Walijaam Hausa Novel Complete
Tag: Walijaam Hausa Novel
Da sunan allah mai rahma mai jink’ai” dukkan godiya ya tabbata ga allah uban gijin talikai Allah ina rokan ka yanda na fara wannan littafi lafiya allah kabani ikon kammala shi lafiya ameen ._
Wannan littafin tun daga farkon shi har karshen WALIJAAM sadaukar ne ga dukanin fulani.
“Wani irin iska ne yake tashi daga sararin samaniya ,wanda in badon yanayin da ake ciki na Rani ba da tabbas ka alamta cewa wannan goguwar ruwan sama ne yake dab da tsinkewa. Wata yar budurwan bafullatana ce na hango wacce a shekaru bazata haura 13 ba tana sanye da kayan ta na sak’i ,da ka gane ta kaga bafullatana ta usul ,sanye take da kayan fulani farar sake da akayi masa ado da blue din abawa hannun ta dauke da dan madaidaicin sanda ,wanda yayi dai dai da tsawon wannan yarinyar bafullatanan .
Walijaam Hausa Novel
Karin wasu littafai da zaku so
-
Matar maza uku Hausa Novel
-
Doctor Eshaat Hausa Novel
-
Mahaukaci ko boyayyen masoyi
-
Wuka a makoshi Hausa Novel
-
Aure da haihuwa Hausa Novel
-
Husna Hausa Novel
-
Musayar Zuciya Hausa Novel
-
Gangar Shedan Hausa Novel
-
Angon mata biyu Hausa Novel
-
A gidan mu take Hausa Novel
-
Bafulatanar Rugga Hausa Novel
-
Matar yaro Hausa Novel
-
Mr Bello Hausa Novel
-
Mijin Buzuwa Hausa Novels
-
Gidan Uncle Complete Hausa Novel
-
Yar aiki return Hausa Novel
-
Raggon namiji Hausa Novel
-
Uncle Datti Jikina yake so Hausa Novel
-
Fataucin Mata Hausa Novel
-
Juhud Hausa Novels Complete
-
Moon Hausa Novels Pdf
-
Yarima Ashman Hausa Novel
-
Bandirawo Hausa Novel
-
Matar makaho Hausa Novel
Powered by: www.mynovels.com.ng
Gyefe guda ta juya da idanun ta tana mai bin shanayen ta da kallo , wanda suke garke guda ,don yawon su ya 6aci dai dai yawon garken shanaye amma duka ita ce mai kula dasu a wannan asararen dajin . Babu kowa daga ita sai dabbobinta . Ganin irin goguwar da sanyayyar iskan dake kadawa ne yasa ta bin sararin samaniya da kallo tana kallon yanayin faduwar rana ,wanda ganin yanayin sanyin da rana yayi yasa ta fahimtar cewa lokacin komawan ta Rugar su tayi .
Nufar shanayen tayi hadi da masu magana ta harshen fulani hadi da fara kadasu da sandar ta ,su kuma shanayen suna yin gaba tana mai biye a bayansu a haka har suka fara ficewa daga wannan dajin .
Tafiya ce sukayi ta mai tsawo kamin su fara shiga cikin rugar su ta Surbajo . Nan na fara hango bukka dai_dai bakaman bukkan sauran rugar fulani ba , don idan ka wuce bukka daya sao kayi dan dogon tafiya kamin ka kara saduwa da wani bukkan .
Nikam Maman teddy nace rugar SURBAJO kenan , rugar surbajo ya samu wannan suna ne daga wurin Makotan wannan ruga ,wanda yawon yammatan wannan ruga yasa ake kirar su da sunan Rugar surbajo .
Walijaam Hausa Novel
Yara tun suna da kankantan shekaru basa wuce shekara 7 ko 8 ake aurar dasu ,sai idan sun yi girma akai su dakunan maxajen su ,bikin al’adar su kadai sukeyi masu wato shad’i.
Hakan yasa wannan ruga da akwai yara kanana sosai ga yammata ,amma ko wacce ka gani da Auren ta ,idan kuma babu karama ce wadda bata shekara shida ba tom da akwai wanda yake rikon ta . A takaice dai duk yarinyar da ka gani indai takai shekara 8 tom tana da miji a wannan ruga .
Rugar surbajo rugace da ta tara fulani ,wanda ba mazauna ba ,idan suka tafi kiwon cirani sai sufi shekara goma biyar basu waiwayo rigar surbajo ba . Idan kaga Budurwa ta waiwayo rugar surbajo tarewan tane yayi daga nan sao ayi bikin shadi a kaiki Garken mijinki .
Walijaam Hausa Novel
Duk wacce baayi bikin tarewar taba to tana tafiya yawon cirani wato kiwo da shanayen ta amma su yammatan da suke da Aure shekara daya ce sukeyi wasu ma basa kaiwa suke dawowa rugar su ,a gansu suna yan kwanaki suke kara komawa…wannan dai shine kadan daga cikin Al’adan wannan Ruga . Bari mucigaba da labari WALIJAAM ,komai xamuji daga gaba .
Wannan yarinyan Bafullatanan ce duk wani bukka da zata wuce sai ta tsaya da garken ta ta masu gaisuwa da cewa Ifini jaam kamin ta wuce ,a takaice dai kamin ta isa bukkan su sai da tadan kara tafiya mai tsawo ,amma ahaka kowa ta gani tsakanin ta dashi Ifini jaam , wanda kowa cike da fara’a yake ambaton sunan yarinyar da SHATTU , hakan ne ya tabbatar mun da cewa Wannan ruga ,ruga ce mai hadin kai toh kun kuma san fulani badai hadin kai ba .
Garken ta nufi da shanayen tana kaisu masaukin su ,kamin ta nufi bukkan Mahaifiyarta da ta tadda bata nan a wajen bukkan .
Bukkan ta kutsa kanta hadi da dan dukawa kadan sannan ta shiga daga ciki ,bata tadda Oumman nata ba ne hakan ya tabbatar mata da cewan Oumman tata tayi nisa ,komawa tayi tana rage kayan jikin ta kallabin dake saman kanta hadi da sauke nishin gajiya kamin ta zauna saman tabarman kaban dake bukkan tana magana ita kadai da cewa ” _Aradu hande miwadi kugal misomi”.
( wlh yau nayi aiki nagaji )
Hannun ta takai tana jawo kwaryar da tasha nono ta rage na safe kamin ta fita kiwo ,tana fara sha hankalin ta kwance hadi da lissafin kwanakin da ya rage mata ta tafi ciranin kiwon su da suka saba .da kuma dogon zongon da suke dauka ,duk da a wannan Karon Shatun ita kadai ce xata tafi ba tare da Oumman nata ba .
” Ni uwar teddy na shirya tsaf don kayatar daku a dadadan littafina mai suna a sama kar ku bari ayi baku…wannan dandano ne daga cikin wannan littafin nawa ta Walijaam ,yanayin sharhin ku comment yanayin yanda xana rinka yin update.
Zaune na hangota a gaban mirrow dake makale a bangon dakin nata ,wanda ya kasance ciki daya ne . Amma kayatuwar dakin ba’a mgn ,ka rantse da Allah dakin wata sabuwar Amarya ce “.
Fatima!!
Naji ankirawo sunan wannan budurwan da ashekaru baxata haura 24 ba a haihuwa . Ba tare da ta amsa kirar ba ne naga ta cigaba da bin la66an ta da lipstick tana jagayewa hadi da gyara zaman Zak’o_zak’on Eye lashes din idon ta .
Bin ta da kallo nake hadi da kare mata kallo sosai ,a takaice dai Ita din ba tsayine da ita ba can gajera ce ,amma batayi kasa sosai ba .
Sanye take cikin damammun english wear riga da wando wanda suka dameta matuka na kuma kurewa . Komai na surar jikin ta a bayya ne suke . Saman kanta kuwa gashin kari ne wato atachment mai dauke da kalon kayan jikin ta Wato light pink .
Glass ta daura a saman fuskan ta mai dauke da colourn pink wanda girman shi ya mamaye rabin fuskan ta .
Takalmi ta saka cover sai daga gaba ya bude blue wannan kuma kalon jeans din wandon jikin ta ne wato blue . Karamar jakarta ta dauka da wayar ta kirar iphone tana taunan swingum ta fito daga dakin nata .
Wani irin girgixa nayi da ganin irin gidan da wannan diya take ,dakin nata ka rantse da Allah a gidan wani hamshakin yake ,amma dana fito wajen dakin na biyo bayan ta sai nagan ni a filin tsakar gidan su . Da flour din arxiki babu .
Wata dattijuwar mata ce naga ta fito tana kare maawa diyar nata kallo ,hadi da dan girgixa kai wanda da kagani kasan shigar ta bai mata ba . Fatima tom gyara mayafin don Allah ,ina kirar ki baki amsa mun ba sai da kika gama abun da kikeyi sannan zaki fito .
Ba tare da tayi duba ga mahaifiyar nata ba ,wanda take ta sharce gumin itacen da suke bata wahala don fitowan ta kenan daga madafi .
Takawa Fatima tafara hadi da nufar hanyar da zai sada ta da zauren gidan nasu kamin tace ” Mama sauri nakeyi yanxu inaso na leka gidan Hjy Dr Haulah .
Tana fadi mata hakan tayi ficewar ta da sauri hadi da wani irin tafiya wanda Maman nata kawai girgixa kai tayi ,a zuciyarta tana cewa” tabbas da’alama sojan gidan ne ya dawo ,sai ta kuma ta6e baki hadi da cewa a sarari iska na wahalar da mai kayan kara .
Inbanda hauka irin naki Fatima inake ina wannan yaro ???. Ai komai yanxu wannan yaron kirkin me xaiyi dake fatima? Ai… Haba Mama wai me kika dauke mune? .
Wani irin mgn ce wannan shi Umar Farouq din ba mutum bane ,kodon yana soja kuma Mahafin shi shine Jurnalist Bashir Mahafiyar shi Hjiya Dr Haula?? Shikenan sai kice fatee batakai matsayin da zai kaunace taba ? Yanda fah kk kallon mu a gida a waje ba haka muke ba .
Asma’u ce ta katse mahaifiyar tasu da sam basa ganin kimarta da girman ta idon su na duniya da kwadayin abun dake cikin ta .
Cigaba da cewa tayi kene kk mawa Liftanal yake ko major ne Umar farouq dai na gidan nake magana ke kike masa kallon mutumin kirki ,amma fasadin da yake a bayan kasa walh gomma wani mazinacin dashi don bambancin su kadan ne! . Kawai don mahaifin sa ne da ya zama mai zafi da jajircewa akan Omar wlh da mazinaci yafishi tafka abun arxiki .
Subhanallahi!!
Futucin da ya fito daga bakin Mama kenan ta fadi da sauri jin irin wannan kalamina Asma’u . Wannan wacce irin mgna ce Asma’u?. Toh wlh ni koya ma dai yake wannan yaron yafi mun ku ,tun da har yanada wanda yake tsawatar masa ya tsawatu ba irin ku ba yan kanku …Kullum dai ina maku fatan shiriya mtswww mama ta karke maganan tana mai jan dogon tsaki hadi da wuce Asma’au da ta kasance Yaya ce Wurin fatima .
Ta6e baki Asma’u tayi ba tare da ta damu da damuwar mahaifiyar nata ba sai ma cewa tayi “,tom idan bamuyi gayu mun fita ba ,so kk mu zauna kullum bamu da abun ci sai tuwo ?? Tuwon bama ta masara ba aa ta dawa?? Ina ?! Wlh ni har kunyar kawo samari na nake wannan gidan jar kasan ,duk yanda nake flexcing wai azo ace nan ne gidan mahaifina ai abun da kunya ina xan iya ,shiyasa muke haduwa a waje baazo ba bare ma wannan gida yakorar mun Alhjazai da samari .
Gwamma mu fita mu saka sutura cikin rufin asiri a cigabada mana kallon silent ajebourters.
A hankali Shattu ta dago ido tana kallon mahaifiyar nata kamin cike da damuwan tafiyar da zatayi ta bar umman nata ta ce” Oumma kinsan gobe xan tafi kiwo xanyi tafiya mai tsawo kamin na dawo rugar surbajo ,ina bukatan addu’ar ki ,kin san da Yagwalgwal xamu tafi.
Tom Shattu allah yakaiku inda xaku lfy ,ku dawo lfy a kullum addu’a na kenan gareki ,sai dai banason kiyi dadewa kar ki wuce Watanni bakwai baki dawo ba duk inda ko xaki je .
Murmushi shattun tayi wanda har sai da gyefe da gyefen kuncinta suka lo6a kamin tace tom Oumma inshaallh baxan wuce ba.
“Yowa diyar Albarka Allah yy mawa rayuwar ki Albarka ya karemun ke daga dukkan wani sharri Amin”.
” Oumma ina Abba yake yakamata muyi sallama kamin mu tafi rabona da ganin shi tun jiya…
Ai kin san yana can rumfar da yake sana’ar aa .
A hankali Shattun ta mike daga tsaye hadi da cewa “Umma bari na leka rumfar Abba na gaida shi ba lalalli mu hadu ba gobe ,bari na tafi yanxu nasan mutane sunyi masa sauki yanxu.
Abunka ga fulani da kuma ita Shattun da take ganin ita din yarinya ce karama a haka ba mayafi daga ita sai sandarta da yake wurin ta tun yarinta kafanta babu ko takalmi ta bar garken nasu don nufar inda Mahaifin nata ke Bada magani .
Don Mahaifin ta wato Malam Bukar Shaharren malami ne a wannan ruga tasu ,sosai yake bada taimakon maganin sa ta gargajiya ,yana bada magani ta fanni dabam dabam …shiyasa mutane ta koina suke zuwa wannan ruga ta Surbajo . Kullum baka ganin sa ba tare da jaama’a ba .
Itakan ta Shattun sai tayi kwana biyu uku basu hadu ba!!
Tom mu tare a page na gaba na WALIJAAM.
Masoyan taurari uku nasan tambayoyin dake tare daku duka , mun dakata da yin taurari sai a zongo na gaba zuwa march haka ,nima naso na dakata da wannan littafi nawa ta WALIJAAM ,tom amma duba ga masoyan labarin da kuma korafin ku akan cewa nayi maku saboda wasun ku da suka fara biyan wannan labari nawa , hakan yasani kar6ar korafi akan xan saki wannan littafi nawa ,a taurari na gaba zan sakar maku da sabon littafina wanda shima nasan xaku so shi kaman yanda kuka nuna kaunar ku a wannan littafin WALIJAAM.
Name: | [ ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Thanks dear
Please complete
Comp
Pls cmplt
Pls complete