Hausa Novels

Tsautsayin Tauna Hausa Novel Complete

Tsautsayin Tauna Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

TSAUTSAYIN TAUNA

 

_✨GAWURTATTU BIYAR✨_

 

*Zainab Babib(Mom Islam*

 

 

Ina mik’a sak’on gaisuwa mai yawa, a gareku masoyana, musamman wanda suka nunamin zallar soyayya gurin siyan littafina *GUNTUN GORO* yauma gani tafe muku da sabo wanda nake ganin zakuyi farinciki, labarin yazo da sark’ak’iya, da zallar soyayya, karku manta da sunan fitaccen littafin wato *TSAUTSAYIN TAUNA* dagajin sunansa kunsan akwai cakwakiya over kudai muje zuwa.

Tsautsayin Tauna

Page 1-2

KADUNA STATE

Anguwar Dosa.

 

Wani irin tsawa ya daka mata tare da cewa ”meyasa kikeson sakani a hanyar da bata dace ba?, sokike inje inyi sata in kawo miki ko Yaya?”,

Matar da zatayi 35yrs bak’a bamai jiki sosai ba, dakaga yanayin jikinta zakasan suna fama da matsanancin talauci,

Ta rik’e k’ugu tana girgiza ta matso gabansa kana tace “inhar bakaje kayi sata ka kawomin ba wallahi baka cika namiji ba”

Rik’e da baki malam Haladu ke kallonta, bai jira me zata sake cewa ba ya fice.

Yana fita ta kalli Aisha yarinya y’ar kimanin shekaru goma sha biyu  duniya, sai bala’in rawar kai, Aisha fara ce sbda Wanda baisan iyayenta bama ya ganta zai rantse y’ar masu kud’i ce, Allah ya azurtata da yalwataccen gashi, ga idanuwannan masu d’aukar hankali y’an madai-daita, gashin girarta kuwa luf-luf yake, sai d’an k’aramin bakinta na tsiwa pink kamar ansa masa janbaki,

“Mama wai baba bazai nemi aikin yi bane? Wallahi yanason zuciyarsa ta mutu ne irin na mijin Hansatu mai waina”

Aisha ta fad’a tana ta6e baki,

“Yo ni ina zan sani, muddin yace zai takuramin wallahi bazan zauna ba ai bashine autan maza ba, gashi tunda talauci ya aureshi muka shiga uku,sudai abin kamar a jini yake kaf danginsu matalauta ne”

“Mama ki fara yimin k’osai in mun sami ribar sai mu dinga adanawa kinga ma kya sami jarin siyarda gawayin ko?”

“Amma Aisha baki da hankali, kina ganin ana fama da cefanen gida ki kawomin yin aikin mangyad’a, yanzu komai da yayi tsada sokike ciwon zuciya ya kamani na murk’ushe kud’in da y’an uwana suka  aikomin dashi?”

Dajin haka Aisha ta cuno baki kana ta mik’e tare da ficewa waje tana gunguni.

Tunda malam Haladu ya fita, yake neman aiki koda kwa6ar k’asa ne ta masu gini amma Allah besa ya samu ba, zama yayi kusa da shagon wata mata mai abincin siyarwa, wata dank’areriyar mata ce ta fito bak’a, kanan yaji gashin doki kai kace ba musulma ba, cikin d’aga murya take cewa “wai yau ina almajiranne duk kunyi shiru, gashi babu masu wanke-wanken?”

Da sauri malam Haladu ya taso jiki na rawa yace “gani ni zanyi”

Cikin yamutsa fuska tace “sai ka shiga ka d’ibo plets d’in da akaci abinci ga ruwan wanke-wanken nan ga omo can” ta nuna masa inda aka ajiye.

“To”  yace jiki na rawa ya nemi leda ya kwashe ragowar abincin da mutane sukaci suka rage ya tara a bak’ar leda, kana ya fara wanke-wanken, yana gamawa cikin d’aga murya yace “hajiya an gama”

D’ari da hamsin ta mik’a masa sai abinci data zuba masa d’an kad’an

Jikin Baba Haladu a sanyaye ya kamo hanyar gida, koda yaushe in zai shigo gida gabansa fad’uwa yake saboda masifar maman Aisha,

Kasancewar akwai abinci a hannunsa hakan yasa ya sami k’warin guwaiwar shiga gidan,

Yana shiga ya sami maman Aisha a  d’aki tana sallahar azhar, mamaki ne ya kamashi a zuciyarsa kuwa cewa yake “wai har anyi sallah ni ban saniba?”

“Haladu me aka samo mana ne? kasan idan mukaga bak’ar leda da bayani”

Malam Haladu ya k’arasa d’akin ya nemi guri ya zauna sannan ya kunce bakin leda kana yace “d’auko kwanon a juye”

Jikin maman Aisha na rawa taje ta d’auko kwano ya juye shinkafar, ya had’a da wacce aka bashi, sai gashi shinkafa ta cika kwano,

Cikin fara’a maman Aisha tace “megida a ina aka samo mana beta?”

Malam Haladu yayi jimm kafin yace “zubar da mutunci na nayi,

Ta dafe k’irji kana tace “ban gane ba?”

Malam Haladu yace “wallahi zaman nayi a shagon mai siyarda abinci shine nayi mata wanke-wanken ta bani”.

“Mtsw nama d’auka wani abun ashan kayi, ai wannan ba komai bane naga kamar da nama a ciki ko?” Kallonta kawai yakeyi Amma a zahiri zuciyarsa nayi masa zafi.

Tsince naman cikin abincin tayi kana ta ajiyesu a roba daban tace “in zuba maka ne ko kaci acan?”

Tsabar takaici kasa ce mata komai yayi.

Sai da taci tayi hani’an sannan ta ajiyewa Aisha tunda shikam yak’i kulata,

Cikin takaici ya fice a gidan ya nufi masallaci, Aisha kuma sai dare ta shigo,

Tana zuwa ta fad’a jikin mamanta a shagwa6e tace “mama baban kowa yana siyawa yaransa kayan dad’i niko baba ko biskit baya siyamin”

Maman Aisha tayi murmishin da zata iya kiransa dana takaici kafin tace “bak’in talauci ke dukansa ki rabu da matsiyacin ubanki kawai, yau dai ya kawo mana abinci harda nama”

Da murna Aisha ta mik’e tsaye tana rawa, Dan rabonsu da nama tun watan babbar sallah.

Abinci mai albarka itama Aishar sai da taci ta k’oshi sannan ta tashi, harzata kuma fita Maman tace “jekiyi alwalah rabonki da sallah tun ta asubha”

Cuno baki tayi kana tace “ke ina lissafa miki naki ne? Kin mance lokacin da kikayi sati guda ba sallah ba azumi?”

Waro ido maman Aisha tayi ta bita da gudu tana cewa “yau naji fitsara zuwa gaba Aisha zata zageni”

Sai da ta tabbatar da mamanta ta shiga d’aki sannan ta fito taje tayo alwalah tazo parlo ta kabbara sallah, kasancewar gidan nasu madai-daci ne mai d’auke da d’akuna uku na maman ciki da parlo sai makewayi sai kicin, shikenan tsakar gidan nasu ma ba wani mai fad’i bane, infact ma gidan haya ne duk shekara malam Haladu yake biyan dubu goma sha biyar kud’in wutar lantarki d’ari biyar.

Koda ta shimfid’a sallahya ba sallahar take ba, kana daga gefe kanajin mis-mis-mis d’inta, mamanta na daga d’aki tace “halin naki dai bazaki fasa ba ko?”

Aisha tayi ruku’u tace “duk nai 6atawa mutun sallah wuta zai shiga ni babu ruwana,taci gaba da sallaharta.

Zuwa dare basu wani samu abincin da zasu sake ci ba, haka sukasha ruwan d’umi suka kwanta, Aisha ce ta fara bacci sai mamanta itama kafin malam Haladu ya  shigo, yaji dad’i sosai dan baccinsu shine kwanciyar hankalinsa, yahau gadon tare da d’ago Aisha ya mayar gefe ya kwanta kusa da mama,

Can cikin dare mama taji ya fara lalubarta, bige hannun nasa tayi taci gaba da baccinta, malam Haladu dai ya kasa hak’uri ya kuma matsowa murya k’asa-k’asa yace “haba maman Aisha kiyi hak’uri ki bani hakkina wallahi nayi hak’uri har tsawon wata biyu sai kace dutse?”

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng

Cike da masifa ta tashi zaune kana tace “mazan k’warai sune ake yiwa lale marhabun kaikuwa mai matacciyar zuciya mene ne abin faranta maka anan ko ance maka ni ina sha’awarka ne?”

Ta d’auko pilo ta koma Palo, kan wata doguwar kujera da ita kad’ai ce a palon sai kwanukan wanke-wanke da randar ruwa, kwanciyar tayi tana jan tsaki lokaci-lokaci har bacci yayi awon gaba da ita.

Washe gari asubar fari, Aisha ta riga kowa farkawa, waigawa tayi taga babu mama, ta fara dukan baba tana cewa “ina maman? sarai ya jita, dan haramar alwalah yake shirinyi ta tashi,

A hankali Aishan ta sakko ta taho parlo tana ganin maman tace “to kekuma meya kawoki nan?”

Jin shiru bata ansa ba, da alamun baccin har yanzu dad’insa takeji,

Aisha ta d’ibo ruwan randar k’asa ta juyewa mamanta a jiki, da sauri maman ta tashi zaune tana goge fuskarta da gefen zani tace “dan ubanki me yasa baki kwarawa ubanki ba saini da kika Raina?”

Shima ina nan zuwa gurinsa ai, naga kuma taimakonki nayi tunda kinaji ana Kiran sallah kikak’i tashi”

Maman na mik’ewa ta wanka mata mari tare da cewa “gaba ki k’ara”

Tsalle ta dingayi tana 6arin kwanuka had’i da wurgi da tukwane, a ranar dai anyiwa Aisha duka tun kafin gari ya waye.

Malam Haladu na kwance yana jinsu ko uffan bai ceba, har Saida ta gama dukan ya fito,bai kulataba ya wuce gurin alwalah.

Tunda yayi alwalah ya wuce masallaci.

Gari na wayewa ya dawo gida, zama yayi a tsakar gida kan kujera y’ar tsugunno ya zabga tagumi, fitowa mama tayi tana cika tana batsewa, tazo gaban malam Halatu ta tsaya kana tace “mene ne nufinka? mun kwana bamu k’oshi ba yanzu ma sokake ka horamu?” ta k’arashe maganar tana yatsina fuska.

“Uhm maman Aisha bazanso mu zauna da yunewa ba, amman idan bani dashi fa?” wata wawuyar cafka takai masa kana ta shak’e kwalar  rigarsa tana cewa “banda mutuwar zuciya irin taka da kanada iyali kana wani cewa baka da kud’i mazan k’warai na zuwa neman aiki kaiko kana gida idan y’an uwana sun bani muci idan basu bani ba mu zauna haka, to wallahi na gaji”.

Malam Haladu dai baima waigo ba bare ya kalli fuskarta,

Zuwa rana wajen 11:34am malam Haladu ya fice daga maman Aisha sai ita Aishar, suna zaune tun safe babu abinda sukaci, sai kame-kame wanda aka sabayi, gurin tukunyar Aisha tayi kana ta bud’e tukunyar tana cewa “mama tsakin ya tsotse”

“Sauke”

Mama tace tana daga zaune, bayan ta sauke ta zuba musu a kwanuka biyu, daga ganinsa ma a iya su biyun koda sunci ba lallai bane ya ishesu, sunfara ci kenan Baaaba Indo ta shigo hannunta rik’e da dubu d’aya, bayan tayi sallama tace “Maman Aisha ko kinada canjin dubu guda?”

Maman Aisha ta rik’e baki kana tace “wuuuu dubu guda fa kikace, d’in mik’o min it’a insa albarka dan rabona da ganinta nakai wata”

“Wallahi ke kikaga dama ga mata nan masu maza wanda suka fiki hali  suna bara amma ke kin zauna, aiko zakiga zama, shi mijin da kike tak’ama dashi gayican a k’ofar gida yana zaune gurin y’an kashe wando”

Maman Aisha ta dafe k’irji kana tace “Aiko banga ta zama ba, tunda abinda ya za6a kenan ni na zamo mijin shi ya zamo matar inhar zamuci musha mu tsira da mutuncinmu”

Baaaba Indo tace “wane irin tsira da mutunci a harkar bara nasiyi akuya nasiyi fili ke har zannuwa na samu, ga wani alhji shahararren mai kud’i kullum yazo saiya fillo mana y’an dubu-dubu”

Maman Aisha ta zabura kana tace “aiko zan biki amma bari ya shigo”

Baaaba Indo ta tafi tana mitar cewa “shi mutuwar zuciya kema haka kikeso ki zamo kenan?nikam bazan dinga jira ba” tayi gaba.

Tana fita Aisha tace “wallahi mama Baaaba Indo ta kawo shawara sai ki mak’ale idonki d’aya ki dinga bara ni zanyi miki jagora inmuka tara kud’i mudingacin abin dad’i”

Suna cikin magana malam Haladu ya shigo hannunsa rik’e da bak’ar leda, da gudu Aisha  taje ta anso tana cewa “oyoyo baba”

Fuskarsa d’auke da murmishi yace “yauwa y’ar baba d’aukomin kujera in zauna”

Bayan ta kawo masa, mamanta tayi masa sannu ciki-ciki, ba yabo babu fallasa ya amsa yana fito da shinkafa da wake da manja da magi had’i da attaruhu da albasa,yace “ayi maza a d’ora mana abinci Allah ya kawo”

Jikin Aisha na rawa tace “mama yau zamuci shinkafa “maman ta bige bakinta kana tace “dan ubanki tunda kin wuni da yunwa dole kiyi magana, Allahn daya haliccemu yabamu munci munsha, ace tun safiya har 12:pm mutum bai k’arya ba Sai kace d’an boko, gara ma y’an bokon sunacin mai maik’o mukuwa wataran ma abincin babu magi”

“Innalilahi wa inna ilaihir raji’un, malam Haladu ya furta tare da dakatar da ita yace “ya isheni haka!! bakisan wannan gorin da kikeyi min yana konamin raiba bakisan tafarfasar da zuciyata takeyi ba, sam wad’annan kalaman basu kamaceki ba”

Malam Haladu na yin shiru tace “abinda kayi ake fad’a, akwai k’arya a ciki ne?” Ko kanada zuciyar nema? acikin abokanka akwai wad’an da suka yi gida da mota wasu har k’asar waje sunje, kaiko baka ma da muhallin kanka bare asa ran zaka taimaki wasu”

Dafe kai malam Haladu yayi zuciyarsa babu dad’i, yakawo masifa bai kawo bama masifa,

Suna cikin haka Aisha ta fice da gudu, zuwa anjima sai gashi an tasota a gaba wai ta fasawa wani d’a goshi, baba yace “Dan Allah kuyi hak’uri kasoshi a barbad’a masa garin ganyen kurna”

Mama ta mik’e tsaye cike da masifa tace “tsoransu kakeji da zaka wani magiyar basu hak’uri?”

“Idan d’anka ne da laifi dole kai zaka bada hak’uri dan haka ki dakatamin”

Aisha kuwa tanata tsalle inda kasan batasan komai ba,

Yaran na tsaye har malam Haladu ya gama basu hak’uri suka fice.

Aikin Aisha kenan kullum sai an kawo k’ararta gida, duk ranar da ba’a kawo ba kuwa bata da lafiya.

“Zaki d’auki kayan cefanen ki girka ko kuma kina ganin in koma dasu”

Malam Haladu ya fad’a a hassale,

“Yo aiba yau ka fara komawa dasu ba”

Ta fad’a tare da shigewa d’aki.

Gurin had’a wuta yaje ya had’a kana ya kira Aisha yaja mata kunne akan neman magana, sannan yace ta tayashi d’ora girki, babu abinda ta iya sai jajjaga kayan miya, iya shid’in tayi ta fice,

Sai daya gama had’a sanwa sannan ya fice yabar gidan.

Maman na ganin ya  fice ta fito tana cewa “ni wallahi sakina nakeso kayi inkuma kak’iji bazakak’i gani ba”

Ta nemi guri ta zauna, da ruwan ya tafasa ta wanke ta zuba ko tsincewa batayi ba,

Sai dare akaci abincin dan hatta Aishar ma sai dai in a yawonta taci dan bata, bata ba.

A wani kwano kamar na bola aka sanyawa malam Haladu abinci itakuma ta cika kwano ta koma d’aki.

Washe gari basuda abincin d’umame, iya kacin ragowar wanda ko Aisha taji ba k’oshi zatayi ba..!

 

# Love

# Romantic

# Funny

Zazzafan labari wanda yazo da sabon salo, wanda yazo da gwagwarmayar soyayya mai sanyi, mai sanyaya zuciyar masoya, saboda wannan karon mun ta6o lovers.

 

Domin magana da marubuciyar 08141799224

 

 

 

_Ummu Maheer_

*DINYAR MAKAHO*

 

_Miss Hajo_

*KHADIJATUL SABREEN*

 

_Mrs Bukhari_

*ANGULU DAKAN ZABO*

 

_Ummu Affan_

*SANDAR MAKAUNIYA*

 

_Mom Islam_

*TSAUTSAYIN TAUNA*

 

*Ga tsarin yanda biyan yake*

 

_Guda d’aya 300_

_Guda biyu 500_

_Guda Ukku 700_

_Guda hudu 800_

_Guda Biyar 1k_

 

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

 

0037219728

FATIMA RABIU SUNUSI

StanbicIBTC BANK

 

Shaidar biya ta nan

 

0810 433 5144

 

Masu turo kati MTN ta wannan number.

 

0702 616 6536

 

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

 

0706 860 6171

 

 

 

*TALLAH*

Ina kuke amare uwayen gida kai har ma da ƴan mata? Ko kun san Mrs Bukhari mai kayan ƙamshi, ai in dai batu na kayan ƙamshi gyaran jiki da na ɗaki to kai tsaye ku  ne mi Badi’at domin gwana ce ta ko wanne fanni a ciki. “Wai ƙamshi kina nufin Badi’at dai marubuciyar nan tamu mai nishaɗantar da mu?”

“Tabbas Fati ita take magana, ai kin dai ji yadda ake magana a kai na, hatta me gidana ya jinjinawa Badi’at domin duk wani ƙamshi da zaki ji a jikina tare da gidana to daga ita ne, ke me kankat ma har gyara na nake yi domin gyaran aurena daga gareta ne, shi ya sa bana wasa da gyaran jikina da na gidana har kuke kirana da ƙamshi.”

“Eh tabbas nima na jinjina mata, kuma zaki bani addireshinta domin nima na kwankwati wannan garaɓasa. Ko zaki iya faɗa mini abubuwan da take sayarwa.?”

“Bari na faɗa miki akwai…

 

Humra

Kulacca

Sudanese Humra

Kulacca ta gashi.

Turaren wuta ɗan gaske, iri daban daban.

Turaren mopping

Room freshner

Turaren turara kaya.

Turaren wuta na toilet

Sannan akwai ingantaccen maganin infection

Ina da magungunan mata, wanda zai gyara amarya da uwar gida.

Wanda zasu shiga daga ciki kuma

Akwai sabulun amare, da dilka ta amare, wanda zaisa amarya ta fito ta haska tas

Kabbasa

Setin kujerar tsugunno

Sannan inayin turaren wuta da kasko, da ashana wanda ake rabawa a taron biki ko suna.

Ina bayar da sari.

 

Ma sha Allahu to taya zan sameta domin mallakar nawa?

 

“Kai tsaye zaki mata magana ta whatsApp ko kiranta ta wannan number.

 

08179523215

 

*TALLAH*

A yau nazo muku  da manya manyan magunguna domin gyaran Auranmu! Saboda yadda zamantakewarmu ta AURE keta kara tabarbarewa. Mata iyayenmu ku fito ku gyara jikinku , domin wallahi har Abadan macen da bata gyara bata isa ta hada kanta da mace me gyara ba har abadan! Mu gane yaku yan uwana mata, ma’aurata! wallahi gyara shine mace Akwai mata dayawa dasuka san magunguna na, a online Suna siya kuma Alhmdulillahi ba wadda ta siya bata dawo tamin godiya ba, Alhmdulillahi!Alhmdulillahi! Alhmdulillahi! Yawancin mata dayawa na nemana ta dayan sim dina sede nayi losing dinsa sede wannan shi yake Aiki 08104335144, A YAU NAZO MUKU DA MAGUNGUNA INGANCI DA IZININ UBANGIJI, WATO AINIFIN HADI Iri ~iri na MALLAKA D’ANA MIJI ALFARMAR ANNABI SAW, ina tabbatar muku da magunguna na babu shamaki base na tsaya bata lokaci a bayaniba zanso ku gwada dan tantance GASKIYA * Akwai cututtukan dake hana maganin mata aiki idan kinason sani ki tuntubeni ta wannan lambar 08104335144 wadannan cututtukan inhar kinadasu wallahi duk maganin daza kisha bazeyi Aiki ba, kuma bazaki taba fahimtar komiba a harkar dadih na magungunan mata.

 

*MUNADA MAGUNGUNA AVAILABLE KAMAR HAKA*👇🏽

 

*ingantaccen maganin infection *

 

Ingantaccen maganin basir

 

Ingantaccen maganin gyaran nono

 

Ingantaccen maganin gyaran hips

 

Ingantaccen maganin kara kiba kiyi dumur~mur dake

 

Ingantaccen maganin rage tumbi  meyi tsakani da Allah

 

Ingantaccen maganin matsin  farji mesa dadin farji ga azzakarin d’ana miji.

 

Ingantaccen MALLAKA TA DOMIN ALLAH (Bata harkoki) shine sunansa, hmmmm Wannan magani inada tabbaci a kansa shidin hadine kawai na mallakar d’ana miji akwai komi a cikinsa na mallaka hajiya ki gwada kisha mamaki Alfarmar Annabi SAW.

 

Se matsin (GAMADIDI) wannan matsi in kikayi amfani dashi har abadan abidina mijinki baze kawo a gaban wata ya mace ba in har ba gabanki bane wannan inada tabbaci a knsa 💯 kuma wadanda suka saya ma sun kara tabbatarmin da kyaunsa na mamaki.

 

Akwai zallan hadi na amarya

 

Akwai hadi na uwar gida sarautar mata wannan seat ne akwai komi a cikinsa.

 

Akwai ingantattun gumba iri iri kamar haka 👇🏽

 

Akwai gumbar Madara

Akwai gumba me rubutu 🤐

Akwai gumbar kankana

Akwai gumbar giginya (sa megida kuka)

Akwai ingantacciyar gumba me suna (BARIN MAKAUNIYA)

Akwai gumbar hasi

Akwai zallar gumba wadda ita ta rubutuce zallarta zaki ganta baka karki damu Aikin kawai zaki duba 😉

Akwai gumbar gero

Akwai gumbar ridi

Akwai gumbar garin gamadidi  ita ta mallaka ce zallarta.🤐

 

Akwai tsumi iri iri sunansu sha yanzu magani yanzu 💯👇🏽

 

Akwai tsumin kankana

Akwai tsumin baure

Akwai tsumin rubutun Ayar Allah

Akwai tsumin kwakwa

Akwai tsumin giginya

Akwai tsumin GORON SUDAN (wannan special ne dan kudinsa ma daban yake)

Akwai ingantattun magunguna na tada shaawah kama daga na turawa har zuwa na Islamic wato namu na gangajiya. Akwaifa maganin maza madam na hausa dana turawa 😉 duk basuda side effects 👌

 

Akwai rubutun mallaka

Akwai zoben mallaka

Akwai hayakin mallaka

Akwai zani na mallaka

Akwai hadin ci da kaza

Akwai hadin yan shillah

(Muna dafa kaji da yan shillar ma dade sauran abubuwa da dama,)

Akwai dambun nama na mata wanda ke dauke da magungunan sirri na mata mesa tsantsi da laushi da ruwa a farjin mace 😉

 

Akwai magunguna na ban mamaki wadanda base na rubutasu ba saboda SIRRI 😉

Muna aika magungunan mu kasa kasa gari gari *UWAR GIDA KI GARZAYO QUEN SANAF Islamic chemist kise magunguna na ingantattun ne insha Allahu kin wuce takaicin d’ANA MIJI * direct to me 08104335144 muna sauraron masu shawarwari a kan zaman AURE insha Allahu, amma in knsan baki shirya siyan magungunan jima’i ba na mata ko na maza pls karki kirani.

 

 

 

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

 

✨GAWURTATTU BIYAR✨

 

*Zainab Habib (Mom Islam*

 

Page 3_4

Iya Aishar ta bawa ita  kuma ta dama kunun gari,

Zuwa rana malam Haladu ya shigo da fara’arsa, yana cewa “yau dai an bani mashin in dinga kabu-kabu,

Ga mamakinsa sai yaga maman Aisha na fara’a har tana tafi, tare da cewa “Allah ya sanya alkairi kuma Allah ya tsare”

Malam Haladu yace “Amin ya rabbi, ya d’auki hularsa ya fice da niyar zai aiko da kayan cefanen.

Yana fita ta k’walawa Aisha Kira, Aisha na zuwa tace “yau bara zamu Allah yasa Baaaba Indo ta shigo”

Aisha ta fara murna sbda a ganinta zasuyi kud’i su faracin abin dad’i,

Kaya maman ta sauya zuwa had’in gambiza na riga da zani na atamfa ta d’auki sandar da suke dukan 6era ta d’auko wani fasasshen kwano da yagaggen hijabi ta d’aukowa Aisha yagaggen kaya da tsinkakken takalmi maman Aishar ta zumbula hijabi gudun kar a fahimci inda zataje, tana zuwa bakin hanya ta tarar musu mashin suka wuce Kano road, suna sauka a mashin tace ina zuwa malam, ta rik’e hannun Aisha sukaje gurin mabaratan dake zaune a tsallakensu ta aro nera d’ari, bayan tace musu mijinta ya gudu ya  barta sam ba’a jin labarinsa.

Tana kawo masa ya wuce it’s kuma ta dawo ta zauna,

Tun safe suke zaune a gurin babu abinda sukaci, gashi har k’arfe goma tayi shiru,

Cikin ikon Allah wata galleliyar mota tazo wucewa suka mik’e da uban gudu har ana ture-ture, Aisha ko sai cewa take “Alhaji ka taimaki mamana bamu da abinda zamuci jiyama da yunwa muka kwana, babana baya kula da ita”

Cikin d’aga murya take maganar,

Rage tsayin glass d’in motar yayi kana yace “ina yarinyar dake magana?”

Aka nunata, mutumin da a k’alla zaiyi shekaru 60yrs ya ciro bandir d’in y’n d’ari-d’ari ta mik’a wa Aisha, sukuma ya mik’a musu na y’an d’ari biyu yace su raba, ya wuce, aka fara danbe da wata budurwa mai yiwa gurguwa kuma makauniya jagora tace ai kud’in su Aisha yafi yawa, Aisha ta fasawa budurwar baki tana cewa “dan ubanki inda zamu dinga zuwa bara kullum sai mun fiku ciniki yasin mtsw taja tsaki tare da cewa “mama tashi mu tafi”

Mabaratan gurin nata kallon su maman Aisha,

Kasancewar sun sami abinda ya kawosu yasa suka fara tarar mai mashin Dan su koma gida, suna tsaye Baaaba Indo ta sauka a mashin hannunta rik’e da buhu da robar bara,

“Wato ni inacan ina jiranku ashe sammako kukayi y’an duniya”

Maman Aisha tace “hmm Baaaba Indo ko karyawa bamuyi ba shiyasa muka fito wallahi gashi munsami na cefane”

Mai mashin d’in daya kawo Baaaba Indo zai juya tasa masa hannu ya tsaya tace ka kaimu Anguwar Dosa, Baaaba Indo na magana maman Aisha ta haye mashin tana cewa “mayi magana a gida idan kikadawo”

Rik’e da baki Baaaba Indo ke kallonsu har sukayi nisa suka 6acewq ganinta,mabaratan gurin sukace wannan mata anyi y’ar bala’i yasin, anbamu kud’i su  rik’e saboda cuta da son zuciya, Baaaba Indo dai bata nunar da tasan mama ba sbda shiru tayi, dan suka gano ita tayi mata hanyar zuwa gurin masifa ta auku.

Suna isa gida suka tarar da malam Haladu a zaune ya zabga tagumi, maman Aisha tayi sallama har sau uku shiru ko waigowa  beyi ba,

Sai da tace “maa…laam!!” sannan ya d’ago fuska irin ta yanayin cikin damuwa ya sauke ajiyar zuciya kana yace “ina kukaje tun d’azu nake nemanku har can k’asa naje amma ko d’uriyarku babu”

“Nifa bance kayimin tambayar k’wa-k’wa ba, dan haka ka k’yalemu”

Shiru malam Haladu yayi tare da mik’ewa ya shige d’aki ya nemi guri akan kujera ya zauna,

Murya k’asa-k’asa yace “wannan wace irin damuwa ce, sai kace ni kad’ai Allah ya jabarta da talauci, ina zansa kaina, yau na nifa aiki mashin ta 6allomin gyaran dubu uku, gashi ko cinikin dubu d’aya banyi ba” sai ya fashe da matsanancin kuka,

Daga can tsakar gida, maman Aisha tacewa Aisha jeki siyo mana shinkafa mudu d’aya da rabi, ki siyo mangyad’a gwangwani d’aya ki siyo mana kifi na d’ari biyu ki had’o da Maggi da onga kiyi sauri tunda munada itace barin had’a wuta in d’ora sanwa”

Tana bawa Aisha kud’in ta fice da gudu tana murna yau abinci harda kifi shikenan suma sun zamo y’an gayu,

Jiki a sanyaye malam Haladu ya fito, ya tsaya a bakin k’ofa kana yace “maman Aisha a ina kika Sami kud’in cefane?”

“Nifa sa idone bana so, tunda dai kaga an d’ora ai saikayi shiru da bakinka ko? amma zaka wani cikawa mutane kunne da surutu”

Maman Aisha ta fad’a tana gyara wuta,

“Allah ya baki hak’uri”

Kalmar daya furta kenan ya k’ara gaba.

Tsaki taja had’i da buga k’afa tace “wallahi gobe ma saina koma maula ai naga gurin zuwa”

Aisha na dawowa aka gyara kayan miya takai nik’a, zuwa dare ana kiran magrib shinkafa da miya ta kammala danma kafin mai awara ta kawo sunci,

Sai da mama tayi sallah sannan ta raba abinci, yaukam ansawa malam Haladu abincin da yawa, bayan ya dawo daga sallahar isha’i ya shiga da sallama,  ga mamakinsa sai yaji tana cewa “oyoyo da mai gida,Aisha mik’a masa abinci”

“Sannunku” kawai yace dan a inda tayi fara’ar sai abin ya bashi mamaki Dan ba kasafai ake ganin fara’arta ba.

Washe gari asubar fari ta mik’e yau babu dogon bacci, kasancewar ta riga kowa tashi hakan yasa ta share gida ta d’umama abinci, taje tayi alwalah sai da tayi nafila sannan ta tashi malam Haladu, yana tashi yayi alwalah ya wuce masallaci, sai da gari ya waye sannan ya dawo, mamaki ne ya kamashi, ragowar shinkafa da miyar jiya harda ragowa kuma cikin kwana, batare da yayi magana ba bare akuma dank’ara masa bak’ar magana, yasa cokali ya fara cin abincin.

Yana gamawa yayi hamdala tare da tura hannu cikin aljihunsa ya ciro wata kod’ad’iyar d’ari biyar ya mik’a mata kana yace “cefanenku na dare da rana wallahi daga fara aiki da mashin d’innan jiya harta 6allomin gyara”

Ko tanka masa batayi ba ta kar6i kud’in tayi d’aki.

Yana fita suka fara shirye-shiryen barin gidan, kamar jiya shigar da sukayi yauma ita suka mai-maita, wato had’in bauta Aisha kuma da yagaggun kaya haka suka haye mashin suka wuce,

Suna sauka ta mik’awa mai mashin kud’i ta kamo hannun Aisha da d’an buhunsu a hannu ta gaishe da matan gurin, suka amsa mata cikin d’agun kai, Baaaba Indo dataga maman Aisha bata hangots ba, ta sunkuyar da kai,

Juyowar da maman Aisha zatayi sukayi ido biyu da Baaaba Indo, maman Aisha ta washe baki kana tace “Baaaba Indo ashe kinzo”

Bayan sun gaisa ko wacce tasa ido a titi, ita kuma Aisha na tsalle tana cewa “a taimakemu babanmu ya gudu yabar mamanmu da yunwa,

Yau dai kamar anyiwa garin shara Dan masu manyan motocin ma basu wani wuce ba bare susa ran samu, har k’arfe ukun rana su maman Aisha ko sisi basu rik’e ba, malam Haladu ya dawo daga gareji yana daga tsallaken titi, ya hango maman Aisha zaune ita da Aishar a layin mabarata, mamaki ne ya kamashi had’i da takaicin, abinda bai ta6a tunanin zata aikatashi ba, ya taho da gudu zai tsallaka titi mota tayi gaba dashi, da gudu mutane sukayo kansa cikin harda mabaratan gurin dasu maman Aisha, wani mai mashin cewa yake “malam Haladu nefa yanzu na ganshi a tsaye, lallai tsautsayi ba’a samasa rana”

Daga jin  mai mashin yace malam Haladu maman Aisha ta rugo da uban gudu tana ihu ta watsar da buhun da sandar hannunta tana cewa “mijina ne, indai Haladu ne wallahi mijina ne”

Kaff mutanen gurin mamaki ya kamasu kowanne sai kallonta yake, wai ashema tanada miji mijinma mai K’arfi Wanda ba musaki ba,

Kasancewar motar data bigeshi ta tsaya aka sanyashi a ciki suka wuce Giwa hospital harda maman Aisha da itama Aishar,suna  isa  aka shiga dashi, likitoci furr sukak’i kar6arsa, sai sun kawo jami’an tsaro,

Duk da ba wani ciwo yaji ba sai kujewa da yayi a goshinsa amman da alamu yana jin ciwon gurin sosai, Wanda ya bige malam Haladu ya d’aga waya tare da matsawa gefe, ba’a jima ba sai ga abokinsa nan yazo aka shiga dashi emergency room, abu d’aya yake ambato wato kansa, idan ka gansa lokacin da akayi hatsarin bazaka ta6a cewa ya bugu sosai ba, sbda kujewa ne kawai, Amma asalin ciwon yana cikin jikinsa,

Sai da akayi masa allurar bacci sannan suka sami lafiya, doctor daya gama y’an gwaje-gwajensa ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, kana yace “ku biyoni zuwa office,

Da maman Aisha da mai motar wanda a k’alla zaiyi shekaru 35yrs a duniya, suka shiga office d’in, nuni yayi musu da su zauna kafin ya cire gilashin idonsa yace “wato a gwaje-gwajen da mukayi mun gano zuciyarsa na daf da kamuwa da ciwo, gaskiya yana cikin damuwa, ke iyalinsa ce?”

“Eh”

Maman Aisha tace tana gyad’a kai,

Ya rubuta musu magunguna yace suje su siya a cikin asibitin,

Jikin maman Aisha na rawa tace “likita maganin zekai nawa?”

“Dubu goma”

Likita ya bata amsa a tak’aice,

“Ina zuwa”

Mutumin yace tare da ficewa,

Itama maman Aisha fitowa tayi ta koma kan dogon bencin dake k’ofar d’akin da aka kwantar da malam Haladu,

Cikin yanayin damuwa “Aisha tace “mama baban ya mutu ne?”

Muryar mama a dashe tsabar kuka dataci tace “ciwon zuciya ya kusa kamashi”

Aisha ta toshe baki had’i da cewa “mama mu dena zuwa yawon maula kinga baba zai mutu”

Buff ta bige mata baki kana tace “yawon maulan ba taimakonsa mukeyi ba ki gayamin?”

Aisha tayi shiru kamar mai tunanin wani abun,

Wanda ya bige babanta ne suka taho shida abokinsa, mama ta mik’e da sauri, tare da cewa “bawan Allah ansami maganin?”

“Eh zankoma office d’nne”

Ya fad’a a tak’aice,

Suna tafe abokin nasa yace “Alhaji Kabir meka fahimta game da wannan baiwar Allahn?”

Wanda aka Kira da Alhj Kabir yace “Jamil abinda na lura dasu, suna cikin matsanancin talauci, dan a inda na lura talauci yana damunsu,

Isarsu office ne yasa sukayi shiru da maganar da sukeyi,

Doctor yace “Masha Allah amma bawan Allah na jinjina maka, irin namijin k’ok’arin da kayi gurin tsayawa ceto ran bawan Allah, sa6anin wasu mutanen babu tsoron Allah saisu gudu”.

Murmishi Alhaji Kabir yayi kafin yace “inaso ka tsoratar da wannan matar..”

“Ina jinka”

Doctor yace, yana kallon Alhaji Kabir.

“Inaso kasanar mata da cewar zuciyar mijinta tana daf da bugawa muddin bata dena yawon maula ba”

“Ai wannan mai sauk’i ne, karka damu Alhji temakonta zamuyi sai dai ta yi gaggawa gurin kashe zuciyarta a yawon maula”

Likita ya fad’a yana mik’ewa,

A tare suka shiga room d’in da malam Haladu yake, sun sameshi ya farka yana ta d’aga hannu,

Da sauri likitan ya k’arasa tare da zuwa kusa dashi yace “baba jikinne sannu Allah zai baka lafiya”

Malam Haladu yafara magana a sark’e yana cewa “ka..ki..ra..min matata”

Da sauri likita ya lek’a ta window yace “baiwar Allah mijinki na magana”

Maman Aisha ta rugo da uban gudu ta bud’e k’ofar ta shigo tana cewa baban Aisha yadai jikinne ko kanason wani abu ne?”

Duk jerin tambayoyin data dinga yi masa d’aya ya sami damar amsawa yace “banason komai ki mayar da Aisha gurin iyayenta sai kici gaba da yawon maula!! Yawon maula kawai Aisha taji, kasancewar yanzu ta shigo, ganin mama a yanyin damuwa yasata matsa kusa da ita ta kalli Malam Haladu kana tace “baba ya jikin?”

Hannu ya d’aga mata yaci gaba da cewa “ki mayar da ita gurin iyayenta inhar kika barta a gurinki ita kanta yarinyar ba yafemiki zatayi ba”

Dama ba kune iyayena ba? dama baku kuka haifeni ba?!”

Kukane ya kubce mata ta fice da gudu,

Alhj Kabir da Jamil da doctor ta wuce suna ta tattunawa akan inda zasu taimaki maman Aisha da malam  Haladu, ganinta kawai sukayi tana kuka,

“Baiwar Allah jikin baban naki ne?”

Kasancewar ta toshe bakinta da hannu yasa d’aga musu kai kawai tayi sbda kukan dake taho mata.

Alhj Kabir ne ya taso yazo inda take kafin yace “baiwar Allah meya faru?”

“Babu komai”

Aisha ta fad’a a tak’aice.

‘Bangaren Malam Haladu kuwa tari ya sark’eshi hannun maman Aisha a nashi tana rok’on gafara, kalma uku ce ta kuma had’ashi da ita wato, “ki mayar da Aisha gurin iyayenta inyaso kije kici gaba da yawon maula! kamar inda ya fad’a d’azu, sai kuma da yace “ana bina bashin d’ari biyar, sai kuma kalimatu shahada da yayi tare da ambaton lahaula wala k’uwawata illah billah” a gigice maman Aisha tayi waje tana hango doctor dasu Alhaji Kabir tace “ka kasheshi ka huta shikenan dama kaso kasheshi ne shiyasa ka bigeshi, ashe duk maganar da malam Haladu yakeyi suna recording, Jamil ya mayar da waya cikin aljihunsa kafin yace “baiwar Allah inda yayi niyar kashe megidanki wallahi ko saurararki bazaiyi ba, ke bama zai tsaya ku gansa ba Dan haka ki iya kalamanki,

“Wallahi sai ofishin jami’an tsaro ya Bimini hakkina”

Jamil yayi murmishi kafin ya fito da I’d card d’insa yace “shari’a daga nan har kotun Allah ya isa inhar akwai muje tunda ke bakisan tauhidi ba, doctor yaja hannun Jamil tare da cewa “just forget muje”

Kai tsaye suka wuce room d’in suka sami likitoci a kansa, suna zuwa aka rufe masa fuska da farin k’yalle…!

# Love

# Romantic

# Funny

 

Domin magana da marubuciyar 08141799224

 

MOM ISLAM

 

Akwai cakwakiya a cikin labarin, nasan yanzu ba lallai ku fahimci inda muka Dosa ba.

 

_Ummu Maheer_

*DINYAR MAKAHO*

 

_Miss Hajo_

*KHADIJATUL SABREEN*

 

_Mrs Bukhari_

*ANGULU DAKAN ZABO*

 

_Ummu Affan_

*SANDAR MAKAUNIYA*

 

_Mom Islam_

*TSAUTSAYIN TAUNA*

 

*Ga tsarin yanda biyan yake*

 

_Guda d’aya 300_

_Guda biyu 500_

_Guda Ukku 700_

_Guda hudu 800_

_Guda Biyar 1k_

 

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

 

0037219728

FATIMA RABIU SUNUSI

StanbicIBTC BANK

 

Shaidar biya ta nan

 

0810 433 5144

 

Masu turo kati MTN ta wannan number.

 

0702 616 6536

 

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

 

0706 860 6171

 

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

 

_✨GAWURTATTU BIYAR✨_

 

*Zainab Babib(Mom Islam*

 

Page 5-6

Wata Norse ta fito da sauri hannunta rik’e da wayar malam Haladu, mama taje da sauri ta k’ar6a tare da karawa a kunne, “ina Haladun”

Akayi magana daga cikin wayar, cikin kuka mama tace “Allah yayi masa rasuwa” ta kuma fashewa da kuka,

Sai da aka kuma magana a cikin wayar tad’au murya tace “Yaya Tanimu ne?”

“Eh nine kuna wane asibitin?”

“Asibitin giwa” ta bashi amsa.

Ba’a jima sosai ba asibitin ya cika da y’an uwa da abokan arziki, duk wani abu da ake bukata Alhj Kabir da Jamil suke gudanarwa har akayi masa sutura aka sallaceshi, sannan aka kaishi gidansa na gaskiya, Baaaba Indo kuwa tariga da tazo ta kasa shiga cikin asibitin, dataga  an fito da gawar ne ta bisu aka wuce gida.

Aisha kuwa ta riga kowa dawowa  dan anan aka sameta,

Gida ya cika sosai da y’an uwa da abokan arziki, a ranar abinci har  neman gurin zubawa sukeyi, Alhj Kabir kuwa dashi ake komai,

Bayan kwana uku an watse daga zaman makoki Aisha ta rame sosai duk da ba wata babba bace Amma tanada zurfin tunani sosai,

Ranar da malam Haladu ya cika sati d’aya, maman Aisha na zaune a d’aki ita da mak’ociyarta, Aisha ta shigo tana sanye da hijabi har k’asa tace “mama dama baku kuka haifeni ba?”

A razane maman ta d’ago, cikin tsawa tace “seme idan bamu muka haifeki ba, idan kika kuma yimin magana mai kama da wannan wallahi saina sa6amiki”.

Sallamar da wasu mata sukayi ne yasa mama yin shiru suka kar6i gaisuwa,

Baaba Indo kullum sai tazo zuwa yamma ta tafi, Alhji Kabir kuwa har iyayensa sai da sukazo sukayi gaisuwa tare da kawo musu kayan abinci.

Rasuwar Malam Haladu da kwana arba’in wato lokacin mama ta fita daga takaba, saura idda, duk da kwanakin da suka kwashe har yanzu abinci bai yanke musu ba,

Wata ranar Juma’a da misalin k’arfe 1:30pm, Zaune Aisha take a cikin d’aki ita kuma maman tana parlo, kamar kullum taci kukanta ta gaji, duk wata tsiwa yanzu babu wani lokacin ma tayi ta rok’on Allah mutuwarta tunda dai batada iyaye meye amfanin zamanta a duniya.

‘DAN ‘DANO💞

Gidane had’adde wanda tsayawa misalta kyawunsa sai mu cika pegi bamu gama ba, zaune suke a babban parlonsu wanda yake da girma sosai, shi kansa parlon abin tsayawa a kalla ne sbda ya tsaru iya tsaruwa, wasu mata ne  zaune a kujera guda su biyu, daga can gefe kuma wata tsohuwace wacce a k’alla zatayi shekaru 70 a duniya, sanye take da riga da zani na atamfa ta kwafa d’aurin d’ankwali abindai gunin ban dariya, kallon matan tayi kana ta Kira sunan d’aya daga ciki tace “Sajida kin wani zauna kin zubawa talabijin ido sai kace yau kika fara kallo ga aiki can a kicin kamar zai kashe uwani me aiki” wacce aka kira da Sajida ta yamutsa fuska tare da cewa “Hajiya mama damafa an kawo uwani ne dan mu huta da wasu aiyukan”

“Ah lallai bari kabiru ya shigo zanyi masa magana idan ya koreta sai ku huta”

Takuma cewa “kekuma Nafisa kitashi ki d’orawa Kabiru abin bud’a baki kinsan dai yau ya kammala azuminsa”

Wacce aka kira da Nafisa ta mik’e da sauri tabar gurin tana gunguni.

Alhaji Kabir babban d’an kasuwane, sana’arsa itace siyarda atamfofi da shaddoji, a Kano yanada manyan shaguna har guda biyu, haka ma a jos yanada shago d’aya, a nan Kaduna yanada shaguna biyu, inda Allah ya yalwata masa arzik’insa, bayan rasuwar mahaifinsa ya d’auko Hajiya mama ta dawo gidansa, wato mahaifitarsa, shi kad’ai Allah yaba Hajiya mama, gashi bata son taga ansami koda nera biyar ne a gurinsa, Allah ya zubawa Hajiya mama k’ananun magana ga gori da sa ido uwa uba wataran ta fasa ihu tace baka bata abinci ba, wannan kenan. Sajida itace babba a halin yanzu bata da d’a ko d’aya, Hajiya mama tasa Alhji Kabir k’aro aure akan Sajida bata aihuwa, shine ya auro Nafisa y’ar k’awarta, wani lokacin ta nuna tafison Nafisa wani lokacin kuwa tayi mata tatass, watan Nafisa bakwai tayi 6ari tun daga nan Allah bai sake bata ciki ba.

“Au eyye, harkinyi samun gurin da zaki dinga yimin k’ananun magana kenan nagode babu komai, kuna yaran mata bakusan inda zaku kula da mijinku ba, wani sa’in ina fad’ar gaskiya ana ganin laifina”

Dole suka watse dukkansu suka bar mata parlon taci gaba da surutunta ita kad’ai,

K’arfe 8:pm bayan Alhji Kabir ya shigo, sai da ya fara shiga d’akin Hajiya mama sannan ya mik’e zai fita ta tsayar dashi, dawowa yayi ya zauna kafin yace “Hajiya kinsani na dawo?”

Eh dama dalilin dayasa na dawo dakai shine, gara ka zauna musha hira tunda dai ba wani abun suke tsinana maka ba, aihuwar ma basuga dama ba, yo banga amfanin shiga d’akunansu ba, sai dai suci suyi Kashi su juya d’uwaiwaka dan iskanci”

Kan Alhji Kabir a k’asa yace “Hajiya dole fa aba kowacce hak’k’inta wanda Allah ya ratayamin”

“Kabiru kacemin wa’azi ka koma yi aibansan wa’azi ka koma ba sai yanzu, ni zaka gayawa hak’k’i? to nace yau ka huta maza jeka, d’akinka ka kwanta”

Har ga Allah wani sa’in yanajin haushi idan tana yi masa haka, dayake mahaifiyarsa ce koda yayi fushi dole yake sakkowa.

Yana fita ya shiga d’akin Sajida, sanye take da sleeping dress pink color rigar mai shara-shara, ana iya hango komai na jikinta, da sauri ya k’arasa tare da rungumeta kasancewar tana tsaye tana jifansa da murmishi, yana rungume da ita ta dinga matsawa a hankali suna tafiya har suka zube kan bed, takai bakinda dai-dai saitin kunnensa ta rad’a masa “ina alfahari da samunka, hasken idaniyata  anurin raina, tabbas samun miji irinka shine abunda mata da yawa suke fata na sameka hakan ya sanya nakejin kamar nafi ko wacce mace sa’a a duniya, ina alfahari dakai mijina ilove you”

Kiss ya bata tare da cewa “love you too my sweet heart”

Suna rungume da juna wayarsa tayi ring, gyara ruk’on da yayiwa Sajida yayi da hannunsa na hagu ya d’aga wayar da hannunsa na dama, kafin ya d’aga sai da ya duba number yaga babu suna, yana d’agawa, daga can 6angaren akace “hubbil khairi nayi kewarka fa”

Da sauri ya sake Sajida tare da kallon number ya kara wayar a kunnensa ya kuma mayarwa kunnensa a karo na biyu kana  yaci gaba da cewa “ban gane dawaye nake magana ba”

Daga can 6angaren wacce ta kirashin tace “kana magana da Safiya, nasan bazaka ganeni ba, amma inaso kasani soyayyarka tana neman hallakani sbda kar in cutar da kaina da yawa yasa nanemi numberka na kiraka pls ka yarjemin”

Ta k’arashe maganar tana jan numfashi.

“Mtsw karki sake Kiran wannan layin ban sanki ba”

Yafad’a ransa a 6ace.

Tare da cilla wayar gefe,

Tashi d’aya mood d’in Sajida ya sauya, sosai kishi ya cika mata zuciya, ta juya baya alamar tayi fushi, a hankali ya isa gareta yana bubbuga mata baya, kana yace “haba sweetheart akwai wani albishir da nakeson yi miki?”

“Ina jinka” ta fad’a batare da ta juyoba,

“Mezai hana muje gidan marayu mu d’auko yarinya koya kika gani?”

Da sauri ta juyo kana tace “ina rok’on Allah ya bani nawa basai munje can ba”

Dole ya hak’ura da shawarar tunda dai batayi na’am da zancen ba.

Sai da yaci abinci ya k’oshi sannan yayi brush yazo ya rungumeta suka kwanta, tayi nisa da bacci sai ta dinga mafarkin wani mutumi na binta da wuk’a, sosai ta firgita ta tsala uban ihu wanda yaja hankalin Hajiya mama da dama rabi bacci rabi sa’a ido takeyi.

Washe gari da asbha bayan sunyi sallah Alhji Kabir ya dawo daga masallaci, dama al’adarsa idan ya dawo daga masallaci sai yaje ya gaisheda Hajiya mama da Nafisa sannan ya koma d’akin Sajida kuma duk wanda yake d’akinta ba itace da breakfast ba, yana shiga ya sami Sajida kwance tanata juyi akan kafet, da sauri ya k’arasa gurinta jikinsa na rawa ya fara tambayarta, “Sajida meke faruwa?”

Toshe bakinta tayi sbda amai daya taso mata, tayi toilet da gudu, amai ta dinga kwarawa kamar zata amayar da y’ay’an hanjinta, sai data d’auraye bakinta ta juyo ta ganshi jingine a bango kamar zaiyi kuka, ” Sajida kifad’amin abinda ke damunki” yayi maganar ne cikin wani irin yanayi”

Ya rungumeta suka dawo bedroom, hijab d’inta ya d’auka kana ya taimaka mata tasa suka fito parlo, samun Hajiya mama sukayi tana zaune tana sana’ar tata wato kallo, “ina kuma zuwa da sassafe?”

Ta tambayesu tana mik’ewa tsaye,

“Hajiya sai amai take zamuje asibiti ne a dubata”

“Ashsha! koda kunje ya wuce suce shawara”

Ita dai Sajida datagaji da tsayuwa ta zauna tana dafe da kanta,

“Honey ina kuma zakaje da sassafe?”

Nafisa ta tambaya tana kallon Sajida,

“Zamuje asibiti Sajida batajin dad’in jikinta”

“Oh Allah sarki barin d’auko hijab sai in taimaka mata” ta k’arashe maganar tana yatsina baki, kafin tace “sannu anty”

Cikin k’arfin hali Sajida tace “yauwa”

“To bazakije ba, nace bazaki ba taje ita da mijin nata taji da kiti fifin munafurcinta”

Nafisa ta sosa kai Dan ba haka taso jiba.

“Allah ya kiyaye hanya”

Hajiya mama tace tana ke6e baki.

Kai tsaye suka wuce parking space, d’aya daga cikin motoci biyun dake jere ya d’auka, suka tafi a ita, kai tsaye suka wuce GIWA hospital, wato asibitin da Malam Haladu ya rasu, kasancewar a iya zirga zirgar da sukayi ya sama da doctor d’in,

Bayan yayi parking ya dinga jerawa Sajida sannu, gyad’a masa kai kawai take har suka isa office d’in doctor,

Bayan sun gaisa ya sanar masa da matarsa ce babu lpy, file aka bud’e musu sannan yace suje test, bayan anyi mata abubuwan daya kamata, Norse d’in tace musu su nemi guri su zauna, bayan wasu lokuta results ya fito ta kai can office d’in kana tace “suje can akwai bayanin da za’ayi musu,

Hanunta ya kama suka shiga office d’in, doctor yayi musu nuni da gurin zama,

“Congrats madam tana d’auke da juna biyu”

Alhj Kabir ya juya yaga babu kowa, a tunaninsa ko da wani doctor yake magana, ganin shi yake mik’awa hannu yasa shi, mik’a nashi hannun da rawar jiki,

Doctor ya kuma nanata “congrats ina tayaka murna ya mik’a masa results kafin yace “mahaifarta bata da k’wari, akwai buk’atar ta dinga samun hutu tare da yawan bacci, da kuma cin y’a yan itace, karta dinga d’aukar abu mai nauyi”

Jikin Alhji Kabir na rawa fuskarsa cike da farinciki yace “insha Allah wannan ai duk mai sauk’i ne, mungode doctor, kuje pharmacy ku kar6i magani ga  card, suna zuwa aka basu maganin tare da jaddada mata ta yawaita shan ruwan gishiri da sugar, daganan suka fito, kana suka shiga mota, suna cikin tafiya ta hango mai yalo, “uhm honey yalo zanci” mamaki ne ya kamashi sbda bata cinsa kwata-kwata, tunowa da juna biyun dake cikinta yasashi saurin parking ya lek’a ta k’ofa yace “mai yalo..!” mai yalo ya rugo da gudu yana gaishe da Alhj Kabir,

“Duka na nawa ne?”

“Na dubu d’aya ne”

“Ok juye mana a leda”

Alhj Kabir ya mik’a masa 1500, mai yalo yace “na dubu d’aya nefa”

“Eh nasani wannan na baka ne”

Mai yalo yayi godiya tare da sanya musu a leda yayi musu fatan sauka lafiya.

Suna cikin tafiya Sajida ta kwantar da kanta jikin kujera, har suka iso bata saji ba.

Bayan ya shigo gidan yayi parking, ya dad’e yana k’arewa fuskarta  kallo, hankali ya shafi gefen fuskarta tare da manna mats kiss a kumatu, a hankali ta bud’e ido da fuskarta datayi fayau tace “harmun iso”

“Eh barin bud’e miki”

Dariya tasa kafin tace “haba sai kace jinjira?”

“Uhm ai kinfi jinjira babyna”

A inda yayi maganar sai ya bata dariya, suka fito a tare, babu kowa a parlon,

Zama tayi tare da jingina da kujerar, “Hajiya..!”

“Nafisa..!”

“Kufito kuji abin farinciki”

Alhj Kabir ya fad’a muryarsa cike da nishad’i,

Har suna rige-rigen fitowa tsabar son jin k’wa-k’waf,

Hajiya mama tana fitowa tace “to muna jinka”

Nafisa ma haka, fuska ba yabo ba fallasa tace “muna jinka”

“Sajida na d’auke da juna biyu”

Ya mik’awa Nafisa results d’in, mood d’inta ne ya sauya tashi d’aya, ita kanta batasan yanayin natan ya sauya ba, sai kuma ta k’ak’alo fara’ar dole tace “wayo dad’i anty Sajida zata haifo mana baby”

Kasancewar babu wanda ya lura da yanayin data sauya suna can suna firarsu da Alhj Kabir da Hajiya mama, ta kalli Nafisa tace “cikin haryakai wata nawa? Wata d’aya ne Hajiya”

Nafisa ta fad’a tana kuma k’ak’alo murmishi, it’s kam Sajida har bacci ya Kuma gaba da ita,

Wata muhimmiyar fara’a Hajiya take ga wani rawar k’afa da take, bini-bini tana d’akin Sajida tana tayata hira, zaman parlo ma tayi masa k’aura.

Washe gari ta kama, lahadi, tun dare aka fara ruwa har asbha tayi ba’a d’auke ba, kasancewar muna watan ogusta, ruwa ake bana wasa ba, Alhji Kabir bai sami zuwa masallaci ba, tare sukayi sallahr shida Sajida, bayan sun idar sunyi adu’oi sun gaisa, yayi mata ya jiki, “da sauk’i” tace masa, har ya murd’a handle d’in k’ofa zai fita tace “honey inason cin tuwon shinkafa miyar wake” angama my baby” kijira zuwansa insha Allah”

Alhji Kabir ya fad’a jiki na rawa ya fice..!

 

# Love

# Romantic

# Funny

 

Domin magana da marubuciyar 08141799124

 

 

_Ummu Maheer_

*DINYAR MAKAHO*

 

_Miss Hajo_

*KHADIJATUL SABREEN*

 

_Mrs Bukhari_

*ANGULU DAKAN ZABO*

 

_Ummu Affan_

*SANDAR MAKAUNIYA*

 

_Mom Islam_

*TSAUTSAYIN TAUNA*

 

*Ga tsarin yanda biyan yake*

 

_Guda d’aya 300_

_Guda biyu 500_

_Guda Ukku 700_

_Guda hudu 800_

_Guda Biyar 1k_

 

Kai tsaye zaku iya turo kuɗinku ta wannan hanya.

 

0037219728

FATIMA RABIU SUNUSI

StanbicIBTC BANK

 

Shaidar biya ta nan

 

0810 433 5144

 

Masu turo kati MTN ta wannan number.

 

0702 616 6536

 

Ƴan Niger zaku turo da naku kai tsaye ta wanna number.

 

0706 860 6171

 

*Mun gode da kasancewa da gawurtattu biyar taku na biyu* 🤘🏿

 

*🫦TSAUTSAYIN TAUNA🫦*

 

✨GAWURTATTU BIYAR✨

 

*Zainab Habib (Mom Islam*

 

Page 7-8

Yana fita kai tsaye d’akin Hajiya mama ya shiga, bakinsa d’auke da sallama, bayan ta amsa ya k’arasa kana ya durk’usa ya gaisheta, gyara zama yayi kana ya kalli agogon wayarsa, “k’arfe 8:30”

“Akwai inda zakaje ne ana tsuga ruwa?”

“Hajiya wallahi Sajida ce tace tanason tuwon shinkafa miyar wake shine nakeson zuwa in sanarwa da y’ar aiki”

“Yo y’ar aikin dana koreta jiya Kuna tafiya?”

Hajiya ta fad’a tana ke6e baki,

Matsalar dai d’aya ce gashi mun Sami k’aruwa dole a nemo y’ar aiki a gidanan kodan Sajida ya’r albarka mai juna biyu”.

Hajiya ta mik’e tana cewa “barinje kitchen d’in in dora mata ahincin”

Da sauri Alhj Kabir ya mik’e shima kana yace “no Hajiya bazakije girki ba zanje in siyo mata”

“Ina babu inda zakaje, jikan nawa zai zo duniya kacemin ba hakaba, kai Kabiru inaga nafika farinciki samun wannan rabo”

Tawuceshi, kai tsaye ya fito tare da shiga d’akin Nafisa, samunta yayi tana waya, yana shiga ta a iye wayar da sauri kamar mara gaskiya, “Nafisa kizo ki taya Hajiya d’ora abinci a kitchen”

Nafisa ta yamutsa fuska kana tace “bacin an kammala breakfast yana dining?”

“Eh nasan da haka kinsan Sajida na d’auke da juna biyu, to shine batason cin komai sai tuwon shinkafa miyar wake shine Hajiya ta shiga kitchen dorawa, kuma ai yakamata kije ki tayata”

“To naji”

Nafisa ta fad’a a tak’aice.

Yana fita ta d’auko wayarta ta danna number Safiya, ring d’aya ta d’aga “Safiya muna cikin waya dake Alhj ya shigo, shin baki kirasa bane ?”

Safiya tayi dariya kana tace “wannan alhjin naku sai ku hmm, yanzu dai me kikeso ?”

“Hmm”

Safiya tace, in inda tayi hakan Safiya ta jiyowa tace kiyi magana kinyi shiru kinsanni bana barin ta kwana,

“Safiya bana son cikin dake jikin Sajida yakai labari bana son d’an data Haifa yazo duniya, saboda zai zamemin ciwo a zuciyata kina sane da bana aihuwa,

Amma na 6oye masa saboda masifaffiyar mahaifiyarsa”

“Nafisa abinda nakeso dake shine, kibar d’an dazata Haifa yazo duniya inyaso sai mubi dare mu kasheshi ba tare da kowa ya sani ba”

Safiya ta fad’a tana tafi alamun duniyar zatayi musu dad’i.

“Nafisa tace “to sis shikenan amma kinsan dole zan ga wulakanci dan har wani rawar k’afa yake a kanta”

Daga nan sukayi sallama.

Har Hajiya mama ta kammala girki Nafisa bata fito ba,

Sai wajen 10:11am, sanye da dogon hijab tayi d’akin Hajiya mama da sallama,

“Antashi daga baccin asarar kenan?”

Hajiya mama ta fad’a tana kai lomar tuwo bakinta,

“Ina kwana Hajiya”

Nafisa ta fad’a batare da koda ruwan fara’a a fuskarta ba,

“Lafiya lau wani abunne ya faru naga kina fushi”

Mik’ewa Nafisa tayi, har tazo bakin k’ofa tajuyo tace “yau zanje gidanmu”

Hajiya mama na sud’e hannu tace “to zuwa yaushe zaki sai in shirya”

“Babu buk’atar kije”

Nafisa ta fad’a tare dayin gaba.

‘Dakinta ta koma ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta shafa mai, kai dakaga fuskarta zaka tabbatar yau babu lafiya, don ko fara’a batayi, bayan ta gama kwalliya ta bud’e drowa ta ciro leshi mai ruwan k’asa anyi masa aikin wuta a wuyan rigar, kasancewarta fara, sai leshin yayi mata kyau, a yanayin inda akayi d’inkin ma ya zauna a jikinta sosai.

Humra ta d’auka ta goga a jikinta kana taje gurin mayafai ta d’auki fari mai duwatsu da takalmi fari mai tsini ta d’auki wayarta ta fito parlo, Sajida da Hajiya mama ne zaune a kan doguwar kujera, sai da Nafisa ta ke6e baki sannan ta k’arasa tace “sannu anty Sajida ya jikin”

Fuskar Sajida d’auke da far’s tace “youwa Nafesa anguwa zakije ne?”

Hajiya mama tace “ni naga tijara wai Nafisa ni take cewa bazan bita ba?”

Sajida tayi murmishi sbda ada inda wacce Hajiya mama ta tsana bai wuce ita ba yanzu Kuma tana ganinsu a rana tunda batada hak’k’insu,

“Sai na dawo”

Nafesa tace tare da ficewa batajira amsaba.

Tana fita Hajiya mama tace “shegiya juya”

“Innalilahi, haba Hajiya mama wannan aihuwar da aketa magana a kanta fa Allah mai bayarwa, bawai dan baya son bawansa bane take hanashi, sai Dan gwada imaninsa, wasu zasu d’auki tsawon lokaci basu aihu ba, wasu kuma zakiga kamar a bakin k’ofa suke tuntu6e dashi, akwai wanda sam harsu koma ga mahaliccinsu bazasu aihu ba, to mezasuce?”

Hajiya mama tace “wato kina nufin ni inayiwa Allah butulci kenan?”

Sajida tace “a’a Hajiya mama inhar maganar ta 6ata miki kiyi hak’uri”

GIDANSU Nafisa.

Horn driver yake a bakin wani tangamemen get, ga dukkan alamu gidan yafi na Alhj Kabir, sbda shima d’in an narka dukiya babu laifi, ana bud’e get drivern ya shiga da mota, kai tsaye parking space ya tsaya, fitowa tayi mayafinta ninke a kafad’arta hannun hagunta Kuma ta rik’e hand bag, kai tsaye taje bakin k’ofar da zata sadaka da sashen mahaifiyarta, part-part ne a gidan har guda uku, k’ofar farko itace ta mahaifiyarta, ta biyu kuma itace ta kishiyar mahaifiyarta, ta uku, wato amaryarsu, mahaifiyar Nafisa zatakai shekaru 74yrs kishiyarta kuwa batafi 40yrs ba, amaryarsu kuma 20yrs dan yarinya ce,

Hajiya Sakina, shine sunan mahaifiyar Nafisa, tanada yara uku, namiji mai suna Kalil zekai shekaru 35yrs, dagashi sai Nafisa, sai kuma k’anwarsu mai suna Salma wato autarsu shekararta 18yrs.

Kishiyarta kuwa sunanta Hajiya Hauwa, yaranta hud’u itama na farkon namiji ne mai suna Bashir Yanada shekaru Ashirin da biyar 25yrs yayi irin saurin girman nan ne, Wanda idan ka gansa sai ka rantse yayi 30yrs, Dan har yafi Kalil girman jiki, sai k’aninsa mai suna Usman yanada shekaru 15,sai k’anwarsu mai suna Juwairiyya, shekararta 13yrs me binta Husna, itace mai shekaru 9yrs.

Amaryarsu sunanta Hajiya Amina sbda taje Makkah, bata ta6a aihuwa ba, amman yarinyar Hajiya Hauwa Husna tana gurinta.

Kai tsaye Nafisa tashiga part d’in mahaifiyarta, samunsu tayi suna hira sai dariya suke, da alamu duniyar tayi musu dad’i, ko sallama bata tsaya yiba ta fad’a jikin momynta tana kuka, cike da damuwa suka matso kusa da ita, Kalil yace “haba sister menene haka daga zuwa sai kuka?”

Yana idda magana Salma tace “anty Nafisat keda waye?”

Momyn ma takasa cewa komai sai binta da kallo take, daga k’arshe tace “daughter meke faruwa?”

A shagwa6e Nafisa tace “momy ciki ne da Sajida harya fara girma, ni bansan ya zanyi ba, d’an tarairayata da Kabir yakeyi duk ya dena soyayyar ta koma gurin Sajida akan cikin data samu” ta k’arashe maganar tana kuka.

“Eeeeh” ciki fa kikace ?, kice bokanta yayi nasara to inhar tasan wata batasan wata ba, narantse da Allah baza’a haifi wannan yaron a gidan ba, inhar an Haifa to lahira ce makomarsa”

Momy ta fad’a tana jinjina kai.

Cikin natsuwa da sigar kwantar da hankali Khalil yace “haba momy sai kace ba musulmai ba, ke da girmanki kike wannan maganar, kinsan iya adadin zunuban da zaki kwasa kuwa?”

“Kai Ibrahim.! inhar bazaka kawo taka gudunmawar ba to kayimin shiru, wato harda Hajiyar tasa ake sakarcin ko?”

Nafisa ta gyd’a kai da sauri,

“Za suci ubansu basai an had’a da malamai ba wallahi sai sun gane kuransu”

Sai da suka lafa da zancen sannan Salam tayi magana,

“A ganina momy abata maganin da cikinta zai zube wallahi sbda anty Nafisa ta samu kawanciyar hankali”

“Yauwa y’ar gari, kekam halinki abin a duba ne, baza’a bata maganin komai ba amman dai zasu d’an d’ana kud’arsu wallahi”

Sum-sum Khalil ya mik’e a zuciyarsa yana binsu da adu’ar shiriya,

Wuni sukayi hirar Sajida da Hajiya mama da Alhji Kabir,

Sai yamma taje part d’in Hajiya Hauwa, da sallama ta shiga ta zauna akan kujera tana jiran fitowarta, Juwairiyya da Husna suna jinta suka rugo da gudu suka rungumeta suna cewa “anty Nafesa ashe kinzo”

Fuska ba yabo ba fallasa tace “eh mana ai nayi fushi ko kud’an lek’o gidan nawa”

“Anty Nafisa dad ne ya hanamu wai makaranta”

Juwairiyya ta fad’a, tana dariya.

Suna cikin hira Hajiya Hauwa ta shigo, fuskarta d’auke da fara’a,

“Ah Nafisat ashe kinzo amma dai ba yanzu kikazo ba ko?”

“Eh Hajiya na sauka da ciwon kai ne shine nasha magani na kwanta, sai d’azu na tashi”

Nafisa ta fad’a tana rik’e kanta, alamun dai bata da lafiyar,

“Ayya ubangiji ya baki lafiya mai d’orewa ya su Sajida da Hajiyar?”

“Suna lafiya tace tana mik’ewa,

Hajiya Hauwa tace “harzaki wuce be?”

“Eh Hajiya wlh yamma tayi Kuma nice da girki”

‘Daki Hajiyar ta koma ta d’auko wata leda mai d’auke da turaruka masu tsada da kamashi ta mik’a mata tare da cewa “ki gaishe da mutan gidan,

Godiya Nafisa tayi mata tace bari taje part d’in Hajiya amarya, haka suke kiran amaryar baban nasu,

Da isarta tayi sallama ta k’arasa, Hajiya Amina na ganinta ta kwa6e baki kana tace “walkslm sannunki da zuwa yau kece a gidan namu?”

Nafisa ta d’an yi Jim sai Kuma tace “nice”

Mik’ewa tayi kana tace “zan wuce sai anjima”

Batare data jira amsarta ba ta fice sbda basa jituwa, Nafisa na ganin dad ya auro musu sa’arsu, ita kuma tana ganin bazata d’auki raininsu ba.

Part d’in momynta ta dawo a gurguje tayi musu sallama, tare da ce mata duk halin da ake ciki zata Kira a waya,

Tafe suke suna hira ita da Salma har suka isa parking space, motar gidansu ta shiga ta koma gida, kasancewar drivern nasu ya koma can gida.

Sun isa gidan k’arfe 6:40pm lokacin anata kiraye-kirayen sallah,

Da sallama ta bud’e k’ofar parlon ta shiga, turuss tayi ganin Alhj Kabir da Sajida suna zaune a parlo su biyu, yana zaune akan kujera mai zaman mutum uku, ya mik’e k’afafuwansa ita kuma ta kwanta akan cinyarsa hannunta nakan gemunsa, suna dariya,

Wani masifaffen kishi ne ya taso tare da tokare mata wuya, cikin masifa tace “to dai sallah ake masoyan asali sai a tashi ayi ibada”

Tana kaiwa nan ta shige,

Tana zuwq d’akinta ta cillar da wayarta da handbag d’inta a kan gado, ta ajiye mayafin a gefe ta zame d’ankwalin kanta, cikin yanayin damuwa da tashin hankali tace “wai sosuke su haukatani?, dama haka abun yake? meyasa Kabir ya koma kamar wani Wanda bazai iya control d’in kansa ba?”

Ta fad’a tana juyi a tsakar d’akin, “kodai asiri tayi masa?”

Ganin wankin hula yana neman kaita dare yasa ta d’aga waya ta Kira k’awarta, layin a kashe dole ta hak’ura, ta shiga toilet ta d’auro alwalah tazo ta shimfid’a sallahya ta kabbara sallah,

Bayan tayi sallama ta dinga kwararo adu’a akan itama Allah ya azurtata da juna biyu ko hankalin Alhji Kabir zai Kuma dawowa kanta kamar da sai abinda tace,

Sai da akayi isha’i sannan ya shigo, hannunsa rik’e da babbar leda,

Kasancewar a d’akin Nafisa yake ya sashi zuwa d’akinta kai tsaye, da sallama ya shiga ya sameta zaune akan gado tana latsa waya, mamaki ne ya kamashi sbda ba haka suka saba yiba,

Ganin bata da niyyar tasowa yasa ya k’araso tare da zama kusa da ita cikin muryar lallashi yace “haba Feenat d’ina mekuma yw faru?”

Sai da tad’au lokaci sannan tace “komai ma”

“Kinje anguwa kin dad’e gashi Hajiya bata nan taje gidan,Mama Mero, da ita da Hajiya mama, uwarsu d’aya Ubansu d’aya, tana zaune a tudun wada batada miji shima ya rasu, tanada yaro guda d’aya Hashim yana da super market babba, wanda take a mazaunin mallakinsa,

Dama abinda take jira kenan tace “kenan babu hali inje in gaishe da iyayena?, ita anty Sajidan a kwance take bata motsi?”

Kamar Wanda aka tunzuro, kamar bashine ya fara lallashinta ba yace “kotanada lafiya fa?, Doctor ya hanata aikin K’arfi, kinsani Hajiya Kuma ta kori y’ar aiki shine kikaje kikayi shiru sai dare zaki dawo ko?”

“Duk cin amanata da kayi bai isheka ba? zakazo kana damuna da fad’a”

Alhj Kabir yace “wato Nafisa wuyanki ya isa yanka, zargina ma kika farayi kenan?, A ina kika kamani dacin amanar taki?”

“Amman dai kasan k’arfe shida nayi ka dawo d’akina ko?”

Alhji Kabir daya fara gajiya da surutu yace “ni na hanaki dawowa?”

Daga haka yaje kan loka ya bud’e flaks na ruwan zafi ya d’auki cup d’in dake gurin ya had’a tea ya d’auki bredi ya koma gefe kan kujerar roba ya zauna yana shan tea,

Da kallon mamaki ta bishi, a zuciyarta kuwa cewa take “a haka zamuci gaba da zama yana gasamin aya a hannu dole in samo mafitar abinyi tunda dai wayar K’awata Salma a kashe.

Kwanci tashi asarar mai rai cikin Sajida yanata girma, ga wani kyau da k’iba data sakeyi, Hajiya mama kuwa kamar zata cinyeta, kullum cikin yi mata hidima take,

Nafisa kuwa, kowanne hali ta tsinci kanta a gidan Sai ta sanarwa da mahaifarta.

Bayan zuwanta gidansu da sati biyu, momy ta kirata a waya, da sauri ta d’aga tare da cewa “aslamu alaikum”

Daga can 6angaren momy tace “Nafisa kina ina ne? idan kina kusada mutane ki kauce akwai important thing da zamu aiwatar, da sauri ta mik’e, kasancewar tana parlo suna kallo, tana zuwa d’akinta ta danna key kafin ta kara wayar a kunnenta tace “momy ina jinki”

Cikin k’asa da murya kamar ta marasa gaskiya, momy tace “Nafisa kinada 50k a gurinki?”

Nafisa ta waro ido tare da dafe k’irji tace “momy ina zanga wanan kud’i, yanzu duk k’arshen watan ma da yake bamu 10k yadena bansan dalili ba”

“To nidai na gaya miki duk inda zakiyi ki samo koda 30k ne kizo muje gidan Hajiya Lami”

Da sauri Nafisa tace “ita kuma wacece?”

“Wallahi mai magani ce daga Niger duk taurin kan namiji da jiji da kansa Tasha gabansa, zata dawo miki dashi kamar k’aramin yaro sai inda kikayi dashi”

Murna ce ta kamata sbda taji cikakken bayanin da momy tayi mata, cikin k’arfafa guwaiwa tace “momy zanyi masa magana koda aro ya bani…?

 



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Tsautsayin Tauna Hausa Novel Complete]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


Powered by: www.mynovels.com.ng

Leave a Comment

error: Content is protected !!