Hausa Novels

Wasu Matan Hausa Novel

Wasu Matan Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

Da Sunan Allah mai rahama mai jinkai

 

Allah yai dadin tsira ga Annabinmu Muhammad Sallahu Alaihi Wasallam da Ahalinsa tareda Sahabbansa baki daya

Ina rokon Allah Mabuwayi Gagara misali yadda ya bani ikon fara wannan littafi mai albarka ya gwadamin na gamashi lapiya Allah yasa kasa Al’ummar musulmii su amfana da da russa na kwarai dake cikin wannan littafi kuma in akwai mai irin wadannan halayyan Allah yasa ta daina Ina ma masoyana fata Alkhairi a ko ina suke.

 

*page* 1~~2

 

Zaune take bisa tabarma tana tsintar shinkafar hausa tana sauraron wakar hamisu breaker, a gidan redio da yar karamar salularta. Akalla baza ta wuce shekara talatin da takwass ko Arba’in ba sai mita take yi “ohni saudatu ni wlh na gaji da wannan rayuwa a ce ko yar shinkafar ga ta gwamnatii dai mallam ya sayo mana mu tuka amma yakiya a’a, ko da yaushe sai dai yace babu babu kamar kansa a ka fara talauci ko wurin abokanansan nan yaje ya aro koda bashine dai ya sayo muci kamar yadda su laure kayi, amma sai dai yace Ayi hakuri wata rana sai labari ni gsky na gaji da hakurin nan mssssstwwwwwssss”.

 

Ta k’arashe maganar tana jan dogon tsaki. Alokacin da aka turo kyauren gidan tare da sallama ciki ciki inna saude ta amsa sallamar yayin da naga wata mata shiyar budurwa wadda ba za ta wuce shekara goma sha bakwai ba ta fito a cikin wani dan madai dai cin daki sanye da wata kodaddiyar atamfa, ta yo wurin wannan mutunen da ya shigo wanda akalla zai kai shekara hamsin amma idan ka kalleshi so daya baza kace yakai hakan ba domin irin jikin fulani ne dashi daka gansa zakace tabbass bafulata ni ne ta durkusa tace “bappa sannu da zuwa ya kasuwa?”. Dadai lokacin da yazauna bisa tabarmar tare da amsa mata da cewa “yawwa mamana da fatan na same ku lapiya”. Tace “lpy lau baffah”.

 

Yayin da ta tashi ta nufi wurin tulun su ta kawo mai ruwa mai sanyi, ya karb’i ruwan yace” nagode mamana Allah ya miki Albarka”. “Ameen Baffana”. Ta fad’a tana murmushi.

 

Bayan ya gama shan ruwan ne yace “Hala ina auta naga bangan ta ba”. wannan yarinyar da ya kira da mamana tace “inna ce ta aiketa gidan su inna laure ta anso mata kuka”. yace “tou”. tare da nufar dakinsa a yayin da ko kallo bai ishe inna saude ba balle ai maganar gaisuwa dan haushinsama take jii yanxu shiya takasa yi masa magana yau kenan ko naman dari biyun bai riko asa a miyaa ba

 

Guduu kawai yake a mota da’alama sauri yake domin gudu yake shararawa a bisa titi Allah ne kawai yakai shi gida lapiya domin yayi mantuwan wasu files a gida gashi kuma urgently ake bukatarsu yana isa bakin wani makeken gate yai parking ko motar bai shiga da ita cikin gidan ba ya bude marfin motar ya zuro kafafunsa waje da dan sauri sauri mashaallh shine abunda nace a lokacin da nai tazalii da kyakkyawar fuskar sa ma’abociya haiba da kamala matashin saurayi kenan maiji da kyau da kudii Aliyu muhammad Ahmad da daya tilo ga Alhj muhammad Ahmad mai xinaree Shahararren mai kudin da yayi suna a fadin nigeria yana da companies a garuruwa da dama za kujii cikaken labarinai nan gaba Noking din gate din yayi Ila mai gadi ya bude ya shiga ko saya amsa sallamar mai gadii bai yiba yai cikin gidan direct da sallama ya shiga cikin palon da sallama kamar yadda yasani haknne ko a yanxun zune take bisa kujerun da suka kawata dakin tana charting a wayar ta kirar iphone 12plus karar takalmi da tajine alamun an shigo yasa ta dago kanta tare da daga yan yasunta tayi waving dine maana hiiii taci gaba charting dinta bai kulata ba dan inda sabo yaci a ce yasaba da halin suhailat direct uptchers ya nufa tareda shiga room dinsa after 3mint ya fito tare da files din ya fita ko adawo lpy bata masa ba gaba daya ma bata san ma ya fito ba yaja motarsa tare da nufar A.M.A COMPANY .

 

2 Comments

Leave a Comment

error: Content is protected !!