Wacece ni Hausa Novel Complete
Wacece ni Hausa Novel Complete
*Duk wadda ta san ba za tai comment da sharhi ba idan ta shiga dan girmam Allah bana buƙatarta a group ɗina karta shiga dan zan fidda ita*
*Bana buƙatar maza a group dan daraja da matsayin amnabi muhammad s.a.w kar namiji ya shiga dan soyayyar annabi s.a.w*
_*WACECE NI?*_
*Tsarawa da Rubutawa*
_Zainab Muhammad Indian Girl (Garkuwar dashen Allah)
*DASHEN ALLAH WRITER’S ASSOCIATION*
*TUNATARWA*
_Wannan labari labari ne da ya zo min a mafarki na kuma labari ne da ya taɓa min zuciya ainun dan haka zan dakata da rubuta *BURIN RAI* sai na kammala wannan_
*GARGAÆŠI*
_Ban yadda wani ko wata su yi amfani da wani sassa na labari na ba ta kowace siga domin yin hakan babban kuskure ne domin ubangiji na kallon ku_
*NOTE*
_Wannan labari ne mai taɓa zuciya gami da raunana zuciya ciki akwai tausayi, cin amana, yaudara, zafin soyayya dama wasu cikin wasu duk cikin littafin *WACECE NI?*_
*P1⃣&2⃣*
Kuka take mai cin rai da taɓa zuciyar mai saurara zuciyarta tana bugawa da sauri numfashinta na sama da ƙasa.
Wata farar mata kyakykyawa dake zaune kusa da ita fuskarta É—auke da damuwa ta dube ta cikin lallashi.
Ta ce”Baby Ifteehal dan Allah ki ragewa kanki wannan kukan ki É—auki Æ™addara ki yadda da jarrabar ubagiji, Baby Iftee mu muka haifeki amma mun É—au Æ™addar dan haka kema ki yadda da ita duk da na san da ciwo ace an maka fyaÉ—e da Æ™uruciyarka”
Runtse idanu Ifteehal ta yi jin kalmar fyaÉ—e data fito a bakin Meemanta bata son ko ka É—an ta sake jin wannan kalmar duk da ita ba fyaÉ—en ne ya fi mata ciwo ba sai abu É—aya.
Taja majina sannan, Ta ce”Meema! Meema!! Meema ba wai ina kuka ne saboda ubangiji ya jarrabeni da ai min fyaÉ—e ba sau dan abu É—aya wanda na tabbatar kema da kin sani zaki iya haÉ—iyar zuciya”
Dammm! Ƙirjin Meema ya cikin kaÉ—uwa, Ta ce”Menene wannan Baby ki faÉ—a min dan Allah idan har wannan damuwar zata barki, Iftee bana son ganin ki a damuwa”
Wani murmushi Ifteehal taimai ciwo, Ta ce”A’a Meema har abada ba zan taÉ“a faÉ—a miki wannan ba dashi zan koma ga mahalicci na”
Meema ta zuba mata idanu tana kallonta ya yin da a zuciyarta take tunanin menene wannan da har Iftee ke wannan maganar akai? Koma menene Allah yafi kowa sani.
Meema Ta ce”Shikenan ba zan takura miki akan sai kin faÉ—a min ba domin na san ba Æ™aramin abu bane da har kika Æ™i faÉ—a min amma abinda nake so ki cire damuwa ki rage kuka”
“Kuka ya aure ni Meema, kuka shine gata na kuka shine zai tallafa min dan haka har abada ba zan dena kuka ba”
Ifteehal ta faɗa tare da miƙewa da gudu ta haye sama tana kuka ta shige ɗakinta tare kullewada key ta faɗa kan gadonta tana mai sake buɗe sabon babin kuka.
Meema ta bi Ifteehal da da ido tana mai ƙokarin tashi ta bita amma sai wayarta ta dake kan centre table ta shiga ruri dan haka ta miƙa hannu a hankali ta ɗauka tare da duba mai kiran ta kara a kunne.
“Assalamu alaikum Daddyn…”
Bai iya bari ta Æ™arasa maganar ba ya katseta da, Ce wa”Khadija d gaskene abinda kunnuwa suka ji mun? Idan kuwa har tatabbata abinda naji hakane ina tausayin wanda ya aikata hakan domin har ahalinsa ba zan bari ba”
Wani gaurannumfashi Meema taja da, Ce wa”Babu Æ™arya a cikin abinda kunnuwanka su kaji maka Daddyn Iftee”
“Innalillahi wa inna ilaihirraju’un! Koma wanene wannan ya aikatawa É—iyata fyaÉ—e ba zan bar shi ba sai na Æ™arar da ahalinsa”
Daddy ya faÉ—a cike da jin zafi a zuciyarsa.
“Daddyn Iftee to yanzu yaushr zaka dawo domin wallahi abin ya yi min yawa”
Meema tai maganar hawayen na bin kumatunta.
Daddy cikin damuwa da jin zafin hawayen matar tasa, Ya ce”Yanzu Ina Maman tawa take?”
Meema Ta ce”Yanzu ta tashi ta tafi daÆ™i a guje tana kuka domin tunda abin ya faru take kuka taÆ™i ta sassautawa kanta da mu kanmu”
Daddy Ya ce”Shikenan ki cigaba da rarrashinta insha Allah yau zan dawo”
Meema ta amsa da, “Allah ya dawo da kai lafiya”
Ya amsa da “Ameen” tare da kashe wayar.
Meema itama ta aje wayar tare da miƙewa ta nufi benan, kai tsaye ɗakin Ifteehal ta nufa amma ko da ta taɓa ƙofar ɗakin sai ta ji ta a rufe ta shiga bugawa amma shiru Ifteehal taƙi buɗewa har Meema ta gaji ta koma falo ta zauna jiran tsammani.
***
Bayan sun gama wayar cikin sauri ya shiga haÉ—a kayansa da sauran abubuwa masu muhimmanci a cikin akwati kafin wasu mintuna ya gama haÉ—awa ya É—auka ya fito harabar gidan inda ya samu ma’aikatansa ya faÉ—a masu za shi gida su kula da komai, nan driver ya É—auke shi zuwa airport nan ya samu jirgi wanda zai kai shi amma da kuÉ—i sosai dan haka ya biya bayan Æ´an mintuna jirgin ya É—aga zuwa nigeria.
Awanni kaÉ—an jirgin ya sauka a filin jirgi na aminu kano, yana fitowa daga jirgin ya samu motar haya ya shiga tare da faÉ—a masa inda zai kai shi.
Mintuna ƙalikan ya kawo su dan haka ya bawa mai motar kuɗinsa bai tsaya karɓar canji ba ya nufi get ɗin gidan sa, knock ya shiga yi.
Nan mai gadi ya leƙo yana tambayar wane, da sauri ya zube ƙasa yana kasar gaisuwa ganin mai gidan sa sannan ya buɗe masa kofa ya shiga.
Akwatin mai gadin ya karɓa kafin su nufi cikin gidan.
Knock Daddy ya yi.
Da sauri Meema dake zaune a falon kan kujera ta rafka tagumi ta ta miƙe ta nufi kofar ba ta ma tsaya tambayar wane ba ta buɗe saboda zuciyar ta yi gaba.
Zubawa juna idanu su kai kafin Meema ta faÉ—a jikin Daddy ta rushe da wani kuka mai cin rai.
Shi kuwa mai gadi ya aje akwatin ya fice.
Daddy ya sake rungume Meema tsam kafin ya mata kiss a goshi.
Cikin kuka Ta ce”Daddyn Iftee ya zan yida rayuwata bani da kowa sai ku duniya su biyu kawai na haifa ita ka É—ai yanzu take a kusa da ni ga wannan abu ya faru da ita ta kasa sukuni”
Bubbuga bayanta Daddy ya shiga yi cike da rarrashi kafin ya saketa daga rungumar da yai mata ya É—ago da fuskarta tana kallonsa.
Ya ce”Sorry kinji Deeja na babu abinda zai faru da Iftee kuma ki sani ba zan taÉ“a kyale mai hannu a cikin wannan al’amari ba, yanzu muje wajanta”
Haka ya riƙe hannunta su ka nufi benan suna zuwa ƙofar ɗakin nata suka shiga knock da iya ƙarfin su amma shiru babu wani alamar za a buɗe.
Cike da rauni da faÉ—uwar gaba Meema, Ta ce”Daddyn Iftee kawai a É“alla Æ™ofar nan zai fi”
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels PdfÂ
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
Daddy Ya ce”Shikenan”
Nan ya samu abu ya buga a sai tin wajan mukullin, aikuwa take ƙofar ta buɗe suka tura suka shiga ɗakin.
Abinda idanunsa ya gani ne ya saka ganinsu ɗaukewa na ɗan wanu lokaci zuciyoyun su ya shiga harbawa da sauri sauri…
*****
Tsayawa tai tana ƙare masa kallo, duk ya zama wani iri a kwana biyun nan ya rame ya yi baƙi.
“Ifsar!”
Ta kira sunan sa amma ina bai ji ba ya yi nisa a tunani, sai da ta sake kiransa da ƙarfi.
“Ifsar!!”
A zabure ya amsa.
“Na’am Ummi!”
Ummi cikin sarewa da yana yin nasa, Ta ce”Ifsar kai kwa meke damunka tun jiya iyye? A kwana É—aya a ce ka zama kamar ba kai ba”
Ifsar ya shiga zazzare ido yana kallon Ummi.
Ummi ta zauna kusa da shi tare da dafa Æ™afaÉ—arsa, Ta ce”Babana lafiyarka kuwa meke damunka?”
Ƙasa yai da kansa sai ga hawaye na bin idanunsa nasu zafi, a hankali ya ɗaga kai ya kalli Ummi kafin.
Ya ce”Ummi yaushe duniya zata gyaru? Yaushe azzalumai za su ga Æ™arshen su? Yaushe ne! Yaushe ne!! Yaushe ne Ummi!!!?”
Sai kuma ya saka wani irin kuka mai taɓa zuciya.
Jikin Ummi ya yi sanyi hankalinta ya tashi ta matsu taji meke damun É—an nata.
A tausashe Ta ce”Babana ba duniya ce za ta gyaru ba mutanan cikinta ne domin sune É“atattu ba ita ba, su kuma shuwagabanni shune azzaluman ba azzaluman bane azzalumai.
Babana ka faÉ—a min damuwarka”
Ifsar ya runtse idanu hawaye na zubowa ya fara magana, “Ummi fyaÉ—e! FyaÉ—e akai mata Ummi”
Cikin zaro ido da fargaba Ummi, Ta ce”Inalillahi wa inna ilahirraju’un! Babana wa akaiwa fyaÉ—en? Domin na tabbata wanda akaiwa mai matsayi ne a gareka tun da har ka damu haka”
“Ummi Ifteehal wadda nake driving a gidan su wadda aka dauke ni nake janta a mota duk inda zata, Ummi n nake kaita makaranta na kaita gidan Æ´an uwansu ko ina Ummi ni nake kaita ta yar da dani sosai ta bani amana shaÆ™uwa mai tsanani ta shiga tsakaninmu amma Ummi addu’a ta riga fata domin sai da aka aikata mata muka dawo naji tana faÉ—awa mahaifiyarta Ummi da na san waÉ—anda su ka aikata mata haka tsab zan bar duniya da su!”
Kan Ummi ne ya shiga sarawa ba ƙarya idan har Ifsar ya damu akan abinda akaiwa wannan yarinya domin ko ita zqta bada tabbacin yarinyace mai ladabi da biyayya tarbiya da girmama na gaba gashi bata da wulaƙanta talakawa.
Cikin raunatacciyar murya Ummi, Ta ce”Allah ya saka mata, duk wanda ya aikata mata wannan É“arna ubagiji karya barshi”
“Ameen Ummi domin ko ni yanzu da zan ga wanda ya aikata hakan ba zan barshi ba”
Ifsar ya faÉ—a a zafafe kamar yadda zuciyarsa ke zafi.
Ita kuwa Ummi ba ta iya ƙara cewa da shi komai ba saboda ta lura kamar sonta ya kama ɗanta, kuma ko ba ma haka ba ta san da ciwo a ce anwa mace kuna yarinya fyaɗe kai ko ba ƴarka ko ƙanwarka bace ko ƴarka ba.
Cike da nutsuwa irin ta iyayen kwarai Ummi ta shiga kwantarwa da É—an nata hankali har ya É—an samu nutsuwa duk da zafin da dafin na nan a zuciyarsa.
*Comments and sharhi*
*Shares saboda Allah*


​
Name: | [Wacece ni Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV
Zaku iya sauke Manhajar Android ta My Novels anan Domin samun littafan Hausa maras adadi

Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na My Novels anan domin samun Littafan Hausa Maras adadi

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram
