Hausa Novels

Ummu Waheeda Hausa Novel Complete

Ummu Waheeda Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai amincin Allah su kara tabbata ga fiyyayen hallita Annabin rahama, ya ALLAH yanda ka bani ikon fara wannan littafi nawa lpy, Allah kasa nagama lpy, ya ar-rahman kayi hani da hannu na wajen rubuta abunda bazai amfane al-umma ba, kuma ina rokon ka da ka bani ikon isar da abunda nakeson isarwa,

 

Typing

Free page

Episode 1to5

 

 

 

*NNAMDI AZIKIWE AIRPORT*

Wata kyakyawar yarinya ce na hango tana saukowa daga mattatakalan jirgin da saukar su ke nan, ko minti biyu ba su yi ba,

 

 

Cikin shigar abaya red colour wace akayiwa ado da black stones ya yin da veil din abayan kuma black colour ne, sai da na kare mata kallo ta’s,

 

Littafan Hausa Novels

Domin samun littafan Hausa guda 10000 masu dadi se ku danna nan

Subhanaka lahuma fatabarakallahu ahsanul khalkin shi ne kalmar da na furta a ya yin da nayi ido biyu da ita,

 

 

Waton yarinyar kyakyawa ce sosai ajin farko, fara ce ta’s hasken fatar ta har wani glowing ya ke,

 

 

Gata da ɗan siririn hanci circle face din ta mai dauƙe da ɗan ƙaramin pink lip, oily eye din ta kuwa dauƙe da zara-zaran gashin ido,

 

 

 

Ƙirjinta cike suke dam tamkar zasu fasa rigar abayar dake sanye a jikinta, gata da manya-mayan hips OMG, wannan idan aka kirata da Queen of beauty ba a yi ƙarya ba, domin kuwa kamar ma ta fi hakan,

 

 

 

Na tabbatar da koda ita ce ta yi kan ta, ba na jin za ta iya yiwa kanta irin wannan kyau da take da shi ba, ba namiji ba ko mace ta kalle ta,

 

 

 

To sai ta kara kalla domin kuwa kallo guda ba zai ishe ka ba, har sai ka kara kallon ta, da sauri wata kyakyawar ƙaramar yarinya mai ƙama da ita sak taje ta rungume ta,

 

 

 

 

Tana fadin “Oyoyo Aunty *WAHEEDA* barka da dawowa gida Nigeria da fatan kin sauka lafiya” zata kara magana ke nan wata matashiyar mata wace ba za ta haura shekara Ashrin da biyar ba aduniya ta dakatar da ita ta hanyar cewa,

 

 

 

 

“Haba Waleedah ki barta haka nan mana, ba ki ga duk ta kwaso gajiya bane? Bari idan muka koma gida sai ki cigaba daga inda kika tsaya, Waleedah dariya tayi ba tare da ta sake furta komai ba,

 

 

 

 

“Aunty shine Daddy bai zo dauka na ba daga ke sai Waleeda? Kuma me ya sa shima Yaya bai zo ba, ba cin duk sun san yau ne zan dawo, gaskiya ni banji dadi ba” ce war *UMMU WAHEEDA* tamkar zatayi kuka,

 

 

 

 

“Kiyi haƙuri ƴar gaban goshin Daddy ai kin san Daddy ba zai fasa zuwa tarɓon ki ba, sai da dalili, kawai kiyi haƙuri Daddy baya agarin su na da vital meeting a Gwarinfa yana can, shi yasa bai zo ba,

 

 

 

 

“To shi kuma Yaya Faruk fa?” “A’a WAHEEDAH stop questioning me like that, haba” WAHEEDAH murmurshi tayi tare da ce wa “Aunty yi haƙuri” ta manta da cewa Yayar ta ta ba ta da son surutu ko kaɗan,

 

 

 

 

A dai-dai wani babban gida mai matukar ƙyan gaske driver ya shiga danna horn, gidan ya haɗu iya haɗuwa, ƙai koda ganin gidan toh kasan gidan wani babban attajiri ne, wanda kudi sun zauna masa iya zaunuwa,

 

 

 

 

 

Wangale musu gate mai gadi yayi, gate din ka ɗai ma abin ƙallo ne, saboda haɗuwar gate din, idan ƴaran unguwa za su yi misali da giɗan, har cewa suke gida mai gate din zinari,

 

 

 

 

Ƙallon kalo suka shiga yi daga shi har ita, ya yin da tunani da take daban haka shima tunanin da yake daɓan, “ƙar dai ace gidan su ne nan, Allah ya sa ba yarinyar nan ne Alhaji yake masa maganar ta ba,

 

 

 

 

 

“Tabb! ashe ko akwai aiki babba, duk maganar zuci ne yake tayi, ya yin da itama ta lula duniyar tunani, “me wannan dan iskan yake agidanmu, da alama ma kamar gate man ne shi din” hanya kuwa wannan MUBASHIR ɗin da na sani ne kuwa, no impossible”

 

 

 

 

 

Wani irin wawan harara ta maka masa, kafin daga bisani tayi gaba abinta, Aunty Zahra kuwa tuni har ta shiga ciki, itama WAHEEDAH shiga parlourn tayi dauke da sallama a ɓakinta, wata ƙyaƙyawar mace na hango zaune saman lumtsuma-lumtsuman royal chair daƙe cikin ƙawataccen parlourn,

 

 

 

 

Da sauri *UMMU WAHEEDAH* taje ta rungume ta, tana “Fadin shi ke nan Mommy ke ba ki yi missing ɗina ba ko?” “Mommy murmurshi tayi tare da ce wa “Ni na isa na ce banyi missing din gudan-gudan auta na ba”

 

 

 

 

 

“Nayi missing dinki my dear da fatan kin sauka lafiya?” “Lafiya qlau Mom alhamdulillah, ashe Daddy baya a garin?” cewar WAHEEDAH, “E yana wajen meeting a Gwarinfa, cewar Mommy,

 

 

 

 

“E haka Aunty Zahra tace mun, “Mommy wai an canza muna gateman ne? Ina Ya Faruk? Shima bai zo airport ba, why? WAHEEDAH ta sake fada “Kin ga don Allah Auta ki tashi ki je ki yi wanka sai ki zo mu ci abinci kin ji?

 

 

 

 

 

 

“Karki damu da rashin zuwan Faruk airport, idan kuma kina son sanin me ya hana shi zuwa, to idan ya dawo kya tambaye shi, maza tashi kije kiyi abinda nace, cewar Mommy, “toh shikenan” WAHEEDAH ta fada tareda haura sama,

 

 

 

 

 

Wani karamin daki na ga ta shiga mai matukar kyan gaske, komai na dakin da pink color akayi ado dashi, kasancewar shi ne favorite color ɗinta, towel ta ɗauko ta shiga cire kayan jikinta, toilet ta shiga, wanka ta yi, ya yin da ta dauro alwala, kasancewar lokacin sallar azuhur ya yi,

 

 

 

 

Sai da ta bada farrilah sa’anan ta sauko kasa, abinci suka ci, daga bisani Waleedah ta fara magana, “Aunty WAHEEDA ai yanzu ba za ki koma London ba ko? Tunda kin riga da kin kammala karatun ki”

 

 

 

 

 

 

 

“E my daughter insha Allah na riga da na kammala karatuna, koda zan koma to ba yanzu ba, oh Walee kin zama big girl fa, sai shegen son surutu, dukkan su dariya su ka yi, ya yin da Aunty Zahra ta zuba musu ido ta na kallonsu, domin kuwa ita bata fiye son yawan magana ba, tun rasuwar mijin ta, ta koma wata kalar tausayi, ko kadan ba ta son yawan surutu.

 

 

 

 

 

 

“Mommy an jima fita zanyi” cewar WAHEEDA “zuwa ina kuma? Kin san dai Daddynku baya son yawon nan ko?” cewar Mommy tana jefe mata kallon kwarilla, “Mommy ba fa wajen yawo zan je ba, kawai shopping ne na ke son na yi,

 

 

 

 

 

 

“Kayana duk ba atamfa, shi ne na ke son na je na siya da kuma wasu abubuwan da ba ni da su, “Okay to, ai shi ke nan, Allah ya ƙai mu an jiman lafiya” cewar Mommy, “To ameen” cewar UMMU WAHEEDA,

 

 

 

 

 

“Ƙai! Mommy ta ce ka yi ka kai ni zuwa stop and shop, zan je na yi siyyaya a plaza ɗin, WAHEEDA ta faɗa ba tare da ta ƙalle shi ba, saboda wani irin mugun haushin sa ta ke ji, magana fa na ke, ko kuma kai din kurma ne? baka jin magana, iyeeee, kuma wallahi sai ka gaya min uban me ka ke a gidanmu, da kai na ke MUBASHIR, WAHEEDA ta fada ta na mai nu na shi da yatsa .

 

 

 

 

 

 

 

*UMMU WAHEEDA* is not for free, don Allah sis kar ki shiga hakkina, ki siya, sai ki sha karatun ki hankali kwance I promise ba zan yi disappointing dinku ba, ba za ki yi, dana sanin siyen book dina ba, insha Allah,

 

 

 

*Comment and Share Fisabilillah, Maryam Yusuf Ummu Juwairiyyah, SAHIBAR ROYAL STAR🪄 CE*

 

Leave a Comment

error: Content is protected !!