Hausa Novels

The sexy boss Hausa Novel

The sexy boss Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

Bismillahir rahmanirrahim!

 

 

 

Da sunan Allah me rahma me jin kai ina ma Allah godiya a bisa niimar da Allah yayi mana Alhamdulillah.

 

 

 

Ina rokon ubangiji Allah yasa na fara wannan rubutu a nasara yasa na rubuta Alkhairi ya kuma hanani rubutu akasin haka.

The sexy boss Hausa Novel

 

 

Wannan shine littafi na farko dana fara rubutawa ina me neman Alfarmar ayimin uzuri da abinda aka gani ba daidai ba, a kuma gyara min inda yake da kuskure nagode.

 

 

 

Page 1

 

 

 

A Masarautar ulwa kuke tunanin zaku iya tsere ma ganin mu lallai azaba ta tabbata a gareku mai tsanani. kuna kaskantattu daku amma kuke ganin zaku iya jada SARKI ABUL UWAIS, maiji da kasaita lallai ina tausaya ma kalan azabar da zaku sha a hannun sa .

 

 

 

 

 

Cikin tashin hankali daya daga cikin wadannan bayin d aka kamo ya kara kwanciya yana cewa “yakai wannan bafade kayi hakuri ka dubi girman Allah ka yafe mana tabbas munyi kuskure amma bazamu sake ba ina bada hakuri amadadin mahaifiyata da kannaina” lallai maitama wato kaine kafisu baki da har kake iya magana tabbas ka kama bakinka kafin ku isa gaban sarki .

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Fadar sarki Abul uwais suka nufa ana gana masu azaba tun kafin isarsu. An gaishe da sarkin sarakuna uban yarima uwais da ubaid baban gimbiya kalba, Allah ya kara maka mulki ya shugabana . Allah ya taimakeka mun kama mahaifiyar maitama da sauran yaranta zasu gudu ba bisa doka ba sunbi ta barauniyar kofa mafi sirri , hakan yasa muka gurfanar dasu gareka shugaba” sarki abul uwais da ranshi ya baci ya daga kai kallesu a wulakance ya dauke kai kusan minti talatin kafin ya bada umarnin cewa A tafi dasu dakin durhun a gana masu azabar da baa taba ma wani mahaluki ita ba sannan a hana masu ruwa a basu abinci me barkono da yawa domin zunubin su mafi girman zunubai ne.

 

 

 

 

 

Rufe bakin sarki abul uwais keda wuya aka tafi dasu durhun domin cika umarnin shugaba. Ana shigar dasu aka ware ammi gefe aka kulleta gaba daga da igiya aka rufe idanunta da bakinta ana dukanta da bulali ana sheka mata ruwan zafi me hade da gishri a cikinsa. Yayinda aka kulle zeenat irin kullin goro ana bugunta ana sheka mata ruwan gishiri gefe kuma ana fisgar gashin kanta

 

 

 

maitama da kaninsa Abdullah wanda a akallaha bai wuce shekara 8 a duniya suna wani daki aka kaisu aka sargafe su kamar za’a jefe su ana bugunsu da karfen rodi wanda ake zaro shi cikin wuta idana bige su iya bugu sai a sheka masu ruwan barkono da gishri sai a cigaba da dukansu.

 

 

 

 

 

Kuka suke sosai tun sunayi har zuciyarsu ta bushe a lkcn aka zo kawo masu wannan abinci me tsananin azabar barkono , a haka aka saka suci dole sunaci kamar zasu shide saboda azaba . Wani bafade ne me tsananin muni ya bushe da dariya yana me jin dadin ganin irin azabar da su ammi kesha yanayi yana kallon su ” tabbas zakusha azaba a hannuna domin ni kaina ban kaunaar kaina balle kuyi tunanin zan so wani har naji tausayin shi a haka zanta gana maku azaba har sai kun tabbatar NAMU BA IRIN NASU BANE ”

 

 

 

 

 

A wahalce Abdallah yace ammi ruwa zan mutu, hamma A A ka taimaka min kar na mutu! adda zeenat ku bani ruwa , gaba dayansu wani irin kuka ne ya kubce masu me tsananin azaba da cin rai domin sunsan babu ta yadda zasu taimake shi . A hankali adda zeenat tace kayi hakuri kanina duk tsanani yana tare da sauki insha Allah wata rana sai labari . Kara fashewa da kuka sukayi yace” adda zeenah nasan ni mutuwa zanyi bazan kai lokacin da saukin nan zaizo ba sai dai ku kadai amma ku kula mana da Ammin mu karsu kashe mana ita kunji .

 

 

 

 

 

Kukan suka kara saki a tare Maitama ne yayi dauriyar tsayar d kukan shi yace haba auta kadaina irin wannan maganar bana hanaka ba uhum kabari kaji zamuyi rayuwar farin ciki insha Allah kaji , hmmmm yaya AA ni nasan mutuwa zanyi nabi abbun mu kasan banda cikakkar lapiya kuma ga azaba ana gana mana kaga ai barinku zanyi kasan yanayin lapiya ta.

 

 

 

 

 

Ammi ki kara hakuri kinji jarabawa ce daga ubangiji Allah ya kawo mana sauki a ciki . Toh auta nah Ameen Allah ya amsa amma ka daina fadar irin maganganun nan kaji muna tare insha saina aurar dakai autah , dariya suka saki gaba daya tare da kuka . Yayinda aka daka masu wata razananniyar tsawa data saka su gigicewa suka Mike tsaye .

 

 

 

 

 

“Allahumma ajirni fi musibatun wa’aklifni khairan minha” Abinda ammi tafada masu kenan sun sani tunda tarbiyarta ne nan take suka shiga maimaitawa cikin ikon ubangiji da kudrarsa sai Allah y dubi kukansu nan inda suke Allah y saka ma wannan bafade ciwon ciki me tsanani wanda nan da nan y kwanta ciwo Allah kenan maji rokon bawansa , ” “Tabbas babu Abinda yakai ka roki Allah a kowane hali zaka shiga domin shi Allah maji rokon bawansa ne ”

 

 

 

 

 

 

 

Ku biyoni don jin wannan labari me cike da

 

Ilmantar wa

 

Fadakarwa

 

Tausayi

 

Cin amana

 

Tsantsar butulci

 

Da kuma nishadan tarwa

 

 

 

Taku ce dai

 

Iieshert

 

 

 

SHARE SHARE SHARE

 

Fisabilillah

 

 

 

 

 

NAMU BA IRIN NASU BANE

 

 

 

 

 

 

 

Mallakar lieshert

 

 

 

Ga duk maison shiga group dina na WhatsApp ga link nan dan Allah kuyi share fisabilillah https://chat.whatsapp.com/HORMe0lAa6vIPWvScOcK5B

 

 

 

Page 2

 

 

 

Cikin kwanaki biyu da faruwar wannan lamari idan kaga Ammi da yaranta saika zubar masu da hawaye saboda tsananin azabar da suka sha amma duk da hakan bakinsu bai gaza ba wajen neman sauki wajen ubangiji domin basu fasa addua da suke ba akowane lokaci Allah kenan ana cikin hakan Aka fara shirye shiryen tarar wani hamshakin sarki dake zaune a kasar Nigerian. Inda sarki ya cika da farin cikin zuwan wannan sarki . Wannan ne karo na biyu da Aminin shi ya taka kasar MALI domin ziyartar sa ,aminin sarki abul uwais ne domin tare sukayi karatu a kasar Egypt kasancewar yayan sarakuna ne a wancan lokacin sai yazama sun dinke sun koma abokai saboda kowa naji da takama da izza ga kuma kyau da dukiya.

 

 

 

 

 

Kasancewar su abokai ko ince aminai hakan bai hana a gane banbancin dake tsakanin suba domin halayyarsu akwai banbanci, sarki Abdulgafar mai lafiya ya kasance me hakuri da son talakawa da dajara dan Adam ,yayinda sarki Abul uwais ya kasance me tsananin kyamar talaka da son mulki da izza ko kadan bai dauki talaka da daraja ba . A yanzu haka wannan ziyara da sarki Abdulgafar ya kawowa sarki abul uwais yazo ne domin sun dauki shekara wajen biyar kenan basu hadu ba saboda tazarar dake tsakanin su.

 

 

 

 

 

Anata hidimar tarar Wannan adalin sarki a lokacin ne su ammi suka samu sauki daga wannan azaba suna zaune sarki ya bada umarmin a sake su albarkacin zuwan aminin sa farinciki ne ya bayyana a fuskar adda zeenat ta Mike ta kama Ammi da autah dake kwance ba lafiya domin take bangaren bayi inda anan suke rayuwar su .

 

 

 

Suna zuwa dakin da yake nasu suka zauna suna maida numfashi ahankali autah yace ammi na inajin yunwa ga kishin ruwa ina ji ki bani nasha sai ki bani magani nasha ko naji sauki kinji ammi . Hawaye ta share tace mashi toh autah bari na nemo maka kaji ka jirani nadawo ina zuwa mikewa tayi ya rike mata hannu yace Ammi ki yafe min ni nasan mutuwa zanyi na barku keda su yaya Ammi meyasa har yanzu bazaki gaya min asalin labarin muba ,? Meyasa kika zabi daki boye mana ki gaya min koda sunan mahaifina ne nasani kafin na mutu dan Allah Ammi .

 

 

 

 

 

Kuka ta fashe dashi domin bata son taji yaran na son jin wani abu daya shafe su tafi son su bar komai su dauka basu da kowa sai ita . Amma ya ta iya dole watarana su sani , kallon shi tayi tace auta bari na nemo maka abinda zakaci kaji . Ficewa tayi d sauri saboda kukan daya taho mata na tausayin yaran nata tabbas suna cikin kuncin rayuwa Allah ka kawo mana dauki abinda tace kenan ta kama hanya zuwa madafar abinci domin karbo masu abinci suci .

 

 

 

 

 

Tana fita daga dakin adda zeenah ta share hawaye ta kalli yan uwanta tace ” har zuwa yaushe Ammi zata daina boye mana asalin mu da kuma labarin mu bansan meyasa ba amma nasan ba karamin abu bane ammi take boye mana ba koma dai menene ni kaina ina son nasani gaskiya” Maitama ne ya budi baki yace gaskiya ne sister ni kaina nasani akwai wani abu a kasa amma koma menene mu kara bata lokaci ina da tabbacin insha Allah watarana zata gaya mana indai muna da rai da rayuwar kaiwa lokacin mu cigaba da addua kawai .

 

 

 

Amma yaya ka duba fa kagani daka taji kishin kishin din zuwan sarkin nan na Nigeria fa shikenan ta tada hankalinta akan mu gudu zuwa wata kasar sai dai bata samu nasarar hakan ba aka kamo mu bansan meyasa ta tana hankali ; ka duba maganar anya babu wani abu data sani game da Nigeria da har take gudu saboda bata son suzo su same su a wannan masarauta !

 

 

 

 

 

Ajiyar zuciya ya sauke tabbas na gamsu da abinda kika fada sis amma kina ganin wannan Dalilin ne zaisa Ammi tace mu gudu mubar Mali batare da wani abu ba ace lokaci daya ta fada hakan kuma ba bata lokaci ta aiwatar gaskiya ni a ganina wannan ba shine dalilinta ba akwai dai wani abu amma koma menene mu jirata mugani zuwa wani lokaci .

 

 

 

 

 

Sallamarta ta hana zeenah cewa komai suka amsa mata ta shigo dauke da wata kwarya an zibo masu abincin a ciki . Zama tayi tace masu kowa yaje ya wanke hannu sai kuzo muci gaba daya, kamar yadda tace haka sukayi domin basuyi ma mahaifiyar su musu komai ta fada indai bai saba ma addini ba suna mata shi . Adduan cin abinci suka karanta kamar yadda manzon Allah (SAW) ya koyar damu suka faraci .

 

 

 

 

 

Ba dabiar su bace cin abinci ana magana hakan yasa tunda suka fara babu wanda yace wani abu harsuka gama suka sha ruwa sannan suka wanko hannuwan su suka dawo daki . Maganin autah ta dauka ta bashi yasha ya kwanta ita kuma ta Mike ta tafi bangaren gimbiya maryama uwar gidan sarki Abul uwais ita kuma zeenah ta tafi bangaren gimbiya kalba domin aikinta acan yake.

 

 

 

 

 

Tafiya take amma tana tunanin wannan wace irin masarauta ce ? kuma ko ina haka masarautun su suke ne ? Anya ana samun masarauta me rangwame kuwa kowane bawa da kalan kaddarar sa mu kuma irin tamu kena n Allah ka bamu ikon cinyewa. Tana isa bakin kofar taji an daka mata wata irin tsawa me ban tsoro nan take tahau furta innalillahi wa inna’ilaihi raju’un .

 

 

 

 

 

 

 

Ku biyi don jin wannan qayataccen labari

 

 

 

 

 

SHARE

 

FISABILILLAH



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [The sexy boss Hausa Novel]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!