Waye Jinnul Ashique Aljanin Soyayya
JINNUL ASHIQ (ALJANIN SOYAYYA)
**********
MENENE JINNUL ASHIQ?
ZAUREN FIQHU :- JINNUL ASHIQ Wani irin aljani ne wanda yake shiga Jikin Mata saboda tsananin soyayyar da yake musu.
MENENE DALILAN SHIGARSA:
ZAUREN FIQHU : Ayawancin lokuta yakan shiga ne ta dalilin SOYAYYA. amma awasu lokutan yakan shiga ta wasu dalilan (kamar sihiri ko tsafi ko ta dalilin gado) sannan daga baya ya juye ya zama na soyayya din.
WACCE IRIN CUTARWA YAKE YI??
ZAUREN FIQHU: Daga cikin nau’in cutarwar da yake yiwa ‘Yan-Mata akwai:
1. Yakan Kore musu samari. komai soyayyar da saurayi yake ma budurwa, sai ita kuma taji ta tsaneshi. koda kuwa ita ce ta fara furta masa soyayyar.
2. Yakan sanya ma budurwa Bakin-Jini mai tsanani. ko kuma ya hana su samarin zuwa wajenta. Ko da sun furta suna Qaunarta, amma babu damar suzo wajenta zance.
3. Yakan rika zuwa yana saduwa da yarinya. zata rika ganinsa yana zuwa mata amafarki yana saduwa da ita. Acikin Siffar Saurayinta ko mahaifinta, ko yayanta, ko kuma wani mutum wanda ta sani ko kuma wanda ma bata sani ba.
4. Motsawar jinyoyi kala-kala da zarar anyi mata maganar aure. sai kaga ta kama ciwon kai da zazzabi ba dare ba rana. Ko kuma da zarar saurayi ya buga mata waya sai taji kanta ya fara ciwo.
5. Daukewar Sha’awa. yarinya zata rinka ji acikin ranta cewar ita fa bata son aure. kuma zataji bata bukatar duk wani Namiji.
6. Wata ma idan abun ya fara nisa, ko unguwa zata je, sai ta rika jin kamar wani yana tafiya abayanta.. To Aljanin ne yake rakata.. Kuma yana bibbiyar mazajen da suke kallonta awaje. da zarar wani ya furta yana sonta, to Aljanin zai shiga zuciyarsa ya sanya masa waswasi. har ya shiriritar da shi.
7. Akwai wacce idan abun yayi nisa Aljanin zai rika zuwa mata AFILI QARARA yana saduwa da ita. koda da rana ne.
8. Akwai wacce aljanin zai rika sanya mata saurin Fushi tana fada da samari. da zarar sun fara soyayya da mutum sai taji Duk duniya bata da Makiyi kamarsa.
9. Akwai wacce Aljaninta Har WARNING yake yiwa samari. zai kira mutum ta waya. yace masa Kar ya Qara ganinsa tare da wance. wani lokacin ma yakan hallakar da saurayin nata. Ko kuma ya sanya masa jinya ko ya lalatar masa da dukiyarsa ko hanyar samun abincinsa.
TA YAYA ZAN GANE INA DASHI??
ZAUREN FIQHU: – Bayan wadannan alamomin da na lissafa, zai hada miki da yawan ciwon kai, faduwar gaba, Wasa da sallah, Qin karatun Alkur’ani, Taurin kai, rikicewar tunani, rashin barci, kasala, Rikicin jinin Al’ada, Saurin fushi, Mantuwar karatu, da sauransu..
NAN GABA insha Allahu zamu fadi irin illolin da yake yiwa matan Aure.
Idan ana bukatar Qarin bayani ko taimako ko shawarwari sai a tuntubi Zauren Fiqhu ta wadannan lambobin : 07064213990 08157968686 08163621213
Da fatan Allah shi karemu. marassa lafiya kuma, Ya Allah ka basu lafiya ameeen. Wannan post din na ZAUREN FIQHU ne. mun rubutashi tun ranar 13-12-2013 (shekaru 6 kenan da suka gabata).
Leave a Comment