Hausa Novels

Tsaka mai wuya hausa novels

Tsaka mai wuya hausa novels

 

 

 

 

 

 

 

 

*TSAKA MAI WUYA*

 

1

 

Irin kallon da Dr din ke musu ya nuna zallar kyankyaminsu dayake saboda babu fara’a ko kadan a fuskar sa haka kuma fuskar a yamutse take yana musu kallon rainin wayo tare da sauraren shirmammen bayaninsu.

Su biyu ne a zaune mace da namiji dai wata yarinya da goyo a bayanta daga gefensu a tsaye fuskarta a kumbure alamar tayi kuka har ta gaji idonta sunyi ja sosai.

 

 

Dapta don Allah kuda kuka san aikinku ga yarinya nan batada aure kawai ana bacci cikin dare se akaji kukan jariri dubawar da za’a yi ashe itace ta haifeshi duk laulayi da renon cikin da tayi bamu sani ba, abin mamaki yarinya ta kafe ba ita ta haifeshi ba bayan kowa ya ganta jina jina da ita da jariri.

 

 

 

Kallon su likitan yayi yace, tsaya malama me kuke bukata yanzu?

Namijin dake gefenta a zaune yace, so muke a duba muna ita ciki da waje tunda aikinku ne kuna gane matar da san maza da wadda bata dade da fara abin ba da wadda tayi sau daya da wadda ta taba haihuwa ma duk kuna ganewa.

 

 

 

Dukar da kansa yayi sannan ya dago yana murmushi kafin ya kalli agogo yaga karfe hudu da rabi patient sun rage, yace to idan ba damuwa ku karbi goyon dake bayanta sai ku bamu waje, da sauri suka Mike zasu fita matar tace, miko min shi nan bakar munafuka idonta sumi-sumi kamar ta kwarai nan kuwa an iya budewa maza kafa.

Jiki a sanyaye ta saukar da babyn dake ta baccinsa ta mika mata suka fita, bin bayansu Dr din yayi ya rufe kofa ya dawo ya tsaya gabanta yana kare mata kallo kafin yace.

 

 

 

Ya sunanki?

Seda ta goge hawayen idonta sannan tace “Nana fadimatu” daga gefen teburinsa ya zauna ya sake tambayar ta “bakiyi kamada mai jego ba sannan wannan jaririn baifi kwana biyu ba, amma inaso in tabbatar sedai ina bukatar hadin kanki, kema ai nasan kinaso ki fita daga zargin da ake miki ko? da sauri ta daga masa kai tana cewa kuma wallahi nidai banyi abinda suke zargina dashi ba sedai in jaririn nan aljanine.

 

 

 

Murmushi yayi yace to yanzu kizo ki cire kayanki ki kwanta anan zan duba hanyar da baby ke fitowa ingani idan ta bude to alamar zargin da ake miki gaskiya ne.

Tsayawa tayi cike da tsoro tana kallonshi.

Ya tabe baki yace idan bazaki iyaba kina iya fita nayi attempting sauran marasa lafiya matsalarki ce wannan ba tawa ba.

 

 

 

Hawaye ya zubo daga idonta, a ranta tana mamakin alakar bincikensa da tubewar da zatayi, wani tunanin yazo bata sai ta fara cire hijab dinta, kallonta yayi yaji zuciyarsa tayi wani irin bugawa har seda ya runtse idonsa, seda ta zauna bisa gadon sannan ta cire rigar jikinta ta rufe idonta duka gabanta na faduwa. Ya dade a tsaye yana kare mata kallo zuciyarsa na kara ingizashi har baisan sanda ya isa kusa da ita ba ya dora hannunsa a kirjinta ta bude da sauri tana kallonsa suka hada ido, se ya wayance da cewa idan mace ta saba da bin maza akwai wasu abubuwa kamar kurji dake cikin kirjinta idan babu su to alamar wani yana yawan amfani dasu kenan inaso inji idan naki na nan. Ajiyar zuciya ta sauke dukda ta fara jin wani iri a jikinta, daga baya ya dawo wajen kafafuwanta yana kallon wurin, jikinsa ya dan soma rawa ita dai dama ta sake rufe idonta kawai se taji kamar abu na kokarin shiga jikinta ta dan bude ido saita ga kusancinsu yayi yawa kuma shima idonsa a rufe dafa gadon tayi zata Mike yayi saurin dannenta yana cewa, inaso inji idan hanyar a bude take ne, saita fashe da kuka tana rokonsa ya taimaka ya rufa mata asiri. Tunda nke a rayuwata ta duniya babu namijin daya taba ganina babu hijab balle acikin irin wannan yanayin da kaddara ta kawo ni, meyasa duk wayanda nake tunanin zasu taimakeni suke karewa da shiga ruyuwata su cuceni, daga zuwa bincike na fiddakai saika sake dulmiyar dani, dalilin zuwana nan saboda inaso awanke ni tas na fita daga zargi da kallon mazinaciya da ake min, meyasa zaka yimin haka don Allah karka lalatamin rayuwata.

 

 

Ana zato hausa novels

Tsaki yayi ya kalleta dakyau yace, daga ke har danginki akaina duk dogara yau kalma daya tawa zata gyara rayuwarki kamar yadda kalma daya din zata dagargaza rayuwarki din batareda kin aikata abinda ake zargi ba, ke zaki taimaki kanki fadimatu kuma abune da bazai wuce mintii ashirin ba ba wanda zai gane ki duba daga dan bincika kirjinki har kin fara amsa kiran, idan kinsan bazaki bani hadin kai ba to ki tashi kifita nikuma zan fada musu duk alamomin masu jego gasunan ajikinki sannan nayi gwaji ajikin ki maza kala uku sunyi amfani dake fiye da sau goma goma.

 

 

 

Dandano ne kawai daga labarin danake son rubutawa amma bansan zuwa yaushe rubutun nawa zai fara ba, may be nan da wata daya ko biyu. Duk lokacin da Allah ya bani iko dai zaku jini koda kuwa gobe ne nagode.

 

Safiyyah galadanchi

Leave a Comment

error: Content is protected !!