Tun ran gini Hausa Novel
*TUN RAN GINI……*
WRITING
BY
*UMMU FU’AD HUMKAM*
FOLLOW ME ON INSTAGRAM
*P 1*
“Wacece ke?ki fad’amin,ke har kin isa nace kiyi girki Amma ki k’iyi? Me Kika taka?” K’afa yasa ya tokare ta, ta bugu da jikin bangon d’akin Saida goshin ta ya fashe Yana fitar da jini,Rad’ad’i da zafi suka ziyarci dukkanin ilahirin jikin ta,cikin sanyi murya ta juya “Zauj Meyasa bazaka min u…..”kafin ta k’arasa taji wani saukar mari a kumatun ta, da hanzari ta d’aga Kafin ya ankara itama ta gaura masa mari Yana juyowa zai kalleta ta k’ara harba masa wani marin. Ran Sultan yayi masifa b’aci fiye da tunani,hakan yasa ya fara dukan ta,kamar an aiko shi,da taga zaici galabatar itama ta shiga ramawa kokawa sosai ya b’arke a tsakanin su,Wata dattijuwa ta shigo parlourn cikin hanzari tana cewa ” ka kyalee dan girman Allah,d’ana kadai na, Allah ya shirye ka Sultan,Yanzu Kai kenan kullum idan k’aramin Abu ya hada ka da matar ka shikenan sai kayi ta jibgar ta kamar an aiko ka? Wannan wani irin rayuwa ne?A ce…”
Duk wannan maganar da take bai ko d’aga Ido ya kalle ta ba bare ma tasa ran zai daina abinda yakeyi,Sai da ya Jibgi *Najala*(matar sa) Ya d’aga jajayen idanun sa ya zubawa mahaifiyar sad Yana haki kafin yace “Babu ruwan ki Dani,ki wuce ki bani wuri(Ni ko nace anya mahaifiyar sa ce kuwa? Baki ta bud’e tana k’ara mamakin halayyar Sultan “Amma sultan…” TV dake jikin bango ya buge ta da hannun sa Saida ya fashe da sauri mahaifiyar Taje gare sa har tana bige k’afar ta da jikin kushin Amma ko tsayawa batayi ba burin bai wuce ta ganta agaban Sulta ba,tana Isa gare shi ta Kamo hannun dake fitar da jini sosai ta cire d’ankwalin da ke kanta daure masa,hawaye masu zafi ke zuba daga cikin idon ta,
“Haba Sultan wannan wani d’abia ne haka?” Umma please ki kyaleni” bazan iya ba sultan ka kalli hannun ka kajiwa kanka ciwo a banza sbd zafin zuciya.” Mtswww” yace ya fita.
Juyawa tayi tana kallon Najala tace”Meyasa kike biye masa tunda kinsan halin sa da bak’in zuciya kinsani sarai idan yaje yayi shaye shayen sa harni baya shakkar gayamin magana”
“Umma na gaji da halin Sultan na gaji! Na gaji! Na gaji! Habaaaaa” ta fad’a cikin tsawa da d’aga muryar daidai lokacin da Sultan ya shigo ya d’auke ta cak zuwa d’aki yasa key ya k’ulle k’ofar da k’arfi Umma sa nata buga k’ofar Amma shiru.
Ahankali ta fara tafiya zuwa part d’inta tunda ta doshi k’ofar parlourn ta fara jiyo hayaniya har ta bud’e k’ofar *MUSHUR* Ta gani da belt a hannun sa Ya nuna *Rim* da hannu Yana cewa Ni sa’arki ne Ina fad’a kina bani amsa to wlh Baki Isa kibar gidan Nan da wa’yan Nan matsiyatar kayan kamar wacce ba musulma ba”Wani irin kallo Rim ta watsa masa kafin ta cigaba da cewa “Malam kafita har kana,Dan baka tab’a Isa ka hanani zuwa birthday din sahibaty na ba”
Ya d’aga belt zai zuba Mata Umman tayi saurin shiga tsakiyar su ta rik’e hannun Mushur “Haba dan Allah Yanzu sai ka zuba Mata wannan belt din naka? Me ta maka haka?” Ummah ki dubi irin shigar da Rim tayi a matsayin na ‘yar musulma gaba da baya shin ya Kama ta tayi wannan shigar?”
Sai a lokacin Nima na dubi jikin Rim Want shirt tasa fari Mai fadin wuya Wanda Duk ka fad’arta tana waje tsakiyar riga anyi drawing na ❤️ red da d’an Baki a tsakiyar sai tsones da aka zagaye heart din dashi suna k’yalli,iyakar riga saman jibiyar ta,cikin cibin tasanya masa wani Abu kamar s’arka saidai baikai sark’a tsayo ba,’yan kunnayen ta red, gashin dake kanta da yasha gyara sai k’yalli yake Yana d’aukar ido,ta zubo shi ta gaba can ka’asa kusa da k’arshen sumar ta Sanya masa Jan ribbon fuskar ta na kalla light make up tayi sai lips d’inta da yasha janbaki red,kan hancin ta Sanya masa wani barima da yad’an sauka.Nace tabarakallah Masha Allah Dan kuwa Rim sak balarabiya. kasan jikin ta wani d’amammiyar jeans ne irin crazy dinnan duk a an hur huda shi, sai gefen shi drawing na heart Amma shi stones d’insa aciki aka zuba,Red cover shoe ta Sanya mara tsini sosai.
Umma ta sauke hannun MUSHUR tace ……
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza 3
-
Zuciya ta
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi
-
Aure da haihuwa
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya
-
Gangar Shedan
-
Angon mata biyu
-
A gidan mu take
-
Bafulatanar Rugga
-
Matar yaro
-
Mr Bello
-
Mijin Buzuwa
-
Gidan Uncle Complete
Powered by: www.mynovels.com.ng
*INA SON JIN COMMENTS DINKU KAN WANNAN LBRN MAI D’AUKE DA SARK’AKIYA*
Leave a Comment