Hausa Novels

Wahalar So Hausa Novel

Wahalar So Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*WAHALAR “SO”*

 

 

NA

 

SA’ADATU BELLO Saadatu99gmail.com!

 

Duk kan godiya ta tabbata ga Allah mad`aukakin sarki mai kowa kuma mai komi.

 

 

Ina rok`on Allah yadda na fara (Rubutun nan nawa lafiya ya bani ikon gamawa lafiya) Darasin dake ciki Allah yabamu ikon amfanuwa dashi akasin haka Allah ya bamu ikon gyarawa.

 

 

*Ina jin-jina ga k`ungiyata mai Albarka Karamci writers Association. (Karamci tushen mu’amala ta gari.)*

 

 

*Ina k`ara godiya ga shugaba Sanazz mai Adalci Allah ya k`ara d`aukaka yasa kifi haka Ameen ya Hayyu ya Qayyum*

 

*Ya Allah ka jik`an iyayen mu da Rahama kasa Aljannah ce makomarsu Ameen ya Hayyu ya Qayyum.*

 

 

*Mijina abun Alfaharina jin-jina gareka  Mal Salisu Umar Karofi Ranka shi dad`e  Allah yak`ara d`aukaka da nisan kwana mai Albarka*

 

K`awayen arzik`i writer’s

 

Mai girma Admin cute Hafsy

 

Mum Mus’ab

 

Deejannuwa

 

Aishatu Falalu.

 

Da duk wanda ban ambata ba writer’s ina ma kowa fatan Alkairi Allah ya Albarkaci Alk`alamin mu baki d`aya

 

*My fans hakuri zan baku domin lokaci bazai bari in ambace ku ba domin yawan ku over sai ku cinye littafin gaba d`aya don haka nagode nagode ina Alfahari da (Rubutu) Domin na had`u da mutanen da ban tab`a zato ba a rayuwa Alhamdulillah Alhamdulillah.*

 

*Takuce SA’ADATU BELLO Sis FATINAH ONLINE*

 

 

*Na sadaukar da wannan littafi ga d`an uwana BELLO MOH BELLO (BMB) Allah K`ara lafiya Magajin Baba.

 

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

 

P 1

 

 

……………Da sauri na hango wani saurayi matashi yana saukowa daga matattakalar bene dake cikin wani k`aton gida wanda zai tabbatar maku cewa naira ta kwanta acikin gida.

 

Wata dattijuwa naga tana kallon saukowarsa tana murmushi mai k`ayatarwa da alama shekarunta zasu kai sitting(60) Amma fa duk da tsufanta bai hana bayyana kyawunta fitowa ba ga kuma kamaninta nan da wannan matashin saurayin.

 

Daga ganinsa dai kaga d`an gata bazai wuce shekara talatin da biyar ba(35yrs) Kai da ka gannsu kasan suna cikin farin ciki.

 

Ni kam abunda ya bani mamaki na tsaya na saki baki da hanci ina kallon yanda parlon gidan ya had`u kamar ba’a cikin birnin katsina gidan yake ba.ban gama jin-jina kyawun parlon ba naji muryar saurayin nan ta doki dodon kunne na!

 

“Granny me yasa baki tasheni a barci ba?” Ja mashi dogon hancinsa tayi.

 

“Kaga Ahmed naga ka kwaso gajiya ne shiyasa na barka ka huta awa nawa kayi a jirgi?” Ya mutsa fuska yayi tare da hugging dinta, Itama sumbatarsa tayi a goshi.

 

“Gaskiya ne Granny Spain akwai tafiya.”

 

“To yanzu dai muje kayi breakfast wannan shirin dakayi nasan na fita ne.”

 

“Yes Granny zan leK`a company ne amma ba dad`ewa zanyi ba. Wai Mami bata fito bane ba?” Ya k`arashe magana yana kallon part din Mami. Jim! tayi kad`an.

 

“Damuwar Ahmed kenan yar uwarsa baya son abunda zai tab`a mashi ita shiyasa har yanzu ya k`i yin Aure.bata gama magana a zuciyarta ba taji muryarsa.

 

” Granny ko bata da lafiya ne?”

 

“A’a Ahmed kawai tashiga ne tayi wanka don itama nasan zata lek`a office ne.”

 

Ajiyar zuciya ya sauke tare da jan kujerar daining ya zauna.gaskiya kowa ya bar gida- gida ya barshi. Kunun gyad`a ya zuba da k`osai wanda k`amshinsa ya cika wurin cup din ya d`aga yakai bakinsa tare da gutsurar k`osai d`in lumshe idanuwansa yayi tare da furta.

 

“I really missing u my sweet Mami wannan hidimar nasan don ni kikayi ta.”

 

Murmushin jin dad`i Granny tayi na jin dad`in yanda jikokin nata ke k`aunar junansu.

 

(Ahmed Ibrahim Galadima) Shine cikakken sunansa.

 

Wayar daya d`aga ne yasa yayi saurin mik`ewa yana cewa ” kujirani nan da 20mins zan iso insha Allahu.”kwashe keys d`in motarsa yayi ya kalli part din Mami again.tsaki yayi “mtssss ya furta a hankali ” ban ganta ba zan fita.”

 

Granny data maida hankalinta a TV ya kalla, Granny kice ma Mami zan sameta Office an kirani a company zan gana da wasu bak`ine daga pakistan.”

 

“To ba komi zan sanar mata adawo lafiya.”

 

“Thank u my Granny.”

 

Da sauri ya fita ya nufi parking lot ya d`auki wata k`atuwar Mazda wadda 2022 ta fito ni kaina kallon motar na tsayayi kai!masu kud`i na sha’aninsu rivos yayi mai gadi ya wangale masa get ya sulala kan motarsa.

 

Dai-dai inda danja ta tsaida su jikake kwatsam!!an bugi bayan motarsa wanda har saida danjar motar ta tsage amma kad`an wani mai mashin ne d`auke da wata yarinya wadda shekarunta basa wuce 18-19 daga gani mai mashin d`in d`an acab`a ne gaba daya wurin kallon sai ya koma ga wanda zai fito daga motar don ganin wane sakarai ne zai buga mashi mota haka.

 

Ganin mace ce bisa mashin din yasa yaji ranshi yayi mummunan b`aci kowa kallon yanda yayi kan mai mashin din yayi kamar wani zaki suna jiran ganin mai zaiyi masa? Yana isa fisgo yarinyar yayi a bayan mai mashin d`in………..

 

To fah akwai fa badak`ala acikin wannan labarin amma vote dinku ne kad`ai zai bani damar updated kullum insha Allahu

 

Ku biyo ni don jin me zai faru?

 

Taku ce Sa’ar Mataa Sis FATINAH ONLINE

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

P 2

 

 

 

 

 

 

 

…………..A fusace ya juya zai wanke mai mashin d`in da mari, da sauri yarinya ta rik`e masa hannu itama afusace ta fara magana.

 

 

 

 

“Me yayi maka?da zaka sanya hannu ka dake shi?ai abunda ya faru ba da gangan bane ba, asalima kai kayi kok`arin haye mu amma saboda kai wani ne shiyasa zaka ci zarafinsa?”

 

 

 

 

Kallon k`aramar yarinyar yakeyi da mamaki fal aransa shi yaushe ma ya tab`a tsayawa mace tana gaya mashi magana data minti biyar ba arayuwarsa? Bare wata k`aramar yarinya.”

 

 

 

 

Ganin ya tsaya kallonta ne yasa ta fisge hannunta daga rik`on dayayi mata takardun dake hannuwanta ta k`ara gyarawa kamar daga sama yaji muryar yarinyar tana fad`in.

 

 

 

 

“Mr” kabamu wuri tunda naga anjaye motar taka daga wurin kuma ga danja ta bada hannu nasan dai baka da tausayin dazaka ba mai mashin din nan kud`in gyara tunda kake niyyar kwashe shi da mari.”

 

 

 

 

“Stop!! That nonsens my frnd!!”

 

 

 

 

Jikinta ne yakama rawa saboda tsabar tsoro kamar zata saki fitsari a wando dama fa maganar data keyi kawai k`arfin hali ne domin dai daga gani wannan wani ne agarin amma saboda tsabar kasada irin ta ta takeyi masa rashin kunya.kamar a mafarki ta sake jin muryasa yana tambayar.

 

 

 

 

“Nawa ne kud`in gyaran mashin din?”

 

 

 

 

Amsa ta bashi batare data san menene ya fito bakin ta ba saboda a kid`ime take ta k`osa ya barsu su wuce kada fitsari ya kubce mata.

 

 

 

 

“Dubu goma.”

 

 

 

 

Dariya taso bashi don ya lura yarinyar ba cikin hayyacinta take ba. Amma fa bata da kunya daga ganinta.k`ara d`aure fuska yayi kafin ya juya wurin da driver ya kawo masa wata motar ya janye wannan dama tun kafin ya fito motarsa yayi ma mutumin text da kuma dai-dai inda yake yana zuwa ya ajiye masa wannan sannan kuma ya janye wadda aka buga da mashin d`in.

 

 

 

 

Bud`e motar yayi ya d`auko wata jaka ya bude ya zaro rapas na 50k ya dawo wurin da take tsaye ya jefa mata su a fuska!

 

 

 

 

“Poor girl kije keda k`azamin mai acab`arki ku raba tunda naga alama kema neman kud`in kika fito.”

 

 

 

 

Gaba d`aya mutane dake kallon drama da sukeyi suka saki baki ganin wulak`ancin da yakeyi mata.

 

 

 

 

Ita kam gyalenta tasanya ta tare kudin.binshi tayi da kallo yanda ya juya ko ajikinsa ya nufi motarsa ya shiga batare da ya K`ara ko waiwayensu ba.

 

 

 

 

Mai mashin din ne ya matso kusa da ita sai lokacin yasamu damar magana.

 

 

 

 

“Amma Hajiya kidaina yin wannan kasadar haka, kinga halin masu kud`in nan bashi da kyau badon ke ba da bansan irin wulak`antar da

 

zanyi ba.”

 

 

 

 

“Karka damu da alama wannan baisan darajar mutane ba zai samu dai-dai dashi muje ina makara ga kud`in gyara mashin d`inka.”

 

 

 

 

“To shikenan nagode da taimakonki.”

 

 

 

 

“Bakomi ka godema Allah.”

 

 

 

 

 

 

 

Haka suka k`arasa har company data ce masa zataje interview anan ya sauketa dama itama naira d`ari biyu ne kacal gareta zuwa da dawowa da kyar ma ta samesu wurin Auntyn ta. 20k ta mik`a ma mai mashin d`in tace yaje yayi gyara sauran kuma Allah ya bashi.

 

 

 

 

Godiya yayi mata sosai kafin tasanya sauran a jaka ta sanya kai cikin company wanda gabansa ke d`auke da tambarin sunan (A .I .GALADIMA DISTRBUSHIN COMPANY.). Ta k`aramar kofar get din tashiga tana ta kalle -kalle irin had`uwar company wai duk na mutum d`ayane.Allah ma ya taimaketa da sauran lokaci ba’a fara ba.tambaya tayi aka nuna mata wurin dazata shiga.

 

 

 

 

Daga sama wurin da zai gana da bak`insa akan benen ya hangota zata shiga k`ofar da zata sadaka da office d`in da akeyin interview d`in da mamaki yake k`ara tsayawa yana kallonta tabbas ita ce!! Wani irin murmushi!! yayi na mugunta da sauri ya juya ya dawo k`asa har yana sarsarfa akan mattakalar benen……

 

 

 

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Masha Allah indai kuna biye dani to zaku nishad`antu da wannan littafin nawa my fans Allah yabar kauna�

Leave a Comment

error: Content is protected !!