Waziri aku sai bango ya tsage

Waziri aku sai bango ya tsage

 

 

 

 

 

Karin wasu littafai da zaku so

Powered by: www.mynovels.com.ng
 

 

 

SAI BANGO YA TSAGE…

 

Gardama ta murtuke tsakanin Jaki da Damisa har abin ya kai su ga É“acin rai. Suka yanke shawarar su je gun Manyan Dawa ya raba musu wannan tankiya.

 

Da isarsu sai Jaki ya ce wa Zaki, “Allah ya ba ka nasara don Allah ka raba mana wannan rigima. Na ce wa Damisa ciyawa shuÉ—iya ce, ita kuma ta dage da cewa koriya ce. A cikinmu wa yake da gaskiya.”

 

Zaki ya dubi Jaki ya ce, “kai ke da gaskiya.”

 

Jaki ya yi tsalle ya buga Æ™afa Æ™asa ya fashe da dariya, ya harari Damisa ya ce, “to, ga shi nan, ba ki san komai ba sai rigimar banza.” Ya hura hanci, ya runtuma a guje cikin daji yana hargowa tare da harbin iska cikin farin ciki.

 

Bayan ya tafi sai Damisa ta dubi Zaki ta ce, “Allah ya taimake ka, ciyawa fa koriya ce ba shuÉ—iya ba.”

 

Zaki ya ce, “i, na sani. Ciyawa koriya ce.”

 

Damisa ta ce, “to me ya sa ka ba Jaki gaskiya?”

See also  Guguwar Fansa Hausa Novel Complete

 

Zaki ya ce, “bai kamata ga irinki mai ilmi da kwarjini ki tsaya É“ata lokaci wajen gardama da Jaki, wanda bai san inda kansa ke ciwo ba, ga shi garin sakacinki yana shirin raina ki. Sau da yawa wasu kan dage da gardama, ko da kuwa sun san gaskiya, amma su rufe ido dole dai sai an yarda da abin da suka ce. Babban sakarci kuma shi ne nuna sani a inda jahilci ya yanke cibi.”

 

Damisa ta tafi tana jinjina maganar Manyan Dawa. Ta ga kuma lalle abin da ya faɗa gaskiya ne, sakacinta ya sa Jaki ke son raina ta har yana yi mata dariya. Sai bango ya tsage kadangare ke samun wurin shiga. Ba za ta sake yin sakaci kamar wanda ta yi ba, domin kuwa sakaci ne ya sa injin niƙa ya kwance wa turmi zani a kasuwa.

 

Bukar Mada

03/10/2022

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Scroll to Top