Hausa Novels

Tsayin Dare Hausa Novel Oum Hairan

 _*TSAYIN DARE!……*_

*Oum Hairan*

*H-P Group*

*_1-2_*

______________________________________

Paid book normal 500 VIP 1000 Special 1500 via acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu Umar First bank or 9031307566 Opay, send proof of payment 09013718241.

_______________________________________

Sanyin saukar yayyafin ne ya farkar da ita daga nannauyan baccin da takeyi cikin rumfar aje motocin ta miƙe zumbur cikin muguwar kiɗima da ganin yanda dare ya fara duhu ta zari takalmanta ta saka ta ɗauki ledar da aka zuba mata abincinta t nufi ƙofar fita daga gidan sarautar duk da tasan cewa zatasha tambaya kafin a barta ta fita Bama wannan ne damuwarta ba yanda zata nufi Hayin bayin unguwar da da rana ma ake neman ketawa mata haddi ina kuma ga wannan tsohon daren? 

Tana tafe gabanta na faɗuwa har taje ƙofar karshe bata samu matsala ba Saida taje fita taji wani dogari ya daka mata tsawa taja baya da sauri cikin in ina tace “Kuk kuyi haƙuri Prince Aleey na tsaya jira har bacci ya daukeni nayi dare don Allah….” Bulala ya zabga mata ta ɗiba da gudu tana sosa wajen tana hawaye ta nufi hanyar da zata kaita unguwar su zuciyarta cike da zullumi tare da addu’ar Allah ya tsallakar da ita sharrin su goga tasan goga rayuwarta yake nema.

Da dabara ta rinƙa bin lunguna har ta samu ta fito daga lungun da suke tare mata suke ƙwaƙulewa ta kuma kwasa da gudu bata tsaya ba Saida taje gida ta banƙaɗa labulen asabarin dake ƙwar gidan ta shiga tana haki Iya ta tareta da sauri tace “Maimoun meyesa kike kaiwa dare yanzu ke bakijin tsoron yaran nan su Goga su tareki suci mutumcinki?”

Zama tayi tana sauke ajiyar zuciya ta buɗe ledar suka juye abincin Gwaggo ta ɗibarwa Baffa ta adana tazo suka zauna sunaci uwar ta sake kallon ƴar tata tace “Hammanat meye yasaki kaiwa dare yau ma? Meyasa duk maganar da nakeyi Miki bakiji?” Sunkuyar da kanta tayi tace “Ba laifina bane Gwaggo ɓangaren Prince Aleey Fulani ta mayar dani kinsan jiya ya dawo to shi tsarinsa ba’a tafiya sai yayi umarni shine na tsaya jiransa kuma bai fito ba har bacci ya daukeni a rumfar motoci Saida aka fara yayyafi na tashi” Numfashi Gwaggo ta sauke tace “Kidai rinƙa kiyayewa rayuwar nan sai kanayi kana tattalin lafiyarka gidan sarautar nan tamu basu da tausayin talaka Banda haka meye na cewa sai an wani jira shi ya shige ya manta dake nifa wlh na gaji da wannan bautar Don dai baffanki yaƙi ne da ya barki kinyi zamanki kina zuwa makarantarki in Allah ya kawo miji kiyi aurenki” 

Turo baki tayi gaba tace “Nifa gsky Gwaggo ki bari ke baki da aiki sai kice aure meye wani aure nawa ma nake nifa ki daina Allah! Allah ki daina zanyi Miki kuka….” 

Jifanta tayi tana cewa ƙundun ubanki nace yo in bamu auraddake ba kwaɗaki zamuyi muci?” 

Zagaye ɗan ƙaramin tsakar gidan suka rinƙayi suna dariya rayuwarsu me cike da nishaɗi talaucinsu bai hanasu walwala da wannan sukayi sallah Hammanat ta watsa ruwa suka kwanta batasan sanda babanta ya dawo ba sai da asuba da Gwaggo ta tashe ta sukayi sallah yanayin

Iyayenta ya nuna mata da damuwa bayan Baffa ya dawo daga masallaci suka gaisa ya fara yi mata darasin addini lura tayi da mahaifin nata yana ɗauke hawaye a idanunsa ta rufe littafin ta kama hannunsa tace “Nayi maka laifi ne Baffa ” girgiza mata kai yayi ya miƙe ya nufi ɗaki ta riƙo hannun Gwaggo idonta ya kawo ruwa tace “Me yake damun Baffa Gwoggo bantaɓa ganinsa a wannan yanayin ba” kama hannunta tayi ta miƙe suka nufi inda ta haɗa mata ruwan wanka takai mata bayi tace “Ya zamuyi haka Allah ya tsara mana rayuwa a ƙasan mutanen da basusan darajar ɗan Adam ba Hammanat duk daren da kikayi a gidan sarauta kina jiran fitowar Prince Aleey hakan baisa mun tsira daga cin mutumcinsa ba ashe bayan tahowarki ya tambaya kina ina akace kin tafi shine yace a faɗa masa waye ubanki a wannan gida da zaki tafi bai fito ba.

Mahaifinki yana can yana yiwa Dawaki wanka kira ya isheshi yazo maza Prince Zaki na kiransa, haka ya taho yana zuwa kafin yakai ƙasa Wai yaron nan Aleey bai duba girma da furfurar kan Mal Ibrahim ba ya ɗauke sa da mari ya hau gaggaya masa magana yana cewa tunda bai baki tarbiyyar mutunta umarni ba shi yaje ya ƙarasa aikinki da kika tafi kika bari! Haka mahaifinki yaje ya durƙusa ya goge masa takalminsa yana hawaye ya shiga ya gyara masa ɓangaren da taimakon Kulu jakadiya Hammanat ita kanta Kulu Saida tace da mahaifinki tana tausayinki da aiki a ƙarƙashin bauɗaɗɗan mutum irin Prince Aleey”

Tunda Gwaggo ta fara maganar Hammanat take hawaye daƙyar tayi wankan zuciyarta ta tsaya da bugawa sai lokacin ta samu damar cewa “Nice naja maka Baffa duk yanda kake takatsantsan wajen ganin ka kiyaye mutumcinmu gashi da gajen haƙuri na kaɗan na jaza maka wulaƙanci, dama bamuzo a bayi ba da hakan bata faru ba Baffa kace mu ba bayi bane mu daina yi musu bauta don Allah” 

Dafa kanta yayi yana mata murmushin ƙarfafa gwiwa yace “Insha Allah ƙarshen bautarmu ya kusa Hammanat kije kiyi abinda ya kamaki nidai ina umartarki da kiyaye haƙƙin Allah a duk inda kike tabbas bana ko shakka shima zai kiyaye ki” da wannan kalamin ya rinƙa rarrashinta saidai haka kawai taji ninkin tsanar Prince Aleey ta kwaranye zuciyarta bata taɓa tsanar wata halitta kamar yanda takejin ta Prince Aleey ba ji take dama ace tanada iko ta ramawa mahaifinta wannan cin mutumcin da yayi masa.

Tunawa da batada wannan ikon ya sanyata jin karayar zuciya har sukaje gidan sarautar sharar hawaye take tana riƙe a hannun Baffa har Ɓangaren Prince Aleey yau ma kamar kullum yana filin motsa jiki yanata fama haka suka samu guri suka rakuye tun farkon zuwansu wajen ya lura dasu amma hakan baisa ya tsaya da abinda yake yi ba har Saida ya gaji don kansa a ƙalla awa ɗaya da rabi sannan ya miƙe yana sharce gumi ya ɗauki jacket ɗinsa ya sanya saman baƙar riga vest dake jikinsa ya nufi hanyar da zata sadashi da cikin part ɗin nashi Mal Ibrahim yayi ƙas da murya cikin ladabi yace.

“Allah ya taimake ka me jiran gado haƙiƙa wannan yarinya ta aikata kuskure kamar yanda jiya na nema mata gafararka yauma ina kara roƙonka bisa adalcinka ka dubemu ka yafe mata wlh sharrin ƙuruciya ne Hammanatu yarinya ce ranka ya daɗe batada wani wayo girman jikin ne kawai”

Turus yaja ya tsaya ya kallesu a wulaƙance kamar zai yi magana sai kuma yayi gaba yana jinjina kai wani dogari dake biye dashi yace “Kin samu sassauci darajar me dattin hula yarinya sai a kiyaye gaba” ajiyar zuciya Baffa yayi ya kama hannunta yace “Kiyi masa godiya Hammanatu banyi tsammanin Zaki zai sauka da wuri ba haka don Allah ki kiyaye kuma ki tsaya iyakar matsayinki banson shisshigi da karambani shi ba mutum ne me sauƙin mu’amala ba”

Bata iya cewa komai ba har Baffa ya ɓacewa ganinta Saida taji an taɓata sannan ta dawo hayyacinta Mairo abokiyar aikinta ta gani taja ajiyar zuciya Mairo tace “Ke bansan irinki ba daga fara aiki jiya jiya har kin fara da laifi Hammanat Prince Aleey yaji haushi jiya har dare yana ƙwafa bansan me ya shiryawa laifinki ba amma tabbas bai wucce ba saboda haka ki kiyaye don Allah.

Jan numfashi tayi tace “Baffa ya mara fa Mairo kawai saboda Allah ya basu mulki shine yasasu jin cewa zasu taka kowa?” Fitowar Shamaki ce ta sanyata nufar ƙofar shiga ɗakin tanajin ninkin faɗuwar gabanta cikin Sa’a data shiga babu kowa a babban falo haka ya bata damar fara gyaranshi kamar yanda aka tsara mata bayan ta gama gyarawa ta shiga na tsakiya ta gyara sannan ta isa falon ƙarshe ta gyara shi ta saita komi, tsayawa tayi tana kallon ɗakin gabanta na tsananta faɗuwa ko jiya Saida yace mata kar ta ƙara fita bata shiga ta bashi ruwan wanka ta gyara masa ɗakin ba. Ita kuma sai take ganin hakan kamar baiyi daidai da tsarin addini ba ace namiji kamar Prince Aleey ta rinƙa shigar masa ɗaki kai tsaye idan wataran ta isheshi a yanayin daidai wataran kuma ya zata isheshi?

Tunanin da ta tsayi yi kenan daga ƙarshe dai ta yanke shawarar knowking door ɗin ta ƙwanƙwasa a hankali ta jima tana taɓa ƙofar sannan taga ta kawo green light alamar anyi mata izinin shiga taja numfashi ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama a bakinta a zaune yake ya tusa system a gaba da alamar wani abun yake dubawa ta isa gabanshi ta zube ta kwashi gaisuwa bai tankata ba ta fara dube² da tunanin ta ina zata fara har ya miƙe bata samu abin yi ba ya nufi bathroom ya jima yana wanka kafin ya fito ɗaure da towel yana kallonta da takaici haɗi da mamaki har yanzu tsaye take inda ya barta ji yayi kamar ya zaneta kawai dama kallonsa tazoyi kenan? Iska ya furzar ya dakanta tsawar data sanyata dawowa hayyacinta takai dubanta gareshi tare da rintse idanun da sauri jikinta ya fara rawar mazari tunda Gwaggo ta haifota ta kawota duniya bata taɓa ganin ƙaton namiji a tuɓe haka ba sai yau jin hucin mutum a kusa da itane yasata matsawa ya damƙi hannunta ya matsa da ƙarfi ta saki ƙara ya ɗora mata hannu a baki yace “Kar kiyimin kuka zanci ubanki ne kawai” haɗiye kukanta tayi ya saketa yace “Dan uwar ki ni dodone da zaki kalleni ki rintse idanunki?” Girgiza kai tayi ba tare data buɗe idon ba ya kuma daka mata tsawar da saida fitsari ya kusa ƙwace mata ya saketa yace kafin na gama shiryawa kiyiwa gurin nan hankali” daga haka bai ƙara magana ba yaci gaba da shirinsa dole ta fara tattare takardun data gani a ƙasa ta fara laluben gurin zubasu bayan daƙyar ta gano inda suke ta mayar dasu daidai lokacin daya fita ta samu damar gyara ɗakin tsaf ta wanke masa toilet, duk inda Prince Aleey yake yakai me tsafta komansa a nutse yake. Haka ta gama gyara masa ta kunna masa turaruka ta fesa wasu ta fice daga ɗakin ta koma kitchen ta ɗauko break ɗinsa ta shirya masa hatta zubawa ita ce, duk a gundure takeyin aikin saboda ta gaji da wannan al’alar.

Komawa tayi ta zauna ya gama yauƙinsa sannan ta ɗebe sai lokacin ta samu damar sakewa daya tafi gaida iyayen sa ta zauna tana gwada yanda yake wani ciccin magani tare da yin ƙwafa a ranta tana cewa “Haisam ma ya fisa kyau shi me fara’a amma shi sai kace sa sai wani ciccin mazu yakeyi” 

Tananan zaune har Azahar hantsi ya fara duba ludayi ta fara hamma ta miƙe so take ta tafi madafi ta karɓo abinci tana jin tsoron ta tafi ya dawo yaci mutuncinta haka tayi ta zaman jiransa bai shigo ba sai wata baiwa Jummala da suke a madafi ce ta shigo da kayan abinci ta miƙa mata tace “Fulani Babba ce tace a kawo Miki” karɓa tayi da sauri ta buɗe gurasa ce da miyar taushe sai ƙamshin man shanu yakeyi aikuwa ta gyara zama ta fara ci tana lumshe idanu bataci da yawa ba domin cikinta ba buɗaɗɗe bane ta tashi ta juye sauran a leda iya gurasar ta ɗauka banda miyar ta zuba a leda ta ɗaure taje ta wanke hannunta tana fitowa yana shigowa ya wucce ɗakinsa wanka yayi ya fito sanye da ƙananun kaya baƙin wando Three quarter da riga Armless baƙa sunyi kyau da farar fatarsa zama yayi a saman soffer ya miƙe kafafunsa ya buɗe idanunsa a kanta ya sake lumshewa yace “Kya iya tafiya” murna ce ta kamata tayi saurin miƙewa tace “Na gode ranka shi daɗe dama ban wanke kayan makarantar asubarmu ba” 

Binta yayi da kallo yana taɓe baki har ta fice ya gyara kwanciyarsa tare da ɗaukar wayarsa yana dannawa

Leave a Comment

error: Content is protected !!