Tayi Man Kankanta Hausa Novels

Tayi Man Kankanta Hausa Novels

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Tayi man kankanta

Sadaukarwa ga Ahalin Sharoo Gambo Yako mazan su da matansu alherin Allah yakai muku a duk inda kuke nayi tawassali ga Annabi Muhammadu (SAW) Allah kai ruƙo da hannayena dan alfarmar ahalin manzon Allah (SAW)

Bissimillahirrahmanir raheem

 

wannan littafin nawa Æ™irÆ™irarsa nayi banyishi dan wani ko wata baduk abinda kaga yayi dede da rayuwarka arashine wannan daban yake da sauran salonsa na dabanne akwai abun dariya zazzafar soyayya tausayi Æ™iyayya da É—umbin danasani karku bari abaku labari “tayi man kankanta” kubishi sannu a hankali dan kwashe darasin dayake tafe dashi.

 

 

 

surbajon ce de har yanzu salo da basirar duk nata ne nice da kaina ba saƙo ba ga me.

 

 

  1. Ummu Aymana
  2. Surbajo
  3. Kano to jiddah
  4. Karen bana
  5. Sanadin kidnapping
  6. ÆŠan karuwa
  7. Cin Amana Ko Fansa
  8. GiÉ—aÉ—o ba Shege Bane
  9. Allah Gatan Bawa
  10. Ƴar Bautar Ƙasa
  11. Aure Da Haihuwa
  12. tayi man kankanta

 

 

Da de sauransu ku kasance da wannan banufiya domin ci gaba da samun nishaÉ—i.

 

 

 

 

 

 

Zahra’u ya kamata ki fito haka fa kizo ku wuce tun É—azu su hanne ke tsaye suna jiranki lbana son sakarcin banza facewar wata dattijuya dake zaune kan kujerar zaman tsakar gida tana É—aure nono a ledar siga.

See also  A Gidan Mu take Hausa Novel Complete

 

Daga can cikin bukkar dake kusa da dattijuwar wacce aka kira da Zahra’u tace Inna do Allah Don Annabijjo ki barni in sa jambakina cikin kwanciyar hankali ke bakisan in bakayi kwalliya ba ko kallonka ba’a yi?.

 

Aykin kawaiyo tun bara kike sa jambakin amma har yanzu ba mashinshini se asarar kuÉ—in siya miki da nike yicewar inna daga wajen da take zaune.

 

Fitowa tayi daga cikin bukkar tana gyara ɗamarar da ta ɗaura a ƙugunta ko ina a fuskarta kwallliyace irin ta fulani.

 

LaÉ“É“anta shafe cikin jan janbaki yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyar ba. *tayi man kankanta”

 

Kede Inna kinada matsalabakin ki be taÉ“a faÉ—in alkha’iri se sharri ni É—oramin mu tafita Æ™arasa maganar cikin turo É—an Æ™aramin bakinta gaba.

 

Gammo ta ɗora sannan ta ɗora mata kwaryar nonon akanta ta miƙa mata ledar viva da aka sa ludaya da ƙorai acikita juya gun su Hanne dake tsaye zaman jiranta tayi murmushi kumatunta suka lotsasiririyar hushiryarta ta bayyana atsakanin fararen haƙoranta masu kyan tsaritace na ɓata muku lokaci kuyi haƙurimu tafi kar mu sake ɓata wani lokacin.

 

 

Murmushi sukai matasannan suka rankaya suka fice bayan sunyiwa inna sallama. “tayi man kankanta”

 

 

Tafe suke suna hirar su ta yau da kullumɗaya daga cikinsu Me suna haule tace wai duk ƙawancen nan namu muna aure inba riga ɗaya muke ba se ya ragu ko?.

 

 

Dariya Zahra’u tayi sannan tace Allah ya kyauta ni aradu ko birnin sin naje aure bazan dena Æ™awance daku babare ma dukanmu muna ruga É—aya ba inda zamu.

See also  Maciji Ne Hausa Novel Download

 

Hanne ce ta amshe zancen da cewa ni Auran ma tsoro yake ban kunga de Ma’u kamar abun arxiÆ™i Rabi’u ya Aureta amma ku dubi wulaÆ™ancin da yake mata yanzu.

 

Shiyasa na shiga makaranta dan bazan yarda namiji yamin wulaÆ™anci bacewar Zahra’u tana murmushi.

 

 

Da wannan hirar tasu suka ƙarasa fitowa daga cikin dajin falgore inda rugarsu takesuka miƙo tsawon titin zuwa inda barikin sojojin dake cikin dajin yakesabida ankawo sababbin sojojin da ake ba training gurin acike yake da mutane kamar kasuwadan motocima in sun zo gurin da ƙyar suke wucewa sabida yawan sojojin.

 

Basu jima da zuwa ba kowa kayanta ya ƙare sabida ƙarancin abincin gurina hannu a hannu ake siyan duk wani abun ci na gurin. Gurin me saida burodi suka ƙarasa kowa ta sayi guda ɗaya sannan suka juya cike da farincikin sun sayi burodin da zasu ci yau agurin alibidin sunan Zinawata ƙawarsu data haihu.

 

Karo suka ci da wani matashi sanye da wandon sojojihannunsa riƙe da bindiga se riga tshits army green da hular sojojiba laifi kyakkyawane raɓewa sukayi zasu wuce ta gefenshi yayi sauri yasha gabansu yace yana murmushi.

 

Don Allah kuyi haƙuri mu baƙi ne anankuma abinci mukeso mu ciisowar mu kenan daga Abujaamma mun rasa .

 

Harara Zahra’u ta galla masa sannan taceamma dan baÆ™in hali ay kuna gani muka kawo tallan nono in yunwar kukeji me ya hanaki siya?.

 

Murmushi yayi dan ya fahimci yarinyar akwai tsiwacikin taushin murya yace Bamu lura bane Æ™anwataayi haÆ™uri. To yanzu me kukeso muyi mukutunda mude ba abinci bane bare ku cinyemucewar Zahra’u batare da tsoron komai ba dan ita ba Æ™aramin abu bane ke firgitata.

See also  Shagalalliya hausa novels complete

 

In anan kuke don Allah ku taimaka mana kuÉ—in cefane zamu baku ku dafo mana abincin ku kawo mana nida abokina. Shuru sukayi sannan hanne tace gaskiya rigarmu da nisa nide bazan iya zuwa gida in dawo ba.

 

Yo inba wahalalle ba waye zeje gida yadawo nan cewar haule. Don Allah ku taimaka abokina yanada lalurar gyambom ciki be jure yunwa don Allah ku taimaka ku yi mana kamin yafara jin yunwa wallahi zamu biyaku ladan yi cewar matashin kamar zeyi kuka.

 

Zahrau tsintar kanta tayi da tausayawa abokin nasa sabida itama tana da lalurar gyambom cikin tasan azabar ziwon dan haka tsintar kanta tayi da cewa.

 

 

 

Dan iskan Namiji Hausa Novels

 

Kawo kuÉ—in zan dafo mukusede muna da nisa zaku iya jira? Da sauri matashin ya gyaÉ—a mata kai sabida tun É—azu yake neman wanda ze dafo musun amma be samu ba ga abokin nashi shegen taurim kai shiba jure yunwa ba amma ko ze mutu baze ci abincin siyarwa ba shiyasa duk yabi ya damu.

 

Hannu yasa a aljihu ya É—ebo kuÉ—in dashi kanshi besan adadinsu ba yabata juya kuÉ—in take a hannunta tana mamaki amma batace komai ba ta É—auka da yawa suke so dan haka ce mishi tayi zan kawo ma insha Allahu ka tsaya a bakin titi de inda zan ganka da wuri.

 

Godiya yay mata sosai sannan yacemu haɗu kawai anan zefi sauƙi sunana Capt Jameel Ahmad zan jiraki anan.

 

 

Bata ce komai ba suka juya suka wuce ita da ƙawayen natawanda gaba ɗaya haushinta sukeji cikin fushi hanne tace. nufinki de bazaki gidan sunan ba ko? shiyasa kika amshi girkin gardawan da baki sani ba.

 

Batare da damuwar komai ba aranta tacedan bakusan ciwon ulcer bane da kuma kun tausaya kun musu nide zan musu sabida Allah. Tana kaiwa nan tai gaba ta ƙyalesu a baya.

 

 

Muje zuwa Kuyi share tare da comments domin mu ci gaba.

 

Surbajo for life.
Zamu ci gaba inshaallah

 



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

​

 

 

Name: [Tayi Man Kankanta Hausa Novels]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

25 thoughts on “Tayi Man Kankanta Hausa Novels”

  1. Pingback: Hausa Novels Littafan Hausa Guda 10000 Masu Dadi JIKI NA YAKE SO COMPLETE HAUSA NOVEL | MY NOVELS

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top