Crypto currency

Token din Floki Inu zasu gina makaranta a Najeriya

Token din Floki Inu zasu gina makaranta a Najeriya

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: floki inu

Nidai a tunani irin nawa, duk ire-iren maganganu na sharri da mahukuntan kasar nan suke jinginawa kiripto a mahangar su, shi Al’amarin Allah ta fuskar cigaban kasar ya haskawa yan kasar suke yin ta – Domin koda kuwa kace makirci da sharrin yahudawa ne ke tunkarar ƙasar, to da a wadanne abubuwa ne kuma suke durkusar da ita?

 

Yanzu haka kamar yanda nake karanta labarin a jaridar IndianCrown, Team din Floki Inu zasu gina makarantu nan bada jimawa a wurare kamar haka: Najeriya, Guatemala da Laos. Wannan kuma yana daga cikin jadawalin token na cigaba da bunkasa Kasuwancin sa a fadin duniya – Shi kansa wannan ai use case ga token din.

 

Kamar yanda shafin tweetstorm ya tabbatar Floki Inu zasu hada gwuiwa da wasu kungiyoyi domin tabbatar da yiwuwar hakan. Makarantar da zasu gina a Najeriya zata kunshi ajujuwa 6, masu ɗauke da kayan fasaha, Library na computer da administrative block wanda zasu hada gwuiwa da gidauniyar Tubitha Cumi dake ƙarƙashin United Nations Economic and Social Council – NGO.

 

Wayoyi 35 da suka daina WhatsApp

 

Ita wannan makaranta da zasu gina a Najeriya zata Koyar da aikin noma da kiwo ne kuma a ƙalla mutane 3,500 ne zasu rika karatu a cikin ta. Wannan babban abun murna ne kwarai da gaske!

 

Mustapha Gfatu

(Dan Fafutuka)

 

 

 

floki inu

Leave a Comment

error: Content is protected !!