Addini Nasiha

Wankan Janaba Yanda ake wankan Janaba da rabe rabensa

Wankan Janaba Yanda ake wankan Janaba da rabe rabensa

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tag: Wankan Janaba Yanda ake wankan Janaba da rabe rabensa

Wankan Janaba((الغسل الجنابة)),a Musulunci shi dai wankan Janaba ba kamar wankan da muke yi ba ne na yau da kullun ba, shi yana da ka’idoji da yadda ake yin shi kamar yadda ya zo a littafan addinin Musulunci, kamar su Fiqhu da dai sauran su.

Wankan janaba

GA YADDA AKE YIN SHI A MUSULUNCI

 

Da farko dai mutum zai yi niyya, niyya kuwa tana

farawa ne tun daga sanda ka dauki ruwanka mai Tsarki.

 

Sannan zaka sami ruwa mai

tsarki, idan abin da ruwan ya ke a ciki mai budadden baki ne sai a ajiye shi a bangaren hannun dama, idan kuma mai rufaffen baki ne sai a sashi a hannun hagu(kamar buta).

 

Sai a fara da sunan Allah

wato BISMILLAH (amma a zuci, saboda ba a ambaton sunan Allah a yayin da ake cikin bandaki). Sannan a wanke hannu kafin a fara komai sau uku (3)

 

Sannan yana da kyau a sake

yin niyya ace”Nayi niyyar yin wankan janaba, Farilla, domin na gusar da babbar dauda(نويت غسل الجنابة فرض رفع الحدث أكبر).” (ita ma niyyar a zuci. Idan ma ba a fada ba, ba laifi, don niyya tana farawa tun daga sanda aka dauki abin wankan, buta ko bokiti da sauransu).

 

Sannan sai ayi tsarki (da

wankewar gaba da kuma kewayensa). Bayan wannan sai ayi alwala shudi dai-dai, idan an gama ana iya jinkirta wankin kafafu sai a karshen wanka. (amma malamai sun ce an hana barin sunnah a cikin yin wanka, barin sunnah makaruhi ne, an qishi, ana so musulmi ya yi wanka cikakke tare da farillan wanka da kuma sunnonshi).

Kun ga kenan alwalar mu zamu yi ta ne cikakkiya kamar zamu yi Sallah.

 

Sai mutum ya hada hannuwansa ya nutsar da su a cikin ruwun wanka, sai ya fito da su ya kakkabe sannan ya shafa kansa gami da murzawa har sau uku zayyi hakan idan ruwan a bokiti ne in kuma a buta ne sai zuba

Sannan a wanke kai sau

uku, za a shigar har da wuya a wankin kai, da wankin kunnuwa ciki da waje, mace kuma zata zuba ruwa a cikin gashinta ta bubbuga sai ruwan ya shiga ciki sosai. Amma idan tana da larura to anso ta shafa kanta sau ukun ko ina da ina.

 

Sannan a wanke tsagin jiki

na dama tun daga kafada har zuwa kafa, sannan a wanke tsagin jiki na hagu shima tun daga kafada har kafa. a cuccuda sosai da sosai.

 

Sannan sai a game jiki da ruwa duka.

TUNATARWA

 

Ana so ko ina ya shafi ruwa kamar su matsematsin cinyoyi,da kuma kwarin cibiya duk a tabbatar an cudasu da kyau.Sannan a kula kada a shafi Al’aura don kada alwalar ta karye,(idan ana nufin yin amfani da ita). Domin za’a iyayin Sallah da wannan Alwalar da aka yi wanka da ita, sallah ta inganta.Amma idan bayan wankan aka taba al’aura to sai an sake alwala. Domin shafar farji ko gaba na warware alwalar wanka.

 

KAMMALAWA

A yi kokari a kiyaye da barin lam’a wato shi ne wani dan karamin wuri a jiki wanda zai zama ruwa bai shafe shi ba, sai a kiyaye. Wankan Janaba ya kammala.

 

Karin bayani akan wankan Janaba

*YADDA AKE WANKAN JANABA, HAILA, BIKI DA*

*SAURANSU*

 

Daga: Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam

[Rahimahullah].

 

(Malam ya yi wannan bayanin ne a Tafsirin

Maiduguri na shekarar 2006M a cikin Suratut-

Taubah aya ta 100)

“Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai

‘siffatul ijza’ (ta wadatar), kuma wacce ake kira

‘siffatu kamal’ (ta kamala).

.

.

*Wankan Janaba a siffar sa ta kamala* shi ne:

Idan ka zo za ka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a

gabanka. Farkon abin da za ka fara yi shi ne:

Za ka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke

hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a

cikin ruwan sai ka debo ka wanke gabanka, a

dai-dai lokacin da za ka wanke gabanka a lokacin

za ka kulla niyya ta wankan Janaba (Ko

waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke

gabanka ma’ana ka yi tsarki kenan, to daga nan

kuma sai ka yi alwala irin yanda kake alwala ta

sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah za

kayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan

za ka kyale shi ba za kayi shi ba, to daga nan sai

ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba

tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka

saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da

maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma

yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude

musammam gashin sa na ka, idan ka zuba ruwa

a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani

abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin

tafin hannunka daya sai ka zuba a kanka ka

tabbatar ya game ko ina a kanka, ka sake

kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko ina a

kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko ina a kanka.

 

To idan ka yi wannan sai ka debi ruwa ka game

dukkanin jikinka da shi kana mai farawa da

bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan

na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko ina. To idan

ka yi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi

ne sai ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka

ta hagu shi ne cikon alwalar da ka riga ka faro.

Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan Janaba.

 

 

In wankan Janaba ne haka za ka yi, in na Haila

ne haka za a yi in ma wanka ne na Biki haka

mace za ta yi, idan wankan Jumu’a ne ma haka

za a yi, wankan Idi ma haka za ka yi, banbanci

kawai shi ne NIYYA.

 

 

*Idan mutum zai yi siffa ta ‘Al ijza’* wadda ta

wadatar ba sai ka yi alawa a cikin ta ba, kana

zuwa ka yi niyyar yin wanka din kawai sai ka

dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko’ina,

in ma wani kududdufi ne ko rami ko “swimming

pool” sai ka yi tsalle ka fada a ciki, dama ka kulla

niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da zaka yi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki dakuma shaka ruwa a hanci da fyacewa. Shi kenan,

kuma ya halatta ka yi sallah da wannan wankan,

Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.

Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fi ka

kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fi ka cikar kamala, ya fi ka lada.

 

Karanta Tarihin Annnabi Muhammad

Kasancewar ba a yi alwala ba ciki, wannan ka’ida

ce ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL

ASGAR) idan sun hadu da babban kari

(HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da babban

kari, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai bane

idan ka kawar da karamin a ce babban ma ya

tafi.”

 

Karin wasu bayanai akan wankan Janaba

YADDA AKE WANKAN JANABA,HAILA, BIKI DADAI SAURAN SU. Wankan Janaba yana da siffa guda biyu kawai

1: SIFATUL KHAMAL (siffar wanka ta kamala) 2) SIFATUL IJZAH

(sifar wanka wacca ta isar)

*1Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka. Farkon abin da zaka fara yi shi ne: zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka {azzakari/farji} a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne, idan ka wanke gabanka ma’ana kayi tsarki kenan to daga nan kuma sai kayi alwala irin yanda kake alwala ta sallah, abin da duk kake yi a alwala ta sallah zakayi sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, har sai ka gama wankan sai ka koma gefe ka wanke{kafafun} Daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowace kofar gashi da ta bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ta rufe yanda yake, don kofar gashin dan Adam takan bude musammam gashin sa na ka, idan ya zuba ruwa a haka na iya haifar masa da ciwon kai ko wani abu daban. , Bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko’ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko’ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko’ina a kanka. To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko’ina. To idan kayi wannan shikenan ka kammala, Abu na karshe shi ne sai ka wanke kafarka ta dama sannan kafarka ta hagu shine cikon alwalar da ka riga ka faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba. In wankan janaba ne haka zakayi, in na haila ne haka za’ayi inma wanka ne na biki haka mace zata yi, idan wankan jumu’a ne ma haka za’ayi, wankan idi ma haka zaka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA. Idan mutum zai yi siffa ta

*2 ‘Al ijza’ { siffar wankan wadda ita ma ta isar} to ba sai kayi ALWALA acikin ta ba, kana zuwa kayi niyyar yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko’ina, inma wani Kududdufi, ne ko Rami ko Swimming Pool sai kayi tsalle ka fada aciki, dama ka kulla niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da zakayi shi ne abubuwa guda biyu, KURKURE BAKI da kuma SHAKA RUWA DA FACEWA Shike nan, Kuma ya halatta kayi Sallah da wannan Wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka. Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fika kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika cikar kamala, ya fika lada. Kasancewar ba’ayin alwala ba ciki, wannan ka’idace ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL ASGAR) idan sun hadu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to idan ka kawar da babban karin, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai bane idan ka kawar da karamin karin ace babban ma ya tafi.

Leave a Comment

error: Content is protected !!