Kannywood News

Umar Hashim Na Murnar Cika Shekaru 13 Da Aurensa

Umar Hashim Na Murnar Cika Shekaru 13 Da Aurensa

 

 

 

 

 

 

 

Wanda yake shirya wasan kwaikwayon hausa na Izzar So wato Lawan Ahmad wanda kuma shine yake fitowa a matsayin jarumi a cikin shirin yana murnar cika shekara 13 da auren matarsa.

 

Lawan Ahmad wanda akafi sani da Umar Hashim acikin shirin Izzar So yakasance yana da aure da kuma mata daya da yara hudu,

 

jarumin wanda yanzu tauraruwarsa take haskawa haifaffan jahar Katsina ne Kuma dan garin Bakori.

 

A yau 25 ga watan October 2021 ya wallafa wani hoto mai dauke da iyalansa wanda yake nunawa duniya cewa yau shekararsa goma Sha uku da aure, Lawan Ahmad ya rubuta a kasan hotonsa tare da iyalansa cewa,

 

“Today Is My 13 Years Wedding Anniversary Masha Allah.”

Jarumin Izzar So din (Lawan Ahmad) yana da ‘ya ‘ya hudu biyu Maza biyu Mata, sai dai ‘yarsa ta hudu jaririya ce ba a dade da haifanta ba.

 

Ku karanta Tarihin Lawan Izzar So

Lawan Ahmad din yana cikin jaruman Kannywood wanda za a ce aurensa yayi tsawon kwana sosai, domin shafe shekara 13 da aure ba karamin kokari bane.

 

Umar Hashim Izzar So dai tsohon jarumin Kannywood ne sai dai tauraruwarsa ta daga sosai ne lokacin daya fara shirya Izzar So Hausa Film, Yanzu shekara biyu kenan harda wani abu da fara shirin Izzar So.

8 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!