Wani Zama Hausa Novel Complete

hotunan bikin ummi rahab

Wani Zama Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: WANI ZAMA*

🌺🌺🌺🌺🌺

 

©Maryam Abdullahi(OumRamadan)

 

 

 

*01*

 

 

*Bismillahir-rahmanirraheem*

 

*FREE BOOK*

 

Cikin nutsuwa ya kammala d’aura tsadaddan agogon azurfarsa da yake kyalli, waiwayawa yay ya kalli matarsa dake nad’e akan gadon bedroom d’in ta lullu6e jikinta da wani lallausan bargo sakamkon sanyin da ake ga kuma AC da take aiki a bedroom d’in,

K’arasawa yay kan gadon ya d’an bubbuga filon da take kai , ta bud’e lumsanssun idanunta tana kallan mijin nata ta 6ata fuska a shagwabe tace “meye haka dear”

Nuna mata agogo yay batare da yay magana ba , ta sake gyara kwanciyar ta tace “yau ba inda zani, na rigada nayi report , ” daga haka ta sake komawa tai kwanciyar ta, sai sannan ya bud’e baki yace “ko shayi bazan samu ba?” Ta sake 6ata fuska tace “Dan Allah dear ka barni nai barcinnan, jiyafa kasan tun daga abuja har nan a mota nazo sbd lattin danai har flight d’in ya tashi , shayi kuma tuni nasan me aiki ta jera a dinning ai , ”

Juyawa yay ba tare da ya sake magana ba yad’au jakar laptop d’insa ya fice daga parlon, inda motarsa take a parking ya nufa ya tayar kai tsaye ya wuce gidansu duk kuwa da lattin da yay shima dan yanzu kusan tara kenan bai k’arasa office ba,

 

“Suhanah!”

wata mata da batafi shekara arba,in a duniyaba ta kwallawa warce take kwance akan dadduma kira ,tana tsaye bakin kitchen hannunta rike da warmer me kyau tace “Wai suhanah bakya jinane?”

Warce take kwance akan daddumar ta d’ago da manyan idanunta da suka k’ara girma , tana kallan matar da bazata taba tunanin takai shekara 40 a duniyaba sbd kyan jikinta , ta turo baki tace “inajinki ammi”

Hararta matar data kira ammi tai tace “wato tsabar iya shegene yasa nake kiranki kinyi mukus ko?” Suhanah ta marairaice fuska tace “Allah ammi wani daddad’an barcine yake nema ya kamani” ammi ta tabe baki tace “toh yayi kyau , yaushe garin ya waye dahar zaki koma barci? Yanzu fa k’arfe goma tai, Tashi ki kaiwa hajiya alalan nan tun kafin ta huce ” dakyar suhanah ta mike tana tura d’an k’aramin bakinta tace “toh ammi”

Daga haka ta juya ta wuce bedroom d’inta ta d’akko hijab dinta tasa ta fito, ta karbi warmer d’in ammi tace “kice ina gaisheta ” tuni tai hanyar get d’in gidan tace “toh” daga haka ta fice daga gidan,

Tafiyar minti biyar tai ta isa k’ofar wani babban gida hadad’d’e , ta kwankwasa k’ofar me gadi ya leko da Kansa , yana ganinta ya washe baki ta d’an rusuna tace “ina kwana baba” yana murmushi yace “lfy lau yata ,ya mahaifiyar taki?” “Lfy lau” ta bashi amsa kafin ta wuce ciki ,cikin second biyar ta k’arewa motocin dake fake a parking space da kallo kafin ta tabe baki ta k’arasa k’ofar parloun gidan ta kwankwasa, me aikice ta bude mata k’ofar ta suka gaisa ta tambayeta hajiya , me aikin ta sanar mata ta tashi tana dining , da sallama ta shige katafaran parlourn da aka narka uwar dukiya a ciki,

Matar dake zaune a dining ta saki murmushi tana kallan Suhanah , har dining d’in ta Karasa tana gulmar matar a zuciyarta sbd iya d’aukar wankan matar , duk kuwa da shekarunta sunkai hamsin da uku, saidai hutu da jin dadi da kuma kula da jiki daya boye shekarun tace “Ina kwana Umma?” Murmushi matar da aka kira Umma tai tace “lfy lau suhana ,ya hajiya Rukayya?” Ta ajiye warmer din dake hannunta tace “lfy lau, gashi tace a kawo miki” Umma ta d’au flask d’in ta bude , tuni daddadan kamshin alalan datasha kifi da kwai ta bugi hancinta , kallan suhana tai data sunkuyar dakai tace “gsky hajiya rukayya ta kyauta , nakuwa gode sosai ” murmushi suhanah tai tana wasa da zoben hannunta , tana kallo Umman ta d’au plate ta zuba alalan guda biyu sannan ta kalli suhanah tace “toh zauna muyi breakfast d’in tare” girgiza kai tai tace “na koshi Umma” Umma tace “yaufa sai kinci, ina sane dake bakya son ko zamane a gidannan baran tana kici abinci , nimafa mamankice , kodai halin naku zaki nunamin na fulanawa?” Murmushi tai tace “Allah Umma nima ban dade da breakfast ba ” Umma tace “to yayi kyau, zauna inaci kinamin hira da labarin saurayinki” rufe fuska suhanah tai ta zauna tana yar dariya ,

Kamshin wani daddad’an turarene ya doki hancinta , ta lumshe ido tana sake baza dogon hancinta kafin ta juyo sallama can k’asan makoshi , Umma ta d’aga kanta ta kalli wanda ya shigo ta amsa sallaman ta cigaba da cin abincinta,

A nutse ya karaso dinning d’in, yana sanye da suite da suka amshesa sosai ya russuna yace “barka da safiya Umma , na sameki lfy?” Umna tace “lfy lau Awwab ,ya aikin?”

Saida ya zauna kan kujerar dining d’in yace “Alhamdulilah” Umma tace “to masha Allah” suhana da tunda ya shigo ta sunkuyar da kanta bata sake d’agowa , dan haka kurum Allah ya d’ora mata tsoron Awwab a ranta , duk ta ganshi sai ta dingajin gabanta na fad’uwa tunda ta girma ta mallaki hankalin kanta kuwa , gefe d’aya kuma tana masa kallan mutum da baida fara,a ko kad’an da rashin sabo ba kamar Umman da sauran yaranta ba , Umma ta katse mata tunanin da take tace “Suhanah bakiga yayanki bane?”

Firgigit tai a miskilance tace “ina kwana” tana fad’a ta tsuke baki ta had’e fuska , can kasan mak’oshi Awwab yace “lfy lau” , suhana ta ta6e baki dan ita kanta badaban Allah yayita me ji sosai ba ba lallai ta jiyo ba ,

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
Mikewa tai tace “Umma sai anjima ” Umma tace ” zauna ban gama dakeba , ” ta marairaice fuska tace “to bari na koma parlour na jiraki Umma” murmushi Umma tai , tuni suhanah ta koma parlour ta zauna ,

“saleemar ta dawone?” Umma tace bayan Awwab ya kammala cin abinci, “ta dawo jiya” ya bata amsa kamar Wanda baison magana , Umma ta tabe baki tace “to Allah ya kyauta, Allah kuma ya basa lfy, in hajiyar Tata ta dawo nakirata ” baice komai ba ya mike yace “sai anjima Umma” Umma tace to mujima da yawa, Allah ya tsare ” akan labbansa ya amsa ya fice daga parloun,

Kai tsaye bedroom d’inta ta wuce bata jimaba ta fito hannunta rik’e da jaka , ta same suhana akan kujera ta zauna tace “to ga tukwicin alala nan , ki fad’awa hajiya Saturday zaki rakani unguwa , amma zan kirata da kaina ma kawai” Kar6a tai tace “to Umma ,nagode sai anjima” Umma tace “harira zata kawo flask din anjima” gyad’a kai tai ta sake mata sallama da godiya ta wuce.

Aminace ta fito hannunta rike da flask din tea da cups ta ajiye akan carpet, dayan bedroom d’in dake cikin parloun ta shiga , ta tadda ‘yarta mufyda ta shirya kanwarta muhibba , murmushi ta sakarwa yaran nata tace “to maza a fito a asha tea kun kusa makara” muhibba ta turo baki tace “yauma tea mummy” amina tai murmushi mufyda tace “wlh mummy na gaji dashan tea ” amina ta rasa yadda zatai da yaran, dakyar ta lallabasu suka fito parlon ta ba kowa bread din sa ta had’a musu tea kowa a cup dinsa,

Habeeb ne ya fito cikin shirinsa na danyar shadda kana kallanta kasan tsadaddiyace sai kamshi yake , muhibba ta mike ta rumgumesa tace “daddy” ba wani sakin fuska sosai ya shafa kanta kafin ya zauna d’aya daga cikin kujerun parlon mufyda ta d’an rusuna fuska d’aure ta gaishe shi , bai kula da yanayin taba ya amsa amina tace “Abban mufyda a had’a maka tea din?” Girgiza kai yay yace “sauri nake ” amina tai wani murmushi kana kallo kasan na takaicine tace “toh” mikewa yay ya shiga store ya fiddo mukulli ya bude k’ofar , ya bude buhun shinkafa ya auno gwangwani uku, ya dakko taliya d’aya ya dora akan shinkafar, ya debo magi guda goma sai mai gwangwani d’aya a cup ya fito ya ajiye gaban amina , ya fiddo dari biyu daga cikin aljihunsa ya d’ora akan abincin ya kalli su mufyda yace “kuyi sauri ku gama fita nakeson yi” mikewa sukai tuni mufyda tai gaba fuska a bala,in had’e ya bita da wani kallo , ya kama hanun muhibba da take ta basa labarin yan ajinsu ana zuwa musu da take way mkrn bandasu yay mata banza , amina ta bisa da kallo ranta na tafarfara ta d’aure tace “A ado lfy ,Allah y tsare” can ciki ya amsa ya fice , saida ya fara ajiye yaran a mkrn sannan ya karya kwana, habeeb bai zame ko inaba sai wani restaurant da ake abinci kala kala na yan gayu yay parking ya shige wajen yana kad’a mukullin motarsa,

A compound d’in gidan suhana ta tadda Awwab yana waya ta watsawa bayansa harara ta wuce , ta gefen Ido ya d’an kalleta yaci gaba da wayarsa.

*Oum Ramadan*💥 08107942566

 

*WANI ZAMA*

 

 

 

©Maryam Abdullahi(OumRamadan)

 

 

 

*02*

 

 

 

 

A parlour Suhanah ta tadda ammi tana goge kayan yusuf kaninta , zama tai akan carpet ta tura mata ledar tace “gashi tace a kawo” ammi ta harareta tace “ni aka bawa?” Dariya Suhana tai ta d’auke ledar , ammi tace “zoki karasawa yusuf gugar nan , 11 tayi a dora abinci kar acici ya dawo ya ishi mutane” Suhana tace “baki ajiye masa alalar ba?” Ammi tace “bayan warce yaci saina ajiye masa wata sbd salubabbiyace ni?” Murmushi tai tace “yau munga yusuf da ammi a rana” itama tai murmushi tace “anjima zaki gammu a Inuwa ,yar sa ido kawai” dariya Suhanah tai tace “eh na yarda ammi”

Ficewa ammi tai d’ora abincin rana, Suhana kuma ta cigaba da gugar , tana kammalawa ta bi Ammin nata kitchen ta kama mata aikin, sunayi suna hirarsu har suka kammala farar shinkafa da stew , sai salad da cucumber da suhana ta yanka ammi tabar mata kitchen d’in ta gyara komai tass , tuni ya dawo kamar ba,ai komai a ciki ba,

Tana fitowa yusuf ya turo get d’in gidan da sallama kamar zai kuka , tabe baki Suhana tai ta amsa tace “kuka zakai yusuf?” Kamar zai kuka yace “dakyar na d’aure banyiba adda suhanah, ke kinji rana kuwa? Ni kamar ba yan hanji a cikina nakeji wllh”

Hararsa tai tace “kuma gashi ka makaro , ko d’ora abincin ma ba,ai ba” zama yay akan kujerar tsakar gidan ya dangwarar da jakarsa ya sake marairaice fuska yace “cene Allah adda” ta d’auke kai sbd kartai dariya tace “saina rantse zaka yadda yusuf?” Ammi ta fito ta jefa mata biron dake hannunta , sai sannan dariya ta kwacewa suhana , ammi tace “rabu da ita auta, wanka kawai zakai abincinka yanan yana jiranka” mikewa yay yace “wllh ammi dakyar in zan iya wanka banci abinci ba, nifa yau kamar banci komai ba na fita” Suhana tace “kaidai ka rage ci wllhy , ina kaje abinci , ina zaka abinci?” Ya had’e rai ya kalli ammi yace “kina jinta ko ammi” ammi tace “rabu da ita, lfy ce ta wadaceka , kaida kakejin yunwa ina zaka tsaya kula warce sai anyi da ita ta nemi abinda zata sawa cikinta” wucewa yusuf yay bandaki , Suhana kuma ta zuba masa rice and stew d’in da nama yanka hudu akai ,

Karfe 2:30 suhana ta fito daga bedroom d’inta sanye da gogaggen Hijab kalar sky blue Wanda yakai mata har k’asa, ta wuce bedroom d’in ammi tace “zamu tafi makaranta ammi” ammi tace “toh Allah ya tsare , karki manta da addu,ar fita ” “insha Allah ammi” suhana tace sannan ta wuce , yusuf yana tsaye shima sanye da uniform d’insa na islamiyya kalar sky blue a tsakar gida , yana ganin suhanah suka rankaya bayan sunyi addu,ar fita zuwa islamiyyar dake can kasan layinsu.

Karfe 6 suka dawo ,motar da suka gani a d’an madaidaicin compound d’in gidan ya tabbatar musu da abbansu ya dawo ,

Saida sukai sallama da kusan minti 2 sannan suka kutsa kai cikin parloun da yake ta tashin kamshin turaran wuta , da gudu yusuf ya d’ane cinyar Abban nasu yace “sannu da zuwa Abba” Abba ya shafa Kansa yace “yaww my friend, ya mkrnt?” Daidai sanda Suhana ta karaso tace ” Abba sannu da zuwa” yace “yawwa daughter, ” ta narke fuska tace “Abba wllh nagaji” murmushi yay yace “to yi wanka ammi tai miki tausa ko?” Ammi da take gefe taci kwalliya tana kallansa tace ” tausa? Ita suhanar zanwa tausa yalla6ai?” Abba yace “to duka nawa take madam? Yarinya dai ta gaji tana bukatar tausa” dariya Yusuf da suhanah sukai ammi ta ta6e baki tace “aa badani ba wannan abun kunyar, har kullum kallar yarinya kakewa suhanah ,yarinyar da ta gama secondary aita wuce ace mata yarinya” suhanah ta marairaice fuska tace “Allah ni yarinyace ammi ” ammi ta tabe baki tace “to sannu jinjira” yusuf ya fashe da dariya yace “Allah adda bazaki dadin daukaba inke jinjirace ” hararsa tai Abba yace “toh ya isa haka, kuje Ku cire uniform d’inku Ku huta kafin magriba tai” mikewa sukai ko wanne ya nufi d’akinsa , bayan sallar ishai lokacin Abba da yusuf sun dawo daga masallaci ammi tana zaune bayan ta idar da sallah suhanah ta shimfida leda akan carpet d’in parloun , ta jera abinci akai da cups sai plates, tuni Yusuf ya zauna ammi ta mike ta kira Abba tare suka fito , ko wanne ya zauna ammi ta d’auki babban faranti ta zuba lafiyayyar jallop d’in spaghetti da wake da allayu da kifi sai Kamshi take , suhanah kuma ta zubawa kowa tsobon da aka had’a da abarba da cucumber a cup ta ajiye , Abba ne ya fara bismilla yasa cokali sai ammi, sannan suhanah da Yusuf,

Tare suka kallama cin abincin, suhana ta tattare duk abinda akai amfani dashi takai kitchen ta gyara wajen tass ta zauna ta kalli abbanta da yake canza channel tace “Abba next week wai result d’in neco d’inmu zai fito” Abba yace “Allah ya kaimu lkcn sai muje a duba” “Amin suhanah tace sannan taiwa iyayanta saida safe,

Washe gari Karfe takwas ammi ta gama shirinta ta kalli suhana tace “yau zan koma aiki , ki kula da kanki kinji, kuma ki tabbatar kin gama abincin rana kafin Yusuf ya dawo ” suhana tace “to ammi sai kin dawo” ta kalli Abban nasu daya gama kintsawa shima tace “A dawo lfy Abba” Abba yace “Allah yasa daughter ,” daga haka ammi ta shiga gaban motar Abba suka fice ammi ta wuce makarantar da take koyarwa Abba ya wuce wajen aikin sa shima,

Washe gari har Awwab ya gama shirinsa cikin suit da sukai mugun masa kyau baiga keyar saleema ba , briefcase d’insa ya d’auka ya fice daga bedroom d’in nasa ya sakko downstairs, a dining ya tadda salima tana sipping tea, tayi shirinta tsaf cikin suit ta mata riga da sket, sai dan baby hijab din da tasa a sama, tana ganinsa ta saki murmushi tace “good morning my barrister” ba tare daya kalletaba yace “morning” ta ajiye cup d’in tean da take kurba ta karasa wajensa ta sumbaci kuncinsa tace “am sorry my Barrister , jiya wani aikine ya tsayar dani wllh a daki, bansan sanda barci ya d’aukeni ba, kasan tafiyar danai Abuja nabar aiki sosai , shiyasa dana dawo kawai nai wasu kafin na wuce office , na tara ayyuka sosai wlh wai yar tafiyar nan kawai danai , bakaji yanda nake jiba toh ban sababa ,” Awwab ya daga kansa yana kallanta da idanunsa dake cike da takaici da bacin rai kafin ya gyada kai yace “hakan yayi kyau ai”.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.