Hausa Novels

Uncle ne Hausa Novels Text

Uncle Ne Hausa Novels

 

 

_UNCLE NE…!

_NIMCYLUV_

*1*

Allahamdulillah Allahamdulillah Thanks to almighty Allah (swt) for giving me opportunity to start this book, Ma sha Allah nasan You have been waiting for me so long,to NIMCYLUV is back sai a KAKKAƁE zani a gyara zama, special greeting to Maimuna Abdullah(heroine) love you wix all my hrt, secondly Hafsat Rano alkairin Allah ya kai maki,Queen Nasmer my sturbbon friend love you,How can I forget my lovely fans…? kuna raina kamar yadda kuke saka ran ganin littafaina thanks for the love and care hrt You all here is my new book UNCLE NE am sorry to say na ajjiye maganar TUGGU BIYU i have a big issues da nayi hakan so guys follow my pen…love my story, dedicated to my papa ALAHAJI SULAIMAN DAGACIN JA’OJI.

 

 

 

wanda bai karanta book ɗin nan ba,bazan ce an barshi a baya ba domin a koda yaushe yana iya karantawa,amma idan ba’a fara dakai ba..it is going to be a hit that i promise You,nayi wannan littafin ne from The very depth of my heart,wani time ɗin nai dry wani lokacin nai hawaye,wani tym ɗin ina jin waƙa.

officially welcome You to the very frist chapter of UNCLE NE..

 

 

_Bisimillah_

IBADAN
is the the capital and most populous city of Oyo state in Nigeria.

SANGO AREA

Unguwar Masu kuɗi ce,Unguwa ce da babu wanda ya damu da rayuwar wani,Unguwa ce mai cike da Attajirai,Malamai,haɗi da ƴan boko,Haka kuma Unguwa ce mai cike da ƴan duniya wanda idanunsu suke a buɗe,basa jin wa’azi balle faɗa,haka nan babu wanda ya isa ya tunkaresu da niyyar gaya masu kuskurensu.

Dugun layine wanda yake shimfiɗe da lafiyayyan titi wanda ya ƙara fito da ƙyan unguwar.
Wasu jajaye fitilone sukaiwa titin unguwar ƙawanya,wanda a kullum suke haska unguwar musamman cikin dare,gefe da gefen titin wasu green flowers ne masu ƙyau wanda suke fidda wani daddaɗan ƙamshi.

 

 

Can kusan ƙarshen layin wani haɗaɗɗan gidane ginin zamani,tun daga jikin tafkeken get ɗin zaka san tabbas wannan gidan bana ƙana nan mutane bane,ajikin get ɗin anyi rubutu inda aka rubuta hause no 133.

 

 

Sosai harabar gidan taƙawatu da kurayan furanni na zamani masu ƙyau da tsari,Compound ɗin gidan cike yake da manyan motoci na zamani irinsu,boggatti,ferari,da sauransu.
Yanayin ginin gidan irin mai sama da ƙasa ɗinanne ma’ana dai ginin bene mai hawa biyu.

Side ɗin parko na gidan wanda ya kasance hawan farko na gidan,babban parlour zaka fara tararwa gefen parlour’n kuma ɗakuna ne masu ɗan yawa kusan bedroom ɗin shida,left hand ɗina nayi domin shine yafi jan hankalina fiye da sauran part ɗin, Tun daga ƙaramin parlour’n dake cikin part ɗin na fara jiyo fitar numfashi mai kama dana zaucewa a hankali na tura kaina cikin bedroom ɗin kasancewar a buɗe yake,saurin tsayawa nayi sabida ganin wata ƙyaƙƙyawar matashiyar mata wacce aƙalla ba zata huce shekara ashirin da biyar ba zuwa shida.

 

Tana durƙoshe gaban bed ɗin dake ɗakin yayinda hannunta ke riƙe da gadon gaba ɗaya jikinta rawa yake,banda nishi da gurnanin wahala babu abinda ke fita a bakinta,yayinda turtsetsen cikinta ya sauka zuwa mararta banda juyawa da motsi babu abinda “ƊAN” cikin nata yake,da alamu shima ya ƙago yazo duniya,karkarwar jikin tane ya tsananta gaba ɗaya ta jigata ta fita haiyacinta banda kiran sunan Allah babu abinda bakinta yake ke faɗi,Can ƙasan zuciyarta kowa maganar data keson furtawa a saman bakinta tane ta kasa,burinta bai huce bakinta ya buɗe ta samu damar faɗin abinda ke damunta cikin rai da kuma zuciyarta,Runtsa idanunta tayi da ƙarfin sabida wani juyi da abin cikinta yay tare da naushin mararta nan take jini ya ɓalle mata ya soma zuba,cikin yanayin na fitar hayyaci tare da zaucewa haɗi da fidda rai ta ɓude baki da ƙyar tace.

 

 

“Ya hayyuu ya ƙayyumuu
ya kaliƙu ya zul arshidd majidd,ya fa’alulluma yurid biraha matika astagisuuu”

Takai ƙarshen addu’ar tana sakin wani fitinanan nishi wanda ya kusa ta fiya da numfashinta ya rabbi nan take wani..

Kamar amafarki Mameey dake ƙwance bisa tangamemen royal bed ɗinta ta jiyo sautin numfashin Zulfa cikin kunnuwanta lumshe idanu tayi tana jin kamar a magagin barci take, da sauri ta miƙe zaune daga ƙwancen da take wani irin hantsilawa Mameey tayi daga gadon zuwa ƙasan gadon,a gigice ta fara gyara ɗaurin zaninta dake kuncewa sabida fargaba,tabbas idan bata manta ba yaune E.D.D Zulfa ya cika gaba ɗaya ta manta,cikin tsoro fargaba kiɗima tashin hankali ta fara sakkowa daga stairs ɗin benen.

Tun a babban parlour ta fahimci aƙwai matsala kuma ta ƙara tabbatarwa kanta Zulfa naƙoda take da sassarfa ta ƙarasa shiga cikin part ɗin Zulfa,cikin sauri Mameey ta ƙarasa shiga cikin bedroom ɗin,tana shiga ta samu Zulfa durƙoshe cikin jinin wanda ya ɓata jikinta gaba ɗaya,da sauri ta ƙarasa wajanta tana salati tare da faɗin.

“Zulfa mene zan gani haka?kika zauna cikin ciwo kin san illar duguwar naƙuda kowa?ohhh ni Salamatu yau naga abinda yafi ƙarfina wannan wanne irin jinine haka?mun shiga uku”,

Ta faɗi hakan tana sakin kukan tausayi halin da Zulfan ke ciki,sabida ganin jinin dake zuba ta jikinta ga kuma yadda numfashinta ke sarƙewa jikinta banda rawa babu abinda yake,da hanzari ta ƙarasa matsawa inda take sabida kan babyn da taga yana fitowa,wata jijjiga Zulfa ta fara idanunta na kafewa.

 

 

 

Ganin hakan yasa Mameey sakinta tare da ficewa da gudu tana tafe tana ƙwala kiran sunan Alhaji!! Alhaji!! Alhaji!!!

Alhaji Kabeer na kishin giɗe saman wata lafiyayyiyar sofa,hannunsa dafe da saitin zuciyarsa,yana jin yadda take buga masa da ƙarfi,ga wani raɗaɗi da ɗaci daya keji a cikin maƙoshinsa,gefe guda kuma yana jin tsoro da fargaba haɗi da zullumi wanda bai san kona menene ba.

 

Ya rasa dalilin daya sanya yake mafalki mara ƙyau akan Zulfansa mace mafi soyuwa a cikin ransa,tabbas bazai jure ganinsa cikin wannan halin mafalkinba,kamar yadda bazai jure ganin Zulfa cikin wani hali ba.

 

 

 

Saurin buɗe idanunsa yay jin muryar uwar gidansa na kiran sunansa,da sauri ya dira daga kan sofar yana fita sukaci karo da Salmerh a birgice ya kalli Salmerh tare da faɗin..

“Salmerh mene ya sami Zulfa?..kada ki sake bakinki ya faɗi babban kalamai dazai sanya zuciyata bugawa..”

Bakinta na rawa tace

“Zulfa haihuwa inajin..”bai bari ta ƙarasa maganar ba ya ƙwasa da gudu zuwa part ɗin Zulfa.
da gudu Mameey ta mara masa baya,suna zuwa tana haihuwa ganin zata danne jaririn ya sanya Alhaji Kabeer saurin isa gareta,yana zuwa ya saka hannu ya gyara mata zama,tare da amsar rezar hannun Mameey ya yanke cibiya,cikin ikon Allah a lkcn mahaifa ta faɗo,yana ganin haka ya saka hannu ya miƙar da ita tsaye cikin murna da farin ciki ya rungometa a jikinsa yana shafa sumar kanta idanunsa fal hawayen farin ciki,bai taɓa tunanin zai samu haihuwa nan kusa ba,sai gashi ubangiji ya azurtashi da ita a lkcn dabai taɓa tunanin samunta ba,tabbas ya yarda da wannan kalmar da ake cewa inda rai da rabo,haka kuma mutum baya fidda rai da samun rahamar ubangiji,domin shine mai bayarwa a lkcn da yaso haka kuma shine mai hanawa a lkcn dayaso,wasu hawayene suka fito daga cikin idanunsa cikin muryar farin ciki yace.

“Thank you soo much my Anuuu,Allah yay maki albarka nagode sosai da ƙyautarki nagode Allah ina sonki Allah ya baki lafiya”

Mameey janye jaririn tayi jin yana tsala kuka a wani zani mai ƙyauta ta ɗaukesa,kana ta zaune bakin bed,catton da zaitun ta fara goge masa jiki da ita,murmushi tayi ganin yadda yake ƙoƙarin sanya hannu a baki da alama da yunwa yazo,sai tsala kuka yake,a cikin ranta take jinjina ƙyan yaron da kuma baiwar da ubangiji yay masa,domin ƙwayar idanunsa ta kasance blue ce,kamarta turawa,ga wani ɗan cindo a gefe yatsanshi.

A sanyaye Zulfa ta rungome mijinta Alhaji Kabeer idanunta na zubar da ƙwalla tace “Yaa rahamanu”murmushi yay tare da sumbatar goshinta,kamar an tsikareta ta sanya hannu ta ture Alhaji Kabeer daga jikinta,a hankali ta fara yin baya ganin hakan ya ƙara matsuwa kusa da ita yana shirin kamata yaji ta fasa wata uwar ƙara,a gigice ya ƙarasa wajanta kafin ya riƙeta tasa hannu ta hankaɗesa tare dayin waje da gudu jinin haihuwa nabin jikinta….

Idan kun bazashi ya amsu wajan mutane za kujine

1 Comment

Leave a Comment

error: Content is protected !!