Kannywood News

UMAR HASHIM YAYI KARIN HASKE KAN FIN DIN SA NA IZZAR SO

UMAR HASHIM YAYI KARIN HASKE KAN FIN DIN SA NA IZZAR SO

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Jarumi lawan Ahmad ko nace muku Umar Hashim yayi Karin haske Dan gane da Shirin nan nashi mai farin jini wato IZZAR SO episode 54.

Masu sauraro Assalamualaikum barkanmu da sake saduwa a wani sabon video acikin wannan video muna dauke da rahoto akan bayanin da shahararren jarumin kannywood din Mai suna Lawan Ahmad Wanda akafi sani da Umar Hashim acikin Shirin Izzar so.

kamar yadda dukkanin masu bibiyar wannan shiri na izzar so suka sani Lawan Ahmad yana Dora film din sa na izzar so ne a tashar sa ta bakori tv dake kan YouTube a duk ranar lahadi da karfe takwas na dare.

Shirin na izzar so anjima ana yinsa sai dai tun daga season 1 mutane suka rinka tofa Albarkacin bakin su agame da Shirin wasu suna cewa ya kare wasu kuma suna fadin yanzu fim din ya dauko dadi.

sai gashi ana kammala haska season 1 din jarumin ya fito dandalin sa na sada zumunta ya sanar da dukkakin masu bibiyar Shirin cewa suyi hakuri suna kan daukar season 2 na Shirin Kuma suna iya bakin kokarin su wajen suga sun farantawa Yan kallo rai ta hanyar kawo musu Abin zai birgesu. bada jimawaba kuwa aka fara haska season 2 na shirin yanzu dai fim din izzar so har ana kammala haska season 4 ana kan daukar season 5 ne.

jama’a kada nacika ku da surutu ga dai Abin da shafin mu na ArewaGuru ya rawaito daga wannan shahararren jarumin Kuma furodusan Shirin izzar so wato lawan Ahmad ya rubuta a shafin na Instagram kamar haka.

jarumin ya wallafa wata sabuwar poster ne ta izzar so sannan yayi rubutu aka santa kamar haka IZZAR SO 54 are coming on you screen soon, ma’ana Shirin Kashi na 54 yana nan tafe A wayoyin ku nan bada jimawaba wannan shine karshen jawabin jarumi lawan Ahmad akan fim din izzar so episode 54.

ga wani karamin tambihi anan Idan masu sauraro sukayi la’akari da yadda aka dauki tsawon lokaci kusan sati uku zuwa hudu kenan ba haska Shirin izzar so ba.

ya kamata ace bayanin da jarumin zaiyi agame da Shirin yafi haka domin ta hanyar cikakken bayani ne kwai hankalin masu bibiyar Shirin zai kwanta su fahimci inda aka sa gaba Dan gane da cigaban Shirin.

sabo da haka munyi mutukar mamaki akan faruwar hakan domin Idan masu bibiyar jarumin basu manta ba hakan Tasha faruwa na tsaiko ko karewar season Amman yakan bayyana dalili Kuma yayi gamsasshen bayanin da zai kwantar da hankalin masu kallo.

wannan shi ne iya Abin zamu iya bayyana muku acikin wannan video kada ku manta ku danna mana subscribe domin samun sabbin labarai da rahotanni daga masana’antar shirya fina-finan Hausa ta kannywood muna godiya da ziyara.

DOWNLOAD IZZAR SO MOVIE APP

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!