Hausa Novels

Ubayd Maleek Hausa Novel

Ubayd Maleek Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Ubayd Maleek Hausa Novel

Qarfe shida da wasu mintuna ya bude idanuwansa dasukai nauyin baccin daya daukesa daga Nan jinginen kan gadon.

Tashi zaune yayi ahankali yana kallonsu sbd har lokacin bacci sukeyi sosai musamman da alamu ya nuna farhat din ta samu sauki sauki sbd numfashinta daya ‘dan daidaita.

Hannunsa dake sarqe cikin na NURU data qanqame ya kalla ahankali tareda dago manyan fararen idanuwansa da bacci ya Dan sauyasu ya zubawa fuskarta datake Kama data ‘yan babies kaman farhat dinsa saiya maida kallonsa kan farhat da itama innocent face dinta tayi haske ya saka dayan hannunsa yakama hannunta ya zare hannunsa Yana kallon fararen yatsun hannunta dasuke farare fes kaman Bata aikin komai dasu ya miqe yaja bargo ya rufe musu jikinsu musamman NURUn da cinyoyinta suka gama Shan sanyi duk da Babu wani sanyi ko kadan a dakin shiyasa ma shima baccin yadan daukesa.

Ficewa yayi dakin ya rufo musu qofa yayi samansa Dan yin sallah da yau yayi latti.

Bayan fitarsa ba jimawa NURU ta farka ta tashi jikinta amatuqar mace da Dan nauyin jiki da sauran ciwon kan dabai gama sakinta ba ta zauna tareda kallon farhat tana tabata tareda duddubata ta tabbatarda tasamu sauqin dannewan numfashin saitaji hankalinta yadan kwanta ta sauko gadon ta nufi toilet din dakin tashiga tayi duk abinda zatayi tazo alwala tana Kai ruwa bakinta zatayi shaqar hanci taji wani irin qamshi a tafin hannunta ta Kai hannun hancinta ta sake shaqa taji wani irin qamshi dayaso kashe Mata jiki Amma Kuma takasa tuna na menene tunda tasan last abinda ta taba kafin baccin was kayan baccin data Sanya ta kwanta.

Cigaba tayi da alwalarta tagama tafito Takoma dakinsu acan tayi sallar tana idarwa tadawo ta duba taga farhat Bata farkaba har lokacin bacci takeyi ta gyra Mata lullubinta tareda gyara Mata kanta Takoma daki ta cire kayan baccin ta Sanya dogon wando da rigar sanyi da hula ta nufi kicin Dan hadawa farhat din pancakes da tea din sabuwar Madara datasan farhat na tsananin so ko zata samu taci Dan duk jiyan bata iyacin komaiba sbd tsanani da azabar ciwo.

Tana cikin aikin mum Sarah da itama baccin rabi da rabi tayi sbd damuwar ciwon na farhat tashigo tana Taya NURU aikin bangare daya Kuma ga Fana na aikin hada breakfast na MALEEK.

Sauri tayi tagama sbd kada farhat din tatashi Bata kusa tana gamawa ta aje jere komai a dining ta nufi dakin farhat din tana waya da Afia data Kira a rude sbd Imran yafada Mata saita kwantarwa afian hankali tana cewa farhat din tasamu sauki inshallah.

Turo dakin tayi tashigo Kai tsaye tana ganin farhat din zaune kan gado ta qaraso da sauri cikin farin ciki idanuwanta na cikowa da hawaye cikeda qaunar farhat din me girma tace”

Finally Sweetie kin tashi””rungumeta tayi tana cewa”

I miss you so very much baby

Kinabani tsoro jiya sosai harbansan tunanin me zanyiba……

Idanuwanta ne suka sauka akan MALEEK dake tsaye gefen gadon daga dayan gefen fuskarsa nakan waya dayake dubawa na Kiran dayayiwa Dr Damien.

Wani irin mummunan firgici da tsoro ne yashigeta tayi Saurin gayara hularta data zame tana tashi daga kan gadon tana gyara wuyan rigarta ta sauke Kai qasa tareda zubewa qasa cikin tsananin girmamawa da sanyin murya tace”

Barka da fitowa.

Bai jita bane kokuwa ya akai itadai dataji shiru ta dago sai taga baya gurin saitaji jikinta yasake yin sanyi sbd wani lokacin mantawa takeda matsayinta na baiwa sai irin hakan ta faru take tunowa da ita din bakowa bace face baiwa ‘yar bawa jikar bawa gadon bauta,

Allah ne yahada qauna me qarfi da tsafta tsakaninta dasu afia da farhat Wanda ta dauka hakan tamkar wata rahamace ga rayuwarta shiyasa dorewa da dawamammiyar qauna atsakaninta dasu afia yazama cikin adduarta tacikin sujjadarta.

Kamo hannunta taji farhat tayi ta juyo kanta tareda zama kusada ita tana kawar da tunanin damuwa tasaki fuska cikin kulawa tace”

Yaya kikeji yanxu sweetie?

Kwantawa tayi jikin NURUn tana gyada Mata Kai alamar da sauqi.

Shafa kanta NURU tayi tana cewa”

Baby muje ayi brush nahada Miki pancakes dinki kici ko kadan ne zakiji Dadi Dr ma Kuma Yana zuwa hakama uncle Imran na zuwa haddama AFIA nason Jin muryan princess farhat.

Kallonta kawai farhat din keyi sbd Bata iya ko dariya haka ta dauketa takaita toilet tayi Mata wanka da ruwa me zafi tayi Mata brush suka fito ta shafa Mata Mai da duk abinda yakamata ta shiryata cikin Kaya masu kauri sosai tareda hular sanyi da socks ta hannun da qafa suka fito Palo tana daukeda ita suna fitowa babban Palo Ana budewa Imran kofa Yana shigowa cikin kayan sanyi shima sbd yau gari akwai sanyi sosai tana ganinsa taji wani irin sanyi aranta sbd dama Wanda zaiyi magana da dadynsu farhat din take neman mafita.

Qarasowa yayi Yana karban farhat din ya kalleta lokacinda ta lafe ajikinsa cikin kulawa yace”

Sorry farhat baby.

Kallon NURU datai Dan zuru zuru yayi yaji jikinsa na mutuwa da wata sabuwar qaunarta me qarfi ya sassauta kallonsa Yana Mata kallon kulawa yace”

How are you?

Numfashi ta sauke tana kallonsa tareda tana nufar dining room tace”

Am gud,ya sanyin yau?

Munsaka tasowa da safe haka.

Zama yayi da farhat daidai tana dawowa daukeda tray din tea da pancakes tazo ta zauna kusa dashi tana daukan cup din tafara bawa farhat dake jikinsa zaune tana sake Masa bayanin Yan jikin farhat din yake jiya shikuwa sai binta yake da ido cikin kulawa Yana sauraronta yanaji acikin ransa kaman itada farhat din iyalinsa ne duk da dai Bata Isa haihuwan farhat dinba Amma sai yaji inama ace acikin gidansu suke da ita amatsayin matarsa da hadasu zaiyi su biyun ya ciyar dasu breakfast din.

Ahankali qamshin dataji da safe a hannunta hakama a kayanta kwanaki data rasa Ina tasamu taji Yana doso hancinta Yana shiga cikin sanyi Bata kawo komai akaiba taci gaba da bawa farhat din daidai tana gama Bata Imran yace”

Ok tunda farhat ta qoshi saura lewanta yanzu.

Murmushi ta ‘dan sake zatai magana qamshin yashiga hancinta sosai ta waiwayo ahankali idanuwanta ayau cikin babbar rashin sa’a suka sauka cikin NASA daidai shigowarsa palon gabaki daya cikin wasu Armani’s dark blue best color dinshi sbd kalar na fidda kalar fatarsa sosai,

Gabaki daya shekarunsa na dattijanka sun boye cikin hutu da izzarsa tareda kamewarsa dake yawo cikin jininsa na sarautar asali,

Babu Wanda zai kallesa Kai tsaye yace shine ya haifi zuqeqiyar budurwa kamar AFIA UBAYD MALEEK ba.

Inda suke bai kalla ba dukkaninsu suka miqe tsaye musamman NURU da tuni tayi ciki daukeda tray Imran yabita da ‘dan satar kallo gashi jeans ne ajikinta Wanda yasa MALEEK qara muryan tv kadan tadawo da Imran din hankalinsa.

Dr Damien yazo tareda nurse yaduba farhat Sosai tareda Bata duk wani kulawan likita datake buqata kafin yatafi yabar nurse dazata cigaba da kulawa da ita harta warke tukuna.

Duk yanda yaso sake ganin NURU harya gama yininsa ya tafi Bata Kuma fitowaba saidai suka rage firan a waya sbd maleek na gida Kuma a palon farkon yake zaune yau Wanda yasa kaf gidan tsayawa iyakarsu sbd ba’a wilgewa idan Yananan.

Saida zai tafi NURUn ta rakosa har mota sbd maleek na sama sai lokacin Imran yaji bayason tafiya musamman yanda NURUn duk ta sukurkurce akan ciwon farhat din Amma haka ya tafi yabarta.

Da daddrema haka batareda sun saniba bayan sunyi bacci yashigo dakin wannan karon NURU kayan baccinta masu Dan tsayine Dan wandon kayan yakai gwiwowinta hakama rigar nada hannu Amma duk Rabin Samanta abude Dan haka ko zama baiyiba ya dubasu ya gyara musu lullubinsu yafice daga dakin.

Kwana biyu tana kulawa da farhat Sosai hartaji sauqi ta warware Takoma kiriniyarta sai alokacin hankalin NURU ya kwanta tasamu walwala itama sbd dama ita tafi zamowa kaman farhat din da dabiun yarinta akan afia data dauki girman Dole ta dorawa kanta na zama babba acikinsu.

Imran kuwa sai zuwansa na yanzu ya ninka na da Dan yanzu Sam yafara saka danne feelings dinsa NURU Dan kusan kowa yafara fahimtar hakan gashi karatunta na tafiya daidai shaquwanta da Imran yasa ta dauki burin zama lawyer itama sai hakan yasake bashi kwarin gwiwan soyayyanta.

**AFIA tagamo karatunta na shekara daya Wanda yayi daidai da gama na NURUn itama Dan haka itama saitaje Las Vegas tayi shekara daya kafin suje University Dan Afia tafadawa dad dinta zata jira NURU tagama tadawo kafin suje University tare

Sanin irin shaquwan dake tsakaninsu musamman yanzu daya sanyata jerinsu ma’ana tamkar ‘yarshi sai bai musa da hakanba ya amince Mata aka fara yiwa NURUn Shirin tafiya Las Vegas itama musamman gashi Imran yadan shiga damuwa na tafiyan Tata sbd tun ba’ayi nisaba NURU tafara cike dukkanin wasu matakanda cikakkiyar budurwa me daukan hankali zata cike to inaga taje tayi zaman kanta idanuwanta da kanta sun bude sbd rayuwace ta wayewa Dan gidan MALEEK ne dake Vegas din zata zauna itama kaman yanda Afia tayi zama itama.

 

‚ÄčAuren Lagos

ubayd maleek

 

 

Name: [UBAYD MALEEK HAUSA NOVEL ]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: November, 2021

 


Leave a Comment

error: Content is protected !!