Tsintar aya hausa novel

Tsintar aya hausa novel

 

 

 

 

 

 

 

*TSINTAR AYA*   FREE BOOK

 

*BILLY GALADANCHI*

 

 

 

 

 

 

*SHAFI NA GOMA SHA TARA*

P19

Zaman fada ake cikin tsananin jin zafin juna, kowanne da abinda yake sak’awa aransa game da d’an uwansa, tsananin takaicin juna akeji a wannan zaman, gyaran murya Me martaba yayi sannan yace

 

,”Hammood ya bada sak’o a gaya mana ta hanyar kawun sa yana neman alfarmar a k’ara d’aura auren sa da waccen  yarinyar da abu ya had’asu a baud’e” Zabura magatakarda yayi sannan cikin girmamawa yace

 

“Ranka ya dad’e ayi haka? Kallon sa me martaba yayi sannan ya d’auke dubansa daga gareshi yace yana kallon Jay

 

“Menene kake tunanin ya dace akan wannan maganar, naso sosai hankalin sa ya soma kwanciya akan matarsa ta farko, banason rigima”  Zubewa yayi yana me bada girmamawa kafin yace

 

“Idan mukayi duba da yanayinsa na farko akan maganar auren zamu iya yiwa Allah godiya hakan yana nuni ne kai tsaye da cewar hankalin sa ya kwanta da iyalansa har yake sha’awar k’ari, dan haka ina ganin gwanda acika masa burinsa kawai” Magajin garine ya zube kafin yace

 

“Allah yaja daran sarki, banaji hakan tunani ne me kyau, idan har akayi hakan ita gimbiya khairiyya nasarautarta bazuji dad’iba sam, duba da cewar dududu auren nanfa ko wata shida be rufa ba”  Sarkin baka cikin girmamawa yace

 

“Mahaifin gimbiya khairiyya yasan da maganar ita wannan yarinyar ai, ai gata ya masa dacen farko kuma yanzu akan gimbiyar ai bazamu fasa cikawa yarima me jiran gado burinsa ba Allah yabaka nasara”  haka kowa da abinda yake fad’a akan maganar daga k’arshe Sarki yace zeyi tunani akai…………

 

******************

Yau Hafsat sun tashi a aschool kai tsaye Bus stop sukaje itada k’awayenta, tunda taketa wannan ciwon tadena yawo ma sam, tana nan zaune suna jiran isowar Bus se ganin Hammood tayi a gabansu, mik’ewa tayi ganin ya jingina da mota ta matsa kusa dashi, seda suka kalli juna na some seconds sannan tace

 

“Yaa Mood Barka da rana” kallon sa take yanda yake wani yamutsa fuska kuma ga mamakin ta seya motsa bakinsa amma ba magana yayi ba, hannu ya nuna mata ta shiga mota seda ta gama karantar yanayin sa sannan ta juya dayiwa cylia da chidi sallama ta bud’e gidan baya ta shiga, shi d’inma baya ya zauna ya janyo New’s paper ya soma dubawa abinda yake shirinyi rayuwarsa banda harbawa babu abinda take amma duk yanda yaso yaji maganar Uncle Jay yau ji yake baze iya ba, shi d’inma namiji ne, ya mallaki hankalin kansa, yanada matuk’ar muhimmanci ya yak’i mak’iyansa, yanzune lokacin daya dace ya zauna acikin mak’iyansa ya dena tsoron su ya nuna musu iyakar su….A b’angaren Hafsat kuwa Allah ya halicceta da saurin karantar halayen mutane, indai har ta nutsu mutum ya nutsu tokuwa sedai idan bashi take kallo ba, amma muddin idanta yana kan mutum to kai tsaye zata iya karantar zuciyar sa akowane yanayi suke atare musamman idan akace idansu yana sark’e dana juna, a irin hakan ta karance Bilal tunkafin ya bayyana manufar sa akanta, a irin haka ta karance halin da Bilal da momy suke ciki tun kafin ta fara jiyo sautuka muryoyin su suna shek’e ayarsu, a irin haka take janye jikinta daga duk wani me sak’a gadar zare iri biyu a rayuwar ta, Hafsa yarinyace da magana be wani dameta ba, amma tanada wayau fiye da tunanin duk wani me tunani, wayonta yakaita gacin nasara ta k’waci kanta a hannun Bilal! Wani mayaudarin murmushi ta sakarwa kanta tunawa da yanayin idan, labarin da zuciyar sa ke bata daban akanta amma idansa yana yawan k’aryata nazarin sa, zuciyar sa tak’i tsayawa akan cutar dashi zatayi idan nashi ma basu gama yadda da hakan ba, abinda ta lura dashi a yanayin sa na yanzu akwai abinda yake shirin aikatawa sedai ya gagara nutsuwa ya aikata koma menene, kawar da kanta tayi daga dubansa zuwa ga hanya taga gaba d’aya ba hanyar gida suka d’auka ba, wani siririyar dariya tayi me had’e da Hmm tana son wannan baiwar da Allah yayi mata, tana tsananin jin dad’i idan tayi karatun faifan fuska da zaren zuci ta canka daidai kanta har wani fad’i yake, d’agowa yayi ya kalleta idansu ya sark’e dana juna ko wannensu ya gagara d’auke idansa ana d’an uwansa har lokacin murmushi ne k’unshe a fuskar ta yayinda yake k’ara had’e tasa fuskar sa a zuciyar sa yanaji tamkar yarinyar nan ta gama raina masa wayau dariyar me take, k’ara fahimtar abinda yake tunani aransa ya tilasta mata k’arayin wata dariyar babu shiri wacce a wannan lokacin kasa hak’ura yayi ya damk’o k’aramun d’an k’walin data rufe kanta dashi me zubin hankici ya had’o tare da sumar kanta, idansa anata amma ga mamakin sa go gezau batayi ba, bata motsa ba, bata kuma nuna alamar taji zafin rik’on ba, d’auke nashi idan yayi anata sannan ya cillar da ita gefe yana jan gajeran tsakin daya fallasa tabbas harshensa yana motsawa ya kwantar da kansa akan jikin sit motar yarasa mesa hankalin sa yake yawan d’aukewa zuciyar sa bata masa sassauci akan kai hannun sa jikin Hafsa, besan wane irin k’i yake mata ba haka, koda yake shi halittarsa ce k’in duk wani mak’iyin sa indai har ya fahimci kai mak’iyin sane tokuwa tabbas shima daga ranar ya dena sonka har abada, driver daya gaji da shawagi dasu seyace

 

“Yallab’ai ina zamuje? Beyi magana ba bashida niyyan yi, har yanzu yana b’oye ainahin gaskiyar magana hafsat ce ta kallesa ya lumshe ido amma bashida niyyan magana tace

 

“Take us home” Bud’e idanshi yayi ya zube su tas akanta tace tana gyaran sumar kanta

 

“Take me home i mean, bansan inda yakeso yaje ba shi, amma ni gida zanje” Parking driver yayi ya waigo yace “yallab’ai muje gida ne?” A hankali ya gyad’a masa kai ita kuwa ta d’auke kanta ganin driver ya d’auki hanyar gida tace a sarari

 

“Ko’a tarihin hikayoyin da suka gabaci zamanin mu ban tab’ajin labarin ko wanda ya tab’a ganin kurma wanda takejin komai amma baya magana ba, se kai yaa Hammood kai d’an baiwa ne, sam harshen ka baya motsi” Yi yayi tammar beji taba, dankuwa ko motsawa beyiba harta k’araci maganganun ta na rainin wayau aganin shi……….Motar yana parkawa da sauri ta fito ta zari jakarta, kanta yana mata ciwo sosai akan rik’on sumarta da yayi, tarasa metayiwa wannan man d’in yakeji da kansa sosai, mugu kawai. A k’ofar shiga parlor tayi karo da khairiyya zata fito ita da muk’araban ta, kallon juna sosai sukayi sannan da k’yar Hafsat tace

 

“Sannu da gida khairiyya” Dama khairiyya ta shak’a ganin Hammood ya d’akko Hafsat daga school sekace ba Bus take dawowa dashi ba, rigarta ta janyo tayi dragging nata gabanta dan ita hartayi gaba abunta

 

“Ban hanaki kiran sunana ba gatsai, ni sa’ankice gimbiya khairiyya zakice jahila kawai” yamutsa fuska hafsat tayi har seda duka gefen chicks nata suka lob’a, tana kallon cikin idon khairiyya tace

 

“Koda wane lokaci ina mamaki idan akace waike gimbiya ce haihuwar babbar masarauta irin ta Baiha, gabaki d’aya yanayin magana kike irinta ‘ya’yan buje, wannan dalilin ne ya sanya bazan tab’a jinginka ainahin sunanki da wata kalmar gimbiya ko princes ba, ki bari tukunna randa duk kika zama me irin kalaman tushenki, ni matsa ki bani wuri danla” Cikin d’aga murya khairiyya tace “Kutmar uban cen kai ni kike gayawa magana a baud’e, hannu ta d’aga zata kaiwa Hafsat mari Hafsa ta tare hannun ta cillar dashi

 

“Idan kika sake kai hannunki jikina karyaki zanyi wlh, sannan kuma dakiketa izgilin cewar ke sarauniya ce kije masarautar Daulatul Dinar kiji wacece ni, nima haka ake kirana Princess Hafsat, kuma nima gimbiyar ce, mijin dakike tak’ama dashi soon enough zamu fara sharing nashi dake, ya kamata kisan me kike ciki danna kula sam bakida wannan ilimin, idan kinaso inke kiranki da suba Princess Riyya kema daga yanzu kike kirana da suna princess Hafsah ina fatan kin gane, laslas karki k’ara tareni a hanya kinamun hayaniya sam banason irin wannan wuce gona da iri” Tana kaiwa nan tayi gaba abinta tabar Riyya sororo baki a bud’e tana mamakin wannan rashin mutunci.

 

 

Da yamma Mood yana zaune a garden Uncle jay ya masa text message

 

“Gaba d’aya a fada komai ya cab’e, zasu d’aura maka aure sa wannan yarinyar gobe amma sunce se idan ka amince zaku dawo Nigeria koda na 4month ne, acewarsu zasuyita fitinane matan” Nisawa yayi yana tunanin mezaice shi bawai danze kwanta da ita koyana wani santa ze auretaba kawai close mark yakeso ya bata ta hanyar dazesan duk abinda take shiryawa akansa, layintama bawai k’yalewa xeyi ba dole seya ringa sanin dawa take waya kuma a wane lokaci, suna kammala aikin dake gabansu ze tattarasu har ita har yan iskan dake sanyata subar masarautar, kansa yayi zafi besan mezaice

 

“Hakan yayi zamu dawo nanda sati biyu su d’aura a goben inyaso bazan gayawa dukkansu ba semun dawo se Bahar ta gaya musu har amaryar” Nisawa Jay yayi, ya tabbatar Hammood is up to something bayason gaya masa ne kawai dan yasan ze iya hanashi yin koma menene, amma bari ya bashi dama tukunna, lolaci yayi daze gwada nashi ilimin ya gani ko zasu dace…..

 

*****************

Sarki be b’ata lokaci ba Bahar kawai ya gayawa daganan aka d’aura auren dan ita dama burinta kenan, wayarta ta d’aga ta kira Hafsat da zumud’i Hafsa ta d’auka tana murnar ganin kiran kakarta me sonta

 

“Ammu na oyoyo” Dariya me sauti bahar tayi kafin tace

 

“Amarsu ta ango, amarya ansha lalli” Da mamaki hafsa tace “Amarya kuma Bahar a ina amaryar take” murmushi irin na manya Bahar tayi ta gano kenan Hammood be sanarwa Hafsat ba setace

 

“Ji nayi ance za’a d’aura muku aure da Hammude ne ai” B’ata fuska tayi

 

“Mejan gashi zakice Bahar mugun zan aura tab Allah ya kiyaye nisai me kirki” Dariya Bahar tayi

 

“Kiyi hak’uri Attatuna kinsan fa alk’awarin dakikamun ko wannan damace da samemu, dan Allah karkiyi musu akan D’an kurma yana neman taimakon ki” Nisawa tayi

 

“To kaka Bahar i lobiyu, zanyi maneji dashi, shid’inma dandai yana yanayi da larabawa ne da badan ba ruwana dashi, kuma Allah ki kirasa a waya ki gaya mar ya dena cin zalina inba hakaba zan rotsa masa waya aka in gudu wurinki” Murmushi Bahar tayi na manya

 

“Attatuwa zanga ranar da xaki girma kinji, nidai yanxu wannan maganar sirri ce karki gayawa kowa” Tana murmushi tace

 

“Bahar na kusa inzo in ganki yaa Hammood yace wai dana kammala exams zamuzo hutu”

 

“Mezan dafa miki.im zakizo? Tsalle tayi daidai lokacin da hammood yashigo parlon tana rawa tace

 

“Bahar ina wannan miyan yauk’in dakejin daddawa sosai? Wanda kike dafawa da kanki acikin wannan tukunyar na laka? Bahar tanata dariya tace “Naganeshi Hafsat”

“Yauwa sweety kin ganeshi sosai toshi zakimun da tuwom dawa me santsin nan seki saka a soyamun zabi kuma sannan amin kunun gyada” Bahar tace

 

“Duk da kaina zan miki ma, ni kinsan ina son shiga kitchen dandai tsufa yaxone amma ko zamanin sarki me rasuwa nice sarauniya acikin matansa amma ninake masa girki ba ruwana”

 

“Yauwa Ammuna i lobiyu lodi lodi zan sayo miki wannan madarar dakikeso sosai” Nan sukayita hira shikuwa yayi tsaye k’ik’am yana kallonta yama rasa meyake kallo ajikinta, yau da aka tabbatar masa an d’aura masa aure da ita shida yayi auren manufa segashi ya tsinci kansa cikin wani irin farin ciki mara misaltuwa. Sanda ta ganshi tsaye abayanta turo baki tayi, shikuwa ya tsaya yana k’arewa d’an tsirut d’in bakin da data turo gaba kallo, cin k’unk’uni tace

 

“Shi mutum kawai baze yi sirri ba se an saka masa ido abinda banaso kenan” Ta antaya da gudu dantasan yaji me take cewa sarai, kuma inya damk’i sumar kannan nata dababu d’an k’wali setayi fitsari, murmushi kawai yayi ya girgiza kansa ya wuce d’akin khairiyya……..kallon sa khairi tayi tana mamakin annurin dake d’auke a fuskar sa kafin tace

 

“Ranka ya dad’e wannan farin cikin dakake yau ya dace muje yawo gaskia, musha iska mu shak’ata” Rungumarta yayi yanajin wani yanayi na musamman dabazece ya tab’a tsintar kansa a irin wannan yanayin ba gaba d’aya rayuwar sa! D’agowa tayi suka kalli juna tace

 

“Honey muje yawo please” Murmishi yayi tare da gyad’a mata kansa, k’ara rungumeshi tayi “Thank you love” Sannan ya soma shiri sauri sauri. A bangaren hafsa kuwa batada masaniyar cewar an d’aura aurenta da Mood dan haka sun gama shirinsu akan zasuje yawo itada Bilal da k’awarta Cylia dan haka batare da b’ata lokaci ta shirya taje gidansu cylia acen aka cab’a ado na musamman Bilal yazo ya d’aukesu suka daushi hanyar Beach…..

Sunsha wasannin a Beach sunta ciye ciye, sun shiga ruwa sunyi jagab, yayinda shima Hammood da khairii Beach d’in suka je, basu suka had’uba seda kusan yamma sosai lokacin har Hafsat suna shirin zuwa gidan kawai Hammood se hangota tayi suna wasa da ruwan da ita da Bilal,idan ya watsa mata itama ta watsa masa, dake tuni khairi taje hawan lilo acewar ta tana tsoron ruwa sosai, Wani irin yanayi mara dad’i Mood ya tsinci kansa aciki, hafsat wane kalan iskanci take koya awurin Bilal da wannan baturiyar me kamada kazar k’auri ? Yaushe yayi saken da har sukayi sabo da Bilal haka? Yasan Bilal yana zuwa dubata sosai ko sanda batada lafiya amma beyi tsammanin shak’uwar su hartakai suyi sakim jiki haka da juna ba, a fusace yaja khairii suka nufi gida, ita kanta tayi tsananin mamakin sauyawar yanayin sa lokaci d’aya! Amma batace masa komai ba har sukaje gida, bayan ya shiga ya watsa ruwa zuwa yayi bakin gate ya tsaya, yana nan har Bilal ya sauke Hafsat lokacin dare yayi kam dandai sedai hasken fitilun street amma ba komai me kamada haske sam! Tana takowa har lokacin wandon dake jikinta da top a d’ame suke da ita d’am babu inda wata iska zata iya kutsawa kuma yasan duk waccen cylia ke rikitar mata da kai, kamar daga sama yaja hannunta seda ta k’walla k’aramar k’ara kafin ta gane shine, har cikin gidan yajata suka shiga kai tsaye d’akinta yashiga da ita seda ya manna masa key tana tsaye tana kallon sa gaba d’aya ta tsorta da yanayin sa dan kuwa ta gama hango fitina kwance a fuskar sa, Juyowa yae a fusace bayan ya gama yiwa d’akin key sannan ya soma tinkarota a hasale, a hankali ta soma ja dabaya ta fahimci bin shawarar Cylia akan ta dena tambayar fita ba abu bane me sauk’i dan ta tabbatar shine abinda yaa mood kewa wannan ciccikar, har seda suka matse bango sannan ya mata rumfa, goshinsa yakai akan nata nan take ta runtse idon ta, k’irjinta yana tsananin dokawa hannunsa ya kai daidai fatar cikinta agefe kunkurunta yayi mugun matsewa seda tayi k’ara, janye kanshi yayi daga goshinta baze iya hak’ura ba yau seyayiwa wannan sharar magana yace muryarsa cen k’asan mak’oshin sa

 

“Idan kina tunanin zan k’yaleki akan abubuwan dakikemun na fili dana b’oye toki dena wannan tunanin danba k’yaleki zanyi ba sam, idan kuma tunani kike kin isa ki fita bada izininaba agidan nan ki kuma gwadawa ki gani, karna k’ara ganinki tare da Bilal, koda gaisuwa ban yadda kukeyi ba bare har kije beach dashi kuna wasan watsawa juna ruwa kinajina ko? Rashin kunyane da Hafsa tak’in k’arawa cikin masifa tacw

 

“Dankai ubanane? Kodan kai waye awurina da duk kake tunanin zanyi duk wad’annan abubuwan dakake lissafomun” hannunsa dake kan kunkurunta ya sanya ya k’are matsewa sesa ta kai hannunta tana magiya kafin yace ko yanzu k’asa k’asa cikin kunnenta

 

“Sabida ni mijinki ne, an d’aura mun aure dake tun safe yau, wannan kayan dakike fita dashi sekace chidera jikar inyamurai ma idan na kuma ganinki dashi a waje sena b’abb’alaki” D’agowa yayi suka k’urawa juna ido cikin ido sannan ta kanne tsoron datakeji tace

 

“Bantab’ajin hikaya mafi ban dariya irin naka ba, ni bebin roba ne? Kokuma a’a ni totuwar rake ce dazakace an d’aura aurena dakai” Bakinta ya matse da hannun sa k’wayar idansa yana yawo acikin nata

 

“Hafsat kinsan Allah, bazan tab’a ragawa rainin wayon nan naki ba, idan kikace tsiwa zakimun a hankali zanyi maganin tsiwar” k’wallah yana fita a idanta tace bayan ya sake bakinta

 

“Mugu kawai me k’aryar kurumta” Tana fad’ar haka ta zame ta k’asa daga rumfar daya mata ta fece ta oc d’insa, toilet ta fad’a amma shi sam bebi bayanta ba tsayawa yayi kawai yana tunanin dalilin daya aikeshi yi mata magana!!!

 

*************

*Bayan sati biyu*

 

Har sati biyu ta cika wasan b’uya akeyi tsakanin Hafsat da Hammood tunda ta kira bahar aka tabbatar mata da zancen auren gaba d’aya se hankalinta ya tashi, wata irin damuwa mara misaltuwa ta shige ta, lallai tabbas yau ta tabbata mara gata wannan wane irin aure ne? Ace koda Ummi bazata iya kiranta ta sanar mata ba, rayuwarta gaba d’aya a baud’e take, koda wanda ya tsinci kansa agidan marayu yafita gata ayau, tanada family, na uwa dana uba yaya zata k’are a haka, babu me saurarar ra’ayin ta, bame saurarar uzirinta bameso yaji me take so ita kenan ba kowa bace, da wannan damuwar ta rage walwala sedai tas kudirinta yana nan nason shiga al’amuransa dasuka shige masa duhu…….A b’angaren Hammood kuwa banda damuwa ba abinda yake ciki, yayi imanin cewar yayi katob’arar yin magana ya bud’ewa hafsat sautin muryarsa, besan da wane ido ze kalli Uncle Jay ba, bare kuma Barra datasha gargad’insa aka ko khairiyya kartasan bakinaa yana bud’ewa dan kuwa mata wawaye ne, acewar su kosu haka suke fama da magana dashi irinta wahala ta kurame,dan haka ya zame masa dole ya iya takunsa, mesa bakinsa yake k’aryata zuciyar sa akusa da Hafsat kullum se idan be ganta ba, amma duk suka kasance a tare babu abinda ke hanawa zuciyar sa bugawa dason furta kalamai irin na baki agareta, yaudai yayi kudirin nemanta su fita dan kuwa nanda kwana d’aya zasuje Nigeria yana da kyau ya sanar mata karta kuskura ta gayawa wani wannan sirrin dan haka sak’o ya tura mata akan k’arfe 5 na yamma ta sameshi a mota parking lot zasu fita, dan magabar tafiyar ma baharce ta sanar mata.

 

Yau d’inma wandone d’amamme ajikinta sedai wannan karon kaftan top ta saka tare da d’aura k’aramin d’ankwali ke zubin hanky akanta, sumarta se yawo take abayanta dan kuwa batayi parking na sumar ba ta zubar dashi abayanta se shek’i take, tana yawan sonyin mu’amala da makeup wannaj ya sanya fuskar nan rad’am take da light makeup wanda gaba d’aya yake shirin turata a jinsin larabawan usul! Kallo d’aya ya mata ya d’auke kanta yauma kamar kullum atare suka zauna a bayan motar driver cikin girmamawa ya gayar da ita sannan suka kama hanya, wani restaurant suka je acen suka jeru domin shiga daga ciki, hannun ta ya kama ya rik’e batare daya kalle taba ita d’inba bata k’wace hannun nataba bata kuma ko kalle saba har suka zauna inda takeda yak’inin an tanadesa ne domin su, lemo aka aka ajiye haka sukai shiru ita ma yau fuskar nan a d’aure tamau, seda yasha lemom ta hanyar zuk’a da straw ya zare gilashin idansa ya ajiye sannan ya shanye idansa anata ya tangale hab’arsa da hannayensa daya dunk’ule sannan yace yana kallon ta

 

“Kinsan dalilin dayasa muka zo nan” Kallon sa tayi ta yamutsa fuska ya dinga yin abubuwa da izza sekace ajiye mutane yayi cikin takaici tace

 

“Saukar wahayi ne inaga” D’an had’e fuskar sa yayi “Me kikace ? Kallon sa take har lokacin sannan cikin tsiwa tace “ka manta” Wani gajeran murmushi yayi da gefen bakinsa kafin yace

 

“Hafsa Abu biyu zan gaya miki, da farko dai wannan shigar dakike kina fita bazan lamunta ba har abada, karki kuskura ki k’ara koda tunanin fita a haka, abu na biyu kuma magana ce akan wannan maganar ta fatar baki damuke nidake, ki sani ko.Ummi na bana magana da ita sabida wani babban dalili damuka barwa kanmu sani, matata zab’ina khairiyya ma dakika gani batasan wannan harshen nawa yana kad’awa ba, inada tarin mak’iya irinki masuso kawai susan sirrin harshena, dan haka ya zame miki dole ki adana wannan sirrin, idan kikayi gangancin zuwa Nigeria koda shadow d’inki kika gayawa mun tab’a magana haka dake wlh sena b’atar dake a doron k’asa, abu na k’arshe dazan gaya miki kuwa shine daga yanxu, karki kuskura kokuma kiyi tunanin zan k’ara miki magana a haka, munyi na farko bisa rashin sani, mukayi na farko bisa kuskure wannan ya zama ma k’arshe kuma munyishine bisa tilas sabida haka anyi farko anyi k’arshe kinaji na ko” sake baki tayi kamar me mamaki seda yakai aya sannan ta tab’e baki tana murmushin kama rainani sannan tace

 

“Kasan Allah wlh sena tona maka asiri, sena gayawa duniya bama masarauta ba duniya setasan kai butulu ne ka butulcewa Allah da Ni’imar bakin daya baka kana living fake life, ur all fake bakada godiyar Allah, sabida haka sena fad’a coward! Kalmar ta ta k’arshe da matuk’ar dakesa a k’irji dukan ya kaiwa table d’in sannan ya tarwatse duk abinda ke table d’in cikin k’araji sannan isa gabanta ya cafki sumar kanta, atake jijiyoyin kansa suka bayyana tsananin b’acin rai ya haddasa masa ganin jiri da kuma harbawar zuciya, take ya sake kanta yayi azamar zaunawa, ya dafe kansa kusan minti biyar be motsa ba, dan haka hankalinta ya tashi da sauri taje ta dafa shoulder’s d’insa

 

“Dan Allah kayi hak’uri” hannun sa ya sanya ya doke hannunta dake kan kafad’arsa da sauri tayi waje kai tsaye taxi ta hau tawuce gida tanata kuka a motar, tayi danasanin abinda ta gaya masa, tarasa dalilin sayasa take yawan fusata akan sha’anin Mood, koda gaje zalinta yakeci shisa.

 

Basu kuma had’uwaba sesa zasuje airport, nanma dai irin wannan shigar ta kumayi amma wannan khairiyya ce ta mata magana akan bazeyiyu ta doshi masarauta a hakaba ko kallon khairiyya batayiba har suka hau jirgi zuwa Nigeria. K’asar dasuka tsaya transit ma bakinta da nashi be had’uba, anan ta sauya kaya dan sesa suka kwana ta sanya jallabiya cream me adon dutse bak’i tayi matuk’ar yi mata kyau, sannan suka d’auki hanya dukda a k’ule take da Hammood dankuwa wannan karon iya shisa Khairii ne kawai a VIP ita tare da kuyangi sukabi yarima sukasha kid’ansu.

 

*Nigeria*

 

Tunda sukazo khairiyya b’angaren hammood sabo acen suka sauka sabida dama yayi gini acikin masarautar me d’auke da part biyu gefe gefe manya da madaidaici a tsakiya, na gefen dama khairiyya anan danginta suka gyare mata wanda dama tanada labarin hakan se hagu da aketa hidima acikinsa na kai kaya k’awata wuri.

Durk’ushe yaukam Ameena take agaban Hafsat tana gaya mata yanda akayi

 

“Ranki ya dade anmun waya da kuma sak’on inda zamuyi meeting da ‘yan k’ungiya a daren yau, tun zuwanmu dama aketa shirin hakan” Murmushi Hafsat tayi kafin tace tana kallon Ameena

 

“Kai abin yazo a daidai lokacin danake sha’awar faruwar hakan, nice zanje taron ba keba” Da sauri Ameena ta kalleta ita kuwa taba dariya tace

 

“Karki damu ai kince basa bari wani yaga wani ko, bazan bari asirin mu ya tonu ba, bazan mayi magana ba akwai abinda nakeso najine da kunnena Meena” Jinjina kanta tayi sannan tace

 

“To babu damuwa ranki ya dad’e, sunce da magrib zasu ajiyemun kayan sakawa a wani wurin zanje na d’auka” Jinjina kai Hafsat tayi kafin tace

 

“Wannan yayi daidai, zanyi basaja da magrib sena sauka a d’akinki kekuma karki fito harse zuwa safiya” Meena kanta a k’asa tace

 

“Amma ranki ya dad’e keda kika fini sanin suma inaga ai kyau kema ace sun gayyaceki sunce babban tarone” Murmushi Hafsat tayi aranta tace ba laifi itama wannan yarinyar akwai brain “Idan suka gayyaceni Hammood ze gane kekuwa, kinsan fa ni komai nawa anfiso ya zama sirri” Jinjina kai Ameena tayi “Ea gaskia Ranki ya dad’e hakane” Hafsat gyaran zaman ta tayi sannan tace

 

“Ina mutumin damukayi zaki had’ani dashi idan mun dawo? Shiru Ameena tayi kafin tace “Na bincikesa ance wlh ya koma ghana” Tsaki kad’an Hafsat tayi sannan tace

 

“Yadai zamar mun dole in ziyarci tsohuwar secondry school d’ina, uncle computer nake nema, akwai abinda nakeso na tambayeshi ni banda waya ba abinda na iya operating sosai gwanda ma laptop yanzu nad’an iya”

 

“Ranki ya dad’e me zakiyi dashi to” tab’e baki tayi

 

“Ba ruwanki kinji, tashi kije” Haka Ameena ta mik’e tana mamakin wayo irinna Hafsat, yarinyar nan seta warwasa ilimin tantiri kai tsaye…..

 

********************

Se k’arfe uku da rabi na asuba sannan aka tashi daga wannan taron wanda tsabar tsorata dajin abubuwa Hafsat kasa d’auka kanta tayi, a wannan safiyar kuwa Hammood yana zaune da waya a hannun sa yana duba labarai na wannan safiyar yaci karo da wani heading .

 

BREAKING NEW’S..*Ashe dama prince Hammood na masarautar Daulatul dinar ba kurma bane?* Da sauri ya mik’e tsaye ya nanata wannan rubutin yakai so goma kafin saitin kansa ya tsaya akan abinda ya gani, k’irjin sane ya doka, tabbas wannan aikin Hafsa ne, dama abinda ya kawota kenan, abinda tazoyi kenan kuma gashi tacika burinta a wurin mak’iya, idan hakane se yarinyar nan ta yabawa aya zak’inta, seya nuna mata iyakarta ayau, setayi danasanin zuwan sa a dumiyar ta me cikeda hazo!!! Wayoyin sane suka hau ruri kusan a tare, nan Uncle Jay ne d’ayar kuma Ummin sane gaba d’aya babu d’aya daga d’aga dankuwa yasan ko zancen me zasu masa!!!

 

 

Hafsat dake rik’e da wayarta a wannan lokacin tana karanta New’s d’in itama murmushi tasake wanda ita kad’ai tasan ma’anar sa.

 

MOM NU’AIYM.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.