Wayyo Dadi Hausa Novel

wayyo dadi

Wayyo Dadi Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

HUZA’IYYA Wayyo Dadi Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

NA KSS.

 

 

NA KUƊI NE MAI BUƘATARSHI TA YIMIN MAGANA TA WANNAN LAMBAR..

WhatsApp only

 

 

 

 

FREE P.1.

 

 

 

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI, ALLAH INA ROƘONKA TARE DA KAMUN ƘAFA DA ISASSUN DAKA HALITTA BA KAMAR MUHAMMADUR’RASULULLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA ALLAH KASA YADDA NA FARA WANNAN LABARI LAFIYA KASANYA NA GAMASHI CIKIN ƘOSHIN LAFIYA.ALLAH KA BANI IKON RUBUTA DAI-DAI DA AIKI DASHI,ALLAH KA HANENI RUBUTA ALFASHA ALLAH KA SANYA AL’UMMA SU DINGAMIN ADDU’A TA GARI ADUK SANDA SUKA KARANTA LABARINA BASUYI KAICO GA ALƘALAMINA BA.TSIRA DA AMINCI SU TABBATA GA RASULULLAHI ANNABIN FARKO DA ƘARSHE WANDA BA’AI KAMARSA BA, BA KUMA ZA’AYI BA,ALLAH KAYI MASA SALATAI ADADIN DUKKAN ABINDA KA HALITTA WANDA YAKE CIKIN DUNIYA DA LAHIRA BAKI ƊAYA.ALLAH KA BARMU DA SOYAYYARSA HAR ƘARSHEN ƘARSHEN RAYUWA…

 

 

 

@@@@@@@

 

HAJIYA LAMI ce atsaye akan wata matashiyar mace me kimanin shekaru talatin da biyu(32) wadda ta ke fara tas kamar atsaga jini ya fito tana kwance akan wata tabarma tana bacci wanda daka ga yadda takeyinsa zaka fuskanci awahale ta ke yinsa ga tsowon cikin da ke jikinta kamar an kifa ƙwarya.Tsaye ta ke kanta tana kiran sunanta tare da zungurinta da ƙafa tana faɗin…

 

 

” HUZA’IYYA..! Ke Huza’iyya tashi nan zan fita”

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
A razane ta farka tare da saurin dafe cikinta da takejin kamar zai huda cikin ya fito bata gama dabarar tashi zaune ba taji maganar Hajiyar akanta tana ce mata…

 

” Ki maza ki tashi daga wannan baccin da kika tsira na raini da nuna isa kifito tsakar gida akwai icce ankawomin da niƙaƙƙiyar dawa ki mulluƙamin tuwon dawa mai kyauma da miyar ɗanyar kuɓewa banson miyar daka gurzata zakiyi ƙananu kiyimin girki mai kyau,sannan kiyi da yawa saboda sadaka za’ayi da shi…”

 

Harta fice daga ɗakin ta juyo da baya tare da faɗin…

 

 

 

 

Name: [KYAWUNA JARABTA TA]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC .HTML
Uploaded By: www.mynovels.com.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: Hausa Novels Documents Hausa Novels Books Complete Hausa Novels Hausa Novels Hausa Novel Romantic Hausa Novels Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: June, 2022

 


Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram


“Wallahi Huza’iyya kikamin ɗanyen tuwo irin na jiya se ranki yayi mummunan ɓaci danke ba yarinya bace da zaki fake da ciki kizauna kinawa mutane iskanci waike ga me ciki,sannan ki saɓewa auta uniform ɗinta da kayan da ta cire kafin na dawo”.

 

 

Bata jira ta bakinta ba ta fice da jakarta ahannu yarinya ƴar kimanin shekara goma sha biyu(12)tana biye da ita abaya.

 

Yunƙurawa tayi tare da lallaɓa jikinta ta fito daga ɗakin da take tare da zaman dirshan aƙasa ta sanya buta agabanta ahaka tayi alwalar tare da zira hijabinta ta miƙe ƙafafuwanta ta gabatar da sallar azahar tare da ɗaga hannuwanta tanakai kukanta ga Ubangiji mai ji da ganin al’amuran da bayinsa suke aikatawa ahaka harta ɗauki lokaci sannan ta lallaɓa daƙyar ta fito tsakar gidan tare da leƙawa kitchen ɗinsu ta sauke idanuwanta akan tafkeken gas ɗin da suke girki da shi yayin da buhun gawayi yake ajje awani ɗan lungu dake kitchen ɗin wanda suke amfani da shi lokaci zuwa lokaci idan gas ya ƙaremusu base sunyi jira har lokacin da za’a ɗuro ba,gefen gawayin ta kalla inda tayi arba da iccen da akamata umarnin aiki da shi ta ke taji wasu siraran hawaye suna sakkowa kan fuskarta masu tsananin ɗumi,jan jikinta tayi ta jingina jikin bango dan ji take yi ƙafafunta suna rawa kaɗan-kaɗan,sakin jikinta tayi ta zauna sosai dan bazata iya jure tsayuwar ba duk jikinnata yayi tsami kamar wadda aka daka.Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Ta faɗa tare da dafa kanta da hannu bibbiyu tahau surutai kamar wata zautacciya…

 

” Nikam shekara nawa ne zanyi arayuwata nakoma ga mahaliccina?,tsawon shekarun da nayi na rayu cikin matsalolin rayuwa da baƙin ciki daga wannan se wannan shin me nayiwa rayuwa haka ne…Nikam wai haka duk wani maraya yake fuskantar rayuwar ƙunci da ruɗani? Me zanyi na samu sauƙin…”

 

Maganar ce ta katse mata lokacin kuka yaci ƙarfinta zufa se tsattsafowa takeyi tako ina na jikinta tanajin yadda ƙirjinta yayi mata nauyi cikintama ya dunƙule waje guda gaba ɗaya jikinta ya saki banda ajiyar zuciya ba abinda ta ke iya saukewa…

 

Sannu ahankali ta ke aikin afarfajiyar gidan dake babu murhu se wasu manyan duwatsu da aka kakkare tukunyar da su,tana yi tana riƙe cikinta da takejin yana wani irin juyi kamar ranar haihuwarsa ta tsaya,ahaka cikin galabaita harta ƙarasa tuwon ta kwashe sannan ta sake miƙe ƙafafuwanta awajan tana gyara tukunyar miyar da ta daɗe da dawuwa tafara gurza kuɓewar da riƙaƙƙu sunfi yawa acikinta,sannu ahankali take juya miyar da ta fara kumfa inda bayan ta dai-daita ta ɗebo ruwa da nufin ta ɗora akan garwashin itacen bata ankaraba seji tayi wani irin zugi da raɗaɗi sun ziyarceta acikin lokaci ƙalilan wanda hakan ya haifar mata sakin ruwan da cikin rashin sa’a tukunyar ruwan ta suɓuce tayi kan tukunyar miya wanda hakan ya haifar da zubar mafi yawansa cikin miya ya nemi waje yayi zamansa a ciki.”Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,ya rabbi ya Rabb! Allah kai kasan me kake nufi da ni da wannan ibtila’in da ya sameni awannan lokacin Allah ka shiga lamurana dan arziƙin tsaftataccen MARAYA Annabinka ka cire ni acikin ruɗanin rayuwa”, Ta ƙarasa faɗi tare da sanya gwuiwoyinta aƙasa ita tama rasa tsakanin kuka da ihu wanne zatayi itadai tabi ta zurawa miyar da ruwa ya fita yawa idanu sai ƙifƙiftasu take yi kamar mara gaskiya.

 

 

“Munafuka Azzaluma macuciya kalar cutar da kikamin kenan yau? wato jiya kinyimin ɗanyen tuwo yau kuma kinyimin miyar ruwa to wallahi kinyi a abincinki kuma yau tsakar gida zaki kwana sauraye su miki hukuncin zaluncin da kikayimini…

Yau naga makirar yarinya wato so kikeyi duk dukiyar da ubanki ya mutu ya bari sekin ƙarar da ita da rashin tattalinki ko?,to wallahi ƙarya kikeyi baki isaba dan nima ɗan uwana ne kingama cin rabonki tunda sau huɗu ina aurar da ke kina dawomin to wallahi wahala yanzu kika farata agidannan dan bazan taɓa ɗaukar raini ba da mutunci na kisa araina ni,a’a bazata saɓu ba bindiga a ruwa tunda abinda kika zaɓawa kanki kenan seki zauna kowane miji kice ya zalunceki nan kwa ba’asan kece baƙar azzaluma ba”

 

HAJIYA LAMI tana kaiwa nan a zancenta tasanya ƙafa ta harbeta tare da hayewa benenta tana ci gaba da sababinta.

 

“Wallahi yanzu ƙwaƙwalwata ta buɗe na gane duk wani tuggunki yanzu sam bazan ragamiki ba dan ba ke kaɗai aka rubutawa ƙaddara ba da har zakiyi aure har huɗu kifito kice baki dace ba kowa yaji wannan ma yasan zancen banza ne,inba haka ba ni yara na nawa amma ko yaji basu taɓa yi ba se ke dan kinga dukiyar ubanki ce kullum seki kaso aure kizo muna gugar kafaɗa to wallahi angama idan zaki fita ki nemo inba haka ba keda abinci sedai kiga ana ci agidannan badai nawa,banza shashasha gaki da kyau da komai amma bazaki nemi kuɗi da kyanki ba sedai ki zauna kina wahalar banza to kizauna yunwa ma ta isheki banza sakarya…!”

 

 

 

Dafe kanta HUZA’IYYA tayi da duka hannuwanta guda biyu wanda ta ke jinsa kamar zai tsage saboda masifa,innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! kaɗai bakinta ke iya ambata dan gabaki ɗayanta jinta ta ke kamar ba ita ba,daƙyar taja ƙafarta ta shiga ɗakin yaran da ta ke kwana domin ta zura hijabinta tayi sallah sai kuma zancen wankin uniformɗin auta ya faɗo mata…

 

 

 

 

 

ƳAR GATAN MAMA.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.