Tun Kafin Aure Hausa Novel Complete
Motsi kadan sai ta daga labule ko zata ga shigowarsa amma shiru. Dawowa tayi falo ta shimfida abin sallah don tana gudun kada ya dawo ya shige daki bata sani ba. Tayi raka’a takwas duk biyu tayi sallama ta sake tashi ta daga leka wajen, wannan karon ruwa akeyi kamar da bakin kwarya tayi ajiyar zuciya…daya daga cikin lokutan amsar addua kenan sai ta koma kan abin sallar ta fara addua. Tana yi tana kuka bukatar tata bata wuce Allah Ya shirya mata Junaid ba. Jin alamar shigowar mota gidan yasa tayi saurin kashe fitilar falon ta koma gefe ta tsaya. Bata dade ba taji ya bude kofar a hankali ya shigo da sanda kamar wani barawo. Mamaki ne ya kamata yadda yake da key din kofar bayan ta rufe ta sannan ta kwashe duka keys din. Yana kokarin hawa sama ne yaji ta haske masa fuska da touch light din wayarta….wane dan kut….maganar ce ta makale a bakinsa ganinta a tsaye fuskar nan kamar bata taba dariya ba. Duk da a buge yake amma sai da gabansa ya fadi.
Saukowa yayi yace Mommy ina wuni…wunin uwarka Junaid? Nace wunin uwarka. Matsowa tayi ta cire hannu ta kwada masa mari har sau uku sannan ta koma ta zauna idanunta cike da hawaye.
Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan
Bai iya cewa komai ba don yasan bashi da gaskiya. Yana kallo tana masa kukan nan da ya tsana har cikin zuciyarsa yake jin abin. Mommy ya kira ta a hankali bata ko kulashi ba sai da tayi mai isarta ta tashi ta haska masa agogon bango.
Karfe nawa yanzu ta tambayeshi. Hudu da minti ashirin ya bata amsa kansa a kasa. Mu je kayi wanka kawai tace masa.
Ba musu ya hau sama tana bayansa yana tangadi amma yana iyaka kokarin dannewa wai kada tace ya sha wani abu. Suna zuwa kofar dakin tace idan kayi wanka kayi alwala ka sauko ina jiranka.
Daki ta wuce ta kalli maigidanta da yake ta uban minshari ta ja dogon tsaki. Ita kam kudi bai zamu musu komai ba sai silar watsewar tarbiyar yaronta. Allah Yasa ma yaran basu da yawa su uku ne. Babbar Nafisa tayi aure itama mai bin Junaid din
Hamida tana gidan mijinta. Shi kadai namiji ya zame mata jarabawa a gidan duniya. Mijinta Senator Rufai Bukar ya rike mukamai da dama har zuwa lokacin da ya fara siyasa yanzu haka karo na biyu kenan da aka sake zabarsa sanata. Ko kadan bashi da lokacin iyalinsa saboda tafiye tafiye idan yana kasar kuwa daga office sai bacci. Baya taba bincikar halin da yaransa ke ciki amma duk karshen wata zasu ji alert mai kauri a account dinsu. Gaba daya lalacewar tarbiyar Junaid bata gabansa. Alwala ta sake sannan ta tashe shi ya sauko suyi sallah a kasa tare da maaikatan gidan tunda ana ruwa.
A falon kasan ta tarar da shi yana nafila tace cikin takaici ko kunya baka ji ka gama aikin sabo ka zo ka tsaya gaban Allah kana neman biyan bukata. Masu aikata laifi bisa kuskure ma suna tsoron haduwa da Allah amma kai naka lamarin kana sane kake takewa. Alhaji dake saukowa daga bene a lokacin yace ni kuwa bana so yaro yana kokarin shiryuwa kina sagar masa da gwiwa… Alhaji kenan ta fada tana shimfida abin sallah wallahi ina dada baku shawara kai da Junaid kuji tsoron Allah. Akwai ranar kin dillaci ranar da dukiya bata da wani amfani. Daga mata hannu yayi to malama naji zan masa fada ince dai shikenan ko.
*********************
Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!! Dagewa tayi ta sakar mata duka a baya. A gigice ta dago kai Ummati lafiya kika doke ni. Kujera ta jawo ta zauna kusa da aminiyarta, naga kin zurfafa a tunani ne. Tunda ansa rana ya kamata ki rage tunanin Saif haka. Ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Ke ko tunanin exams kike? Nima da tawa ‘yar brain din ban tsorata ba sai ke. Ajiyar zuciya Hafsi tayi ta kalli kawarta Ummati wai kinsan ya mukayi da Saif kuwa jiya? Me ya faru ta tambaya cike da zumudi. Ita dai soyayyar Hafsi da Saif tana burge ta. kamar abin arziki ya nuna min hotunan wasu abokansa da sukayi da matan da zasu aura sai daga baya yace ai tunda ansa rana muma yana son muje muyi. Dadina dake sokonci kin manta mun taba hirar dake lokacin da muka ga na Aliya Yunusa duk muka ce muna so. Ke kanki kin yaba da kyan da suka yi. Gara da kika ce yabawa kinsan ko da wasa bazan iya tambayar Mama ba ma balle Baffa. Bazasu taba barina naje ba shiyasa ma na cire abin a raina, amma ina fada masa haka da fushi ya tashi rai a bace.
Ummati ta dafa kafadar Hafsi bari mu fito daga exam dinnan sai muyi shawara. Karatu suka cigaba har malamansu suka shigo ajin aka fara jarabawa.
Suna tsaye a bakin gate din makarantarsu Health Technology dake cikin birnin Kanon dabo. Ummati ta zunguri Hafsi tana waigowa ta danyi murmushin yake. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa. Ke na samo mana mafita fa. Nan take hankalinta Hafsi ya kwanta har suka samu adaidaita sahu suka tafi gida.
Batul Mamman
TUN KAFIN AURE 2
A tsakar gida ta tarar da mamanta tana dinki. Bayan sun gaisa Mama ta tambayetajarabawa. Alhamdulillah tayi sauki sosai. Hmmm kinji ki wai tayi sauki sosai to a bita da addua dai. In sha Allah ta bata amsa tare da shigewa daki. Tunani kawai take yi na yadda zata gabatar da plan din da suka yi da Ummati idan ba haka ba sai dai Saif yayi hakuri. Amma tasan halinsa sarai na fushi. Gado ta fada tana juyi. Idan akwai abinda ta tsana bai wuce fushin Saif dinta ba. Ina ma dai yayi hakuri har zuwa lokacin aurensu sai ayi kowanne hoto yake so ta fada a ranta.
Sauransu jarabawa uku su gama makarantar gaba daya sai dai har yau ta kasa fadawa Mama. Hafsi ta rasa me yake mata dadi domin kuwa daren jiya da Saif yazo baram baram suka rabu. A cewarsa bai taba tambayarta komai ba sai wannan ta gagara yi masa. Da bacin ransa tayi bacci ‘yar wayar daren ma da suke yi yaki kiranta da ta kira kuma yaki dauka.
Shewar Ummati ta jiyo tare da kannenta Amira da Anisa. Da sauri ta fito ta jawo hannunta suka koma daki. Ummati ta kalle ta to sarauniyar masoya yau kuma me ya faru? Tunda naji muryarki kamar zaki yi min kuka nasan an taba zuciyar. Ba kya ma tausayina wallahi naga abin har dariya yake baki. Plate din abincin da Hafsi ta zuba amma tunani yasa ta kasa ci shi Ummati ta dauka tana ci…bakinta cike da abinci tace bana tausayinki zan zo yau. Ai don nasan Baffa yana gida yau ba aiki ne ba bari zaiyi ki fito ba. Ni fada min me ya faru. Hafsi ta zauna kan dadduma tace akan zuwa daukan hoton nan ne fa. Kwarewa Ummati tayi tana kokarin yin magana. Amma dai ke anyi banza wallahi Hafsi, ina ce tun last week muka rufe zancen nan. Ajiye plate din tayi ta tashi ina zuwa…ganin zata fita Hafsi ta bita da gudu tsaya don Allah ina zaki. Ko sauraronta bata yi ba ta shige kitchen wurin mama. Mama kinga Hafsi ko…dago kanta tayi daga tsintar waken da take yi me tayi miki kuma ku da ba kwa rabo da fada. Wai nace mata ranar da muka gama exams tunda ta safe gare mu ranar tazo muje daukan hoto shine tace wai bazata ba. Mama tun shekaranjiya nake mata magana tana kin bani amsa shine nace bari nazo kawai na fada miki. Kun fiye shirme ke da yar uwar taki meye abin fada a nan. Kinsan halin Baffanku sarai baya son fice fice ba gaira babu dalili nasan abinda take tsoro kenan. Ummati wadda ta zauna a kasa tana taya ta tsintar waken tace Mama dama wai na tarihi nake son muyi ranar tunda kinga ni Bauchi zan….karasa mana bauchi zamu kaiki ko. Tashi tayi zata gudu Mama tace ba komai zan fada masa ranar da ku ka gama din sai kuje kuyi hoton shikenan ko. Nagode nagode nagode abinda ummati take ta fada kenan har ta fita daga kitchen din. Ita kuwa Mama dariya take sai dai bata san me yaran ke kullawa ba.
********************
Kwance yake kan makeken gadonsa yana zukar wata irin taba mai kauri da tsaho, bai ankara ba kawai sai ganinta ya yi a tsaye bakin gadon. Ah sis saukar yaushe…harara ta galla masa kafin ta fizge tabar. A jikin wandonsa ta kashe ta ai kuwa ba shiri yayi ihu tare da mikewa yana kokarin cire dogon wandon. Sis don mugunta sai ki kona ni me nayi miki kuma daga zuwanki. Ko da ya cire wandon saman gwiwarsa ya fara alamun tashi. Ta zauna ai kadan ma ka gani wutar can tafi wannan. Jin yanayin maganarta yasan mommy ta kai shi kara wurinta ne. Daure fuska yayi yace to idan kinzo ganewa idonki ne kinyi sa’ar gani sai ki fita….rayuwa kowa da tasa so please let me be. Duk ranar da na gaji ke zan fara sanarwa. Yana gama magana ya shige toilet tare da banko kofar da kafa daya. Har zuciyarta taji sautin ta mike a sanyaye. Zuwan Junaid America certificate kala kala ya samu banda na school harda na shaye shaye, neman mata da tsabar kin ji. Baya ganin kowa da gashi ciki kuwa harda mahaifin nasu da ya dage sai dansa yayi karatu mai tsada.
Dakin mommy ta shiga ta zauna a gefen gado tayi tagumi tana jira mommyn ta idar da sallah. Ya dai Nafisa kunyi magana da kanin naki. Hmm mommy ai lamarinsa sai addua kawai ta fada tana tabe baki. Nan ta labarta mata yadda suka yi. Mommy tace to ni dai na gaji zan sanar da Hajiyan Dangi halin da ake ciki kafin yaron nan ya dauko mana magana. Zaro idanu Nafisa tayi cikin tsoro tace Hajiyan Dangi….wai .
Batul Mamman
: TUN KAFIN AURE 3
Cike da murna Hafsi ta kira Saif ta sanar da shi an bata izini a gida amma sai ta gama exams. Yayi matukar farinciki da jin hakan. Hafsi kyakkyawa ce ga kyan jiki. Tun farkon haduwarsu yayi ta fama da samarin da ke sonta kala kala Allah Ya taimake shi ta zabe shi kuma yayi saa mahaifinta bashi da wasa wurin sa ido akan lamuran ‘ya’yansa. Duk da kasancewarta ba fara ba saboda babanta mutumin maiduguri ne amma yanayin fatarta mai kyau ne kamar ‘yar hutu. Duk wanda ya kalle ta sai ya kara saboda haka Saif yake godewa Allah da wannan tsaleliyar budurwar take sonsa.
‘Yan ajinsu suna ta faman rokonta su tsaya ayi hoton tarihi ciki kuwa harda Ummati amma ita duk hankalinta yayi gaba. Gefe ta jawo kawar tata. Ummati wai kin manta da abinda ke gabanmu ne yau kin tsaya sai hira kike yi. To sarkin azarbabi ko dan jan aji ai kya yi masa yasan kema kina ji da haduwa. Ki bari muyi sallama da mutane cikin mutumci. Da kyar Hafsi ta bari sukayi hotuna sannan suka wuce gida. Cike da doki tayi wanka ta debo kayan sallarta da wasu kaya masu kyau har kala hudu ta zuba a leda. Tana cikin shiryawa Saif ya kirata. Tana dauka ya suma magana.
(Matar baku shirya bane? Na kusa karasowa gidanku fa)
Ji tayi gabanta ya fadi don bata fada masa da yadda aka barta ba. Kashe murya tayi cike da shagwaba.
( Saif kada ka zo please Baffa zaiyi fada. Ka jira mu a bayan layin su Ummati idan ka iso yanzu zan fito nima.)
(Ai duk yadda kika ce haka za’ayi matar. See you soon)
A gaggauce ta fito ta ce Mama zan je gidansu Ummati daga can zamu wuce. To Allah Ya kiyaye amma don Allah banda bude jiki gaban mai hoto. To kawai ta amsa tana sauri ta fita. Hafsa! Taji mama ta kira ta ….a hankali ta juyu tace baki karbi kudin hoton ba da kudin mota ko duk saurin ne. Da gudu gudu ta koma ciki ta karbi kudin tayi godiya sannan ta fita.
Tana zaune gaban motar Saif suna ta hira sai dai gaba daya ta kasa sakin jiki sosai saboda basu gama fita daga unguwarsu ba. Karshe dai fakewa tayi ta duba kasan takalminta ta sunkuyar da kanta har sai da taji sun hau titi sosai. A gaban wani sabon gidan hoto da ake ji dashi a kano Treasures suka tsaya. Zata bude kofa ta fita Saif yace haba matar ai nine mai bude miki kofa daga yau, tunda gashi nayi sa’a kin shiga motata. Ummati da ke baya tayi shewa lallai ma Saif wato ni ko oho. To Allah bazan fito ba sai nima wani cikin ku ya bude min ai nima ina da nawa rabin ran. Dariya duk suka yi sannan suka shige ciki. Zama suka yi a reception ya gama magana da receptionist sannan yayi joining dinsu kafin azo kansu. Wai Saif yau babu aiki ne ka fito yanzu? Matar kenan Lukman na bari ya kama min kafin mu gama. Dayake aikin sa kai ne ba. Da haka nan nace ka zo a wannan lokacin cewa zaka yi aiki aiki. Ledar hanunta ya kala yayi saurin dafe kai kinsan har na manta ba taho da kayan canjawa ba. Bata fuska tayi don Allah da gaske kake? Dariya yayi mata sannan yace ina son shagwabarki matar kinga yadda kika yi kyau kuwa…buga kafa tayi a kasa ni fa da gaske nake yi Saif….nima da gaske nake yi Hafsah ya kwaikwayeta. Zanyu kuka fa dariya yakeyi sosai sanan ya tashi ke wasa nake yi suna mota just give me a minute.
Bayan ya dawo suka shiga aka bar ummati tana jiransu idan an gama na masoya sai ayi na kawaye kamar yadda ta fada.
Suna shiga mai hoton ya ce da Hafsi cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba zaka yi cire wanan veil ko yana nuna mayafinta. Saif ta kalla da alamar tambaya yace ta cire akwai wanda zasuyi nan gaba da mayafin. Nan fa aka rinka hotuna kala kala…babu wanda jikinsu baya taba na juna tun Hafsi tana dan jin kunya har ta saki jikinta. Sunyi kusan kala goma suna canja kaya dama ga ta gwanar kwalliya da daurin dankwali. Mai hoto yace da Saif, Alaji ba zakiyi na english wears ba amarya? Dariya Hafsi tayi tace kaji min mutum baza muyi ba. Saif yace ni nayi tunanin zaki zo dasu fa matar. Juya masa idanu tayi mai hoto yana kallonsu wannan sai bayan biki. To na yarda ya amsa mata sai tana shirin daukan mayafinta sai kawai taji saif ya cire mata dankwali ya kuma fizge mayafin ki dan baza gashinki sai muyi a haka a madadin kananan kayan tunda naga wannan rigar ta kama ki yadda yake maganar wani kasa kasa. Daure fuska tayi sosai Saif meye haka ya zaayi nayi hoto a haka. Ita saboda ma yanayin rigar bata yadda sunyi hoto da kayan ba mayafi ba. Fitted gown ce a jikinta wadda ta bude daga kasa. Saman kuwa ya kama mata kirji sosai gashi gaban yana da dan zurfi ana ganin saman kirjinta.
Shi kanshi Saif ya kadu da ganin surarta banda mai hoto da yake gefe yana ganin bati. Please matar ko daya ne ki bari muyi please, please. Bata son bata masa rai amma ba karamin haushi taji ba. A haka ta bari aka yi guda daya da kyar ta tsaya gabansa bayanta a jikin kirjinsa ya sakalo hannuwansa duka biyu ya ta gaban cikinta. Wani irin yanayi duka suka tsinci kansu shi da kansa yace ya isa guda dayan.
Da rashin fara’ar nan aka dauke su tare da Ummati wanda zasu nuna a gida. Bayan an wanke musu ya bada wayarsa aka tura masa. Ita Hafsi dama tata wayar ba wata mai tsada bace tace bata so. Wanda aka wanke ma cewa tayi ya rike duka a wajensa. Ganin duk ta bata rai bayan sun shiga mota yace Ummati ta bata hakuri. Ko da ummati taga dalilin fushin duka ta kai mata a baya shegiya Hafsi irin wannan pose haka ko ni da Lawal bamuyi irinsa ba. Hawayen da take kokarin boyewa ne suka sakko ba shiri. Saif na gani ya tsaya da ribas din da yake shirin yi da mota…. matar don Allah kiyi hakuri nima sai da nace muyi abin duk ya dameni. Bani da niyar wulakanta ki, ummati ki sa baki mana. Haka suka yi ta bata hakuri har ta dena kukan amma a zuciyarta ba karamin tsanar kanta tayi ba da ta biye masa irin wannan runguma haka kamar an shafa fatiha. Ga wani bakon feelings da takeji tunda ta hada jiki da Saif abinda ko hannunta bai taba rikewa ba. Anya tayi wa kanta adalci kuwa. Da wannan tambayar a ranta suka isa unguwarsu.
Kamar yadda suka tafi yanzu ma a bayan layi suka sauka. Haka ta shiga gida sukuku kannenta suka karbi hotunan da tayi da Ummati suna gani. Baffa ne ya kula da yanayinta Hafsa me ya faru ne duk kinyi wani iri. Kago murmushi tayi Baffa kaina ke ciwo. Daki ya shiga ya samo mata magani Mama tace sannu ai abin ne da yawa ga karatu, kinyi jarabawa sannan kuma baki huta ba kin sake fita. Ai zan baki hutun kwana biyu kafin ki cigaba da tayani dinki kinga sun taro. Baffa ya harareta nifa na gaji duk kin mayar min da yara teloli. Kowa dariya yayi harda Hafsi da ta kakalo ta dole.
nice story
Thaks
Wooow gsky littafin tun kafun aure yamatikar haduwa pls karashen shifa