Kannywood News

Wacece Aisha Aliyu Tsamiya

Wacece Aisha Aliyu Tsamiya

 

 

 

 

 

Shin wacece Aisha aliyu tsamiya Asalin sunanta aisha aliyu ta samo sunanta na tsamiya ne sakamakon film din ta na farko wato tsamiya an haifeta a karamar hukumar nasarawa dake garin kano.

haka zalika aisha tsamiya tazo duniya a shekarar 1992 zuwa yanzu shekaruta 29 zuwa 30. tayi karatun ta na primary da secondary a giginyu dake garin kano inda daga bisani ta samu admission a babbar jami’ar north west.

Aisha aliyu tsamiya ta shigo masana’antar kannywood da kafar dama dub da yadda ta shahara cikin kan kanan lokaci. an fara yi mata lakabi da tsamiyane tun bayan fitowar film din ta na farko wata tsamiya daga baya kuma akaci gaba da kiranta da suna Aisha Aliyu tsamiya.

Aisha Aliyu Tsamiya tayi fina finai da yawa kamar irin su.

Tsamiya

Ranar Baiko

Hanyar Kano

Bahaushiya

Da Kishiyar Gida

Dakin Amarya

Husna

Jamila

Mai Dalilin Aure

Makahon Gida

Munubiya

Niqab

Nisan Kiwo

Rayuwa Bayan Mutuwa

Zeenat

Uzuri

Salma.

sannan tafi shahara ne a fina finanta guda biyu wato dakin amarya da kuma salma. Aisha tsamiya ta bayyana yadda wadan nan fina finan sukayi mutukar tasiri akanta wato dakin amarya DA kuma salma.

da ake tamayarta akan wanne tasiri ne wadannan finafiani guda biyu sukayi a rayuwarta sai tayi jawabi kamar haka film din dakin amarya na sha mutukar wahala acikin sa domin har rauni na gaske aka jimin yayi daukar shirin.

Download Izzar So Movie App Here

A bangaren film din salma kuma shi wannan labarin film din ne yake bani mutukar tausayi sabo da yadda nake mutuwa na bar saurayina cikin tsanani da kuncin mutuwata.

Idan muka dawo bangaren kudi zamu iya cewa aisha aliyu tsamiya tana daya daga cikin yan matan kannywood masu kudi sosai. wannan shi ne abin da zamu iya kawo muku acikin wannan shiri.

Leave a Comment

error: Content is protected !!