na glass,

yarinyar tayi kyau matuka.

Tanata tsalle2 ta acikin motarta a harabar gidan,

motar Aliyu ta shigo yana ganin Ihsan yaji

zuciyarsa ta cika da farin ciki da annashuwa

direban bai gama tsayawaba da motar ya bude

ya fito da saurinsa Ihsan tana ganinsa ta kama

dariya, tana dago masa hannu da cewar Abbana!

Abbana ya dauketa ya kankame yana murna, ya

jiyo da daddan kamshi sahibar tasa ya daga kai

yana kallonta tana masa murmushi, ya dago

mata hannu ta taho ta shige jikinsa, suna dariya

yayi mata kyakyawar runguma yasa hannunsa a

mararta, ya rada mata a kunanta ya bebyna?

Ta rangwadar da kai lafiyarsa lau sai maraicin

Abbansa da yayi.

Ya rada mata ai gani nazo zamu kasance dashi

na tsawon awa biyar.

Ta kwace jikinta tana dariya, “a nifa yaya ba haka

nake nufi ba.

Yace ai kin manta da bashina da kika ci ta waya?

Tasa dariya niba ruwana.

[8:09AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**13

Tasa dariya nidai ba ruwan ga ‘yarka nan me

shegen wayo tana jinka.

Ya sumbaceta yace Ihsan din Abba

yarinyar tayi dariyarta tace Abban Ihsan, gaba

daya suka sa dariya suka fada cikin gida yana

rungume da iyalansa.

Suka zube a falo,

ina Amadina.

Yana can ya fara zuwa makaranta yau.

Ta rinka cire zare masa kayn jikinsa ta barshi

daga shi sai gjrn wando taja hannunshi zuwa

toile inda ta hada masa ruwan wanka.

Yana fitowa ta tareshi da tawul ta goge masa

ruwan jikinsa, ta shiryashi kamar karamin yaro, ta

rikoshi zuwa tebir.

Yana cin abincin yana zuba mata santi, zainab

kici gaba da tallafin rayuwata, kina min tattalin

so, kada ki barni naje kasa don kece farin cikin

rayuwata.

Ta taso da sauri ta rungumeshi, ta hada bakinta

da nasa, tana yi masa hot kiss da ya rikitashi,

yake kokarin mantar dashi a wacce jiha yake.

Ta cika shi tasa bakinta daidai kunnensa, i luv u

yayana, i care 4 u, life iz gud.

Ta rikitashi da kalamanta inda ita kuma ya

rikitata da soyayyarsa, tuni ya manta da batun

cewar abinci fa yake ci a falo.

Sai da ya samu nutsuwa shi kadai ya rinka yiwa

kansa dariya, zainab kuma abun ya bata kunya.

Ta fada dakinta ta shiga toilet, shima dakinsa ya

shiga ya fada toilet.

*** *** *****

Rayuwa mai dadi zainab tana zamanta cikin

kwanciyar hankali, bata da damuwar komai tana

cikin danginta da ‘yan uwanta, kowa yaso ganinta

zai zo gidanta su wuni suna hira, amma ita bata

fita ko ina, sai dai in fitar ce ta kama dole.

Sai dai in Aliyu yazo du inda take son zuwa zasu

je tare.

Mansura kuma tana abuja, amma du abun duniya

ya isheta, saboda bata saba da zaman kadaici

ba.

Ahmad in ya fice tun safe ya tafi makaranta sai

yamma zai dawo.

Haka Aliyu tun safe zai fice ofis sai dare zai dawo

da ya gama abunda yake yi bacci zaiyi don

gudun kada ya makara.

Bata da lokaci na samun hira dashi

ko magana dashi, gashi ba wanda ta sani, kuma

baya barinta fita ko ina.

Kokari me aiki tazo tayi mata gama abunda take

yi ta fice.

Abun duniya ya isheta, bata da wani aikin yi sai

kallo, sai dai idan ta gaji ta kwanta ta dauki waya

ta bugawa iyayenta da ‘yan uwanta.

Da abokanan arziki suyi ta hira dasu.

Take gayawa yayarta saratu matsalarta dake

damunta, kawai inba babu dama kice ya dawo

dake gida, ba gwanda zaman ki acikin dangi da

‘yan uwa ba.

Ko wani abune ma ai inkin ga danginki kyaji

sauki.

Tce to bari inya dawo daga ofis nayi masa

maganar zuwana tunda gobe jumma’a zai zo to

sai anjima kya bugo naji yanda kuka yi dashi

sukayi sallama kowacce ta ajiye.

Karfe takwas na dare Aliyu ya shigo saida ya

kammala du abunda zaiyi ya zauna.

Tace Aliyu.

Yace um hum, inajinki.

Tace gobe inaso in bika naje gida.

Yayi mata wani irin kallo, yace zancen ne baki

gaji dayi ba.

Na gaya miki keda gida ba yanzu ba.

Tasa kuka, wannan wane irin al’amarine, kai baka

da lokacin da zaka zauna a gida Ahmad sai

yamm yake dawowa,

ana biki ana suna da mutuwa amma bazaka kaini

naga gida ba?

Yace itama wacce kike kishi da ita tana nan din

kika bambareta ke kika dawo, itama haka take

zaune.

Kuma baki ga ina yawan kaita gida ba, saita

shekara, don haka wlh kema saikin shekara

sannan zakije gida.

Ta dora masa hannu aka ta kurma masa ihu

wayyo na shiga uku, baya son jin kukan dan haka

ya tashi daga falon ya koma daki ya kwanta.

Ta zauna a falo taci kuka saida ta gaji dan kanta

tayi shiru.

Ta tashi ta koma dakin ta rabe kusa dashi ta

kwanta, tana ajiyar zuciya ya jawota jikinsa, baki

daina kukan nan kina so kanki yazo yana ciwo

ko?

Tace ko meye ai kaika jawo min, nagane bansan

abunda yasa baka kaunta ba, iya bakin kokari dai

inayi maka don na kyautata maka, kuma kai baka

so kasani farin ciki, kafi so kaita ganin raina a

bace.

Yace mansura inkika fadi haka bakimi adalci ba,

tun kafi na auri zainab naso na mayar dake

kaduna wajen aikina, kika nuna min baki da

ra’ayi, ashe don na dawo da zainab wajen da

nake aiki har kyace nayi miki rashin adalci?

Kika je kika hadani da kawuna, wanda shine

mahaifin yarinyar nan, ya rinka min fada akan

bana miki adalci. Yasa aka bar jikarsa da ‘yarsa

aka taho daku.

Makarantar Ahmad mai tsada yaron nan yana

ganewa, kika sa aka rabashi da makarantar, aka

canja masa wata, gashi nan saida suka maidashi

baya, saboda karatun nasu ba iri daya bane.

Sannan yanzu kuma kice min zaki koma kano ki

rinka min wasa da makarantar yaro, ni da ke

waye mijin? Ko ina tsoronki ne, bare a fara cemin

mijinta ce?

Don haka keda zuwa gida saikin shekara, anwa

suma Ahmad hutun shekara. Se kuje.

*** *** ***

Ranar wata jumma’a yake ce mata mansura zan

kai tsawon sati uku fa a gida ban dawo ba.

Ta dafe kirji saboda me?

Yace. Lokacin da sakanni din cikin zainab ya

nuna ya kusa, kinga dole na zauna kusa da ita,

don kada haihuwar tazo mata bakowa

tayi masa wani irin kallo saboda in haihuwar tazo

kai zaka cire mata ciwon?

To wllh bazan dauki wannan rashin adalcin ba.

Ko mu tafi tare ko kuwa kayi kwana ukun ka ka

dawo.

Ya daka mata tsawa, ki rinka sanin irin kalmar da

zaki fadamin, ko kuma zan bar matana da tsohon

ciki ne kullum ina farga bar halin data..

[8:09AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**14

Kina tunanin zan bar matana ne da tsohon ciki,

nazo na zauna anan kullum ina fargabar halin

data ke ciki? Kinyi kuskure nasan darajar da, da

haihuwa, bazan iya kwatanta miki yanda nake

kaunar ‘ya’ya ba, ya’ya na daban suke a

zuciyata. Ki kiyaye abunda kika san zai tabamin

‘ya’yana, koda harara ce wllh saina dauki

mummunan mataki akai, ya fice ya barta.

*** **** ****

Ranar talata, ranar kwanan Aliyu hudu a kano,

cikin dare zainab tana rungume a jikin Aliyu yana

lallabata.

Cikin baccin taji an mintsineta, ta farka firgigit,

tana salati Aliyu ya mike a rude, yana tayata

salatin, saida suka kai karshe sannan yace mata

menene zainab?

Yaya ciwo, Abban Ihsan wayyo ka taimakamin, ya

rungumeta yana rarrashinta, tare da lailaya mata

bayanta, tare da busa iska kadan2 a kunnenta har

bacci ya dauketa, ya shimfideta yasa kayansa da

sauri ya fito mata da nata kayan.

Ya dauki Ihsan ya kaiwa talatu ita.

Yana dawowa dakin ya samu zainab ta farka da

wani azababben ciwo tana ta murkususu.

Yayi saurin rungumeta sannu zeeyta, ya salube

mata rigar baccin yasa mata kayanta, ya dauketa

zuwa mota.

Da kyar suka karasa asibiti, tana ta salati tana

murkususu, gashi tana jikinsa ya lafe da hannu

daya.

Suna isa asibiti likitoci suka karbeta, mintuna

goma sha biyar da shiganta dakin kukan beby ya

cikawa Aliyu kunne, wani farin ciki da murna suka

baibaye shi.

Ya daga hannu sama yana tayiwa Allah godiya,

saiya ga hakan ma baiyi masa ba, yayi alwala ya

shiga masallacin asibitin yayi nafila raka’a biyu ta

nuna godiyarsa ga ubangiji.

Ya nufi dakin da zainab take, sun gama gyarata

ita da jaririn fes dasu, kamar ba ita ta haihu ba.

Ya karaso da fara’arsa, sannu zeeyta Allah yayi

miki albarka, nagode zainab, ya dauki jaririn fari

sol dashi ya rungume dan yana jin wata irin

kaunarsa tana ratsa shi.

Yace zainab yanzu wannan yaron ma nawa ne?

Zainab nagode, kin kawomin Alheri cikin gida, kin

sadani da farin ciki mara yankewa

zainab ‘ya’ya rahama ne, inason ‘ya’ya da yawa,

zeeyta ki daure kita haifo min kinji?

Ya shafi kanta.

Tace yaya haihu ta uku, amma sai sambatu kake

yi, kamar wanda bai taba yi ba?

Yace, zeeyta kin san kuwa yanda nake son

haihuwa? Inaso naga na tara ‘ya’ya da yawa,

naga na hada family kamar mutum guda arba’in

ace du nawa ne.

Ta bude baki, A yaya arba’in fa kace kana

sha’awar kara aure kenan?

Yace um-um du ke zaki haifamin da auntynki.

Tayi dariya yaya ai sunyi yawa, ba zamu iyaba.

Zaku iya tunda kuna tare da gwarzon namiji.

Ya dauki waya ya buga gida, karfe uku na dare ya

fada musu albishir din haihuwa.

Da sha daya na safe aka sallamo su ta taho gida

da tawagar ‘yan uwanta.

Saida suka dawo gida Aliyu yayiwa mansura

waya, yake gaya mata zainab ta haihu a daren

jiya

tace “me kuma ta haifa?

Yace kyakyawan , sankacecen dana fari kal dashi

me kama dani sak dana miji.

Gabanta yayi wata irin mummunan faduwa,

dakyar ta iya cewa Allah ya raya.

Suna gama wayar, ta bugara yayarta saratu, take

gaya mata abunda ya faru, tace kin gani kin cuci

kanki da yanzu kina da ‘ya’ya hudu ko biyar dole

du abunda zata haifa a bayan naki suke, yanzu

kuwa fa ba gashi harta fiki ba?

Tace na shiga uku yanzu ni ya zanyi, kina gani a

abujan ma nayi ziyartar asibiti yafi guda nawa,

likita yace mahaifata normal ba abunda ya

sameta, a shirye take ko yaushe zan iya daukan

ciki.

Amma har yanzu shiru babu labari.

Kedai ki samu ki lallaba shi ya barki zuwa sunan

nan, sai musan abunda za muyi akai, don dole

sai an hada da rokon Allah.

Ranar kwana biyu da haihuwar tayiwa Aliyu waya

tace zasu zo wajen suna.

Yace a’a aina gaya miki sai kun shekara zaku zo

dan bazan yarda ki cutar min da ki rinka yi masa

wasa da karatu ba.

Tasa masa kuka, ni gaskiya ba yarda da abinda

ka shirya yi wanda ba kaso in gani shiyasa kawai

zaka hanani zuwa.

Du abunda naga damar yi kin isa ki hanani ne?

Karki manta fa da na samu, zan iya kyautar da

abunda na mallaka don nuna bajinta, da godiyar

Allah bisa kyautar mutum da yayi min.

Kema ga key din mota sabuwar kira, ta yayi na

baki, ki hada da dayar sun zama biyu, albarkacin

wannan haihuwa da akayi min.

Tasa kuka banaso bana farin ciki da kyautar da

kayi min, ka barni ni kawai nazo naga abunda xa

ayi.

Ya kashe wayar yayi murmushi kawai ya girgirza

kai.

An sha shali ranar suna, a ranar kuma aka aiko

masa da takardar karin girma, a ranar Aliyu

yayiwa ‘yan uwansa bajinta kanansa su hamza

dasu sadik da faruk yayun zainab, ya basu gidajr

guda hudu a jere da aka gama ginasu, yace su

nemo matan aure, ya fito da keys na gidaje

kanana ya bawa sadiya da ni’ima, yace gashi

kuma kwasa ‘yan haya.

Ya bawa Abba da daddyn zainab mukullayn

gidansu da aka gama.

Tsawon wata uku basa cikin gidansu suna na

gidan zainab data zauna aciki.

Haka ya rinka bin ‘yan uwa da dangi yana musu

alheri, aka radawa jariri sunan Abbansa, suna

kiransa Arfat.

Aliyu yaje da kansa ya bawa maihaifin mansura

key din gida mai kyau.

Du abunda akeyi mansura tana samun labari ta

waya, hankalinta atashe yake don ita gani takeyi

bari da dukiyarsa yake yi kamar zata kare.

via #Justice_Hamzat

[8:10AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4**15

Rayuwa ta mike, jin dadi da kwanciyar hankali

sun saukar musu, basu da matsalar komai

Arfat yayi bul-bul dashi, fari sol kyakyawa.

Watan arfat hudu dai-dai wannan lokacin ne

kuma mansura suka cika shekara a Abuja.

Ranar litinin da yamma mansura, tayi masa

maganar zuwansu gida, yace su fara shiri saura

kwana shidda su tafi.

Tace kayi mana alfarma mu tafi jibi, kaga saura

kwana bakwai bikin yaya saratu, ma fara shirye-

shiryen da zamuyi.

Ya girgiza kai kwana shidda na fada miki in kinje

kwayi shirin da zaku yi.

Taso tayi magana ganin ba fuska ta zumbura

baki ta bar wajen.

Da dare suna cin abinci da Ahmad mansura tana

gefe daya tana kallo

Ahmad yace, Abba dazu fa da ina waya da Ihsan

cikin maganarta tace min arfat bashida lafiya.

Cikin sauri Aliyu yace, um-uhum?

Har yana kwarewa, yace dazu da mangariba fa

munyi waya da zainab, amma bata gaya min ba.

Ya dauki wayansa ya kira zainab ringin daya ta

dauka, yace zeeyta me yake damun babana?

Wallahi yaya zazzabine, inaga dai awon hakorine,

don yanata amai

ya daka mata tsawa da gaske bashida lafiya

kenan, amma baki gaya min ba?

Yanzu me kika yi masa ina kika kaishi?

Tace ba ko ina?

Ya doka mata tsawa kina haukane ki barmin yaro

da ciwo?

Dif ya kashe wayar ya bugawa hamza, “hamza

maza kaje gidana ka dauki arfat ka kaishi asibiti.

Yanzu nan zanyiwa doctor waya.

Yana kashewa ya mike yana zagaye falon,

hannunsa goye a bayansa, yanata busar da huci.

Ya sake buga wayar yauwa doctor za a kawo

maka yarona.

Ai gashima sun iso.

Yauwa dr ka kulamin dashi sosai

likita yace kada ka damu, zan kula sosai.

Yauwa nagode.

Yana kashe wayar ya kalli mansura ke ki hada

abunda zaki hada, da asuba zamu tafi.

Ta kalleshi cikin mamaki ba cewa kayi sai nanda

kwana shidda ba?

Ya girgiza kai bazan iya ba, bansan wane hali

yarona yake cikiba.

Karfe tara na safe suka shigo gidan ba wanda

yasan da zuwan su.

Gidan a gyare, mansura tayi bangarenta, Ahmad

ya biyo Aliyu bangaren zainab.

Zainab tana zaune cikin kwalliyarta tana ta

kamshi.

Umma da mama da ummi sunzo tun bakwai na

safe duba arfat, yana hannun ummi tana bashi

magani ta dabara, Aliyu yayi sallama, zainab ta

bude baki cikin mamaki a ranta tace jiya da

sassafe ya tafi.

Kallo daya yayi mata ya dauke kai,

tace yaya sannu da zuwa.

Ya daga mata hannu kawai, Ihsan ta taho da

gudu ta rukunkumeshi

ya dauketa yana sumbatarta.

Ya durkusa yana gaida iyayensa, ya ajiye Ihsan

ya dauki arfat, yana duddubashi yayi tsaki, yaro

jikinsa du ya saki, babu kuzari, babu wani karfi.

Ummi tace sharrin amai ai yafi ga haka, ya dauki

maganganun yana dubawa ya fice dashi a kafada.

Yace musu, umma bari na maidashi wani asibitin.

Ihsan ta biyo shi a guje, Abba zanje, ya riko

hannunta suka fita

Ahmad ya shiga da gudu ya fada kan cinya

zainab, ta rungumeshi

amadina tare kuka taho da aunty?

Umma tace me gidan saukar yaushe?

Sannan ya kula dasu, ya nufi wajensu yana

dariya, ya gaishesu ya fice da gudu ya nufi

bangaren mansura, yana gaya mata su umma

suna nan dole tazo ta gaishesu, tayi musu barkar

haihuwar zainab.

Tare da tambayar ya mai jikin? Suka ce da sauki.

Zainab ta dan rissina aunty ina kwana?

Ta dago ta kalleta, a zuciyarta tace wai wani irin

kyau da kullum kamar kara mata sabuwar halitta

ake. Ashe ba rayuwar abuja ce tasa ta wannan

kyaun ba? Ko ina take kyan nan bazai gushe ba.

Zainab ta sake maimaitawa aunty ina kwana?

Firgigit tayi ta amsa lafiya lau.

Ta ttashi ta fita daga dakin.

Ummi ta bugawa Aliyu waya, lafiya kuwa mukaji

shiru?

Aliyu yace bakomai ummi sun canja masa magani

ne, sun kuma sa masa karin ruwa, yana karewa

zamu taho.

Tace to shikenan yanzu mu zamu biya muga jikin

nasa, sai mu wuce gida.

Suka yiwa zainab sallama suka tafi

zainab ta mike ta shiga kicin ta dafa musu

wannan, ta soya wacan wai duk kokarinta ta

faranta masa

taga yayan nata yana fushi da ita.

Sha biyu dai-dai suka shigo, abun mamaki Arfat

ya ware, yanata wasansa da dariya.

Zainab tayi kwalliya ta daukan hankali, tana ta

zuba kamshinan nata mai dadi, ta tareshi yaya

sannu da zuwa.

Ya kauce ya barta a tsaye ya wuce ciki, ya

shimfide arfat ya shiga wanka, ta dauki arfat

tanayi masa wasa yanata dariya, tasa masa nono

a bakinsa yasha ya koshi.

Ahmad ya shigo aunty mami naga sun dawo,

Ihsan tana gurin mama kawo arfat din.

Tace gashinan Amadina.

Ya daukeshi, kai aunty mami kin iya haihuwar

turawa, masu kyau, ni dadi nakeji naga kannena

masu kyau haka.

Tayi dariya, Allah Amadina, zoka kaiwa mama

abinci kazo kuci kaida Abbanku.

Yace to aunty mami rikemin kanina yanzu zan

dawo.

Ya dauki ya tafi, ta saka arfat a ruwa, ta sake

masa wanka, ta canja mishi kaya yanata kamshin

hoda ta sashi cikin kekensa na zama.

Aliyu ya fito ya nufi arfat, ya daukeshi, Abbana ya

jikin? I luv u Abbana, ta zauna kusa dashi, yaya

barka da dawowa ga abincinka.

Bana ci.

Haba yaya don Allah kayi hakuri

meyasa bazaka ciba?

Ki kyaleni kawai zeey kin batamin rai, ki barmin

yaro da ciwo ki ki yimin waya, to da ya mutu

saidai na tarar da gawa kenan?

Ya tsaya bakin taga yana kallon Ahmad da ihsan

suna ball.

Via #Justice_Hamzat

[8:13AM, 07/05/2017] 💞@lh@ji💞: TATTALIN SO 4***16

Ya tsaya bakin taga yana kallon Ihsan da Ahmad suna ball

a harabar gida.

Yaji dadi a ransa, zainab ta taso ta daura kanta abayansa

tana magana, cikin sanyinta.

Kayi hakuri yayana ka gafartamin

naga baka dade da tafiya ba, kuma ka barshi lafiya lau,

saina kasa gaya maka, ina gudun tashin hankalinka.

Saina rasa ya zanyi da yaron, ga talatu ta tafi duba jikarta

ba lafiya, na rasa ya zanyi dashi, ni nasan bazan iya fita

bada izninka ba, shiyasa kawai nasa yaron a gaba ina

kuka.

Yaya ka yafe min, bada niyya nayi hakan ba.

Ya juyo ya rungumeta yana share mata hawayen, yaji

tausayinta, ya juyo da ita ya rungumeta yana rarrashinta.

Shikenan naji, ya isa daina kukan, na hakura muje ki bani

abincin.

**** *** ******

da yaje gida yake cewa Alh yana so zai rubuta takardar

neman alfarma a dawo masa da ofis dinsa kano, saboda ya

zauna cikin danginsa da iyalansa.

Alh yace wannan shawara tayi daidai, tunda ka fara tara

iyali dole ka zauna a waje daya, ko don kulawa da ilimin

‘ya’yanka ma.

Hakan akayi kuwa baisha wata wahala ba, wajen amince

masa, aka bashi ofis a kano.

Ga harkokin kamfaninsa komai yana garawa yanda yake

so.

Zaman mansura da zainab babu irin kyara da wulakanci da

cin mutunci da mansura bata yiwa zainab, amma zainab

saita kwantar mata da kai tana binta a sannu, bata kuma

bari Aliyu ya sani, bare yayiwa mansura fada, ita dai zainab

ta dage da gayawa Allah basu zaman lafiya.

Cikin hukuncin ubangiji kuwa, Allah ya amsa addu’arta.

Ta shiga falon mansura arfat na biye da ita, watansa sha

biyar yanata yawonsa ko ina, amma bata yaye shi ba.

Tace aunty zanje dubo jikin hajiya, ga arfat nan kafin

Ahmad da Ihsan su dawo islamiyya.

Har zata fita, mansura tace ke dawo ki dauki danki.

Zainab tayi murmushi tace dana ko danki aunty? Ai kin fini

karfi akan ‘ya’an nan dani dasu du mallakarki ne.

Mansura tace wai ‘ya’yanki da kike turowa su wuni a

bangarena ke kina naki bakya tunanin na cutar miki dasu,

kona dakesu, ko nayi musu wani mugun abu?

Zainab tace haba aunty na dade fa da sanin halinki, tun ina

‘yar shekara takwas nake hannunki, da kina da mugun abu

dani zaki fara yiwa.

Aunty kina da kirki da hakuri kullum dauriya nake yi, har

nake iya hada ido dake. Amma ina mai jin nauyi da kunyar

aure miki miji danayi. Tasa kuka.

Mansura ta taso ta rungumeta, kada ki damu zainab na

dade dayin nadaman irin abubuwan da na rinka yi miki, don

kin auri Aliyu

wanda wauta nayi da son zuciya, tun fil-azal Allah ya rubuta

ke matarsa ce, to ya zanyi da wannan rabon?

Tunda kika haifi Ihsan Allah ya cusa min kaunarta a raina,

haka arfat gani daya nayi masa naji kaunarsa ta ratsani.

Kiyi hakuri zainab da abunda nayi miki.

Ta rungumeta, wayyo aunty dan Allah ki bari ban taba

rikonki da komai a raina ba, na yafe miki aunty nima ki yafe

min.

Na yafe miki zainab.

Aliyu ya fito daga daki yana yi musu tafi, yace nagodewa

Allah da kuka hade kanku, ga cek na milyan biyar-biyar kuja

jari.

Suka yi tsallen murna suka rungumeshi, suna masu yi masa

godiya.

Sun hade kansu bame jin kansu, tare suke harkar business

dinsu.

Dubai zuwa kano suna harkar gwala-gwalai, mansura ta

samu ciki ta haifii ‘yarta mace.

Ansha murna da bidiri, akasa wa jaririyar Ikram, Ihsan du

tafi ‘yan uwanta murnar zuwan Ikram don gani take yanzu

ta samu abokiyar shawara.

A tsakanin mansura da zainab baka iya gane ‘ya’yan, don

gaba daya sunfi zama bangaren mansura. Aliyu kullum

yana cikin godiyar Allah.

Kamar yau da kullum nima da nake cikin godiyar Ubangiji.

TAMMAT BI HAMDULILAH.

 

Sai wani jikon kuma  @Khadija Idris ringing

1 Comment

Leave a Comment