WATA KISSAR SAI MATA HAUSA NOVEL

WATA KISSAR SAI MATA HAUSA NOVEL

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

KADAN DAGA CIKIN LITTAFIN…

[Bismillahir rahmanirrahim
Ban rubuta wannan littafi dancin zarafin wani ko wata ba, nayi shine dan ɗebewa masoya na kewa sakamakon hutun da zan tafi da se Allah ya kaimu September zan cigaba da kawo muku littafin AƘIDA TA, Se dai kash farincikin ku shine nawa, zan baku wannan gajeren labari dan ɗebe muku kewa, ina fatan mu amfana da darusan dake ciki
Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan Bismillahir rahmanirrahim
Ban rubuta wannan littafi dancin zarafin wani ko wata ba, nayi shine dan ɗebewa masoya na kewa sakamakon hutun da zan tafi da se Allah ya kaimu September zan cigaba da kawo muku littafin AƘIDA TA, Se dai kash farincikin ku shine nawa, zan baku wannan gajeren labari dan ɗebe muku kewa, ina fatan mu amfana da darusan dake ciki
Amma zamu tafi in random direction ne, babu specific lokacin posting, zan iyayi a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers.

* a kowane lokaci, bazan samu kawo posting akai akai ba saboda uzurrurikan da suka shamin kai, dan Allah include me in your prayers.

Page 1

Tuƙin Babur ɗin a daidaita sahun sa yake cikin nutsuwa da ƙwarewa, yana yi yana duba agogon hannun sa, ga dukkan alamu yana hanzari ne yaje wani guri, kiraye kirayen sallar la’asar da’ake ne yasa shi yin parking ɗin baburin nasa domin bin jam’in salla.
Koda’aka idar da salla, komawa yayi cikin baburin sa ya cigaba da tuƙi.

Wata ƙaramar Unguwa ya nufa, me ɗauke da gidajen talakawa, wani matsakaicin gida ya nufa yaje yayi parking ɗin baburin sa.

Da Sallama ya shiga gidan, amma yanayin sallamar tasa kaman anyi masa dole ya furta.

Wata babbar mace ce da wasu mata guda biyu kewaye da ita suna hira, da gani kasan ‘ya’ yan tane, saboda kamar da take da su.

Amsa masa Sallamar suka yi gaba ɗaya, tare da yi masa Sannu da zuwa.

Ba wadda ya kula a cikin su ya shiga ɗakin sa, ya ɗau kusan mintuna Ashirin sannan ya fito ya nufi matsakaicin kitchen ɗin dake tsakar gidan.

Yana shiga ya fara buɗe tukwane, wani uban tsaki yayi ya fito tsakar gida ya kalli inda Mahaifiyarsa da yayyen sa suke yace

“Umma wai ba wani abu se tuwon nan, dan Allah ki dafa min wani abun, ni bana son tuwon nan”

Kallon sa ɗaya daga cikin matan tayi tace “iyeee wai har yanzu Ammar baka dena wannan taɓarar ba? Ayi Abinci amma kai se wanda kake so?”

Haɗe rai yayi yace “ina ruwan ki? Gidan ki ne?”

Ɗayar tace “Taɓɗijan nikam Zanga abunda za’a dinga girkawa a gidan ka, ka fiye ƙaƙale Ammar”

Tsaki yayi yace “Umma dan Allah akwai wani Abincin ne?”

Umma tace “Dan Allah kar kuyi min faɗa, ba yadda zaku haɗu se kunyi rigima, nasan dama ba cin tuwon zakayi ba, duba na dafa maka shinkafa da miya yana ɗakina”

Bece komai ba ya nufi ɗakin mahaifiyarsu domin ya ɗakko Abinci.

“Hmm gaskiya Umma kina sangarta Ammar, Abinci se wanda yaga dama? Har yanzu be dena wannan iyayin ba? Wallahi matar Ammar ta shiga uku, ga masifa da zafin rai, ga jin kai da isa”

“Taɓ lallai Yaya Maryam akace miki zeyi wa matarsa ne? Taɓɗijan ai irin sa in suka shiga hannun mata se yadda akai da shi, baze mata wannan muzuran ba, musamman ya haɗu da yaran zamanin nan masu wankaken ido”

Ammar yana jinsu ya fito ya kalle su yace
“har yanzu ba’a haifi yarinyar da zata juyani ba, ƙare wa ni bazan auri yarinya ba, sena samu wadda aƙa llata kai shekara talatin, dan bazan ɗauki hauka da rawar kai daga kowace yarinya ba, Munafukai kunzo se zigamin uwa kuke, baku da aiki se zarya a gida, wallahi nine mijin ku baku isa ba, bazan yadda da wannan gantalin naku ba”

Yaya Maryam tace
“‘yar shekara talatin fa sa’ arka kenan? Kana shekara talatin da biyar ka auri ‘yar talatin da biyar?”

“eh’ yar shekara talatin ɗin, wadda tasan meye zaman Aure, ba wannan banzayen yaran masu rawar kai da fitsara ba”

Amina tace “mhmm wai Mune munafukan, Allah ya bamu rai da lafiya, zamu ga matar Ammar, zamu ga irin zaman da za’ayi, ‘yar shekara talatin din tayi maganin ka yarinya ba tayi ba”

“Ba’ a haife ta ba, macen da zata juya Ammar babu ita”

Yaya Maryam tace “to ina batun Amirar gidan Baffa salmanu, ai kaga ita da girman ta dan zata kai shekara ashirin da biyar, da ko ita seka aura”

“Nine zan auri wannan yarinyar? Banda hauka da yarin ta babu komai akan ta, ko ciwon kanta bata gama sani ba”

“shekara Ashirin da biyar ɗin ce bata san ciwon kanta ba?

Umma tace “dan Allah ya isa haka, ku idan kun haɗu baku da aiki se faɗa, jeka kaci Abincin ka, ni ɗazu gidan Malam Lawan sunzo, sunce dan Allah ranar Lahadi zaka kai musu ‘yan ɗaukar Amarya, ka faɗi nawa zasu baka”

Yamutsa fuska yayi “ɗaukar Amarya kuma?”

Umma tace “Eh mana, ko ba kaji me nace ba?”

“Bazani ba” ya bata Amsa
“me yasa?”
“Ni bazan ɗauki wannan mahaukatan yaran ba, in tafi titi suna hauka da ihu a cikin babur ɗina ba, dan sam hankali be ishi matan unguwar nan ba, daga su har iyayen su, basu da kintsi, duk gayyar ballagazai, bana san shirme ko nawa zasu bani ba zani ba”

Maryam tace “hada mu kenan? Tunda muma ‘yan unguwar ne”
Wani mugun kallo yayi mata yai gaba abun sa ba tare da ya bata amsa ba

**********

Tafiya take a sannu uniform ɗin ta na makaranta sun ɗau guga, dukda lokaci ya ƙure kusan tara da rabi na safe, ta makara sosai amma tafiyar ta take cikin nutsuwa.

Tana isa makaranta ta shiga kanta tsaye ba tare da fargabar komai ba ta nufi hanyar Ajin su.

Ji tayi an ƙwala mata kira daga bakin staff room “Mufeeda” tsayawa tayi ta dai daita nutsuwar ta sannan ta juyo ta nufi inda ake kiran ta, yanayin tafiyar ta zaka kalla kasan bata da lafiya.

Discipline Master ne tsaye shida megadi tana zuwa ta zube har ƙasa ta gaishe shi, ya amsa ransa a haɗe ya kalle ta

“ke se yanzu ake zuwa makaranta?”
Cikin sanyin murya tace “Sir am sick that’s why I come late”
Ta faɗa tana ɗan yamutsa fuska tareda ƙwalla a idon ta alamar tana jin jiki.

“Meyasa kika zo bayan kin san baki da lafiya”?

“Naji na ɗan samu sauƙi ne shiyasa”

“Shikenan jeki Allah ya sawwake”
“Ameen thank you sir”

Ta miƙe tana juya masa Baya ta kama dariya tareda gwali ta tafi Aji.

Bayan an fita break an dawo, class ya kaure da surutu da hayaniya, prefect ne suka zo sukayi magana a class ɗin akan principal yace ayi shiru yana da baƙi, sannan a rubuta masa noise makers duk wanda sunan sa ya fito a ‘yan surutu akwai horo me tsanani .

Hakan yasa ajin yin tsit, dan ko kwakwaran motsi kika fiye yi se a rubuta sunan ki, saboda punishment ɗin principal ba sauƙi.

Mufeeda ta kalli ƙawar ta Fati tace “Kin san meyasa na makara yau?”

Fati ta girgiza kai, Mufeeda tace “Anguwar su Anty murja na biya, naje na samu Yaya Usman me mana ɗinki nan ƙanin mijin ta na sauke masa kwandon bala’i, na gaya masa an jima da yamma zan koma ya bani dinki na kona masa rashin mutunci, dan wulaƙanci biki saura sati ɗaya amma be gama min ɗinki na ba, Anty murja ta hanani kuɗin mota wai tunda nayi wa ƙanin mijinta rashin mutunci ba zata bani kuɗin mota ba, ni ko nai amfani da kuɗin makaranta na, nai taho wata”

“Mufeeda wallahi zan rubuta sunan ki, tun ɗazu kike surutu fa” cewar class captain ɗin su

Cikin tsiwa mufeeda tace “eh da yake nika ɗai kika raina ba, karki fasa saka sunan nawa”
Aikuwa aka rubuta sunan Mufeeda cikin masu surutu.

“Fati dan Allah bayan la’asar zanzo gidan ku ki raka ni, idan be gama ba koda me yake yawo seya bani kayana”

Seda Mufeeda tayi surutun ta me isar ta sannan ta fara tunanin me zata yi wanda zesa ta ɓata sunayen ‘yan surutu da’ aka rubuta.

Miƙewa tayi ta tafi gurin zaman class captain ɗin su, tana zuwa ta fizge takardar sunayen,
“Kai lallai wannan sunayen hada san kai a ciki, ku saurara kuji sunayen wanda aka tsana, aka rubuta sunan su”
Nan Mufeeda ta shiga karanto sunayen wanda babu su a cikin takardar, nan da nan aka ɗau hayaniya, wanda suka san ba su yi surutu ba suna son jin ba’asin dalilin rubuta sunayen su.

Nan da nan Class ya kaure da hayaniya, class rep na ƙoƙarin kare kanta akan bata rubuta sunan wasu ba, yayin da Mufeeda ta hana ta magana, aka yaga takaddar sunaye, se zage zage da hayaniya sosai.

Ana cikin hayaniyar ne head girl ta leƙo ajin tace “SS2 on your knees under the sun inji PC”

Nan suka fara salallami, wanda basu jiba basu gani ba suna Allah ya isa.

Dama sun saba shan punishment, saboda tsabar rashin jin ‘yan ajin.

Sunyi tsit a rana suna kneel down, ga ranar ta ɗau zafi sosai, kasa jurewa Mufeeda tayi dan haka ta miƙe ta ƙwalla ihu, ba shiri ba tare da sauran ɗaliban sun san me yasa ta ihun ba suma suka miƙe suka sa gudu suna ihu, hakan ya bata damar ɗaukar jakar ta ta nufi gate ɗin fita.

Tana zuwa ta daidaita nutsuwar ta, ta kalallame me gadi akan cewar bata da lafiya ne zata gida ta sha magani, da yake ɗazu a gaban sa ta gayawa discipline master bata da lafiya.

Ya barta ta tsere abun ta.

Aikuwa da principal yazo, babu wani gamshashashen bayani da yasa suke ihu, haka yasa aka zane su aka basu noma, yayin da wadda tai laifin tuni ta tsere.

*************

Ƙarfe huɗu Mufeeda ta shirya zata fita, duk yadda tayi maman ta ta bata kuɗin mota hana ta tayi, tace “na gaji da kisan kuɗin da kike sani babu dalili, ni auren ‘ya ne a gabana tafi ki bani guri”  haka ta haƙura ta fita, naira ɗari biyu ce kawai da ita.

Ta tafi gidan su Fati domin ta raka ta unguwar da zasu karɓo ɗinki, suna tafe Fati na bawa Mufeeda labarin irin Azabar da suka sha a makaranta yau, sakamakon abunda tayi, Mufeeda kam se dariyar mugun ta take.

Suka hau napep, tafiyar naira ɗari biyu a ɗari aka kaisu, suna zuwa telan ya kalleta ya ɗakko wata leda ya miƙo mata yace
“gashi nan jarababbiya na gama”

“Ai wallahi da baka gama ba sena kwaso maka ‘yan sanda, kabani kayana kuma kabani kuɗi na”

Telan yace “daga yau bazan ƙara karɓar kayan ki ba mara kunya”

“haba kai ka isa haushi ka bani shiyasa na maka hakan ai”

Ya kalli abokan aikin sa yace
“baku ga tijarar da tayi min ba ɗazu akan dinkin ta da sassafe tazo seka ce zata ritsa ɓarawo”

Ɗaya ya kalle ta yace “Muffy dama haka kike?”

“Wallahi ba haka nake ba, rashin cika Alƙawarin sane ya sani haka”

“Naji jeki karki ƙara kawo min kayan ki”

“wallahi sena kawo, sedai in zaka dena ɗinki gaba ɗaya”

Haka suka bar shagon ɗinkin nan suka fito titi domin samun babur su tafi gida, Mufeeda ta tsaya ta saimusu guava ta canjin naira ɗarin nan.

Fati tace “Mufeeda da kika kashe kuɗin a me zamu koma gida?”

Mufeeda tace “Ai na Allah basa ƙare wa, bari kiga semun zaɓi Napep me kyau, me kiɗa da tsafta me ƙamshin turare, semu hau muce ya kaimu gida sabil”.

Wani me Napep ne yayi parking a gefen su, ya sauke wasu ‘yan mata su uku, me Napep ɗin tsaf da shi ba kace shike tuƙin babur ba, seka zata zaka ganshi da haɗaɗɗiyar mota, yayi shiga ta kamala gashi kyakywa a nutse yake, Napep ɗin nasa ma fes da shi.

Ɗaya daga’ yan matan tace
“dan Allah ko zaka bamu lambar ka, in zamu wani gurin semu kira ka”

Fuskar nan tasa babu alamar wasa yace

“malama kubani haƙƙina in tafi, ba raba lamba ne ya fito dani ba”.

Dariya Mufeeda ta dinga yi ganin abunda yake faruwa, se yarfa ‘yan matan nan yake, da alama ko magana ma baya son yi.

Mufeeda tace “bari a gama waccan rigimar, wannan Napep ɗin zamu hau wallahi”

Ɗan zare ido fati tayi
“kina ganin yana yiwa wannan haɗaɗɗun ‘ yan matan muzurai, muka raina masa hankali ai zane mu zeyi”

“Dalla matsoraciya zuba ido kiga”

Jan babur ɗinsa yayi ze wuce, Mufeeda tai sauri ta ɗaga masa hannu ya tsaya, fati ta gaya masa inda ze kaisu, har zasu hau mufeeda tace

“Zahradeen”
Waigowa yayi ya kalle ta yace bashi bane.
Mufeeda tace kai
“wallahi kaine Zahradeen ne mana”
Tsaki yayi yace “in ba hawa zakuyi ba zan tafi”

“Yi hakuri zamu hau” suka hau Napep sun fara tafiya Mufeeda tace
“Gaskiya nayi mamaki daka ce ba kaine Zahradeen ba, anya ba wasa kake min da hankali ba?”

Fati tace “dan Allah ki ƙyale shi yace bashi bane ba, waima waye Zahradeen ɗin ne?”

Mufeeda tace “Saurayi na ne, Amma yanzu ya maze wai bashi ne Zahradeen ba”

Waigowa yayi ya kalleta, ya kalli yarinyar da ba tafi shekaru sha shida ba amma tana kiran saurayi girgiza kai yayi ya ci gaba da tuƙin sa.

Mufeeda tace “dan Allah Zahradeen ka dena min wasa da hankali”

A fusace yace “ke niba Sunana Zahradeen ba, Sunana Ammar”

Ɗan lumshe ido tayi dama abunda take sonji kenan

“Wow sunan ka me daɗi Yaya Ammar, Amma kayi kama da Zahradeen ɗin da ya yaudareni”

Ita kam Fati abun mamaki ya bata wai Yaya Ammar daga haɗuwa da mutum harta liƙa masa Yaya, gaskiya halin Mufeeda se ita
Shiru yayi bece komai ba, bata damu ba tace
“Kasan wani Abu Yaya? Ka birgeni gaba ɗayan ka a nutse kake ba kaman wasu daga cikin masu Napep ba, ga shigar ka ta kamala, ga komai naka a nutse da gani baka da hayaniya irin na sauran ‘yan uwanka masu babur”

Ɗan girgiza kai yayi, sam ko gajiya ba tayi da surutu, gata wata ƙwaila da ita amma se zuba uban iyayi take yi tana surutu.
Sam shirun da yayi mata be bata haushi ba.

“Yaya Ammar kalli wancan me Babur ɗin ta nuna wani me napepe
” kalli Askin kansa da shigar jikin sa, ina me hankali ze shiga babur ɗin sa? Da irin su ake haɗa kai a cuci fasinja, ko a haɗa maza da mata a Napep ɗaya, Amma kai tunda ka ɗauke mu baka ɗauki namiji ba”

Ammar yace “Idan na ɗauki Namiji ya zakiyi?”

Ɗan murmushi tayi dan ba tayi zaton ze magana ba

“Ai nasan ba zaka ɗauka ba ma Yayana, Samun nutsatsen me Babur irin ka ai se an tona, gentle da kai sam ba kayi kama da tuƙin Napep ba ma”

Ammar yace “Meyasa banyi kama da me Napep ba?”

“Taɓɗijan yadda maza ke mugun raina sana’a ne namiji kaman kai ze tuƙa Napep, aini ba ƙaramin burgeni kai ba Yayana, wani kaman kai ɗin nan ga kyau ga nutsuwa baze tuƙa Napep ba, cewa zeyi se aikin office or something like that”

Ɗan girgiza kai yayi yace “Hmm”

Duk rashin son maganar Ammar haka Mufeeda ta dinga jansa da surutu, jefi jefi yana mayar mata, gaba ɗaya mamaki ya cika Fati, yadda suka ganshi ɗazu yana wa wasu ‘yan mata muzurai, Amma se jansa da hira Mufeeda take yi.

A titi suka yi ze sauke su, Amma seda Mufeeda ta jashi ya kaisu har ƙofar gida fati ta sauka a bakin layin su, ya ƙarasa da Mufeeda.
Se a lokacin ta tuna ashe sun kashe kuɗin motar tasu.

“Yaya Ammar dan Allah kayi haƙuri ban gaya maka tun kafin mu hau ba, kuɗin motar mu muka zubar garin ɗakko kuɗin mota muka zubar da kuɗin bamu sani ba, Amma kaga gidan mu nan bari in shiga in karɓo maka.

Shiru yayi yana kallon ta, ƙasa tayi da murya tace “please Yayana am sorry, nasan bamu kyauta ba, a lokacin nan daka ɗau zafi dana gaya maka ba lallai ka ɗakko mu ba, kayi haƙuri dan Allah ba haka halinmu yake ba, bari in shiga in karɓo maka, ka yi haƙuri kaji Yaya Ammar” ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya.

Shi gaba ɗaya yadda yarinya ƙarama ke wannan iyayin da kwarkwasa shike bashi mamaki.
Kunna baburin sa yayi ze tafi, Mufeeda tace

“Haba Yaya Ammar Allah yasa ba fushi kayi ba? Ka tsaya in shiga in karɓo maka dan Allah”
“Ku bashshi kawai” ya ja babur ɗin sa yai gaba.

Yana tafiya Mufeeda tai tsalle, “wo ni Autar Baba na, Allah ya bani Yaya a titi”

Tai shigewarta gida tana dariya Maman ta ta kalleta “ke ina kayan ɗinkin? Kika shigo kina dariya”
Zumɓura baki tayi
“ba hanani kuɗin mota kika yi ba, na je na karɓo me Napep ɗin ya ajiyeni a titi nikuma na manta da kayan a Napep”

Buɗe baki Maman tayi  “Kayan kala biyar kika barmin a a daidaita sahu dan uban ki, kuma ko a jikin ki kike dariya? Kinyiwa kanki ranar bikin se dai ki bar gidan nan, inda na gode Allah bani na sai miki ba uban kine ya siya, shashasha mara hankali”

Indai faɗan Mama ne Mufeeda ta saba shansa, dan haka ko a jikin ta, ta shige ɗakin su, wani irin farinciki ke ratsa zuciyar ta wanda bata san dalilin hakan ba, tasan dole Ammar ya dawo saboda kayan da ta bari da gangan a Napep ɗin sa.

Kwana Mufeeda tayi mafarkin Ammar, da tuno shi se ta saki murmushi.
Yayar ta ta kalleta “professor Autar Baba wai farincikin me kike haka? Mama se faɗa take kin bar kayan ki a ɗan sahu, amma baki damu ba? Yanzu me zaki saka ranar bikin?”

“haba Yaya ke an isa ayi bikin ki bani da kayan sawa ne? Ko naki sena saka, ina Addu’a insha Allah nasan me Napep ɗin ze kawomin abuna”

“ya akayi kika san hakan?”
“jikina ne ya bani”.
Inma be kawomin ba baba ze saimin wasu.
************

Wasa2 kwana biyu Ammar be dawo ba, yauma tana makaranta sam bata walwala, Fati tace “Muffy wai yana ganki haka?”

“ke barni har yanzu Yaya Ammar fa be zoba”
“to mezezo yai miki?”
“wallahi fati so nake kawai in kuma ganin sa ya haɗu, a Napep din fa nabar ɗinkuna na, Amma har yanzu be dawo ba”

“kayan naki kika bari a Napep, gaskiya baki da kai, yanzu idan be kawo miki ba fa?”

Mufeeda ta taɓe baki “ke nifa bata kayan nan nake ba, Baba baze bari ayi biki bani da sabon kaya ba, ni kawai shi nake so in kuma gani”

Tsaki fati tayi tai bar gurin dan ba ƙaramin ƙular da ita Mufeeda tayi ba.

************

Bayan magariba Mufeeda na kwance tayi shiru tana ta tunanin Ammar, ji tayi ta gaji da kwanciyar, ta miƙe ta fito tsakar gida, Maman su haushin ta take ji, sam bata shiga sabgar ta saboda batar da kayan da tayi, shirye shiryen biki kawai sukeyi.

Yaro ne yayi sallama yace “wai ana sallama a waje, inji wani”

Mufeeda bata tsaya jiran meza’ace ba, ta zari hijjabi tai waje, kaman yadda ta zata Ammar ne a tsaye a gefen Napep ɗin sa.

Da sauri ta ƙarasa inda yake
“Yaya Ammar kaine? Ina wuni?”
“Lafiya ƙalau, dama nazo in tambaye ki ne, ko kune kuka manta kaya a Napep ɗina, tun shekaranjiya nake yawo da su”

Ajiyar zuciya tayi  “Kayan ɗinki nane Yaya, na shiga damuwa sosai, zuciya ta ta bani zaka kawomin dama, dan na yarda kai me amana ne”

“Seki kiyaye gaba, idan kin shiga abun hawa ki dena surutu, in ba haka ba wataran dake za’a tafi”

Ya Ɗakko kayan ya miƙo mata
Bata karɓa ba ta tsaya tana kuma ƙare masa kallo, murmushi ta sakar masa tace

“bana surutu a abun hawa ai, ranar ma dan kai ne, nagode sosai Yayana, Allah ya ƙara Arziki, ya kiyaye ka daga sharrin maƙiya, Allah ya azurta ka da halal ya nesan taka da haram, Allah ya sakawa iyayen ka da Alkhairi Addu’ar su da tarbiyar suce ta sa ka zama mutumin kirki ”

Ammar yana mamakin yadda yarinyar ke sarrafa harshen ta. Ba ta karɓi kayan ba tace
” Dan Allah ina zuwa”

Ta koma cikin gida, ba tafi mintuna biyar ba ta fito hannun ta ɗauke da leda, ta miƙawa Ammar.
Ya kalleta yace “menene wannan?”

“Yaya Ammar yaba kyauta tukuici, bani da abunda zan biya ka, kawai dai na baka ne”

Girgiza kai yayi  “bazan karɓa ba, ungo kayan ki, ina sauri zani wani guri ne”

Kallon sa tayi “zaka zance ne? Idan baka karɓa ba zan barka da kayan sedai ka koma da su ko ka barsu anan dan wallahi bazan karɓa ba”
Tai maganar tana kallon cikin idon sa, dagaske take abunda take faɗa.

Hannu yasa ya karɓa, sannan ta karɓi kayan ta, cikin iyayi tace
“yauwa ko kaifa Yayan Mufeeda”

A ransa ya maimaita “Mufeeda”
Tace “ungo wannan invitation ne, bikin yaya ta za’ayi a wannan satin dan Allah kazo kaji Yaya na”

“ban miki Alƙawari ba gaskiya, Amma Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lafiya”

Wani irin kallo take masa wanda ya kasa gane kallon menene haka?

“Idan ba kazo ba bazanji daɗi ba, kuma zanga kaman kamin wulaƙanci ne, ko kuma maybe… Shikenan dai nagode ka gaida Mama, Allah ya kaika gida lafiya, ya tsareka daga sharrin maƙiya”

Ta juya ta nufi gate ɗin gidan su, yai shiru na ɗan lokaci ya shige baburin sa ya tafi.

Ɗakin Baban su ta nufa, tana zuwa ta tarar da yayyen ta na gidan Aure sun cika falon baban su da mahaifiyarsu suna ta hira ana shirye2.
Tana zuwa taje gaban Maman ta ta ajiye mata kayan ɗinkin tace

“Mama ga kayan nan, me Adaidaita sahu ya kawo min, seki dena haɗemin rai”

Wani daga cikin yayyen ta ya kalle ta

“Ahh kaga professor, kuma Autar Baba da Maman ta”

Mufeeda Ta ɗan tura baki  “Autar Baban dai, Mama tafi son Yaya akaina, kuma na fasa zama professor ana aurar da Yaya nima Aure zanyi”

Dariya suka dinga mata, Babbar yayar su tace  “kiji min yarinya da rashin kunya, kin fasa zama professor kafin kiyi auren?”

“Na fasa dan Yaya na barin gidan nan Mama zata kasheni da sa aiki, dama kaman bata sona nima Aure zanyi”

Mama tai murmushi tace “naji bana sonki ɗin, nafi son Amina ke kam baki da nutsuwa ga wauta, tunda babanki yana sonki ai shikenan, waye ma ze aure ki a haka, baki iya komai ba, se son jiki da rashin kunya, ko Saurayi baki da shi”

“Wallahi na samo Saurayi, me Adaidaita sahun da yakawo min kayana nake so”

Yanayin yadda tayi maganar ne kanta tsaye da confidence ɗin ta yasa ta bawa kowa dariya, suka ɗau maganar tata shirme.

Domin gyara, sharhi, ko shawara
07063065680

Kuma yaseen ba comments se Allah ya kaimu September zan cigaba da typing.

]

KU SAUKE CIKAKKEN LITTAFIN ANAN KASA👇👇👇Preview: [DOWNLOAD COMPLETE BOOK 👇👇👇]

 

Name: Wata kissar Hausa Novel
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: MYNOVELS.COM.NG
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents, Hausa Novels Books
Groups/Writers: Billyn Abdul, Benaxir Oumar, Eyshat, Nadia Buhari, My Novels, Zamani Writers Association, Exclusive Writers,Alheri writers,Best Hausa Novels
Novel Price: Free
Last Modified: July, 2021

 

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.