Tsintar Aya Hausa Novel na Billy Galadanchi

Tsintar Aya Hausa Novel na Billy Galadanci

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*TSINTAR AYA*

 

*BILLY GALADANCHI*

 

*Bansaniba ko a wannan lokacin alk’alamin dana d’aga ze samu daidaito a tsakiyar zuciyar makaranta litattafaina tsofaffi da wanda zasu fara a yanzu! Abu d’aya na sani shine tabbas wannan salon daban yake, wannan salone me tsawon tafiya kana kuma salone da ban tab’a zuwar muku dashi ba. Ban shirya siyar muku dashiba, haka kuma bazan sayar d’inba, littafin kyautane babu tantama. Maganar dazan fad’a kai tsaye anan itace Akwai kalmomin dake jingine da nauyi acikin su, musamman awurin yaranmu, salone daze amfani kowa anawa ganin, amma ina roqon alfarma awurin yara su jingine wannan amfanin zuwa lokacin da karanta littafin ze amfane su.*

Maganin Cikowar Gaban Mace

 

*Babu batsa aciki, sedai kamar yanda na fad’a kalmomi da abubuwa masu nauyin d’auka, banida hanyar sakaya kalaman masu jingine da nauyi abayansu, sedai inshaa Allahu zanyiwa kalaman kwaskwarima daidai da sakaye zuwaga zallar batsar.*

 

*Ban saniba ko zakuyi farin ciki da hakan, amma saukar kowane shafin zezone bayan na ajiye wanda ya gabacesa da kwana biyu, ina fatan hakan ze dawwamar da farin ciki a zukatanku masoyana.*

 

*A nawa b’angaren ra’ayi kuwa strictly matan aure zallah.*

 

*Tukuici zuwa gareki k’awata Ayusher muh’d, Alkhairin Allah ya kaimiki a duk inda kike, Allah ya d’auka kaki ya raya miki zuri’arki,yakuma albarkace su fiyeda iyawarki. Son so fisabilillah.*

 

*SHAFI NA D’AYA*

 

Duk yawan mutanen dake bayansa suna k’ok’arin ganin sun take gabansa da bayansa hakan yaci tura, sabida yanayin sauri da Hamood keyi, saurin kuwa tamkar ze tashi sama haka yakeji, sabida lokaci zuwa lokaci yakan wurga kallonsa zuwaga agogon hannun sa yana me k’ara sarrafa k’afafunsa zuwa ga d’an sassarfa, tafiya dabata wuce ta mintuna uku ba ya sauya akalar k’afan nashi daga sassarfa zuwa d’an gudu lokaci d’aya yana tattare hannayen rigar sa zuwa sama. Mabiyan nasa ma gudun suka soma tamkar wasu zararraru haka suka dawo acikin fadar kowa se kallon su yake ido k’asa sabida sunsan halin Hamood yanzun nan zece kana kallon sa kai munafiki ne. A sukwane suka k’arasa cikin fadar, a tsaitsaye ya taradda d’aukacin dattawan fadar da kuma  masu babban muk’ami acikin fadar kamar su waziri,sarkin yak’i, Magatakarda da sauransu.Dukkansu sunyi layi gefe da gefe sunbar fili a tsakiyar su inda dagacen zaka hango me martaba a zaune saman wata kujerar mulki ta alfarma wacce aka k’era da zallan ruwan zinariya rubuce a saman ta an rubuta Daulatul Dinar! Be wani b’ata lokaci ba wurin k’arasawa kusa da me martaba lokaci d’aya ya sunkuya yana nuna alamar gaisuwa amma bakinsa be motsa ba babu kuma alamun ze motsa d’in! Kallon k’ur me martaba ke masa na wani lokaci yayinda wasu lafiyayyaun mintuna goma suka wuce amma har lokacin Hammood be gayar da Mahaifin nasa ba! gyaran murya murya Me martaba yayi inda sabo ya saba da halin Hamood d’in, wasu ‘yan dak’ik’un seconds suka shud’e kafin yace.

Karanta Littafin Rumah Hausa Novel by Oum Hairan 

“Hammood Menene dalilinka na kawo ‘yan mata acikin fada? kana sani kuwa cewa hakan babban laifine da wannan masarautar bazata iya gafarta maka akanshi ba!Idan kana wajen masarautar kayi abinda kakeso mahaliccinka na kallon ka. Amma anan bazamu lamunta ba, sabida haka daga yau karna kumajin makamanciyar wannan halin a fadar nan” Shiru wurin ya d’auka na wuccin gadi, tsakanin mintuna da dak’ik’u an samu shud’ewar kusan minti talatin amma be motsa ba be d’ago kansa ba bakuma ze motsa d’inba kamar yanda koda ba gaskiya bane baze tab’a iya musawa ba. Shirun dayayi yawa ne ya sanya Me martaba cewa dashi

 

“You are dismiss” Be jira komai ba a sukwane ya mik’e tare da k’ara sauke kai k’asa alamun girmamawa sannan ya juya a hanzarce kamar yanda yazo yana shirin barin wurin kusa da galadima ya tsaya suka kalli juna, lokaci d’aya galadima ya d’auke kansa shikuwa seda ya gama k’are masa kallo sannan ya wuce cikin hanzari.

 

zuwa wannan lokacin gudu yakeyi amma idansa duka biyu a rufe yake, yayinda mabiyansa ke biye dashi cikin tashin hankali. Timing dama yake sabida haka adaidai sanda ya iso inda yakeson tsayawa sekuwa ya tsaya d’in yana mayarda numfarfashi sama sama, Babban cikin mabiyansa ya kalla sannan ya d’aga hannu ya masa nuni da cewar ya bashi biro da paper. Atake jikin su duka ya mutu dan kuwa sunsan an tsokano musu yau, a hanzarce ya rubuta

 

“Nextweek” ya mik’awa mutumin shikuwa jikinsa har rawa yake ya wurgawa takardan kallon baya ya karb’a sannan yace yana russunawa

 

“Sun dad’e sosai suna jiranka yallab’ai, dan Allah a dubawa uzurin su” Lumshe idansa yayi sannan ya bud’esu ya zuba tas akan mutumin sannan ya kuma yi masa nuni da biro da paper, da hanzari ya k’ara mik’o masa matsakaiciyar Joter…

 

“Kainane yake ciwo, kayi musu dukkanin abinda ya dace ka bani bayani a rubuce, kada ka manta ina kallon komai”

 

“Nagode da wannan karamcin yallab’ai, i will send ur doc right away” Murmushin gefen baki ya sakar masa sannan yad’anje baya da baya da gudu kafin ya juya ya runtuma aguje sekace wanda yake gasan tsere!

K’ofar part d’in nasa da kanshi ya bud’e ya shiga ciki, ma’aikatan dake gyaran k’asa ya tsaya ya k’urewa kallo sosai dukkanininsu sesuka zube suna kawo gaisuwa dukda yake sun tabbatar da cewar bawai ze tab’a amsa gaisuwar tasu bane, Lumshe idansa yayi sanda standing AC dake parlorn ya watso masa wani had’add’en sanyi da k’amshi sannan ya zube hannayensa duka a aljihun sa ya haura saman batare dayace dasu ci kanku ba. Yara ‘yan mata biyu dake k’ok’arin gyaran b’angaren basusan da zuwan saba kwata kwata, wannan ya sanya me ‘yan shekarun aciki take nunawa k’aramar wani hoto

 

“kalli da kyau ki gani Amina, yana magana fa, ba abinda ya iya se tsagwaran iskanci, amma mu sekace ba matan ba ya iya sha mana mur, kalli dai a hoton nan yanda ya rungune wannan macen sekace matarsa, uban kowa kuma yasan cewar be tab’a aure ba, haka zezo da mata da maza acikin gidan nan ayita sowa aci asha amma dazaran ya fito seki nemi koda murmushi a fuskar sa ki rasa tsinanne” k’aramar ciki ce ta karb’a da cewa

 

“Lallai ma, inatajin labarin mutumin nan, masarautar nan kowa ya bud’i baki prince Mood dai prince Mood, nina zata wani kamilalle ne ashe aminin shed’an ne” Dariya dukkansu sukayi kafin suka tafa suna shewa. Tamkar beji me sukace ba haka ya wuce batare dayace dasu kanzil.ba ya shiga bedroom dayake mallakin sa a part d’in. Sosai ganinsa ya firgita k’aramar harta riga babbar zubewa tana k’ok’arin gayar dashi muryanta yanata faman rawa, For the very first time ya waigo ya k’arewa dukkansu kallo, suna tsugune dazaka saurara a wannan a lokacin dakaji yanda cikin kowaccen su yake bada sauti k’uuuu alamun cewar tabbas k’ir suke jira su b’arke da zawo! batare daya ce dasu kanzil ba ya shiga d’aki abunsa, Babbar ce ta soma mik’ewa

 

“kurma ne dama kamar yanda akace uwarsa ma kurma ce, ni tunda nake dashi bantab’ajin maganar saba” Kallon ta Amina tayi

 

“Amma yanajin duk abinda ake cewa, cutar kurumtar ce dai ban saniba ko tabbas ce danko yanzu indai ba kurman bane ya dace yaji me muke cewa akanshi” Dariya siririya Babbar tayi sannan tace

 

“Ni idan naga ire iren hotunan nan a part d’in san nan se inga kamar tas yakejin komai damuke cewa, amma idan muna zaginsa ya kamamu kuma baice komai ba se inga kamar tabbas bayaji d’in,to amma fa komai a rubuce yake bayar dashi, idan an masa magana seya baka amsa a rubuce kinga dai inhar yana fahimtar maganar ka toko tabbas yana jin magana ba kurma bane” Cigaba da goge gogen da take tayi kafin tace

 

“Koma dai yanaji ko bayaji kanshi akeji, ni gwarama da naya magana akan wancen D’an galidaman me kafirin girman kan tsiya sarakan iya zagi” haka sukayita tsigarar wanda basaso har xuwa lokacin sa suka kammala ayyukansu tatas.

 

***************

 

Wayarsa dake kusa dashi ya janyo ya soma k’ok’arin aika sak’o kamar yanda yakeyi kullum sabida baya magana, yajima sosai rik’e da wayar a hannunsa yana aika sak’on shima kuma ana dawo masa dashi, rayuwar tana masa tsananin zafi zuciyar sa tana masa suya, mesa kowa baya sansa ne wai? me yayiwa mutane? akwai wani aibune a tattare dashi? waya matsawa a rayuwa? shidai gani yayi bako magana yake ba bare ace yana shiga harkar mutane, abinda Me martaba ya gaya masa ya tabbatar cewar galadima ne ya k’ulla masa wannan sharrin, kodai London ze koma ne? idan yabar musu garin yana ganin hakan shine mafi, A’ala agareshi kawai, amma ya zeyi da Mamin sa? ko duniya ze tara akanta ya tabbatar bazata tab’a bari ya k’ara d’agawa agarin ba, shiyaya zeyi? Kwanciya yayi a hankali yabi lafiyar lallausan katifar dake kan gadon ya kwanta tare da lumshe idansa, abubuwa da dama suke masa yawo akai, zabura yayi sannan ya zari wayarsa kamar ko yaushe da sassarfa yabar d’akin nashi zuwa k’asa kafin daga bisani yabar cikin gidan ma gaba d’aya da k’afarsa cikin sassarfa. Track suit ne ajikinsa kalar baki me ratsin ja da alamar mark ajiki me nuni da cewar kai tsaye kayan na k’irar kampanin Nike ne, Yanayi irin na zafi ya haddasa masa had’a uban gumi musamman dayake har yanzu gudu yake irin na masu motsa jiki, yayi tafiyar nisan zango dan kuwa har yaje ya zago ya dawo gaba d’aya, hankalin sane yakaishi akan matashiyar yarinyar daya gani xaune a gindin wata bishiyar baobab dake gefen wani gidan, tun sanda yabi ya wuce yaganta a wurin ga magarib tanayi yaya zata zauna a k’ark’ashin bishiyar kuka? wannan layin ba layi bane da mutane suke binsa shi kanshi dayake namiji kok’ari yake yaga cewar ya isa gida kafin sakkowar dubuwar daren nan to ita me take anan? dukda kanta acikin k’afafunta yake bawai yaga fuskarta bane ba amma ya tabbatar cewar yarinya ce k’arama sosai to menene haka kuma? tunawan da yayi cewan yanzu duniyar ba tabbas ya sanya ya d’auke kanshi daga dubanta kawai zuwa wani b’arin yaci gaba da gudunsa har zuwa lokacin daya isa masallacin k’ofar fada! Anan ya yada zango yayi alwala sanyin AC da fankar dake acikin masallacin sune suka busar dashi dankuwa duk tsananin gumin daya had’a tamkar gumin turare yakeyi, bebar masallacin ba seda ya sallaci isha kana ya d’aura da shafa’i da wutiri. Fitowar sa a masallacin yana k’ok’arin shiga cikin gidan seyaji zuciyar sa ta karkata akan son sanin halin da yarinyar cen take aciki, wani b’ari na zuciyar sa yana sanar dashi cewar tabbas yayi kuskure dabe ce tabar wurin ba amma shin ta iya karatu? ‘yar bokoce? da wanne bakin ze mata magana? tunawa da hakan ne ya tilastashi jan burki zuwa shiga cikin gidan da sassarfa kamar ko yaushe, wata k’il Hamood yana ciwon dabaze iya tafiya bane a nutse kokuma hala aljanun gudu ne dashi dasam baze iya tafiya yanda kowa keyi ba se surfafa uban gudu.

 

kamar kullum yauma aguje yashiga part d’in nasa dukda yake gudun dayake bawai wanda zesa kayi tunanin ana binsa abaya bane amma tabbas ko shakka babu gudun yakeyi, irin na maza majiya k’arfi wanda suke a murd’e tako ina! yauma kamar kullum yana jiwo surutun ma’aikatan sa suna gulmar sa amma ko kallon inda suke beyiba sabida bashida lokacin su ko kad’an shikam! a gurguje yayi wanka ya shirya tsaf tamkar wanda zeje club acikin k’ananun kaya harda facing cap ya mannawa idanshi farin gilashi k’al, ras dashi idan ka ganshi se tashin k’amshi yakeyi, zuciyar sa ba komai se tunanin waccen yarinyar ta k’asan bishiyar kuka anya kai yanzu ma ai ta tafi, ya furta bayan ya wurgawa agogon hannun sa kallo yaga k’arfe 8:30 ta buga hadda k’arin mintuna biyu! nisawa yayi sannan ya fice daga part d’in sedai wannan karon ba gudu yake ba Tafiya yakeyi tamkar wanda k’wai ya fashewa aciki!

 

Jikinta har rawa yakeyi sanda taga duhun yana yawa, babu abinda takeso illa taga wurgawar motar mominta, idan ta tsaya anan tabbas wani abu ze iya samunta sabida k’arfe takwas da rabi ya wuce abinda agogon wayarta ya iya nuna mata kenan,tafi gwammace dukan da Mommy sauda zata mata akan dai ace yau ta koma gidan ta tarar Bilal yana gidan, amma ganin lokaci ya tafi haka ya tilasta mata bin hanyar gidan cikin tsananin fad’uwar gaba da tashin hankali. Cikin sand’a ta tura gate d’in gidan ta shiga sannan a hanzarce ta lab’e bayan flower’s dake gidan karaf taji an damk’o hannunta cikin ihu tace

 

“Wayyoo momy” Fizgota Bilal yayi yaja hannunta har cikin parlorn su, hijabin jikinta ya zare yana murmushi sannan yakai hannunsa yashafi k’irjinta. juyata yayi ta fuskanci gaba shikuma ya manna k’irjin sa asaman bayanta hannayensa suna kan nonuwan ta, hab’arsa ya d’aura akan wuyanta sannan yace

 

“Ke banza ce Hafsat, ke bakisan arzik’iba, yadai dace ki sani ni jibi zan koma makaranta kuma kota k’arfin tsiya sena biya buk’atana akanki, wannan karon idan kika ce zaki gudu bundigar dana nuna miki zan saka in harbeki sekin shek’a lahira wlh” Jikinta yana rawa tace

 

“Bilal dan Allah kaji tsoron Allah, ka taimakeni ban maka komai ba ni marainiya ce kada ka lalatamun rayuwa” Zip d’in rigarta ya zuge ya zame har k’asa sannan yana dariyar mugunta yakai hannun sa ya b’alle botirin rigar mamanta, da lalubo ya shafko nonuwan ta,lumshe idansa yayi sannan yace cikin wani sauti “Asshhh shhhiiii, Haba Hafsat, tayaya zan rayu ban moreki ba, taya wannan lallausan maman naki zan bari su kufce a hannuna ban moresu ba, hak’uri kawai zakiyi” Runtse idan ta tayi ta soma ambatar sunan Allah a hankali, horn da aka rangad’a a bakin gate na gidan alamar dake nuni da cewar tabbas matar gidan ta iso shine ya tilastawa Bilal sakin Hafsat, cikin tsawa yace

 

“Tattare kayanki dan kutumar ubanki kije d’aki, ko alama na gani dake nuni da cewar na miki wani abu a fuskarki sena wulak’antaki wlh, oya now” Jikinta yana b’ari ta d’auki hijabinta da sauran rigarta tayi hanyar d’akin daya mallakin ta, rufe kanta tayi ta suturta jikinta kan nononta da Bilal ya matsa yana mata tsananin zogi sabida zuwan period d’inta, jitake inama k’asa ya bud’e ta shiga tsabar bak’in ciki, itama ace tanada dangi masu kirki, inama ace ita Hafsat a nemi wani a k’auye a had’ata aure dashi ta dena ganin Bilal, data huta data huta da wannan kayan bak’in cikin datake kwasa a rayuwa!

 

******************

Daga bakin gate kuwa Bilal ne ya bud’ewa hajiyar sa k’ofa ta shigo da mota, a small parking lot dabaze wuce d’aukar mota biyu ba tayi parking tuleliyar Lexus d’in ta fara k’al C350 model, kafin ta fito a motar bayan tayi parking ta zuge glass ta zube idanta a kansa, shikuwa cikin sassarfa yazo wurinta suka kafe juna da ido, dan kishingid’a tayi ajikin sit na motar cikin wata murya tace

 

“Malam Garba fa? har yau basu dawo ba kuma bakuyi waya ba” Sosa kansa yayi sannan yace

 

“Nakira su d’azu yace dani se gobe zasu dawo” Nisawa tayi sannan tace tana kafeshi da ido

 

“Bilal Nagaji, tausa nakeso, da wannan abin yau kuma sune suka motsa, acikin bayan motar nan akwai gasassun kaji hud’u, na k’aramar leda sune na ‘yar shara, sauran namune yau kaza nakeso kaci nikuma in fanshe ajikin ka” Murmushi yayi

 

“Momy aiko baki bani kaza ba se yanda kikayi dani, ni nakine momy aurema se idan kin yadda zanyi” Yamutse fuska tayi

 

“Bilal banason shiririta wane irin aure kuma? aure kam aiba yanzu ba seka k’ara girma tukunna” Murmushi yayi bece komai ba

 

“Ka nutsu kasan me kake karnajika da shirmen ‘yan mata, maida aure banan kusa ba, idan bakayi sallah ba kaje kayi dan yanzu nake buk’atar ganinka a b’angare na” To yace cikin girmamawa sannan ya kwashi kayan zuwa cikin gida….

 

Yar shara kuwa bayan ta karb’i Namanta a hannun Momy umarni aka bata akan karta kuskura ta k’ara fitowa waje se washe gari, haka nan ake rufeta ata wajen d’akin ta tanaji tana gani…… Lokacin dabefi sa’a d’aya ba kawai ta soma jiyo kururuwar muryan momy dana Bilal da irin wannan Shiiii Aaaa dayake mata duk sanda yake yagalgalarta, tunda su Baba Lami sujayi tafiya take cikin wannan halin, tagaji da wannan ihun, tagaji da wannan halin anya bazata gayawa Baba Lami ba kuwa, anya shirun nan zeyi kuwa, Momy da Bilal lalata sukeyi ita ta sani mesa momy zatayiwa su Baba Ladi haka, mesa zata zalunci ubangijinta akan me zata b’ata yaro k’arami? Sautin ihun su yana k’aruwa takai yatsunta duka biyu masu zaman manunai ta toshe kunnuwanta bazata iyaba inama zata iya kawar da kanta akan wannan bak’ar rayuwar? shin dabata hutaba wai, kai bazata shiru ba tabbas idan ta gayawa Baba Lami gaskia itama zata iya kub’uta a hannun Bilal, tabbas zata gaya mata cewan shida Momy lalata sukeyi.!!!!

 

**************

 

*Washe gari*

 

Bilal yana zaune da momy a parlor suna breakfast, wannan karon ‘yar sha tana jinsu, a tsammaninsu bata gane abinda suke fad’a amma sarai tana jinsu, mopping d’inta kawai takeyi, hajiyar ce tace

 

“Bilal naga jiya ka k’ara himma sosai, ban saniba ko hakan baya rasa nasaba da kudad’en dana kashe wurin mayar da tsohuwa yarinya” Murmushi yayi

 

“Kai sosai abubuwan suka k’ayatar jiya wlh, nayi matuk’ar jin dad’in komai da komai, gabaki d’ayan hanyar shiga garin seta matse sabida yawan mutane ga kuma tsantsin ruwan saman da aka lafta abin ba’a cewa komai” Dariya shak’iyanci tayi

 

“Ni karka saka na makara dan Allah, yaro k’arami dakai se iya zubo zance” Dariya sukayi a tare sannan suka mik’e dukkansu.

 

*********** Su Baba Lami sun dawo, kuma lokaci d’aya ‘Yar sha tayi summoning courage na gayawa Baba Lami abinda takeda yak’inin shi yake faruwa, sedai kuma yanayin fuskar Baba Lami kad’ai ya isa ya nuna mata cewar ba’a karb’i maganar tata da muhimmanci ba! Isowar Momy gida keda wuya se kukan Baba Lami tajiyo a parlor

 

“Yanzu hajiya ace yarinyar dakika rik’a tsakani da Allah dukda abinda ubanta da uwarta suka aikata kika taimaketa da mugun sharrin dazata biki kenan? me kika tsare mata arayuwa? maganar bazan iya gaya miki itaba sabida nauyinta amma ita tazo ta maimaita da bakinta” Jikin ‘yar shara (Hafsat) ne ya fara rawa sosai sabida tsoro ta k’ure a toilet anata kiranta amma bata fitoba, seda momy taje ta fincikota sannan ta fito tanata zare ido, Baba Lami tace

 

“Ke ‘Yar sha maimaita abinda kikazo kika gayamun Hajiya da yaro sunayi agidan nan” Jikinta rawa yakeyi sosai yanzu kam har fitsari ya soma fito mata tace

 

“Baba Lami dan Allah ki rufamun asiri” Mari Baba Lami takai mata

 

“Na rufa miki asiri kamar yaya? kina neman tona mana asiri kice in rufe naki, kimga hajiya zuwa tayi tana gayamun waikeda yaro Lalata kukeyi kullum cikin dare nan yake kwana sanda bama nan” Da mamaki momy ta kalli’Yar sha sannan tace

 

“Hoo yaron zamani, Lallai na yarda duniya tayi gurb’acewar dabazata gyaruba sesa gyaran Allah, kokin san dabakwa nan bilal k’ararta ya kawomun, fita takeyi idan na fita na zaneta namata fad’a shine zaki dawo da sharrin akanmu? ko shakka banayi wannan yarinyar dalilin kenan dayasa mutan garinsu ma bame sonta, amma ni bazance miki komai ba, bari Bilal yazo ya maidaki garinku tunkan kinb’atan suna agari, aniyarki ta biki Yar shara” Haka suka tasata agaba da uwar Bilal da momy suka mata tatas!

 

kuka ta kwanayi a wannan daren babu k’auk’autawa, washe gari bilal da duka ya tashi mata tamkar ze kashe ta, haka suka fita akan ze kaita garinsu insunso su kasheta, ita tasan cewar bilal baze barta ta rayu a farin cikiba, tanada yak’inin cewan abinda yakeso ajikimta baze hak’uraba harse ya karb’a.

 

 

*MOM NU’AIYM.*

 

*TSINTAR AYA* FREE BOOK.

 

*BILLY GALADANCHI*

 

*Sak’on gaisuwa zuwaga Babbar Antyna, mace me karamci kuma me girmama, babba da yaro, Alkhairin Allah yakai miki a duk inda kike  Anty mejidda musa*

 

*Makaranta Littafin tsintar Aya nagode da rububin son dakuka nuna masa tun a shafin farko, Allah yabar k’auna.*

 

*SHAFI NA BIYU*

 

Dariya ya kwashe da ita sanda ta shigo motar jikinta yana b’ari, sanda ya fita a gidan ya saisaita kan motar sosai akan titi sannan ya waigo ya kalleta yana wani kashe ido

 

“Tsuntsu daga sama gashashe, wato lallai ‘yar sha bakida hankali, tsammani kike wai Baba zata tab’a yadda da zancenki,kokuma kina tsammanin kamar akwai abinda ze tab’a hanani cimma burina akanki, wlh sekin gane kurenki a hannuna” Batace masa komai ba banda kukan datake kanta asaman cinyoyinta.Batayi tsammanin cewa zekaita garin nasu ba, amma ga mamakinta setaga ya d’auki hanyar garin nasu se faman wak’e wak’en sa yakeyi tamkar wanda akawa bushara da gidan aljanna!

 

Harsuka isa be kuma koda kallon inda take ba, gidan nasu babban gidane sosai me yalwar shiguhu kala kala, kana kuma ko wane b’angaren bayan ka wuce shiguhun runface ta bunu da kuma d’akuna wasu ginin laka wasu kuma bukka ce, tsarin gidan kana ganinsa zaka shaida cewar irin gidan daya had’a dukka kowa da kowa ne, ma’ana Extended family…. Tun a soro na k’arshe Bilal yake rafka sallama har ya bazama cikin gidan, harya cire rai da za’a amsa masa sekuma kaman daga sama ya soma ganin mutane tamkar ana yayyafin su suna fitowa, Atare d’aukacin mutanen wurin suka had’a baki wurin ambatar ‘yar shara! wanda hakan ba k’aramin k’ara rikitar da ita yayi ba cikin tsananin firgici take kallon kowa idan ta ya sauka akan Baba jere daya tsatsareta da ido tamkar ze cinyeta d’anya. Bilal gaggaisawa yayi da mazan ta hanyar musabaha sannan yace

 

“Hajiya Barira ce tamun umarni akan in dawo da ‘Yar shara gida, tace in sanar daku kuyi hak’uri da k’in zuwan datayi da kanta ta dawo da ita, tanajin kunyar kune ta kasa rik’eta kamar yanda tayi alk’awari, tace hakan ya biyo bayan cikin shegen dake jikin ‘Yar shara ne harna tsawo wata biyu, bazata iya abun kunya ba ita kam, sabida haka na dawo da ita tushiyar ta” Tas wurin ya d’auki salati yayinda lokaci d’aya duniyar ta soma juyawa da ‘yar shara tana shawagi da ita, wannan wane mummunan k’azafi ne Bilal yake shirin manna mata, sama sama tajiyo muryar Baba jere yana cewa

 

“Kayi tafiyar ka Bilal, zamu mata hukuncin daya dace da ita” Haka.ta ruk’unk’une wuri d’aya tana gunjin kuka amma sam ta kasa magana har Bilal ya juya sekuma ya dawo kusa da ita ya sunkuya ya ajiye mata wata leda, ga kati nan ajiki lambar wayana, idan azaba tayi azaba kika yanke hukuncin bani kanki seki nemeni a waya kud’ine acikin wannan biredin sekiyita tattalinsa dan nasan kwana bazaki k’ara agarin nan ba zasu koraki” Batace masa komai ba, babu kuma wanda yaji maganar dasuke se ita kad’ai sabida yanda yazo daf da ita yana magana k’asa k’asa…… Haka ya tafi banda kuka babu abinda ‘Yar shara takeyi.Kallon tsana Baba jere yabita dashi sannan yace

 

“‘Yar k’wai bani kayan wuta da alamar k’ira” Inna suwai ce tayi azamar kallon sa, murya yana rawa tace

 

“Jere me zakayi? kallon ta shima yayi

 

“Bakiji tayi shege ba, yanda nayi da ubanta haka itama zan mata” Idanta ne ya kawo ruwa babu musu ko gaddama a atsakanin su, babu wanda yake ja da hukuncin jere shine me garin garin gaba d’aya kuma biyayya agaresa batada hijabi awurin su dole sesunyi jikinta yana karkarwa ta zube akan gwiwowinta

See also  Best romance Hausa Novels

 

“Jere ka dubi girman Allah ka sassauta mata, karka manta azabar k’irane yayi sanadin Djoro, kabar ‘Yar shara itakam ita kad’ai ne a tsatson Djoro dazan kalla inji sanyi” Wani kallo ta wurga mata yanzu a hautsine

 

“Bana buk’atar tsatson Djoro a zuri’a ta, Yanda Allah ya kashe Djoro Allah ya kashe D’iyatai daya bari, Idan zan mata k’ira har a tafukan hannayenta zan manna mata sabida azaban wutan yajewa d’an shegen dake shikinta shima ya mutu atare da ita” Kuka ta saka da iyakacin k’arfin ta ruga ta rungume ‘yar shara, zuwa lokacin da aka kawo kayan k’ira aka hura huta aka soma d’o’d’in k’arfen iyakacin gigicewa Hafsat ta gigice, batasan me ma’anar hakan ba, amma menene ya kashe mahaifinta ance rashin lafiya yayi, itama ciwon zasu zasu saka mata kome? k’aramar akwatinta ta janyo ta cura wayarta aciki sannan a hankali ta ware biredin nan ta zaro kudinta ta cura a rigar mamanta tanabin kowa da kallo, katin da lambar wayar Bilal yake aciki ma sanda ta d’auka ta adana ajikinta se zare ido take, batasan me za’a mata ba amma tabbas tasan akwai alamun zata dauki yar mitsitsiyar akwatinta ta kwasa aguje inhar ya kasance azabace! Lokacin da k’arfen yayi azabar zafi se wasu maza tagani datakeda yak’inin yan uwanta ne sukazo suka daddafeta tun a nan ta soma ihu mik’ar da k’afarta akayi aka dafe Jere ya daddage ya manna mata k’arfen a tsakiyar tafin k’afarta!!! Wata uwar k’ara data k’walla tsabar azaba seda ta saki fitsari a wando ba shiri, haka ya mata tambari biyu a kowace k’afa zuwa wannan lokacin ta suma batasan inda kanta yake ba, k’ara dafa k’arafan yake yana ik’irarin manna mata a hannu Inna suwai ta rungumeshi tana kuka akan yabar ta a haka, kallon ta yayi yana yamutsa fuska

 

“kona manna mata kokuma akaita kan hanya ta kama gabanta” Dama bata saka ran ze barta ta zauna ba dan haka da sauri ta amince akan a koretan tasan koba jima koba dad’e zata nemi gida, koda babu ransu kuwa. Kallon masu dafeta yayi yace

 

“Ko inuwar wannan karku barmun agidana, ku fita da ita daga garin nan kuje cen bakin titi ku ajiyeta itada kayan ta da komanta” Haka suka amsa masa suka kwasheta a some ita da kayan ta, akan hanyar su aka soma ruwan sama ga duhu ya soma sauka wannan ya sanya babu wata tazara da garin suka ajiyeta suka ajiye mata akwatinta suka juya inda anan dukan ruwan sama ya dawo da ita cikin hayyacin amma seme ta farka cikin tsananin azaba da radad’i sannan babu akwatin kayanta a ranta ta ayyana acen aka kwace mata, ta godewa Allah daya sanya bata saka kud’inta a jakar ba, amma me tana lalubar rigar mamanta seta ji wayam! bata sani wad’an nan yan uwan nata sunga sanda ta saka kud’i a wurin, sune suka zace wayarta da kud’in suka barta da akwati wanda kafin ta farfad’o wani mara imani ya kwace. Babu takalmi a k’afarta batasan ammata lahani ba seda ta mik’e nan take ta zube awurin sabida wata sabuwar azabar data ziyarce ta ga ruwa ana tsulawa ga dare yayi, kukan ma a wannan lokacin gagararta yayi, jefi jefi motoci suke wucewa gata a gurfane bazata iya taka k’afarta ba bare ta saka musu hannu su taimaketa!

 

**************

*Washe gari*

 

Anan ta kwana cikin tsananin radad’i da fargaba me tsanani, ilahirin ruwan akanta ya kare a gindin wata bishiya, da asuba ma se taimama tayi tayi salla a zaune, har azahar ba yalwar mutane akan titin, tunanin abinyi takeyi ga azabar k’unar dake tafin k’afarta, haka ta mik’e tanaji tana gani ta soma tafiya akan duga duganta inda wutar bata kaiba, haka tayita tafiya se la’asar ta samu wata motar yaji ta d’auketa asama nanma da k’yar ta samu hawa sabida wuyar datake ciki,tare da alk’awarin zata bashi Naira hamsin idan sun isa gari.

 

Yamma sosai ya dawo daga wurin motsa jiki ya tsaya yabi wurin da kallo, yau ina wannan yarinyar ne? idan baze manta ba ya ganta wurin yafi so bakwai, kota dena zama a k’asan bishiyar ne? meke damunsa na damuwa da ita sosai haka ya tambayi kansa? Bafa komai kawai tausayi take bashi ko ba’a fad’a ba yasan akwai abinda yake damun ta, besan fuskarta ba dan kuwa kullum kwanan duniya kanta a sunkuye yake amma ta masa tsaaye tsayin alif ajikin allo a zuci kome yasa oho! Nisawa yayi kawai  yaci gaba da gudunsa jikinsa yana nan a murd’e se gumi yake had’awa a sukwane ya isa gida amma kamar kullum a masallaci ya tsaya yayi sallah tukunna har isha sannan ya shiga ciki. A gaggauce yayi wanka ya shirya yauma kamar kullum, wurin Muhsin ze tafi suyi maganar abinda ya shafi kasuwan cinsu sabida harga Allah k’asar yake neman dalilin daze d’aga mata idan ba yabar k’asar ba D’an galadima ze sanya yazo ya aikata abinda bashi kenan ba, D’an galadima munafiki ne…

 

‘Yar shara kuwa a tasha da suka sauka anan dirama ta tashi akan kud’in motar da tace zata bayar idan sun iso, dan kuwa batada ko k’wandala banda uban zogin da k’afafunta ke mata na rad’ad’in k’una… wata iriyar kallon banza kwandastan motar ya wurga mata yana lashe leb’ensa sannan yace

 

“Idan kin yarda in bashi kud’insa in rufa miki asiri, kekuma ki biyani daga baya” jikinta yana rawa ta amince da hakan aganinta zata samu kud’insa seta biyasa daga bayan koma a inane, dan haka ta masa godiya shikuwa ya biya kud’in cas bisa ass. Godiya ta masa azuwan idan ta samu zata biyasa kud’insa shikuwa yace alambaran kwana zasuyi atare ya fanshe hamsin d’insa, tun suna magana a cikin rad’a har maganar ta tashi atasha aka zagayesu, atake ya murd’eta akan itace ta masa alk’awarin ze fanshe ajikinta, gashi ta gaji da tsayuwar sabida akan duga duganta take tsaye, wani mutum ne yace da kwandastan

 

“Shinkai Zubairu dakata, nawane kud’in nata” Seda ya kalleta sannan ya kawar da kansa yace “D’ari bakwai ne” Mutumin ne ya zaro d’ari bakwai ya mik’a masa sannan yace yana kallon sa

 

“Bata amince da kaiba, dan haka gankud’inka nan ta biyaka, wannan yarinyar yar luwai caras da ita bazatabi k’azami kuma karen mota irinka ba zubairu, kumama akan wannan gajeran farashi, yarinya muje nizan baki dubu biyu” Cikin kuka tace

 

“Niba karuwa bace dazaku rik’a cilli dani tamkar wata k’wallo, wannan salon wani wulak’ancine kuma, ni a k’auyen d’an biram suka d’akkoni akan idan munzo zan basu naira hamsin, yaya kuma zezo yace d’ari bakwai ne? banisa hamsin amma inada zoben azurfa na tabbatar zekai dubu biyun da kai kake ik’irarin zaka bani, sabida haka gashi kaje ka sayar kabiya karuwa irinka badai niba” Ta k’arashe maganar tana cilla masa zoben ya daki k’irjinsa ya fad’i a k’asa

 

“Abinda kukamun se anwa ‘ya’ya ko matanku ko k’aninku wlh, na barku da Allah shine ze sakamu  mugwayen banza” Ta juya tana d’ingishi ta fita tabar cikin tashan yayinda su kuwa sukayi cirko cirko suna kallon ikon Allah.

 

A bakin junction taje ta zauna ta sunkuyar da kanta, ga dare yayi koda babu waya a hannunta ta tabbatar cewar tara na dare yayi idan ma be gota ba, koda ganin yanayin yanda mutane suka rage kai kawo kasan cewar dare ya ruga sosai, Ganin zata b’atawa kanta lokaci ya sanya ta mik’e ta soma d’ingishin datake gidan momy zata koma, itace rufin asirinta gwanda zama wurin Bilal idan Allah yaso baze samu abinda yakeso awurin taba amma wadannan mutanen ba Allah a ransu ko dukkansu farmata zasuyi, tana wannan unguwar datasha yake da nisa sosai da gidan momy amma haka zata taka, bazata hau wani abin hawa batada kudiba dan batasan yanda za’a k’arb’eta ba agidan, da wannan shawarar taci gaba da d’ingishi tana takawa a hankali………

 

Hamood be bar wurin Muhseen ba se k’arfe sha d’aya da ‘yan mintuna, babu yalwar abun hawa kazalika jefi jefi zakaga mutane suna yawo, kuma duk wanda ka gani zakaga alaman sauri a tattare dashi, yanayin yanda take tafiya ya shagaltar dashi, d’ingishi takeyi alama sun nuna cewar da dugaduganta take takun tome yasa? yasan wannan kalan hijabin da zanen jikin amma a inane ma? yaya take tafiya babu takalmi a k’afarta? da wad’an nan tunane tunanen yaje gida batare daya tsaya wurin yarinyar ba sedai tambayoyi marasa amsa fal a kansa.

 

‘Yar shara tayi tafiya sosai har k’arfe d’aya na dare ya tadda ta babu alamun zata isa gidan Momy, hankalinta ya soma tashi sabida ta kula cewan daga ita se karnuka akan hanyoyin datakebi d’in, sannan idan ta kaucewa titunama bawai b’ullewa zatayi ba, kana ko yanzu a yanda take hange akwai nisa sosai da inda take hari….. Takun dataji a bayanta ne ya sanya tayi hanzarin waigowa mazane sunkai su bakwai, a yanayin yanda ta gansu kuwa babu alamar mutunci a tattare dasu, wannan ya bata damar k’ara mai a tafiyar datakeyi dukda bata iya taka k’afarta sedai d’ingishi, tun suna k’ara saurin dasuke har suka soma gudu kad’an, ganin haka itama ta k’arawa dokinta linzami ta soma gudun cikin azabar k’una da radad’in da k’afarta keyi,dama gashi tana lokacin al’adarta wannan ya sanya mararta ta murd’e mata wuri d’aya lokaci d’aya jini ya kuma b’alle mata ga dama matarin data saka tuni ya jik’e sharaf! gudun fanfalak’i suka somayi atare suna ihu suna sowa suna mata dariya tsuntsu daga sama gashashe shine abinda suketa fad’a!

 

Agogon dake ajiye agefen bed side drawer d’insa ya kalla, k’arfe d’aya saura kwata, mesa ya kasa bacci, yarinyar batayi kama da cewar tana cikin nutsuwa ba, mesa yakeji a ransa tamkar ya baro wani aiki me muhimmanci atiti beyiba gameda yarinyar, ya ganta a yanayi irin na rashin lafiya yakuma ganta tabbas tana neman taimako, ba wannan bama ya ganta lokacin da dara yaja k’afar mata sosai tayi k’aranci akan titi shin mesa be tsaya yaji meke damun taba? zabura yayi sannan ya zari key na motar sa, gajeran wando ne ajikinsa iya gwiwa sekuma riga mara hannu med’an fad’i, hanyar waje kawai ya nausa aguje yauma kamar kullum, hadiman dake hidima a b’abgarensa wanda basuyi bacci ba se gulmarsa suke…..

 

A hankali yake tafiya da motar sa haryakai inda yake tsammanin ganinta, direction datakebi anan yabi amma sam ko alamarta babu, beji ya karaya ba haka yaci gaba da zagayen titunan yana k’arewa wuraren kallo, cen ya hangota a kwance sedai wannan karon babu zani ajikinta babu hijabin duk gasunan agefen ta, da hanzari yayi parking motarsa yafito aguje ya k’araso inda take, bin yanayin ta yayi da kallo yana me haske ta da hasken fitilar wayar hannunsa, hannunta taja ta rufe fuskarta inda zata karewa musamman idanta, sannan taja hanninta d’aya tana k’ok’arin rufe jikinta dake a tsiraice ko pant d’inta yana gefe cen a yashe iya rigarta ne kawai ajikinta kuma itama duk an yaga ta, alamomi tas sun nuna fyad’e aka mata tunda gashi harda jini sosai ajikinta, zaninta yayi hanzarin zara ya rufa mata sannan ya juya bayansa kawai ya koma motarsa.

 

 

*Idan baku manta ba na gaya muku bazan samu daman yin posting kullum ba, bayan kwana d’add’aya zankeyi da izinin Allah.*

 

*Mom Nu’aiym.*

 

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

 

*BILLY GALADANCHI*

 

*SHAFI NA UKU*

 

Sumar kansa ya shafa zuwa k’eya cikin tsananin damuwa da fad’uwar gaba mara misaltuwa, mekenan ya faru wa ‘yar mutane? yaya zeyi da ita a yanzu? wannan laifin sane ko me? mesa dacen datake tafiya acikin dare tana d’ingishi be tsaya yaji inda zataje ba? menene amfanin zuwansa yanzu? ina ze kaita? Asibiti? they will surely ask of police report ta ina ze fara? besan komai ba, acikin dare yaganta akan ttii anyi raping nata sai kuma me? shi daga ina yake? iska me zafi ya furzar daga cikin bakin sa sannan ya juya ya kuma kallon ta. Wayarsa ya janyo ya kira Muhseen be d’aukaba dama baze d’auka d’inka ba dan yasan baze masa magana ba, dan haka ya masa txt na wurin daze sameshi yanzu amma shiru shiru babu alamun dawowar sako har zuwa mintuna goma,yanada yak’inin cewar tabbas Muhseen bacci yake. k’ara mayarda dubanshi yayi zuwa ga yarinyar k’ok’arin d’aura zaninta take daga kwancen, sanan kuma seja baya take dashi, ganin yana nufota ya tilasta mata mik’ewa da k’yar tana kuka tare da motsa labb’anta sedai sam baya jin metake cewa, gyaran zaman zanin take kokarin yi amma ina se jiri ya d’ebeta ta tafi luuu zata fad’i a sume, da hanzari yayi azamar rik’ota sannan ya zube akan gwaiwowinsa d’auke da ita, kallon fuskarta yake tabbas suma tayi, lallai abun yafi k’arfin tunanin sa, be b’atawa kansa lokaci ba ya zurata a mota ya finciki motar se gida, nanma kwasarta yayi hannu bibbiyu zuwa b’angaren sa yanzu ma aguje kamar kullum, sedai wannan karon kana gani kasan a uzurcen gaske yake, be had’u da kowa ba se mutanen dayake da tabbacin idansu biyu wato munafukan fada, ya tabbatar munafukan fada idansu yanzu yake bude ma, be wani damuba ya haura samansa da ita.

 

Yafi minti 30 yana tunanin abinda zeyi da yarinyar har lokacin idanshi be kaishi akan tafukan k’afarta, daga bisani sai ya mik’e ya debo ruwan sanyi ya soma kokarin dawo sa ita hayyacin ta ta farka amma ga alama she’s unconcious dafe kanshi yayi ya kalli lokaci k’arfe hud’u saura yan mintuna, yaya zeyi? Family Dr. nasu yawa message akan by 6 ya kasance a b’angaren sa akwai patient daze duba masa sannan ya koma yaci gaba da aikin kallon ta har zuwa sanda yaji ana kiran sallan asubah wannan ne ya tilasta masa mik’ewa ya d’auro alwala ya fita masallaci!

 

Bayan idar da sallan yajima sosai yana lazimi bayan yayi azkhar d’insa da komai sannan ya mik’e tsaye yana duba message d’in likitan dake tabbatar masa da cewar baya k’asar gaba d’aya, k’aramin tsaki yaja ya fito sekuma yayi karo da Muhseen dake jiransa a k’ofar masallacin dakuwa ko ba’a gaya masa ba ya tabbatar cewar yana masallacin a irin wannan lokacin musabaha sukayi sannan yabi bayanshi zuwa ciki danya tabbatar baze samu amsar komai ba se’a rubuce. Turus Suka tsaya suka kalli jama’ar dake wurin motar Mood ciki kuwa hadda me martaba, k’arasawa yayi shida Muhseen atake muhseen ya zube ya gayar da Me martaba, shikuwa yayi tsaye tamkar an dasashi a wurin ya kafe Me martaba da ido yana jira yaji mezaice wanne kalan labari zezo dashi yau kuma da sanyin safiyar nan, shid’inma shi yake kallo cikeda takaici

 

“Munaso musan wannan jinin daya fito daga motarka daga ina yake? menene asalin abinda ya faru? munyi tsammanin cewar ai rauni kaji sekaga fess dakai, amma wannan layin jinin dayayita d’iga har zuwa k’ofar d’akinka yake tun daga mota, gashi ana iya hangowa daga motar daka hau jiya aciki akwai jini a sit d’in baya dukda bame yawa bane ba, meke faruwa?” Har wannan lokacin be motsa ba ya daddage ya kafeshi da ido bayako k’iftawa, Muhseen ne ya rik’o hannunsa suka kalli juna yamai magana irinta kurame ma’ana sighn Language yace dashi

 

“Bro mana meke faruwa? karka bari wani mugun abu ya faru dakai a wannan safiyar, bannason kafiyar nan kakuma sani please talk” Nan d’inma kallon Muhseen kawai yake seda ya gama k’arewa Muhseen kallo sannan yayi amfani da sighn language(Yaren kurame) yace dashi

 

“Duk Munafukai ne fa! bakaga suna kallona ba, sunsai komai kome zanyi konace bazan wanke kaina ba sun gama shirya komai tsaf so i will not say a word” Dafe kai Muhseen yayi, Me martaba yace da Muhseen

 

“Ni banna gane wannan yaren na kurame kai Muhseen meyace maka? Wasu yawun takaici ya had’iya sannan yace

 

“Ni d’inma be bani amsa ba” Gyaran tsayuwa Me martaba yayi sannan yace

 

“Idon Masarauta sun tabbatar mana da cewar da mace ya shigo rai a hannun Allah tana d’akin sa, mukasan wacece? yau bazan lamuntaba wlh, muje d’akin nasa” Matse hannunsa Muhseen yayi amma seya warce hannun ransa a tsananin b’ace ya juya zuwa d’akin duk suka rufa masa baya ciki kuwa hadda sarki……. Tun a parlor k’asa ya tarar ma’aikata sunyi cirko cirko suna tsegumin jiya ya shigo da mace a hannu kuma maybe rauni taji jini duk a k’asan tile basuma goge wurinba tsabar sonjin mezaije yazo, ganin me martaba ya tilasta musu zubewa a k’asa dukkansu suna kwasar gaisuwa shikuwa cikeda sassarfa ya haura saman inda duk jama’ar suka rufa masa baya. Be b’ata lokaci ba wuri bud’e k’ofar d’akin dayake mallakin sa, duk kuwa suka rutsa aciki ciki kuwa hadda Muhseen dake fatan abunda suke son gani karsu gani d’in sedai kuma turus suka tsaya kallon ‘Yarsha dake zube akan gadon zaninta a yafe kawai rigarta ata gaba a yage sumar kanta a hautsine sannan yanayin fuskarta kad’ai ya isa bayyanar maka cewar bata cikin hayyacinta, Me martaba cikin k’araji yace

 

“Hamood!!! meka aikatawa ‘yar mutane wai? wacece wannan kwance a haka, Hammod neman matan naka haryakai kawa ‘yar mutane fyad’e ka kawota cikin fada!” Babu alamun tsoro ko fargaba a tattare da Hammod girarsa ta sama ta had’e tas data k’asa fuskarsa babu annuri, beko motsaba amma ya tabbatar wannan shirine, baze tab’a iya kare kansa ba anyi amfani da tsananin tausayin dayake dashi akan al’umma an had’a kai da yarinyar dabe saniba an cutar dashi, anyi destroying rayuwar sa acikin sa’o’i dabasufi 12 biyu, da wanne bakin ze kare kansa koda yanadashi tunda wanda suka aikata masa sun shirya abunsu tunkafin yasani, ya afka acikin muguwar ramin su, ya tsunduma sosai acikin bak’in kogin da aka k’irk’ira domin sa kawai!! Muryar yarinyar ne ya dawo dashi daga duniyar tunanin dayaje na wuccin gadi!

 

“Karka k’onamun k’afata, ban maka komai ba, kayi hak’uri, dan Allah kaikuma karka mun fyad’e, karka zo kusa dani, ku rabu dani karku ketamun haddi na, niba ‘yar iska bace dan Allah kayi hak’uri” Wani uban ihu ta saka sekuma ta farka a zabure, ganin mutane a kanta kuma duk maza ya sanya tayi azamar soma rufe k’irjinta dake a bayyane, sannan ta soma gyaran zaninta tana kuka sosai! kalaman datake furtawa sune suka tabbatar da zargin dake zuciyar Hammood akan cewar had’a baki akayi da ita ake shirin cutar dashi, sannan tsawon dare yana tare da ita amma bata farkaba seda suka shigo wannan duk shiri ne. Salati wurin ya d’auka Manyan Fada suka dinga tsinewa Hamood, seda surutu ya lafa sannan Me martaba ya taka har wurin da yarinyar take yace yana kallon ta

 

“Ki kwantar da hankalinki yarinya, nan wurin kina wurin dazamu k’watar miki hakk’inki da tsare mutuncinki, kina hannun iyayen wanda basuda iyaye” Cikin kuka tace

 

“Hijabina zaku bani intafi dan Allah” Idan D’an Galadima ne ya sauka a kan tafukan k’afanta yahau salati

 

“Me martaba kalli k’afafun yarinyar nan, wai anya akwai imani akan Mood kuwa, haba mana se maganar karya k’ona mata k’afa takeyi” Ita dai se kuka take su kuwa mutane se lek’en tafukan k’afarta suke suna k’arawa da salati, sallamar kowa me Martaba yayi ya tura akan akira masa Jakadiya, yarage a d’akin iya shine dakuma Hammod se kuwa ‘Yar Shara, kallon sosai Me martaba yayi masa sannan yace

 

“Ka sauk’ak’a abubuwa sosai agareni Hammood, nagode daka bari mukazo wannan lokacin acikin sauk’i kajiko” Har lokacin kallon sa yake bayako k’iftawa idan nan ya kad’a yayi jajir jijiyoyin dasuke a murd’e se walk’iya suke gaba d’aya sun k’ara fitowa sunyi rud’u rud’u, zuwa wannan lokacin zuciyarsa tafarfasa takeyi k’irjinsa se ciccira yake alamun abubuwan na shirin taso masa, suna haka Jakadiya ta iso, janye fuska me martaba yayi daga ta Hamood koda wane lokaci karonsu baya kwashewa lafiya besan dalili ba shikam

 

“Jakadiya a suturta yarinyar nan fyad’e aka mata, a duba idan akwai rauni a jikinta, a k’asan k’afarta duka biyu akwai rauni me alamun k’una ce, zan tura akawo likita kokuma akaiku asibiti, na baki izinin ajiye duk abinda kike ki kula da ita sosai dan kuwa Matar da Hammood ze aura ce, daga yanzu zuwa lokacin dazata samu sauk’i” Zubewa k’asa tayi tana me.jadda da masa bin umarnin sa shikuwa Hammod siririya dariya yayi yanzukam wacce harta bayyanar da sautin muryarsa da babu wanda ya tab’ajinsa a duk fad’in duniya! shi kanshi bazece ga amon sautin dariyar saba sabida bayi yake ba, Aransa yace here we are @ last! Dama nasan da manufa akayi dukkan wannan shirin, girar sa d’aya kawai ya d’age har lokacin murmushi bebar fuskar saba, Me martaba yace yana kallon Jakadiya

 

“D’akin dake kusa da nasa zaki gyara mata, ai b’arnar sace, idan mun gama gyarata sesu tare” Har lokacin bece komai ba se murmushi haka me martab’a ya fice yabarshi a tsaye, Jakadiya ta hau gyaran ‘Yar shara da har lokacin kuka takeyi, tanayi tana mata sannu sabida yanayin tausayin datake bata a ranta tanata tsinewa Hammood akan b’akar halayyarsa mara kyau…..Yajima sosai tsaye yana k’arewa ‘yar shara kallo, tunda yake tsanar mutane be tab’a tsanar wata halitta sama da wannan halittar daya zata abar tausayi bace ada, dajin sautin kukan nan nata gwanda jiyo sautin kukan mutuwar sa, ya tsani munafuki, bayason munafuki konan dacen, meya mata wacece ita? zata d’and’ani kud’arta a hannunsa tabbas! Muhseen ne yazo yaja hannunsa suka bar d’akin kai tsaye ma gidan yajashi suka bari sukaje gidansu muhseen d’in, atake ya rubuce masa tun farkon ganinsa da ita dakuma abinda ayake zargi zuwa yanzu, nisawa Muhseen yayi sannan ya fara magana a hankali

 

“Ban saniba ko abinda kake tunani hakanne amma banaso ka yankewa yarinyar hukuncin abinda bashikenan ba, wannan zargi kawai kake amma bamuda tabbacin cewar had’in baki ne, abu d’aya na sani, acikin biyu kodai hakan take had’in bakine kamar yanda kace kokuma inaga an sarane akan gab’a” Cikin fusata ya soma magana irin ta kurame ransa a b’ace

 

“Muhseen niba yaro bane ba, nasan sarai me suke nufi dani, tayaya wannan yarinyar duk inda nabi acen itama takebi? mesa ze zamana seni kad’ai, sunyi amfani da halina da suka sani na tausayi suka cutar dani, kaima kayi tunani mana ina iyayen yarinyar? daga faruwar abu se zancen aure? kaji sun tambayeta danginta ne? kokuma kaji sun tambayeta wani abu daya faru a tsakanina da ita, they used me suka kuma cutar dani, gayamun idan kaji sunyi wata magana dake nuni da cewar basusan komai akanta ba, ka dubafa ka gani muhseen awurin dana sameta ita kad’ai ba kowa, jinin dake fita ajikinta is not real, they planned everything they set me up” Ya k’arashe alamar maganar da hawaye a idanshi” Jinjina kai Muhseen yayi

 

“Yanzu na hango abinda kake hangowa tun d’azu mood, yanzu na harbo jirgin tabbas shirine, amma ya zamu b’ullowa lamarin? Da hannayensa yaci gaba da amfani da sign language wurin yi masa magana

 

“Sun rigada sunje sun gayawa Mami nssani, bansan mezance mata ba yanzu, she will not listen to me, please muhseen help me out” Rungumesa D’an uwan nasa yayi yana patting bayansa a hankali

 

“Calm down mana Mood, komai zezo ya wuce ne kamar yanda na baya suka wuce kaji” Shiru dukkabsu sukayi se sauke ajiyar zuciya da Mood keyi cikin jin zafin zuciyar sa.

 

**********

 

Gabaki d’aya kan Hafsat ya d’aure, bazata manta meya faruba itada wad’an nan gayun, lokacin da take k’ok’arin tserewa se k’afafunta suka gaza, k’unar dake k’afarta ya tsananta azaba, hakan ne ya tilasta mata tsayawa tana mayarda numfarfashi har suka cimmata, a lokacin ne ogansu ya musu umarni akan su b’are masa ita haka suka dinga jan kayan jikinta har sukayi nasarar rabata da zaninta da hijabinta suka kuma yaga mata rigarta, tayi iya k’ok’arinta taga cewar ta k’waci kanta amma haka suka daddage seda suka rabata da har pant d’inta, sesukayi rashin sa’a tana period, bayaga haka kuma ya b’alle mata tamkar ruwa sabida tsananin firgicin datake ciki, ogansu dayaji haushin haka seyace shiba k’azami bane bazeyi ba amma gudun data sakashi su lakad’a mata shegen duka, wannan ne abinda ya k’ara haukatar da ita dan kuwa tasha duka sanda sukaga bata iya koda iya d’aga k’afarta sannan suka tsere suka barta agun tsirara! To meyasa wad’an nan mutane masu magana daban suke cewa wani ya mata fyad’e ita babu wanda ya mata fyad’e, hasalima a fuskar wanda suke alak’antawa da fyad’en bata tab’a ganin saba, dan harga Allah sanda yaje gunta bataga fuskar saba batamasan me take ba, shin meke faruwa da itane a rayuwa? su waye anan kuma waya kawota nan d’in?…….

See also  Shareef Hausa Novels Complete

 

***************

 

Lokacin da Hammod da Muhseen sukazo wurin Mami sun jima a zaune kafin ta fito, bayan sun gayar da ita ta amsa sekuma sukayi shiru, sedaga bisani Muhseen ya gyara zamansa ya kwashe komai ya gaya mata yanda ya faru da yanda abubuwa suka juye, kallon nutsuwa tayi masa sannan dayake matsalar ta iri d’ayace da Hammood sunaji amma basa magana seta shiga mayar masa da sighn language cikin fad’a

 

“Shishi kad’ai yafi kowa yawan mak’iya a masarautar nan, idan bashi bane yayi meye nakaita d’akinsa, idan taimako yakeso ya kawota guna mana, koya kaita wurin daya dace, yakaita a sibiti mana ko ya kira en sanda, yanada iko isa da matsayin daba wanda ze tunkareshi akan yayi karya idan ya aikata d’aya daga cikin wad’an nan, ina goyon bayan me martaba, hukuncin sa daidaine tabbas seya aureta” Tana k’arashe maganar ta mik’e zuwa ciki ranta a b’ace. Mik’ewa Mood yayi ya lumshe idansa, banda mahaifiyar sa, baze tab’a jurar fushinta akan saba har abada, Muhseen da azama ya mik’e ya rik’eshi amma seya zame hannun sa ya soma aikin daya saba wato gudu yana zuwa b’angarensa gaba d’aya yayi umarni akan a sallami hadiman sa baya buk’atar aikin aransa yana nazarin yanda zeyi sa wannan wawiyar yarinyar seta yabawa aya zak’inta seya wulak’anta asalinta indai sunan sa Hammood!!

 

Mom Nu’aiym.

 

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

 

 

*BILLY GALADANCHI*

 

 

*SHAFI NA HUD’U*

 

 

kai tsaye d’akin da aka tanada dominta ya shiga yana me banke k’ofar da iyakacin k’arfin sa, idanuwansu suka tsark’e dana juna atake jikinta ya soma b’ari tana zaune asaman gado ta takure wuri d’aya se rarraba ido takeyi! Yafi mintuna goma a tsaye yana kallonta bece komai ba, seda dan kanshi ya gama tunanin dayake sannan ya juya da zummar barin d’akin abinda yajiyo je daga waje ya dakatar dashi ad’an lobin dake tsakanin waje dacikin d’akin

 

“Bari bari bari prince mood anji haushi, ai yanzu ance ko sarki yaji komai, jakadiya ta tabbatar wa sarki wannan yarinyar ‘yar hannu ce cikine sukaje su zubar yazo da gaddama, ance tutsiye yarinyar akayi ta fad’i gaskia akan dama saurayintane dasukaje azubar da cikin daya mata shine fa aka samu matsala seya d’akkota ya kawo ta nan besan asirinsa ze tonu ba” Dariya d’ayar tayi

 

“Daba sunce aure zasu masa da itaba? to yanzu naji ance sarki yace a koreta tunda abun hakane, yazata hakk’inta yaci daze d’aura aurensu yanzu kuwa korace” Tafawa sukayi

 

“Bakiji yanda na tsani yarinyar ba wlh, da akace ze aureta nace su kurma an iya zab’e wannan yarinyar kyau kamar aljana shegiya se gashi,yanzu danaji labarin za’a koreta se wani sanyi ya mamayeni, dankuwa ni wlh inasan sa haka” Duka d’ayar ta d’aka mata a cinya

 

“Banza yafi k’arfin ma’aikata da bayi ki kama kanki” Be jira sun k’ara wata maganar ba ya fito daga d’akin,yauma kamar kullum beko kallesu ba ya shiga d’akinsa jikinsa a matuk’ar mace wai meke faruwa ne? menene gaskiyar maganar mutanen nan su kuma manyan munafukai ba? yaya yakejin maganar tana juyawa up side down?….. Mik’ewa yayi yanzun ma da sassarfa ya sakko k’asa ya nufi motar sa, beko nemi Muhseen ba dankuwa yaga motarsa a sukwane ya nufi gidan *UNCLE JAY*…….

 

Tunda Anty Barra taji tsayuwar motar da gudun tasan D’an kurma ne agidan yau kamar yanda take kiranshi, dan hakanda azama ta juya daga parlor zuwa ciki

 

“Uncle Jay bazan iya da rigimar Kurma ba, naji tsayuwar motarsa nakumaji gudunsa dan Allah ka tashi kaje” D’ago kai yayi ya kalleta yana murmushi

 

“Dama nasan zezo ban tsammanin zezo yanzu bane ba” Murmushin ta mayar masa “amma lafiya dai?”

 

“Ba lau ba dai, Mood ne bashida wayau ko kad’an, duk abinda zeyi seya saka rashin wayau se uban zurfin ciki da miskilancin tsiya” Tana kallon sa harya kai aya, nisawa tayi tace

 

“Ka saurareshi yanzu, tunda yazo mayi maganar daga baya” Mik’ewa yayi

 

“Noo wife agabanki zamuyi maganar muje kawai, its good kina wurin with those ur boosting idea’s i belive abubuwan zasuje mana da sauk’i” Ba musu suka fita atare hannayensu sak’ale ana juna, a parlor suka sameshi harya shigo yana zaune akan sopa ya sunkuyar da kanshi hannayensa duka cure acikin sumar kansa. Gaisawa sukayi dashi da yarensa sannan ya mik’awa Uncle Jay duk abubuwan da suka faru a rubuce a takarda har gulman dayaji ma’aikatan dayace a kora sunayi, ga alama be isa yace ayi ba ayi a yanzu! Tare da Barra Jay ya zauna suka karance takardar tatas kallon sa yayi sannan yace

 

“Naje gidan da safe gun Maminka tamun bayanin farko akan yanda ka shigo da ita, dakuma ya da maganar ta k’ara juyewa akan na ciki, sedai sarki be yarda da maganar jakadiya ba akamar yanda kaji ana tsegumi, hasalima ya kashe wannan maganar, abu d’ayane ya dai ya kafe akan seka auri yarinyar ranar juma’a” Da sauri ya d’ago ya kallesa,cikin yare irin nasu kurame da tsananin b’acin rai ya soma magana da hannayensa wannan karon har kansa da wuya mosti yake yana yi tamkar ze tashi sama. Seda ya lafa sannan Uncle Jay ya kalli Barra

 

“Barra me kike hasashe, da gaske kema abinda muke zargi akan had’in bakine da yarinyar haka kema kike zargi” D’an shiru tayi na wani lokaci kafin ta nisa tace

 

“kaso saba’in harda biyar acikin d’ari yana nuni kai tsaye da cewar had’in bakine musamman idan akayi duba da yanayin yanda al’amura suke tafiya acikin fada tsakanin Mood da sauran ‘yan uwansa kai harma da mahaifin sa daya haifeshi da cikinsa,na biyu kuma ita yarinyar bata musa akan dikkanin abubuwan da ake cewa ba alhali ya tabbatar mana cewar ta ganshi sanda yaje d’aukan ta har tashi tayi se kuma ta kasa, kaga anan ya dace ta kareshi idan har taimakon daya mata yakai mata matsayin taimako bawai sharri ake k’ulla masa da ita ba. Abu na biyu kuma shine kaso 25 acikin d’ari suna nuni da cewar faruwar komai co-incidence ne kawai aka samu, duba da irin wowtar dashi yayi, mesa sanda ya d’aukota bezo nan gidan ba, besa beje wurin Muhseen ba, shin mema ya hanashi zuwa gun Mami koya sanar da ita a waya, wannan zargine dabaze goguba musamman da idon Fada suka tabbatar k’arfe biyu ta wuce sanda ya shigo da ita, CCTV ma ya shaida hakan, bayaga haka ga jini kuma, bansan yaya ze faruba su k’ulla sharri irin wannan hadd fake jini, kaina yana k’ullewa sosai” Ta k’arashe maganar taname jingina bayanta da bayan kujerar. Gyaran zama Jay yayi

 

“Melon think mana, say something please” Nisawa tayi

 

“I need an audience with the f**king bitch, kafin ince komai Swt” Ta k’arashe maganar tana me zube lumsassun idanta akan mijin nata” Mik’ewa yayi

 

“Get ready now, kema kinsan halin kurma baze barni in hutaba harse ance an fasa aura masa Munafuka kamar yanda yake kiranta” Dariya sukayi sannan suka wuce d’aki a tare, shikuwa yana nan zaune dafe da kansa yana lissafa maganganun Anty Barra.

 

Tunda suka doshi b’angarensa aketa kallon su, shi yasan duk munafukai ne suke kallon sa, ‘yan sa ido masu jira suji me zasuyi anan, sanda yakai k’ofar hawa a saman sa sannan ya tsaya ya kalli wani daga cikin securities d’insa dasuka shigo tare dashi ya mik’a masa hannu alamun ya bashi paper da pen, da sauri ya d’akko ya mik’a masa shikuwa ya rubuta

 

“Dismiss everyone from here” Da sauri ya juya ya soma aikin tattara mutanen har zuwa sama.

 

*****Da sallama suka shiga d’akin sedai yauma kamar kullum atakure suka tadda ‘Yar shara rakub’e ta k’ule a k’arshen gado k’afarta d’aure da bandage duka biyu alamun an mata dressing na wutar har an rufe ta. Jay da Mood akan kujerar dake d’akin suka zauna yayinda Barra ta zauna asaman gado ta tattare hankalinta duka zuwa kan ‘Yar shara tana sakar mata lallausan murmushi a fuskarta, tsorone bayyane akan fuskar ‘yar shara wanda yasan abinda ake cewa tashin hankali yana kallonta ze tabbatar cewar hankalinta a tashe yake

 

“Sannu yarinya ya jikin naki kuma” Tsatsareta tayi da ido tana rarrabasu akan ta amma batace da ita ci kanki ba, anty Barra ce ta kuma cewa

 

“Wannan Uncle d’in Hammood d’in sunansa Jamil ni kuma matarsa ce sunana Anty Barratu amma yara kamarki suna kirana da Anty Barra, yayinda shi kuma kawun naku ake kiransa da suna Uncle Jay, dafatar zamu zama Ant da Uncle naki kema” Nanma batayi magana se k’ara matsawa take akuryar gadon sekace wacce za’a yanka.Shiru Barra tayi na adadin wasu seconds sannan ta kuma cewa da ita

 

“Banaso kiji kunyar idon mu ki gagara gaya mana gaskia, so bake ki gayamun tiryan tiryan meya faru, da gaske Mood shine ya miki fyad’e? Ta k’arashe maganar da alamar tambaya tana me nuna Hammod dake zaune yana fuskantar su” Jikin ‘Yar shara ne ya shiga shivering lokaci d’aya duk sanyin ACn seya haifar mata da saukar wata iriyar zufa me wahalar controlling, idan ta ya kawo ruwa sosai har lokacin Barra take kallo amma batayi magana ba, banda ma rawa da jikinta ke k’arayi sekace wacce ta d’aura aure da zazzafan zazzab’i. Mik’ewa Barra tayi ta zagaya ta rik’o hannayenta duka biyu se a lokacin ta kula da cewar jikinta ciccira yake ma bako karkarwa ba, tsatsareta itama da ido tayi sannan tace

 

“Yarinya ya sunanki? kuka wiwi tasomayi sedai batayi magana ba sam,kan anty Barra sosai ya d’aure ta waigo tana kallon su Jay wanda suma mamakin sukeyi, amma kafin wani acikin su yayi magana se ji sukayi an bud’e k’ofar d’akin an shigo, atare suka kalli k’ofar Me martaba ne dasu D’an Galadima da sauran manyan fada, bayansu kuwa likita ne wanda sananne ne agidan, MOOD ne kawai baya dubawa shi likitansa daban. Mik’ewa sukayi Me martaba ya zauna sannan suka zube suka gayar dashi,Mood ya had’e rai tamkar an aiko masa da manzan mutuwa, ita kuwa Yar shara ganin Me martaba da wannan tawagar ba k’aramin tsoratata yayi ba atake tashiga zare ido fiye da da, wanda Barra tana lura da yanayin sabon firgicin data shiga ganinsu, d’akin ya d’auki shiru bakajin komai se saukar numfashin mutanen dake d’akin dakuma k’arar AC da Fan dake yawo a d’akin, seda aka shafe sama da mintuna bakwai sannan Me martaba yayi gyaran murya yace

 

“Abinda ka aikata Hammood ka cutar da yarinyar mutane, gashinan yanzu likita ya tabbatar mana tayi loosing memory d’inta, abun ma tamkar ace ya shafi kanta ne, ko sunanta bata sani ba, gabaki d’aya ma ga alama kanta ba saiti, sabida hakankamar yanda na fad’a kaine zaka aureta, tunda mu munyi k’ok’arin sanin ina iyayenta suke amma batada bakin magana dan batasan komai nata ba, sakamakon fyaden daka mata yasa k’walwarta ta shafe komai ba abinda take iya tunawa dan gane da abinda ya shafi rayuwar ta ta baya, wani lokaci cen idan Allah yaso zata warke seta mana bayanin dangin ta, dan haka na yanke hukuncin d’aura maka aure da ita a babban masallacin juma’a ranar juma’ar bayan an idar da sallah” Har me martaba ya gama maganar dayake kan Mood a k’asa yake be d’ago ba, babu me halin yiwa Me martaba musu seda Jay ya tattaro courage d’insa sannan yace

 

“Amma ranka ya dad’e tunda har an tabbatar ta manta ita wacece aibe dace a d’aura mata aure dashi ba, idan kuma memory d’inta ya dawo aka kuma yi rashin sa’a da aure akanta fa? bayan haka ni Hammood ya tabbatar mun bashi yayi mata fyad’e ba” Mik’ewa me martaba yayi

 

“Yarinya dai batada aure dan kuwa k’aramar yarinyace likita ya duba raunin ta ya tabbatar mana sabon shiga ce, se abu na gaba maganar bashi yayi ba idan bashi bane kaine? Da sauri Jay ya d’ago ya kalli Marik’insa tun yana yaro se kuma ya sunkuyar da kansa Tuba nake ranka ya dad’e ka gafarceni” Yana wani k’arewa d’akin kallo yace

 

“Hammood shine ya mata fyad’e Jay, banza girman mahaukaci akace k’aramin me wayau ya fishi” Shiru d’akin ya d’auka, me Martaba ya kalli Barra datake k’anwa awurinsa uwa d’aya uba d’aya yace

 

“Barratu dama inaso nayi kiranki, ki d’auki yarinyar kije da ita wurinki, bamusam menene a k’afarta ba amma dai nasan k’unace kamar an manna mata wani k’arfe me wuta dan akwai zane da tambari ajikin wutar se ayita kulawa, kullum akaita dressing asibitin Dr mark’az” Cikin ladabi tace

 

“Inshaa Allah Me martaba” Daga haka ya juya muk’arrabansa suka rufa masa baya se likita ne ya tsaya yana yiwa Barra bayanin yanayin wutar da abubuwan daya dace amata.

Mood idanshi yayi ja sosai, jijiyoyin wuyansa sunyi rud’u rud’u, ilahirin muscles nashi sun mik’e sun fita sunyi rad’am se k’yalli suke alamar ya fusata, yanayin yanda sautin numfashi da bugun zuciyar sa ke fita kanaji kasan a tsananin fusace yake, watsa idanshi yayi akan Hafsat datayi saurin janye nata har lokacin cikin tsananin rawar jiki take,tas ya k’arewa yarinyar kallo be yadda da ita ba, da ita aka shirya komai itama munafuka ce, koda yazo da ita bayan ta farka aida magana abakin ta, yanzu za’a gayan masa maganar kawai akan me!!!! Wani duka ya kaiwa Table dake gefensa gashi glass ne take ya tarwatse be damuba ya bige side lamp d’in dake kan bedside duka ya tarwatse komai duk iya k’ok’arin likitan da Jay akan su hanashi amma be hanu ba seda yajiwa kanshi ciwo, duka hannayensa glass ne, karo na farko dayayi hargowa irin na bebaye sannan ya buga kansa da gina, be saurara ba seda ya dena motsi dama abinda Jay yakewa gudu kenan, ya tabbatar idan me martaba ya matsa se ankaiga fin haka ma, ya tabbatar idan aka aurawa Mood yarinyar nan wannan ciwon nashi ya taso komai ma ze iya faruwa, besan mesa me martaba baya duba condition na Mood ba, besan menene tsakanin uban da d’ansa ba, Mood yarone me tsananin nutsuwa da kawar dakai, besan yanda akayi mahaifin sa baya gani ba, damuwa tayiwa yaran nan yawa har yana ganin tamkar kowama ya tsane sa, duk k’arfin hali irin na Jay seda yayiwa Hammood kuka, yasan yaron is innocent akan abinda yake zargin sa, sedai fuskar yarinyar ma looks so innocent bayaji wani conspiracy aka shirya harda ita, amma bari Barra ta nutsu zeji meta karanto akan yarinyar….. Likitan ne yayi k’ok’arin taimakawa Mood amma ya kasa dole aka wuce dashi asibitin sa dannkuwa likitansa baya gari, sedai asibitin likitan nasa suda suke da record na komai daya shafi rayuwar sa.

 

*****************

Lokacin da suka barta ita kad’ai acikin d’akin lokacin ne ta firgita sosai da ganin haukan da wannan yakeyi, mutumin data gane shine wanda aketa ik’irarin ya mata fyad’e kuma za’a aura masa ita, me yasa abubuwa suke faruwa da rayuwarta cikin sauri tamkar a mafarki,yaya wannan mutumin ze kashe kansa akanta, akan me zasu masa haka, bari taje ta gayawa wannan matar gaskiya, kome zasuyi sesuyi Allah baze kama taba danta fad’a gaskia, a hanzarce ta sakko daga kan gadon bata damu da irin azabar ciwon da k’afarta ke mata ba, so take taje kawai ta samu wannan matar datace sunanta anty Barra ta gaya mata gaskiya, so take taje ta samu wannan balaraben ta sanar masa gaskiya karya kashe kansa, ina zatakai hakk’i idan ya mutu?….. Da gudu ta fito a d’akin tana k’ok’arin sakkowa k’asa domin ta taradda Anty Barra setayi rashin sa’a Ameena ce a saman tana mopping, da gayya ta sanya mop stick a k’afarta abinda yajanyo ta fad’i harta soma gangarowa daga matattakalar benen babu inda kanta be daka ba kafin ta gama gaggarewan banda ihu babu abinda takeyi tun tana ihun zuwa lokacin data gama gangarewa ko motsi batayi, harga Allah Ameenan bawai da miyya tayi ba, tsammani take zata d’an zamene sesuyi dariya kamar yanda suka tab’a yiwa abokim Mood, segashi yarinya ta gangare harma ga alama ta suma.

 

***************

Jay kanshi yana kallon sama sanda Barra ta shigo d’akin lokacin tafito daga wanka d’aure da k’aramun towel a k’irjinta, saman kanta kuwa sanye da hulan wanka take, zama tayi a kusa dashi tana goge fuskarta da gefen towel d’in jikinta, hankalin ta kacokam ta mayar a kanshi sannan a hankali tace

 

“Jay” Be kalletaba yace

 

“Water melon” Murmushi tayi jin sunan daya kirata dashi sannan tace “Swt kasaka damuwa sosai aranka akan issue d’in nan, dan Allah ka ragewa zuciyar ka nauyin daka d’aura mata, kasani Mood baya buk’atar komai sama da addu’a a yanzu, bamuda wata hanyar dazamu karkare ko goge masa wannan mugun tabon, ubangijin daya k’addaro faruwar hakan shishi kad’ai ya isa ya warware matsalar nan” Nisawa yayi yana matuk’ar k’aunar barra, batada had’i agunsa shikam komai bata da dogon nazari take aikatashi, cikin tsananin damuwa yace

 

“Melon baki gayan komai dangane da abinda kika fahimta akan yarinyar nan ba d’azu” Lumshe idanta tayi sannan ta bud’esu a hankali ta zube su a kansa

 

“Jay yarinyar tasan wani abu, and ba wani memory datayi loosing,after that kuma duk abinda aka shirya da ita bawai bisa son ranta bane tsorata ta akayi da wabi abu gaskiya, na hango tsananin tsoro a idanta nakuma hango gaskiya shinfid’e a fuskarta” Zaune ya tashi ya karb’i man shafawar datake k’ok’arin bud’ewa ya b’alle murfin seda ya tsiyaya a hannun sa sannan ya sako k’afafuwanshi agefen bazaunanta ya sanya ta a tsakiya a hankali ya zame towel d’in jikinta ya soma shafa man a gadon bayanta a hankali

 

“Me kenan ya dace muyi yanzu barratu na” Ya k’arashe maganar habarsa tana kan gefen wuyanta yana goga masa gashin gemunsa a hankali, tare suka lumshe ido sannan cikin wani yanayi tace

 

“A haka kakeso muyi magana me muhimmanci Jay” Murmushi yayi

 

“Wannan irin zaman da akazo akamun, da wannan k’amshin dake tashi ajikinki kin fito daga wanka yaya kikeso nayi dan Allah Melon? Hmm ina magana” Shiru batace komai ba sabida harga Allah yanayin sak’on dayake aika mata tako ina ya soma karb’ar jikinta, tanaso ta gaya masa labari akan yarinyar data fad’o daga kan stair case d’azu amma batason d’aga masa hankali, bataji ya zata abun yayi tsanani har yanda aka sanar mata, yana cikin damuwa sosai ta ina zata fara? hannunta takai ta shafi gemun sa sannan tace tana me manna gadon bayanta asaman k’irjin sa

 

“Jay nice ma nake k’amshi, so kake ka kasheni da wannan salon, a duk lokacin daka mannamum wannan had’ad’en gemun naka ajiki, wani irin electric shock ne yake d’ibana wani zubin harsenaje America da k’afa ban sani ba” Siririyar dariya yayi ya d’aura hannunsa asaman dukiyar fulaninta yana shafawa a hankali, shiru wurin ya d’auka na wani lokaci banda saukar numfashin su babu abinda kakeji da ganta ta juya ta lalubi bakinsa ta saka a nata, passionately take kissing nasa tana murza wuyansa zuwa bayan kunnensa da d’ayan hannunta d’ayan kuma yana safa da marwa a bayansa cikin salon tafiyar tsutsa irin na k’warewa, bashida zab’in daya wuce sakar mata akalar rayuwar sa tayi yanda takeso dashi, seda ta gama kashe masa jikinsa sannan tabi lafiyar faffad’an k’irjinsa ta shige tare da d’aura kanta asaman k’irjin nasa, gsrgasan dake kwance luf akan k’irjin ta soma wasa dashi sannan a hankali tace

 

“Jay yarinyar nan tamkar anyi magana da bakin mala’iku, likita ya gayamun da yamma danaje asibiti cewa zamuyi CT scan, so munje munyi but before the result comes out nabar asibitin se yanzu Mami tamun waya” Hannunshi akanta yana shafa sumar kanta daya zare hular wankan dake kanta yace

 

“Emhm metace”

 

“Akwai matsala akan buguwar da kan nata yayi suna tsammanin cewar zata dawo tana wani behaviour kamar na yara haka, ban gama fahimtar bayanin Mami ba dai, amma akwai ‘yar matsala” Wata iska me zafi ya furzar har lokacin idansa a lumshe sannan yace

 

“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel, abubuwan nan suna yawa fa Barra, na rasa ta ina zan b’ullowa al’amarin nan, Allah kayi mana maganin musiba”

 

“Ameen” ta furta a hankali sannan tace

 

“Jay Zulaiha tana jiranka fa, ko wanka bakayi ba, ga 8 ya gota tuni please ka tashi” Shagwab’e fuska yayi

 

“kema kinsan banason fita idan ina tare dake, ni tausayin kaina ma nake duk ranar dazan kwana ba tare dake ba” Zame jikinta tayi a nasa

 

“Jay ya zakayi? Ehm dole dai kayi adalci ka sani, ni bazan iya kallo kake wuce ka’idar tafiya ba” Mik’ewa shima yayi bece komai ba ya fad’a wanka ita kuwa anan tayi wata irin rikitacciyar kwalliya ta d’auka hankali acikin atamfa kalar ka me ratsin fari da kuma bak’i tayi kyau ainun, kallon farko zaka d’auka cewan wurin wani taron biki zataje amma zahiri mijinta daze koma b’angaren abokiyar zaman ta shitayiwa kwalliyar ban kwana…. A parlor ya sameta ta gama turara gidan da turaruka masu k’amshin gaske, tana k’ok’arin goge takalmin da ze saka, murmushi tayi sanda ta hangoshi sannan da hanzari ta ruga ta rungumeshi tana dariya

 

“My jay kayi kyau kamar ango, irin wannan karkace hula harkasa naji kamar ka zauna inta kallon ka” Murmushi yayi ya zagaye kunkurunta da hannayensa

 

“Melon da safe zanzo muje wurin Mood, hankalina sam baya jikina, gabaki d’aya tunanina yana wurin yarancen idan ya farfad’o lafiya k’asar zansaka ya bari, hanlalina yafi kwanciya ace Mood baya k’asar akan wannan wahalan dayske sha sekace mara gata” Gemunsa ta shafa

 

“Please karka fita anan da damuwa Jay, banaso katafi ka barni da tunanin damuwar da kake ciki sam bazan iya bacci ba” Sumba ya sauke mata a wuya

 

“Bazan shiga wata damuwa ba Melon, wannan kalan wankan dakika mun sallama dashi kad’ai ya isheni guzurin dare, Allah ya miki albarka” Ringumeta yayi sannan sukayi sallama cikeda shauk’in juna, ko wannensu yanaji yana tsananin kewar d’an uwansa….

 

Tun daga k’ofar parlor part d’in zulaiha wani wari mara dad’i ze fara taryarka, bayaga haka kuma kana shiga acikin part d’in zaka soma cin karo da abubuwa kamar su kopi plate da sauransu, kawar da kanshi yayi ya zaga ya shige bedroom nashi, yafi awa biyu a gidan amma zulaiha bata nemeshiba, daga baya ma dayaje neman ta seya tarar tana kwance tana sharar bacci abinta. Washe gari ma harya shirya yabar gidan baccinta take cikin jin dadi.

 

kai tsaye asibiti suka nufa, shida Barra abinda yafi d’aure masa kai shine rashin ganin Mood a d’akinsa, a birkice ya soma tambayar mutanen sedai be samu gamsasshiyar amsa ba, hakan ya tilasta masa neman likita inda anan sukejin cewar har lokacin Mood be farfad’o ba, kuma sabida yanayin komai nasa deja ja baya an mayar dashi ICU karo na biyu kenan yana shiga irin wannan halin, gargad’in da wani likita ya masa a london ne ya fad’o masa arai.

See also  Zuciyar Mutum Hausa Novel Complete

“Kudena bari yana shiga damuwar daka iya haifar masa da soma buge buge, idan kunyi nasarar ciroshi daga ICU yanxu nan gaba kad’an faruwar irin hakan ka iya janyo rasa rayuwar sa gaba d’aya, har wannan lokacin bamu gano taka maimai wanne irin ciwone dashi ba amma koma menene akwai damuwa sosai a k’walwar sa” Zufa ce ta karyowa Uncle Jay, banda Mood shine ya raine sa da hannun sa, besan me Allah yake nufi dashiba akan rashin haihuwa amma ya tabbatar Mood d’ansa ne, idan wani abu ya sameshi seyayi gunduwa gunduwa da naman Wannan yarinyar kafin ya gama lalubo su waye suka sakata, ko yanzu baze k’yale taba, seya bata azaba fiye da tunanin me tunani akan Hammood d’insa!

 

 

Mom Nu’aiym.

 

*TSINTAR AYA* FREE BOOK

 

*BILLY GALADANCHI*

 

Join my telegram page through the link below.

https://t.me/joinchat/FgfKMiS_mYc-DIjC.

 

*SAK’ON GAISUWA ZUWA GAREKI K’AWATA HAR ALJANNAH HAFSATUL ELHAM, INA MIKI FATAN ALKHAIRI ADUK INDA KIKE, ALLAH YA NESANTAKI DA AMINAI MASU FUSKA BIYU YAKUMA KAREKI DAGA SHARRIN DUKKAN WANI ABUN K’I….IYA WUYA K’AWAR ALKHAIRI.*

 

*SHAFI NA BIYAR*

 

Rik’o hannunsa Barra tayi yana kuka tamkar k’aramin yaro, bata damu da zaman likitan agun ba ta runguneshi gaba d’aya, daidai saitin kunnensa take rad’a masa

 

“Calm down mana heroin, ban sanka haka ba, karka yanke kowane hukunci acikin fushi, nutsuwa zakayi mu baiwa Mood duk kannin kulawar daya dace a yanzu, nasanka nasan halinka fiye da yanda kai kasan kanka Jay, a yanzu na tabbatar zuciyarka tana raya maka kayi wani abu mara kyau, please let it be,just let the situation be for now kaji” Sauke nannauyan ajiyan zuciya yayi sannan cikin rauni yace

 

“He’s my only son Barra, how can this happened? duk iyakar k’ok’arina seda yarinyar nan ta tayar masa da ciwon nan, idan ya mutu yazanyi?” D’agoshi tayi tamkar wani k’aramin yaro suka fuskanci juna

 

“Bana so ka d’auki alhakin abinda ya faru ka d’aura akan yarinyar nan, har yau nidakai ba wanda yasan ainahin menene gaskiyar abin nan so dole semunyi taka tsantsan da shiga hurumin Allah dakuma hakk’in wani” Shiru sukayi dukkansu, likitan ya k’ara kwantar masa da hankalin sa akan komai ze daidaita sannan suka juya zuwa wurin likitan dake duba Yar shara.

 

“Bata samu wani injury a ko inaba se  wannan na kanta, wanda shima ba wani matsala bane dukda matsalar nekam, zata iya warkewa yanzu, gobe kokuma anjima, zata iya bazata warkewa ba har abada, abune dayake tafiya da lokaci shi d’inma ba komai bane, memory d’inta yana nan daram sedai matsalar dazata fuskanta shine wani lokacin kawai zata rik’a muku al’amari tamkar wata k’aramar yarinya, yanzu yanzu setana lafiya yanzu yanzu kuma seta soma muku da childish behaviour,anan abinda zan iya cewa biyu ne, da farko dai zamu tura asibitin dasuke kula da masu matsalar kai sabida su d’aurata akan magungunan daya dace, na biyu kuma sekunyi hak’uri, kunce shekarunta 17 to akwai haushi ace babba abun yara wannan shine hak’urin dazakuyi da ita for the time bn, dan azahirin gaskia bazamuce se yaushe zata warke ba, k’unan k’afarta kuma munada wani likita daya k’ware a wannan fannin ya duba k’afar kuma harya soma saka mata  wani cream yanzu haka wurin ya soma bushewa so within a week komai zai daidaita inshaa Allah” Tun sanda ya soma magana shi Uncle Jay yake kallo harya kai aya, abun akwai bam tsoro, dama akwai irin wannan ciwon ne shikuma? Nisawa yayi sannan yace

 

“Dama akwai irin wannan cutar kanne likita? Gyaran zaman file dake kusa dashi yayi sannan yace

 

“Sosai kuwa, amma gaskia da wahala kaga ansamu d’in, dan acikin shekaru biyar befi kaga irin case din so biyu ba koma k’asa ga hakan, ita kanta nayi mamakin abubuwan nata yanda suka juye akan k’aramar buguwa irin wannan, ina tsammanin dama akwai irin ciwon ajikinta batun yauba, samuwar sanadi se abun yayi k’amari” Jinjina kai yayi cikeda gamsuwa da bayanin sa sannan ya masa godiya sosai kafin suka juya b’angaren Mood. Basu samu daman shiga ba sabida ba’a shiga wurin sa, anan suka masa addu’a suka juya gida.

 

********************

 

Yanayin zaman da tayi awurin kad’ai zaka kalla ka tabbatar cewar tacika kamilalliya, dukda yake shiga ce ajikinta irinta wayewa sosai amma hakan be isa ya hanaka fahimtar zallar kamilancin taba, handout ne da biro a hannun ta tana karatun handout d’in yayinda take k’ananun rubutu a wani small jotter haka, gabaki d’ayan hankalinta yana kan karatun datake, zuwa yayi ya zauna kusa da ita,lokaci d’aya dadd’an k’amshin turaren sa ya daki hancin ta, d’agowa tayi a hankali ta k’are masa kallo cikin d’ak’ik’a k’asa da talatin, dukda bataga fuskarsa gaba d’aya ba sabida ba gefen datake yake kallo ba amma kallon farko ta ayyana aranta wannan kyakyawa ne, bayan saurin kawar da kan datayi daga dubansa hadda yakice tunanin daya ziyarceta mara tushe akansa. Yafi mintuna talatin agun yana wayarsa batare daya nuna yakosan da wanzuwarta agunba, hakan ne ya masifar k’ularda ita, bayan kammala wayarsa ta farko sekuma ya gincira sannan ya kuma dialing wata number, ana d’agawa kuwa ya soma magana cikin d’aga murya yana fara’a, wannan abun ba k’aramin k’ular da Khairiyya  yayi ba, cikin zafi tace

 

“Haba bawan Allah, kai wane irin mutum ne dason kan tsiya, wannan ai shiga hakk’i ne” Dakatar da abinda yake yayi ya shiga waige waige kamar yana neman wani abu sannan daga bisani yace a wayar da yake

 

“I will get back to you” sekuma ya ajiye wayan ya kalleta sosai yace

 

“Are you talking to me? wata iriyar b’acin raice ta ziyarce ta, cikin tsananin fusata tace

 

“Noo am talking to your shadow”  Sake baki yayi alamar mamaki sannan yace

 

“En mata meyayi zafi haka? Tsaki taja sannan tace

 

“Kawai kazo ka taddani ina karatu, kawani tsaya akaina kanata waya sekace a parlon gidanku” Da mamaki d’auke a fuskarsa yanzu kam yake kallonta, cikin isa yace

 

“kanki d’aya kuwa? Haryau cikin masifa tace

 

“Kaina d’ari tara ne da casa’in da tara cikon d’ayan nake nema ya zama d’ari, da naka zan cikasa da amma na fahimci gwanda nakan bola dakai” Yanzu kam maganganun ta sun soma tafarfasa zuciyar Bilal, yaso yayi hak’uri amma ya fahimci batada mutunci, wani shak’iyin murmushi yayi

 

“Jambito ceke ko, naga alama bakisan a jami’a kike ba, to bari kiji gwanda parlon gidanku akan nan din dan kuwa kaf school d’innan babu wanda yace dan wata bebin roba tana zaune karwani ya zauna” Idan tane ya kawo ruwa tace tana kallonsa

 

“Waye babin roba? ni kake gayawa haka? Yana d’age kafad’unsa alamun kanki akeji yace

 

“Toda nine? kece bebin robar an fad’a kiyi duk abinda zakiyi” Tab’e baki tayi ta soma ruwan hawaye

 

“Allah sena gayaka da Anna, abinda kamun se Allah ya sakamun akanka, mugu kawai” Dariya Bilal yayi yace aranshi”Yau naga sakaryar wofi, wannan anya a jami’a take kuwa?…. Daganan yabar wurin aranshi yana mamakin shirme irin na wannan yarinyar.

 

A b’angaren Khairiyya kuwa nanda nan seta d’aga waya ta kira Anna, tana d’aukan wayan seta saka mata kuka, a rud’e matar tace

 

“Alkhairin Allah waye ya tab’aki kike kuka keda ke makaranta, wane ja’irin ne kuma? cikin shagwaba da muryan kuka

 

“Anna bayan wanine ya gayamun waini bebin roba ce, ya zageni yace koma me zanyi inyi” Mik’ewa tsaye Anna tayi daga zaunen datake

 

“Kutme, aikuwa ya ebo ruwan dafa kansa, Alkhairin yake gayawa wannan maganar yasan ko wacece ke kuwa? karki damu, ke yanzu kin girma kidena kuka a makaranta, gobe idan zakije makarantar zanga wanda ya isa ya hanani zuwa insa a d’aure munshi harse igiya yayi saura” Tana murna tace

 

“To Annah na, ina sonki kinji”

 

“Nima inasonki sosai Alkhairin Allah, k’yale D’an jakar uba” Haka suka ajiye wayoyin Annah masifa nacinta arai, lallai dabadan hidimar bak’in nanba babu abinda ze hanata zuwa yau taci jakar uban yaron cen, amma ba damuwa idan darai da lafiya gobe ma rana ce!

 

Bilal yanada abinda ze kaishi gida, dan haka washe gari sammako yayi asubar fari ya d’auki hanyar barin gari. Koda ya isa ba kowa agidan tsakanin mahaifinsa dakuma mahaifiyar sa, se motar hajiya, da kanshi ya bud’e gate ya shiga ciki yayi parking sannan ya fito kai tsaye cikin gidan ya nufa yanata sallama amma ba amsa se wayar ta yashe a parlon saman kujera, zama yayi kusada wayar ya d’auka yana jujjuya waya, ta masa kyau ainun yanaso ya rik’e irin wayar be tab’a rik’e wayar Hajiya a hannun saba sabida sam bata bari, amma yau data shigo hannun sa seya tsinci kansa dason shiga phone gallary nata, yana bud’e screen d’in wayar abunda yaci karo dashine ya zaburar dashi zaune, Momy ce zaune da yarinyar dayakeda yak’inin cewar itace sun d’auki hoto sunyi kyau ainun, kuma kallo d’aya zakawa ‘yar ka tabbatar wa kanka cewar tabbas yarinyar ‘yartace sabida tsananin kamanin dasuke da juna, yarinyar Jiya itace wannan ko shakka bayayi menene alak’arta da momy? Ta tab’a gaya masa cewar tanada yara biyu mace da Namiji ko wannan ce macen, ta sanar dashi sunan macen Khairiyya Namijin kuma Bilal, ko wannan itace, da sauri ya shiga gallary ya soma duba pictures ba shakka, dukkansu biyun da ita suke kama, ga hotunan su nan bila adadin tare da ita, har wani zuwa da tayi dubai ashe tare taje da yaran ta, lallai matar nan tunda suke da ita babu wanda acikinsu zece ga koda garinsu matar, lokaci tayi da itama zata d’and’ani kud’arta a hannun sa, seyayi amfani da kyawun dayakedashi da cikar kamala ya lalata rayuwar Khairiyya kamar yanda ta lalata masa rayuwa shima, da hanzari ya fita a komai daya shiga ya ajiye wayar ya sauya mazauni gaba d’aya, daganan ma wayarsa ya hau latsa tamkar ba abinda ya faru. Sosai tayi kwalliya cikin doguwar rigar abaya bak’a wuluk, ta nad’e kanta da d’ankwalin abayar bak’i hakan ba k’aramin fito da kyawun fatarta dake fara sol yayiba, tayi caras da ita tamkar wata balarabiya, bazaka tab’a cewa ta ajiye ‘yara kamar Bilal da kuma khairiyya ba, fuskar nan kamar yar 25yrs, kallo d’aya xaka mata ka tabbatar hutu ya ratsa ta sosai, se tanshin k’amshi take, da wani irin takun k’asaita ta tinkaro parlon tana wani irin k’ayataccen murmushi dayayi matuk’ar karb’ar fuskar ta. Akusada Bilal sosai ta zauna ta d’aura hannunta saman sumar kansa dake bak’a wuluk tasha gyara se shek’i take tana murmushi tace

 

“Son i missed you” Murmushi shima ya mayar mata dukda hankalinsa baya nan yace

 

“Same with me swt mom” Ya k’arashe maganar yana me d’aura kansa asaman k’irjinta, rungumesa tayi gaba d’aya

 

“Da Baba Audu da Baba Lami duk na turasu yawon ziyara dan kawai in huta dakai kad’ai, and kasan me? d’ago idansa yayi yana kallonta

 

“Menene momma? tana kashe masa ido tace “I have bought a new phone for you, amma bazan bakaba seka gajiyar dani gaba d’aya” Murmushi yayi yace

 

“Koba waya Mom aikin danazoyi kenan ai, in baki wahala sosai sekince son na tuba” Dariya tayi yanzu kam me sauti tace tana jan karan hancin sa

 

“Bayan haka kuma idan naji dad’in wannan ziyarar zan cika maka alk’awarinka” D’agowa yayi ya kalleta sosai da serious face

 

“Ban gane wanne alk’awari daga ciki ba” Mik’ewa tayi tana dariya tace

 

“2.5 million dakace rannan with a brand new car” Wara idanshi cikin tsananin mamaki dajin dad’i, cikinta yayi gaba d’aya ya d’agata yana zagayen parlon da ita tamkar wata k’aramar yarinya se dariya suke tamkar wanda suke raya sunnar ma’aiki suna tsumayin samun lada, bayan ya direta yace

 

“Tome zanyi na fanshi duk wad’an nan” kawar da kanta tayi gefe tace

 

“Abinda bakaso ne Bilal, sedai ni inaso, kasan ina maka kishin kaina bazan bari wani yazo koda kusa daniba, but seriously nagaji ina buk’atar wannan gently n sweet sucking naka, and for that even if i have to buy it with all i have, i will still buy it, because it worth it! ur just so different from everyone, i never get enough of u” Murmushi yayi ya rungumeta gefen kunnenta yaje da bakinsa, if thats what u really wan’t so be it, i will suck the hell out of your juicy p*****y today, tomorrow and for ever, amma fa ba saya zanyiba, for the love we had for each other i can even sacrifice my life for you, bare d’an wannan kawai dan ina amai ne nake k’inyi, bansan kinaso sosai haka, amma tunda har haka kikeso swt mom koda zan amayar da duka hanjina i will keep sucking it till u cry and scream no more” Gaba d’ayan sa ta rungumesa yanzu kam suka fad’a wata duniyar masha’a tun a palon….Wal iyazu billah, Allah ka shiryar damu.

 

***********

 

Bilal bebar garin ba se monday da safe wanda aranar iyayensa zasu dawo, mom kuwa dama Manager ce ta banki, ya zame mata dole taje office momday d’in, 3.M ta saka masa a acc nasa sannan a sunday sukaje ta sayar da motarsa ta saya masa biggest dream of his life wato Lesus C350 bak’a wuluk! se shek’i takeyi kusan 11.M ta saya masa, shida kansa Bilal yasan cewar Momy bawai aikin datake yake bata kud’in datake samu ba, duk wata 300k take bashi, mutane da dama suna zaginsa akan me mahaifinsa har yanzu yake gadi bayan kowa ya gansa yasan cewar tabbas shid’in yanada rufin asirin Allah, ga k’anwar sama batada maraba da mara future tunda yake ank’i a sakata makaranta shekarun goma amma kullum tana makale da Baba Lami. cikin tsananin jin dadi ya koma makaranta zuciyarsa fara k’al duk department nasu babu wanda yakaishi zama d’an k’walisa sedai kuma be isa yayi budurwa ba, ya rasa dalilin dayasa ya kasa son wata, duk inda ta motsa Mommyn sa kad’aice aransa daram!!

 

*************

*Bayan kwana uku*

 

Se a wannan ranar aka samu kan Mood wanda dole Juma’a ta wuce me martab’a be d’aura masa aure ba sabida yanayin conditin nasa, wannan karon kuma se ayi rashin sa’a ya farka amma kowa bayawa magana, baya rubutu bakumaya demostraring da hannu kamar yanda ya saba, hankalin Uncle Jay yayi matuk’ar tashi akan wannan abun, hartakai baya iya kula kowa shima, yauma kamar kullum zaune yake kusa da Mood hannunsa sak’ale acikin na Mood, ya k’ure masa ido baya ko k’iftawa, Mood d’inma idansa biyu kuma shima Jay yake kallo cikin tausayin kansu Jay yace

 

“Mood please dnt punish me like this, bani nayi laifin ba please talk to me kaji” Murmushi ya k’ak’alo ya sakarwa Uncle d’in nasa, wanda shima atake ya mayar masa cikin tsananin farin ciki “Mood me kakeso zakasha fura? Yanzukam seda hak’waran mood suka bayyana ganin so na hak’ik’a a fuskar Uncle Jay d’insa, Banda Muhseen,U Jay barra da Mamin sa babu me k’aunar sa, mak’iya sun masa yawa yanzu kuma ga wata sabuwar Mayya munafuka tashigo rayuwarsa, babu dangin iya babu kuma na baba amma ta janyo masa matsala fiyeda tunanin me tunani.A hankali ya gyad’a masa kansa akan zesha furar aikuwa nan danan ya kawo masa furar da dama tun safe yazo masa da ita, shiya taimaka masa ya zauna sannan da kanshi ya bashi yasah sabida hannunsa akwai raunin daya jiwa kansa sakamakon dukan glass dayayi. Sosai yasha furar sannan aka d’aura masa da maganin sa, Ganin Maminsa tazo dubasa ba k’aramin kwantar masa da hankali yayi ba,matsalar d’ayace yak’i yayi magana, idan matsayin ka yafi k’arfin k’yaliya seyayimaka murmushi kokuma ya gyad’a maka kai, A haka harcika sati d’aya wanda aka sallamesu rana d’aya da ‘Yar shara da aka kai asibitin k’walwa suka kuma d’aurata akan magunguna.

 

********************

Lokacin da Bilal yashiga school wuri ya samu a tsakiyar mini mart yayi parking motarsa, dama kuma Bilal sananne ne sosai a school d’in yanada gayu mabiyan sa kamar su masa sujjada, lokaci d’aya wurin ya d’auki sowa da hargowa aka soma yi masa kirari Bilal Babban Yaro Bilal babban yaro, seda sowar ta lafa sannan yace

 

“A wannan cafteria zakuci abinci ko a waje” Da ihu gayun sukace anan ma girmane Babban yaro” Yana wani jinkai yace

 

“Kowa yayi ko tayi iya yinta, daga nan zuwa k’arfe goma na daren yau a sanar nace duk wanda yaci wani abu a wurin nan nine zan biya” Ihun ne ya k’ara yawa sannan yace ciki isa

 

“D’an madami ze baiwa duk wanda ke wurin nan kyautar naira dubu goma daga yanzu zuwa k’arfw goma na dare” Nanma wata sabuwar sowar ce shima d’in a babban wurin dayafi kowanne k’ayatuwa ya nufa shida manyan abokanan sa don suci nasu abincin…….

Lokacin da khairiyya ta kammala cin abincin ta tana zaune jiran waitress d’in for payment amma batazoba.Wani ne yazo kanta ya irga dubu goma ya ajiye agabanta,kallonsa tayi “Na meye malam?” ta buk’aci sani cikin zafi “Calm down mana sis, kyauta ce daga Babban yaro” K’are masa kallo tayi “Bana karb’ar gift from strangers ka mayar masa” Wani xaro ido yayi “Ke ba’a mayar da kyautar babban yaro, cikin takaici tace “Malam na gode ka had’a nawa da naka nabar maka” Godiya ya mata ya juya ko’a jikinsa, aranta tana mamakin waye kuma wani babban yaro? se zuba tsaki take lokaci zuwa lokaci tana kallon agogon hannunta, ganin waitress d’in batada niyyan zuwa ya tilastawa Khairiyya mik’ewa taje reception nasu, kallon waitress d’in tayi tace “What is my bill you guys kept me waiting since, it is unusual naga kune kuke zuwa karb’a ko? Matar tana fara’a tace

 

“Bakiji ba kenan, ai Babban yaro ya biyawa duk wanda zeci abinci yau kud’i daga yanzu har goma na dare” D’an k’aramin tsaki tayi

 

“Count me out of that bullsh**t , my dear will u please tell me my bill” Kallon k’ofar tayi dake bayan ta,tace

 

“Ma’am its as simple as that fa, ba kud’inki ya huta ba” Duka Khairiyya ta kaiwa table d’in abinda k’aranshi ya karad’e ilahirin wurin harya janyo hankalin d’aukan mutan wurin akansu

 

“I said i will settle my bill, i have spoken!!! wane d’an iskan ne ya isa ya biya kud’in abincina, who the hell did he think he is, bannaso bana buk’atar alfarma awurin kowane d’an rainin hankali” Bilal dayaji kalamanta tamkar gaushin wuta seya kasa hak’uri ya tako yazo har gabanta yana watsa mata wani kallo

 

“ke! waye d’an iska” D’agowa tayi ta kalleshi ta wani yamutsa fuska

 

“Ohh God you again, Annah the mad man is here again” Be fahimci inda kalamanta suka dosa ba, kafin yayi magana wasu gayu sunyo kanta tamkar zasu cinyeta d’anye cikin isa tace

 

“You guys calm down mana, is he ur hero? kodan ya saya muku abincin wuni d’aya? waigawa tayi ta kalli waitress d’in datayi tsaye tamkar an dasata tace tana murmushi

 

“Daga yau zuwa wata shekarar iwar haka duk wanda zeci abinci a wurin nan na saya masa, be it breakfast, lunch or dinner or both the 3 meals per day!! Jakarta ta zuge ta zaro wani card a wata k’aramar waled ta d’aura akan table d’in

 

“Kullum kije ki cire kud’i adadin yawan abincin da kuka sayar a wannan card d’in” Harta juya babu wanda ya koda motsa ciki kuwa hadda Bilal, sanda takai k’ofa sannan ta waigo tana murmushi tace “3753 is the code, remember wata shekarar iwar harka i will come for my card so take care of it sosai sosai” Tana kaiwa nan ta juya tabarsu da sakakken baki kowa se mamakinta yake, Bilal wani bak’in ciki ya ziyarcesa yama rasa me zaiyi, ya tsani yarinyar dayakeda yak’inin ‘yar sugar mommyn sace shizata wulak’antar har haka, amma idan yace ze gwada fushi yanzu shine zai wahala, dan baze samu abinda yakeso ba kenan, da sauri yabi bayanta dogarawa yagani a wurin motar dataje shiga atake aka bud’e mata k’ofar har zasu rufe ya k’araso yana haki

 

“I come to appologise, am very sorry please, am not bragging, am not doing it for my name, I’m only trying to help, bansan kina cikiba, dana zare sunanki aciki Ur royal highness” Ya k’arashe maganar kanshi a k’asa, this is exatly what Princess Riyya want, a duk’a mata, a nuna mata ita watace ,a girmama ta and he got her just right there, lokaci d’aya ta manta daduk wani abu daya shiga a tsakanin su na b’acin rai, ta sakar masa murmushi

 

“Bakada matsala, mun fahimceka” Yana murmushi yace

 

“Nasan ban isaba nasan ban kaiba, amma ina neman alfarma” Tana murmushi tace “Haka mukeso tame kenan?” Sosa sumarsa yayi

 

“I just want to befriend her Royal Highness” Tana murmushi tace

 

“Grab this. 08030000000, princess Riyyah from the kingdom of Baihatul Mulk. the code is 3753, i will be expecting ur call friend” Wayewar ta ta gama dashi, wannan tashin k’asar nan ce kuwa? ya ayyana a ranshi lokaci d’aya ya haddace komai sedai kuma be gane wanne code bane wannan, any ways kallon ta yayi

 

“Thanks for everything your royal Highness” Matsawa yayi aka rufe mata sannan ta zuge glass tace dashi

 

“Remember just friends” Had’e hannunsa yayi alamun godiya sannan yace

 

“My pleasure” Ya juya yana murmushin samun nasara!!!!

 

 

**************

Tunda suka dawo be sanya wannan munafukar a idanshi ba, bayamason ganinta, yanaso yaje gidan U jay amma bayaso yaga wannan mayyar Munafukar, dan haka bejeba se waya ya masa, a wannan yammacin ne aka aiko neman sa daga fada, badan yasoba ya shirya sosai ya nufi fadar idanshi a lumshe yana aikin daya saba na gudu. Mutanen fada yauma kamar kullum suna nan a jere kamar yanda suka saba, a tsakiyar su ya ratsa yaje gaban sarki, bayan ya duk’a ya gayar dashi sekuma yayi shiru seda fada tafi mintuna goma shiru sannan sarki yace

 

“Hamood yarinyar daka lalata zamu d’aura maka aure da ita nanda sati biyu, dukda kaji tanada matsalar k’walwa.” bece komai ba se kallon uban dayake, shikuwa sarki yaci gama

 

“Na gayawa Aminina kuma abokina Sarkin masarautar Baiha, na Baihatul Mulk yakuma yi fad’a sosai akan zubar mana da mutinci dakayi, yace lallai a aura maka wacce ka lalata d’in bayan haka ya baka auren ‘yarsa Khairiyya sabida dolene jini irin naka se naka, wato sarauta, ‘yar talakawa sam bata dace dakai ba, dankai kajane” Wani irin bak’in cikine ya lullub’e Hamood tozarcin har nisan wata masarauta aka kaishi? Lallai mahaifinsa baya k’aunarsa, auren mata biyu aciki babu wacce yakeso, da k’yar ya had’a hannayensa biyu alamar godiya ya sunkuyar dakai sannan ya mik’e, me martaba cikin isa yace

 

“You are dismiss” Ba musu ya juya da gudu kamar yanda yazo da gudu, koyau dayazo kusada D’an galadima seda ya tsaya suka kalli juna atake ya karanto zuciyar D’an galadima dake kallon sa yana murmushi!!!

 

*****************

“Annah, wane magana nakeji wai, aure ni kuma am just 18 fa kasheni zakuyi, kuma bansan mijinba bance ina sansa ba se wani aure, wani abun takaicin ma shine wai kurma ne fa, duk ajina? Mik’ewa Annah tayi tana zagayen d’akin ta amma batace komai ba, me Sarki Mu’az yake nufi da itane wai? ita ba uwarsa bace ba, matsayinta da queen mother batada wani isa ne kam da za’ake mata wannan abun?..

 

*Bansaniba ko kuma kun rud’e yanda na rud’e, ku sani ko hawa bamuyi bare gangara, kuna kallon wannan puzzle d’in, anya zamu iya kuwa….kumuje zuwa, kuci gaba da bibiyar alk’alamin Mom Nu’aiym domin jin yanda zata kaya..

 

 

Yawan comment yawan typing, i cannot come and kill my self….lolxxx.

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top