Ummie Hausa Novel Story
Tag: ummie hausa novel
Cup din tea dake bakinta ta sauke tana kallon Umma dake shafa butter a jikin bread ta ce ” Zan tai dan akwai wasu client É—in *_YUSUF_* da zasu zo by 9am, É—akin taron ba’a gyara yake ba ya kamata inje office kafin 8″
Bata jira cewar Umma ba ta dauki hand bag dinta ta rayata tana gyara mayafin abayar dake jikinta.
“Toh Allah ya kiyaye, ki kula kinji?
Murmushi Budurwar tayi wanda ya bayyanar da dimple dinta me matukar kyau. Gyara zaman gilashin dake fuskarta tayi tana faÉ—in ” Amin Ummana”
Daga haka ta fice daga gidan. Murmushi Umma tayi a fili ta ce ” Allah yayi miki albarka *_ZARAH_* Allah ya tsare miki mutuncinki a duk inda kike”
Tana fita ta samu napep kasancewar kusa da titi gidansu yake.
Tafiya ce me dan tsayi kafin ta iso wani gini me dan karan kyau da kuma tsayi dan ya kai hawa 5, a saman ginin an rubuta *TWO BROTHER’S*
Sallamar me napep din tayi tana shiga ginin ta ƴar ƙaramar ƙofar da aka tanada saboda shiga.
Sai da akayi checking É—inta saboda tsaro sannan ta wuce tana sauri tana gaisa kuma da mutanen da ke daga ma ta hannu.
Lifter ta nufa dan bazata iya bin stairs ba saboda zai ci ma ta lokaci. Tana isa office É—inta ta ajiye jakarta ta fito. Wani office din ta shiga wanda ke É—an nesa da nata bakinta dauke da sallama.
Matashi ne zaune yana amfani da na’ura me Æ™waÆ™walwa. ÆŠagowa yayi yana kallonta fuskarsa a sake ya amsa ma ta sallamar yana É—orawa da cewa ” Yanzu nake Æ™oÆ™arin kiranki ai” ummie
Zama tayi a kujera tana fadin ” Lafiya dai?
“Eh, ya shirye shiryen biki?
Ya faÉ—a yana mata murmushi.
“Komai normal fa, so nake ka kira Kabiru saboda inaso a gyara dakin taro sannan ayi ordering abinci sai a kawo ruwa lemo by 9am wasu client da za muyi wani project tare zasu zo”
“Uhm, Zarah sarkin aiki! Kiran da zan miki ai a kan wannan taron ne, Me gida ya ce in sanar da ke ya baki hutu sai bayan bikinki”
“Seriously?! Ta fada tana zara idonu cike da mamaki.
Dariya yayi yana faÉ—in “Nima nayi mamaki ai kinsanshi baya son wasa a aiki, maganar taro kuma nasan maybe ya soke dan yace in sanar dake ma karkizo aiki”
Relaxing tayi a kujerar tana Murmushi tayi ” Gaskiya naji dad’i wallahi”
“Ok naji karki cikani da surutu ki tashi ki tafi gida, anjima Zainab zata zo maybe tayi deciding abubuwan da zakuyi a bikin”
Tashi tsaye Zarah tayi tana gyara glashin dake fuskarta ta ce ” Ai Umma tayi fushi da kai _*ZAYD*_ ko Allah ya sanya alkhairy baka zo kayi ma ta ba ko?
Tsayawa yayi da abinda yake kafin ya kalli Zarah ya ce ” Zanzo insha Allah ki bata hakuri” ummie
Taɓa baki tayi tana ficewa daga office ɗin.
Zarah bata tafi gida ba, office ta nufa ta fara rage wasu ayyukan ta har kusan 10am. Ummie
Ganin ko ina yayi tsit yasa ta game Yusuf yazo dan baya son hayaniya kowa yasan da hakan. Zaro ido tayi waje tana kalle² ko zata samu wajen ɓuya tasan by now Zayd ya sanar masa da cewa ya faɗa ma ta sakonsa amma kuma ta zauna a office har yanzu tsaf zai iya cewa ya soke hutun daya bata.
A gaban cabin dinta ya tsaya dan yaji motsi. Matashi ne ɗan gaye me ji da kanshi yasha Desmond merrion supreme suit me dan karan kyau da tsada, ƙafarsa sanye da Crockett shoe, hannunsa sanye da smart watch, bashi da suma haka zalika bashi da saje amma fa akwai kyau, ba fari bane yana da duhu.
A hankali ya Æ™arasa bakin cabin dinta yana É—an kalle² kafin ya ce ” Zarah! Cikin muryarsa me amo.
“Na’am” Ta masa batare da ta sani ba. RiÆ™e bakinta tayi cike da takaici kafin ta fito a hankali cikin sanÉ—a. Kallon sama da Æ™asa yayi mata kafin ya ce ” Zayd be sanar dake saÆ™ona ba?
“Eh” Ta fada a takaice.
“A’aaaaa… Uammm.. I..ina nufin ya sanar dani yanzu nake shirin tafiya”
Daga haka ta koma cikin cabin É—in ta da sauri har ta fito yana tsaye a inda ta barshi.
“Nagode” Ta fada tana Æ™oÆ™arin wucewasa. “Tsaya” Ya faÉ—a yana juyowa. Itama juyowa tayi tana murmushin dole.
Envelope ya ciro a aljihunsa na cikin suit din ya miÆ™a mata yana faÉ—in ” Inji *_FAROOQ_* yana miki fatan alkhairy.
Girgiza kai tayi da sauri tana faÉ—in “Ka ce masa Nagode”
Ajiye wayi a kanta yana fadin ” Allah ya baku zaman lafiya”
Daga haka ya barta a wajen. Hannu ta saka ta ciro envelope É—in tana murmushi.
*****
“Zarah! Zarah! Yadda yake kiran sunanta shi ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi na rayuwarta na baya kafin ta auri wannan azzalumin mutumin……
​
Name: | [UMMIE HAUSA NOVEL ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | November, 2021 |

Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe

Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram
