Wata Amarya Complete Hausa Novel
Tag: Wata amarya
Littafina wata amarya hmmm bazan ce komai ba kedai biyo ni kawai.
Yau ta kasance Monday kamar kullum fitowa sukayi daga lecture da suka Shiga 12-pm na Gse daga hall din zasu cafeteria domin wani yunwa ce ke kwakular hanjin cikinsu har ya Kai ga dishi dishi take gani ga wani bugawa da kanta keyi
Kallonta yasira tayi tace”Rumsisa da alamu yau kin galab’aita na gan Baki magana”
Ajiyar zuciya ta sauke ba tare da tayi magana ba domin ita kadai tasan me take ji
Chika resturant staff din resturant din ta tambayesu me za a kawo musu
Da kyar ta bude bakinta tace”white rice no extra meat ,”
Yasira tace’ni ab’u zanci with mix soup”
Ba a Jima ba aka kawo musu abinci babu b’ata lokaci suka Fara ci dukda tana Jin yunwa a natse take cin abinci.
Yadda Amarya Zatayi a daren farko
Wani Gaye ne ya shigo da yan Mata uku suka zauna dan nesa dasu kallo daya zaka Masa kasan ba student bane irin manyan samarin Nan ne masu shigowa jami’a suna niman Mata.
D’ayen shadda ce jikinsa Mai kyau da tsada gashi Yana Zama kamshi restaurant din ya sauya daga domin tuleraisa ya danne na kowa harda kamshin abincin nasu dake tashi hakan yasa idanuwa Suka Koma kansa.
Manyan wayoyinsa guda biyu ya Ciro ya ajiye a saman tebu
Toh shifa ya Saba duk inda ya Shiga in akwai Mata sai sun bar abinda suke sun kallesa saboda kyau ne dashi ta bugawa a jarida
Ko anan dinma haka’ ne ta faru Banda Rumaisa da ko kallo inda yake batayi ba Kai tamkar ma Bata San da hallita ba a wurin saima d’aure fuska da tayi Wanda har ga Allah haka’ rayuwarta take Bata Shiga harka wani Bata son a Shiga nata
Yasira ko ta kalleshi sai dai itama kallo biyu tayi me ta d’auke Kai
Anyi serving dinsu abinda suke so sai’dai fa ya kasa ci Yana mamakin yariyar me son breaking record dinshi ta nuna ko in kulla a lamarinshi
Bin ko Ina yayi da kallo ya gan harta mazan shi suke kallo domin ya birge Amma har yanzu Rumaisa Bata kalli inda yake ba
Wani iri yaji jikinshi nayi me, sai kawai ya ciza kasar lips dinsa da d’an karfi ya zuba Mata Ido
Lura da idanu na yawo a jikinta yasa ta mike tana tattara jakanta
Yana ganin haka ya mike ya karasa inda ake biyan kudi yana magana da cashier din
yasira ta Kai muryarta kasa ta inda baza a jisu ba tace”Rummaisa dan Allah ki bari in biya kudin yau kinji”
Rummaisa ta zuba Mata Ido kafin tace”karki damu Ina da kudi Ranan da bani dashi Zan Bari ki biya”
Cikin rashin Jin dadi yasira tace”kullum haka kike cewa Kuma shekara uku kenan ko so d’aya Baki tab’a amshi wata taimako daga guna ba wallahi bana Jin dadin haka da kikeyi bayan kinsan Ina da kudin da Zan d’auki nauyin ki a makarantar Nan ai sai ki Bari in ragewa baba aiki ko?”
Rummaisa tayi murmushi tace”kiyi Hakuri yasira”bata jira cewar yasira ba ta karasa inda ake biyan kudi ta bawa cashier dari uku na abinci plate d’aya Daman Bata ci extra meat ba
Kin amsa yayi yace”an biya muku ”
Zuba me Ido tayi ba tare da janye hanunta ba tace”ka maidawa ko ma waye ne kudinsa please”ta Kare da ajiye me kudi a saman table ta bar wurin
Yasira ko binta tayi a baya ba tare da ta bayar da nata ba tunda ance an biya musu,abin zai baka mamaki in nace maka mahaifin yasira Mai kudin gaske ne Amma ji Yar talaka ta fita sanin mutunci kanta
Suna fita Rumaisa ta ji an Kama Mata ganin Ashe lab’ewa yayi Yana jiran fitowarsu
Juyawa tayi ta gan namiji ne baligi ya rike Mata hanun abinda ba Wanda ya tab’a yi Mata haka sai abin ya b’ata Mata rai ta kalli hanun zuwa fuskarshj da yake Mata wani irin murmushi da ta fassarashi da na rashin d’a’a
Zata janye hanunta ya damke Yana cewa minti biyar please
Idanun Rumaisa ya canja kala zuwa jazir Ranta ya fara suya dan b’acin Rai
Cikin wani irin murya daya tsoratar da yasira tace”malam sakar min hanun
Yace”bazan sake ki ba sai kin fad’amin sunanki da number ki”
Wani abu ne ya tokare Mata makoshi ai da zuciya ya d’ibeta wanka me Mari tayi daya bada wata Kara tassss.
Ba shiri ya sake ta ya dafe kuncinshi da sauri yan matan daya Baro a ciki suka fito
Ta nuna shi da yatsa cikin b’acin Rai tace
Diran dare na muku saboda Wanda suka biya nayi alkawarin typing yau
Maman Nur.
Name: | [WATA AMARYA HAUSA NOVEL ] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML |
Uploaded By: | www.mynovels.com.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books, Complete Hausa Novels |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | November, 2021 |
Allah yakara basira