Waziri aku asalin taguwa complete
ASALIN TAGUWA 1
Jiya da na kai wa kakata Tasalla ziyara a ƙauye, sai na same ta zaune a ɗaki rungume da kaskon wuta tana ta ƙahon dandi. Muka gaisa, na samu wuri na zauna na fara raba ido a cikin ɗakin ina kallon tarkacen da tsohuwar nan ta tara. Ita har yanzu ba ta yarda ta rabu da wasu karikitan nata ba.
A can wata kusurwa ta bangon ɗakin na ga an jingine zunguru an kuma zube azargagi kusa da shi. A wani ɓanggaren kuma ga mazari bisa taskira har da abawa, ga kuma akwasa jingine. Na ga kuma gafaka rataye a jikin agalemin da aka kafe a bango. Hatta akushi da ƙoshiya tsohuwar nan ba ta watsar ba, ba maganar gidauniya da tarde ake yi ba. A ɗaya gefen kuma an girke tulu an rufe bakinsa da jemo ga kuma ɗan jallo kusa da shi. Da na ƙyalla ido wani saƙon sai na hangi shantu, na ce a raina lallai su Kaka an yi duniyanci.
Da na gama nazarin kayan ɗakin sai na ce mata, “kaka sanyi kike ji hala, na ga kin tasa wuta gaba kamar za ki faɗa ciki?”
Ta ce, “kai dai bari ɗan nan, wannan ruwa da ake shatatawa kwanan nan, ga kuma ɗan karen sanyi sai ka ce jaura ke wucewa, idan mutum ya yi sake sai a yi masa sakiyar da ba ruwa.” Ta jawo ɗan kindai daga tsariyar gado ta buɗe, ta ɗauki farsa ta cika bakinta. Ta dube ni ta ce, “dube ka, ko taguwar kirki ma ba ka sanya ba. Ahir ɗinka da sanyi!”
Na dubi ‘yar shet ɗin da ke jikina na yi dariya na ce, “to ni tsoho ne kamarki da zan ji sanyi?”
Ta yi dariya, bakinta ya yi bajau ya fara ɗaukar ala. Ta ce, “garin da za a me ake yi wa albada?” Ta sake duba na ta ce, “amma dai ka samu taguwar kirki ka riƙa sanyawa, ina amfanin wannan figaggiyar riga kamar ka roƙa?”
Na ce mata, “yadda kike jin sanyi, to ni zafi nake ji, shi ya sa na sanya ta domin na sha iska.”
Ta ce, “to ai wannan rigar Nasaru ce, ka kuwa ji an ce Nasara asarar duniya. Ka nemi ‘yar shara ita ce taguwar Bahaushe ta shan iska.”
Na ce, “to ita ma ‘yar sharar ai ga Bature Bahaushe ya kwaikwaye ta.”
Ta tsarga yawu a cikin kurtu ta ce, “yaro dai yaro ne. Ai ko da iska ya zo ya tarar da kaba na rawa. Ko da Bature ya zo ƙasar nan ya iske Bahaushe da cikakkiyar suturarsa, ba kamar wasu ƙabilun da ya tarar tumbur suna ɗaura ganyaye ba. Bari in ba ka tarihin asalin taguwa ka ji. Wani mutum ne mai suna…”
Na katse ta domin na san idan ta fara zuba, sai dare ya kwace mini ban sani ba. Na ce mata, “yanzu babu lokacin jin wannan tarihi, kin ga rana har ta yi gora za ta fara ruɗa-kuyangi, ga hanyar taku babu kyau idan an yi ruwa, ko yanzu sai da kwiɓin bazawara ya yi kusa ya kayar da babur ɗina. Ga kuma rashin tsaro da ake fama da shi. Idan Allah ya kai mu jibi, amaryar wata, zan dawo na ji wannan tarihi.”
Na zaro kuɗi daga cikin aljihuna na miƙa mata, na ce ta sayi goro. Ta sa hannu ta kalmashe tana godiya, ta jawo mayani ta dunƙule kuɗin ta jefa ciki. Muka yi sallama, na ɗage asabari na fita daga ɗakin, na buga babur ɗina na nufi gari, kamar mil biyar daga ƙauyen, ina ta hirji a cikin zuciyata.
.
Menene ma’anar waɗannan kalmomi kamar yadda suka fito a cikin labarin?
1. Ƙahon dandi
2. Zunguru
3. Azargagi
4. Mazari
5. Taskira
6. Abawa
7. Akwasa
8. Gafaka
9. Agalemi
10. Akushi
11. Ƙoshiya
12. Gidauniya
13. Tarde
14. Jemo
15. Jallo
16. Shantu
17. Jaura
18. Kindai
19. Farsa
20. Albada
21. ‘Yar shara
22. Kurtu
23. Ala
24. Ruɗa-kuyangi
25. Kwiɓin bazawara
26. Mayani
27. Tsariya
28. Asabari
29. Hirji
30. Amaryar wata
#RanarHausaTaDuniya
Bukar Mada
26/08/2022
ASALIN TAGUWA 2
Kamar yadda na ce idan Allah ya kai mu amaryar wata zan koma ƙauye wurin Kaka Tasalla domin jin tarihin asalin taguwa. To, da ranar ta zo sai na haye babur ɗina na nufin ƙauyen. A kan hanya na ga gonakin da aka noma an fara girbe gero, waɗanda kuma aka bari saura saboda matsalar ‘yan ta’adda, duk hambama ta cika su. A nan na gane lallai damina ta tsufa.
Da na isa gidan sai na tarar da matan wan mahaifina a gindin murhu suna gasa tumu, yara kuma sun samo taure a gona suna sha, wasu kuma na shan takanɗa. Na kafe mashin kusa da dabin tumaki, muka gaisa da matan gidan na nufi ɗakin Kaka, na same ta a kan karauni tana taɓa ƙailula. Na yi sallama, ta yi zumut, kamar wadda aka tsikara da allura, ta tashi zaune tana murje idanu.
Ta dube ni ta ce, “Garbati, kai ne tafe da yamman nan?”
Na ce mata, “I, ni ne Kaka.” Na zauna a gefen gado, na fara raba idanu kamar yadda na saba, ina kallon tarkacen da ke cikin ɗakin. Bayan mun gaisa sai ta jawo gidauniya ta yi mini idon kwaɗi ta ba ni. Na karɓa na shanye. Ita kuma ta ɓalli goro ta jefa baka. Ta kalli kayan da ke jikina ta ce, “ko kai fa ɗan nan, ka ga yau dai ka yi shiga irin tamu ta Hausawa, ba kamar kwanaki da ka zo da shigar Nasaru ba.”
Na ce, “to, da ma zuwa na yi ki faɗa mini tarihin asalin taguwa tun da kin ce ba daga Turawa muka kwaikwaye ta ba.”
Ta ce, “af, an kuwa yi haka. Ai na gaya maka tun kan a haifi uwar mai sabulu balbela take da farinta. Ko da Nasaru suka zo sun iske mu da suturunmu.”
Ta zubar da yawu kana ta ci gaba, “Tun can tale-tale Bahaushe bai da wata sutura da ta wuce mayafin saƙi, shi yake ɗaurawa a ƙugu sannan ya yafa shi saman kafaɗa har ya sauka bisa gadon bayansa. Ana kiran wannan shiga da suna lage. To akwai wani mutum wai shi Guwa wanda mayafi ɗaya kurum gare shi, ko datti mayafin nan nasa ya yi, idan zai wanke shi, sai dai ya yi ƙato-gulbi.
Ana nan har mayafin nan ya kai ga hujewa a tsakiyarsa. Da Guwa ya ga haka, ya rasa yadda zai yi, sai wata dabara ta faɗo masa a rai. Ya ƙuga kansa inda mayafin ya huje, sai ko ya ga ya sauka ya rufe masa jiki kaf. Ya samu ɓawon ice ya yi ɗamara don kada iska ya riƙa ɗage shi. Da ya fita waje mutane suka gan shi, sai suka yi sha’awar shigar da ya yi. Suka riƙa huje mayafinsu a tsakiya suna cewa bari mu yi ta-Guwa, watau irin dabarar Guwa.”
Kaka ta dube ni ta ce, “to ka ji asalin taguwa. Daga bisani kuma aka samu dabarar ɗinke gefe da gefe na mayafin aka daina yin ɗamara. Don haka rigar Bahaushe ta farko ita ce ‘yar shara, wacce ake fid da wuya kawai babu hannuwa. Daga nan Nasaru suka gani su ma suka kwaikwaya.”
Na yi dariya na ce, “ikon Allah, lallai Bahaushe akwai hikima.”
Ta riƙe baki ta ce, “kai ɗan nan, me ka ɗauki Bahaushe hala? Ba ka san cewa asalinsa daga Misira yake ba? Ko ba ka san cewa Misira ce tushen ilmi da wayewar kai a duniya ba? Don haka ba abin mamaki ba ne don Bahaushe ya daɗe da wayewa a duniya.”
Na ce, “toh, ai ni ban sani ba. Amma wata rana zan so na ji wannan tarihi.” Na miƙe tsaye ganin hantsin gwauro ya fara kawo jiki. Muka yi sallama da Kaka, na ba ta na goro na fita. Na bar matan gidan na ɗibar garafuni a jikin damfami, na haye mashin ɗina na nufi gida.
…
Ga ƙarin wasu kalmomin da muke so a gano mana ma’anarsu kamar yadda suka fito a cikin labarin:
1. Saura.
2. Hambama.
3. Tumu.
4. Taure.
5. Takanɗa.
6. Dabi.
7. Karauni.
8. Ƙailula.
9. Idon kwaɗi.
10. Ƙato-gulbi.
11. Hantsin gwauro.
12. Garafuni.
13. Damfami.
Bukar Mada
03/09/2022
#RanarHausa